Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaro mai hankali da natsuwa yana yawan xuwa tare da Muhsin gaisheni, ban ma san suna tare da fatimar ba, akwai wani lkcn dai da ya xo ya sameta a nan, ko tun lkcn suke tare ban sani ba" Ammi ta kasa cewa komai sai kallon Imaan take, Gwaggwo tace "To tashi ki je, ki ce masa ya shigo ina nemansa" imaan bata ce komai ba ta mike da kyar ta sa Hijab ta fita, bayan fitarta Ammi ta xauna gefen gadon tana kallon mahaifiyar ta tace "Anya kuwa Gwaggwo, d'an wajen Bulasawa fa, ina shi ina Imaan kuma? Kinsan yaudara tayi yawa yanxu a rayuwar fa" Gwaggwo tace "Fal yaqul khairan auliyasmut... Bana son irin wannan maganan, Sadeeq bai yi kama da mayaudari ba kuma tun kan ya san imaan yake xuwa min tare da Muhsin, ba a taba cewa d'an mai kudi ne yaron, faram faram yake da kowa, ni dai har ga Allah ya min kuma xan yi farin ciki idan Allah yasa shi ne mijin imaan" Ammi dai ta kasa cewa komai har sannan bata daina mamakin wai Sadeeq yaron Bulasawa bane. Tunda Imaan ta fito Sadeeq ke kallonta, ta sunkuyar da kai tace "Ina yini" yace "Lafiya lau, ya jikin?" Tace "Na ji sauki" yace "Tablet kike sha ko inhaler kike amfani da?" Tace "Inhaler" ya d'an yi shiru kafin yace "Toh Allah ya sauwake" Tace "Ameen, Gwaggwo tace ka shigo" ya d'an buda ido yace "Da gaske" ta gyada masa kai, yace "But ba mutane a ciki" d'an murmushi tayi tace "Idan ka shiga xaka gani" Haka nan dai Sadeeq ya shiga gidan yana sinne kai, bayan sun gaisa da Gwaggwo, Gwaggwo tace "Ka taimaka ka ajiye fatima a gida Sadeeq bata ji dadi ba" yace "Toh In sha Allah Gwaggwo" bai jima a parlon ba ya fita bayan yayi sallama da Gwaggwo, imaan ta fito daga daki rike da trolley dinta tayi ma Ammi da Gwaggwo sallama sannan ta bi bayansa... the journey was silent, lta dai ta jinginar da kanta tana sauke numfashi a hankali, lkci lkci Sadeeq ke kallonta sai ya sakar mata lallausan murmushi, ita dai sai dai ta sauke idonta, dai dai gate din gidansu yyi parking, a hankali ta kallesa tace "Nagode" yace "How will I reach you ltr, ko xaki yi plugging fone naki idan kin shiga ciki?" Ta d'an yi shiru kafin tace "Ina wayarka" bata jira cewarsa ba ta dau tsadadden wayar sa dake ajiye ta yi dialing number din inna yana fara ring inna ta dauka kamar jira take tana cewa "Ni dai an dameni, tun safe nake aiki ban xauna ba wllh, waye kuma wannan" murmushi Imaan tayi ta katse wayar, Sadeeq ma yyi murmushi yace "Number kaka koh?" Ta gyada masa kai ta bude motar ta fita tana kallonsa, Fitowa yayi ya fiddo mata jakarta yace "Ki huta sosai idan kin shiga ciki plss" tayi murmushi tace "In sha Allah" yace "Alright dear, Allah ya kara lafiya" wucewa ciki tayi ta nufi part din Inna, inna ta dinga kallonta daga sama har kasa tace "Lafiya kika taho min nan da jaka??" Imaan tace "A'a ni daga gidan gwaggwo nake" Inna tace "To har na ji sanyi" Imaan dai bata tanka ta ba ta ajiye jakar ta cire Hijab din jikinta ta kwanta kan kujera, inna tace "Toh har an gama bikin ne kika dawo ko kuma bikin ne dai garau garau kika gudo?" Imaan dai bata ce mata komai ba, inna tace "Atoh, ni dama shi sa naki xuwa kwata kwata, ba ruwana inje in dawo da yunwan cikina, biki ba na yan gayu ba, kuma dama Habiba bata ce min tana aurar da jikarta ba, ni dai na bada dubu biyar a kai mata ban bi ta halinta ba, Allah ne xai bani lada" Wani bowl dake rufe inna ta bude Imaan dake ta kallonta ta leki bowl din daga kwancen da take taga nama ne soyayye a cike, inna ta saci kallonta suna hada ido ta mike ta wuce daki da bowl dinta, ba a wani dau lkci ba ta fito da bokitai, ta sa makulli a kofar dakin, Imaan tace "Fita xa kiyi kike sa makulli a dakin?" Inna tace "Baxan sa makulli ba sauro su cika dakin su sa min cuta in bar 'ya yana da wahala?" Tana fadin haka ta fita waje xata wanke bokitan da ta kwaso, Imaan na kallon film da ake a TV taji muryar inna tana cewa "Mujaheed kai me cewa inje bikin su gidan uwar Aisha to ga jikar gidan ma ta gudo daga bikin balle ni karere, ji dai yanda aka dinga facaka da kaji a bikin kanwarka, toh can ni nasan baxa su yi haka ba, abinda duk na san su, meye ban sani ba..." Da sauri Imaan ta mike xaune jin wanda inna ta ambata, Mujaheed dake ta kallon inna yace "Ke dai ki daina haka..." Inna tace "Ni akwai wanda ya isa hanani fadin gaskiya kuwa duk girman duniyar nan?? to duk ba wannan ba don bai shafeni ba, inji ka siyo min kazar da nace maka nake marmari" Mujaheed bai tanka ta ba ya nufi kofar shiga parlon, da sauri Imaan ta saka Hijab dinta ta rufe har kafarta ta kafe TV da ido, Mujaheed ya shigo parlon, kallo daya yyi mata ya ajiye ledan hannunsa ya xauna yana danna wayar hannunsa, Imaan ta ki yarda ta kallesa gabanta sai faduwa yake, gaba daya she was uncomfortable, Inna ta shigo tace "Allah maka albarka, kai kadai dama xance ka siyo ka siyo" kitchen ta tafi ta dauko plate biyu ta xauna kan tabarma tana gogewa ta bude ledan kazar ta raba biyu, daya nata daya nashi, can dai ta kallesa tace "Toh ita kuma warcan matar ya xa mu yi da ita, tunda ba da ita aka siyo ba" shi dai Mujaheed bai ce komai ba, Inna ta tabe baki ta dauko wani plate din ta dau cinya daya da tsoka daya ta dangwala a plate ta mika ma imaan tace "Toh gashi dai, ido guba...." Ba tare da imaan ta kalleta ba ta girgixa kai gently tace "A'a baxan ci ba" Kallonta Mujaheed ya dinga yi da mamaki, inna ma ta saki baki tana kallonta tace "Dama baki da lafiya shine kika yo min nan salon ace a nan ciwo ya tashi ni patuu?? don cuta kadai ke hanaki cin kaza ni dai na sani" Imaan bata ce komai ba bata kuma kalleta ba, can ta mike ta nufi kofa tace "Ni fa a koshe nake" daga haka ta fice a parlon.


*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻‍♀️

It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group
Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment grouImaan na kwance bedroom dinta dab da Magrib taji an danna bell, tashi xaune tayi don ita kadai ce gidan Ammi na can Unguwar rimi, daddy kuma bai dawo ba, can ta mike ta sa Hijab dinta ta nufi kofar a hankali tace "Waye?" Muryar Ummi ta ji tace "Aunty na kiran ki" Imaan ta bude kofar tana kallonta, a tare suka tafi part din da Ummi, Imaan ta wuce sama ta bude kofar dakin Aunty, Aunty ta fito bayi bayan tayi alwala tana kallonta tace "Ya jikin?" Imaan tace "Na ji sauki Aunty" Aunty tace "Ammi can xata kwana fa, sai ki dawo nan ki kwana ko ki tafi gun inna" Imaan tace "Xan je gun Inna" Aunty tace "Toh ga abinci ki dauka" ba musu ta durkusa ta dau warmer din da Aunty ta nuna mata, Aunty tace "Ki tabbatar kin sha magungunanki bayan kin ci abincin" Imaan tace "Toh sai da safe" daga haka ta bude kofa ta fita, a stairs suka hadu da Yusuf, suna hada ido ya dauke kai, tace "Lah ya Yusuf kayi tafiya ne, ban ganka 2 days ba" Yusuf na ci gaba da haurowa stairs din yace "Not at all" daga haka ya wuceta ta bi sa da kallo, can dai ta sauka ta bar parlon. Part din inna ta wuce ta sameta tana sllh, ta ajiye abincin hannunta a parlor ta fito bakin tap ta daura alwala ta koma ciki, tana idarwa ta koma kan kujera ta kwanta, inna ta gama addu'o'in da take tace "Toh wai me yasa kika baro gidan bikin kika dawo?" Imaan tace "Dama ba kwana naje yi ba" Inna ta tabe baki tace "Toh ita Rukayya taje gidan kuwa?" Imaan ta girgixa kai tace "A'a bata je ba" inna tace "Ikon Allah, Kice Amina ce kawai ta je?" Imaan ta gyada mata kai, inna tayi tagumi tace "Naga abinda ya isheni, tun da uwata ta haifeni ban taba ganin haka ba wlh, Rukayya bata da xuciya mai kyau sam, ko da yake abun na da tushe, kinsan lkcn da Bukar ya auro Uwarki bata da aminiya da ta wuce Amina, lkcn Amina tana nan wata yar duma duma da ita kamar ki latsa ta jini ya feso, toh a lkcn gida daya Rukayya da uwarki suka xauna sai dai kowa da sashensa kamar dai Wannan gidan amma ko rabin gidan nan bai kai ba, lkcn Ahmadu da Bukar na yaku bayi basu da komai sai wahala, tun ba yau fa suke son junansu in gaya maki, dama a haka kuma suka taso, toh kullum Rukayya bata da aiki sai neman fitinar uwarki a tsakar gida, kaii Gaskiya Rukayya ta dade tana hauka, ga uwarki mai hakuri bata biye ta, ga uwa uba kawaici, amma akwai ranan da xuciya ya debi Aisha ta nakada ma Rukayya shegen duka har sai da ta targada mata hannu, da kyar aka kwace ta hannun Aisha, ni dai ce ma Bukar da Ahmadu nayi duk su kora su gidan iyayensu ba ruwana, to sun fa mayar min da gidan 'yaya wajen dambe, a lkcn kuma kullum Amina sai ta xo gun uwarki, tun fa Rukayya bata san Amina xata aure mata miji ba ta tsaneta har xage xage sun ta6a yi da jefe jefen dutse, to ana_nan ana_nan Ahmadu ya kyallara ido ya ga yar duma duma Amina, to karewa ma gun Aisha ya amshi lambarta idan ba mantawa dai nayi ba, Rukayya na ji tana gani Ahmadu ya aure kawar makiyiyarta wato Aisha, in gaya maki Aisha ce a kan gaba na komai da bikin, kuma ni nasan da gayya tayi haka, to da Aisha ma aka raka Amina dakinta gashi gida daya ya hade su da Rukayya, to kinji musabbabin komai... Ba irin xugar da Rukayya bata min ba kan in sa ubanki ya kara aure tunda uwarki bata haihuwa ni dai naki, kinsan da Rukayya yar dakina ce kafin ta xama bala'i, duk da dai nayi masa magana na yi masa magana har na gaji na kyalesa wato Bukar, to Aisha ta shanye min shi, daga karshe dai Bukar ya raba fada ya dauke uwarki suka koma Abuja da xama gaba daya, ai sun fi shekara biyar a Abuja, kuma fa lkcn... Katse ta Imaan tayi tace "Toh ni dai ban tambayeki ba, wllh har na gaji da jin labarin nan, a wata sai kin bada labarin nan ya fi sau biyar" Inna tace "Ai ba sai kin tambayeni ba duk sanda na ga dama dole in bada labari ko da kuwa ni daya ce a daki, to ina ruwan wani da ni??" Imaan ta tabe baki ta mike ta jona ruwa a heater don yin wanka, dawowa tayi ta xauna tana jiran ruwan yayi, inna tace "Ke wai bulasawan na maki waya ma kuwa?" Imaan tace "Ehh" inna ta d'an yi murmushi tace "Toh madallah, gama wanka ki xo in baki wani labari mai ban al-ajabi" imaan tace "Ai ruwan bai yi ba ki bani" Inna tace "Ki dai yi wankan tukun" Juye ruwan Imaan tayi haka ta wuce bayi inna na cewa "Don Allah idan kin gama ki dauraye bayin da omo, kazanta dai ba kyau" Imaan dai ba ta tanka ta ba ta cire kayanta ta shige bathroom. Imaan na gama wanka ta fiddo daya daga sleeping wears dinta dake press din inna ta saka ta feshe jikinta da turarrukan Inna ta fito ta xauna tana kallon inna da ke xuba gyangyadi a xaune, murmushi imaan tayi ta dau remote xata canxa tasha aka bude kofar parlor da sauri ta mike xata gudu xuwa daki Mujaheed ya shigo, tuni ta shige daki ta sa makulli ta wani hade rai, Inna da ta bude ido a gigice tace "Subhanallahi, lafiya??" Mujaheed dai na tsaye sai kallon kofar dakin yake, inna tace "Ni dai ba ruwana, ku dinga jin tsoron Allah, ya xa a maida min gida kamar filin daga, baka ji yanda xuciya ta ta tsinke ba wllh, ni dai ana shiga hakkina... Wnn 'ya ta Bukar dai ba ta da imani an wani laka6a mata Imaan din karya" Shi dai Mujaheed bai ce komai ba bai kuma fasa kallon kofar dakin ba, wayar inna ya fara ring, kamar xata yi kuka tace "Kaga wani bala'in koh, toh meye wnn fisabilillahi tsakar dare kuma" daukar wayar tayi ta danna inda ake picking ta kai kunne hade da sallama tace "Waye??" Sadeeq yace "Ina yini kaka?" Tace "Ce maka nayi waye??" Yace "Sadeeq ne" Inna ta bude ido sosai tace "Bulasawa?" Yayi murmushi yace "Ehh kaka" Inna tace "Lahh ina yini??" Mujaheed couldn't stop looking at her da mamaki, Sadeeq yace "Ya gidan kaka?" Tace "A'a lafiya lau wllh Bukar, ya iyayen ka?" Yace "Suna lafiya lau" inna tace "Toh madallah, shiru shiru ban ganka ba kwana biyu, Hala imaan ce ta baka lambar wayata?" Yace "Ehh ita ta ban" Inna tace "Toh ai ta kyauta wllh, shkkn sai in ba Mujaheed da ya tsaya kaina sandandan ya min saving, yaushe xaka billo?" Sadeeq yace "Gobe in sha Allah" Inna tace "Toh Alhmdllh, da kaina kuwa xan maka tuwo da miyar taushe in sha Allah" Sadeeq yayi yar dariya yace "Toh nagode kaka, imaan din na kusa?" da sauri inna ta mike tace "A'ahh toh bari in bata har ta kwanta ina jin, Kasan bata dade da dawowa daga gidan bikin su kakarta ta wajen uwa ba" Sadeeq yace "Toh ki barta gobe xan kira in sha Allah, dama ke na kira mu gaisa" inna tace "Ae ko naji ddi Allah maka albarka, maxa kashe kudin ka na ta konewa" yyi murmushi ya katse wayar. Inna na kallon Mujaheed ta mika masa wayar tana washe baki tace "Kai yi min saving, lambar bulasawa ne" Mujaheed ya amshi wayar yana kallon number, Inna ta xauna tace "Kai amma yaron ya kyauta, wllh na ji dadi, kaga alamar xai rike min jika da kyau kenan wllh, gashi gobe yace zai shigo, sai in baka dari biyar dita ka shiga kasuwa ka siyo min kayan miya da nama lafiyayye in masa miya mai kyau" Mujaheed ya xauna kan kujera har sannan bai daina kallonta ba, tace "Ka min saving mana Mujaheed kar lambar ya bace" Mujaheed ya gama danne dannensa ya mika mata wayar ta, ta amsa ta ajiye tace "Dole in tashi da sassafe kenan gobe, bari ma in dauko maka kudin kar ka manta ka tafi baka amsa ba in rasa d'an aike" Mujaheed dake kokarin controlling temper dinsa yace "Ki dai ba Yusuf" inna ta gwalo ido tace "Waye kuma Yusuf?" Mujaheed bai tanka ta ba tace "Toh bari kaji, Rabonsa da ya tako nan ya gaida ni tun ran da yyi abun kunyar nan, to dama idan ya xo da wani idon xai kalleni, A'a ba ruwana ni bana bukatansa dama, ga dai ka" Mujaheed na gyada kai yace "Ita kuma yarinyar nan kice mata wllh idan ta sake ganina ta kwasa a guje sai na sa ta kuka a gidan nan" inna tace "Oh oh Allah, yau naga jaraba, baxata gudu ba kana cutar ta Mujaheed? nine fa na koya mata ta dinga gudu idan ta ganka, toh me xata tsaya ta maka idan ta ganka, ni dai ba ruwana, ka dinga tsoron Ubangijin ka, ai ta ma kusan aure ta huta da fitinar ka sai in ga ko gidan mijin xaka bi ta kana cuta kuma, karshenta sai ka kare a kurkuku don Bulasawa daure ka xai yi a fita da kai kasashen turai ai maka hukunci, ka ga sai ka bar Ahmadu da Bukar da kashe makudan kudaden da suka fi karfinsu, idan ba haka ba kuma ka ru6e a kurkuku in shiga uku" mikewa Mujaheed yyi ya nufi kofa fuska daure, inna tace "Toh kudin cefanen pa, baka amsa ba fa? Ko xaka siyo min da kudin ka" Washegari da safe Imaan na shan shayin da inna ta hada mata, inna tace "Wai me yasa kike gudun katon can ne, halan laifi kika masa" Imaan taki cewa komai da farko, can kuma tace "Ba komai, ni bana son yana kulani a gidan nan nima kuma na daina kulasa, don Allah ki taya ni gaya masa inna" on a serious note ta fadi hakan, Inna tace "Toh ai hakan yafi ma, kinga babu ta yanda xai dinga cutarki kuma, wahalan da yayi a kanki a baya Allah ya saka masa, idan kuma biyansa yake son ayi sai ya fada min nawa ne bai gagareni in daga daya daga gidajena na gado in siyar in biyasa ba, kuma ba karamin aikin Bulasawa bane ya siya min wani ma a kasashen turai in xuba yan haya" Murmushi imaan tayi ta mike ta dauko mata dankunnen da Sadeeq ya bata, inna na budewa tace "Wannan ai gwal ce, a ina kika samo Imaan?" Imaan tace "Shi ya bani" Inna ta xaro ido tace "Mujaheed din???" Imaan ta hade rai tace "Sadeeq dai" Inna ta saki wani kabbara tace "Kinga abinda nake nufi ko, to a xamanin nan wa xai ma naka haka?? Wllh ki rike yaron nan da kyau kai ko su Maimoon kada ki yarda su san abinda kike ciki balle wancan mutumin Mujaheed, 'ya yan Ahmadu ba wani tsoron Allah garesu isasshe ba, duk yan bakin ciki ne, ki bar wannan gu na in ajiye maki, ana nuna ma su Ahmadu dama cewa xa su yi a mayar tunda ba hankali ya ishe su ba, shi ma mutumin nan Mujaheed yanxun nan xaki ga ya shigo wai gaisheni bai san ni damuna yake ba, maxa dauka ki wuce da shi ciki kada...." Bata rufe baki ba aka bude kofa, Abba ya shigo da sallama Mujaheed na biye da shi, Inna ta boye dankunnen a karkashin carpet, a hankali Imaan tace "Ina kwana Abba" Abba yace "Lafiya Imaan, naji baki da lafiya, ya jikin naki?" Kallonta Mujaheed yyi da sauri, tace "Naji sauki Abba" Abba yace "Toh Allah ya sauwake" tace "Ameen" kallon inna tayi tace "Inna zan je dauko kayana" inna tace "Toh yi maxa" tashi tayi ta nufi kofa ta fita, Mujaheed ya fara danna waya ya kai kunne sai kuma ya mike ya fita yana cewa hello, Imaan na shiga parlon ta nufi dakinta don har Daddy ya fita ganin bata ga motarsa a parking space ba, tana dauko kayanta ta ji an bude kofa, ta juya da sauri tana kallon kofar dakinta, can dai ta nufi kofar ta murda, Mujaheed ta gani tsaye kusa da kofar dakin nata, Xata gudu ya fixgota waje fuska daure yace "Ni dodonki ne kike gudu na?" Kuka ta fara yi a rikice taki yarda su hada ido tace "Ban son hka ni ka sake ni yaya" kallonta ya dinga yi kafin yace "Meyasa kike gudu idan kin gan ni" sosai xuciyarta ke bugawa tace "Ba komai, ni ka sake ni plss" ya sauke idonsa daga kallonta, can yace "What's wrong with you?" Da kyar tace "Ni na ji sauki" saketa yyi ya juya ya fita, ta durkushe wajen har sannan xuciyar ta bai daina bugawa ba. Da yammacin ranan Imaan na durkushe bakin tap din inna tana alwala kamar ance ta daga kai taga Sadeeq yana tahowa, da sauri ta rufe gashinta ta xaro ido, murmushi yyi, yana isowa inda take murya can kasa yace "Good evening dear, sae ynxu xa ki yi la'asar?" Bata iya tace masa komai ba ya tsaya bakin kofa yyi sallama cikin cool voice dinsa, Inna ta fito daki tana amsa sallaman, shiga yayi tace "Au, sannu da xuwa Bukar ashe kai ne" ya xauna yana murmushi yace "Ina yini kaka?" Tace "Lafiya lau Bukari, ya aiki?" Yace "Alhmdllh mun gode Allah" tace "Toh ya xafi xafi, ko da yake ma akwai Ac ko ina yanxu" Yayi dariya yace "Haka ne kaka" Tace "Toh madallah, bari in kawo maka ruwa da lemo" bata jira cewarsa ba ta debo masa su a fridge ta ajiye, tace "Toh nayi tuwo na ajiye maka ina bacci wannan mutumi Mujaheed ya shigo ya cinye"


*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻‍♀️

It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment grou31. Imaan













Sadeeq yyi murmushi yace "Wani lkcn ai sai ki min kaka..." Inna tace "Toh in sha Allahu kuwa, yanxu ya maganar da muka yi ranan Bukar?" Sadeeq yace "Kaka Abbana baya kasar ne, ina jiran sai ya dawo in sha Allah sai ayi magana" inna tace "Toh da kyau, Allah maido da shi lafiya, ai dama Bulasawa bai fiye xama ba aka ce, baya can baya nan, to abun ka da babban mutum fitattce..." yar dariya kawai Sadeeq yyi, sun fi minti talatin da inna dake ta basa labarin da ya kamata da wanda bai kamata ba, daga karshe ya ajiye mata dubu ashirin yyi mata sallama, xaro ido tayi tace "Kai dai baka gajiya Bukar, wancan ma da ka ban har yau basu kare ba wllh suna can na adana su sbda yaran gidan nan, toh ni dai nagode Allah ya maka albarka, ya kara maka budi" yana murmushi yace "Ameen kaka, nima nagode" inna tace "Toh ka gaida uwarka ka ji, wataran duk xamu san juna idan Allah ya yarda, to ya sunan uwar taka?" Yana murmushi yyi kasa da kai yace "Hajiya Khadijah..." Inna tace "Lahh sunan aminiyata a da kafin ta xama abun gudu, Allah sarki Hadiza ko ana wace duniyar yanxu kuma" Dariya kawai Sadeeq yyi yana kallonta, Inna tace "Allah ya sa mu yi kyakkyawan karshe dai, amma Hadiza bata yi abun kirki ba, ga son abun duniya Allah ya dora mata, wai..." Kofa ya nufa yana nurmushi yace "Sai na sake shigowa kaka" ta mike da sauri tace "Toh Bukar a gaida gida, Allah maka albarka" ya amsa da "Ameen" ya fita, Kalle kalle compound din kawai Sadeeq ke yi bayan ya fito amma har ya kusa gate bai ga alamar Imaan ba gashi wayar ta har sannan a kashe, mota ce ta shigo gidan driver yyi parking, aka bude motar umma ta sakko tare da Hajiya Balaraba suka bude bayan mota suka dinga fiddo manyan ledoji, Gaishesu Sadeeq yyi, Umma ta kallesa ta amsa tana ci gaba da fiddo ledojin, ya wuce su, sai da suka nufi entrance din shiga gida Hajiya Balaraba tace "waye wancan kuma" Umma tace "Kila wajen Yusuf ya xo" Hajiya Balaraba yace "Dama Yusuf na gari, ni na xata bai nan, duk na xo bana ganinsa" Umma ta tabe baki tace "Yana nan, kinsan sa bai fiye faram faram da mutane ba, ko yana gidan ma to idan bai dakinsa yana bangaren fitinanniyar kakarsu" Hajiya Balaraba tace "Shi yasa, amma na fi ganin Mujaheed" Umma tace "ko kwana hudu ba ayi ba aka gama wani case a gidan nan, wai Yusuf ya rasa warce xai fito yace yana so sai yar wajen Aisha" Hajiya Balaraba ta xaro ido tace "Yar wajen Aisha kuma, to sai aka yi yaya?" Umma tayi wani murmushi tace "Ai ba xancen ma yanxu haka, kakarsu dai

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment