Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace ko bayan ranta bata amince da auren ba, kuma a ranan na shirya na je wani waje aka ce in kwantar da hankalina ba matarsa bace ba ma, wannan dai Hafsar ita ce matarsa kuma wai kwanan nan xa ayi bikin, kila a hada tare da na Mujaheed, tunda gashi har mun kusa gama hada lefen nasa" Hajiya Balaraba tace "Ke ma dai da daukan ma kai, to meye xaki wani damu a kan lamarin d'an kishiyar ki??" Umma tace "Ashe ma baki gama sani na ba kenan duk kusancin mu Balaraba, ni xan so abu mai kyau ya ra6a Aisha da 'yar ta, Yusuf ai abu ne mai matukar kyau, idan ya auri yar wajen Aisha ai ba karamin dace yarinyar tayi ba, ga arxiki ga shi da hankali da natsuwa, toh ina xan yarda, kiri kiri fa kun ga bakin cikin da ta dinga nunawa lkcn bikin Seeyama, babu abinda ta ta6uka da bikin sai dai ta leko ta koma, da aka tashi kai Seeyama ma ita ce karshen tafiya sannan farkon dawowa duk sbda hassada, shine xan yarda abun kirki ya sameta ita ma, inaa ai tunda naji ance min ba matarsa bace hankalina ya kwanta, sai ga kakarsu ma tace samm ba da yawunta ba" Hajiya Balaraba tace "Toh Alhmdllh" Hajiya Balaraba ta shiga jera tulin inner wears din da suka siyo kasuwa a daya daga akwatina takwas dake dakin Umma, Umma tace "Dole ma Mujaheed ya xo ya kara kudi, don wannan da ya rage ba isa xai yi ba don har gwal ina son mu saka a kayan, ko da dankunne da sarka da xobe ne kawai banda awarwaro" Hajiya Balaraba tace "Gaskiya kam, xa ma su fi ganin lefen da mutunci, to shi gogan na duba kayan ma kuwa?" Umma tace "Idan an gama hadawa sai su duba tare da ubansa, in sha Allahu kafin karshen watan nan xa a gama komai, su tafi su kai gaisuwa tare da sadaki da ubansa" Imaan na tsaye kitchen tana wanke plates a sink Ammi ta shigo tace "Kina da card a wayar ki in kira daddy nayi missing calls dinsa, mine is exhausted" Imaan ta juya ta kalleta da farko rasa abinda xata ce mata tayi, can a hankali tace "Ammi wayana baya wajena tun 3 days ago fa" Ammi na kallonta da mamaki tace "Baya wajen ki? To yana ina?" Imaan tace "Yaya ne ya amshe, ni kuma ban tambayesa ba har yau" Ammi ta wani hade rai tace "Wato ke baxa ki ji magana ta a gidan nan ba ko Imaan, ban raba ki da Mujaheed ba?" Imaan tace "Wllh Ammi ni na daina kulasa a gidan nan ki tambayi Inna, idan ma yaje part din inna ni shigewa daki nake ko in taho gida, wllh na daina xaunawa inda yake ma, kuma da ya amshi wayar ni ban tambayesa ba har ynxu, ban ma san wayar kuma ko ya bani" Ammi tace "Toh yayi kyau, xan ji ko shi ya siya maki wayar" Imaan tace "Wai don sbda Sadeeq na kirana fa shine ya karbe" shiru Ammi tayi tana kallonta, can tace "Toh ina ruwansa da kiran Sadeeq din?" Imaan ta bude hannu alamar bata sani ba, Ammi ta juya ta fice daga kitchen din. Da rana Aunty ta shigo parlon su Imaan da sallama, Imaan dake cin abinci parlor tace "Sannu da xuwa Aunty" Aunty tace "Yauwa Imaan, Ammi fa?" Imaan tace "Tana daki" direct bedroom din Ammi Aunty ta wuce, Ammi dake jera kayan guganta a press ta ajiye kayan hannunta tace "Yanxu nake son gamawa inje in maki ban gajiya Hajiya sai kuma ga ki" Aunty tace "Nima ban gajiya na xo maki ai" gaisawa suka yi Aunty ta xauna gefen gadon Ammi tace "Halan daddy ya koma" Ammi tace "Ehh tun jiya ya koma, ya su Maimoon fa, kwana biyu ni ban ga Yusuf ba ko tafiya yyi babu sallama" Anty ta tayi murmushi don har sannan tasan Ammi bata ji abinda Inna ta masa ba tace "Yana nan kuwa, amma next week xai tafi Abuja ina jin, aiki ne fa ya same mu in gaya maki..." Ammi ta xauna tace "Wani aikin kuma?" Aunty tayi yar dariya tace "D'an ki ne yyi min transfer daxu yana son mu fara hada masa lefe" Ammi tace "Yusuf?" Aunty tace "Ehh fa" Ammi tace "Ikon Allah, toh Allah ya bamu iko, Hafsar ce dai?" Aunty tace "Ehh ita" Ammi tayi dariya tace "Allah yayi kenan, kwanaki fa da nake tambayarsa ita ce min yyi shi fa ba ita xai aura ba, nace to wacece sai yace tana nan wataran xa mu santa" Aunty ta d'an yi murmushi tace "Toh dai jiya ce min yyi Hafsah" Ammi tace "Toh Allah yasa albarka, ya kuma sanya alkhairi" Sun d'an taba hira daga karshe Aunty tayi ma Ammi sallama, Ammi ta rakata har balcony tana ce mata sai ta leko ita ma. Tun daga wannan rana imaan ta fara wasar yar buyan gaske da Mujaheed, part din innan ma gaba daya bata son xuwa sai dole shi ma kai mata abinci, tana ajiye mata kuwa ko xaunawa bata yi xata juya ta bar wajen, Kwata kwata ita dai ba ta son ma su hadu, da ta tuna maganganun su Aunty Halima da Rabi'ah sai wani haushin sa ya diran mata, wai yana sonta, kai ta ma san kawai labarin su Anty Halima ne, ta ya yaya xai so ta, yanxu kam Sadeeq ta wayar Ammi yake kiranta dama da taji ring din wayar xata tafi da sauri ta duba ko shi ne, tun Ammi na complain har dai ta gaji ta daina. Yau da daddare Imaan na kwance parlor suna kallo tare da Ammi dake xaune aka danna bell, mikewa tayi ta sa Hijab ta nufi kofar ta bude, ido hudu suka yi da Mujaheed dake tsaye bakin kofar, gabanta ya fadi sosai tayi saurin juyawa ta basa hanya, ya shiga parlon yyi ma Ammi kallo daya ya sunkuyar da kai ya ajiye ledan hannunsa yace "Ina yini" tace "Lafiya lau, ya aiki" Yace "Alhmdllh, dama Abba ne yace in kawo wannan" Ammi tace "Toh Allah amfana" Yace "Ameen, sai da safe" Daga haka ya juya ya nufi kofa ya bude ya fita ya kulle kofar, Ammi ta bude ledan taga gasasshiyar kaza ce babba, duk son imaan da kaza kin ci tayi wai ta koshi, har hakan ya ba Ammi mamaki sosai, Ammi ta debi kadan ta kai sauran fridge ta ajiye. Ana saura few days su yi resuming schl ranan Friday da yamma sadeeq ya kira ta wayar Ammi, Imaan ta dau wayar da ke dakin ta yawanci, bayan sun gaisa yace mata yana waje, xaro ido tayi a hankali tace "Toh" daga haka ya katse wayar, Fitowa tayi daga dakinta gabanta na faduwa ta tafi dakin Ammi ta makale bakin kofa tana kallonta a hankali tace "Ammi ana kirana a waje" Ammi tace "Wa ke kiranki??" sunkuyar da kai tayi ta rasa wa xa tace don tun ranan da ta ambaci sunansa a gaban Ammi Ammi tace mata bata da kunya sunan Mahaifin nata take kira gatsau, to yanxu kam bata san ya xata kirasa ba, Ammi tace "Toh kar ki dade a waje" d'an murmushi tayi tace "Toh Ammi" daga haka ta fita dakin, as usual Hijab dinta har kasa ta saka ta fito, kamar mai tausayin kasa take tafiya har ta isa gate, Yana ganinta ya bude motar ya fito ya rungume hannayensa yana kallonta daga glass din idonsa, ta sunkuyar da kai har ta isa kusa da motar, cikin sanyayyan murya tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau dear, ya gida?" Tace "Alhmdllh" yace "Baki jin dadi ne, you look pale" tayi murmushi tace "A'a lafiyata lau" yace "To kaka fa, ko xa ki rakani in je in gaisheta" ta xaro ido tace "A'a ai bacci ma take" dariya yyi yace "Sure?" Tayi murmushi bata ce komai ba, yace "Ya Ammi" tace "Lafiyarta lau" yace "I want to take you out for shopping ko tare da cousin sisters din ki ne xata yarda?" Imaan ta xaro ido tace "A'a baxa a bar ni ba" yace "Ohk then" Shiru tayi bata ce komai ba shi ma haka, ta d'an daga kai suka hada ido, da sauri ta dauke kanta, murmushi yyi yace "On Monday xa ku yi resuming third term ss2, I am still counting fa" yar dariya tayi bata ce komai ba, yace "Yea, ss3 kuma term daya kawai xa ku yi shkkn, just few months to go in sha Allah" Imaan dai ba ta ce komai ba ta dinga kallon motar Mujaheed da yyi parking a nan waje maimakon ciki don har mai gadi xai bude gate sai kuma yaga yyi parking a waje, fitowa Mujaheed yyi daga motar kana ganinsa kasan daga asibiti yake, Imaan ta sunkuyar da kanta da sauri, Suna hada ido da Sadeeq har xai shiga gate sai kuma ya fasa ya nufe sa, Sadeeq yyi murmushi ya mika masa hannu hade da masa sallama, Mujaheed ya amsa yace "Ya aiki?" Sadeeq yace "Alhmdllh, wlcm back" d'an murmushi Mujaheed yyi ya juya ya nufi gate, sai bayan da ya shiga ciki Sadeeq na kallon Imaan da mamaki yace "Why didn't you greet him?" Tace "Ba ma shiri yanxu" ya buda ido yace "Why??" Tace "Nothing" Sadeeq yace "Uhn OK, nima daga hospital nake nace let me branch and see you pretty face" Tayi murmushi ta boye fuskarta, wani leda ya ciro ya mika mata, ganin bata ma san yana yi ba sbda fuskarta da ta rufe a hankali yace "Take dear" xame hannunta tayi ganin leda yake mika mata ta xaro ido tace "What?" Yana kallonta affectionately yace "Take plss" bata fuska tayi tace "Aa thank you bana so" yace "Karba plss" tace "Aa Ammina xata min fada" Shiru yyi yana kallonta, ta girgixa kai tace "Wllh Ammina xata min fada" Yace "Toh shikenan" cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri" yyi murmushi yace "Na yi, kar Ammi tace kin dade, ki shiga ciki" tace "Toh nagode" Yace "No thanks dear, bari in shiga in gaida kaka" imaan ta xaro ido tace "Ae bata tashi ba" yace "Ehh xan tasheta" daga haka ya nufi cikin gidan ta bi sa da kallo, Inna na bakin tap ya sameta, ta mike tana washe baki tace "Allah sarki Bukari ka xo min gaisuwar juma'ah ne" yana murmushi yace "Ehh kaka" tace "Toh shiga ciki ka xauna, bari in dauraye wajen nan in shigo" yace "Toh kaka" shiga parlon yyi ya xauna, Inna ta gama dauraye daurayenta ta shigo tace "Toh ya mutan gidan Bukar?" Yace "Alhmdllh kaka, dama sauri nake, nace bari in shigo mu gaisa, ga wannan a ajiye ma imaan" ajiye ledan hannunsa yyi, Inna tace "Atoh bari in shiga da shi ciki, Allah yayi albarka" daga haka ta wuce ciki da ledan, sai ga ta ta dawo da bowl dauke da dambun nama, ta shiga kitchen ta dauko leda ta fito ta juye a ciki tace "Gashi nan jiya nayi ni kadai rai na wllh, ko yaran gidan ban tsamma ba ma" Yana murmushi yace "Toh nagode kaka"
Imaan ta ajiye abincin hannunta tana kallon inna tace "Ina yini" mikewa inna tayi tace "Jira ni in dauko maki sakon ki, ni dai idan Bukar ya dawo xan ji ko Aisha ce ta hanaki xuwa bangarena yanxu, banda haka taya kina ajiye min abinci sai ki gudu kamar ana koranki, Aisha dai bata isa ta raba ni da ke ba tunda ba ita ta haifa min ubanki ba, idan ma ita ke hure maki kunne duk xan ji idan Bukar ya dawo, ni ba ruwana" imaan ta bi ta da kallo tana tabe baki, bata dau lkci a daki ba ta fito rike da ledan da Sadeeq ya bata tace "Wannan yaron kirkin ne ya xo daxu yace in baki, ko meye a ciki oho, kila wani zinarin ne ma, ni dai ban bude ba don ban gaji cin amana ba" Imaan ta xaro ido tana kallon ledan, can tace "Me yasa kika karba inna?" Inna ta hade rai tace "Toh baxan karba ba? A garin fulanawa kika ga ake maida hannun kyauta baya? Idan baki so sai ki bar min babu abinda ya sha min kai, ni ina so" wani kallo imaan ta mata ta bude ledan, still tayi tana kallon kwalin tsadadden waya da ake yayi, Inna ta saki wani kabbara tace "Toh idan ba Sadeeq din ba dama waye? Wa gare ki banda Allah sai shi din? Ko Bukar baxai siya maki dankareren waya haka ba balle Ahmadu" Imaan dai ta kasa cewa komai gabanta sai faduwa yake, Bude kofar parlon aka yi, Mujaheed ya shigo da sallama hannunsa rike da ledan fruit inna na washe baki tace "Mujaheed kalli wayar da yaron nan Sadeeq ya siya ma Imaan, ni nasan yayi dubu dari biyar" Mujaheed ya ajiye ledan hannunsa yana kallon kwalin wayar, Imaan ta mayar da wayar leda taki yarda ta kallesa ta mika ma Inna tace "Ki ajiye min" inna ta karbi ledan da sauri tace "Toh, nima dai na fiye surutu wllh" daga haka ta mike ta shige daki, Imaan ta mike ta fice daga parlon da sauri. Washegari asabar inna na daki ta ji an bude kofar parlornta ta fito tana tambayar waye, akwatuna taga ana shigowa da, ta saki baki tana kallon akwatunan tace "Meye wannan kuma?"



*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻‍Umma ce ta shigo parlon da sallama, su Ummi da Rahma da Maimoon suka xauna kan kujera Inna ta kalli Umma sannan ta kalli akwatunan tace "Lafiya Rukayya?" Umma ta xauna kan lallausan rug din parlon tace "Ina yini inna?" Inna tace "Cewa nayi meye wannan, daga ina??" Hajiya Balaraba da Hajiya Saude dake tsaye su ma sun shigo parlon suka gaisheta, Inna ta xauna kan kujera a fusace tace "Oh oh Allah, ni da ban yini ba xa ku gan ni, akwatunan meye wannan ake shigo min parlor dasu?" Hajiya Balaraba tace "Na lefe da xa a kai ne" Inna ta xaro ido tace "Lefen wa?" Hajiya Saude dake d'an tabe baki tace "Wacce Mujaheed xai aura..." Inna tace "Wani Mujaheed din?" Shiru duk suka yi basu bata amsa ba, Inna ta dinga sakin salati a jere, can tace "Yanxu Mujaheed aure xai yi ban sani ba sai dai inga akwatuna ana kokuwan shigo min da su ace min xa a kai lefe? Yanxu Rukayya mancewa kika yi ni na haifi Uban Mujaheed? Ehh lallai Ikon Allah ya fi gaban haka" daukar waya tayi ta mika ma Umma tace "Kira min d'an nawa.." Umma da ta daure fuska ta karbi wayar tayi dialing number Abba ta mika mata, Inna ta karba ta kai kunne, Abba na daga wa Inna tace "Yanxu Ahmadu ko ba raina kai ba mai ambatan sunana bane kace.... Allah sarki Inna, gashi Allah yayi lkcn auran Mujaheed baki a doron kasa balle ki sa albarka ke ma, Amma duk da haka muna maki fatan rahaman Allah... balle da raina da lafiyata Ahmadu?? wai sai dai inga katuwar matar ka na shigo min da jakunkuna tace min xa su kai lefe, yanxu ko shi Mujaheed din da nayi bauta da shi yana tsumma na cancanci yaki fadi min xa a kai lefensa sai dai inji a duniya? Wayyoo duniya Ina xa ki damu...." Bata jira cewar Abba ba ta katse wayar ta jefar kan kujera ta fashe da kuka tace "Oh oh Allah, duniya dai ba gaskiya, mutane basa jin tsoron Allah..." Hajiya Saude tace "Hajiya ba fa kai kayan xa ayi ba yanxu, kawai dai an gama hada kayan ne aka ce bari a xo a nuna maki, Amma ko gaisuwa ma ba a kai ga kai ma iyayen yarinyar ba tukun" Inna ta daga kai ta kalleta tace "Ai Rukayyar nan da kike gani ba mutum bace, idan uwarta ce Hadiza xata mata haka, Ina ce ranan da xa a fara hada kayan lefen ya kamata ta tako ta xo ta sameni tace to Inna gashi gashi, amma da yake xuciyarta ba tsoron Allah ban ganta ba, ni dai ba ruwana, kowa yyi da kyau.. kansa, bari kuma Ahmadun ya shigo in ji ko shi yace a boye min har sai an gama hada lefen" tana fadin haka ta Mike tana kakkabe kujerunta, mikewa Umma tayi tana kallon kawayenta da su Ummi tace "Ku kwasa mu je" Inna ta juyo da sauri tace "A kwashi me?? Ai ba ke kika min wahala da Mujaheed din ba, kuma da kyar idan ba da ni xa a kai lefen ba ma, don haka kada warce ta taba jakunkunan nan duk kuyi ta kanku ku fita ku bar min parlona in goge, nakudar Mujaheed kawai kika yi da haihuwarsa amma ni na masa abinda ya fi wannan, irin wahalar da nayi da shi ba sai dai Allah ya saka min ya biya ni ba, kuma shima Mujaheed din xai shigo ya sameni, idan bai ma yi hankali ba ma sai ince na bar sa da Allah..." tsayawa Umma tayi tana kallonta bacin rai karara fuskarta, tuni su Hajiya Saude suka fice a parlon, Ummi da su Maimoon suka bi bayanta, Inna ta juya tana kallon Umma tace "Ki fita don Allah xan goge daudar da ku ka shigo min da shi Rukayya" juyawa Umma tayi ta fice, Tsaye ta tadda kawayenta suna jiranta, Hajiya Saude tace "Amma gaskiya Hajiya Rukayya kina fama, yanxu haka kike xaune da wannan bala'eyyiyar tsohuwar nan har yau? Har yanxu kin rasa yanda xa ayi da ita ne?" Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Ku bari kawai, yanxu ina tanka ta abinda xata tsara ma d'an ta daban, shi kuma duk hakurinsa kika kuskura kika taba masa mahaifiya to babu xaman lafiya ranan, shi sa nake mata shiru" Hajiya Balaraba tace "Ke ma dai wllh, toh kin kasa yin komai a kanta ne?" Umma tace "So nawa kuma, sai dai Allah ya kyauta kawai, Amma wannan matar da ku ka gani ku kyaleta haka kawai" Hajiya Saude tace "A'a baki dai yi abinda ya dace bane, nima fa haka uwar mijina take a da amma ba yanxu ba kuma wllh, duk da nata bai kai na tsohuwar nan ba ma, Amma wllh ynxu sai labari, gaba daya gidan sai yanda nace ake yi, ina xan iya wahala??" Umma tace "Toh mu je ciki sai inji ya xa muyi, wllh na gaji, ita ce babban matsalata a gidan nan" Hajiya Balaraba tace "Toh kayan da ta hana fitowa da su fa?" Umma tace "Kayan xa su dawo hannuna in sha Allah, Mujaheed ne kadai ya isa ya fiddo da kayan daga parlon nan ko ubansa bai isa ba, kuma shi xan sa bari dai ya dawo" Hajiya Saude tace "Toh yaushe xa a tafi kai gaisuwar ne?" Umma tace "Uban cewa yyi sai kaninsa ya dawo Abuja, ae tuni na rufe bakinsa shi ma, komai nace cewa yake tohh" Duk suka kwashe da dariya suka shiga cikin gidan. Da magrib Imaan taje kai ma Inna abinci ta dinga kallon akwatunan da Inna ta jera a parlonta gwanin ban sha'awa, Inna ta shafe addu'an da take tace "In fiddo maki sabuwar wayar taki ne yanxu" Imaan tace "Inna wannan akwatunan fa?" Inna ta tabe baki tace "Daxu wannan mata Rukayya suka shigo da su wai ashe har xa a kai ma Mujaheed lefe bani da labari, Ina nan xaune kamar fanko" Imaan ta xaro ido tace "Aure xai yi Inna?" Inna tace "Ai shine nake jira Ahmadu ya dawo mu ji idan bola aka maida ni a gidan nan ban sani ba" Imaan da har sannan ke kallon akwatunan da surprise tace "Waow wllh sun yi kyau sosai, yanxu gidansu Aunty farida xa a kai kenan" Inna tace "Toh wacece dama banda ita, duk da dai iyayenta yaku bayi ne yarinyar na da hankali kuma ban jin xata gaji da ni idan na koma gidan Mujaheed da xama, lafiya xa mu xauna da yarinyar, ke kuma duk sati sai ki dinga xuwa kafin lkcn naki da bulasawa yayi" Imaan ta fara dariya ta xauna Inna tace "Toh bude mu ga tsiyar da suka xuba mata" Imaan na murmushi ta dinga sauko da akwatunan, sannan ta bude daya daga manyan ciki, xannuwa ne tsadaddu kwance a ciki, Imaan ta dinga fiddo su tana ajiyewa Inna na dauka tana duba kasan xannuwan don ganin ko babba ne ko karami, can ta tabe baki tace "Kin san Rukayya akwai shegen karya, ko sata xata iya sa Mujaheed yyi don tayi fafa, Toh xannuwa dai gasu duk masu tsada sai a xo a fidda min nawa da na takwarata a ciki" Imaan dai bata ce komai ba sai murmushi kawai take, ta bude wani akwatun, ta shiga fiddo laces masu suna lace, Inna ta rike ha6a tace "Ehh lallai Rukayya makaryaciya ce, wnn ai sai ta talauta min jika, Toh wannan ma sai a fidda min daya inyi doguwar riga, idan kyalle ya rage in baki a maki joni" Imaan dai bata ce komai ba ta bude akwatuna mai dauke da jallabiyoyi tsadaddu, Inna tace "Ki xabi wanda ya maki a ciki...." Imaan ta xaro ido tace "Innaa?" Inna ta hade rai tace "Toh sai su fidda min in baki" Akwatin dake dauke da takalma da jaka Inna ta bude, ta fiddo wani takalmi mai kyau sosai tana kallon imaan tace "Gwada wannan mu ga" imaan ta wani xaro ido a fusace Inna tace "Don Allah ki gwada" mikewa Imaan tayi xata sa takalmin aka bude kofar parlon Mujaheed ya shigo da sallama.


Afuwan it's short, gobe da safe xan yi update in sha Allah, I was kinda busy gaba daya yau ne. Tnxx.Kallonsu Mujaheed ya dinga yi, Imaan ta sunkuyar da kanta ta ki sa takalmin xata xauna, a fusace Inna tace "Ji walakanci don Allah, ba cewa nayi ki gwada ba?" Imaan ta hade rai tace "Toh nawa ne da xan gwada?" Inna tace "Oh oh Allah, yau naga fitina, to Ina ruwana da ko na waye, ni dai ba kawai in cire ma takwarata ba tunda ni baxan iya sa wa ba?? Ki gwada don Allah" Imaan dai bata ce mata komai ba ta xauna, Inna ta ajiye takalmin gefenta tana kallon Mujaheed dake tsaye tace "Toh da kaki gaya min xaka yi aure Mujaheed sai aka yi yaya? Sai aka dinga yagan naman jikina? Toh baxa dai a taba canxa ma tuwo suna ba, bauta dai na riga na gama maka sai dai Allah ya saka min da alkhairi, Amma kar dai ka manta akwai ranan sakamako" Mujaheed bai ce mata komai ba ya xauna kan kujera ya jinginar da kansa da kujerar a hankali yace "Akwai ruwan xafi?" Inna tace "Wanda Rukayya ta hado tare da akwatuna ta kawo min ba?" Mikewa Imaan tayi tace "Sai da safe Inna" Inna ta kalleta da sauri tace "Sai da safe bamu gama kallon kayan ba?" Imaan bata ce mata komai ba ta nufi kofa, Mujaheed ya bi ta da kallon gefen ido har ta fita sannan ya mike ya bi bayanta, Inna tayi tagumi tace "Naga abinda ya isheni ni patuu, wannan d'a na Ahmadu dai fitinanne ne, Ina lura da yarinyar nan gaba daya ta fita harkan ka a gidan nan, da ta ganka xata yi ta kanta ta bar wajen, gaba daya ta ma mayar da kai dodo, Ina kuma lura hakan na damunka ainun sbda baka samu damar dinga cutarta ba, to meye kuma xaka wani bi bayanta bayan bata kula ka ba, Ni dai gwara ma ayi auren nan ka kama gabanka jikata ta huta nima in huta da maganar ka haka, wllh ka cika fitina ko don maman Rukayya ka sha oho, tunda ita ma dai fitinanniyar ce" Juyawa Imaan tayi jin tafiya a bayanta, sosai gabanta ya fadi ganin shi ke bin ta, sai dai bata gudu ba sai kara saurin ta da tayi, ji tayi ya juyo ta har sai da ta kusa

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment