Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wani babban mutum, a gidan sa ma ya sauka sanda yaje, mutumin ya saka ersa Sa'adatu ta kawo musu ruwa da kayan motsa baki, anan ne Dad ya had'u da Mom (Maman Don), tunda ya ganta yaji inama ace wannan mutumin me dattako ze bashi auren wannan er tasa? Beyi k'asa a gwuiwa ba ya sanar da mutumin k'udurin sa, ga mamakin sa se yaga mutumin ya nuna jin dad'in sa da kuma amincewar sa akan lamarin, amma yace ze bashi auren Sa'adatu ne matuk'ar itama tana son shi, idan kuwa bata son shi toh se dae yayi hak'uri, aekuwa ana tambayar Sa'adatu game da bak'on d'azu seta rufe fuska tana dariya, mahaefin ta yaji dad'i ya sanarwa da Dad ya turo iyayen sa a nema masa auren ta. Sanda ya sanarwa da Mami zancen auren nasa ta tada hankalin ta matuk'a har cewa take wae ko dan yaga bata haehuwa ne da yarintar ta da komae ze mata kishiya, Dad yace mata ba haka bane kawae dae Allah ne ya k'addara zeyi auren, a ranar ta kira k'awar ta Hajja Kaltum take bata labarin auren Dad d'in tana yi tana kuka, Hajja Kaltum tace

"Ke baki da wayo Hadeeza wlh, waya fad'a miki yanzu ana haka? Abinda zaki yi kawae shine ki tarbe ta da hannu bibbiyu kada ki ta6a nuna bakya son ta, ni nan zan k'arasa saeta miki kan labarin"

"Allah ko k'awata" Mami ta fad'a tana share hawayen ta, daga nan kuma seta kwantar da kan ta gaba d'aya ta nunawa Dad tana maraba da auren nasa hannu bibbiyu, yaji dad'i sosae tunda dama ba zeso ace kan matansa sun rabu ba, toh gaba d'aya dae da had'uwar Dad da Mom da kuma yin auren nasu ba'a wuce wata 5 ba, daga nan aka wanke amarya aka mik'a ta gidan Dad, Mami ta kar6e ta kamar zata maeda ta ciki haka suka fara rayuwar su, sanda Mami ta lura Mom na d'auke da juna biyu hankalin ta yayi mugun tashi, ta rasa meke mata dad'i, hauka ne kawae bata yi ba tana tunanin idan Mom ta haehu ita bata haehu cikin gidan nan ba ae akwae matsala, bata yi k'asa a gwuiwa ba ta sake kiran Hajja Kaltum a waya ta sanar da ita abinda ke faruwa tana kuka kamar zata shid'e

"Ni dae kin cuce ni Kaltume wlh kin gama dani, yanzu mene fa'idar hakan da kika bari na aekata?" Hajja Kaltum tayi murmushi sannan tace

"Mtswww, Hadeeza gajen hak'urin ki yayi yawa, wallahi baki da hak'uri, amma kuma yanzu gwara da kika kira ni kika fad'a min, akwae wani malami zanje wajen sa zamu san yadda za'a yi akan cikin nan kada a barshi yazo duniya" Mami tayi shiru sannan tace

"Kina ganin hakan yayi?" Hajja Kaltum tace

"A'ah idan beyi miki ba shikenan sena k'yale ki, kinji ni da mata"

"Shikenan Kaltum zan kira yaya Amina muyi shawara duk yadda muka yi zaki jini" daga nan Mami ta kira Momy (Momyn Simrah) ta sanar da ita abinda ke faruwa, nan Momy ta nuna goyon bayan ta akan hakan ta sake tunzura Mami har tana ce mata daga zarar ta bari wata ta riga ta haehuwa a gidan shikenan ta zama fanko, haka dae ta yadda da zancen nasu, tare da Hajja Kaltum suka je wajen wani malami se dae anan yake sanar dasu se dae su bari idan d'an yazo duniya se a musu aeki akan sa saboda ya duba yanzu aekin baze yiwu ba, haka suka dawo gida Mami ta cigaba da nuna tana tare da Mom a koda yaushe, kulawa take bata ta musamman kamar er uwatta wadda suka fito ciki d'aya, idan kaga yadda take nuna mata abin seya baka mamaki, shi kam Dad hakan ya masa dad'i sosae, yana sake fatan Allah ya k'ara had'a masa kan matan nasa, Shekarar Mom d'aya da zuwa gidan ta haefe kyakykyawan d'an ta namiji me kama da ita sakk ranar suna ta zagayo yaci suna ADNAN, da farko jikin Mami ya k'ara yin sanyi har taso ta d'aga hankalin ta ganin d'a namiji ta haefa amma data tuna lokaci kawae suke jira seta manta da hakan ta cigaba da harkokin ta, idan kaga yadda Mami ke nunawa d'an nan k'auna tun mahaefiyar sa na raye idan baka sani ba zaka yi tunanin itace ta haefe shi, seda aka haefe shi sannan suka koma wajen malamin ya sake fad'a musu se yaron ya kae shekara 10 sannan zasu fara aeki akan sa, Mami ta dinga kuka tana jin ita kam ae ta riga data mutu, shekaru goma ae ba wasa bane, haka dae Momy da Hajja Kaltum suka dinga tausar ta ta hak'ura, da farko harta fara chanjawa daga yadda take musu, seda Hajja Kaltum ta taushe ta sosae sannan ta koma nuna musu soyayyar kamar da..


Haka rayuwar ta cigaba da tafiya har lokacin ita da Ummi shiru babu labarin haehuwa, ga Adnan yana ta wayo yana girma kamar d'an larabawa saboda kyawun da yake dashi, tun tashin Adnan ya kasance miskili ne shi na k'in k'arawa, bayan uwarsa se ubansa kawae yake yadda ya zauna suna hira amma ko Mami baya kulawa, akwae ranar daya dawo daga makaranta ya shigo parloun gidan sanye cikin uniform da suka yi masa mugun kyau bayan sa d'auke da jaka, Mami na zaune ita da Mom suna kallo jefi jefi suna hira, Mami na ganin sa ta mik'e tana fad'in

"Oyoyo Son" ta fad'a tana bud'e masa hannun ta alamar yazo ta rungume shi, ya 6ata fuska sannan yayi inda Mom take ya rungume ta, d'ago shi tayi fuskar ta a had'e tace

"Wato Adnan baka da kirki koh? Baka ga Mamin ka bane?" ya turo k'aramin bakin sa bece komae ba, Mom tace

"Oh yah jeka gaeda ta" matsawa yayi kusa da Mami yace har lokacin yana tura baki

"Gud afternoon" Mami ta jan yo shi tana fad'in

"Ko kaefa Son.." Washe_gari daya dawo lokacin Mami ce kawae a d'akin tace

"Sannu da zuwa Son" ya had'e miskilar face d'in sa yace yana tura baki

"Ni ki dena kula ni, ba akan ki Mom kemin fad'a ba" ya fad'a yana shirin wucewa, Mami tace

"Eyyah zo kaji, daga yau Mom ta dena maka fad'a a kaena kaji koh?" ya jinjina kae kawae... daga wannan rana duk sanda Mom zata ga Adnan yayiwa Mami wani abun da be dace ba zata tsawatar masa ta nuna masa abinda ya kamata yayi, shikenan kuma seya fara sakin jiki da Mami, tafi tafi dae ya koma kamar iyaye mata 2 ke gare shi, Mami kuwa nunawa take kamar ma tafi son sa akan Mom d'in tasa..

Shekaru suka cigaba da shurawa har aka kuma shafe shekaru 8, lokacin Adnan na shekaru 8 kenan, ya k'ara kyau mara misaltuwa kamar shi yayi kan sa, A k'arshen shekarar ne Abba ya fara shirye shiryen tafiya India, se yayi amfani da wannan damar ya tafi da Ummi dan a duba lafiyar ta, a lokacin ya sanarwa da Dad ko ze d'auki Mami su tafi tare, Dad ya bashi uzurin shirye shiryen da yake yi na wani had'in gwuiwa da zasuyi wajen bud'e wani company, toh abinda yasa kenan Abba suka tafi India shi da Ummi kawae, seda ya gama abinda ya kawo shi sannan suka je wani babban asibiti dake yankin maharashtra, bayan yayi wa likitan bayanin abinda ya kawo su sannan ya fito, ita kuma Ummi aka shigar da ita wani d'aki wanda anan ne za'a duba ta..


A lokacin daya fito d'in nan anan ya had'u da Ammi suma sunzo asibitin kawo mahaefin su da bashi da lafiya, tunda ya ganta yaji ta kwanta masa, komae nata ya burge shi, nutsuwar ta hankalin ta komae ma ya burge shi, daga nan yayi yadda zeyi har ya samu number ta, itama kuma akayi sa'a Abban yayi mata, cikin lokaci k'ank'ani soyayya me k'arfi ta shiga tsakanin su, anan ne take sanar dashi abinda ya kawo su k'asar amma suna dab da komawa, nan yayi mata alk'awarin daga zarar sun koma d'in iyayen sa zasuzo su nema masa auren ta. Basu wani dad'e a k'asar ba Abba da Ummi suka tattara ya nasu ya nasu suka koma Nigeria saboda anyiwa Ummi gwaje gwaje an tabbatar lafiyar ta k'alau ba tada wata matsala kawae dae haehuwar ce Allah be kawo ta ba, amma an bata wasu magungunan da zata ke sha ko Allah zesa a dace. Sanda suka dawo se Abba ya duk'ufa wajen neman auren sa, ya sanarwa da iyayen sa maganar auren nasa, haka akaje aka nema masa auren Ammin sannan aka saka watanni k'alilan saboda iyayen ta zasu bar garin ne nan da lokacin da aka saka saboda aekin da mahaefin ta ya samu, kuma shima Abban zeje wata k'asa ne yin wani aeki na shekara guda, ko da ya sanar da Ummi ita kam haukan ta ta nuna a fili, Abba yace mata wannan abinda take ba shine ze sanya yak'i yin auren nan ba, Ummi fa ta tada hankalin ta sosae haka dae har akazo akayi auren, washe garin ranar da aka d'aura auren, Abba Ummi da kuma Ammi suka d'aga zuwa U.S, da farko nunawa tayi ita babu inda zata je ya tafi da matar sa kawae se taga ko a jikin Abban ya nuna mata bata da hankali, se kuma ta dawo hayyacin ta kawae ta bisu, Ummi dae data tabbatar da gaske anyi auren gashi ta rasa mafita, ranar da suka isa k'asar ta kira Mami a waya tana kuka take fad'a mata

"Ni kam na shiga 3 Hadeeza, ban farga akan auren Abbakar ba se yau, ashe da gaske mutumin nan auren zeyi? Kin gammu yanzu cikin gida d'aya" Mami tace

"Ae kinyi kuskure wlh, d'azun nan Kabeer ke fad'a min zancen auren Abbakar da akayi, kin san shima baya k'asar shiyasa ma ashe ya manta be fad'a min ba, nayi mamaki har nake tunanin garin yaya hakan ta kasance kina cikin gidan?" Ummi ta sauke ajiyar zuciya sannan tace

"Na d'auka tashin hankali na ze hana shi yin auren nan ashe ba haka bane, ni dae yanzu mene mafita!?"

"Mafita 1 ce dole sekin dawo tukunna.." Ummi tace

"Toh shikenan, ae bana tunanin zamu wuce sati 2 anan d'in.." Wasa wasa fa Ummi taga suna shirin shafe wata a cikin k'asar, ga amarya na nan se k'ara kyau take, dan haka ta tambayi Abba sanda zasu koma, anan yake fad'a mata aeki ne ya kawo shi k'asar saboda haka besan ranar komawar su ba, daga nan fa Ummi ta cigaba da saukewa Ammi kwandon rashin mutunci kala kala, dan ita sam ba zata yadda da wani nuna soyayyar k'arya ba, a fili take nuna k'iyayyar ta ga Ammi, ita kuwa Ammi bata tanka mata baewar Allah, haka suka cigaba da kasancewa cikin k'asar, watan su 1 da zuwa k'asar Ummi ta fara rashin lafiya, Abba ya d'auke ta zuwa asibiti anan aka tabbatar musu tana d'auke da juna biyu, farin ciki kamar ze kashe Ummi haka Abba ma yayi farin ciki k'warae da gaske, tun daga nan Ammi ta fara fuskantar chanjin da Ummi tayi, rashin mutuncin yau daban na gobe daban, haka gori kamar akan ta aka fara yin ciki, ta manta ita seda tayi fiye da shekara 10 sannan ta samu, wataran idan tawa Ammi rashin mutunci se dae ta shiga d'aki tayi kuka ta godewa Allah, seda Abba ya fahimci hakan sannan ya takawa Ummi birki yaja mata kunne sosae, sanda cikin nata ya isa haehuwa ma aekuwa sun sha ta6ara a wajen Ummi, akwae ranar da suna zaune su duka a parlour, Ummi na cin fruit ga abinci dasu biscuit duka gaban ta se nad'a take yi, Abba ya kalle ta yace

"Ki bar cin kayan zak'i haka nan ko dan saboda lafiyar ki" Ummi ta d'an ta6e baki tana satar kallan Ammi tace

"Toh ae kaga gwara ni, baci kawae nake yi ina kasayarwa ba, tunda gashi na kusa ajiye maka magaji" kallan ta kawae Abba yayi sannan ya kalli Ammi data nuna bata masan tana yi ba, Abba yaji dad'in hakan kawae se yayi murmushi yana girgiza kae, mata dae sha'anin su se su, seda Ammin ta tafi d'aki sannan Abba ya kalli Ummi yace

"Ke meyasa ne kullum cikin neman fitina kike?" Ummi takae alawa bakin ta sannan tace

"Fitina kuma!? Meye abin fitina anan gaskiya ce fa na fad'a" Abba yace

"Toh yayi miki kyau, kada na sake jin irin wannan maganar a cikin gidan nan kin dae ji na fad'a miki". Ummi ta cigaba da gurza rashin mutuncin ta musamman da taga kamar basu da ranar komawa k'asar su, Ummi na tashi haehuwa ta haefo en 2 duka mata tubarkallah, fariya a wajen ta ta k'aru, gori ma ya k'aru haka rashin mutunci ya k'aru amma fa tafiyi ne a bayan idon Abba, dan idan a gaban sa ne ze taka mata birki ne dan baze d'auki kowacce daga cikin su ta wulak'an ta wata ba, (ni kam nace wannan da maza ta haefa da anga abubuwa, Allah y kyauta) yara suka ci suna Meemarh da Meemee, haka kawae idan suna zaune se kiji Ummi na musu wak'a me cike da habaeci, hakan ne ya sanya Ammi dena fitowa ma gaba d'aya musamman idan tasan Ummin na waje, kishi ya rufewa Ummi ido bata tashi ankara cewar Ammi nada ciki ba seda cikin ya fito sosae saboda Ammi nada tsayi shiyasa ba'a ganin cikin nata sosae, lokacin da twins d'in ta suka kae wata 2 kenan, babban hauka ne Ummi kawae bata yi ba amma fa tayi k'aramin hauka, haka ta d'aga hankalin ta sosae tana tsoran kada ace Ammi ta haefi d'a namiji ya gaje musu gida, nan ta k'ara rikicewa Abba akan su koma gida mana, ya fad'a mata yana dab da k'arasa aekin daya kawo shi, a daddafe Ummi ta k'arasa wata d'ayan da suka k'ara duk tayi wani sukuku da ita, Ammi na cikin watan haehuwar ta ne suka baro U.S zuwa Nigeria, farin ciki kamar ya kashe Ummi, ranar da suka dawo ko hutawa bata yi ba ta fice daga gidan, suka had'u da Mami suka tafi wajen Malamin nan nasu, anan yake sanar dasu cewa

"Idan so kike a 6atar miki da ita kan ta kishiyar taki da abinda ta haefa ma zamu iya miki aekin nan" Mami da Ummi suka kalli juna sannan Ummi tace

"Hakan ma yayi, yanzu ya za'a yi?" dariya yayi kana yace

"Ranar data haehu zamu saka ta fita a hayyacin ta, kome zaki ga tayi kada ki kula ta, ki barta, zamu saka tayi nisan kiwo taje ta yadda abinda ta haefa d'in da kanta, in dae kuma hakan ta faru wato da hannun ta ta yadda abinda ta haefa toh har abada ba zata ta6a dawowa hayyacin ta ba, zata k'are rayuwar ta ne a haka ita ba matacciya ba ita ba rayayyiya ba, sannan zamu juyar da hankalin mijin naku akan ta yadda baze ta6a neman ta ba har abada" Nan suka yi na'am da maganar tasa haka suka ajje masa kud'i suka tafi cikin farin ciki, Mami na fad'awa Ummi itama lokacin da zata salwantar da nata matsalolin sun kusa zuwa...


__Washe_gari Ammi ta fito daga wanka ta shirya cikin riga, zanin atamfar na ajje kan gado kafin ta kaega d'aura shi taja stool ta zauna d'aure da wani zanin, sannan ta gyara fuskar ta da hoda hadda kwalli tana d'an mazewa yadda taji marar ta na d'an mata zafi, d'auri tayi kana ta mik'e a lokacin da taji marar ta ta wani murd'a mata, salati ta saka tana dafe cikin ta, sannan ta zube a gefen gado tana ta murk'ususu, gashi bata san inda ta jefa wayar ta ba ballantana ta kira Abba ta sanar dashi, a haka ta cigaba da kasancewa cikin zafin ciwo har lokacin data haehu ita kad'ae babu taemakon kowa sena Allah, kukan jaririya ne ya fara karad'e cikin d'akin, Ammi ta saki kukan farin ciki tana goge hawayen idanun ta sannan ta saka hannu ta d'auki jinjirar dake kwance cikin jini, ta janyo towel d'in dake ajje kan gado ta saka babyn a ciki tana kallan ta cike da wata matsananciyar k'aunar ta mara misaltuwa, tafi minti 2 tana kallan babyn ta ta kafin daga bisani ta ajjiye ta kan gadon sannan ta mik'e da k'yar tana jin yadda take jin jikin ta kamar ana sassara mata shi, ta d'auki zanin data ajje d'azu ta chanja shi dana jikin ta, kana ta yafa mayafi har lokacin k'arfin hali kawae take yi, sannan ta sake d'aukar babyn cikin k'arfin hali ta d'auko wani d'an k'aramin zoben gold data gaje shi tun tana jinjira itama ta zurawa babyn shi a d'an yatsan ta, sannan ta fara k'ok'arin ajiye ta, ji tayi kanta ya wani irin sarawa, cikin sakannin da basu wuce 30 ba taji kanta yayi mata wani gingirin, gaba d'aya tunanin ta ya tsaya cakkk, kamar wadda ake ja haka ta mik'e ta sa6a jinjirar a bayan ta, sannan ta fara takawa zuwa k'ofar d'akin, a parlour Ummi ta ganta ta fito sa6e da jinjira ce ko jinjira ita dae bata sani ba, seta shek'e da dariya tana fad'in

"An fito kenan, toh Allah ya raka taki gona kinji" ta k'arasa fad'a cike sa izgili, Ammi kuwa kawae tafiya take yi a haka harta fice daga gidan, tafiya kawae take yi dan gaba d'aya bata cikin hankalin ta, kawae tafiya take yi bata sanin inda take tafiya har duhu ya farayi, bata saurara da tafiyar ba kuma duk nisan tafiyar da tayi ba taji ta gaji ba, haka ta cigaba da tafiya har zuwa sanda asuba ta fara gabatowa, mutanen dake wucewa wasu su kalle ta wasu kuma su wuce tunda babu wani abu daya nuna yanayin hauka a tattare da ita ballantana wasu su mata kallan mahaukaciya, haka ta cigaba da tafiya....


Daga nan kuma Cigaban yana PAGE 1.. Zamu d'ora ne daga inda aka kad'e Ammi........



08124818273

✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION43*



___Da sauri yayi parking motar ya fito daga ciki yana kallan Ammin daya kad'e wadda ke kwance kamar matacciya, ya juya ya juya bega kowa ba haka kuma be ji motsin mutane ba dan haka kawae ya d'auke ta ya sanya ta cikin motar tasa 'kirar taxi, ya tashi motar ya cigaba da tafiya da sauri har ya isa wani asibiti, nan aka shiga duba ta, ba wani rauni tayi ba dan haka dressing kawae suka yi mata suka sallame ta, a lokacin ne Abbu (Baban su Zarah da Abunnas) ya fahimci kamar wani abun ne ya samu Ammi kuma kamar tana da ta6uwar k'wak'walwa dan kuwa bata umm bata umm umm se dae kawae ta k'urawa waje 1 idanu tayi shiru, haka ya d'auke ta ya tafi da ita gidan su wanda anan shima yake tare da matarsa da er sa guda d'aya Zarah, baban sa babban malami ne wanda ke tare da almajirae, dan haka sanda Abbun yaje masa da maganar Ammi akan kad'e ta da yayi da kuma k'ok'arin maeda ta gida da yayi ya fahimci kamar akwae motsuwar k'wak'walwa a tare da ita, abinda dae be sani ba shine dama tana tare da hakan ne ko kuma yanzu a kad'e tan da yayi ne ta samu, baban nasa na ganin ta ya gane asiri ke aeki a jikin ta dan haka bek'i kar6ar ta cikin gidan nasa ba, aka mata masauki, anan ne mahaefiyar sa ta gane haehuwa Ammin tayi nan ta dinga mata abinda ya kamata wanda akewa me jego, amma fa tsoro ya kama su dan da alama raba ta akayi da abinda ta haefa a ranar data haefe shi, haka dae har ta samu ta warke sosae daga ciwon haehuwa, sannan baban Abbu ya fara mata addu'o'i da rubuce rubuce da sauran su, cikin ikon Allah kuwa cikin abinda be wuce wata 5 ba Ammi ta fara magana kad'an kad'an, cikin hakan ne suka sake fahimtar Ammin ta manta wacece ita, wato ma'ana ta manta da abinda ya faru a rayuwar ta ta baya, haka suka cigaba da kasancewa cikin gidan, dukkan su suka cigaba da yiwa Ammi addu'a akan Allah ya dawo da ita cikin hayyacin ta su samu su maeda ta cikin en uwan ta, har lokacin da Allah ya horewa Abbu yayi gidan sa anan cikin garin kano, a lokacin da suka fara k'ok'arin tashi daga gidan nan nasu a cikin tsukun ne kuma Allah yayi wa Baban Abbu rasuwa, haka akayi zaman makoki sannan bayan wani lokaci gaba d'ayan su suka koma sabon gidan Abbun da zama, a 6angaren babar Abbu anan Ammi ke zaune, tun tashin Zarah tayi wani mugun sabo da Ammi dan seki rantse idan baki sani ba kice Ammi ce ta haefi Zarah, Zarahn ce ma ta saka mata suna Ammi...


... A d'aya 6angaren kuwa Dad ya samarwa Mom aeki a wani asibiti, anan ne ta fara tunanin yadda zata yi da kula da Adnan, tunda dae baze yiwu ta dank'awa kishiya komae ba, sanda ta nunawa Dad tana buk'atar er aeki ko daga cikin dangin su ne da suke a k'auye se Mami ta nuna 6acin ran ta akan hakan

"Gaskiya banji dad'in hakan da kike cewa ba, ae se naga kamar na gaza ne, ni me nake yi a cikin gidan? Mene amfani na idan ban kula da Son ba?" Mom ta girgiza kae tace

"Ba haka bane, bana so na d'ora miki nauyi ne sosae" Mami ta sake 6ata rae kamar gaske tace

"Ae idan da kin d'auke ni kamar wadda na haefi Son baza kice haka ba" Mom tayi murmushi sannan tace

"A'ah ba haka bane, kawae dae zan sama masa ko me masa girki ne in yaso kema seki huta.." Dad yace

"Ya isa haka, ke za'a samo miki er aekin, ke kuma se ki cigaba da kula da harkokin sa na cikin gida shikenan koh?" Mami taji kamar ta shak'e Mom dan haushi, haka dae aka cigaba da tafiya, daga nan ne Dad ya sanarwa da me gadin sa zancen neman er aekin da suke, shi kuma ya sanarwa da gidajen dake kusa dasu na masu k'aramin k'arfi, anan ne Ammi taji zancen, nan ta sanarwa dasu Abbu zancen son yin aekin, Abbu yace shi kam a'ah base taje ko'ina tayi aeki ba basa buk'atar wani abu, nan take nuna masa ba dan wani abun zatayi aekin ba, kawae dae zaman gidan na mata yawa ne shiyasa, seda maman sa ta saka baki sannan ya amince da hakan ba dan yaso ba, ba tun yau ba Abbu ya nuna sha'awar auren Ammi amma haka kawae taji bata da sha'awar yin wani aure wanda bata san dalilin ta na yin hakan ba, Maman sa tace ya k'yale ta tunda bata da ra'ayin auren, haka dae Ammi ta fara zuwa gidan su Don, tun farkon zuwan ta Mom taji Ammi ta burge ta ta kwanta mata a rae, amma bata nuna hakan ba seda ta fara gwada Ammin sosae, ba ita ta fara bata yin girki ba seda ta dad'e sosae a gidan lokacin sun zama tamkar k'awaye dan har sukan bawa junan su shawara, a lokacin ne Ammi ta farawa Adnan girki da yaddar Mom, 6angaren Mami kuwa she's eager Adnan ya cika shekara 10 ta aewatar da nufin ta akan sa, gefe guda kuma tana sake jin haushin yadda ta lura da Ammin tana da amana.. Tafi tafi dae kullum shak'uwa na k'aruwa tsakanin Ammi da Mom har shi kansa Adnan d'in ya d'an fara sakin jiki kad'an da ita.. Ranar juma'a ne Mom ta tashi da ciwon kae na 6ari guda, da k'yar take iya komae cikin k'arfin hali, tunda ta tashi bata fito parlourn ba dama kuma Dad baya garin amma a ranar ze dawo, ta riga da tasan Ammi na nan tana jiran ta, kuma macece me takatsantsan tasan ko menene ba zata ta6a shigo mata cikin d'aki ba, a hankali ta mik'e ta fito zuwa parlourn se dae ga mamakin ta babu kowa cikin parlourn, hakan ya bata mamaki sosae seta taka ta d'an yaye labule kad'an ta lek'a compound d'in gidan sannan ta fara k'ok'arin komawa cikin d'akin

"Wallahi kuwa shegiyar wata matar fa ta samo

Please Login or Register in order to submit comment