You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
kae ta kalle shi sannan tayi saurin d'auke kan ta, ya k'arasa yaja stool ya zauna sannan yace yana kallan ta
"Gobe idan Allah ya kaemu zamu je Sudan k'asar su Mom, ki shirya kaya kamar kala 5 haka Uhmm?" A hankali ta furta
"Toh.." ya kalle ta ganin bata tashi ba seya mik'e yace
"Bari na had'a miki" da sauri ta d'aga kanta ta kalle shi tana shirin yin magana se tsintar sa tayi a gaban wardrobe d'in ta ta ya bud'e ya fara hautsino kayan ciki, yana ware wad'anda zata tafi dasu d'in a gefe guda yayin da yake maeda wad'anda basu masa ba, seda ya gama sannan ya bud'e wani 6arin, daga inda take zaune ta zare ido ganin yadda ya fara ciro pant da sharbale d'in ta (u gerrit ba🤐🥱), idanun ta suka ciko taf da k'walla
"Guda nawa zan d'aukar miki?" Ya fad'a yana k'ok'arin juyowa, babu shiri ta mik'e ta gudu ta fad'a cikin toilet, ya bita da kallo yana sakin wata miskilar dariya
"Zan cire miki wannan kunyar da tsoron soon.." ya fad'a yana taune lips d'in sa na k'asa.
...K'arfe 11:30 agogon k'asar Sudan d'in suka sauka a cikin k'asar, k'ofar gidan Alhaji Mas'ud wato mahaefin Mom kenan, da tare da Fawaz zasu zo amma saboda makaranta yasa suka barshi a gida, wanda ya kawo su shine ya shiga cikin gidan ya musu iso zuwa wajen dattijon Alhaji Mas'ud, a babban parlourn gidan nasa akace su shiga, Alhaji Mas'ud na zaune akan kujera shi da er sa Hindatu (k'anwar Mom) wadda kafatanin en gidan ke kira da Aunty Hindu, ta kalle shi tace
"Papi bari na koma ciki, idan bak'in naka sun tafi sena dawo" girgiza kae Papi yayi sannan yace
"A'ah yi zamanki Hindatu, nasan kowanne irin bak'i ne ba dad'ewa zasuyi ba saboda haka ki zauna suna tafiya semu k'arasa maganar mu"
"Toh Papi" ta fad'a dae_dae lokacin da sallamar su Dad ta shigo cikin parlourn, gaba d'ayan su suka d'aga kae suka kalli masu sallamar, akansa idanun ta suka fara sauka ta mik'e a razane tana kallan sa sannan cikin rawar murya tace
"Ad..nan.." inda yaji sunan nasa ya fito nan ya d'aga kae ya kalla, d'agowar da yayi ya sake bawa Aunty Hindu tabbacin Adnan d'in su ne d'an Aunty Sa'adatun su, dan haka babu 6ata lokaci ta k'arasa inda yake da sassarfa ta rungume shi tana sakin kuka me cin rae, Papi ya kalli Dad daya k'araso ya zauna k'asan kujerar da yake, yayin da Azrah ke tsaye ta rasa inda zata zauna, sun kae kusan minti 1 a haka sannan Aunty Hindu ta sake shi sedae har lokacin hannun ta na rik'e da nashi hannun ne, se a lokacin ta lura da Azrah dake tsaye ta kalli Don dake kallan Azrah tace a hankali
"Kayi aure ne?" Ya jinjina mata kae a nutse, seta saki hannun sa ta k'arasa ta kamo hannun Azrah tana fad'in
"Oyoyo taho ki zauna kusa dani kinji!" Ta fad'a dae_dae sanda ta k'arasa da ita kan kujerar data ke kae tace
"Zauna kinji..gata kuma kyakykyawa tubarkallah" ta k'arasa maganar tana kallan Don, murmushi kawae yayi sannan ya kalli Papi da tun d'azu shima shi d'in yake kalla, seya mik'e ya k'arasa ya zube kusa da Dad dake fad'in
"Mu d'in ne dae ranka ya dad'e.."
"Barka da wannan lokaci" Don ya fad'a, se a lokacin Papi yace
"Barkan ka dae Adnan, kaema se yau ka tuna damu?" Shiru yayi bece komae ba se Dad ne yace
"Ayi mana afuwa yalla6ae, mun san mu masu laefi ne dogon labari ne amma dae tunda gamu munzo da kanmu muna fatan za'a mana uzuri" jinjina kae Papi yayi sannan ya kalli Aunty Hindu yace
"A basu masauki idan sun huta zamu yi magana" Aunty Hindu ta saki hannun Azrah dake cikin nata sannan ta mik'e tana goge idanun ta da k'walla ta kasa tsaya mata, fita tayi daga d'akin babu jimawa suka shigo tare da wani yaro da baze wuce 10yrs ba tace tana kallan Don
"Ka kae yayan ka part d'in su Ahmad, ka kar6i mukulli a hannun Amma" da "toh" yaron ya amsa, sannan ta kalli Don tace
"Adnan tashi kaje ze raka ka inda zaka zauna kayi wanka ka huta" bece komae ba ya mik'e ya d'an saci kallan inda take kanta na k'asa ne dan haka bata san ma ya kalle ta ba, seya bi bayan yaron suka fice daga d'akin, se a lokacin tayi murmushi tana kallan Dad tace
"Barkan ka da zuwa, kunzo lafiya?" Papi ne ya amshe zancen da fad'in
"Se yanzu kika ganshi kenan? Bayan kin nuna bama ki ganshi ba saboda farin cikin ganin d'anki" ya k'arashe maganar da murmushi kan fuskar sa, itama murmushin tayi sannan ta koma inda Azrah take bayan Dad ya amsa gaesuwar ta ta, ta kalli yadda Azrah d'in duk ta kasa sukuni tace
"Tashi muje kema ki huta kinji?" Babu musu ta mik'e tabi bayan Aunty Hindun, basu fita daga d'akin ba seda ta k'arasa suka gaesa da Papi, ya amsa mata cikin sakin fuska sannan suka fita daga d'akin, kae tsaye wani parlour suka isa wanda mutane da dama ke cikin sa, wasu na kallo wasu na danna waya wasu kuma na wani abun dae, da sallama suka shiga parlourn, duk se kallan su ya koma kan bak'uwar fuskar da suke gani, babu 6ata lokaci Aunty Hindu tace
"Yau Adnan d'in Aunty Sa'adatu yazo cikin gidan nan, ga matar sa nan" idanu suka sake dawowa kan Azrah sannan wata tsohuwa dake kan kujera tace
"Wae don Allah da gaske kike Hindatu?"
"Wallahi kuwa Amma da gaske, yanzu haka yana sashin su Ahmad ze huta ne kafin yazo ku gaesa" wata daga cikin en mata biyun dake cikin parlourn tace
"Woww, dama ni ban ta6a ganin sa ba se a hoto, yau dae zanga favourite d'in Aunty Hindu" ta fad'a tana k'arasowa inda Aunty Hindun take tana kallan Azrah tace k'asa k'asa
"She's beautiful" murmushi Aunty Hindu tayi sannan taja Azrah zuwa gaban Amma (kishiyar babar su dan mahaefiyar su ta dad'e da rasuwa), Azrah ta zube tana fad'in cikin sanyayyiyar muryar ta
"Barka da wannan lokaci"
"Barkan ki dae en nan meye sunan naki?"
"Azrah..." Ta furta shima a hankali, dukkan su seda suka maemaeta sunan kafin Aunty Hindu tace
"Suna me dad'i.. Amma bari na kaeta d'aki na tayi wanka ta d'an huta zuwa anjima" ta fad'i maganar lokaci guda
"Toh ba damuwa" Amma ta fad'a sannan Azrah ta mik'e suka wuce tare da Aunty Hindun zuwa cikin wani bedroom, Aunty Hindu ta kalle ta tace
"Kiyi wanka zan d'an fita in dawo"
"Toh" ta amsa tana jinjina kae, seda Aunty Hindun ta fita sannan ta bud'e akwatin kayan ta ta d'auki wata doguwar riga da mayafin ta kana ta fad'a toilet tayi wankan ta shirya a ciki sannan ta fito ta nemi waje a k'asa ta zauna, tana nan zaune kafin kace mene aka fara shigo mata da abinciccika kala kala haka lemuka ma kala kala, sannan mutane da dama se shigowa suke yi suna ganin ta sannan su fita, ita dae gaba d'aya ta kasa sukuni cikin d'akin har zuwa lokacin da Aunty Hindu ta shigo, ta kalli abincin sannan ta kalli Azrah tace
"A'ah mezan gani? Ya naga baki ta6a komae ba?" Se tayi k'asa da kanta tana wasa da k'asan mayafin ta, Aunty Hindu tayi murmushi yarinyar na sake burge ta tace
"Kiyi hak'uri kici kinji? Yanzu haka Adnan suna d'akin Papi suna tattaunawa amma In Sha Allah zuwa anjima kad'an zaki ganshi" wayyo Allah kunya, seta sake yin k'asa dakae tana jin wata matsananciyar kunya na lullu6e ta, ita sam ba abinda ya hanata cin abincin ba kenan, kawae dae ta kasa sakewa ne, bata san sanda ta janyo wani plate ba da aka yanka fruit a ciki ta fara ci har lokacin ta kasa d'aga ido ta kalli Aunty Hindun, ganin da tayi ta fara ci yasa ta bar mata d'akin dan ta samu taci ko yaya ne.. Basu suka shigo cikin gidan ba se dab da maghrib suka shiga suka gaesa da Amma sannan Don ya gaesa da cousin sis and brothers d'in sa wad'anda be san su ba, ba laefi ya d'an saki jiki sun gaesa amma daga nan be biye musu ba duk da yadda suke ta k'ok'arin jansa da hira, shi kam gaba d'aya hankalin sa na kan Inda ze gano ta amma har suka bar part d'in be ganta ba.... Wajen k'arfe 8pm ne dae_dae lokacin data idar da sallahr isha'i Aunty Hindu ta shigo d'akin, ta kalle ta sanda take k'ok'arin ninke dadduma tace
"Yawwah, gama shiryawa kizo ki kaewa Adnan abinci" tsayawa tayi da ninke daddumar kafin ta k'arasa ta ajje ta sannan tace
"Na gama" kallan ta Aunty Hindu tayi sannan ta d'an yi murmushi tace
"Ko dae in baki waje ki shirya ne?" Bata san sanda ta kulle idanun ta da hannayen ta ba tace kamar zatayi kuka
"Allah kuwa ni a'ah" murmushin itama Aunty Hindun tayi sannan tace
"Ohk toh wuce muje kitchen na d'aukar miki" tare suka fita zuwa kitchen d'in... A hankali ta tura k'ofar d'akin da sallama a bakin ta sannan ta tsaya, daga inda yake zaune yace
"Shigo" seta shigo cikin nutsuwa zuwa cikin d'akin, idanun sa dake a lumshe ya sake lumshewa yana k'ara shak'ar k'amshin da hancin sa ya zuk'o masa, seya bud'e idon da sauri se kuwa ya sauke su a kanta sanda take k'ok'arin ajiye babban plate d'in a k'asan carpet, besan sanda wani k'ayataccen murmushi ya wanzu akan kyakykyawar fuskar sa ba, ba tare data kalle shi ba tace
"Ina yini?" Kallan ta yayi yana nazarin ta na wasu lokaci, ya zama dole ya koya mata yadda ya kamata ta dinga gaeda miji, dan shi sam wannan gaesuwar ta ta bata masa ba amma seya basar a hankali ya fara mik'ewa sannan lokaci d'aya yana fad'in
"Lafiya ta k'alau ya mantawa dani kuma?" Seta ji wani banbarakwae dan haka ta d'an d'aga kanta ta kalli inda yake, shima ita yake kalla seya d'an karyar dakae yana kanne mata idanu, da sauri ta janye idanun ta tana jin wani iri, k'arasawa yayi wajen k'ofar da mukulli a hannun sa yana k'ok'arin zurawa dan kulle k'ofar saboda yayi kewar matar sa na kwana biyun nan, yau so yake ya kwanta gashi gata, wayar sa dake ajje kan kujera ta fara ruri, seya dakata da kullewar ya k'arasa ya d'auki wayar sannan ya dawo inda ta mik'e da alama fita zatayi, bata yi tsammani ba se jinta tayi cikin jikin sa ya rungume ta ta baya lokaci d'aya kuma yana amsa wayar idanun sa a lumshe, jin tana k'ok'arin zame jikin ta ya sanya shi sake rik'e ta sosae yana cigaba da amsa wayar, Sameer ne suna magana akan ginin daya d'ora shi akae kafin su taho Sudan d'in, se daga baya sannan suka fad'a kan hirar company, magana ta k'arshe da Sameer d'in yayi itace
"Pls ka duba takaddar idan tana cikin kayan daka taho dasu se kamin snapping ka turo min"
"Ohk" ya fad'a yana sassauta rik'on da yayi mata, sannan a hankali ya sake ta yana fad'in
"Am coming pls.." ya fad'a yana shigewa cikin bedroom, ajiyar zuciya ta sauke sannan tayi sauri ta k'arasa ta bud'e k'ofar ta fice daga d'akin, kae tsaye ta koma part d'in da aka sauke ta a ciki, cikin ikon Allah bata samu kowa a parlourn ba dan haka da sauri_sauri ta shige cikin bedroom d'in ta haye kan gadon tayi kwanciyar ta tana rufe idanun ta, bata dad'e da kwanciyar ba taji alamar shigowar mutum d'akin, seta sake runtse idanun ta tana rik'e blanket d'in sosae, murmushi Aunty Hindu tayi dan daga ganin yadda eye lashes d'in ta ke motsi ansan ba baccin gaske take yi ba, seta girgiza kae tana ficewa daga d'akin, bata tsaya ko'ina ba se part d'in da aka sauki Don, ta tura ta shiga da sallama, baya cikin parlourn da alama yana bedroom, dan haka ta nemi waje ta zauna tana jiran sa, wajen minti 5 se gashi ya fito, da mamaki yake kallan Aunty Hindu tunda shi dae yasan ba ita ya bari cikin d'akin ba, Amma seya k'araso kawae ya zauna kan kujerar dake facing nata, kafin yace komae Aunty Hindu tace bayan ta kalli abincin dake k'asan carpet
"Ashe an kawo maka abincin?" shima kallan abincin yayi sannan yace
"Ehh" gyara zama Aunty Hindu tayi sannan tana kallan sa tace
"Tambayar ka nake so nayi, ina fatan ba zaka 6oye min komae ba?" seya kalle ta kawae, besan me zata tambaye shi akae ba amma yana mata kallan Mom ne dan haka ya gyad'a kae kawae
"Gud.. A'ina kuka had'u da matar taka?" cikin rashin fahimta yake kallan Aunty Hindun, fahimtar hakan ya sanya ta fad'in
"Is ohk.. Nasan wannan sirrin ku ne amma ka fad'a min kana k'aunar ta?" ya lumshe idanun sa yana jin wannan tambayar ae kamar ta raenin hankali ce, itama ta 6angaren ta kuma bata buk'atar amsa daga bakin sa yanayin sa kad'ae ya bata amsar tambayar ta dan haka tace
"Ita kuma fa?" seya d'an yamutsa sumar kansa sannan ya girgiza kae yana 6ata fuska
"I don't even know, but ina k'ok'ari wajen sanin hakan beside koma dae menene ya faru is my fault amma I regret it wallahi nayi danasani kuma na bata hak'uri" ya k'arasa fad'a a maraeraece, murmushi Aunty Hindu tayi sannan tace
"Ohk kada ka damu, ka bud'e kunnen ka da kyau kaji abinda zan fad'a maka, indae kabi In Sha Allah ina me tabbatar maka komae zezo da sauk'i" ta fad'a tana sake gyara zama, nan dae suka tattauna sosae kafin ta baro d'akin..
.... Washe gari da safe wajen k'arfe 7 ta gama gyara d'akin tass sannan ta nemi waje ta zauna, se taji kamar idan ta fita ta gaesa da mutanen gidan hakan zeyi kyau, dan haka seta mik'e ta fita daga d'akin zuwa cikin parlourn, kamar jiya yau ma da yawan su cikin parlourn yara da manya, tsohuwar jiya yanzun ma tana zaune kan kujera, ta k'arasa a hankali ta tsuguna a k'asa sannan tace
"Ina kwana?"
"Lafiya k'alau, kin tashi lafiya? Ya kwanan bak'un ta?" seta d'an yi murmushi sannan tace
"Alhamdulillah" yaran dake cikin d'akin suka dinga zuwa suna tsugunawa har k'asa suna gaeshe ta, sannan en matan kuma suka gaesa, seta cigaba da zama duk da a takure take amma ta cigaba da zama tana kallan yadda familyn ke rayuwar su cike da nishad'i da kuma k'aunar junan su, se taji sun burge ta sosae, dan haka ta cigaba da zama, Amma ce ta kalli d'aya daga cikin en matan tace
"Aleena ke kam kije ki kamawa Abida aekin nan mana, kika bibiya aekin ya cakud'e mata shiyasa har yanzu shiru" babu musu ta mik'e zuwa kitchen d'in dake cikin parlourn, babu dad'ewa yaran cikin parlourn suka dinga mik'ewa zuwa kitchen suna fitowa da kayan break, tana nan zaune Amma na d'an saka ta cikin hirar su sega Aleenan ta fito daga kitchen ta matso kusa da ita ta ajje mata nata abin karin, sannan ta koma cikin en uwan ta, ba zata ta6a iya ci ba dan haka ta cigaba da kallan T.V kawae, har zuwa sanda Aunty Hindu ta shigo d'akin ta kalle ta tace
"A'ah Azrah ya naga haka?" seta sake yin k'asa da kanta kawae tana d'an murmushi, Aunty Hindu ta kalli Ruma tace
"D'auki ki kae mata d'aki, may be tafi sakewa taci a can" mik'ewa wadda aka kira da Ruman tayi ta d'auki abincin ta wuce d'akin, Aunty Hindu ta cewa Azrah
"Toh kije kinji?" hakan ya mata sosae dama kuma ta gaji da zaman dan haka ta mik'e tabi bayan Ruman zuwa cikin d'akin, seda ta ajje sannan ta juya zata tafi tace
"Auntyn mu idan kin gama seki fad'a azo a kwashe kwanukan" murmushi tayi dan komae suka yi burgeta suke yi, daga ganin Ruman tasan ta girme mata amma ta kira ta da Aunty, se tace
"Toh nagode" Ruman ta fita ita kuma ta nemi waje ta zauna, babu laefi taci abincin seda ta gama sannan ta killer ragowar a gefe guda.... Wajen k'arfe 3pm ne tana zaune cikin d'akin Ruma tayi sallama, ta amsa mata tana wanzar da murmushi kan fuskar ta, Ruma tace
"Wae ki fito ayi hira.." da "toh" ta amsa dama da hijab a jikin ta kawae seta bi bayan Ruman suka fito zuwa parlourn, tun data fito ta hango shi zaune kan kujera one sitter, yayin da Aleena ke kan d'ayar one sitter d'in dake kusa da tashi, hira suke sosae kamar ba Don ba, haka kawae taji k'irjin ta ya buga amma ta maze suka k'arasa zuwa cikin parlourn ta nemi waje kan kujerar ta zauna dan babu babba a wajen su kad'ae ne se yara dake ta kallan su wasu kuma na wasa, duk da fitowar ta hakan be hana su cigaba da hirar su ba seka rantse dama akwae wani sabo me kyau a tsakanin sa da Aleenan, daga inda take duk ta kasa sakewa dan tana jin idanun sa a kanta amma duk da haka hirar su suke yi, zata iya cewa tunda take bata ta6a ganin yana hira kamar haka ba, seta lumshe idanu tana jin yadda bugun zuciyar ta ke k'aruwa, tayi tayi ta jure ta cigaba da zama amma ta kasa, ba tare data cewa kowa komae ba ta mik'e jikin ta na rawa ta bar d'akin, ya bita da kallo yana jin tamkar ya mik'e ya rungume ta amma ya basar.. Koda ta koma d'akin kwanciya tayi ta lumshe idanun ta tana so kada wani abu ya d'arsu a ranta ko kuma ta manta da sha'anin sa amma ta kasa, bata san meyasa kawae take jin wani irin zafi a cikin zuciyar ta ba, haka dae tayi watsi da komae dan ta samawa kanta salama.... Kamar jiya yau ma tana idar da sallahr isha'i Aunty Hindu ta shigo d'akin ta kalle ta tace
"Yawwah na shirya miki abincin suna parlour kije ki kae masa" kamar tace base ta kae ba ko kuma wani ya kae masa amma ba zata iya fad'ar hakan ba dan haka seta amsa da
"Toh.." ta fita daga d'akin ta d'auki abincin zuwa part d'in da aka sauke shi, haka kawae tunda ta durfafi sashen take jin wani irin haushin sa da bata san dalili ba a haka har ta k'arasa k'ofar d'akin, sa6anin jiya yanzun k'ofar a bud'e take dan haka ta tura kanta da sallama a bakin ta zuwa cikin parlourn, ya amsa mata yana kallan ta sosae hadda lumshe ido, ba tare data kalle shi ba ta k'arasa ta ajje abincin sannan tace har lokacin tana a tsugune bata zauna ba sannan kanta na a k'asa
"Ina yini?" daga inda yake zaune k'asan carpet d'in ya amsa mata da
"Lafiya k'alau.. Kina lafiya?" ba tace komae ba, tana shirin mik'ewa sallamar Aleena ta karad'e parlourn dukkan su suka d'aga kae suna kallan ta tana sanye cikin riga da skirt na wani yadi da mayafi hannun ta d'auke da flask d'in abinci ta k'araso ta zauna tana kallan Azrah tace bayan ta ajje kayan hannun ta
"Laaa, Aunty Azrah ashe kin riga ni?" ta fad'a da murmushi kan fuskar ta, d'auke kae tayi ba tare da tace komae ba, tana jin yadda ranta ke sake 6aci
"Yaya Adnan bari ni na tafi, tunda ga Aunty Azrah tazo" ta fad'a tana kallan Azrahr da kanta ke k'asa
"Ohk" ya fad'a gaba d'aya hankalin sa akan Azrah, seda ta fita daga part d'in sannan ya d'auki wayar sa yana satar kallan Azrahn ganin hankalin ta baya wajen ya sanya shi kara wayar a kunnen sa, ya d'an yi jimm na wasu sakanni sannan yace a hankali
"Ina fatan dae ba fushi kikayi ba?" ya d'an yi shiru har lokacin idanun sa na kanta sannan yace
"Ohk toh godiya da abin arzik'i" ganin har lokacin tak'i kallan sa ya sanya shi zame wayar daga kunnen sa sannan ya sake zube k'wayoyin idanun sa a kanta yace bayan ya lumshe idanu
"I love u.." yanzu kam ta kasa rik'e kanta ba tare data sani ba wani irin kuka da gudu ya k'wace mata aekuwa ta shiga rerashi, daga inda yake ya saki wani miskilin murmushi kana ya sake lumshe idanun sa yana jin wani irin yanayi cikin zuciya da gangar jikin sa, a hankali kuma kukan da take ya cigaba da ratsa dodon kunnen sa seya bud'e idanun sa da sauri kana ya taka zuwa inda take.........
✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION57*
___ya rik'o ta cikin jikin sa, ta fara k'wace jikin ta tana cigaba da kukan me cin rae, ya sake rik'e ta sosae yana sake shigar da ita jikin sa yadda bama zata samu damar k'wacewar ba, yana jin ta tana kukan be hana ta ba sedae ya rasa ma ta ina ze fara rarrashin ta, wannan kukan nata d'aga masa hankali yake yi, toh me zece mata? Da wane kalmomi zeyi amfani wajen kare kansa, seda ya d'an lumshe idon sa sannan ya fara magana a hankali
"Kiyi hak'uri kiyi shiru ki saurare ni" ya fad'a sanda take sheshshek'a, bata san me kuma zece mata ba bayan ta kamashi dumu_dumu yana waya da wata har yana fad'a mata cewar yana sonta, toh meye amfanin cigaba da zaman su, yasan dama yana da wadda yake so meyasa be aure ta tun farko ba, dan ya sake tabbatar mata da rashin muhimmacin ta shine ma yake wayar akan idanun ta, se kuma yazo ya dinga mata dad'in baki, ta sake runtse ido tana jin wasu sabbin hawayen na zubo mata, yana jin yadda hawayen nata ke zuba akan rigar sa, yace akan la66an sa
"Oh god" ya fad'a yana gyara mata zama sannan ya fara magana a hankali
"En garin nan so suke su bani aure, ni kuma bansan yadda zan musu ba, da ina da tabbacin matata na sona dana sanar dasu bana buk'ata ina da matar da take sona, amma bani da tabbacin hakan, nasan dae ni inaso amma ba'a sona, inaga suma sun fahimci matar da nazo da ita bata sona shiyasa suke k'ok'arin bani wata, kinsan yadda suke k'aunar Mom, toh duk soyayyar ta ni suka juyewa ita yanzu ni suke yiwa, shiyasa basa so d'an su yasha wahala a soyayya yana so ba'a son shi, inaga kawae zan kar6i auren ko zan samu salama nima na samu me sona" ya k'arasa maganar a tausashe kamar wani maraya, se a lokacin ta fara tuhumar kanta dalilin da yasa take jin haushin kalaman nasa, yanzun ma ji take yi kamar ta fasa wani kukan, aekuwa bata ankara ba wani sabon kukan ya 6alle mata, ya bud'e idanun sa akanta yana tunanin anya kuwa baze k'yale wannan wasan haka ba dan harga Allah ya gaji da ganin ta tana kuka, a hankali ya sanya hannun sa ya d'ago fuskar ta ya zuba mata lumsassun idanun sa yace bayan ya k'ara matsar da fuskar ta dab da tasa
"Open ur eyes" hucin numfashin sa da taji akan fuskar ta yasa tayi saurin bud'e idanun ta da har lokacin ke cike taff da hawaye, ya kuwa zuba mata nasa idanun cikin nata, yau d'aya taji ta kasa janye nata idanun, sun kae wajen minti 1 a haka seda yaji ta dena sauke ajiyar zuciyar da take sannan ya fara magana har lokacin be rage kusancin dake tsakanin su ba
"Am sorry ki bar kukan nan, am not talking with Aleenah, dake nake magana, tunda na fara magana baki kalle ni ba abinda yasa na za6i nace ina son ki kenan, dake nake bada wata ba uhmm?" duk seta ji wata kunya ta lullu6e ta yanzu kenan meye zezo ransa ae shikenan zeyi tunanin ko kishin sa take yi, wayyo ita kam meyasa ta kasa rik'e kanta ne, seta fara k'ok'arin sauke idanun ta daga cikin nasa amma ya sake matsar da fuskar sa dab da tata har hancin su na gogar na juna suna musayar numfashi
"Kina sona?" ya fad'a sanda bakin sa ke dab da nata, ita kam gaba d'aya ta rasa yadda zatayi dan haka bata iya cewa komae ba har zuwa sanda taji bakin sa a akan nata, ya shiga bata zazzafan kiss dan ba k'arya yayi missing nata sosae, a zafafe ya cigaba da aeka mata da sak'onni cike da matsananciyar k'aunar ta, seda yaga dae zaman nasu