Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Don ya fad'a yana kallan Sameer, d'aga kafad'a Sameer yayi sannan yace

"Bansan ta ba, wadda dae ta shigo sanda muke cikin d'akin.." d'an shiru yayi se kuma can yace

"Meemarh..?"

"Woww.. Suna me dad'i, don Allah ya za'ayi Allah kuwa ni da gaske nake" murmushin gefen baki Don yayi kana yace

"Tsofae tsofae da kae zaka ce kana son yarinya?" ya fad'a cikin basarwa

"Ae shiyasa naga kae ka auri wadda ta girme ka" Sameer ya fad'a yana galla masa harara

"Ohk kar kayi biyayya ka gani" Don ya fad'a yana yamutsa fuska

"Sorry mana Abban Twins mijin Azrah.." ya fad'a yana murmushi, tilas shima seda ya murmusa sannan yace

"Sister'n Azrah ce" d'aga kae yayi ya kalli Don sannan cikin rashin fahimta yace

"Sister'n ta kuma? How?"

"Yeah.. Step sister ba.."

"Ohk, yanzu dae how can i get her contact" Sameer ya fad'a yana kallan Don.



.. Seda Twins suka yi sati 2 sannan akayi suna, wanda Aunty Hindu ce tace gwara ayi tunda dae Azrahn ta samu sauk'i, sunan daya tara mutane da dama, akaci akasha akayi mankas, me jego tayi shiga kala kala ta alfarma.. K'arasawa yayi gaban gadon yana kallan kayan da Sameer ya kawo masa, ya d'aga ya kalla ya sake kalla, ta6e baki yayi gami da d'aga kafad'a ya d'auka ya sanya kayan, k'arasawa yayi yana kallan kansa a mudubi, se yayi murmushi kawae, kayan sun zauna sosae a jikin sa kuma sun masa kyau amma dae shi a wajen sa be gani ba, bashi da wata hula da ake sakawa in an saka manyan kaya kuma Sameer be had'o masa da ita ba dan haka ya k'arasa wajen kayan sa ya d'akko facing cap ya saka akan kwantacciyar bak'ar sumar kansa kana ya d'auki wayoyin sa bayan ya saka takalmin sa ya fice daga d'akin... A sitting room d'in gidan ya zauna yana sake kallan kansa ya d'akko wayar sa ya danna number ta, se a kira na biyu sannan ta d'aga, ya maraeraece murya kamar wani k'aramin yaro yace

"Wato an manta da Dadyn Twins koh?" se tayi murmushi daga inda take zaune kana tace

"A'ah fa ni kam kana mak'ale a rae na, tun d'azu nake tunanin ta ina zaka 6illo" ta maeda masa amsar itama a maraeraece, ya gyara zaman sa sannan yace

"Ohk toh ina sitting room, maza ki sato jiki ki taho"

"Uhmm tohm" ta fad'a, tana shirin katse wayar ta jiyo muryar sa

"Ki taho min da yara na..".. Da k'yar ta samu ta sato jiki daga cikin mutanen, Zarah ta mata rakiya da Twins zuwa k'ofar sitting room d'in sannan ta kar6e su ta shige ita kuma Zarah ta juya tana fad'in

"Kada dae ki dad'e ah toh" bata kula ta ba se murmushin da tayi kawae ta shige dan ta k'agu taga mijin nata, akansa idanun ta suka fara sauka, seta tsaya tana kallan sa yadda yake saye cikin wata dakakkiyar shadda me kyau, a hankali ta cigaba da takawa zuwa cikin d'akin, se a lokacin shima ya k'araso suka had'u a tsakiyar parlourn dan yadda yaga ta sake wani kyau ta kuma murmurewa, cikin wani had'ad'd'en less kamar wata babbar mace, kar6ar Twins d'in dake cikin wani farin towel me taushi yayi wad'anda ke baccin su su duka ya sumbaci goshin su kana ya ajje su kan kujerar, ya k'arasa ya rik'o hannayen ta yana kallan cikin idanun ta

"Kinga yadda kikayi kyau kuwa?" ya fad'a a hankali, seta lumshe idanu kafin tace

"Hala yau baka kalli mudubi ba?" ta fad'a tana murmushi, seya narke fuska yace

"Seda nace miki dama kar na saka, nasan ba kyau zanyi ba" dara daran idanun ta ta bud'e sosae akansa tace

"Kaee..nifa ina nufin saboda kyan da kayi, Allah kuwa kayi kyau sosae" ta fad'a tana had'e babban yatsan ta dana kusa dashi fuskar ta akansa, hannun sa ya saka ya janyo k'ugun ta ya had'e tazarar dake tsakanin su yana cigaba da bin ta da kallo yace

"Ban kae ki ba, ki bari na d'an mori kwalliyar nan" ya fad'a yana bin lips d'in ta da kallo, kukan da d'aya daga cikin yaran ta saka ne ya sanya su duka suka kalle su, kusan a tare suka k'arasa suna kallan su, seya lumshe idanu yana fad'in ganin yarinyar ta koma bacci

"Yaushe zaki dawo ne?" kallan sa tayi idanun ta a bud'e sannan ta d'an tura baki tace

"Se nayi arba'in.."

"A'ah ae kuma baki isa ba" ya fad'a yana 6ata fuska, kallan sa ta cigaba dayi dan se taga ya koma mata Don na wancan lokacin, ya juyo ya jefa mata harara kana yace

"Kamar ma ni kad'ae nayi kewar ki koh?" matsawa tayi kusa dashi sosae kana tace

"Fad'a ma 6ata baki ne.."

"Koh??" ya fad'a dae_dae lokacin da wayar sa tayi k'ara, da mamaki yake kallan me kiran nasa, ya d'aga kae ya kalli Azrah, seta maeda duban ta kan wayar, ta d'an zaro ido kad'an sannan ta kar6i wayar ta d'aga da sallama, daga can 6angaren Meemarh tace

"Hajiya base kin nuna mana so kike mu maeda ki gidan mijin ki ba, za'a maeda ki, toh wallahi kiyi sauri ki d'auko yaran nan ku taho se neman ki akeyi.." yamutsa fuska tayi kafin ta ajje wayar, baya buk'atar jin abinda aka fad'a a cikin wayar dan ya riga yaji, ta mik'e tana shirin d'aukar Twins d'in yace bayan ya rik'o ta

"Lemme kiss dis ur cute lips" ya fad'a yana d'an taune bakin sa, seta zaro ido kafin tace

"Na saka lipstick fa.." bata k'arasa maganar ba ya cafke bakin nata yayi kissing nata na wajen second 20 sannan ya sake ta, ta d'auki Twins d'in ta fice daga d'akin, ya bita da kallo yana jin kamar ya tashi ya bita...


.. Seda tayi kwana 40 cif sannan Ammi ta tattara ta Ummu ta maeda ta gidan ta bayan tasha wani gyara na musamman, Twins kam sun k'ara girma sunyi ku6ul6ul dasu gwanin sha'awa.... Wajen k'arfe 8pm ne ya shigo gidan, tun daga parlour ya tabbatar an dawo masa da matar sa dan wani irin daddad'an k'amshi da yake tashi, kae tsaye d'akin ta ya wuce ya tura k'ofar idanun sa a ciki, tana kan stool d'in gaban mudubi tana k'ok'arin parking d'in gashin ta ya tura k'ofar, seta dakata tana kallan sa ta cikin mudubin, lumshe idanu yayi sanda yake cigaba da takawa zuwa cikin d'akin, sanye take cikin wasu riga da wando wad'anda suka kama jikin ta sosae, tayi wani shahararren kyau, babu 6ata lokaci ya k'arasa inda take ya d'ago ta sannan ya bata wata kyakyawar runguma idanun sa a lumshe yana shak'ar daddad'an k'amshin dake tashi daga ko'ina na jikin ta

"U're welcome.." ya fad'a da wata shak'ak'k'iyar murya, itama rungume shin tayi sosae idanun ta a lumshe, sun kae minti 2 a hakan kowanne yana sauke numfashi a hankali saboda missing d'in juna da suka yi, kafin ya zame ta daga jikin sa yace yana kallan shigar ta lumsassun idanun sa sun sake lumshewa

"Wannan shigar.." ya kasa k'arasawa ya d'an lumshe idanun sa kad'an sannan ya bud'e ya maeda kansa kan wuyan ta ya fara aeka mata da sak'onni masu tsayawa a rae da zuci, kukan da Iffah da Afaaf suka fara kusan lokaci guda ne ya sanya shi sakin ta yana d'an sauke ajiyar zuciya, tare suka k'arasa wajen yaran, ita ta d'auki Iffah yayin da shi kuma ya d'auki Afaaf, ya sake lumshe idanun sa yana jin wani irin farin ciki mara misaltuwa, feeding d'in Iffah ta fara yi, ya dube ta sanda yake fad'in

"Bari naje nayi wanka kafin ki sallame su" ya fad'a da wani k'ayataccen murmushi akan fuskar sa, itama murmushin ta maeda masa kana ta cigaba da kallan sa yana d'an rarrashin Afaaf kafin ta gama da Iffah, seda ta tabbatar Iffahn ta k'oshi sannan ta maeda ta cikin gadon su kana ya mik'a mata Afaaf sannan ya fice daga d'akin... Sanda ya dawo cikin d'akin Twins d'in sunyi bacci tana zaune gefen gadon tana kallan su cike da matsananciyar k'aunar su, ya k'arasa ya rufe musu net d'in sannan ya jata kan gadon zuwa cikin jikin sa

"Uhmm dama inaso muyi magana.."

"Let's talk tomorrow.." ya fad'a yana sake shigar da ita cikin jikin sa, babu 6ata lokaci ya shiga aeka mata da sak'onni cike da kewar ta, itama kuma ta zage tana maeda masa martani dan ita kanta tayi missing nasa sosae, ranar dae sun gwadawa junan su yadda suke k'aunar kansu, se ranar ta sake kasancewa wata ta mussamman a gare su baki d'aya.


... Se wajen k'arfe 10 ta farka sakamakon kukan da yaran keyi, ta bud'e idanun ta tana kallan sa yadda ya sa6a su dukan su a kafad'ar sa yana ta safa da marwa a cikin d'akin, murmushi ne ya su6uce akan fuskar ta dae_dae lokacin daya juyo yana kallan ta, seya sauke ajiyar zuciya yana fad'in

"Maza jeki shirya, azo a sallame mu" lumshe idanun ta tayi sannan ta mik'e ta fad'a toilet tayi wanka kana ta fito ta kalle shi tana dariya ganin har lokacin be zauna ba tace

"Dadyn Twins.." murmushin ya maeda mata sannan yace

"Ke dae ki shirya kawae.." k'arasawa tayi ta shirya cikin riga da skirt na atamfa kana ta kar6i yaran, shi kuma ya zauna yana ta kallan su yana ji kamar ya maeda su ciki.






_BAYAN SHEKARA 5_

Soyayya ce me tsanani ta cigaba da ha6aka a tsakanin Adnan da Azrah, Afaaf da Iffah suna ta girma abin su kullum kuma kyawun su dad'a bayyana yake.. A gefe guda kuma abubuwa da dama sun faru cikin shekarun ciki kuwa hadda auren Sameer da Meemarh yanzu haka ma tana da 'ya'ya 2, Meemee ma tayi auren ta nan cikin garin Kanon haka zalika Zarah ma tayi aure, kuma duk suna da 'ya'yan su suna zaune cikin farin ciki da k'aunar juna, Simrah ta auri wani Alhaji me mata 1 wanda yake son ta sosae, cikin ikon Allah suna zaune lafiya da mijin nata sedae matar sa da kishi ke sakata ta dinga wasu abubuwan da ba'a rasa ba, Azrah ta koma makaranta yanzu haka ma tana shekara ta biyun k'arshe ne a B.U.K, Baban Ilyasu ya rasu tun cikin shekarar da Azrah ta haehu, Inno ta koma garin su, An kawo kud'in Buhaesa yanzu haka ya rage saura sati 2 ayi bikin, Azrah sun cigaba da zumunci da Umma (matar me gari) haka zalika jefi jefi takan ziyarci k'auyen Kima ko dan k'awar ta Hauwa'u wadda yanzu mijin ta ke aeki a companyn Don.. Kullum arzik'in Alhaji Kabeer Tajuddeen ha6aka yake yi, haka zalika shi kansa me gayya me aekin Adnan, cikin ikon Allah daga Company guda d'aya yanzun ya cigaba ya gina kansa yanzu haka Companyn sa 3, Sameer kuwa aboki na gari yana nan tare dashi suna cigaba da gudanar da harkokin companyn a tare..



*** *** ***


.. A hankali ya zuro k'afar sa daga cikin motar sanye cikin wata Ash d'in shadda wadda ta amshe shi sosae, ya sake fari kuma yayi kumari dan idan ba ido na ke gizo ba har k'iba naga yayi, hannun sa ya saka ya zare hular kansa dae_dae sanda wasu kyawawan yara farare tass dasu ku6ul6ul suka taho da gudu sanye cikin uniform hannayen su rik'e da basket

"Daddy..." dukkan su suka fad'a suna rungume Don d'in dake tsaye jikin motar sa, tsugunawa yayi ya had'a su su duka ya rungume sannan ya jasu ya zuba su a front seat kana ya koma driver seat ya zauna ya tashi motar, Afaaf ce ta kalle shi da maganar ta da har yanzun bata gama iyawa ba tace

"Daddy yau mun riga Mommy dawowa?" ya d'an kalle ta da murmushi shimfid'e kan fuskar sa sannan yace

"Ehh yanzu zamu wuce mu d'auko ta.."

"Yess na siyo mata tsaraba har dakae Daddy" ta fad'a tana d'an tsalle daga inda take zaune, kallan Iffah yayi kana ya maeda kansa kan titi yace

"Uhmm kefah? Waya ta6a min ke?" rufe baki Afaaf tayi tana dariya sannan tace

"Daddy..wata k'awar mu ce tace wae nafi Iffah kyau" bud'e idanu yayi yana kallan Iffahn dake ta wuwwulgawa Afaaf ido ita a lallae dole harara take yace

"Kwantar da hankalin ki kinji Mum d'ina"

"Kuma Daddy ae dae na fita kyau koh?" Iffahn ta fad'a kamar zatayi kuka

"Dukkan ku kuna da kyan ku" ya fad'a yana murmushi dae_dae lokacin da yayi parking a wajen da Azrahn ke jiran su, dan baya yadda wani ya d'auko masa mata, ya gwammace kome yake yi ya taso ya d'auke ta.. Sanye take cikin doguwar rigar atamfa da mayafin ta wanda ya rufe jikin ta sosae, kanta yasha d'aurin ture kaga tsiya ta yafa mayafi akanta, hannun ta d'auke da wasu littafae yayin da take saye da jakar goyo me kyau, a hankali ya sauka ya bud'e mata front seat d'in, kamar yadda ya tsammata dama yasan yaran ba zasu koma baya ba sedae duk su baebaye ta anan d'in, ta sakar masa tattausan murmushi sanda take shiga cikin motar kana ya rufe ya koma ya tashi motar

"Gud evening Mummy" suka had'a baki wajen fad'ar hakan, kowaccen su ta kama kumatun ta tayi kissing sannan tace

"Kuna lafiya?" tuni Afaaf ta kwanta a jikin Azrahn dan dama tafi Iffah k'ulafucin uwar, yayin da Iffahn gaba d'aya wani miskilancin uwa da uban ta had'a ta d'auko har rashin surutun

"Uhmmm shagwa6a66iya tah yau kuma me aka miki?" Azrah ta fad'a tana shafa kan Iffah da itama ta kwantar da kanta a kafad'ar Azrahn, kafin Iffahn tace komae ta jiyo nutsattsiyar muryar sa yana fad'in

"Madam ya karatun?" ta lumshe idanun ta sannan tace

"Alhamdulillah.."

"Mummy anyi test d'in fa" Afaaf ta fad'a bayan ta d'aga kae ta kalli Azrahn, kumatun ta ta d'an ja sannan tace tana kallan su su duka

"Toh ya test d'in?" tashi zaune Iffah dake kan kafad'ar ta tayi tace

"Mummy Allah kuwa na fad'a miki nafi Afaaf k'ok'ari.." itama tashi zaune Afaaf d'in tayi tana ta6e baki da fuska kamar zata saka kuka

"Daddy wae haka?" ta tambaya kamar zatayi kuka, idan zasu biyewa wad'annan yaran se su kwana suna abu d'aya dan haka kamar koda yaushe yanzu ma se cewa yayi

"Dukkan ku kuna da k'ok'arin ae, ba kiga position d'aya kuke d'auka ba?" se tayi murmushi tana yiwa Iffah gwalo, da wannan suka isa gida yaran nata musu hira, duk da rabin hirar Afaaf ke yin ta se idan ta ta6o Iffahn sannan seta saka baki... Suna isa gida kae tsaye d'akin yaran ta wuce dasu ta taemaka musu dukan su suka cire jaka da takalmin sannan ta musu wanka ta shirya su cikin wasu had'ad'd'un dogwayen rigu na sannan ta sanya su suka fito da littafan da aka basu assignment zuwa parlourn ita kuma ta wuce kitchen ta d'ora girki sannan ta koma cikin d'akin, yana zaune kan gadon ganin ta ya sanya shi mik'ewa yana fad'in

"Babe ke nake kira fa tun d'azun" murmushi tayi sannan tace

"Na tsaya rage wani abun ne a kitchen"

"Ohk let's go, na had'a ruwan wanka.." ya fad'a yana d'aga ta gaba d'ayan ta zuwa toilet d'in. Tare suka shirya sannan suka fito a tare zuwa parlourn, ita ta wuce kitchen yayin da shi kuma ya wuce masallaci dan lokacin maghrib ya gabato... Seda yayi sallahr isha'i sannan ya dawo, da gudu suka taso sukayo kansa suna fad'in

"Oyoyo Daddy" sunkuyawa yayi ya rungume su sannan ya jasu zuwa cikin d'akin, yana kallan yadda har lokacin littafan ke akan kujera, da mamaki ya kalle su yace

"Har yanzu baku gama ba?"

"Daddy Afaaf ce tace muyi kallo kafin ka dawo" kallan TVn dake a kunne yayi, ya mik'e ya kashe ta sannan ya dawo ya zauna k'asan carpet d'in yace

"Oh yah ku sauko.." babu musu suka sauko kowaccen su ta tankwashe k'afa rik'e da pencil d'in ta a hannu, shiya koya musu assignment d'in duka, suna zaune suna jiyo k'amshin girkin Azrah dake ta tasowa daga kitchen zuwa parlourn, suna kan na k'arshe Azrah ta fara fitowa da warmers d'in data kwashe abincin a ciki, ta k'araso ta ajjiye su kan carpet d'in sannan ta koma ta kwaso ragowar kana ta dawo ta zauna

"Sannu Madam" ya fad'a a narke, d'aga ido tayi ta kalle shi sannan tace

"Yawwah Abbun Twins, an gama Assignment d'in ne?"

"Ehh Mummy an gama" Afaaf ta fad'a tana kallan Azrah

"Ohk toh maza ku maeda cikin jaka, ku fito muci abinci.." dukkan su suka mik'e da gudun su zuwa cikin d'akin da littafan a hannun su, ya matsa kusa da ita ya janyo ta cikin jikin sa, zaro ido tayi tana fad'in

"Yanzu zasu fito fa.."

"D'umin mata ta nake son ji yanzun"

"Kae Babe" ta fad'a tana kallan yadda yake bin lips d'in ta da kallo, aekuwa bata rufe baki ba se gasu sun fito, yayi saurin sakin ta, Allah yaso hankalin su baya wajen dan haka basu gansu ba suka k'araso wajen suka zauna, Azrah tayi serving nasu a plate d'aya suka ci abincin cikin farin ciki sannan suka kora da sassanyan fruity zo6o d'in data had'a musu.. Seda suka d'an dad'e a parlourn suna hira sannan Azrah ta kalli Twins tace

"Oh yah, time for sleep.." tare suka tashi suka k'arasa wajen Don ya rungume su kana ya basu kiss a goshin su yace

"Asuba ta gari"

"Seda safe Daddy" suka had'a baki wajen fad'in hakan sannan suka yi gaba zuwa cikin d'akin su, kowacce ta haye kan gadon ta me kyau sannan Azrah ta k'arasa ta musu Addu'a sosae kana tayi kissing nasu su duka sannan taja musu blanket tace

"Ayi bacci lafiya.." ta fad'a da murmushi kan fuskar ta

"Mummy goben zamu je gidan Aunty Meemarh?" Afaaf ta fad'a tana kallan Azrah, murmushi Azrah tayi dan tasan tunda ta fad'a d'in nan seta cika dan haka tace

"Ehh yanzu dae kiyi bacci Uhmm?" ta jinjina kae tana rufe idanun ta, daga haka ta mik'e ta kashe fitilar d'akin kana ta koma d'akin ta. Yana zaune kan gadon yayi shirin bacci, ta k'arasa ta hau kan gadon, babu 6ata lokaci ya jata cikin jikin sa yana fad'in

"Sunyi baccin?" gyara kwanciyar ta tayi akan faffad'an k'irjin sa sannan tace

"Ehh.."

"Ohk nima yanzu aeki na ne na saka ki kiyi bacci" ya fad'a yana sake rik'e ta sosae, murmushi tayi tana lumshe idanun ta tace a hankali

"Abbun Twins ina k'aunar ka.." bud'e ido yayi kafin ya d'an lumshe su kad'an yace

"Nima haka Momyn Twins Allah yayi miki albarka.." ya fad'a yana kae bakin sa kan goshin ta yayi kissing nata a nutse sannan yace

"Oh yah Sleep.." ta sake lumshe ido tana kuma zagaye hannayen ta a bayan sa, ya kuma gyara mata kwanciyar kana ya d'ora kansa akan kwantacciyar sumar kanta dake kan k'irjin sa...


_Haka rayuwar su ta cigaba da kasancewa cikin farin ciki da k'aunar juna, kullum kamar ana sabun ta musu k'aunar junan su ne, haka kowannen su naji tamkar yafi d'an uwan sa k'aunar d'an uwan sa_

*GAME OVER!!!* πŸ”₯

_*ALHAMDULILLAH ! ALHAMDULILLAH !! ALHAMDULILLAH !!!*_

*AZAAD*

_*ANAN NA SAUKE WANNAN LITTAFIN NAWA ME SUNA SANADIN KADDARA TA, ABINDA NA RUBUTA DAEDAE ALLAH YA HAD'A MU A LADAN, ABINDA NAYI KUSKURE KUMA ALLAH KA YAFE MIN, GODIYA TA MUSAMMAN A GARE KU EN SANADIN KADDARA TA PAID GROUP MUSAMMAN MA*_

1_Kulsum
2_Queen
3-Beauty and wellness by Ayush
4_Phauzerh A mumin
5_Gilimah
6_A'isha Sabo
7_Aisha Usman Zakari
8_Jamilahmuhammadbello
9_Q pretty
10_Mmn Humaera
11_Humaera Bashir
12_Amwal
13_Maman shureim
14_Yar amana
15_Rukayya Yahuza
16_Maman fadeelah
17_Princess Autarh
18_RCHP fateema Zarah
19_Khadijart
20_Deejah
21_Hindatu
22_Uwar alkhaeri
23_Hapseenart
24_Maeeshart
25_Mhiz Umcy
26_Good Muslim Ambassador
27_Rukayya UST
28_Darling Fee
29_Shafa'atu Bello
30_Rukayya Rabi'u
31_Maryam Garba Hamisu

_*Da sauran wad'anda ban lissafo ba, ku sani ina qaunar ku one thousand, kada fa ki zaci dan ban saka sunan ki ba ban dake a'ah Ina qaunar ku dukan ku kawae dae sunan wad'annan d'in ne yazo min, nasan ran wata nacan yana 6aci toh lemme mention ur name Fatima Aliyu Rabi'u*_
_*Ba dan halin ki ba*_πŸ˜—πŸ˜

_*ALLAH YA BAR ZUMUNCI YA K'ARA MANA HAK'URI DA JUNA, I HEART U ALL πŸ₯ΊπŸ–€*_



_*Godiya ta musamman zuwa ga Uwa ta ta kaena Maama na wadda kullum itace ke qara bani support da shawarwari akan rubutun da nake πŸ₯ΊπŸ˜© Allah ya qara miki lpia d nisan kwana me amfani πŸ₯° Abba na Allah y qara maka lpia d arziqi me amfani πŸ–€*_

_*En uwana rabin jiki na kuma Yaya, Abdoul, Mubarak, Faruk, Kauthar, Allah ya qara mana hadin kae da qaunar juna πŸ₯Ί*_

Aunty Meemarh
Aunty Sadiya
Mum Sayyid
Aunty A'isha
Sarki Sameer

*Kuma ina gaeshe ku one thousand*πŸ˜©πŸ–€



_*Idan da wadda na ta6a yiwa laefi tun fara SANADIN KADDARATA har zuwa gamawar sa Ina neman afuwar ta, ni kam na yafe muku idan ma an min laefin kenan, ban ta6a yin magana akan masu fitar da littafi ba bare har nakae ga Allah ya isa dan gani nake kamar 6ata lokaci ne, kawae dae abinda zance yanzun shine pls ku dinga barin mutane suna patronizing d'in mu, idan mutum yana son littafin ya saka kud'i ya siya...*_

_*Don neman qarin bayani, sharhi ko qarin haske za'a iya tuntu6ata ta wannan number*_
_*08124818273*_

_*Se mun had'u cikin sabon littafi na wanda ze fara zuwar muku nan ba da dad'ewa ba me suna ZAZZAFAR K'AUNA πŸ₯Ί*_


*SUBHANAKALLAHUMMA WA BI HAMDIKA ASHHADU ALLA ILA HA ILLA ANTA ASTAGFIRUKA WA ATUBU ILAEKA*...

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment