Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZANBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


ECRITE:


_PAR_


*QUEEN ZEEFAT*


Yar
Mutan
Niger


Wattpad@nazhabibou

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_BISMILAHIR RAHAMANIR



Page 1



Dandanzon matasa ne maza da mata ke fitowa daga cikin wata babba kofa wada a samata aka rubuta *LYCEE TECHNIQUE DAN KASAWA DE MARADI* hakan ya nuna cewa makarantar boko ce gashi kuma kowane matashi da jakar makarantar sa a baya wasu kuma a hannu kowa sai kama gaban shi yake sanadi tashi da akayi daga makarantar, wata yarinya ce ke tafowa tana nufo kofar makarantar hannun rike da wata farar takarda da jikar makarantar a dayan hannu sanye take cikin dongon hijabin ta har kasa da nikaf a fuskar wada ko eyes inta ba'a gani don fuska rufe take gaba daya ga safa da take sanye da ita ta hannu da ta kafa duka ilahirin jikinta rufe yake babu abinda ake gani, tana tafiyar ta mai kama da hawainiya cikin kwonciyar hakali da nutsuwa kamar mejin tausayin kasa a haka har ta kawo baki kofar makarantar tayi wajan wani shago dake gefan makarantar mai shagon dake zaune daga daya bangaren shagon yana ganin ta ya taso yace malama mikike bukata banji mitace ba sai gani nayi ta mika masa takarda hanuta ya karba yayi cikin shagon da takadar a hannu sa ba'a fi minti biyu ba sai gashi ya fito daga shagon ya mika mata takarda biyu a maimakon guda da tabasa karba tayi ta bude jakar makarantar ta fido kudi ta mika masa ta juya takoma cikin makarantar da takardun a hannu ta daidai wani office ta tsaya ta kwonkwasa sai ga wani datijo ya fito wanda baza ya fuce 50 years tadan rusuna ta mika masa daya takardar ta juya da dayar wajan parking space dake cikin makarantar ta nufa tsayawa tayi daidai wata hadadiyar benz kirar mercendy ta bude jakar ta makaranta ta fito da makulin mota budewa tayi tashiga ta tayar da motar tare da barin cikin makarantar a lokacin da daliban dake cikin makarantar basu huce mutun shida sabida kowa ya kama gabansa.

Driving tayi natsawon minti 20 kamin take kawowa wata kayataciyar anguwa daga ganin anguwa ba me yawon mutane bace sabida yanayin ta ya nuna hakan ga wani hadadan kuma babban filin ball daya ya karama anguwar kyau macha allah
Wajan wasu mayan tsararu kuma kayatacin gidaje guda biyu dake irin daya naga ta nufa komin su gidajan irin dayane sedai guda yafi guda girma shima ba sosai ba wanda ya fi girma a cikin gidajen ta nufa tana dana hon mai gadi ya wangale mata tagamemiyar porte (get) in gidan ta tura hancin motar ta a ciki, tsaruwa haduwa kayatuwa kai yayine gidan karsha ne wajan haduwa babu abinda ba na rayuwa a gidan parking space kadai ma na gidan abin kalon to baran tanama farfajiyar gidan

Parking in motar tayi a parking space dake cike da motoci sun kai kala 10 ta fito daga cikin motar ta kule tareda fitowa daga parking space in tayi hanyar shiga gidan, gidan dauke yake da sashe guda uku daya a gefen hagon gudan a kefan dama se dayan natsakiya kuma shine bangare mafi girma da ke cikin gidan hanyar babban bangaren tanufa tare da murda wata daleliyar kofar da zata sadaka da falon gidan shiga tayi hade da salama a bakin ta wada in ba kusa kake da itaba ba zaka taba jin abinda ta fada wooow nace tare da furta allah sarkin dadi inji barawon takanda lokacin dana tsintsi kaina a wani katarfaran falon da ya tsaru iya tsaruwa komi na falon brown and milk color ne, falon dauke yake da bedroom guda biyar da cuisine (kitchen) guda se set uku na kayatatun kujeru sabida girman falon da dan madaidaicin table central (center table)milk color shi ba babba ba shiba karami ba wanda ya kawata tsakiyar kujerun se TV stone dake jikin bangon falon akasa tare da wata tangamemiyar TV dake manne a bango babu ce kadai ha babu a ciki ga wani kayatacen kamshi dake tashi a falon mara misali
sabida shagalta danayi wajan kalon tsaruwar falon har na manta da rahoto nake dauko maku falon ne ya tsaru irin tsaruwar da ban taba gani irinta ba sai a TV

Babu kowa a falon hakan yasa ta nufi kofar daya daga cikin bedroom din dake falon ta mudar kofar tashiga da kafar dama hade da yar siririyar salama a bakinta wani ni'imtacan kamshi mara misiltuwa ya daki hancina nace macha allah, babu wani tarkace a ciki amma ya hadu daga bed da wardrobe sai dressing miror da kujera babba guda dake gefe sai douche interne (bathroom) da abin ajiyar jaka kusa da armoir (wardrobe ) da abin rataye kaya da ke manne da bangon dakin sai agogo itama manne a can saman bango babu abinda babu a cikin na more rayuwa kana ganin yanayi dakin zaka gane na yan mata ne daki dai macha allah

Tana karasa shiga dakin taje dan gaba da kofar dakin tacire takalmin dake kafarta ta juya tayi bakin gadon dake cikin dakin ta zauna ta cire nikaf da hijabin da ke jikin tare da cire safar hannu ta da ta kafa ta mike tare da nufar wardrobe ta bude ta ciro serviette (tawel) juyowa tayi da niyar nufar hayar toillet take nan takardata da biro dake hannu na suka subice min la'illaha illa anta subhanaka inni kuntum bina zalim ku kuke ganimu bamu muke ganin kuba na furta tare dajan baya da karfi sanadiyar tozalin da nayi da kyakyawar fuskarta juyawa tayi tare da shigewarta toillet da sauri nayi wajan peper da biro na dan na dan labarta ma masu karatu haduwar yarinyar da kyau dinta bai musultuwa banta ganin kyau irin nataba ko acikin larabawa da turawa

Yarinya yace da bazata fuce 18 years ba dogowa amma ba can ba tsayin ta daidai da ita siririya ce amma ba sosai ba ita ba fara ba kuma ba za'a sanyata a layin bakake ba yarinyar cafΓ© au lait ce (shacolate in milk color) irin black americain din nan ce idan kanganta a kusa da wani black americain din ita zaka iya cewa tanada haske amma ba sosai ba da kaire mutun zai tantance kalar fatar ta ma saidai a kimanta gashi girar ta ya kwanta luf luf sai sheki yake da daradaran idanun ta farare tas dasu se bakin da ke cikin idanu ita nata brown ne mai kamar baki da zarazaran gashi idanuta tsaf dasu sai dogon hancin ta har baka da dan karamin bakinta da ya karama fusakar kyau da sheki allah ya mata kyau na gasken gaske baza taba iya musulta kyau irin nata sedai a kiman tashi shima sabida du yanda zaku misilta ta tafi da hakanan

Turo kofar toillet din tayi ta fito daure da tawel da ya sauko mata har ga gwiwa sanan da daya kuma a saman kanta ga ma zauna da allah ya azirtata dasu kamar ba na karamar yarinyar yar shekara 18 ba wajan dressing mirror tanufa ta ja dan taburan ta zauna mika hannu tayi saman dressing mirror din ta dauko wasu hadadun turare guda uku irin na shafawa ajiki ta shafe jikinta gaba daya dake da damshin ruwa kafin ruwan su tsane a jikin ta janye tawel din dake saman kanta saiga gashi ta ya bayana wanda yake dogon baki kirin dashi daga zaune da take gashi yakai har kusa da ma zaunanta da kadan bai ida tabo suba ta dauki abin busar da gashi tana busar dashi da ya bushe ta dauki man kai mai kyau ta shafa masa tare da daukar mashaci ta shace gashin take gashi ya gara kyau da sheki ta dauki shoushou (ribon) zatasa saka ta kasa sabida yawa da tsayin gashi baza iya daure shiba tayi tayi ta kasa a haka ta hakura ta barshi zube a bayan ta tashi tayi ta nufi wardrobe ta fido wata hadadiyar doguwa riga mara nauhi baka mai ratsin ja tasaka tare da dauko hijab da darduma ta rufe wardrobe komawa tayi wajan dressing mirror din ta feshe jikinta da dadadan turare na fesawa mai kamshin gaske tsakiya dakin ta dawo tashinfida darduma tasaka hijab tare da tayar da salllah.
Tana idar da sallah tayi adu'o inta ta mike ta linke dardumar da hijab sanan ta mayar dasu inda suke komin ta cikin tsari nutsawa da kwonciyar hankali take yinshi ta dauko dan kwalin rigar dake saman gado ta aza a saman kanta daya rufe duka ilahirin kanta sai dan jelar gashi daya fito a bayan ta da ya kusa tabo mazaunan ta komawa tayi wajan dressing mirror din ta dauko ribon din ta fita daga cikin bazata



CommentΓ©

Et

partager


Comments

And

share
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZANBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


ECRITE:


_PAR_


*QUEEN
ZEEFAT*


Yar
Mutan
Niger


Wattpad@nazhabibou




πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_ BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM




Page 2



tana fita daga dakin ta nufi stairs dake dauke da bedroom uku dakin dake gefen dama ta murda ta shiga da salama, wata mata ce da ba zata fuce 45 ans (years) ba fara tass da ita kamar ka kwontala jini ya fito matar tayi masifar haduwa kana kalon fuskar ta zaka hango muguwar kamar da suke sosai da yarinyar sedai sosai tafi yarinyar haske amma yarinyar ta fita kyau nesa ba kusa amma kana ganin ta zakasan cewa mahaifiyar tace sabida kamar da suke dakin mahaifiyar tata shima yayi matukar haduwa masha Allah




Murmushi ne dauke ga fuskar mahaifiyar tata ta lokacin da ta dago tana mai amsa mata salama oyoyo AFREEN dina diyar albarka karaso ki zauna wada aka kira da AFREEN ta karaso ta zauna kusa da mahaifiyar ta da murmushi a fuskar tace Maman sannu da gida yawa AFREEN ya akayi yau kuka jima baku taso daga makaranta tunda zu nike falon kasa inajiran zuwan ki har nagaji da zama na taso na tafowa ta daki dan nayi sallah danaga lokaci yayi, AFREEN tace wly Maman wani exercise ne mukayi na mass mai wahalar gaske duk ya caza mana kwakwalwa sai fah 12:30 muka fito daga aji kuma sai na karbi peper excercise din ga malamin mu nayi copin ta a wani shago da ke jikin ecole (school)din tamu sabida inaso nasake yinta a gida sanan na mayar masa da tasa tarkardar sanan natafo gida da copie din danayi, kamin na nufo gida 12:50 tayi shiyasa gashi har lokacin komawar mu da yamma ya kusa tayi maganar cikin wata irin murya me nuna nutsasiyace yarinyar ce, mahaifiyar tata tace gaskiya kam yanzu karatu se kun kara bada hima sabida kuna shekarar ku ta karshe kinga ga exam din ku na karshan shekara sai kun shirya masa tun yanzu fa ba se lokaci ya kure maka kinga kuma in mutun na son samin cikar burin shi dole sai ya wahala kamin ya ke cin ma nasara dan haka AFREEN a dage da karatu nasan bakida wasa amma akara saman wanda akeyi Allah dai ya taimaka kuma yamaki albarka tace ameen Maman bari naje na kwanta koda na minti 30 kamin lokaci ya karasa yi ta na fadar haka tare da mikewa tsaye maman tace to jeki amma kitabatar da kinyi Sallah kamin ki kwonta tace maman ai har nayi sallah da wanka kamin na shigo nan to madala kinci abinci ma kuwa a'a maman ban jin yunwa AFREEN ta fada a takaice, maman tace ko alama, yama zaki cemin bakin jin yunwa alhalin daga makaranta kike nasa da har kikaje kika dawo baki ci komi ba muje nazu ba miki abinci kici ina aka taba yin karatu ba cin abinci sai mutun ma yakasa gane abinda ake koya masa maman ta fada tana mikewa daga zaman da take ta nufi kofa kamin takai ga fita dakin AFREEN tace to Maman ga ribon ku daure min gashi na ni nakasa amsa ribon din Maman tayi ta daure mata gashi tareda juyawa ta bar daki ba musu AFREEN tabi bayan ta suna sabka down stairs din suka nufi dinning table taja kujera ta zauna maman zata zuba mata abincin tayi maza ta karba tace Maman bari dan Allah zan zuba ma maman ta barmata ta zuba tare da komawa cikin falon ta zauna daya daga cikin kujerun dake falon tana ganin maman tabar dinning ta fara cin abinci, ba dayawa taci ta tashi ta nufi cikin falon tace maman na koshi fah maman tace kedai AFREEN bakya son cin abinci ko??? to tashi ki tafi ki kwanta ki futa amma da dadare sai kinci da yawa to maman insha Allah



Tashi tayi ta nufi dakin ta tana shiga tayi kan gado ta kwanta tare dayin bismillah hade da karanta adu'o in da ake karan tawa idan za'ayi bacci, bata jima da kwanciya ba barci yayi awon gaba da ita.
Maman na zaune a falo tana kalon TV aka bude kofar wani daki wada ke daya daga cikin bedroom din dake falon wata farar mata doguwa mai matsakaicin jiki tafito daga dakin ta karaso cikin falon ta zauna tace Maman fauzia barka da warhaka barka dai umman Zeinab har kin fito tace eh a takaice daganan ba wanda yasake cewa komi falon yayi shiru baka jin motsin Komi tv sunfi minti 10 a wajan kamin ake kara bude wata kofar nan ma dai wata matar ce ta fito ita ba doguwa ba kuma ba gajeriya amma wanan baka ce kuma macha Allah tana na dan jikin amma ba irin mai yawan nan ba, murmushi dauke a fuskar ta karaso falon ta nemi guri ta zauna tare da furta sanun ku da futawa a tare suka juyo suka amsa wada aka kira da Maman fauzia tace Tanti yara yau najiki shuru tun dazu baki fito ba injin dai lafiya tanti yara tace wly Maman fauzia kaina ne naji ya na min ciwo shiyasa amma koda nayi sallah nasha magani wanzu kam da sauki cikin nuna kulawa Maman fauzia tace Allah Sarki da bacci ma kikayi da shikenan da kin tashi sai kiji kin warware tanti yara tace a'a bama sai na kwanta ba yayi sauki ina yata sabida itama nafito Maman fauzia tace Allah kara sauki tana ciki dakin ta tana bacci kin san yau sai kusan 1:00 tazo gida tace wani exercise aka basu mai zafi shiyasa suka jima a makaranta Allah sarki diyata ta kwaso gajiya kenan gashi kuma lokacin komawa na yama yayi Tanti yara tafada hade da daga kanta a saman bangon falon tare da kalon agogon dake manne da bango tace kinga ma har 2:20 tayi bari naje na tasheta kada ta makara Tanti yara tafada tare da mikewa tana mai nufar dakin AFREEN murmushi kawai Maman su fauzia tayi tareda maida hankalin ta ga TV umman Zeinab dake wajan batasa masu baki a maganar suba tabi bayan Tanti yara da harara tace wajan neman a sanka har a manta dakai Allah rabamu da shishigi da cusa kai taja wani dogon tsaki hade da mikewa ta nufi dakin abinta binta da kalo Maman fauzia tayi har ta shige dakin ta banko kofar Maman fauzia ta girgiza kanta tace Allah ya shirya sabida ita yanzu abin umman Zeinab ya daina bata mamaki



Tanti yara nashiga dakin AFREEN bata sameta a ciki ba amma taji kara ruwa a toillet alamun tana ciki hakan yasa ta nemi gefan gado ta zauna tana jiran fitowarta bayan kamar minti 5 da zaman ta aka turo kofar bayin AFREEN dake ciki ta fito daure da da tawel da alma wanka tayi, bata lura da tanti yara dake cikin dakin ba kawai ta nufi wajan dressing mirror ta zauna tana mai tsane jikinta kamar daga sama taji murya Tanti nacewa AFREEN diyata har kin fito da sauri ta juyo ta sauke mayan idanun akan Tanti ta saki wani kayatacan murmushi tare da tasowa ta nufo wajan tanti da sauri tare da rungume ta tace tanti na yanzu nake cewa idan na shirya sai naje wajanki kamin na fuce makaranta sai gashima Allah ya kawomin ke Tanti tayi dariya tare raba jikin da na AFREEN tace kai AFREEN kedai kinki girma dubi fa yanzu da a tsaye nake da kin kayar dani wai yaushe zaki girma ki daina shirme cike da shagaba AFREEN tace wlh tanti nidai bason na wani girma nayi zamana a haka ya fimin tanti ta dafe kanta tace kinji shirmen ko bafa kiyi kiba nake cewa ba a'a nufi na yaushe zakiyi hankali tanti ina fa da hankali kinga fa shekara ta har 18 fah AFREEN ta fada tana mai turo dan karamin bakinta cike da shagwaba to shikenan naji jeki ki shirya ki karasa shiryawa kada kiyin lati AFREEN tace to tashi tayi daga gaban Tantin ta koma ta zauna gaban dressing mirror tafara shafa mai da turare cikin nutsuwa take komi ha ta gama shirya wa cikin wata hadiya doguwa riga ta Atanfa da ta karbi jikin tayi matukar yi mata kyau saka safarta ta hannu da ta kafa tayi tare da dauko dogon hijabin ta tasaka har ya najan kasa taje ta sake bude wardrobe ta ciro nikaf ta ruke a hannu ta juyo wajan tanti da tunda tafara shiryawa take kalonta tace tanti na kamala ajiyar zuciya tanti ta sauke tace waike AFREEN yaushe zaki daina irin wanan shigar haka an ce mutun ko fuskar sa ba ya bari a gani to koni dai ni dake da aure a kaina bana irin wanan shigar taki to wai tayaya wani zai ganki yaji yana sonki har ayi wata maganar aure a cikin wanan shigar du wanda ya ganki zaiyi zaton matar wani baban malami ce ke



AFREEN ta waro idanu ta tareda turo dan garamin bakin ta tace tanti ni ina ruwana da wani kuma nida ke harakar karatu na nidai nafison nayi shigana a haka kofa cikin class bana cire nikaf dina tanti kinga fa shekarana biyu yanzu ina cikin ta uku a school din mu amma bu wanda ya taba ganin fuska na kwanaki da aka kawo mamu wani sabon malami yace dole sai na bude fuska na ko na fitar masa daga aji ni kuma nafita bayan fitana wai yake tambayar yan ajimu wai miyasa bana bude fuskana sukace ce masa suma basu sani ba suma tunda suke basu taba gani fuska na ba ko ance na bude bana budewa sai kawai yace aje acemin na dawo nazo na zauna haka na dawo ajin na zauna ba tareda na fida nikaf din ba amma ana ganin eye dina.



AFREEN tace tanti bari naje kada nayi lati tare da saka takamin a kafarta Tanti tace yi maza ki fuce naga har 2:50 tayi amma yau AFREEN ki ban mamaki yada kika yi magana da yawa haka AFREEN tasaki murmushi tare da bari cikin dakin tanti na biye da ita a baya tace tanti wai ina anti khairat tunda nazo ban ganta ba Maman ki ta aiketa gidan yayar ku amma yanzu ta dawo nasan dai sai kin dawo zaku hadu tanti ta fada AFREEN tace to Tanti dan Allah ki fada ma maman cewa nafuce sabida nayi lati kamin na je saman

Please Login or Register in order to submit comment