Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dakatawa ta juya ta kalli cikin d'akin sannan ta juyo ta kalli Azrah kana ta d'ora da fad'in.. Ba tare da ta jira amsar Azrahn ba

"Ki dinga duk shigar da kika ga dama a cikin gidan nan, tunda dae kin riga kin saka a ranki ke d'aya ce a gidan, wannan hijab d'in malama don Allah ki cireshi ki dena sakawa idan kina cikin gida" Azrah ta girgiza kae da sauri

"A'ah wallahi bazan iya ba, meye kuma na zama babu hijab kamar wata er iska, ni kam ki barni..na d'auki dae shawara ta farko.." Meemarh tayi dariya tana kallan yadda Azrahn ke magana cike da sakalci, Meemarh tace

"Duk yadda akayi idan ke ba er fari bace toh auta ce ke kam.." Azrah ta kalli Meemarh kawae ba tare da tace komae ba..........


.........Da sauri sauri take k'arasa aekin dan tana so ne ta gama ta koma d'aki kafin ya dawo, dan bata san da wanne ido zata ganshi yazo wucewa ta d'auke kae ba, kwarjininsa yana da yawa haka zalika tsoron sa da take ji ma Allah yayi yawa dashi, dan haka tana gamawa ta d'ebo tazo ta jere su kan dinning, da sauri ta juya dan komawa saman, dae_dae lokacin daya shigo d'akin kenan, aekuwa zuciyarta ta wani irin bugawa ta sunkwi da kanta k'asa tana saeta tafiyar ta dake neman kwafsa mata, cike da sassarfa ta haye saman tana rik'e saetin zuciyar ta, shi kam gogan ko kallan inda take beyi ba, yadda ma ya nuna kamar besan da wanzuwarta a wajen ba, seda ta tabbatar ta shiga d'akin nata sannan ta sauke wata gauruwar ajiyar zuciya tana lumshe idanunta, seda taji bugun zuciyar ta ta ya saetu sannan ta janyo wayar ta ta kira number Ammi,

"Ammi ya jikin?" Ammi tace

"Jiki Alhamdulillah Azrah, ya wajen naki.." Azrah tace

"Alhamdulillah, Ammi dama kira nayi na fad'a miki.." Se kuma ta d'an yi shiru, Ammi dake zaune ta mik'e tsaye tana fad'in

"Ina jin ki Azrah, me zaki fad'amin" Azrah tace

"Ya gane ni ke masa girki, kuma ya cigaba da ci" Ammi tace

"Kae masha Allah, naji dad'i sosae Azrah, maganar dana fad'a miki kada ki fad'awa kowa kinji koh?" Azrah tace

"Toh Ammi.." Daga haka sukayi sallama kowacce ta ajje wayar ta...


____Washe_gari ma da safe tana idar da sallahr Asuba ta sakko ta wuce kitchen ta d'ora abin kari, tana gamawa ta jere kan dinning sannan tayi komawar ta d'aki abinta ko karyawar ma ba tayi ba... A 6angaren sa kuwa dama yau be tashi da zuwa ko'ina ba, but yana tunanin ya d'an haura wani club d'in ko shisha ce ya sha, dan haka yana fitowa daga wanka ya shirya cikin wasu had'ad'd'un riga da wando en ubansu, bayan ya gama shiryawa ya fito daga d'akin kae tsaye yayi dinning area, yana shirin k'arasawa wayarsa dake cikin aljihun wandon sa tayi k'ara, seya saka hannun sa still dae yana tafiya ya d'akko wayar dae_dae sanda kwalin taba ya fad'o daga cikin aljihun nasa, be lura da hakan ba kawae ya k'arasa dinning d'in ya zauna yana kara wayar a kunnen sa, daga can 6angaren Irfan yace

"Don har yanzu shiru fa.." Don ya kalli abubuwan dake ajje kan dinning d'in sannan yace

"Kana ina yanzun?" Irfan ya fad'a masa inda yake shi kuma yace

"Ohk ka jira ni.." Daga haka ya yanke wayar yayi serving kansa, sannan yaci abincin, seda ya gama kana ya mik'e ya fice daga d'akin kae tsaye ya haye motarsa ya ja ya bar gidan..... A bakin titi suka had'u da Irfan d'in, Irfan na ganinsa ya k'arasa ya bud'e front seat ya shiga, ba tare da Don d'in ya kalle shi ba ya ja motar suka fara tafiya, seda suka hau titi sannan Irfan yace

"Aboki har yanzu baka fad'amin meyasa akak'i gayya ta na bikin nan ba?" Don ya runtse idanunsa yana cigaba da driving, kamar ba zece komae ba se kuma yace

"Zaka iya yin shiru, ko kuma na sauke ka?" Irfan yace

"Am sorry" daga haka ya ja bakin sa ya tsuke dan yasan tunda ya fad'a d'in ba k'aramin aekin sane ya cika ba. Suna shirin shiga layin nasu wayar Irfan tayi k'ara, ya kalli me kiran nasa sannan ya kalli Don, ganin alamar hankalin sa na kan abinda yakeyi yasa ya d'aga wayar ya kara a kunnensa, ko da yake idan ma hankalin nasa ba'acan yake ba ya san babu ruwansa da wayar da yake yi, daga can 6angaren Simrah tace

"Hello Irfan kana lafiya?" Irfan yace

"Lafiya k'alau kefa" Simrah tace

"Alhamdulillah.. Kana jina?" Irfan yace

"Ehh.." Kawae, Simrah tace

"Ohk dama akan maganar abokin ka ne pls inaso ka taemakamin.." Irfan yace yana kallan sanda suke shiga cikin gidan

"I will call u later.." Daga haka ya katse wayar dae_dae sanda Don ke parking motar a wajen da aka tanada dan ajje motoci............ Bata sake sakkowa daga saman ba seda ta tabbatar ya fita, sannan ta sakko dan wucewa kitchen ta samawa kanta abinda zata ci, tana k'ok'arin wucewa idanun ta suka sauka kan kwalin tabar nan data fad'o daga aljihunsa d'azun, seta dakata kana ta k'arasa zuwa wajen a hankali tana sake kallan abinda idanun ta ke gani, seta tsugunna kawae ta d'auka da hannun ta na hagu, ta riga da tasan waye ya shigo da ita, tunda babu kowa cikin gidan daga ita se shi, dan haka ko dama ba su kad'ae bane ta san yana sha tun ba yau ba dan haka wannan d'in ba abin mamaki bane, abin takaecin kawae shine wae irin wannan mijin aka aura mata? wane irin zama akeso tayi dashi? ko da yake ae tasan zaman ta a gidan na wucin gadi ne tunda da kansa ya fad'a mata ta cigaba da zama kafin lokacin da iyayen ta zasu gaji da zaman ta suzo su d'auke ta, se kawae ta mik'e har lokacin abar na hannun ta ta kalli ko ina a cikin parlourn sannan ta fice, kae tsaye ta wuce can gefen gidan dake d'auke da wasu korayen shukoki koraye sharr da ratsin ja hadda fari, a hankali ta k'arasa wajen sannan ta fara dube dube, idanun ta suka sauka akan wani katako, seta k'arasa da sauri ta d'auki katakon ta tsugunna a wajen ta hak'a wani rami ta saka kwalin a ciki sannan ta maeda k'asar ta rufe, ta sake kallan cikin gidan kana ganin ta dae kaga mara gaskiya, se taji kamar kunnuwan ta sun jiyo mata bud'ewar gate amma ta k'arya ta kanta tunda tasan shi kad'ae ne ze shigo gidan kuma lokacin dawowar sa beyi ba dududu ma yaushe ya fita da har ze dawo? se ta mik'e ta fara tafiya tana kad'e hannayen ta dan komawa cikin parlourn..... Dae_dae lokacin da Don yayi parking motar sacikin gidan kenan, Idanun Irfan ya sauka akan ta sanda ta sake juyowa ta kalli cikin gidan ba tare da ta gansu ba ta cigaba da tafiyar ta, cikin Irfan ya wani irin juyawa har seda ya rik'e cikin nasa, ya kalli Don dake k'ok'arin fita daga cikin motar yace da d'an rud'ewa a cikin muryar sa wanda har hakan seda ya bayyana a yanayinsa

"Don wae nan ne gidan naka?" Kallan sa kawae Don yayi ba tare da yace komae ba, hakan ya bawa Irfan damar gane amsar tambayar da yayi, Don na shirin fita Irfan ya dafe hannun sa yana fad'in

"Kaga yanzun nan baba ya kira ni yana son gani na.. Bari naje kar yayi fushi pls" Nan ma kallansa Don yayi se can kuma yace

"Ohk.." Daga haka Irfan ya fita daga cikin motar kae tsaye ya fice daga cikin gidan zuciyar sa na wani harbawa cike da tunane tunane iri iri..... Yana fita daga gidan ya fito da wayarsa ya kira Simrah a wayar, ringing take tayi amma bata d'aga ba, ji yake yi kamar yayi tsintsu ya ganshi a gaban Simrahn dan haka se fad'i yake

"Ki d'aga wayar mana, ki d'aga wayar pls.." Aekuwa tana dab da tsinkewa Simrah ta d'aga wayar, seda ya sauke wata ajiyar zuciya sannan yace

"Ina jin ki Simrah me kike k'ok'arin fad'amin d'azu?" Simrah ta nemi waje ta zauna sannan tace

"Yawwah.. Don Allah so nake yi ka taemaka min akan abokin ka.. Wallahi ina son shi amma shi kam ya kasa gane hakan inaso kayi wani abu ne..." Irfan yace

"Kinga Simrah just go straight to the point me kike so na miki?" Seta d'an fara kame_kame tace

"Uhmm dama so nake.." Irfan yace

"Ina jin ki.." Simrah ta sake yin jimm, Irfan ya katse shirin da fad'in

"Kin san wani abu? Na fad'a miki kada ki ji komae ki fad'i duk abinda kike so wallahi zan miki, saboda Don ya cuceni, ya mayar dani wawa, sha sha sha kuma lusari, na dad'e ina son yarinyar daya aura, kuma na dad'e ina masa magana akan yarinyar seya dinga nuna min kamar zancen bashi da muhimmanci, lokacin bansan meyasa in dae na kawo masa zancen ta yake nuna baya son maganar ba, ashe shi ya san abinda yake sak'awa ya barni ya6e_ya6e a gefe ashe shi ya dad'e yana cin amana ta, so yake ya fara d'and'anar zumar yarinyar nan kafin ni in cika buri na in biyawa gangar jiki na buk'atar kwana da kwanaki da na dad'e ina so game da yarinyar nan, ashe shima abinda yake so kenan, shiyasa yayi sauri yayi wuff da ita kafin in samu wannan damar? toh wallahi kome ake ciki sena rama wannan cin kashin da Don ya min, na dad'e ina kwad'aetuwa, zuciya ta na rinjaya ta game da halittar yarinyar nan amma wannan mutumin yamin karan tsaye, saboda haka ki fad'i duk abinda kike so zan miki, nima inaso kimin wani taemako dan kuwa in dae ina raye wallahi nima sena d'and'ana abinda yake kwad'ayi shima abinda na dad'e ina buri wata da watanni......"




Kuyi manage da wannan pls 🥹


08124818273






✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION29*


_____Simrah tayi wani murmushin jin dad'i sannan tace

"Wato Irfan k'udurinmu iri 1 ne, bansan yadda zanyi in jawo hankalin Yah Adnan ba ya tare dani, in dae hakan ta kasance shikenan ni zan kammala wasan..." Murmushi Irfan yayi yana cije la66ansa sannan yace

"Kada ki damu, abinda za'ayi yanzu had'uwa ya kamata muyi se mu k'arasa maganar" Simrah tace

"Tohm shikenan Irfan nagode sosae.." Irfan yace

"Kada ki wani damu"



__________A k'ofar ajin Fawaz ya tsaya ya kalli Azrah yace

"Toh Aunty Azrah se mun fito, in da wani abun seki fad'a min" Azrah tace

"Toh Uncle Fawaz" Murmushi Fawaz yayi yace

"Wae Uncle.." Bata ce komae ba ta wuce cikin ajin shima ya wuce inda ajin su yake, duk da ba da wani wuri tazo ba se taga bata ga Meemarh ba, seda ta zauna sannan ta lura da Meemee a zaune a inda ta saba zama, se tayi mamakin ko dae tazo ta fita ne dan haka se kawae tayi shiru har malaman farko suka shigo suka fita Meemarh bata shigo ba, seda wani malamin ya fita sannan ta kalli Meemee duk da ba kasafae magana ke had'a su ba tace

"Meemee lafiya kuwa Meemarh bata zo ba?" Meemee ta kalle ta sannan tace fuskar ta ba yabo ba fallasa

"Ehh bata da lafiya ne.."

"Eyyah don Allah ki gaedamin ita" Meemee tace

"In Sha Allah" daga haka babu wadda ta sake cewa komae, duk jikin Azrah a sanyaye yake ranar kwata kwata bata ji dad'in makarantar ba kawae dae basarwa take... Aekuwa tana komawa gida ta kira Meemarhn a waya seda taji yanayin jikin nata sannan ta mata sannu kana ta shiga kitchen.........




............Seya kalli Irfan sannan ya d'auke kae yana cigaba da danna wayarsa kana yace har lokacin be kalle shi ba

"Ina da aekin yi!" Irfan yace

"Haba don Allah kayi hak'uri Don, wallahi ranar Baba ne ya kira ni kuma Inda sabo ae ka saba da halin Baba" Shiru yayi kamar be ji abinda Irfan d'in yace ba, Irfan yayi shiru yana kallan sa se kuma can yace

"Pls mana Don.." Se a lokacin Don ya d'aga idanun sa ya kalli Irfan yace yana tsare shi da idanun nan nasa masu kwarjini

"Kamar gida kace zaka gani?" Irfan yace

"Ehh..ehh..haka nace.." Don yace kafin Irfan ya dire maganar tasa

"And so..?" Irfan yace

"Shikenan toh Don, amma ae ko parlour idan na shiga na sha ruwa ae kaga zan d'orar akan zuwa gidan ka koh?" Irfan ya fad'a ba dan yana nufin abinda ya fad'a d'in ba

"Pls just leave me ah beg" Don ya fad'a yana mik'ewa, Irfan ya bishi da kallo har ya shige motar sa, seya mik'e shima ya hau motar sa yabi bayan sa, yana cikin driving wayar sa ta fara k'ara, ya amsa yana saka ta a hands free ya ajiye ta ya cigaba da driving d'in, daga can 6angaren Simrah tace

"Kamar kaena gani yanzu koh?" Irfan yace

"Ehh ni ne kam" Simrah tace

"Wani wajen zaka je ne?"

"Ehh zan je gidan Don ne, inaso na sake tabbatar da abinda nake zargi" Simrah ta sauke numfashi sannan tace

"Ohk toh don Allah ka bi a hankali dae kada ya fahimci wani abu" Irfan yayi murmurshi kana yace

"Kada ki damu zan kira ki idan na fito.." Daga haka ya katse wayar......... Tana zaune akan kujerar da ta saba zama tayi karatu taji wata iska me dad'i na kad'a ta, seta mik'e ta ajje biron hannun ta ta lek'o compound d'in, iska sosae ce ke kad'awa me dad'i ga k'amshin ruwa kuma, hakan ne ya alamta mata cewar ruwa za'ayi seta saki murmushi tana jin dad'in hakan sosae, juyawa tayi ta koma cikin parlourn ta gyara zaman curtains d'in d'akin kana ta dawo cikin d'akin ta d'auki duk littafan ta ta wuce dasu d'akin ta sannan ta d'auko wata riga mara nauyi ta chanja da kayan dake jikin ta, sannan ta zura hijab ta sakko daga benen, kae tsaye ta sake komawa bakin k'ofar ta tsaya tana kallan yadda iska ke sake kad'awa, ga k'arar ruwa wanda ke nuna a koda yaushe ruwan ze iya saukowa, tana nan tsaye har aka fara ruwan sosae, ta cigaba da kalla tana rungume jikin ta saboda sanyin dake shigar ta idanun ta a lumshe, murmushi se wanzuwa yake a fuskar ta saboda tana mugun jin dad'in irin yanayin nan, a hankali ta bud'e idanun ta tana kallan cikin gidan, ta san babu kowa cikin gidan daga ita se halin ta kuma ta san shima lokacin dawowar sa beyi ba, ga kuma ruwa da akeyi tana da tabbacin dawowar sa ba yanzu ba, kawae seta saka k'afafun ta ta fito daga cikin parlourn ta shiga ruwan, aekuwa ruwan ya fara sauka a kanta, seta lumshe idanun ta kana ta fara juyi cikin ruwan zuciyar ta fari tass, jin ta take kamar bata da wata damuwa, kanta na kallan sama ruwan na sauka akan kyakykyawar fuskar ta.......... Yana dab da shiga gidan ya dakata bayan ya bud'e gate d'in ya koma cikin motar sannan ya tsaya yana kallan yadda ruwa ke gudu, seya juya bayan sa ya kalli motar Irfan sannan ya d'auki wayar sa ya danna kiran Irfan d'in, Irfan ya d'aga kae ya kalle shi sannan ya d'aga kiran kafin Don yace komae Irfan yace

"Sorry Don, kawae inaso ne in sha lemo da ruwan gidan ka.." Don ya lumshe idanun sa kansa akan kujerar daya kwantar da ita yace

"Ohk..ka fito ka dawo nan.." Irfan ya kalli ruwan da ake sannan yace

"Ruwa fa akeyi.." Don ya bud'e idanun sa yana kallan ruwan sannan yace

"Nacin ka yaja maka, in zaka fito ka fito other wise.."

"Gani nan kawae.." Irfan ya katse Don daga maganar da yake, katse wayar Don yayi ya ajje ta a gefen sa yana sake kwantar da kansa kan kujerar. Cikin sakannin da basu wuce 30 ba Irfan ya shigo cikin motar yana sauke numfashi yace yana kallan Don

"Yawwah gani.." Ba tare daya saurari abinda yake fad'a ba ya tashi ya gyara zaman kujerar sannan ya kunna motar ya jata zuwa cikin gidan..... A 6angaren ta kuwa sam bata ji shigowar mota ba saboda har lokacin idanun ta na a lumshe ne da wani k'awataccen murmushi akan fuskar ta, ga kuma yanayin yadda ruwan ke sauka da k'arfi, dae dae nan idanun Irfan ya sauka akan Azrah, se yayi k'uri yana kallan ta kamar wani maye, ji yayi kamar ze zauce da ganin surar jikin ta, be san sanda ya fara fad'in

"Innnalillahi, lallae Allah yayi halitta a wajen nan, wayyo Allah na" ya fad'a yana dafe saetin zuciyar sa, Don ya k'arasa parking motar sa ba tare daya kalli Irfan ba, saboda ba sabbin abu bane a wajen sa ba, ya d'auka ma a waya ne yaga wata yake zuzuta halittar ta, se dae me? Irfan be gushe ba yana fad'in

"Dama na sha fad'a maka yarinyar nan zazzafa ce, yanzu dubi ka gani.." Se a lokacin Don ya d'aga idanun sa ya kalli inda Irfan ke kalla, tana tsaye lokacin data lumshe idanun ta kamar ba ruwa ne ke dukan ta ba, yanayin rigar dake jikin ta yasa saboda ruwan daya jik'a ta ta kwanta tayi luff luff sannan hijab d'in ma yabi jikin ta ya kwanta sosae hakan ne ya bayyana surar jikin ta daga cikin hijab d'in, runtse idanun sa yayi sannan ya bud'e k'ofar a hanzar ce ya fara takawa cike da sassarfa ya k'arasa har inda take, beyi wata wata ba ya sanya hannun sa ya kama tsintsiyar hannun ta dake cikin hijab, da wani irin sauri ta bud'e idanun ta tana kallan wanda ya rik'e mata hannu, lokaci guda taji zuciyar ta tayi wani irin bugu, take kuma k'walla ta cika kyawawan brown eyes d'in ta, yanayin yadda ya rik'e mata hannun da tsauri ya sanya ta k'ara runtse idanun ta, kawae seya fara jan ta zuwa cikin d'akin, se kuwa ta sake runtse idanun ta tsoro fall cikin ranta, har suka k'arasa cikin parlourn hannun sa na rik'e da nata, suna shiga ya sake ta da k'arfi wanda hakan yasa tayi taga taga zata fad'i seta dafe gefen kujera sannan ta tsaya akan k'afafun ta, seda ta tsaya d'in sannan ya d'aga hannun sa da niyyar kae mata mari, seta saka hannun ta ta kare fuskar ta tana fashewa da kuka, ya d'aga rikitattun idanun sa ya watsa mata sannan ya runtse su yana sauke hannun sa ya fice daga d'akin kae tsaye ya wuce compound d'in, har lokacin Irfan na zaune cikin motar kamar an kafe shi, Don na zuwa ya bud'e k'ofar front seat yana kallan Irfan yace

"Fito.." Kallan sa kawae Irfan yake ya sanya k'afa ya fito cike da mamakin abinda yake gani, Don yace har lokacin yana kallan Irfan

"Wannan ya zama first and last da zan sake ganin k'afar ka a cikin gidan nan idan ba haka ba duk abinda na maka ka kuka da kanka" shi fa Irfan gaba d'aya mamaki ya kusa kasheshi dan haka ya kasa furta komae kawae seya saka kae ya fice daga gidan saboda lokacin ruwan ya fara janyewa kad'an kad'an yake zuwa, Irfan ya jinjina kae yana sake sak'awa a ransa lallae seya tashi tsaye saboda ya fuskanci wani babban al'amari a yanayin Don d'in, shi kuma yayi rantsuwa seya rama cin amanar nan da Don ya masa....... Ta riga data sadak'ar marin ta zeyi, se dae taji shiru dan haka a hankali ta d'ago kanta ta kalli inda yake da jajayen idanun ta se taga baya nan, dan haka ta sauke wata ajiyar zuciya tana zubewa a wajen tana sake had'e jikin ta waje d'aya saboda sanyin A.C dake ratsa ta, ta d'ora kanta akan cinyoyin ta ta rasa ma wane irin tunani zata yi, tana nan zaune ya shigo cikin d'akin tana kallan sa ta runtse idanun ta zuciyar ta na bugawa, ba tare daya kalli inda take ba yayi wucewar sa sama kae tsaye ya wuce d'akin sa, yana shiga ya k'arasa kan gado ya zauna yana cusa hannayen sa cikin sumar kansa yana jin yadda zuciyar sa ke zafi, se kuma ya mik'e ya d'ora hannayen sa akan mirror yana kallan fuskar sa, kafin ya lumshe idanun sa na tsawon minti d'aya kana ya bud'e ya sake komawa ya zauna, dogon tsaki yaja yana jin haushin kansa, what comes over him ne yake behaving lyk dis? Ina ruwan sa? Meya dame shi dan wani ya ganta ya tanka halittar ta? Meye nasa a ciki? Kafin ya gama tunanin wata zuciyar ta bashi amsar "ae ka riga kasan halin Irfan d'an iska ne, kuma koda ba ita ba kowacce mace ka gani a irin wannan halin zaka nuna 6acin ran ka" seya mik'e kawae ya fad'a toilet dan watsa ruwa, abinda yake ta bashi mamaki shine har lokacin zuciyar sa zafi take masa, gaba d'aya ma ranar a fusace yake jin sa dan haka ko abincin daya keci ranar beje yaci ba yana kwance a d'akin cikin rashin sanin abinyi......



_____Shigowar Sameer kenan zuwa cikin office d'in ya k'arasa yaja kujera ya zauna yana kallan Don dake danna waya yace

"Waya dae!" Don ya d'an d'aga kae ya kalle shi sannan yayi murmushin gefen baki yace

"Toh Mr complainer.." Sameer ma murmushin yayi kafin yace

"Sunan da ka bani kenan?" Don ya d'aga kafad'a har lokacin yana danna waya yace

"Yeah, u deserved it ae couz babu ranar da zaka shigo babu complain" Sameer yace

"Well, koma dae menene ka ajje wayar kaji" seda ya k'arasa abinda yake yi sannan ya ajje wayar ya d'aga ido ya kalli Sameer yace

"Uhmm" Sameer yace

"Yawwah maganar aekin nan ne..ya kamata mu ware wasu ranakun dan mu gama settling komae kafin next week.." Don yace

"Shikenan?" Sameer yace

"Yeap" Don ya sauke ajiyar zuciya sannan yace

"Ohk.." Be baro companyn ba seda suka yi ayyuka sosae a office d'in nasa sannan ya baro companyn kae tsaye ya wuce gida....... Tunda ta tashi take jin jikin ta ba dad'i gashi se tari take yi, a haka dae ta sakko ta d'ora abincin rana tana sauri ta gama taje ta ajiye kafin ya dawo saboda tun abinda ya faru jiya tsoron sa da shakkar sa suka sake shigar ta, ta gama komae sannan ta kwashe ta zuba kowanne a inda ya dace, ta kae ta jere kan dinning d'in, sannan ta koma kitchen d'in ta d'auko spoon ta dawo cikin parlourn, dae_dae lokacin daya shigo cikin parlourn, tana ganin sa taji bugun zuciyar ta ya k'aru, cike da sassarfa ta fara k'ok'arin juyawa ba tare da ta kalli inda yake ba, dama ba tun yau ba hakan ke k'ona masa rae kawae basarwa yake yi, idan ta gansa seta dinga nunawa kamar taga dodo, dan haka cikin zafin nama ya sanya hannu ya rik'o hannun ta dake d'auke da spoon, seta runtse idanun ta tana jin wasu hawaye na zubo mata, ita kam ta shiga uku meyasa ta shiga cikin ruwan nan jiya gashi nan ta janyowa kanta, ita kam tayi nadama, fuskar nan babu annuri ya kalli fuskar ta da har lokacin idanun ta ke a rufe yace

"Keee.." Bata iya d'agowa ta kalle shi ba dan ji take kamar zata saka ihu, da d'an d'aga murya yace

"Keee.." Babu yadda ta iya haka ta bud'e idanun nata da suka yi rau rau tana kallan k'asa dan kome za'a mata ba zata ta6a iya kallan sa ba, lokaci guda kuma tana jin yadda hannun ta daya rik'e ke mata zafi, yace a dake

"Idan kina ji da rashin kunya karkice zaki gwada a kaena saboda baza kici riba ba, dodo kika gani? Ko kuwa ba'a koya miki gaesuwa ba?" Se tayi shiru tana jin maganar tasa kamar wani wasan kwaekwayo, kamar shine fa yace mata baya buk'atar gaesuwar ta, toh yanzu kuma ta dena yace zeyi k'orafi akae? Yace ta kama kanta! Ta kama kan nata yanzu kuma yana maganar dodo ta gani da take gudu idan ta ganshi.. Kafin ta kaega k'arasa tunanin da take ta sake jiyo muryarsa yana fad'in

"Idan kina tunanin wata rana zan chanja toh pls stop deceiving ur self couz I will never accept u as my life partner...."




08124818273




✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION30*



______"Kina zama ne kawae saboda darajar su Mami, so ki cigaba da zama har lokacin da zasu gaji suzo su d'auke ki" daga haka ya saki hannun ta yayi gaba yana cusa hannun sa cikin kwantacciyar sumar kansa, runtse idanun ta tayi tana bin sa da kallo, da tana da qwarin gwuiwar da zata iya kallan sa ta fad'a

Please Login or Register in order to submit comment