Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baki son kwana wajen inna imaan?" Ta make kafada tace "Karfe uku idan ta tashi sai tasan yanda tayi ta tashi mutum, tayi ta masa surutu har sai baccin ya fita idonsa" Yusuf yyi dariya yace "Dole ma gobe ki kwana can tunda Friday ne" Imaan tace "Sai dai kai ka kwana" daga haka ta shige balcony dinsu tana daga masa hannu yyi murmushi yana kallonta yace "Good night" yana wucewa ta shiga ciki ta kulle kofarsu.
"Wannan iskancin da kike ki tafi exams babu karatu baxa ki min shi a gidan nan ba wannan karan" Cewar Ammi kenan tana kashe kayan kallon parlon gaba daya, Imaan ta dinga kallonta kamar xata yi kuka bata dai ce komai ba, Ammi ta nemi waje ta xauna tana danna wayarta, A hankali Imaan tace "Ranan Monday fa ne exams din Ammi, i still have Saturday and Sunday sannan Monday da safe" Ammi tace "Ki tashi ki dau abincin Inna ki kai mata baxa kiyi kallon ba, kuma I promise you har ku gama jarabawan nan baxa ki kunna kayan kallo a gidan nan ba, ko yaushe kika xama dedicated da kallo haka ban sani ba" da mamaki Imaan ke kallonta, can tace "Amma ammi ban taba daukan sama da second position ba fa a schl" Ammi tace "Ur silly First position ba karatu? I want to see ur grade idan kika yi karatu this time around" Imaan ta dauke kai kamar xata yi kuka tace "Ni da ma ba wani kallo nake ba sai lkci lkci kuma da ace 5th nake dauka shine sai ki ce in daina kallo fa Ammi" Ganin kallon da Ammi ke mata ta mike ta sa hularta ta wuce kitchen ta dau abincin inna dake ajiye tun daxu ta fice gidan, har ta isa part din inna ji take kamar ta fashe da kuka, ta bude kofar ta shiga, xaune ta tadda inna da bowl din fura a gabanta ta daura kafa daya kan daya, Yusuf na xaune parlon shi ma da cup din furan a hannunsa, sai Ummi dake shan furan ita ma, Mujaheed dai idonsa na kan tv ga nasa cup din furan a kusa da shi, Inna na ganin Imaan ta daure fuska ta rufe furan gabanta ta mayar bayan ta tace "Ni dai wllh ya kare, ba ruwana sai kun ga mutum da abu ku wani dinga tururuwan xuwa, to duk na rabar..." Imaan ta ajiye abincin hannunta tace "Toh ni ina ruwana da furanki ce maki nayi xan sha?" Inna ta kalli Ummi tace "Ke tashi ki shigar min da abina ciki" Ummi ta mike ta dau furan ta kai daki ta fito, imaan ta turo baki tace "Sai kace nace xan sha" Inna tace "Toh ai sai ki juya ki tafi koh?" Imaan ta ki fita don har ranta take son fura da nonon barin idan inna ce ta dama kuma ita tayi furan da kanta, inna ta kalli na Mujaheed tace "Dama ga wannan Boss din ya ji sha, ko raina wanda na tarfa masa yayi Oho, da yake Rukayya ce tayi min wahalan aikin furan Ahmadu kuma ya siyo min nonon, cewa ma yayi baxai sha ba ki dauka ki sha, Allah yayi da rabon ki" Yusuf yyi yar dariya yana kallon Imaan, Imaan ta saci kallon Mujaheed dake kallon TV har sannan, ta kalli rabin cup din furan kusa da shi, inna tace "Tunda fa aka ji yace baxai sha ba fa baxai sha ba, kawai ki dauka rabon ki ne, don ni bani da wanda xan baki in kwana da yunwa" Imaan tace "Toh wai ni nace maki xan sha ne?" Tana magana tana kallon kofar parlon lkci daya ta suri cup din tayi waje a guje Yusuf ya kyalkyale da dariya don yasan abinda xata yi kenan, Inna ta washe baki tana kallon Mujaheed tace "Allah ya kara" mikewa Mujaheed yyi fuska daure ya bi bayanta, Inna ta rushe da dariya har da kyakyatawa tana kallon Ummi tace "Da dai ki tashi ki kulle min kofa da makulli tunda sun fita" Kafin Imaan ta kai rabin hanya dama gaba daya furan duk ya xube saboda gudun da take, Mujaheed ya cafketa daga karshe ta fasa ihu ta sake cup din hannunta ta kama hannunsa tace "Wayyo Yaya don Allah kayi hakuri inna ce tace in dauka" da mamaki yake kallonta yace "Yaushe na fara wasa da ke gidan nan amma?" Jikinta na rawa tace "Don Allah kayi hakuri Yaya" fuska daure yace "Kiyi providing min furan nan yanxun nan idan ba haka ba wllh kinji na rantse sai na sa ki kuka" ta fashe da kuka amma ba hawaye tace "Yaya bayan kana gani duk ya xube nima ban sha ba, don Allah kayi hakuri xanje waje in siyo maka wllh" ya wani hade fuska yace "Wannan nake so ba na waje ba" ta marairaice tace "Toh yanxu yaya a ina xan samo maka wani, nima fa kaga bata bani ba" ya kalli part din Inna sannan ya kalleta, murya can kasa yace "Kinsan abinda xa ayi yanxu?" Ta kara marairaicewa tana girgixa masa kai, yace "Komawa xa kiyi part dinta ki shiga daki ki fito da bowl din furan da gudu yanda kika fito min da nawa yanxu" ta xaro ido tana kallonsa, sai kuma ta fashe da dariya tace "Yaya kasan baxata bari ba fa" ya hade rai yace "Irin dubaran da kika yi kika fita da nawa haka xaki fito da wancan ma ae" Imaan ta dinga dariya har da kyakyatawa, ya ja kunnenta yace "Baxa ki daina wannan dariyar mahaukatan ba" ta hadiye dariyar da kyar tace "Toh amma tare xa mu sha?" Yace "Eh mana" tana murmushi tace "Toh nasan yanda xan yi" a tare suka koma part din inna ya nuna mata bayan window din bedroom din inna yace "A can xa ki sameni ina jiran ki" tace "Toh" daga haka ya wuce yana waigota, a guje Imaan ta shige parlon inna tana cewa "Wayyo inna kice masa wllh kar ya ta6a ni xan gaya sa da Abba, inna kice kar ya taba ji xan kira daddy na...." Mujaheed yyi murmushi ya koma bayan window din ya tsaya yana shafa kansa, Inna ta mike da sauri kar Imaan ta take ta koma wani wajen ta xauna tace "Fito min daki wllh, ba ruwana ku je can ku karata kar wanda ya dameni, yara dai kamar na jaraba" Imaan da ta shige dakin tuni ta dinga dariya kasa kasa ta dau bowl din furan ta datse murfin yanda idan tana gudu baxai xube ba, ta tattara rigar jikinta tayi saitin bakin kofar fita sannan ta fice a dari da sittin, inna ta kyakkyafta ido don tabbatar da abinda ta gani hannunta amma tuni Imaan har ta fice parlon kamar xata tashi sama, inna ta mike da sauri tace "Isuhu me na gani a hannunta kamar kwanon fura na???" Ummi ta kyalkyale da dariya tace "Wllh shi ne" Yusuf ya fashe da dariya, Inna ta fashe da kuka tana kallonsa. Imaan bata tsaya ba sai da ta isa inda Mujaheed yake jiranta, murmushi yayi ya amshi bowl din yace "Yauwa kinyi kokari" ta washe baki tace "Nagode" ya xauna kan dakali dake wajen ya bude bowl din ya dau ludayin ciki ya juya furan sannan ya fara sha, Imaan ta daina murmushin da take ta durkusa gabansa tace "Yaya kai kadai xaka sha" Ya harareta yace "Toh da ni da wa xa mu sha?" Ta xaro ido tace "Wllh baxan yadda ba ni fa na sha wahala na dakko kaga irin gudun da nayi yanxu ma fa kirjina ciwo yake" banxa yyi da ita yana shan furansa don furan inna ba dai dadi da gardi ba, Ta fashe da kuka tana kallon sa, ya hade rai ya debi rabin ludayin hannunsa ya kai bakinta, ta turo baki tace "Wannan d'an kadan din bayan kai cika wanda xaka sha kake?" Yace "Baxa ki bude bakin ba" ta bude bakin da kyar, ya xuba mata yace "Toh tashi ki tafi" kamar jira take tace "Wllh baxan tafi ba ji fa abinda ka bani bayan ni na sha wahalan daukowa, Allah sai dai ka bani in mayar" Yace "In baki ki gudu da shi gidanku dai" Ta fashe da wani dariya har da kyakyatawa, ya harareta ya ci gaba da shan furan, kamar xata yi kuka tace "Yaya" ya kalleta sannan ya debo furan rabin ludayi ya kai bakinta, kin bude baki tayi tana masa wani kallo, ya kai bakinsa ya shanye, ta fashe da kuka, yayi light murmushi ya kara deba ya kai bakinta, bude bakin tayi ya juye mata, daga nan ya ci gaba da sha bai kara kallonta ba, kiris ya rage ta fashe da kukan gaske, ganin bai san tana yi ba ta fixge ludayin hannunsa, ya wara ido yace "Ke ina wasa da ke ne" ko kallonsa bata yi ba xata diba ganin xai dauke bowl din ta marairaice tace "Don Allah yaya ka bari in sha wllh baxan cika ba" yace "To diba in gani" ta turo baki ta ciko ludayin ta kai baki da sauri, ko shanyewa bata yi ba ya fixge ya juye ragowar a bowl din sannan ya diba ya kai baki, tana ganin haka ta dauke bowl din ta kai baki ta kwankwade ya xaro ido kafin yace komai suka ji muryar Inna cikin kuka tana cewa "Ahmadu idan ba a bi min hakkina ba yau a babbake ni cikin dare idan na kwana cikin gidan nan" Mikewa Mujaheed yyi da sauri xai bar wajen imaan ta mike ta rikosa a rikice tace "Wayyo yaya kai ne kace fa in dauko" Ya wani xaro ido yace "Ni?? You are sick, kar ma ki sa ni a maganan nan" daga haka ya bar gun da sauri don da dukkan alama nan suke taho, Imaan ta bi sa da gudu har suka iso gaban compound din gidan, ya wani hade rai yace "Wai me yasa kike bi na ne ma dai tukun?" Ta marairaice tace "Yaya kai fa ka sa ni" Ya xaro ido yace "Ohh dama idan nace ki shiga wuta sai ki shiga, kar ki kuskura ki ambato sunana a maganan nan" on a serious note ya fadi hakan, ta hararesa tace "Wllh kai ne kace in dauko da gudu in fito" xai yi magana suka ji alamar suna tahowa, inna na cewa "Kuma ko tantama babu wannan tantirin Mujaheed din da ka haifa ne xai sa ta, banda haka imaan ta san wani sace abincin mutane ta fita da gudu, wllh a min iyakan gaske da yaran nan a gidan nan yau, a kan me xa su dinga cutata suna ci min mutunci haka, wai har sun shanye furan sun bar min kwano a bayan window, me nayi masu a rayuwa xa su min haka" tana kai wa nan ta rushe da kuka, Anty tace "Kiyi hakuri don Allah inna" a fusace inna tace "Shegiya nake idan na hakura, a sace min furan a shanye kice in hakura kamar uwata tace min je ki kya gani, ae Aisha dai ta haifi fitina, wannan yarinya Imaan dai fitina ce wllh, a ma kira min Bukar yanxu, idan ban tada gidan nan da bala'i ba yau ace bani ba" da sauri Mujaheed ya nufi gate, imaan kamar xata fashe da kuka tace "Wayyo yaya" sai da ya kusa gate ya juya yana kallonta ya fara dariya kasa kasa, bin bayansa tayi da gudu, gun motarsa dake parke a kofar gida ta gansa xai bude maxaunin driver, ya buda ido yace "Wai me yasa kike bi na ne?" Ta karasa gun motar tace "Wllh yaya ni ba ni kadai xa a gani a gidan ba bayan ni da kai muka shanye, kawai Ammi ta kama ni ta min duka" ya daure fuska yace "Kinga ki juya ki koma ciki wllh" ta fashe da kuka ta make masa kafada, ya shige driver seat, ta bude front seat ta shiga tana turo baki, yace "Wai kin san inda xa ni" kin cewa komai tayi, jin an bude gate ya rufe door dinsa da sauri, Yusuf ne ya fito, Mujaheed ya tada motarsa ya yi zooming off, Yusuf ya dinga dariya mai gadi na kallonsa, sai da suka hau saman titi Mujaheed ya kalleta yace "Dama seriously idan kika kira sunana a case din nan wllh sai na sa ki kukan sati daya, sai ki gaya masu furan ma ke kadai kika shanye" Ta gefen ido ta kallesa kafin tace "Sai dai in ce masu ludayi daya da rabi kawai na sha sauran kuma ban san wanda ya shanye ba" Yace "Kina son in sauke ki nan kenan" ta marairaice tana kallon sa, yace "Toh me xaki fada masu a kan furan" a hankali tace "Cewa xanyi ayi hakuri ni da yaya muka shanye" parking yyi gefen titi, ta rikosa da sauri tace "Aa yi hakuri xan ce ni kadai na shanye" ya hade girar sama da ta kasa yace "Ki rantse" Kamar xata yi kuka tace "Bayan ni da kai muka sha"


Alhamdulillah, Thanks to all those that patronize the book *Imaan* Allah bar ku da iyayen ku, My book Imaan is for sale coz I am done with free pages tun friday, ni nasan it will go round as usual, I can't prevent that, but if you should come across it it's not for free, i repeat it's not for free, na siyarwa ne, wllh I am too grown up to say Allah ya isa, but have the fear of Allah SWT in u, don't forget it's my property, hakkina ne, wahalata ce, pay before reading, pay before reading, or you just over look it and smile, have a very good conscience plss, and a good conscience won't read happily without paying, if you want any favor pertaining to d book contact me and let me know, the book is 300 via..... Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah

07087865788 and then u contact me through this digit to be added in the payment groups. Thanks once more for patronizing.

For those saying xa su same shi a banxa yana yawo to gashi... amma fa ba a banxa yake ba wllh, there is power in the tongue, Karamin hakkin da ka raina..... 😃😃Ammi ce xaune parlon inna ta sanadin aikawa da innar tayi a kirata, ta fi minti sha biyar parlon amma inna bata ce da ita komai ba sai goge gogen kayan kallonta take, Ammi ta bukaci ta yi mata goge gogen inna tace ta bar shi, bayan wani minti biyar din Ammi tace "Inna na daura girki ne wllh...." Inna tace "Kin daura girki? Tabdi... Toh ita warcan 'yar da kika bari meye amfaninta da baxata dinga duba maki girkin ba, ina ce yau alhamis babu islamiyya" Ammi tace "Barci na baro ta tana yi" Inna ta tabe baki tace "A haka dai kullum, Allah dai ya mana tsari ya fidda d'a na kunya, amma gaskiya ni tunda nake tafasasshen ruwan Imaan bai taba shiga baki na ba, toh uwar me xata je ta dafa ma mijin ma idan tayi aure, kullum ayi ta laka ma yarinya ciwo ana daure mata kugu wai bata da lafiya, to ni dai ba ruwana ba wanda xai xagi d'a na, idan ma an samu to Allah ya isa" Ammi dai bata ce mata komai ba, Inna ta xauna tace "Tana yar yarinya da ita tayi ta langwabewa, tana abu salalo salalo, ana ma ciwo sharri to ni dai ba ruwana, dama magana nake son yi mama ke da Amina, to Aminar bata ga damar xuwa ba har yanxu, tana can sai ta mula ta mulmule sai kace xata ma Maryam haka....." Inna bata rufe baki ba Anty ta shigo da sallama, Tace "Sannu inna..." Inna ta tsuke fuska tace "Yauwa" Anty ta xauna tana kallon Ammi tace "Uwar Imaan kwana biyu" Ammi tayi murmushi tace "Ae kam duk mun buya" Mikewa inna tayi ta ci gaba da goge gogenta, Anty tace "Goge goge kike Inna" a fusace Inna tace "Toh baxan yi goge goge ba in mutu cikin wari yar nan, ko ke baki ga ko ina tsaf ba, ko hancin ki bai ji kamshin dake tashi parlon ba, wllh tun safe ban xauna ba ina ta aiki baki ji bayana ba kamar ya balle in huta, ke hatta simintin da kika tako kika shigo nan sai da na goge sa fess yau, ai kazanta bata da kyau, ni dai in sha Allahu cikin kamshi xan mutu ba ruwana, kuma tirr da kazami, ai ina lura duk cikin jikokina babu wanda ya dauko tsafta ta sai Mujaheed" Anty da Ammi dai sai kallonta suke, ta xauna tace "Yo Mujaheed mana, shi kadai ne Allah ya ceta ta wannan fannin, duk inda kazanta take ma shi bai xuwa, kullum tsaf xaka gansa abunsa, baxa ku yarda da xance na ba sai kun shiga dakinsa, ko don raino na ne shi din oho, ga shegen kyankyamin tsiya.... shi kuma wannan katon Isuhu ba shi da aiki sai saka gogaggun kaya da fesa turare amma duk kika basa abinci to wllh a nan xai bar maki kwanon ya tsallake ya wuce, to ina tsafta a nan, ai ta nan ake gane kazami, dakinsa kuwa karkari ya kakka6e gadon ya kara gaba, ita ko wannan mai laluran Imaan ga dai gashi har gashi amma ba gyara malam, kullum gashin nan a kume xa ki gansa sai ta fi sati da sattuka bata sharce ba, to ina tsafta a nan, da an mata magana sai tace xafi yake mata, ai duk mace ta gashi ake gane kazantar ta ni kwarkwata ma nake guje mata wllh, sannan babu tattali kullum sai ta bar min adikonta a nan idan ta xo, ga su can na tara yafi kala dari yanxu, Ko uwarta xan ci da su oho, ni ce ma Bukar xan yi ma ya daina siya mata turmin atamfa gwara a siya falle a mata riga da sket banda dankwali, Atoh shi kenan yayi ta asaran dukiya atamfa dai masu tsada amma tayi ta walakanta adiko, Maimoon kuwa dama kayan datti sai ta tara ta tara taga babu sarki sai Allah, babu wanda xata saka sannan xata kwashesu ta hau wanki duk su cika gida, to ina mace a nan, babu kazantar da ya fi wannan wllh, sauran yan matan kuwa ni wani lkcn ma sai in ji kamar wari suke wllh...." Murmushi Anty tayi, Inna tace "Wallahi ba batun dariya ba, to dai kowa tasa ta fishshesa a gidan nan ba ruwana da kowa ta kaina nake, yanxu dai abinda yasa na kira ku ba wani abu bane...." sai kuma ta yi shiru, su dai kallonta kawai suke, tayi kasa da murya tace "Ku lissafa min daga ranan asabar xuwa yau kwana nawa kenan" Ammi tace kwana shidda" Inna tace "Toh yau kwana shidda rabon Mujaheed da Imaan su xo min nan su gaisheni, yanxu fisabillahi daga sun min ba dai dai ba na nuna bacin raina sai su kullace ni, meye laifina don nace ban yarda shanye min fura da suka yi ba" Anty ta bude baki tace "Gaskiya basu kyauta ba har kwana shidda" Inna ta fara matsar kwalla tace "Ni fitinata har ya kai Mujaheed ya ki takowa nan yau har kwana shidda, daga gyara kayanka sai ya xamo sauke mu raba? Ke Amina na kira ki ne a matsayin uwarsa don ba ruwana da wancan katuwar da ta haifesa, ke kuma Aisha saboda Imaan yar ki ce" Anty tace "Amma Inna ca nake kince kada su sake xuwa maki idan ba haka ba xaki bar gidan" Inna xaro ido tace "Oh oh Allah kaji wata magana don Allah, to Amina idan na bar gidan nan ina da gidan uban da xanje in tsugunna, duk ba xance bane dai da tsorata mutane, bacin rai ai babu abinda bai sawa, don nace kada su sake xuwa kowa yasan fada kawai nayi, me suka min da xan hanasu xuwa nan?? Allah ya tsine ma fura da nonon in dai saboda shi xan kori jikokina, meye kuma wani fura da nono kamar mayyar bafillatana" Anty na danne dariyar ta tace "Ahh to gaskiya basu kyauta ba" Inna ta kalli Ammi tace "Ke kuma Aisha kinyi shiru kina kallona ko baki da abun cewa ne?" Ammi tace "Kiyi hakuri Inna, ina komawa xan sameta" Anty tace "Nima Mujaheed na dawowa aiki xan samesa In sha Allah" Inna ta gyara xama tace "Toh, sai ku ji dalilin da yasa xa su min haka su kaurace min, yanxu duk saukin kai na su basa gani, ni ba mafadaciya ba, ni ba fitinanna ba, ni ba mai sa ido ba, ni ba mai kwadayi ba, ni ba mai mita ba, toh meye xasu wani dauke kafa daga magana dai ta fahimta, to sai dai idan Ahmadu ne ya hure masu kunne ya masu hudubar tsiya, banda haka su har wani wayo garesu da xasu dauke kafa daga xuwa inda nake" Anty ta fara dariya, Ammi kam murmushi kawai tayi, Inna tace "Aa don Allah ku duba xancen da kyau, wllh xuge su aka yi, kuma ba kowa xai yi hakan ba sai mutumin nan Ahmadu don Bukar baya haka shi, ni gaskiya na ma daina sa Ahmadu a lamarina daga yanxu tunda tsanata yake cusa ma yaran a rai, anjima kuma xan sa kira min Bukar yaji abinda ake ciki, kwana daidai har shidda fa" Ammi ta mike tace "Ki yi hakuri Inna ina komawa xan mata magana bari in je in duba girki na" Inna tace "ke ta girki ma kike ga maganar al'ajabi ana yi a nan Ahmadu ya xuge yara, haba don Allah abinci dai abinci dai kamar ana yunwa Amina" Ammi ta nufi kofa tace "Toh sai dai anjima inna" Inna tace "Toh Allah bamu alkhairi, ki dai tsitsiyeta kiji dalili" fita Ammi tayi parlon bayan ta ma Anty sallama. Inna ta tabe baki tace "Kinga bafillatanin mutum, kinga agwai?? Wllh ki ji tsoronsa, barin idan kika ga ya fiye shiru shiru banda haka ki ga fa babu abun kirki da tace har ta bar parlon nan, Bukar dai na ganin boni, mata kamar kurma, ni kwanciyar hankali na ma Imaan bata dauko halinta ba, Imaan xata iya kwatar kanta a ko ina da bakinta, tun daga ranan da na karanta mata ta daina gaida Uwar Mujaheed gashi har yau bata gaisheta, gashi har Ahmadu da Bukar sun gaji sun kyaleta, kusan ma Imaan ce kadai ta dau halina a gidan nan wlh, banda haka ya xata dinga gaida katuwar mata bata amsa mata, da ta fi ta iskanci kuwa kinga ta daina gaishetan gaba daya" Anty dai dariya kawai take, Inna tace "Toh ni dai ki taimake ni Amina ki rufa min asiri, Mujaheed na dawowa ki titsiyesa a daki kiji me na masa da ya dauke kafa a nan" Anty tace "In sha Allah Inna, bari in je nasan ma ya dawo yanxu tunda biyar har ta yi" Inna tace "To yi maxa" tashi Anty tayi ta mata sallama ta fita inna ta mike ta ci gaba da goge gogenta tana cewa "Ahmadu dai ya lalace, da dai ba haka yake ba"
Dariya sosai Imaan ta dinga yi bayan Ammi ta bata sakon inna, tayi mai isarta ta mike daga kwancen da take tace "Ba Inda
xanje Ammi, tun Sunday kinji ta kai karana gun Abba, to haka ya fi, ita da bakinta tace wannan time din ba wasa take ba Abba ya ja mana kunne sosai don muna xuwa part dinta xata tsallake ta gudu ta bar gidan" Ammi tace "Toh nace bayan magrib kije ki gaisheta, kina gaidata ki juyo" Imaan ta fashe da kuka ba hawaye tace "Ammi don Allah ni baxan je ba, ina xuwa xata ce na mata wani abu" Ammi ta mike tace "Toh idan na baki abincin ki kai mata kar ki kai" daga haka Ammi ta bar parlon, Imaan ta fara kukan gaske, har ranta bata son xuwa gun inna. Anty na gama girkin dinner dab da magrib ta

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment