Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

plate din dankali kamar jaka ai sai dai ni din..." Imaan dai bata kulata ba ta mayar da hankalinta kan Tv, Da sallama Mujaheed ya shigo parlon rike da ledan bread l, ya karaso ciki yana kallon empty cup din shayin da ya hada kafin ya fita, Imaan ta wani daure fuska tana kallon TV, Inna tace "Toh ba kya daure fuska ba dama kin handame komai kamar mayunwaciya, wllh Mujaheed yanda ka san ta shekara bata ci abinci ba, dubi abinda ta bar min fisabilillahi, ko mage aka bar ma wannan xata koshi balle mutum irina, yarinya dai sai ci kamar saniya" Imaan sai kallon Inna take kamar xata yi kuka, Mujaheed dai yayi murmushi ya ajiye bread din hannunsa yace "Toh tunda dai ba da kudin ki aka siyo kayan abincin ba kuma ba Amadun ki ko Bukar suka siyo ba me xai dameki? Gidan yayanta ne fa" Bai jira cewarta ba ya wuce sama, imaan ta dinga kallonta tana murmushi ranta fess, tabe baki Inna tayi ta bude bread din ta yagi kato a ciki a hankali tace "Toh da ban haifesu ba xa su haife ku?? da na sani ma in ki haifan nasu in ga ta tsiya, sai in ga ta yanda xa a same ku gantalallu kawai marasu tarbiya" sakkowa kasa imaan tayi ta dinga 6a66aka dariya, ita dai Inna bata ko kalleta ba ta tsuke fuska tana cin bread. Sai da tayi nakk dama ta mike ta kai plate da cup kitchen duk ta wanke duk abinda aka bata ta kife ruwan ya tsane sannan aka fara goge gogen kitchen din har wall din kitchen dai sai da ta goge sannan ta fito ta share parlorn tasss, sannan aka fara goge goge, tana goge sabbin kujerun da d'an kyallen da take goge goge tace "Babu wanda xai ce datti baxai fito daga parlon nan ba, kaii aji tsoron datti, datti ba kyau...." Ita dai Imaan kallonta kawai take, Inna ta gama goge goge ta wuce dakin su Hansai ta kwanta saman gado, nan ta dinga sharar bacci uwa tana dakinta. Sha daya da kusan rabi Mujaheed ya sakko parlon sanye da kananun kaya da suka amshe sa sosai, ya dinga kallon Imaan yana tsaye kusa da stairs, can yace "Ina Innar" ba tare da ta kallesa ba tace "Nima ban sani ba" juyawa yyi yana kallon Safeenah dake sakkowa a bayansa kamar mai tausayin stairs din, riga da skirt ne jikinta na atamfa da suka amsheta matuka, kayan ya haska ta ba kadan ba, she's really beauty.... fuskarta babu walwala har ta karasa sakkowa, tunda suka hada ido sau daya Imaan ta dauke kanta ta wani tamke fuska, ita ma Safeenar haka tayi tana jin wani mugun tsanar imaan har xuciyarta, Mujaheed ya karasa ya bude dakin dake downstairs yana kallon ciki, ganin Inna na bacci ya rufe ya dawo yana kallon Safeenah da fuskarta ke dauri tana kallon direction daban yace "She is sleeping" kamar jira take ta Juya da sauri ta koma sama, kallon Imaan yyi sai kuma ya bi bayanta, Imaan ta mike a hankali ta tafi dakin da Inna ke kwance ta bude jakarta ta dau dari biyar da ta gani a ciki ta rufe jakar sannan ta fito, kofa ta nufa direct ta fita parlon tana murguda baki, Mai gadi ya tashi ya bude mata gate tayi ficewarta tana ce masa sai anjima yayi mata Allah ya kiyaye, tana isa babban titi ta samu adaidaita ta shiga ta gaya masa anguwarsu. Safeenah na shiga bedroom dinta Mujaheed ma ya shigo ya rufe kofar ya juya yana kallonta yace "Toh girkin fa...." Xaunawa tayi gefen gado tana cire dankwalin kanta dogon gashin ya sauka kasa, a d'an fusace tace "Toh wai ba cewa kayi tana bacci ba, and you brought the idea of asking her first before cooking, plss Mujaheed let me... Sannan gaskiya kada yarinyar nan ta sake xuwa min gidana daga yau, am sorry to say this wllh I dislike her with passion, I don't know why amma gaba daya naji na tsaneta with all my heart" Kallonta Mujaheed ya dinga yi da wani expression, fuska daure yace "You are looking into my face and telling me u dislike my blood, are you on ur right senses Safeenah??? meye damuwar ki da ita, to bari ki ji, ba ki isa ki hana imaan shigowa gidan nan ba tunda ba gidan ki bane.... Kuma ki sakko yanxu ki girka ma grandmum dita lunch" a mugun fusace tace "It's better ka fita ka tafi eatry ka samo masu lunch don wllh wlh baxan yi ba, Banda hauka ma ni na taba jin inda ake tilasta amarya sai ta yi girki on her third day a gidan miji, to baxan yi ba, ka fita ka siyo masu ko kasa blood din taka ta girka" tana kai wa nan ta mike a fusace ta tafi can karshen gado ta xauna, shi dai kallonta kawai yake trying hard to control his temper, underneath his breathe yace "I will treat ur f**kup soon" daga haka ya fice daga dakin, ta bi sa da harara murya can kasa tace "Xaka san blood din ka ce" Mujaheed na sauka downstairs ganin Imaan bata parlor ya tafi kitchen nan ma bai ganta ba, dakin da inna ke kwance ya shiga nan ma bai ganta ba, Inna ta d'an bude ido cikin muryar bacci tace "Azahar yayi Mujaheed?" Yace "Imaan fa?" A firgice ta mike xaune tace "Wacece kuma Imaan" bai ce komai ba ya fito dakin ya tafi compound nan ma bai ga alamanta ba, juyowa yayi da mamaki xai dawo parlor ya kusa cin karo da Inna tana xaro ido tace "Ina take?" Yace "Yanxu na sakko ban ganta ba" salati Inna ta saki ta fashe da kuka tace "Ai ni na shiga uku daga fito da yar mutane ta min rakiya ta 6ata, toh Ina ta shiga Mujaheed, ka rufa min asiri ita kenan Allah ya ba Bukar, har a koma ga Allah Bukar baxai taba yafe min ba wllh, ka cece rayuwata Mujaheed a nemo ta" Wani kallo Mujaheed ya dinga yi mata ta bangajesa ta nufi gun mai gadi da gudu tana hawaye tace "Yaro wata yarinya fara yar doguwa siririya kamar xata karye ta fita ta get din nan daxu??" Mai gadi yace "Ehh ta fita, har ma mun yi sallama" Inna ta saki wani dogon salati a rude tana tafe hannu tace "Amma kai d'an banxa ne sakarai gantalalle, ya xaka bar yarinya ta fita bayan tare kaga muka shigo, ita kenan fa gun uban a duniya, mutane dai ba tsoron Allah, ya bar yar mutane ta fita ta shiga gari, yanxu ta ina xan fara nemo Imaan ni patuu, ya ubangijina ka dubeni....." fashewa tayi da kuka ta fice daga gate din da gudu ko Hijabi babu, Mujaheed dai ya koma ciki ya dauko makullin mota ya fito ganin har Inna ta fice ya bude motar yyi warming dinsa Mai gadi ya bude masa gate ya fita, kafin Inna ta isa titi ta tare mutane sun fi biyar a hanya tana masu describing din Imaan ko sun ganta, duk aka ce mata ba a ganta ba sai ta rushe da matsanancin kuka tana cewa "Bukar baxai ta6a gafarta min ba har duniya ta nade" hakuri aka dinga bata tana tafiya tana kuka har ta isa titi, Parking Mujaheed yyi ya sauke glass, ya wani daure fuska yace "Shigo mu wuce" a fusace ta kallesa tace "In wuce gidan ubanwa ba yarinyar mutane, gidan ka dai ya xama na jaraba daga xuwa Imaan ta 6ata...." A fusace yace "Wai imaan din yarinya ce da xaki tsaya titi kina nemanta?" Ta xaro ido tace "Yarinya ce a gun ubanta wlh, ita kadai fa garesa, wllh ba ruwana ka rabu da ni Mujaheed, me xanje ince ma Bukar da Aisha idan na shiga mota...." Sai kuma ta rushe da kuka mai ta6a xuciya, ganin mutane an fara taruwa kanta Mujaheed ya ja tsaki yaja motarsa ya bar ta wajen, gida ya wuce direct, yana parking kofar gida ya shiga ciki, babu kowa compound din ya tafi part din su Imaan, ya kusa minti daya tsaye a balcony kafin yyi sallama murya can kasa ya bude kofar ya shiga parlon, imaan ce xaune parlon da plate din abinci gabanta tana ci tana kallo, suna hada ido ta mike da sauri har tana tuntube ta nufi dakinta da gudu ta shige ta kulle kofa, Ammi ce ta leko daga kitchen, yyi kasa da kai yace "Ina yini Ammi" tace "Lafiya lau, ya gida" yace "Alhmdllh" komawa kitchen tayi ya xauna saman kujera a parlon, ba a dau lkci ba Ammi ta fito tace "Ya amarya fa..." ya d'an yi murmushi yace "Tana lafiya" tace "To maa sha Allah, a xubo maka abinci?" Yace "A'a Alhmdllh" dauke abincin da imaan ta bari a parlon tayi ta kai dinning ta ajiye ta dauko wani plate ta rufe, Ammi tace "Ka dawo da Innar ne?" Yace "A'a, tana dai tahowa" Bai rufe Baki ba sai ga Inna duk ta hada xufa tace "Ina Bukar yake?" Ammi na kallonta da mamaki tace "Sannu da xuwa Inna" Inna tace "Ke tambayar ki nake Ina Bukar, ban ga imaan ba wllh..." Ammi tace "Imaan kuma, ae ta dawo tun daxu" salati Inna tayi a hankali tana tafe hannu tace "Ta dawo?? Amma wannan 'ya ta Bukar axxaluma ce wllh, Allah kaga yanda yarinyar nan ta daga min hankali na dinga tona ma kai na asiri a titi, Allah kaga yanda ta sa na bar jakata da dubu daya a gidan mutane na fito ba shiri, Allah kaga yanda ta sa cikina ya rude a titi na dinga neman bayan gida...." Sai kuma ta rushe da kuka ta fita parlon tana cewa "Bukar dai ya haifi jaraba, don imaan jarababbiya ce, ko da yake uban nata ma fitinanne ne" Ammi dai banda murmushi ba abinda take, ta kalli kofar dakin imaan tace "Imaan" sai da ta kirata sau biyu sannan Imaan ta yi ma Sadeeq sallama a wayan da suke yi, ta fito da hijab har kasa tana sunkuyar da kai, Ammi tace "Meyasa kika taho baki sanar da Inna ba?" Kamar xata yi kuka tace "Ammi bacci fa take ta yi, kuma ni na gaji ina son dawowa gida" Ammi tace "Toh ai kin kyauta" Imaan ta saci kallon Mujaheed dake ta kallonta, ta juya da sauri ta koma daki ta rufe kofarta. Some days later aka fara shirye shiryen saukan su Imaan a gidan, during this period soyayya mai xafi imaan suke yi da Sadeeq amma ta waya, gaba daya ya ki xuwa ta rasa me yasa sai dai ya kirata, kullum xancensa shi dai ji yake kamar ya jawo kwanakin duk da bai fi saura wata biyu xa su xana jarabawan waec ba, ko da xai xo gidan kuwa dama Inna yake xuwa gaidawa kuma ko ita imaan bata sani sai ya tafi xai kirata yace ai ya xo gidansu, ranan asabar ya kama saura sati daya saukansu, ranan kuma ya kama sati biyu da bikin Mujaheed, misalin sha daya da wani abu na safe ya xo gida tare da Safeenah, ubansun lace ne jikinta sai mayafi da ta sakale a wuya hannunta rike da handbag sai takalmi mai tsini da ta sa, tayi kyau har ta gaji, sai xuba kamshi take, fuskar nan nata ya sha make up ba a cewa komai, part dinsu ya nufa tana biye da shi, su Maimoon da Ummi suka yi welcoming dinta da fara'a, ta amsa masu da siririyar muryarta tana murmushi, Maimoon ce ta tafi sama ta kira Aunty, Aunty na sakkowa tace "A'a Aunty amarya ce a gidan namu, Sannu da xuwa" Safeenah ta kalleta tace "Yauwa..." Aunty ta xauna tace "Fatan an tashi lafiya" Safeenah tace "Lafiya lau ya gida" Aunty tace "Alhmdllh, ya naku gidan" Safeenah tace "Lafiya lau" Aunty tace "Toh madallah..." Mujaheed dai sai kallon Safeenah yake jin bata gaishe da Aunty ba, Bai dai ce komai ba ya kalli Aunty yace "Abba fa?" Aunty tace "Tun safe ya fita" Mujaheed ya mike yace "Ohk bari mu gaida Inna" Aunty tace "Toh shkkn sai kun dawo" yace "Yusuf ya dawo?" Aunty tace "A'a bai dawo ba" kofa ya nufa Safeenah ta mike ta bi bayansa Aunty ta bi ta da ido har suka fita ta girgixa kai ta mike ta je ta ci gaba da abinda take, suna fita Mujaheed ya kalleta rai bace yace "Abinda kika yi kin kyauta kenan Safeenah, mum dita ce ita ma fa?" Tsayawa tayi tana kallonsa da mamaki tace "Me nayi kuma?" Yace "Did you greet her?" A fusace tace "Kai komai kace fada da bala'i, to ni ban ma sani ba, da muka fito sai kayi correcting dina ba ka dinga min fada ba haba" Bai tanka ta ba ya ci gaba da tafiya ta bi bayansa tana tabe baki, part din su Imaan ya shiga tana biye da shi tace "Nan ne part din innar?" Ya kalleta yace "Part din uncle dina" Bai jira cewarta ba ya shiga parlon da sallama, d'an tsaki tayi ta shiga ita ma, Ammi na xaune parlon ta mike ganinsu tana masu sannu da xuwa da fara'a, Mujaheed ya xauna ya gaisheta ta amsa tace "Sannun ku da xuwa" Safeenah da kallo daya tayi ma Ammi ta gane ita ce Mahaifiyar Imaan coz it's soo obvious, ta wani daure fuska tana kallon Tv, Ammi tun da ta kalleta sau daya taga bata gaisheta ba dama bata sake kallonta ba, ta tafi kitchen tana cewa "Bari in kawo maku ruwa" wani kallo Mujaheed ya dinga yi ma Safeenah da ta bude jaka ta fiddo chewing gum ta 6are ta jefa a baki tana tauna, murya can kasa tace "Did you greet her Safeenah?" Banxa tayi masa tana taune taunenta, Ammi ta fito ta ajiye ruwan kusa da shi, Yana kirkiran murmushi yace "Ae daga gida muke ma" Ammi ta xauna tace "Ae ruwa ne" daukan bottle water daya yayi yace "Daddy fa?" Ammi tace "Yana Abuja" Mujaheed yace "Toh xa mu je gaida Inna yanxu" Ammi tace "Toh maa sha Allah, nagode kwarai" mikewa yyi ya nufi kofa Safeenah ta mike ta bi bayansa Ammi ta bi ta da kallo, sai da suka sauka balcony ya juya yana kallonta kafin yace komai ta wuce sa da sauri tana kas kas da cingam fuska daure, gyada kai yyi ya dau hanyar part din inna ta bi sa a baya tana kyabe baki, Inna na share parlornta ta daga kai tana kallon Mujaheed tace "Waye wannan" Bai tanka ta ba ya cire takalmi ya shiga parlon, Safeenah ta cire takalmanta tana kirkiran murmushi tace "Sannu da aiki Inna, kawo in karasa share maki" Inna tace "A'a bar shi yi wucewar ki ciki, daga xuwa kuma sai ki hau shara ba ruwana, balle ma na gama" tace "A'a don Allah ki bari Inna, ki kawo in karasa" ajiye tsintsiyar Inna tayi ta mike ta amshe jakar hannunta tace "Toh ai nagode dama bayana kamar xai cire wllh, ita wancan mata tana kwance daki wai ba lafiya, dadin abun ma an san bata da lafiya kafin ta taho nan balle ace a parlon Inna, shi sa ban wani gigice ba, Allah dai ya yaye mata wannan bala'i da ba a san kansa ba....." Mujaheed sai kallon Inna yake sannan ya kalli kofar dakin bai dai ce komai ba, Safeenah ta gama tattare parlon ta kwashe dattin da bai taka kara ya karya ba a Parker sannan ta mike tana murmushi tana kallon Inna tace "A Ina xan xubda dattin?" Inna tace "Can bayan window xaki tafi kwandon sharan yana nan xaki gansa fess na wanke wllh sai a iya xuba tuwa a ciki a ci, sai ki xuba a hankali kar ya bata jikin kwandon har hypo na sa yayin wankewa" Safeenah ta fita parlon ta sa takalminta mai tsini ta wuce bayan window, Mujaheed na kallon Inna da sauri yace "Me ya sameta?" Inna na kakkabe kujera tace "Wai Imaan, toh ga ta nan dai ya dama da xaxxabi ta tashi, ko ina ciwo sai ga al'ada shi ma ya xo ya sa ta gaba, daxu ta gama sharban kuka a nan, duk babu inda bata mirgina ba a parlon nan, ni dai baranda na koma nayi xamana ba ruwana, to nace ta tafi gidansu ta ki tafiya ya xan yi da ita...." mikewa yyi da sauri tace "A'a kar ka tasheta ka rufa min asiri, daxu wannan d'an albarkan Bulasawa ya xo dubata ya taho da magunguna da allurai...." Tsayawa Mujaheed yyi yana kallonta, Safeenah ta shigo parlon ta xauna kasan rug tace "Ina yini Inna?" Inna na murmushi tace "Lafiya lau 'yar nan, amma ku daina cika powder a fuska, kin dai yi kyau wllh powdern ne yyi yawa har kina naso..." Sunkuyar da kai Safeenah tayi tana ta kirkiran murmushin karfin hali, Mujaheed xai shiga daki Inna tace "Kinga fitina ko, Mujaheed nace kar ka tasheta, wllh allura aka mata ta samu bacci, ya xan yi da raina idan ka tasheta yanxu?" Bai tanka Inna ba ya shiga dakin, Safeenah na kallonta da sauri taace "Waye ba lafiya?" Inna ta marairaice tace "Wllh imaan, kamar baxata yi ba yau, nace kar ya tasheta ya ki saurarata, duk ya rikice...." Mikewa Safeenah tayi da sauri tace "Subhanallah bari in masa magana" daga haka ta shige dakin.
aa


*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.p.p.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment