Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana kallan ta

"Fito" kallan sa tayi tana jin yadda bugun zuciyar ta ke k'aruwa, waye shi? Ina ya kawo ta nan da zece ta fito? Dan haka shiru ta masa kawae ta cigaba da share k'wallar, zagayowa Irfan yayi ya kalli cikin motar yana sakin wani shu'umin murmushi yana shafa ha6ar sa, yanzu kam kallan sa take sosae tana iya bakin k'ok'arin ta dan tuna inda tasan fuskar amma ta kasa, muryar sa ta katse mata tunani sanda yake fad'in

"Ki fito mana Hajiya" ya fad'a yana matsowa dab da ita, ciki ta matsa da sauri k'irjin ta na bugawa, seya sanya hannun sa yana shirin rik'o ta ta kuwa sake fashewa da kuka cikin rashin sanin abinyi tace

"Karka matso kusa dani"

"Saboda me?" ya fad'a yana d'age girar sa gami da bud'e bakin sa, ba tace komae ba dan gaba d'aya a tsorace take

"Ki fito ki shiga ciki da kanki idan ba haka ba wallahi da kaena zan d'auke ki na shigar dake" ya fad'a yana k'ok'arin shiga cikin motar, seta tura k'ofar dake gefen ta ta zura k'afafun ta ta sauka wani sabon kukan na 6alle mata

"Ki shiga mana Hajiya, ko in d'auke kin ne?" yayi maganar sanda yake sake matsawa dab da ita, Se tayi gaba kawae tana janyo duk addu'ar da tazo bakin ta tana sake jin yadda marar ta ke k'ullewa, D'ayan mutumin ne ya sanya mukulli ya bud'e parlourn suka shiga, Irfan yabi parlourn da kallo yana fad'in

"Wowww, gaskiya fa komae yayi" Komawa tayi waje d'aya ta cure tun tana kuka me sauti harta dena, ta cigaba da addu'a kawae, seda Irfan ya gama kalle kallen sa sannan ya fara rage kayan jikin sa, mutumin ya shek'e da dariya

"A'ah master ae ka bari a shiga ciki koh?" wani murmushi Irfan ya saki kafin yace

"Ba zaka gane yanda na k'agu na fara buga wasa na bane" ya k'arashe maganar sanda ya gama cire rigar jikin sa ya zama daga shi se dogon wando, sannan ya fara takowa zuwa inda take hannun sa d'ore akan tazugen wandon sa yana warwarewa yana fad'in lokaci d'aya

"Ka kullo min k'ofar dan inaga daga nan zamu fara, Hajiyar ce akwae taurin kae da alama" runtse idanun ta tayi a wajen wani sabon kukan da babu sauti na taho mata ta dinga maemaeta "La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin" shin me tayi wa mutanen nan? Me suke shirin aekata mata? Innalillahi wa inna ilaehi rajiun, ji take yi tamkar ta bud'e idanun ta ta ganta cikin kabarin ta, da dae wannan tashin hankalin, wani d'a namiji ke neman tarwatsa mata rayuwa, a matsayin ta na mace, macen ma macen aure, wannan wace irin bak'ar rana ce a wajen ta, kalle kalle ta fara yi gefen ta koda zata samo wani abun daze zama kariya a wajen ta se dae bata hango komae ba dan haka kawae ta mik'e tana kallan Irfan dake sake matsowa kusa da ita. Knocking d'in da aka fara yi ne daga can gate d'in gidan ya sanya Irfan dakatawa daga abinda yake niyyar yi, ya kalli mutumin dake shirin fita yace

"Kamar knocking naji anayi fa?"

"Ba mamaki mak'ota ne suka zata masu gidan na nan, amma bama a cikin satin nan zasu dawo ba" ya bashi amsa yana kallan Irfan d'in

"Ohk ka tabbatar ka fad'a musu masu gidan basa nan" bece komae ba ya fice daga d'akin zuwa compound d'in ya k'arasa wajen gate d'in yace

"Waye?" shiru babu amsa ya sake maemaeta tambayar nan ma shiru, yana shirin juyawa ya koma yaji an sake buga k'ofar hakan ya bashi haushi, dan haka a fusace ya bud'e k'ofar yana fad'in

"Wae uban waye ne haka, kuma anyi magana babu ams.." kafin ya k'arasa fad'a Don ya tunkud'a shi ciki wanda yayi sanadin daya bugu da wani k'aton katako dake ajje a bakin gate d'in, se kuwa ya fad'i k'asa sumamme, cikin sauri Don yayi gaba ya kalli cikin gidan, kae tsaye yayi hanyar daya tabbatar itace ta parlour ya saka hannu ya tura ta cike da hope d'in ganin Azrahn a ciki kuma babu wani abu daya same ta, dae_dae lokacin da Irfan ya gama warware tazugen dogon wandon jikin sa ya fad'i a k'asa sannan ya matsa kusa da ita yana fad'in

"Ki bar gudu na mana baby, yau zan nuna miki nafi mijin ki iya sarrafa mace.." abinda ya sauka a cikin kunnen sa kenan, yayin da idanun sa ma suka sauka kan Irfan da yanzu yake saye da gajeran wando kawae, yayin da Azrah ke gefe tana kuka idanun ta a runtse saboda bata san kallan Irfan d'in a haka, se dae kuma tana bud'ewa saboda kada ta rufe d'in ta tsince shi a kusa da ita, dae_dae lokacin data bud'e idanun ta kamar ance ta d'aga kae idanun ta suka sauka a kansa, seta lumshe ido ta sake bud'ewa a kansa, cikin wani irin gudu da bata san tana da shi ba ta k'arasa inda yake ta rungume shi da iya k'arfin ta tana sake sakin kuka, se a lokacin Irfan ya kae duban sa zuwa wajen, abinda be ta6a tsammani ba, be ta6a zata ba shi ya gani wato Don a tsaye, take jikin sa ya d'auki wata irin rawa har lokacin kallan Don d'in yake yi, shi kam Don gaba d'aya mamaki ya hana shi aekata komae, kamar Irfan yake gani tsaye yana neman ketawa matar sa haddi fa? Irfan ke son raping matar sa ta sunnah? "Ya salaam" ya fad'a yana kae hannun sa zuwa kansa daya sake sara masa, se a lokacin ya fara dawowa hayyacin sa lokacin data rungume shi d'in, seya d'akko duka hannayen sa biyun ya zagaye ta dasu ya rik'e ta tsam a jikin sa yana jin yadda take kuka kamar ranta ze fita, sun d'au wajen minti 1 a hakan har seda yaji ta dena kukan sannan ya fara zame ta daga jikin nasa, a hankali ya matsar da ita gefe se dae har lokacin bata bar sheshshek'a ba, ya kalli inda Irfan yake a tsaye ya gama rikicewa haka zalika ya kasa ta6uka komae, ilahirin jikin sa rawa yake yi, a hankali ya fara takawa zuwa inda Irfan d'in ke tsaye duk da jirin da yake ji yana d'iban sa, kansa na sara masa, haka har lokacin bugun zuciyar sa yak'i dawowa dae_dae, Irfan kam ya kasa cewa koma se rarraba idanu yake yi dan gaba d'aya ya gama rikicewa, a hankali ya fara magana cikin karyayyiyar murya wadda seka rantse ba tasa bace

"Irfan da gaske kae d'in ne?" ya fad'a yana sake runtse idanun sa ya bud'e a lokaci guda sannan yace yana sake matsawa kusa da Irfan d'in

"Meyasa kake so ka aekatamin hakan..?" ya k'arasa fad'a cikin d'aga murya yana kae hannun sa wuyan Irfan ya shak'o shi sosae, sosae Irfan yaji damk'ar daya masa take idanun sa suka raena fata, ya rik'o hannun Don yana girgiza kae, be k'yale shi ba seda yaji ya fara kakarin mutuwa sannan ya sake shi da k'arfi ya fad'i wajen kana ya sake kae masa wani dukan, seda yaga yayi laga laga sannan ya tashi yace har lokacin muryar sa bata koma dae_dae ba amma yanzun cikin zafi yake yinta

"Duk rashin mutuncin da kake ka rasa akanwa zaka yi shi se akan matata? Gona ta zaka shiga Irfan? Me nayi maka a rayuwa kae kuwa? Na baka duk wata yadda da amana ta meyasa kaci amana ta? Meyasa Irfan?" Ya k'arasa maganar a nutse kuma a hankali sa6anin yadda ya fara da farko, sosae zuciyar sa ke masa zafi haka kuma tana bugawa da wani irin gudu daya wuce na misali, ya sake runtse ido yana tuna a yadda ya shigo ya samu Irfan d'in, ya bud'e da sauri yana sake matsawa ya kaewa Irfan duka a baki wanda yayi sanadin da bakin nasa ya fashe ya fara zubar da jini, sannan yace

"Ni zaka ci amana? Ni zaka yaudara?" Hannun sa ya kae kan bakin nasa ya shafo jinin bakin sa a lokacin ya kasa tsaeda hawayen azabar da yaji yace yana kallan Don d'in

"Ni ba yaudarar ka nayi ba, ae ka riga kasan na dad'e ina son nayi tarayya da yarinyar nan, amma bayan tafiya ta kayi yadda zaka yi ka aure ta, na kasa jurewa shiyasa na aekata hakan dan na kasance da ita" hakan daya fad'a ba k'aramin tunzura Don yayi ba, wato fansa yake nufin ze d'auka a kansa? Lallae kuwa zeyi dana sani

"Zakwa kayi dana sanin niyyar shiga gona ta da kayi, and daga yau ka manta cewar kasan wani me suna Adnan ballantana kuma akae gani, u're nothing but a green snake under green grass, nayi nadamar sanin ka a rayuwa ta, sannan ka sani dole seka girbi abinda ka shuka kafi kowa sanin wane ni.. " daga haka ya juya ya bar Irfan a zaune da fashashshen baki hannun sa rik'e da wuyan sa, tana tsaye har lokacin tana kuka, a hankali ya kae hannun sa ya rik'o nata hannun ya jata zuwa cikin jikin sa, babu musu tayi shiru kawae, a haka har suka fita daga d'akin sannan Don ya kulle k'ofar da mukulli kana ya ajje shi a k'asa, ya zaro wayar sa dake aljihun sa yayi kira na tsawon mintuna 2 sannan ya cigaba da takawa zuwa waje har lokacin tana jikin sa dan gaba d'aya har lokacin a rud'e take, seda ya saka hannu ya bud'e wajen me zaman banza ya sanya ta ciki sannan ya koma ya bud'e driver seat ya shiga ya zauna yana lumshe idanun sa, shi kad'ae yasan abinda yake ji a cikin jikin sa, lamarin duniyar ya fara bashi tsoro, abubuwa se faruwa suke yi dashi suna zuwar masa a bazata, mutane 2 da yafi yadda dasu sunci amanar sa, meyasa haka? "Ya salaam" shiru yayi bayan zaman sa cikin motar ya tashe ta amma be tafi ba, ita kam tana zaune cikin kujerar ta cure waje d'aya amma ba kuka take ba se dae ita kad'ae tasan yadda marar ta ke mata zafi, kamar ana kartar ta, suna nan zaune wata mota ta shigo cikin layin, hannu kawae ya d'agawa na cikin motar sannan yaja tasa motar ba tare da yace komae ba ya hau kan titi, lokaci lokaci ya kan runtse idanun sa har lokacin zuciyar sa wani irin zafi take yi, can ta d'ago jajayen idanun ta ta kalli inda yake seta mayar har lokacin hannun ta na rik'e da cikin ta, haka suka cigaba da tafiya, jefi jefi takan d'aga idanu ta kalle shi yadda yake ta faman lumshe ido kamar wanda yasha wani abun maye, daga yanayin yadda yake tuk'in a hankali kawae zaka fahimci akwae wani abun da yake damun sa, wani irin murd'awa da marar ta ta sake yi ne ya tilasta mata sakin k'arar da bata shirya ba, da sauri ya juya ya kalle ta yana sake jin wani tsoron na kamashi, kada dae Irfan ya mata wani abun? Ya sake kallan ta yadda take yarfe d'ayan hannun ta yayin da d'ayan ke kan cikin ta tana kuka hawaye na zuba akan kuncin ta, gangarawa yayi gefen titin ya kashe motar gaba d'aya, sannan ya kae hannu ya rik'ota yana fad'in a cunkushe

"Meya faru?" bata iya cewa komae ba se hawayen daya cigaba da sauka akan fuskar ta, dae dae lokacin daya matso da ita dab dashi, ya lura da hannun data rik'e ciki dashi, a hankali ya kae hannun sa kan hannun nata ya sake fad'in

"Meke miki ciwo?" d'ayan hannun nata ta kae da sauri ta rik'o hannun nasa tana girgiza kae wasu sabbin hawayen na tsere akan kuncin ta, hannun data rik'e yabi da kallo yana bin yadda hannun nata yayi wani irin kyau mara misaltuwa cikin ja da bak'in lalle, bata saki hannun ba sema sake rungume shi da tayi a cikin ta tana sakin wasu wahallalen numfarfashi, ya lumshe idanun sa, kawae seya jata cikin jikin sa yayi mata kyakykyawar runguma, aekuwa ta sake rik'e hannun nasa dake cikin nata da k'arfi tana fashewa da wani kukan dan yadda take jin ciwon yau bata ta6a jin koda makamancin sa ba, a hankali ya wara lumsassun idanun sa akanta yana mamakin abinda ya sameta d'in a hakan, yadda take sake ruk'unk'ume shi sosae kuma tana sake k'ank'ame hannun sa kad'ae ya isa ya nuna maka bata hayyacin ta, seya sake k'arfin halin fad'in da muryar sa da bata fita sosae a saetin kunnen ta

"Meke miki ciwo?" dae_dae lokacin data saki wani numfashi, a hankali ya kae hannun sa ya d'ago ta dae _dae sanda ta biyo hannun nasa, cikin tashin hankali ya sake kallan fuskar ta ta da idanun ta ke a lumshe ya zame hannun sa dake cikin nata ya shafi lallausar fuskar ta amma bega tayi wani abun da zesa ya fahimci tana tare dashi ba, zuciyar sa ta buga da k'arfin gaske kafin ya kalli titi seya maeda ta ya kwantar da ita a jikin sa sannan ya tashi motar da gudu, duk yadda yake ji a jikin sa se yaji wannan tashin hankalin yafi d'aga masa hankali

"Wallahi sena yi kisa idan har wani abun ya same ki" ya fad'a a raunane kuma da kaurin murya yana runtse idanun sa....



✨MHIZ INNOCENT✨
*SKTHECONCLUSION51*



___Yana driving d'in yana sake jin gaba d'aya zuciyar sa a cunkushe a haka har ya k'arasa asibiti, ya sauke ta daga jikin sa sannan ya kukkule motar da sauri kana ya d'auke ta kamar baby zuwa ciki har lokacin idanun sa na kan kyakykyawar fuskar ta, be jira ba kawae ya shigar da ita d'akin da likita ke duba marasa lafiya ya dire ta akan gadon sannan ya watsawa likitan jajayen idanun sa yace

"Pls doctor ki duba min ita.." ya fad'a muryar sa ciki ciki, tashi likitan tayi ta k'arasa inda Azrahn take tayi dube duben ta sannan ta koma ta d'auko wani rubber water dake ajje akan kujerar ta ta k'arasa ta zubo shi a hannun ta sannan ta shafa mata a fuska, nan da nan kuwa ta fara alamun bud'e idanun ta, zara zaran gashin idanun ta nata motsi se kuma ta bud'e su tarr, wata gauruwar ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe idanun sa, likitan ta rik'o ta sosae a hannun ta ta taemaka mata ta tashi zaune, hannun dake rik'e da cikin ta ta kalla sannan tace

"Meke damun ki dear?" ta fad'a tana jin yadda jikin Azrahn yayi zafi, kallan ta Azrah tayi, se a lokacin ta lura da wanda ke tsaye a cikin d'akin yana kallan su, tayi saurin d'auke kae sannan tace a hankali

"Ciki na ke ciwo!" Likitan tace

"Bayan shi fa?"

"Zazza6i.." ta fad'a tana yatsina fuska kuma tana k'ok'arin zamewa ta kwanta akan gadon, juyawa likitan tayi tana kallan Don dake dafe da wani bench idanun sa a lumshe yanzu tace

"Amma yalla6ae kaema kana buk'atar a duba ka fa"

"Babu buk'ata, meke damun ta?"

"Zazza6i ne da ciwon ciki, ina tunanin zamu rik'e ta ko zuwa gobe ne, zan rubuta mata maganguna se ayi k'ok'ari a bata.." kallan inda take ya sake yi sannan yace

"Ohk.." ya fad'a yana k'arasawa wajen da take d'in, nurse likitan ta tura aka kira mata dan ta musu jagora zuwa d'akin da za'a kwantar da Azrahn, ya k'arasa yana kallan ta idanun ta a rufe kafin ya kae hannun sa ya rik'o nata, da sauri ta bud'e idanun ta ta fara k'ok'arin zame hannun nata, sedae ya d'auke kansa daga kallan ta ya kuma rik'e hannun gam sannan ya mik'ar da ita zuwa d'akin, seta hak'ura kawae ta bishi har zuwa d'akin ya zaunar da ita akan gadon, mazewa kawae take yi amma tana ji a jikin ta ko hijab d'in jikin ta be 6aci ba toh fa tasan kayan jikin ta sun 6aci, ya nemi waje ya zauna gefe yana kallan ta yace

"Ba abinda ke miki ciwo?" ita duk banbarakwae take ji idan yana mata irin wannan abubuwan, dan haka ta d'an saci kallan sa kawae ta maeda kanta k'asa, ya lumshe ido kawae kafin ya mik'e ya fice daga d'akin.. Wayar sa ya zaro ya danno number Ammi bugu 2 ta d'auka ko iya gaeshe ta beyi ba yace

"Ammi..muna asibiti an kwantar da Azrah..!"

"Ya salaam" Ammi ta fad'a tana mik'ewa tsaye, bata iya tambayar meke damun ta ba kawae ta tambaye shi sunan asibitin, ya sanar da ita sannan ta katse wayar, addu'a kawae take a cikin ranta tana tunanin abinda ya samu d'iyar ta ta, kenan Ummu ta sani tunda dae tana gidan Ummun, dan haka kawae d'aki ta shiga ta d'an d'auko kaya da wasu abubuwan buk'ata ta fito.. Sanda ta isa yana cikin d'akin a zaune yayi shiru kamar me tunani ya k'urawa Azrah idanu kamar ze cinye ta, ita kuwa bacci take hankalin ta kwance, Ammi ta k'arasa da sallama, se a lokacin ya d'aga idanun sa ya kalli Ammin, sannan suka sake gaesawa kana tace tana kallan sa

"Kamar kaema baka da lafiya, ya kamata kaje ka huta, Ummu ta fita ne?" girgiza kae yayi kana yace

"A'ah basu sani ba" da mamaki ta kalle shi amma bata tambaye shi ba tace

"Toh kaje ka huta dae.." babu musu ya mik'e, ya sake kallan ta sannan ya lumshe idanun sa yana yin gaba, Ammi ta bishi da kallo har ya fice sannan ta dawo da duban ta kan d'iyar ta ta dake kwance tana bacci amma hannun ta nakan cikin ta, tayi wani shahararren kyau tayi fresh da ita, Ammi ta k'arasa ta rik'o hannun nata, se kuwa ta farka da sauri, ganin Ammin ya sake karyar mata da zuciya aekam ta fashe da kuka

"A'ah meya faru kuma? Meye na kukan?" bata iya cewa komae ba tayi shiru tana cigaba da sheshshek'a

"Meke damun ki?"

"Ammi mara ta ke ciwo, kuma zazzabi ke a jiki na"

"Toh sannu kinji, zaki warke In Sha Allah" se a lokacin Ammi ta lura da 6acin da hijab d'in Azrah d'in yayi dan haka babu 6ata lokaci ta fita daga d'akin taje ta samo duk abin buk'ata kana ta dawo ta sanya Azrahn a gaba ta gyara jikin ta tass sannan ta koma ta kwanta, dae_dae nan wata nurse ta shigo da leda a hannun ta ta mik'awa Ammi tace

"Gashi yalla6ae yace a kawo nan" kar6a Ammi tayi gami da godiya sannan ta kalli Azrah data runtse idanun ta sosae saboda jin an ambaci maganin, Ammi tace

"Tashi ki sha maganin seki koma baccin" tayi shiru tana jin kamar ta fashe da kuka, ganin kamar baccin ya d'auke ta ya sanya Ammi k'yale ta idan ta tashin seta sha.



..."Baze yiwu dan ina zaune a gidan ki ki dinga min abinda kika ga dama ba, haka kawae toh wallahi kije ke da Allah amma ban yafe miki ba" Mami ta fad'a tana k'arasa shirya kayan ta

"Kya dae ji dashi, tunda dae ni nasan bani ce nake d'auke miki kaya ba, gwara dama kiyi maza ki tattara yanaki yanaki ki bar min gida ahtohh" Hajja Kaltum ta fad'a cikin kumfar baki, k'arasa had'a kayan ta Mami tayi sannan taja akwatin ta kana ta juya ta kalli Hajja Kaltum

"Dan babu kud'i a hannu na ne yanzu, kuma ina da abubuwa masu muhimmanci da zan gabatar banda haka wallahi sena shigar dake k'ara, amma duk da haka kema ki jira sakamakon ki" daga haka taja akwatin ta ta fice daga d'akin, Hajja Kaltum tace

"Ehh ba komae, kedae kika sani aje can a k'arata nima na huta".. Kae tsaye Mami gidan su Simrah ta wuce ta tura k'ofar parlourn da sallama a bakin ta tana tura akwatin hannun ta, Momy dake zaune ta mik'e tana fad'in

"Toh fa, ni ameena me zan gani haka? Matar Alhaji Kabeer ce ta koma haka?" ta fad'a da izgili, Mami ta k'arasa tana kallan ta tace

"Tunda kinyi sanadiyyar da kika raba ni da gidan aure na, toh gani nazo gidan ki zan cigaba da zama tunda dae kinsan bani da wajen zuwa daya wuce nan d'in" dariya Momy tayi kana tace

"A da ba, a da mana, da kin amince mun had'a kae munci arzik'i tare toh da idan ta kwa6e dake nime iya taemaka miki ce, amma fa nunawa kikayi bakya sona da arzik'i, bakya so mu dandali arzik'in da kike ciki, yanzu kuma ta kwa6e miki kizo waje na? A'ah wallahi" ta fad'a tana yatsina fuska, Mami ta girgiza kae kamar zata yi kuka

"Amma dae kinsan ta dalilin ki aurena ya mutu koh?"

"A'ah ke bari mana, ya haka? Dama ae kinsan rana dubu ta 6arawo rana d'aya takk tame kaya, toh kamar haka ne ya faru, gashi nan don Allah idan kin gama abinda kike yi kya d'auka kiyi kud'in mota" Momy ta fad'a bayan ta ajje wata 500 akan kujera, kud'in Mami tabi da kallo tana jin ciwo a cikin zuciyar ta, ganin Momy na shirin wucewa d'aki ya sanya ta fad'in

"Don Allah ki aramin wayar ki zan kira Fawaz"

"Toh wannan kam zan iya yi miki shi" Momy ta fad'a tana dawowa ta mik'a mata wayar, kar6a Mami tayi ta danno number Fawaz d'in yana d'agawa Mami ta fashe da kuka, seya mik'e tsaye daga inda yake yace

"Mami.."

"Fawaz nifa uwar kace Fawaz, yanzu k'yaleni da kae baka tunanin Allah ya kama ka?" girgiza kae yayi k'walla na taruwa a idanun sa yace

"A'ah Mami, bansan yadda zanyi bane wallahi, kiyi hak'uri don Allah"

"Shikenan, a'ina zamu had'u ka kawo min ATM d'ina da waya ta?" Fawaz yace

"Mami wallahi Dad ya kar6e duka"

"Innalillahi wa inna ilaehi rajiun, shikenan nikam na shiga 3, ya zanyi da rayuwa ta ni ennan" ta fad'a tana sauke wayar daga kunnen ta, Momy ta kar6i wayar sannan tace

"Toh Allah dae ya yafe mana, yanzu dae kinga kamar ba'a yi Habeeba ba" Da sauri Mami ta d'aga kae ta dubi Momy sannan tace cikin k'arfin hali

"Wace Habeeban? Meya same ta?"

"Kar kice min baki san Habeeba ta rasu ba?"

"Innalillahi wa inna ilaehi rajiun" Mami ta fad'a tana komawa tayi zaman da6aro a k'asan tiles d'in d'akin, se kuma kuka ya 6alle mata, ta dinga yi babu k'akk'autawa tana maemaeta istighfari, hak'ik'a tsoro ya sake shigar ta sosae da sosae, Habeeba ta rasu fa? Mik'ewa tayi tana share hawayen ta ta kalli Momy tace

"Zanje na nemi yafiyar mutanen dana cuta koda kuwa babu wanda ze taemaka min, fata na kawae shine su yafe min" Momy tace

"Toh Allah yasa su yafe d'in" ita dae Mami bata jira ta sake cewa komae ba ta fice daga d'akin.


... Kwanan Azrah 2 a asibitin, Ummu ko Ammi ke kula da ita, yayin da Don kullum se yazo safe da dare, ita dae bata ko d'aga kae ta kalle shi ballantana wata magana ta had'asu, shi kam ze zauna yayi ta kallan ta yana jin k'aunar ta na k'ara ratsa shi kamar ze maeda ta cikin sa, tun Ammi na fad'a harta gaji ta zubawa sarautar Allah ido, dan lamarin Azrahn se addu'a, ranar aka sallame su suka tattara zuwa gida, Ammi ta kalli Ummu tace

"Bana so yarinyar nan ta k'ara kwana a gidan nan don Allah ki shirya ta a maeda ta d'akin ta" wannan karan babu musu Ummu ta amsa da "toh" sannan ta wuce d'akin da Azrah d'in take, tana toilet da alama wanka take yi, ganin ta dad'e a wankan ya sanya Ummu fita daga d'akin, wajen minti 10 se gata ta dawo ta nemi waje ta zauna tana jiran fitowar ta ta, Ummu na zaune kan gadon sanda ta fito daga toilet d'in ta mik'e tana kallan ta tace

"Kina sallah ne?" tambayar Ummun ta bata kunya dan haka tayi k'asa da kanta tana wasa da yatsan ta kana ta d'aga kae tace a hankali

"Yanzu dae zanyi"

"Yawwah" Ummu ta fad'a tana ficewa daga d'akin, binta da kallo tayi tana mamakin abinda yasa ta tambayetan, seta koma ta zauna kan stool d'in gaban mirror ta fara shafa maya mayan ta, tana nan zaune Ummu ta sake turo k'ofar d'akin ta shigo hannun ta d'auke da kaskon turaren wuta da wata kujera, turo baki tayi tana d'auke kae dan ta gane meye wannan d'in, ita kuma harga Allah ta gaji, Ummu ta

Please Login or Register in order to submit comment