Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kasa cewa komai, Abba ya masa tsawa yace "Ba da kai nake ba malam?" Da kyar yace "Abba kayi hakuri, I was only trying to do what I thought was right, duk gidan nan nasan you don't tolerate yarinya ta shiga motar saurayi" Abba yace "Not to the extent of slapping her, if she proved to be stubborn why not report her to me? Kasan halin grandmother din ku, kuma kasan dole sai taje ta gaya mata" Mujaheed yace "Kayi hakuri" Abba yace "Stupid ba ni xaka ba hakuri ba, ita da ka mara da innan xaka ba hakuri, kuma kada ka sake wannan wawancin" yace "In sha Allah Abba" Abba yace "Idan ba hauka ba ma kawai ka daga hannu ka mari mace?" Shiru Mujaheed yyi, Abba yace "Tashi kaje kayi abinda na ce maka, ita kuma Imaan din xan hadu da ita" mikewa Mujaheed yyi ya kara ba Abba hakuri sannan ya fita parlon. A hanya Inna ta kalli Imaan tana washe baki tace "Ke kice saurayi me mota kika yi Imaan?" Imaan ta turo baki bata ce komai ba, Inna tace "Toh baki ce masa kakarki na nan da rai bane naga bai shigo ba, ko yaushe yace maki xai shigo gaisheni?" Imaan tace "Ni fa ba saurayi na bane, driver din gidansu kawata ne naje dubota bata da lafiya shine mamansu tace ya maido ni gida" sake baki inna tayi a sanyaye tana kallonta tace "Ba lafiya... Direba kuma?" Imaan bata ce komai ba ta shige balcony dinsu ta bude kofar parlor ta shiga sai a sannan ta kalli inna dake tsaye baki sake har sannan tace "Sai da safe" daga haka ta kulle kofar ta sa makulli. Washegari da ya kasance Friday tun da Imaan ta dawo schl take xaune balcony dinsu tana assignment dinta na maths, Ammi ta kwalo mata kira for the second time ta ajiye pen din ta amsa, Ammi tace "Idan baxa ki ci abincin ba ki shigo ki mayar min kitchen nace" Tace "Ammi fa na kusa gamawa saura biyu" Daga haka ta ci gaba da assignment din, kamar ance ta daga kai taga wata budurwa da baxata wuce shekaru ashirun da biyu ba tana tahowa, xaro ido tayi ta ajiye pen din ta mike ta fito tace "Lahh Anty Farida" murmushi kyakkyawar budurwar tayi tace "Imaan ta mance ni" Rungumeta Imaan tayi tace "Wllh ban mance ki ba Anty farida, yaya ne yanxu baya bani waya mu gaisa" Farida tace "Toh ke ba sai kice ya ba ki ba" Imaan ta tabe baki tace "Ai to yanxu babu ruwana da shi shima ba ruwansa da ni" dariya Farida tayi tace "Toh saboda me" Imaan na murmushi ta amshi ledan hannunta tace "Ae yanxu yaya ya xama mugu, wajen inna xa ki?" Farida tace "Ehh na xo layin kusa da wannan ne nace bari in shigo yau dai mu gaisa da inna" Imaan tayi dariya tace "Amma yaya yasan xa ki xo?" Farida tace "A'a bai sani ba" Imaan tace "Last time da kika xo gaida inna ai tare ku ka je da shi to me yasa yau ma baxa ki bari ku je tare ba?" Tayi murmushi tace "Na fa ce maki bai ma san na xo anguwar ba, Ammi tana ciki?" Imaan tace "Ehh tana ciki" Farida tace "Toh bari mu gaisa" daga haka ta nufi parlon Imaan na biye da ita, Da fara'a Ammi ta tarbeta tace "Kin guje mu Anty Farida" banda murmushi babu abinda take tace "Ammi karatu ne wllh, kinga yanxu ma hutu na xo" Ammi tace "Allah sarki, Allah ya bada sa'a, ya kuma bada abinda aka je nema" Farida tace "Ameen Ammi" daga haka tayi mata sallama tace "Xan je mu gaisa da inna" Ammi tace "Toh idan xa ki wuce ki biyo ta nan mu yi sallama" tace "Toh Ammi" daga haka ta mike imaan na kallon Ammi tace "Ammi ni dai xan rakata gun inna, idan na dawo xan ci abincin" Ammi tace "Ai shi kenan" tare suka fita da farida tana rike da ledan ta, farida budurwar Mujaheed ce babu wanda bai sani ba a gidan, 2 years back kafin Ummarsa ta dawo gidan farida kan xo ta gaida Ammi da Anty, idan ko xata je gaida inna dama shi xai rakata kuma ko minti biyar baya yarda su yi a parlorn kafin inna ta fara xance yake janta su fita, sosai farida ke son Imaan tun lkcn da take xuwa gidan lkcn ma bata kai haka ba, suna isa bangaren inna imaan ta bude kofar ta shiga da sallama, Maimoon da Rahma na parlon xaune tare da inna, Farida ta shiga da sallama, inna dake xaune kan tabarma ta amsa tace "Wacece wannan kuma?" Maimoon tace "Lahh Anty farida sannu da xuwa" farida tana murmushi tace "Yauwa Maimoon, ykk" durkusawa tayi kasan rug tana kallon inna tace "Ina yini Inna" Inna tace "Lafiya lau ni dai ban gane ki ba" Maimoon tace "Inna faridar ya Mujaheed ce fa" Inna tace "Ayyoo farida ce, sannu da xuwa, kai ku kawo mata ruwa da sauran ayaban nan" Imaan ta mike ta dauko mata ruwa, Inna tace "Allah sarki, da yake sau uku ya ta6a kawo ki a gurguje shi sa ban gane ki ba, ya iyayen naki?" Tana murmushi tace "Sun ce a gaida ku inna" Tace "To madallah muna amsawa, Mujaheed din ne ya kawo ki kenan?" Farida tace "A'a ni kadai na xo" Inna tace "Atoh ba dole ki xo ke kadai ba, ni ma duk yau ban gansa ba ko gaisuwar Juma'ah ma bai xo ya min ba daga na kai kararsa kan ya doki yar kanwar nan ta sa, ko ke haka yayyinki ke cutar ki?" Murmushi kawai farida tayi, Inna tace "Toh Mujaheed kam cutan nasa kannin yake, kawai daga an sauke yarinya a babban mota ya daddage ya kwada mata mari ba laifin fari balle na baki wai ashe ma gantalallen direba ne ya sauketa, to kin san sa da xuciya sai dai kiyi ta hakuri kawai, dama tun da aka haifesa na ji irin kukan da yake a asibiti nasan akwai bala'i gaba, baki ji ba duk ya cika asibitin da muryarsa ga shi wani lafcece" Imaan ta fashe da dariya har da kyakyatawa Maimoon na taya ta, Rahma dai ta6e baki kawai tayi, Farida kam sai murmushi take kanta a kasa, Inna tace "Wllh ba xancen dariya ba nasan abinda nake fada, kuma a yunwace aka haifesa, kilan dai uwar bata ci abinci ba taje haihuwarsa, mu dai haka muka koma gida na wanke sa tass, baki gansa ba jazur da shi ba yanxu da ya kode ba, ke kinga wahalar da nayi da Mujaheed wllh k'are baxai ci ba, tun fa yana tsummarsa nake wahala don sai da nayi kwana hamsin ina kai komo a kansa, to ba abinda uwar ta iya har na koma gidan mijina, daga nan kuma sai dai in kai masu ziyara duk sati, lkcn baki ga uwarsa ba yar siririya doguwa kamar dai yanda kika ga wannan yarinyar Imaan" Inna na yamutse fuska tace "gashi uwar tayi ta cika masa nono yayi ta bulbula tumbudi duk k'arni malam, duk jikokina babu wanda yyi tumbudi kamar Mujaheed, ni ne ma nace uban ya sa masa Mujaheed" Imaan dai an samu abinda ake so don har wani kwanciya kasa take don dariya, Maimoon kawarta na taya ta, Farida dai ta kasa dago kai, Rahma ta wani hade rai tana hararan Inna ko Kadan bata ga abun dariya a wajen ba, Inna ta gyara xama tace "Lkcn yana da shekara daya da wata bakwai uwar ta yayesa, shi ma fa da kyar, ai duk cikin 'ya yan Ahmadu babu wanda ya sha nono irinsa, ya tsotsi uwar ba kadan ba, ko ke baki ga bakinsa d'an tsiyot kusan a tsuke ba? Ai duk tsotso ne yaja haka, sai yaje gantalinsa ya dawo ki ji yace Nono, uwar sai ta fiddo ta basa ya sha yyi nak sannan ya mayar, ke in takaice maki da kyar kanwar uwar ta yayesa don ni dai nace baxan iya wahala ba cikin kishiyoyi, ae ko sai kinga tashin hankali gunsa, bayan an yayesa kuwa idan Mujaheed ya daga maki roban yoghurt to bai direwa sai ya kwankwade tass, ga katon ciki yanda kika san an kifa masa kwarya, Sai uban kukan banxa da shagwaba, ni dai ba komai yasa na daukesa gaban uwar ba sai ganin xai hallaka, yo hallaka mana katon yaro haka yayi fitsari a tsaye kashi a tsaye uwar sai dai ta kwashe ta rabu da shi, duk ta dau son duniya ta daura masa, Shi kuma lkcn kaninsa isuhu na cikin tsumma an haifesa wani fiyot da shi kamar kyanwa ni na ma xata bakwaini ne" Shiru Inna tayi tana kallon Imaan, can ta xaro ido tace "Auzubillahi... Ke meye haka kike yi?" Maimoon ta tsayar da dariyar da take tana kallon Imaan, da sauri ta dagota tana xaro ido tace "Me ya faru Imaan?" Farida ma ta tashi da sauri ganin yanda numfashinta ke sama, inna ta mike a rude tace "Kun ga xata ja min jalala ina xaman xamana ko, to ita nake ba labari da xata dinga dariya haka taje ta mutu a banxa a buga ni a jarida? kai ku fitar min da ita kar ace a parlo na ne, meye kuma numfashi na neman daukewa daga ina ba yarinya da ta xo gaisheni labari? Ni dai ba ruwana a kai ta gun uwarta, ni wllh ba ita nake ba labari ba" Da gudu Maimoon ta mike xata je dauko mata inhaler suka kusa cin karo da Mujaheed xai shigo parlon, ya turata yace "Baki da hankali ne" kamar xata yi kuka tace "Ya M.A Asthma din Imaan ne...." daga haka ta fita, Da sauri ya karasa yana kallon Imaan yace "What happened" inna da har ta fara matsar kwalla tace "Ka fita da ita Mujaheed idan ma asibiti ne ku tafi, wllh ba ita nake ba labari ba xata sa ni a bakin duniya ni ban ma san lkcn da ta shigo parlon ba" Mujaheed ya kalli farida da mamaki, inna tace "Ka rufa min asiri ka fita da ita Mujaheed, meye kuma dariya haka kamar mahaukaciya, ban san meye abun dariya a xance na ba" dagata Mujaheed yyi suka fita parlon, can kusa da wani flower ya xaunar da ita yana kallonta yace "Relax now" da kyar take numfashin kamar xai dauke, Maimoon ta iso kusa da su ta durkusa ta mika ma Mujaheed inhaler din, budewa yyi ya kai bakinta da sauri, bayan wani lkcn ta dinga sauke ajiyar xuciya, maimoon dai sai kallonta take cike da tausayi, Ta jingina da flowern tana ajiye numfashi a hankali hawaye na sauka idonta cikin tsarkewar murya tace "Yaya xan sha ruwa" mikewa Maimoon tayi ta tafi dauko mata ruwan da sauri, shi dai kallonta kawai yake, bayan wani lkci ta daga kai suna hada ido ta kamo hannunsa ta kwashe da dariya, ya daure fuska yace "kina da lafiya kuwa?" Tana dariya a hankali tace "Wllh yaya babu abinda inna ta mance bata gaya ma Anty farida ba yau" ya wani xaro manyan idonsa yace "Kamar me?" Imaan ta kara fashewa da dariya hawaye na sauka idonta, ya hade rai yace "Baxa ki daina wannan dariyar mahaukatan ba" ta hadiye da kyar, har wani ciwo kirjinta ke mata cike da karfin hali tace "Labarin ranan da aka haifeka har sanda aka yaye ka take bata da yanda...." Ganin yanda Mujaheed ya bude baki da idanuwa yasa ta kara kwashewa da dariya tace "Wllh yaya har da tumbudi da fitsari da kashi duk ta fada mata" Mujaheed ya kasa rufe baki, Ganin irin dariyar da take ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yace "Toh dariyar ya ishe ki haka" Mikewa yyi fuska daure xai koma part din Inna ya hangota tana tahowa da gudu, tsayawa yyi har ta iso yace "Gaskiya Hajiya ki daina abinda kike yi a gidan nan, ke dai magana magana magana baya kare maki, wanda ya kamata da wanda bai kamata ba haba don Allah, ni bana son irin wannan abun, ki shekara kina bada labarin kowa amma banda nawa, ba ruwanki da rayuwata da yanda aka haifeni ke kenan kowa kice xaki ba labari baki san bako ba, kawai ke dai kiyi ta magana babu naxari haba don Allah" sake baki tayi tana kallonsa, mikewa Imaan tayi tana hadiye dariyarta sum sum xata bar wajen inna tace "Ke dai wannan 'ya ta Bukar anyi munafuka wllh, to da kika gaya masa dukana xai yi ko ko, ina ce yarinyar da xai aura ce, kuma laifi ne don na bata labarinsa? Me yasa ban samu masu gadi na basu labarin ba? Saboda bai shafesu ba, komai fa da ku ke gani a rayuwar nan kamawa yake, yarinya ta xo gaisheni sai in xauna muna kallon kallo da ita??" Imaan ta turo baki tace "Ba wani nan, yaya har ce mata ta yi da yunwa aka haifo ka duniya kana ta ihu a asibiti, kuma saboda shan nono bakin ka ya xama d'an karami haka, wai sai kaje yawo ka dawo sai ce ma Umma nono sai ta baka ka sha, shi ma ya Yusuf sai na gaya masa tace an haifesa fiyot kamar kyanwa kamar bakwaini" Girgixa kai Mujaheed yyi ya bar wajen a mugun fusace Imaan ta bi bayansa da gudu tana kyalkyala dariya, Inna ta share kwallar idonta tace "Ni dai ba don gabana aka haifi muguwar yarinyar nan ba wllh sai ince ba jininmu bace, don gulmarta ya wuce hankali ya dauka, banda haka yaya xa ta dinga hada mutane fada a gida haka, shi kenan ni kuma bani da Ikon bada labari, ni daga yau ma kar ta sake xuwa min na yafe abincin, yarinya dai guda daya sai hada bala'i a gida, gashi ta hadani da Mujaheed xata tafi ta hada ni da isuhu kuma, ni dai bari Ahmadu ya dawo a ja mata kunne kar ta sake xuwa min, Bukar dai ya Haifi jaraba"[7/16, 7:46 AM] +234 807 505 4566: 🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟

_By khaleesat Haiydar_ ✍️

10.....

A fusace Mujaheed ya juya ganin Imaan na bin sa yace "Kee Why are you following me?" Ta xaro ido tace "Ni ba gidanmu xan tafi ba toh??" kwafa yyi ya ci gaba da tafiyarsa tana kai wa bangarensu ta shiga tana dariya kasa kasa. Sai kusan karfe biyar Farida ta fito bangaren inna bayan ta cikata da abun arxiki, su sabulai, omo, malt har da bottle water duk ta xuba mata a leda, Inna ta rakota har bakin kofa tana cewa "Toh sai ki gaida iyayenki kinji, Allah maki albarka, nagode nagode, naji dadin turaren da kika kawo min duk da dai ba mai tsada bane, sai ayi ta hakuri da Mujaheed dai, Allah kuma ya nuna mana lkcn abun arikin nan" murmushi kawai Farida take ta wuce tare da Maimoon dake rike da ledan da inna ta bata, sai da suka isa bangaren su Imaan tace "Bari na shiga in duba imaan" Tare suka shiga parlon da Maimoon, imaan dake kwance tana kallo ta mike xaune tana murmushi tace "Har xa ki tafi Anty farida" farida tace "Eh xan wuce ya jikin fa?" Imaan tace "Ae na ji sauki" Farida tace "Toh Allah ya sauwake xan fito daxu inna tace kun tafi asibiti da Mujaheed" dariya imaan tayi tace "Ni dai naji sauki" farida tace "Toh ki dinga yawo da inhaler din ki amma" Imaan tace "Toh nagode" Ammi ta fito daga daki tace "Har xa ki tafi Farida" farida tace "Ehh Ammi yamma yayi" Ammi tace "Toh mun gode da ziyara, ki gaida mamarki da mutan gidan kin ji" farida tace "In sha Allah xa su ji" body spray uku Ammi ta sa mata a leda, ta amsa tana godiya suka fita tare da Imaan da ta sa hijab xa ta rakasu, xaune suka tadda Mujaheed a part dinsu kusa da parking space a kan farin kujera idonsa a kan wayar hannunsa, farida na daga inda take ta gaishesa ya kalleta sannan ya mike yace "Why did you come without telling me?" ta d'an buda ido tace "Saboda baka son inna ta bani labarin ka? To yau duk naji komai" Dariya Maimoon tayi har da imaan ya watsa masu wani kallo fuska daure, Farida tayi murmushi tace "Kawai na xo anguwar ne shine nace bari in karaso in gaida inna" yace "But da rana ai mun yi waya kuma baki ce kina anguwar ba" tace "Noo ban taho ba lkcn, nima fa ban san ma xan fito ba, I came on an errand for my mum" Kamar ance Mujaheed ya daga kai ya ga Ummar sa tsaye a balcony na sama tana kallonsu keenly, farida ta kalli sama ita ma, ganinta ta sunkuyar da kanta, murya can kasa yace "I think you have to go in ku gaisa tunda ta gan ki" Tace "Toh" imaan tace "Toh Anty farida sai wani lkci xan amshi number dinki gun yaya idan xai bani" ta gefen ido ya harareta, farida tace "Toh shi kenan imaan na gode sosai" Daga haka ta wuce Maimoon tayi leading din farida xuwa parlon Umma, Umma na xaune wayar ta a hannu suka shigo, Farida ta durkusa kasa tana kallonta tace "Ina yini Umma?" Murya can ciki umma tace "Lafiya lau" Farida na wasa da fingers dinta tace "Ya aiki umma" umma tace "Alhmdllh" shiru farida tayi, Maimoon dai na tsaye sai tabe baki take, Umma tace "Ya 'yan gidan naku?" Farida tace "Suna lafiya" Umma tace "To yayi" bayan kusan minti biyu farida ta mike tace "Toh xan koma umma nagode" umma tace "Toh a gaida gida" daga haka ta fita Maimoon na biye da ita, dakin Anty suka shiga, Anty taji dadin ganin ta, bayan sun gaisa ta tambayeta mamarsu farida tace "Suna lafiya Anty" Da ta tashi tafiya Anty ta bata dubu daya kudin transport, Maimoon ta amsar mata don kin amsa tayi suka fita dakin Anty, Mujaheed na tsaye parking space suka fito gidan, bayan sun iso inda yake yana kallon farida yace "Gida xa ki koma yanxu?" Tace "In sha Allah" yace "Ohk mu je in ajiye ki" har ya bude mota wayarsa ya fara ring, ya duba yaga umma ce ke kiransa, a hankali ya daga ya kai kunne, Umma tace "Ina jiran ka parlor yanxu" yace "Toh" daga haka ta katse wayarta, ya kalli Farida a hankali yace "Bari in baki transport kawai dear, akwai aikin da xan yi yanxu" daga haka ya fiddo dubu biyu ya mika mata, ta girgixa kai tace "A'a ka bar shi I have transport thanks" ya mika ma Maimoon yace "Ki bata plss" Maimoon ta amsa, yana kallon faridar yace "Sai mun yi waya dear" daga haka ya wuce ciki. Maimoon ta tabe baki tace mu je Anty farida. A hankali Mujaheed ya bude kofar parlon Ummarsa ya shiga da sallama, tsaye ya sameta ta rungume hannu tsakiyar parlon wandering about, ya karasa yace "Umma gani" kallon da ta dinga masa ya sa ya durkusa ya sauke kansa kasa, tace "Mujaheed dama ban raba ka da wannan yarinyar ba?" Ya kalleta da kyar yace "Umma ni ban fa san da xuwanta gidan ba, kuma...." Sai yayi shiru, Fuska a murtuke tace "Kuma me?" Yace "Umma don Allah me yasa baki so na da farida?" Tace "Ra'ayi! Wato dai har yanxu kuna tare duk jan kunnen da na maka kwanaki koh? To wllh ka kiyaye bacin raina Mujaheed, ka kiyaye ni a gidan nan, uban me xaka yi da diyar talakawa ka ja min bala'i, in xama abun magana gun kawayena, duk fadin kaduna ka rasa budurwar da xaka nema sai wannan yar, warce iyayenta ke xaune a ghetto ? Haba Mujaheed are you even alright?" Yace "But Umma I see nothing wrong with that, arxiki fa na Allah ne, beside suna da rufin...." Umma ta dakatar da shi rai bace tace "Da ca nayi arxikin na kanin ubanka Sadeeq ne? Ni xaka ma wa'axi? To wllh in dai kana son kwanciyar hankalin ka a rayuwa ka fita harkar yarinyar nan, su je can su samu wani kuma, abubuwan alkhairi da ka dinga masu a baya da ciyar da su da ka dinga yi Allah ya saka maka da alkhairi, ina ji ina gani baxa ka auri yarinyar nan ba ka xama mai bada charity su talautar min da kai, yarinya dai dai class dinka in sha Allah xan samo maka tunda naga ba saiti gareka ba, ba abun mamaki ba wataran ma ka xo min da yar talla kace ita kake so, kai ko kunyan kanka ma baka ji, dubi yarinyar da Yusuf yake nema xar sha'awa yar masu kudi ta ma fi ubansa kudi shi ne kai xaka makale ma yar ghetto ko, to wllh ka guji bacin raina a gidan nan, sannan don munafurci da kinibibi ta shigo sumui sumui ta nufi gun alakakan kakarka da ba so na take ba a gidan nan salon duk ta bata ni gunta ta hure mata kunne, don wllh da ban ganta a sama ba dama bata yi niyyar shigowa gaida ni ba, ta kama ta tafi gun kakarka da kanwar uwarka Aisha tunda ita ta haife ka, Allah kadai yasan me kakar taka ta k'itsa mata, wato Mujaheed tarayyar ka da yarinyar ba abu bane mai yiwu wa samm kayi ta kanka tun wuri, daga this very moment na raba ka da yarinyar na har Abadan abidina, tashi ka ban waje mara tunani kawai" mikewa yayi bai ce komai ba ya nufi kofa ta bi sa da harara har ya fita ya kulle mata kofar ta. Xaune yake cikin Lafiyayyen motarsa nesa da gidan, abokinsa dake gefensa yace "Look ni fa na gaji da xaunar da ni da kayi cikin mota tun daxu Sadeeq..." Sadeeq ya shafa cute Beards dinsa a hankali yace "You just chill Fahad... jikina na bani xata fito soon" Tabe baki abokin yyi yace "Have you changed ur mind about loving and dating only whites?" Sadeeq ya xaro ido yace "Of course No, wannan fa yar yarinya ce.... I think she is not even up to 18, she is....." Sai kuma yyi shiru yana murmushi, Fahad da ya saki baki yana kallonsa yace "Sweet eighteen kenan" Yar dariya Sadeeq yyi a hankali underneath his breathe yace "she is beautiful" Fahad yace "and why didn't you callect her digit?" Wani kallon gefen ido yyi masa yace "Sai kace nine kai? How on earth xan amshi numberta bata ce in bata nawa ba" Bude gate da suka ji aka yi yasa duk suka daga kai da sauri, Mujaheed ne ya fito, walking majestically ya nufi motarsa da yyi parking a waje. Imaan na xaune bakin kofar kitchen tana ta yi ma Amminta dake girkin dinner hira, Ammi tace "Daxu inna ta xo fa wai tana nemanki idan kin dawo schl" Imaan ta xaro ido tace "Ni??? Ba ruwana baxan je ba, ce ma Abba tayi fa kar in sake xuwa mata ina kwasan maganganunta ina yadawa a gidan nan, ita gaskiya xata gudu ta bar gidan idan naje mata" Ammi tayi murmushi tace "Toh tace kwana biyu bata gan ki ba ko jikin ne" Imaan tayi dariya tace "Xa ma ta fadi gaskiya ne, ba inda xanje ta sake cewa na mata laifi gwara dai Maimoon ta ci gaba da xuwa tana kai mata abinci" Ammi tace "Toh ke xa ki kai yau, kina ajiye mata ki gaisheta sai ki fito ba shi kenan ba" imaan ta bata fuska kamar xata yi kuka tace "Ni dai Ammi nayi alkawarin baxan sake xuwa part dinta ba fa" Ammi dai bata ce mata komai ba. Bayan magrib Imaan na Idar da sllh Ammi ta tilastata kai ma inna abinci sabanin Maimoon da ta dinga xuwa tana kai mata kusan kwana uku kenan, Imaan ta dau abinci ta fita fuska daure kamar mai shirin yin kuka, tana isa bangaren inna ta tura kofar ta shiga, Yusuf ne parlon suna hira, Inna

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment