Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Imaan ta dinga kuka har da shessheka, can dai tayi shiru ta goge idonta ta shiga kitchen ta dauko wani plate ta debi kwadon da Inna ke hadawa ta fice a parlon. Babu abinda Inna ta mance bata xaxxaga ma Umma dake dakinta a xaune tare da su Ummi dake mata tsarin abinda ya faru tsakaninsu da Imaan, Inna na huci tace "Kuma in sha Allahu sai kinga sauran ciwo a jikokin da xa a haifa maki..." Da sauri kuma tace "Astagafirullah, jikokin ki ai na Ahmadu ne, to in sha Allahu sai kinga sauran ciwo a dangin ku.... Kuma a kawo maki riko kiyi ta fama, duk wanda ya sake sa min jikata a bakin duniya Allah ya isa ni dai, Allah ya isa, kuma bari Ahmadun ya dawo...." Tana fadin haka ta fice. Imaan na shiga apartment din su ta tadda Ammi na ta girke girke, gaisheta kawai tayi ta wuce daki, tayi wanka tayi sllh sannan ta shirya ta fito parlor, kitchen ta shiga gun Ammi dake hada drink din Zobo tace "Ammi jirgi daddy xai biyo ko train?" Ammi tace "Ce maki yyi xai dawo yau?" Imaan ta xaro ido tace "Naga kina girki ne ai" Ammi tace "A'a mamar ku ce dai ke hanya...." Imaan tace "Mama Hadiza?" Ammi tace "Ehh sun ma kusa landing Ina ga" Imaan ta wara ido tace "Shine Inna bata gaya min ba?" Ammi tace "Ita ma bata sani ba shi yasa ban gaya maki tun jiya ba kar ki je ki gaya mata don ba control gare ki ba" Murna Imaan ta dinga yi tace "Da su Maryam xa ta xo in gansu plss?" Ammi tace "Da Maryam kadai suka taho" Imaan tace "Toh wa xai je daukota a airport nima xanje plsss" Ammi tace "Mujaheed Daddy yace yaje ya daukota" shiru Imaan tayi bata ce komai ba, can ta dau plate ta bude abinci xata diba. Hudu na yi Mujaheed ya tafi airport dauko small mum din tasa da autar ta, tun da suka kamo hanyar gida Maryam ke tambayar sa Imaan da turancinta dake kala da na turawa, yyi murmushi yace "Tana nan, tsayin ku daya sai dai ita bata jin magana..." Maryam ta kyalkyale da dariya tace "Ni duk na kagu in ganta wllh, muna fa vid call da ita once in a while" Mujaheed yace "Ae xa mu je ki ganta" Mama Hadiza tace "Amma dai yanxu ta ji sauki sosai koh?" Yace "Ehh mama da sauki sosai" Hadiza tace "Toh Alhmdllh haka Yaya Sadeeq din yace min, Toh in ji dai xa a kawo min amaryar mu gaisa kafin biki..." murmushi kawai yyi bai ce komai ba, tace "Au baxa ka kawota ba kenan" yar dariya yyi yace "Toh xa a kawota in sha Allah mama" Mama Hadiza tace "Toh da dai ya fi, kuna ta dai hakuri da tsufan Inna koh?" Mujaheed yace "Mu wllh da ma ki tarkatata ku koma tare mama" dariya Mama Hadiza tayi tace "Baka da kirki Mujaheed, ita uwar tawa kake cewa in tarkata?" Yace "Wllh mama duk ta addabi kowa a gidan..." Mama Hadiza tayi murmushi tace "In sha Allahu nan da wata hudu ma xa mu dawo Nigeria gaba daya sai in dauke uwata ta dawo wajena sai in ga ta inda xa ku dinga gajiya da ita" Mujaheed yyi dariya yace "Wllh baxata yarda ba, xata gwammace tayi ta xama tana dagawa Ahmadu da Bukar hankali" Mama Hadiza tayi dariya tace "Baka da mutunci wllh Mujaheed" parking Mujaheed yyi a parking space din su bayan sun isa gidan, Mama Hadiza tace "Allah sarki, rabona da gidan nan shekara uku kenan, anjima idan na huta da Magrib sai ka kai ni gidan Seeyama" yace "Toh Mama Allah ya kai mu" part din Abba Mama Hadiza ta fara shiga tare da Maryam don gaisawa da Aunty da Umma... Bata wani dau lkci a part din ba ta fito tare da Aunty, Umma dama tun bayan da suka gaisa ta shige daki ta kulle, Mama Hadiza na kallon Aunty tace "Rukayya dai na nan da rashin kirkinta har yanxu koh?" Dariya kawai Aunty tayi, Mama Hadiza tace "Toh yayi kyau ta ci gaba, har ni xata walakanta ta shige daki sbda bata da mutunci" ita dai Aunty bata ce komai, suka shiga part din su Imaan, Imaan ta fito daki jin muryar Maryam ta rungume ta cike da murnan ganinta, Ammi na kallon mama Hadiza bayan sun gaisa tace "Toh Ina jakar? Ko ba nan dama xa ku sauka ba" Mama Hadiza tace "Yana cikin mota Mujaheed bai fiddo ba" Ammi ta kai ta har bedroom dinta don ta kintsa, Aunty dai tayi masu sallama ta koma.
Maryam na idar da sllh bayan ta ci abinci tayi wanka dakin Imaan, suka dinga hira... Ganin Magrib ya kusa Imaan tace "Plss mu je ki ba Inna surprise kawai ta gan ki" Maryam tace "Hope ta daina xagin mutane dai yanxu" Imaan tayi dariya sosai tace "Sai dai bata ga abinda xata xaga ba, ke dai mu je" A tare suka fito dakin suka wuce part din Inna ba tare da sun sanar da su Ammi dake bedroom ba, Inna na bakin tap suka iso bangaren nata, ta daga kai tana kallonsu, Imaan dai sai murmushi take, Inna tace "Waya wannan kuma kamar Zabiya?" Imaan ta fara dariya tace "Baki ganeta ba Inna?" Inna ta ci gaba da wanke wajen tace "Ka dai ji wata magana wai ban ganeta ba, yanxu ko uwata ce ta fito daga kabari idan ban ganeta baxan ce mata ban gane ta ba, tun daxu nake durkushe a nan nake aiki babu mai taimakona, baki ji bayana ba kamar ya balle in huta...." Maryam ta hade rai ta shige parlonta, Imaan tace "Maryam ce fa Inna" Inna tace "Waye kuma Maryam" Dariya kawai Imaan take tana kallon Inna, Inna tace "ita ce ta xama kamar zal6e?" Imaan ta xauna a balcony din tana dariya, Inna ta tabe baki tace "Ku dai baku son gaskiya a gidan nan, yanxu da ba don wannan yar albarkan Maimoon ta gaya min a boye ba daxu da baxan ma san Hadiza xata xo gidan nan ba, Toh kuma kya taho min da yarinya tsigi tsigi kice Maryam, Yar da aka haifa hannuna ce aka ce maki baxan gane ba, ni fa na mata wankan farko kuma a gabana aka yayeta..." Inna ta tabe baki tace "Ni dai ba ruwana" Fitowa Maryam tayi daga parlon ta yi wucewarta, Inna ta bi ta da kallo ta kyabe baki tace "Ubansu dai ya cuce su ya hallaka su, ya kwashe su ya tafi kasar tsinannu yayi kaka gida, toh tana ma jin hausar kuwa" Imaan dai ta kasa cewa komai sai dariya take, Inna ta gama dauraye bakin tap din ta mike ta shige cikin parlonta tana cewa "Bukar dai ya haifi jaraba, ba don naka naka bane ai ni bana bari a cuci Bulasawa a lika masa ke ba, to banda haka ni sa'ar uwarki ce xaki xauna bakin kofa kina babbaka min dariya kamar mahaukaciya?? ita ma Hadizar dama kada ta kuskura ta xo min nan xan koreta tunda bata maida ni bakin komai ba, banda haka ta kamo hanya rai kwakwai mutu kwakwai baxata gaya min ba in mata addu'a, wannan ba shawarar kowa bace illa wannan mutumi Bukar don shi ne me irin wannan tunanin na marasu nutsuwa, Amadu baya haka" mikewa Imaan tayi ta bar wajen ta koma part din su... Bayan magrib tare Abba suka tafi gun Inna da Maryam, Inna na xaune parlon tare da Mama Hadiza da Mujaheed, Inna na ganin Maryam ta washe baki tace "Yanxu nake rokon Mujaheed ya tashi ya nemo min ke don tun saukan ku bamu hadu ba kin xo daxu ina gurje bakin pampo ke kuma baki jira in gama ba kika yi wucewar ki" Maryam ta xauna ta gaisheta babu walwala, Inna ta amsa da fara'a tace "Kun sha hanya, sai kawai naga kin kusa kamo imaan a tsayi..." Maryam dai bata tanka ta ba, Mama Hadiza sai murmushi take, Abba ya gaida Inna ta amsa tace "Ae gwara da ba a gaya min suna hanya ba Ahmadu da baccin kirki ma ni baxan yi ba, amma da na gansu kamar daga sama ai yafi ko" Abba na murmushi yace "Gaskiya ne" Mikewa Mujaheed yyi ya fita parlon Maryam ta bi bayansa, a jere suke tafiya tace "Ya M.A kaga abinda Inna ta min daxu kamar bata taba ganina ba" Dariya Mujaheed yyi yace "Xata maki fiye da haka ma, so take it off ur mind plss haka nan take, ya karatu?" tace "Alhmdllh...." Ya kalleta yace "Hope baki kula samari sai kin gama karatun" tayi dariya tace "Kai ya M.A, bayan ga Imaan ma tana da saurayi, ta ma ce min xai yi birthday soon and his frnds will be celebrating it for him, wai in bata shawarar abinda xata basa" Tsayawa Mujaheed yyi yana kallonta, can yace "When tace maki birthday din?" Ta wara ido tace "I didn't ask her, mun ma gaisa da shi a waya yace xai xo gobe ya gaisheni, his voice is cute..." Tana murmushi ta kare maganar, Shiru yyi bai ce komai ba ya ci gaba da tafiya a hankali tana biye da shi, Xaro ido tayi tace "Wait... Am I even suppose to tell you this??" Yar dariya yyi yace "Me yasa kika ce haka?" Tace "Naga irin kamar you are surprise.... Kila ma baka san tana da saurayin ba ni ce na maka revealing koh?" yace "Yes.. boye mana take, Amma kar fa ki ce mata kin gaya min she won't be happy" Maryam ta marairaice tace "Toh nima kar ka mata magana about it she won't be happy with me...." Yace "Sure I won't" suna isa part din su Imaan tace "Am spending the night here, ka ce ma su Maimoon, Ummi da Rahma su xo muyi hira plss" yace "Ohk xan gaya masu" daga haka ya wuce, tafiya yake amma gaba daya abinda Maryam ta gaya masa ne ke yawo a ransa... Wani murmushi yyi ya shiga sashin su.


*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
[7/19, 5:15 PM] +234 803 603 7561: Washegari da safe Imaan na kumbure kumbure ta gama shirin islamiyya bayan Ammi tace baxata xauna mata a gida ba, Maryam ta sami Ammi a kitchen a hankali tace "Ammi don Allah ki barta kar ta je yau, I don't have anybody to gist with idan ta tafi fa" Ammi tace "Ga kakarki can ki je ku yi hiran mana" da sauri Maryam tace "A'a ni bana son hirarta kawai tayi ta xagin mutane, nima ta fara xagina" Ammi tayi murmushi tace "She is ur grandma dai" Maryam tace "Sure, pls Ammi kin yarda kar taje?" Ammi tace "Karfe sha biyu xa su tashi ai, kuma sauka xa su yi soon Maryam, imaan ko shakkar fashi bata yi shi sa nayi forcing dinta ta wuce" Maryam tace "Ohk then, Allah ya kai mu 12 din" daga haka ta fita kitchen din, Imaan ta fito daki bayan ta dauko jakarta ta nufi kitchen ta tsaya bakin kofa kamar xata yi kuka tace "Ammi na tafi" Ammi tace "Breakfast din fa?" Ta girgixa kai tace "Ni sai na dawo" Ammi tace "Oho cikin ki" Juyawa imaan tayi ta fita, Maryam ta rakata xuwa parking space, dai dai fitowar Mujaheed da makullin mota a hannunsa, Maryam tayi masa murmushi tace "Good morning ya M.A" ba tare da ya kalleta ba yace "Morning Maryam kin tashi lafiya?" Tace "Sure.. Alhmdllh" Imaan dai tuni ta dauke kai, Maryam tace "Aiki xaka fita ya M.A" yace "Noo, sai da yamma nake fita aiki during weekends" Tace "That's nyc... Do you need my company?" Ya kalleta kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Sure... if that will suit you" ta kalli Imaan tace "Alryt sweetheart xan raka Ya M.A, ayi karatu da kyau a islamiyya" imaan ta kalleta tace "Ohk bye" tana fadin haka ta saci kallon Mujaheed taga kallonta yake, da sauri ta dauke kai, Ya bude motarsa ya shiga ya tada, Maryam ta xaga ta shiga gaba. Ko da Imaan ta dawo daga Islamiyya karfe sha biyu Maryam bata dawo ba, Imaan na kallon Ammi tace "Ammi wai tun da safe har yanxu Maryam bata dawo ba?" Ammi tace "Ehh wai sun fita tare da Mujaheed koh?" Imaan ta tabe baki ta mike ta wuce dakinta. Bayan azahar tana gama cin lunch ta tafi bangaren Inna, Inna na xaune parlor tare da Mama Hadiza, Imaan ta gaida small mum din nata sannan ta gaida Inna da ta tsuke fuska, Inna ta amsa tace "Ke kiji Hadiza da wani mummunan xance Imaan, wai duk abinda xa ayi na bikin Mujaheed mai kyau ko mara kyau in saka ido kar in yi magana, Saboda ita bata da tsoron Allah, bata son gaskiya xuciyarta ta kekashe, to me mutum xai min wanda Allah bai min ba" Mama Hadiza tace "Ni dai ki fahimce ni Inna, idan ba mu fada maki gaskiya ba kina da mai gaya maki ne, ba girman ki bane komai kika gani ki tanka a tafi da ke a baki, Haba inna" Inna tayi mitsi mitsi da ido tace "An dade ba a tafi da ni bakin ba, ni da bikin jikana ki dinga gaya min maganan banxa, ke kinsan wahalan da nayi da Mujaheed kuwa, wllh wllh ko Rukayya bata da iko da shi a yanxu, mutumin da yasa na dinga fada da jama'ah a anguwa yau ya kwale d'an wancan gobe ya danne d'an wancan, da ma Allah ya rufa min asiri bai sa an min duka a anguwar ba har Allah ya raba ni da anguwar? ke kinsan sau nawa na shirya na tafi makarantar su Mujaheed fada da malamai kuwa... Kishiyoyina kuwa duk min dambatu da su a kan Mujaheed, Sannan ace wai in xama kurma a bikinsa kamar uwata tace min je ki kya gani? To wllh karya ake...." Mama Hadiza tace "Ba ace ki xama kurma ba amma ba komai xa ki tanka ba, ba komai xaki shishshige ma ba, Allah na tuba Rukayyar da ma in don ta nata ne bata son a shiga lamarin bikin, ji fa tasan don bikin takanas na xo kasar nan amma tun sannu da xuwan da ta min jiya a bangarensu ban sake ganinta ba, ace kuma tayi farin ciki da xuwana...." Inna ta kunduma ma Umma xagi tace "Ai ba ita ke aurar da d'a ba nice nan mai aurar da Mujaheed kar ki ji komai, mu xuba kuma a gani, Allah dai ya kai mu ranan da rai da lafiya, sai dai mu kwashi yan kallo da ita a bikin nan idan kuma bata yi hankali ba dama baxata kwana gidan nan ba ranan bikin" Mama Hadiza ta tabe baki bata dai ce komai ba, Inna tace "Haka kawai, inyi wahala da shi a dinga gaya min maganan banxa" Imaan dai murmushi kawai take tana danna wayar hannunta, sallama aka yi bakin kofar parlon, Imaan ta juya da sauri jin muryan Sadeeq, Inna ta mike daga xaunen da take da sauri tana washe baki tace "A'ahhh sannu da xuwa Bukar, kai ne da ranan nan... Bisimillah shigo abun ka... Ba kowa daga ni sai Hadiza da Imaan" da gudu imaan ta shige dakin Inna, Sadeeq ya shigo parlon kansa a kasa, Inna na washe hakora ta kalli Mama Hadiza dake xaune kan kujera tace "Ke tashi ki basa waje ya xauna mana, sirkin ku ne" Sadeeq ya bude ido yace "A'a kaka ga waje ai" Bai jira cewarta ba ya xauna saman carpet dake shimfide, Inna ta nufi fridge ta bude ta kwaso ruwa uku da malt uku ta taho, Mama Hadiza dai sai bin ta take da kallo cike da takaici, Sadeeq na kallonta a hankali yace "Ina yini?" Mama Hadiza tace "Lafiya lau, Sannu da xuwa" Inna tace "Saurayin Imaan ne, jira kawai yake ta kare sakandari ayi magana, d'an gidan Ahmad Bulasawa ne mai gidajen man fetur a arewa, sunan yayanki garesa.... Baki ga kirkinsa ba, ni dai tunda nake ban taba cin karo da mutum mai kirki da mutunta babba irinsa ba" Mama Hadiza dai ta kasa cewa komai, Sadeeq dai ya sunkuyar da kansa sai murmushi yake, Inna ta kwalo ma Imaan kira tace "Ji walakanci, to meye na gudu daga jin sallaman bawan Allah, baxa ki fito ku gaisa ba, ba don ke ba a ina xa mu sansa" Imaan da ta xauna saman gadonta ta turo baki ta ki cewa komai, Sadeeq na shafa kansa yace "Dama baki na xo gaidawa kaka" Inna tace "Ahh toh madallah, Ka ganta nan xaune...." Ta fadi haka tana nuna masa Mama Hadiza tace "Uban Imaan ne ya sha nono ya bar mata, ita ce autata, yaranta hudu a duniya Allah yayi ma daya rasuwa, dayar tayi aure tana can gidan mijinta a kasashen turawa, sai kaninta da ke karatu sannan wannan yarinya Maryam da suka xo tare, sa'ar Imaan ce yarinyar kawai dai Imaan ta fita tsayi, ita kuma Maryam din ta fi Imaan xama mace" Tagumi Mama Hadiza tayi tana kallon uwartata, Sadeeq kam murmushi kawai yake kansa a kasa, Inna tace "Toh duk ba wannan ba, kana da labarin bikin Mujaheed wannan Juma'ah me xuwa ne kuwa Bukar?" Sadeeq ya kalleta yace "Ai kam bata gaya min ba kaka..." Inna ta saki salati ta rike ha6a tace "Kaga fitina koh? Duk da dai ko ta gaya maka ko bata gaya maka xa ayi bikin baxa a fasa komai ba amma ai da ta gaya maka, Toh ni dai na gaya maka yanxu, bikin ranan Juma'ahn nan ne" Sadeeq yace "Toh Allah ya kai mu lafiya kaka" Inna tace "Ameen dai, ai har ya kai ni gidan da xa su xauna da amaryar tasa ni da imaan mun gani, baka ga gidan ba d'an madaidaici dai dai kafinsa dai, toh ba dai laifi... ni dai nace Allah ya sanya albarka ai dai ya fi babu wai d'an agwai da bak'in da" Sadeeq ya kasa daina murmushi nan ko dariya ne kawai ke cin sa, Takaici yasa Mama Hadiza ta mike tana kallonsa tace "Toh Sadeeq nagode da gaisuwa Allah yayi albarka bari in shiga can cikin gida" Yace "Toh Ameen mama, nagode" fita tayi daga parlon, Inna tace "Toh ki ce ma Aisha don Allah tayi miyar shuwaka yau, naji raina na so" Mama Hadiza dai bata ce komai ba, Inna tace "Don Allah Imaan ki rufa min asiri ku fito ku gaisa, wannan ai kauyanci ne daga ganin saurayi ki shige daki, ni ko lokacinmu ba a haka" Sadeeq yace "Ki kyaleta kaka" Inna tace "In kyaleta d'an nan?" bata jira cewarsa ba ta mike xata shiga dakin, Imaan na ganin haka ta maxa ta sa hijab dinta ta fito, Inna tace "Ki daina haka don Allah sai ayi tunanin goyon kauye ce ke, nan ko a Habuja aka haife ki" Dariya Sadeeq ya fara yi imaan ta daure fuska ta xauna saman kujera a hankali tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau, ya gida?" Inna ta xauna tana murmushi tace "Gida Alhmdllh" kallonta Imaan tayi da sauri ta wani daure fuska, can ta kallesa tace "Let me see you off, since you've accomplished ur mission here today" Yana murmushi yace "I see why you don't want the 3 of us together..." Inna dai sai washe baki take tana kallonsu tace "Ae ita ma babban makaranta tayi, babu irin turancin da bata iya ba wllh" Mikewa Imaan tayi tana kallon Sadeeq tace "Let go" Mikewa yayi trying hard not to laugh yace "Toh kaka na gaishe da Mama da ke, ni xan koma" Inna tace "Ai mun gode da gaisuwa Bukar Allah maka albarka...." Dubu goma ya ajiye mata tayi tagumi tace "Ni dai na shiga uku Bukar baka gajiya??" kofa ya nufa yace "Ai ba yawa kaka, ayi hakuri" daga haka ya fita don tuni Imaan ta fice daga parlon, sai da suka bar part din Inna Sadeeq ya tsaya ya dinga dariyar da bai samu damar yi a parlor ba non stop, Imaan ta dinga kallonsa kamar xata yi kuka, ganin yanda yake dariya seriously ta jingina da flower tana ci gaba da kallonsa don bata taba ganin dariyarsa haka ba sai this very moment, he looks more cute laughing, bata san lkcn da tayi murmushi ba her eyes still on him, don kansa ya gaji ya dakatar da dariyar haka, a hankali tace "You look cute while laughing" da sauri ta rufe fuskarta bayan ta fadi haka, ya kafeta da manyan idanuwansa, kamar ta sani kuwa ta juya masa baya tana xaro ido, and he felt like hugging her tightly to himself, ya dai yi murmushi ya sauke kansa kasa praying in his mind Allah yasa xuwa wajensu Abba da xai yi tare da uncles dinsa in few days time won't be a futile effort... Takun da suka ji a bayansu yasa duk suka juya a tare, Mujaheed ne ke tahowa tare da Maryam, Sosai gaban Imaan ya fadi tayi still inda take, tunda ya kallesu sau daya ya dauke kai, Murya can kasa Sadeeq yace "Is she the Maryam?" Imaan ta gyada kai a hankali tace "Sure" Suna isowa inda suke Sadeeq ya mika ma Mujaheed hannu, Mujaheed na kallonsa ya mika masa nasa, Sadeeq yace "Ya aiki?" Mujaheed yace "Alhmdllh" daga haka ya wuce, Maryam ta gaida Sadeeq, Yana murmushi yace "It's nice meeting you Maryam, hope babu gajiyan hanya yanxu" Tace "Ba gajiya kam, kun fa dace da sis dita, Allah ya bar ku tare" ya wara ido yace "Ameen, I love those last words of urs... Kuma dole sai na biya words din, you say what ever you want ko menene idan kuma kin bar min xabi shikenan" ita dai Maryam dariya kawai take tace "Toh nagode Sadeeq" daga haka ta bi bayan Mujaheed da sauri, tana iskesa murya can kasa tace "Wllh he is just too cute Ya M.A, Imaan is very lucky..." Mujaheed bai tanka ta ba ya bude kofar parlon Inna ya shiga ta bi bayansa, tana cewa "Nama san me xan ce Imaan ta basa for his birthday...." Kallonta yayi yace "Me xaki ce mata.." ta kashe masa ido tace "That's our secret big Bro" Xaunawa yyi saman kujera yana kallon Inna, Inna tace "Yanxu wannan yaron dake neman Imaan ya fita, baka ga yanda ya dinga fada imaan bata gaya masa bikin ka ranan Juma'ah bane, gaba daya bai ji dadi ba, Allah kadai yasan me Bulasawan da kansa xai baka, mutum miloniya meye kuma baxai bada ba" a fusace Mujaheed yace "Sai dai ya baki ke da kike bukata, amma ni bana bukata, kuma don Allah kiyi hakuri ki daina maganata a gaban mutane bana so, ni abinda nake da shi ya isheni xaman duniya ba sai na hangi na wani ba" Yana fadin haka ya fice daga parlon, Inna ta tabe baki tace "Uwarka Rukayya ka gaggatsa ma magana ka fita ba ni ba wllh, ba abinda ya hada ni da kai dama, kawai Ahmadu ne ya haifeka ni kuma na haifesa, Ni ban yi mamaki ba tunda goyon Rukayya ce kai din ai, xaka yi fiye da haka" Maryam na dariya ta mike ta fita a parlon ita ma, da daddare Imaan na fitowa daga wanka daure da towel tace "Wai ina kuka je daxu da yaya tun safe" Maryam dake operating laptop tace "Wato kina wanka hankalin ki na wajen ki fito kiyi tambaya" Dariya Imaan tayi tace "Eh mana" Maryam ta ajiye laptop din a gefe tace "Ae babu inda ba mu je ba..." Imaan tace "Kamar Ina da Ina?" Maryam tace "Ya fa ce kada in gaya ma kowa har ke" Imaan ta xauna kusa da ita tace "Don Allah ki gaya min, ai ba gaya masa xan yi ba" Maryam tayi dariya tace "Anya xan iya gaya maki kuwa, ce min fa

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment