Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'akin tana share 'kwallar idanunta, Mami ta bita da kallo harta fice sannan ta dawo da kanta cikin parlourn tana sauke ajiyar zuciya....... Da sauri ta fad'a cikin parlourn babu ko sallama tana kuka kamar wadda akayi wa mutuwa, Momy dake zaune kan kujera ta mi'ke da sauri tana fad'in

"Na shiga 3 ni ennan, meya faru?" Ta fad'a tana ri'ko Simrahn, Simrah ta sake fashewa da kukan hadda sheshshe'ka, Momy ta mi'ke ta 'karasa ta bud'e 'kofar parlourn ta duba ita dae bata ga komae ba, seta sake dawowa inda tabar d'iyarta ta ta kamota tana fad'in

"Kiyi shiru ki fad'amin mana meya faru?" Seda Simrah ta gama kukan dan kanta sannan tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya tace a rarrabe

"Wae Yah Adnan...yayi..aure.."

"Keee..bansan hauka hajiya, wanne Adnan d'in?" Simrah ta sake goge hawayen fuskarta da ya'ki tsayawa tace

"Momy Yah Adnan dae da kika sani" Momy ta sake kallan Simrah, tana da tabbacin 'yar tata bata shaye_shaye amma tabbas yau kam Simrah tasha wani abun, ganin kallan da Momyn take bin ta dashi ne ya sanya Simrah fad'in

"Wallahi Momy da gaske nake, Mami da kanta ta fad'amin yanzun nan" Momy ta mi'ke tsaye ta fara zagaye d'akin kamar me tunani se kuma ta dawo ta zauna tana kallan Simrah sannan tace

"Ehh lallae yau na tabbatar hadeeza bata da kirki, ni zata yiwa haka?" Momy ta fad'a tana ri'ke ha6a, sannan ta cigaba da fad'in

"Toh wallahi bata isa ba, nasan manufar ta nayin hakan kuma wallahi tayi kad'an.. ita d'in banza, kinga share hawayen ki, Adnan koh? Toh dole Adnan ya aureki ko yana so ko baya so, ki share hawayen ki" ta k'are maganar tana ri'ko Simrahn, Simrah ta kalli Momyn sannan tace

"Momy da gaske?" Wani muslikin murmushi Momy tayi kana tace

"Nice fa? Ko kin manta wacece ni?" Simrah ta sake turo baki sannan tace

"Momy nifa bana son asiri kinsan aekin asiri ze iya warwarewa fa yazo ya dena sona" Momy ta sake yin murmushi sannan tace

"Shashasha, waya fad'a miki ta wannan hanyar zanbi? Yanzu ae an waye, marasa wayo ke bin wannan amma ni kam babu boka babu malam kuma nice na fad'a miki Adnan seya aureki" Simrah ta rungume Momy tana fad'in

"Shiyasa nake 'kaunarki Momy na" wayar ta dake cikin jaka ce tayi k'ara, ta saki Momyn sannan ta k'arasa ta d'auki jakar ta fito da wayar tana karawa a kunne, daga can 6angaren akace

"Simrah an kafe fa, wallahi sun sake posting d'inmu" Simrah ji tayi kamar ta fasa ihu tace kamar zata saka kuka

"Don Allah da gaske?"

"Wallahi kuwa ki hau online na tura miki"

"Ohk" kawae Simrah ta iya cewa tana dawowa ta zauna kan kujera tana kallan Momy ta sake maraeraece fuska, Momy dake ta kallanta tace

"Meya faru kuma?"

"Wae an sake posting d'inmu"

"Kamar yaya?" Momy ta fad'a cikin rashin fahimta, Simrah tace

"Wallahi kuwa Momy, yanzun nan Ameemah ke fad'amin"

"Toh fa wata sabuwa kuma...." Momy ta fad'a tana jinjina kae......


...........Washe_gari kuwa bayan tayi wanka ta tabbatar ya bar gidan sannan ta sakko k'asan kamar yadda ta saba zama dan kuwa tafi jin dad'in zaman nan d'in, tana nan zaune shiru kamar ko da yaushe ta lula duniyar tunani dan haka bama taji shigowar mota cikin gidan ba, se sallamar Ammin kawae taji, ta tashi da fara'a kan fuskarta tana kallan Ammin, Ammi ta 'karaso cikin parlourn ta zauna, Azrah tace bayan itama ta zauna

"Sannu da zuwa Ammi!"

"Yawwah sannu Azrah, ya zaman kad'aeci" se tayi murmushi kawae, Ammi tace

"Yalla6ae baya nan ne?"' Azrah tayi k'asa da kae sannan tace

"Ehh.." Ammi tace

"Toh maza maza tashi mu fara abinda ya kawo mu" Azrah tace a hankali

"Ammi ko ruwa ban kawo miki ba" ta fad'a ba dan tana da niyyar yin hakan ba, dan seta dinga ganin kamar ta zak'e da yawa a cikin gidan mutane, Ammi ta mi'ke tana fad'in

"Babu komae Azrah..ina kitchen d'in?" Mik'ewa Azrah tayi ta wuce gaba duk a kunyace Ammi na biye da ita har suka k'arasa cikin kitchen d'in, Ammi ta kalli Azrah ganin har lokacin hijab ne a jikinta tace

"Toh da hijab ake shiga kitchen ne madam?" Sunkuyar da kae Azrah tayi kawae tayi murmushi, Ammi tace

"Toh jeki cire kizo mu fara" Seta sake yin k'asa da kae kamin tace cikin sanyi

"Ammi..zan iya a haka fa"

"Toh shikenan.." Ammi ta fad'a a gajarce ta cigaba da aekin da take tana jinjina kae... A ranar abu guda d'aya Ammi ta koya mata, saboda seda ta tattambayeta wasu abubuwan na gargajiya taji ta iyasu sannan suka koma d'aki, Ammi ta nuna mata sabulan da zata dinga amfani dasu haka turaruka da mayukan ma da zata dinga amfani dasu masu saka laushi da taushi hadda santsin fata, ita dae Azrah bin ta kawae take yi, tana mamakin yadda take nuna mata abubuwa da yawa kuma duk a fatarta zata dinga shafawa da jikinta, Abu na k'arshe da Ammi ta koya mata kafin ta tafi shine Alwala da Sallah saboda yadda ta lura akwae kura_kurae da dama a yadda Azrahn ke sallah, ta sake koya mata wasu abubuwan da suke na addini sannan ta shirya dan komawa gida, ta kalli Azrah dake binta da kallo tayi murmushi tace

"Ina fatan kin fahimci komae?" Azrah ta jinjina kae kana tayi murmushi, tana jin k'aunar matar har cikin 'bargon ta tace

"Ehh Ammi, nagode sosae"

"Haba meye na godiya kuma Azrah?" Ita dae Azrah ba tace komae ba se mi'kewa da tayi tabi bayan Ammi dake fad'in

"Toh ni na tafi, se Allah ya kaemu gobe uhmmm?" Azrah tace

"Toh Ammi, a gaeda su Zarah" Ammi ta amsa da "Zasuji" tana ficewa daga d'akin, yayinda Azrah ta koma cikin parlourn ta zauna tana sake tuna abubuwan da Ammin ta koya mata... Good one week Ammi ta d'auka tana koyawa Azrah girki da sauran wasu abubuwan da ba'a rasa ba na dangane da jikinta da sauransu dae, haka Azrah ke bin komae a sannu sannu tana kuma bin duk abinda aka koya mata d'in tana kwatan tashi, tunda Ammi take zuwa gidan basu ta6a had'uwa da Don ba dan kuwa kafin ya dawo ita kuma ta koma gida.... Ranar da aka cika satin d'ayan Ammi ta bar Azrah da kanta tayi girkin, ba tare da ta saka hannu ba, seda ta gama sannan ta d'ebo a plate ta fito daga kitchen d'in ta mik'awa Ammi tana fad'in

"Ammi gashi na gama" murmushi Ammi tayi sannan tace

"Madallah da wannan yarinya, bari na d'and'ana" Ammi ta fad'a tana kae spoon bakin ta, Azrah ta kafe ta da idanunta tana kallan ta ko zata gane yanayin fuskarta, Ammi ta tauna tana jin yadda d'and'anon girkin yayi kamar nata, seta saki murmushi tana kallan Azrahr kafin tace

"Weldone! Yayi sosae Azrah, se naji d'and'anon kamar nawa" Itama Azrahr murmushi tayi sosae tana jin dad'i kafin tace

"Nagode sosae Ammi, Allah ya saka da alkhaeri" Ammi tace

"Ki kwashe su a warmers, ki ajje akan dinning" babu musu Azrah ta koma kitchen d'in tayi yadda Ammin ta umarce ta, Kafin ta dawo Ammi ta d'auki wayar ta tayi dialing wata number, Ringing 1_2 ya d'auka yana karawa a kunnensa bece komae ba ya lumshe idanunsa akan kujerar da yake zaune, Ammi tace

"Barka da wannan lokaci yalla6ae" Seya bud'e idanunsa kad'an yace

"Barka dae.." Ammi tace

"Ka ganni a gidan naka na girka maka abinci, base ka dawo gida ba, kuma In Sha Allah daga yau zan dinga zuwa har nan d'in ina girka maka, idan ban samu damar zuwa ba zan aeko wani daga can gida ya kawo maka" Don ya sake lumshe idanunsa yana bud'ewa a lokaci guda yace

"Kar a wahal dake!" Ammi tace

"A'ah babu wani wahala Yalla6ae"

"Toh madallah" ya fad'a a tak'aece, Ammi ta katse wayar ta dae_dae lokacin da Azrah ta dawo cikin parlourn ta kalli Ammi tace

"Ammi na ajjiye"

"Toh madallah, ni bari na wuce.." Azrah ta kalli Ammi da d'an mamaki a fuskarta tace

"Abincin fa?" Ammi tace bayan ta mi'ke

"A'ah ni kam naci nawa Azrah kuma Alhamdulillah" Azrah ta kalli dinning area sannan ta dawo da dubanta kan Ammi ba tare da tace komae ba, ganin inda Azrahr ke kalla ya sanya itama Ammi ta kalli wajen sannan tace

"Ohhh...wancan na me gidan ne, daga yau ki dinga d'aukar wasu daga cikin abubuwan da mukayi, ko kuma na gargajiya dana koya miki ki dinga yi, sannan ki jere su kan dinning uhmm?" Azrah ta jinjina kae kawae zuciyarta na bugawa, daga haka Ammi ta mata sallama sannan ta fice daga gidan...... Bayan Maghrib ya shigo gidan, kamar ko da yaushe ya haye step dan bashi da damuwar yaya wadda ke cikin gidan take rayuwa, yaya cinta yake haka zalika yaya shanta yake, shi duk wannan ba damuwarsa bace, dan sau tari yana mantawa ma da wata halitta a cikin gidan, Yana shiga d'akin ya fad'a toilet yayi wanka sannan ya fito ya shirya cikin 'kananan kaya, ya sakko 'kasan yana kallan dinning arear, seya k'arasa ya nemi waje ya zauna yana janyo 1 daga cikin warmers d'in ya bud'e, take wani daddad'an 'kamshi ya doki hancinsa wanda ya tilasta masa lumshe idanunsa, sannan yayi serving kansa ya d'auki spoon ya fara kae loma dan ya riga da yasan d'and'anon girkin Ammi, so wannan d'in ma yasan da hannunta ta girka masa, yana cikin ci wayarsa dake ajje kan dinning d'in tayi 'kara, ya kalli sunan dake yawo kan wayar sannan ya tsiyaya ruwa me sanyi cikin tambulan yasha kana ya d'aga wayar ya kara a kunnensa yana fad'in

"Barka da dare Dad" Dad yace

"Barka dae Son..ya aekin?" Don ya sake lumshe idanu sannan yace

"Alhamdulillah" Dad yace

"Amm dama magana ce akan matarka" se yaji wani banbarakwae wae namiji da suna Hajara (Yaane hajaratyy gud muslim ambassador 😹😹) Seda yayi d'an jim kafin ya sake jiyo Dad d'in na fad'in

"Kana jina?"

"Ehh" ya fad'a a gajarce, Dad yace

"Ohk..kana da ra'ayi akan cigaban karatun ta?" Ya sake yin jim yana mamakin meye nasa a cikin karatunta? Ina ruwansa ko da a can bangon duniya zata tafi karatu, Dad yace

"Ba kace komae ba.." Don ya sauke ajiyar zuciya kana yace

"Duk yadda kuka gani Dad" Dad yace da d'an fad'a a maganarsa

"Kamar yaya? Mu muke zauna maka da ita ko kuwa?" Don ya dawo da wayar daga rik'e ta da yayi da hannun dama zuwa na hagu sannan yace

"Babu komae.."

"Toh madallah, gobe idan Allah ya kaemu seta shirya ka kaeta makarantar kayi komae dae a goben" seya 6ata fuska kafin yace

"Dad akwae inda zanje, pls I have a lot to do" Dad ya sake 6ata fuska shima kamar yana ganin Don d'in yace

"Oh....k wato ni bani da aekin yi kenan koh? Wae Adnan meyasa ba'a baka umarni sau 1 ne kayi amfani dashi? Kae wane irin d'a ne?" Don ya lumshe lumsassun idanunsa yana jin yadda zuciyarsa ke zafi yace

"Ohk Dad zanje"

"Better" Dad ya fad'a yana katse wayar, mik'ewa yayi daga kan dinning d'in saboda gaba d'aya abincin ya fita a ransa, ya koma cikin d'akinsa ya zauna yana tunanin yadda zeyi ya sanar da ita tafiyar nan dan kuwa wallahi idan ta wuce lokacin fitarsa sedae tayi ta zama babu makarantar hakan ba damuwarsa bace, amma kuma hakan baze faru ba indae be sanar da ita ba, shi kam bega abinda ze had'ashi da ita ba ballantana har magana ta had'asu, dan haka seya d'akko biro da takadda yayi d'an rubutu kana ya fito daga d'akin nasa ya sauka downstairs dan shi bema san tak'amaemae inda take zaune ba, ya ajjiye takardar kan kujerar parlourn ya danne ta da wani d'an 'karamin kwali sannan ya koma saman...... Washe_gari da safe da asuba ta farka tayi wanka da sabulan da Ammi ta kawo mata, ta fito sanye da hijab d'in ta kamar yadda ta saba shiga dashi da kuma fitowa dashi, se zuba wani sassanyan 'kamshi take yi na sabulan da tayi amfani dasu, ta k'arasa taja stool ta zauna tana janyo mayukan ta masu 'kamshi sosae, ta mulke farar fatarta da maya mayan, kowanne ta saka shi a wajensa kamar yadda Ammi ta umarce ta, ta janyo wata powder ta shafa sannan ta zizara kwalli kana ta shafi d'aya daga cikin maya mayan ta ta shafe cute lips d'in ta dashi sannan ta shirya cikin doguwar rigar atamfa ta saka hijab d'in ta, sena tsaya ina kallan ikon Allah dan kuwa se naga Azrahr ta fara chanjawa daga Azrahr k'auyen Kima zuwa wata sabuwar Azrahn, dan kuwa hatta da fatar ta ta fara chanjawa tana glowing har wani laushi tayi, tana gama saka hijab d'in ta sakko 'kasan dan d'ora abin kari, amma kafin ta d'ora girkin seta fara da tsaftace ko'ina na gidan, parlourn ne a 'karshe dan haka ta fara shareshi kamar kullum, tazo dab da zata gifta ta wajen kujerar taga wata takadda danne da wani kwali, seta 'karasa ta d'auki takardar tana mamakin ganin rubutun dake jiki, seta fara karantawa da karatun data iya wanda sanadiyyar Hauwa'u ne ta koye shi harma da wasu kalmomin data iya na turanci duk ta dalilin Hauwa'un, a zuciyarta take karantawa kamar haka

"Make sure dat 7:30 kina compound, idan kuma kin wuce lokacin left for u, couz bana jira sedae a jira ni," ta riga da tasan babu wanda ke a cikin gidan daga ita seshi, toh kenan shine ya rubuta? Seta d'aga kae ta kalli stairs d'in sannan ta dawo da dubanta kan tan'kamemen agogon dake a d'akin wanda ke nuni da 7:15, da sauri ta ajje takardar hannun ta ta koma saman da sauri, ta chanja kayan dake jikinta sannan ta sake hijab kana ta d'auko wani takalmi ta sakko 'kasan tana sake kallan agogo, kae tsaye ta wuce compound d'in zuciyarta na bugawa dan bata san meke tafe dashi ba, amma tana fatan ace alkhaeri ne, tana nan tsaye kamar maraeniya se tunane_tunane take, ya fito daga cikin parlourn yana tafiya majestically hannunsa d'auke da wayarsa yana waya, ko kallan inda take beyi ba ya 'karasa wajen motar yana cewa wanda suke wayar

"Kana ina yanzu?" Sameer yace

"Ina cikin layin ku fah"

"Ohk" ya fad'a yana katse wayar, Cikin rawar murya ta kalli saetin inda yake a kaekaece kana tace

"Ina kwana?" Iskar data d'ebo tama be kalle ta ba ballantana kuma wadda tayi maganar, kae bema nuna yasan da halittar ta a wajen ba, yayi gaba zuwa wajen gate d'in gidan, seta bishi da idanunta tana jin yadda 'kwalla ta tarar mata a idanunta, ita kam ba daban Ammi ce tace ta dinga gaeshe shi ba ba zata sake gaeda shi ba ko dan gudun karya wula'kantata... Sameer ya shigo da motarsa cikin gidan, sannan ya sakko yana kallan Don bayan sun gaesa yace

"Friend..wae meya faru ne?" Don ya d'an murza goshinsa kafin yace

"Taemako zaka min!" Sameer ya gyara tsayuwarsa yana fad'in

"Ohk ina jinka!" Don yace bayan ya d'aga kae ya kalli Sameer

"Waccan zaka taemaka ka kae makaranta, ka gama komae ko zuwa gobe suna so ta fara zuwa!" Ya fad'a cikin rashin damuwa, se a lokacin Sameer ya kae dubansa inda Don d'in ya nuna ya hango ta tsaye hannayenta hard'e a k'irjinta, seya watsawa Don kallo kana ya wuceshi ba tare da yace masa komae ba ya k'arasa wajen Azrah yace da murmushi kan fuskarsa

"An tashi lafiya madam?" Seta d'ago kae kad'an tana sauke hannayenta sannan tace

"Ina kwana?" Yace

"Alhamdulillah.. Ya 'kok'ari?" Ta sake yin k'asa da kanta kafin tace

"Alhamdulillah.."

"Madallah" Sameer ya fad'a yana komawa inda ya bar Don wanda keta auna masa wata uwar harara, yana zuwa yace

"Wannan d'in ce waccan?" Don yace

"Ba ka zubar min da mutunci ba? Ko har yanzu hakan be ishe ka ba?" Sameer yace

"Ohk zuwa da nayi muka gaesa shine zubar da mutunci?"

"Yeah.." Don ya fad'a a gajarce yana kallan Sameer, Sameer yace

"Well, kaga malam ni tafiya zanyi"

"Ohk ba zaka kaeta ba?" Sameer ya watsa masa harara sannan yace

"Wallahi ko zanje ba dan kae bane, karma kaji kanka a sama, amma kuma wallahi ba zanje ni kad'ae ba sedae muje tare" Don ya lumshe idanunsa yana bud'ewa akan Sameer cikin 6acin rae yace a hankali kamar wanda baya so aji abinda yake fad'a d'in

"Saboda?"

"Saboda matar kace!" Wani dogon tsaki Don ya ja yana dafe kansa, ya tsani wannan kalmar da suke fad'a masa, wae matarsa! Ta ina ta zama matarsa?, kawae dae tana zaune ne a cikin gidansa kafin lokacin da iyayensa da kuma nata iyayen zasu gaji suzo su d'auke abarsu, Sameer ya katse masa tunani ta hanyar fad'in

"Malam idan ka amince da hakan fine..yanzu seka wuce mu tafi makarantar, idan kuma baka amince ba zan d'auki motata ne na wuce inda zanje...."..............



08124818273



✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION25*


_____"Ohk dan na kira taemako a cikin lamarin, dats why kake nema ka wulak'antani?" Don ya fad'a a d'an zafafe yana watsawa Sameer idanunsa, Sameer ya dafe kansa kafin yace yana kallan Don

"Noo, ka riga da kasan kafi k'arfin haka a wajena, but inaso ne na nuna maka abinda kakeyi ba dae_dae bane Don, ya kamata ka dinga tunawa cewa...."

"Enough pls.." Don ya katseshi da fad'in hakan yana d'aga masa hannu, kafin ya d'ora da fad'in

"Will u just help me or not?" Sameer ya kalli Don sosae kafin yace

"Muje but tare.." Bece komae ba yayi gaba, Sameer yabi bayansa har zuwa wajen motarsa, Don ya shiga 6angaren me zaman banza, yayinda Sameer ya bud'e Driver seat yana 'ko'karin shiga, seya tuna dalilin fitar tasu, ya kalli Azrah dake tsaye har lokacin wadda ta dad'e da gajiya yace da d'an murmushi kan fuskarsa

"Sorry Madam ki shigo mu tafi" Seta d'ago a hankali kana ta taka zuwa wajen motar ta saka hannu ta bud'e tana fatan kada tayi 'kauyenci wajen bud'ewa, se kuwa gashi ta bud'e d'in sannan a hankali ta shiga cikin motar ta kullo 'kofar, Sameer yaja motar suka bar gidan bayan ya sauka ya kulle gate d'in.... Tunda suka fara tafiya babu wanda yace komae, kowa da abinda yake sak'awa, shi Sameer mamakin yadda akayi Don yak'i kar6ar wannan tsaleliyar kyautar da Allah ya masa yakeyi, ita kuwa tayi shiru a gidan bayan kamar me tunani sedae har a lokacin k'irjinta be bar bugawa ba, Se can Sameer ya katse shirun nasu da fad'in

"Wace makaranta?" D'an shiru Don yayi kamar ba zece komae ba se kuma can yace

"Ina tunanin tasu Fawaz"

"Kana tunani ko ka tabbatar?" Sameer ya fad'a yana kallan Don kana ya maeda dubansa kan titi

"Yeah nan" Don kawae ya furta dan kuwa haushin Sameer d'in yake ji sosae, a haka har suka 'karasa makarantar.... Suna isa kae tsaye Sameer ya shige cikin ta da motar ya sami waje yayi parking sannan ya kashe motar, Don ya bud'e motar ya fita ba tare da ya cewa Sameer komae ba, ganin haka ya sanya Sameer girgiza kae sannan ya fito daga cikin motar yana kallan Don yace

"Mu wuce koh?" Don ya juyo yana kallansa sannan yace bayan ya d'auke kansa

"Kana nufin sena shiga? Sameer..?" Ya fad'a a zafafe, ganin da idanun mutane a wajen ya sanya Sameer fad'in

"Is ohk..seka jiramu" daga haka be jira amsar Don d'in ba ya zagaya dama glass d'in 6angarenta a zuge yake yace yana kallan cikin motar

"Madam ki fito.." Bugun zuciyarta ne ya k'aru amma ta basar ta fito daga cikin motar a hankali tana kallan cikin makarantar dan tun daga waje ta fahimci inda sukazo, Sameer yace bayan ta fito

"Muje" Ko kallan inda Don yake beyi ba dama kuma shima be kalleshi ba ya koma cikin motar, shi kuma Sameer ya wuce gaba yayinda Azrah ta bishi a baya har suka isa office d'in principal d'in makarantar, Seda Sameer ya tabbatar ya gama komae a ranar har aji an bawa Azrah bayan an gabatar mata da interview wadda Allah ya taemaketa taci duk a dalilin abubuwan da Hauwa'u ke koya mata da wad'anda take gwadawa a gida, a ranar kuwa hauwa'u tasha addu'a kamar babu gobe, sannan Sameer ya gabatar musu da uzurin se zuwa gobe zata fara zuwa, saboda yanayin yadda kayan nasu suke wanda suke bayarwa a makarantar wanda ga ita yadda take matar aure yasa yaga gwara a d'inka mata daga gida.... Yanzun ma da suka fito Sameer na gaba ita kuma tana biye dashi, ganin komae take kamar a mafarki wae yau ita Azrah itace aka saka a makarantar boko? Makarantar da ta sota tun yarinta amma Allah be nufa zata yita ba se yanzun, kae lallae Allah abin godiya ne, se kawae taji wasu hawaye sun zubo mata akan kuncinta, karo na farko kenan a rayuwarta data ta6a kukan farin ciki, dan kuwa duk kukan da tasha yinsu a baya sa6anin haka ne, a hankali ta saka gefen hannunta ta d'auke hawayen tana cigaba da tafiya kamar mara laka...... Yana nan zaune har lokacin yana danna wayarsa, har Sameer ya 'karaso ya bud'e 'kofar ya shiga, bayan Azrah ta shiga ya tada motar kae tsaye ya tashe ta ba tare daya kalli inda Don d'in yake ba, shima be nuna alamar yaji shigowarsu ba ya cigaba da danna wayarsa hankalinsa kwance, a haka har Sameer ya 'karasa gidan bayan ya saukesu ya d'auki motarsa, seda yazo tafiya ne sannan ya kalli Don yace

"Thank u" Don ya d'anyi wani miskilin murmushi kana yace yana shafa sajensa

"Ohhhh..indae Thank u ne ae ba raguwa zanyi ba.. So Thank u, but i think...ohk then shikenan kawae" Sameer yace

"Ahh toh ashe kasan da hakan" daga haka sukayi sallama Don ya koma cikin gidan...... Tana shiga d'aki ta zauna kan gadon tana rufe fuskarta wani sassanyan murmushi na bayyana a cute face d'in ta, seta tashi ta sake kallan kanta a mudubi wae yau ita Azrah itace zata fara zuwa makaranta, woww, seta sake rufe fuskarta tana murmushi, wayarta dake ajje kan mirror d'in ce tayi k'ara, seta k'arasa a hankali ta d'auka, ganin number Ammi ce data saka mata ranar da tazo yasa ta d'aga tana karawa a kunnenta, daga d'aya 6angaren Ammi tace

"Azrah!" Azrah tace

"Na'am Ammi ina yini?" Daga can 6angaren Ammi tayi murmushi jin yadda taji alamar farin ciki a muryarta sedae batace komae ba bayan ta amsa gaesuwarta ta, seta jiyo Azrah na fad'in

"Ammi ki tayani murna, gobe zan fara zuwa makaranta" ta k'arashe maganar da murmushi kan fuskarta me kyau, Ammi tace

"Kae Masha Allah.. Allah ya taemaka Azrah"

"Ameen nagode Ammi" Ammi ta d'an ja numfashi kad'an sannan tace

"Yaci girkin kuwa?" Azrah ta jinjina kae kamar Ammin na ganinta, se kuma data tuna bata ganinta sannan tace

"Ehh Ammi.."

"Toh madallah, Inaso ki bud'e kunnenki da kyau..kina jina?" Azrah tace

"Ehh Ammi"

"Kada ki fad'awa kowa ya fara cin abincinki ko waye kuwa kinji koh?" Azrah ta d'anyi jimm tana mamakin dalilin Ammin na fad'in hakan, se kuma can tace

"Tohm"

"Kinji koh?" Ammi ta sake maemaetawa, tace

"Ehh In Sha Allah" Ammi tace

"Yawwah a kula sosae" da "toh" ta amsa kana sukayi sallama, ta ajje wayar kamar yadda ta saba dan babu abinda takeyi da ita, dan kuwa ma mantawa takeyi da ita kwata kwata......


........ Washe_gari da sassafe ta gama aekin komae na gidan, ko karyawa batayi ba saboda d'oki kuma dama banda abincin safe a yadda Ammi ta fad'a mata zata dinga masa girki, sanda ta fito share d'akin ne taga wata leda a ajjiye, seta k'arasa ta d'auki ledar ta bud'e se taga uniform ne a ciki da jaka hadda takalmi, bata san sanda ta buga wani tsalle ba tana dariya, se kuma ta fara juye juye in order to make sure ba wanda ya jita, sharar da bata k'arasa ba kenan ta wuce d'akinta da sauri ta fad'a toilet, tayi wanka sannan ta fito, bayan ta shafe jikinta da maya mayanta da turarukan ta na jiki sannan ta d'auki uniform d'in ta saka, se kuma duk taji kunya ta kamata bayan ta saka hijab d'in, dan kuwa hijab d'in dududu k'irjinta kawae ya rufe, se riga me dogon hannu da kuma skirt shima be k'arasa har k'asa ba, seta koma ta zauna kan gadon tana turo baki kamar wadda akama wani abu, yanzu fisabilillahi a haka zata shiga cikin mutane?, seta d'akko takalmin dake cikin ledar wanda ke had'e sa socks ta saka sannan taga babu inda ya bayyana a k'afarta, se a sannan ta d'anji dama_dama, bata bi takan wani turare ba tunda tasan fita zatayi, dan haka kawae seta d'auki jakar dake d'auke da dozen d'in exercise book

Please Login or Register in order to submit comment