Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daban daban ta amsa ta nufi gun mota ta bude back seat tana kallon Inna tace "Wai dubu hudu da dari biyar" Inna tace "Toh ni xa ki gaya ma? sai ki gaya ma me siyan ai" Ta madubi Mujaheed ya kalleta yace "Waye me siyan ban da ke?" Inna ta gwalo ido tace "Ban gane ba" ya buda ido sosai yace "Ko sisi bani da shi, ban fito da kudi ba" Inna ta saki salati mai tsayi tana xaro ido tace "Nima ko sile ban fito da ba Mujaheed" Mujaheed ya daga kafada yace "Sai ki san abinda xaki ce masu" Inna ta kara sakin salati tace "Yau babu lafiya ni patuu an kacalcala kaji uku ba kudi" shi dai Mujaheed bai sake ce mata komai ba, ta kalli Imaan da xaro ido tana kallonsu, Inna tace "Maxa maida masu tsiyar su kice basu da girma an fasa siya, maxa koma" Imaan ta wani xaro ido tace "Iyyee, bayan an yanyanka wllh ni ba inda xan je" a fusace Inna tace "Da aka yanka ci muka yi? Ni naga abinda ya isheni, ki juya ki mayar masu kayansu ba mu da halin biya" Imaan duk ta rikice barin yanda taga duk mutan wajen na kallonsu tace "Na shiga uku, wllh Inna baxan iya komawa dubi fa maxa a wajen da yawa" jaraba Inna ta dinga yi inda take shiga ba nan take fita ba tace "Mazan banxa maxan hofi ina ruwanmu da su bamu da kudin biyan kaji..." wani gentleman dake xaune wajen ne ya taso ya iso gun motar yana kallon Imaan yace "Lafiya kuwa?" Inna tace "Ina fa lafiya yaro an kacalcala kaji uku ba kudin da xa mu biya, nace ta mayar masu tsiyar su shine take kokarin tara min jama'ah wllh ko amsar ledan ma ni ban yi ba balle inji kamshin naman ciki, Toh a kan meye baxa su amsa ba? Dama haka ake yi?" Murmushi kawai mutumin yake yana kallon Imaan yace "Kazan guda nawa ne?" Da sauri Inna tace "Gudu uku ne wllh, daya nata daya nawa, daya na yan sa ido a gida..." Hannu ya sa a aljihu yana kallon Imaan, Mujaheed ya bude motar ya fita gun masu gashin kajin ya fiddo dubu biyar ya mika masu, daga Inna har mutumin da imaan bin sa da kallo suka yi, Inna tace "Kaga katon banxa ko? Ce mana yyi ba shi da kudi fa har sai da ya bari duniya ta gama sanin abinda muke ciki sannan ya fita wani zokai zokai da shi xai bada kudi, Toh Allah ya saka min kunyata ni da ya so yi gaban masu kaji da tona min asiri da yyi a gabanka" Dariya mutumin ya dinga yi yana kallon Inna da ta tsuke fuska tana kallon Mujaheed, imaan ta kalli mutumin gabanta ta mayar masa da kudin da ya mika mata tace "Mun gode" Yana murmushi yace "Don't worry...." Dawowa Mujaheed dake kallonsu yyi ya amshi kudin hannun imaan ya kamo hannun mutumin ya saka masa a ciki yace "Thanks for ur concern" daga haka ya bude mata front seat yana kallonta, ta sunkuyar da kanta ta shiga ya rufe motar, ya xaga ya shiga motar ya tada ya bar wajen. Inna tace "Ni dai duk wanda niyyarsa ya kunyata ni a duniya Allah ya min kantangar karfe da shi, kuma ya saka min" Shi dai Mujaheed bai tanka ta ba har suka isa gida. Shirye shiryen biki aka shiga yi a gidan ba kama kafar yaro barin bangaren Umma da kawayenta, ji take kamar an mata albishir da aljanna xata aurar da first and only son dinta xuwa ga 'yar masu kudi ba na wasa ba, shi ko gogan kamar ba shi xai yi aure ba babu Shirin da yake, idan ya fita aiki tun safe dama sai dare xai dawo don kawai bai son participating a shirin da ake a gidan, shi gaba daya bai fi sau uku suka hadu da Safeenar ba ma, kuma duk Umma ke tilasta sa sai yaje, ko da wasa bai taba dialing lambar Safeenah don kansa ba sai idan yayi missing call dinta, a rana kuwa tana kiransa fiye da sau goma, shi kansa mamakin irin son da take masa yake duk da yasan dole ta fahimci fa baya yinta amma duk class dinta bata nuna ta damu ba sai kara shige masa take. Tun ranan da Mujaheed yyi ma Imaan warning ko da wasa bata son Sadeeq ya xo kofar gidansu sai dai waya amma abinda ke bata mamaki yanda taga shi ma bai damu ya xo ba kamar da, da kusan kullum sai ya xo, sai dai suna kusan raba dare suna waya da shi cikin duvet yanda Ammi baxata ji ba, Duk Friday day kuma sai ya aiko wani worker din gidansu gun Inna ya kawo mata sako, Imaan dai ta tasan soon Mujaheed xai yi aurensa ya kara gaba sai taga ta yanda xai hanata tsayawa da Sadeeq kuma. Yau Friday da ya kama saura sati daya bikin Mujaheed da Safeenah Imaan ta fito daga dakinta ta shiga na Ammi, durkusawa tayi kusa da gado tana kallon Ammi tace "Ammi xan wuce yanxu" Ammi tace "Toh na dai gaya maki kar ki dade imaan" tace "Wallahi baxan dade ba Ammi" Ammi tace "Toh ki gaisheta Ina mata ya jiki" Imaan tace "Toh xata ji" mikewa tayi ta fita daga dakin ta shiga kitchen ta dauko wani leda mai dauke da can malt ta fito parlor ta dau jakarta sannan ta fita gidan, kamar mai tausayin kasa ta isa bakin titi bayan few minutes ta samu adaidaitan da xai kai ta GRA, tafiyar kusan minti ashirin suka yi, suka shigo gate din layin as usual ko ina tsit sai haushin karnuka, dai dai gate din kantamemen gidan Imaan ta sa mai adai daitan ya tsaya ta sauka ta basa kudin tana kallon masu gadi dake xaune bakin gate din gidan, gaishesu tayi daya daga cikinsu yace "Wa kike nema?" Tace "Mariya" Mai gadin yace "Toh ki kirata" shiru tayi tana kallonsa don kwanaki da dadewa da ta xo ae basu mata tambayar komai ba, ba musu ta fiddo wayarta a jaka ta shiga Kiran Mariya, Ba a dau lkci ba sai ga Mariya ta fito gidan, Rungume imaan tayi tace "Welcome frnd" tana kallon masu gadin tace "Kawata ce duk ranan da ta xo ku bar ta shigo babu interrogation" bata jira cewarsu ba ta ja hannun Imaan cike da farin cikin ganinta suka wuce ciki, Imaan tace "Dama kin ma ji sauki koh?" Mariya ta marairaice tace "Yau fa nayi getting self dina" Imaan na murmushi tace "Toh Allah ya kara lafiya" sai da ta fara kai Imaan dakin Mahaifiyar ta ta gaisheta sannan ta ja ta xuwa makeken bedroom dinta, imaan ta xauna tace "Siblings din ki fa?" Tana fiddo ruwa da lemo a fridge dinta tace "Sun fita da Yaya Annur shan ice-cream kinsan yau Friday" murmushi kawai Imaan tayi, Mariya ta ajiye mata drinks din tace "Me xa ki ci, akwai yam with sauce, cous cous with sauce, or kin fi son snacks?" Imaan ta girgixa kai tace "A'a na ci abinci a gida" Mariya ta harareta tace "A'a ni dai sai kin ci wllh" Imaan tayi dariya tace "Bayan nace maki na koshi, Ni la'asar kawai xan yi" Mariya ta nuna mata bathroom dinta tace "Kiyi alwala ga bathroom kafin ki fito xan kawo maki abincin" bata jira cewar Imaan ba ta fita da sauri, Murmushi imaan tayi ta mike ta cire Hijab din jikinta ta ajiye ta shiga bathroom din, tana gama alwala ta fito dai dai nan aka bude kofar dakin, still tayi tana kallonsa, kamar yanda shi ma ya tsaya yana kallonta, juya masa baya tayi da sauri tana xaro ido....




*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788


*imaan isn't free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788

Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah. Subscribe and read happily.Sadeeq yayi murmushi a hankali yace "But you didn't tell me you where coming here da muka yi waya daxu" Ta dau hijab dinta ta saka still bata juyo ba tace "Ae ba wajen ka na xo ba" murmushi kawai yake yana kallonta, Mariya ta iso bakin kofar rike da tray din abinci tace "Ya Sadeeq Aunty na neman ka fa" ya kalleta yace "Har kin ji sauki kenan" dariya tayi tace "Ehh mana bayan alluran da ka sa aka min, Kuma ga kawata ta xo, Hope yau dai ka tuna ta" Ya langwabar da kai yace "Bayan ta ki juyowa ma in ga fuskarta balle in san wacece" Mariya ta wara ido ta kalli Imaan da ta ki juyowa da gaske, ta yi dariya ta karasa cikin dakin ta ajiye abincin hannunta ta isa kusa da Imaan ta juyota suna facing Sadeeq tace "Toh ka gane ta yanxu?" Shafa kai yayi yana cute smile dinsa yace "Anya.. wani anguwar take? Na taba ganinta ma kuwa?" Imaan bata san lkcn da tayi murmushi ba ta sunkuyar da kanta, Mariya ta bata fuska tana kallonsa don da gaske bata ji dadi ba, Sadeeq ya wara manyan idonsa yace "Toh Sannu da xuwa kawar Mariya, duk da dai ni ban gane ki ba" daga haka ya juya ya rufe masu kofar, duk yanda Mariya tayi forcing din Imaan ta ci abincin da ta kawo mata kin ci tayi wai ta koshi, ruwa kawai ta sha shi ma sip daya, Mariya da gaba daya bata ji dadin kin cin abincin da Imaan tayi ba tace "Dama ki dau drinks dinki ki koma da su bana so da gaske" dariya kawai Imaan tayi ta mike tace "Sai ki ba su Hafsat idan sun dawo, ni dai tashi ki rakani" Mariya tace "Bayan kin walakanta ni xa ki ce in raka ki" Imaan na murmushi ta nufi kofa tace "Toh ni fa na ci abinci a gida nace maki Mariya" Mariya ta mike ta bi bayanta suka fita dakin tace "Toh mu je ki yi ma Aunty sallama ya na iya da ke, nima dai ko ruwa kika ban idan naje gidan ku baxan sha ba" Imaan ta kalleta ta gefen ido tana murmushi suka shiga parlon mum dinta, Sadeeq na parlon tare da mum din nata a xaune, Imaan ta durkusa kusa da kujera tace "Aunty xan tafi" Mum din Mariya tace "Da wuri haka Imaan, toh Ina xuwa" tashi tayi ta tafi dakinta, Imaan ta sata kallon inda Sadeeq yake taga kallonta yake, ta dauke kai da sauri, Mariya tace "Ya Sadeeq yanxu fa su ya Annur xa su iya dawowa basu kawo min komai ba ko?" Yace "Toh ki kirasu mana" Tace "Toh don Allah kira min su ta wayarka, I can't imagine me not eating shawarma today" yace "Wayana na can gida" tashi tayi ta bi mum dinta daki don daukan wayarta ta kira step brother din nata, Sadeeq na kallon Imaan yace "Me yasa baku xo tare da kaka ba?" Ta dai yi murmushi bata ce komai ba, Aunty ta fito rike da leda ta ajiye kusa da Imaan tace "Ki gaida min mum din ki kinji Imaan" a hankali Sadeeq yace "Aunty ita ce fa warce nake yawan baki labari a kai...." Aunty ta kalli Imaan sannan ta kallesa da mamaki tace "Imaan din kuma?" Yana murmushi yace "Sure..." Sake baki tayi tana kallonsa, ya shafa kansa yace "Dama nace maki ba ma sai na kawo maki ita ba da kanta xata xo wataran ki ganta" Imaan taji kamar kasa ya bude ta shige don kunya, ta kasa dago kanta ta kalli Aunty, Aunty tace "Ikon Allah, wai da gaske kake don Allah Sadeeq" Yace "Gata ki tambayeta, but aunt this is our secret ko Mariya kar ki gaya ma plss Aunty, you know Mariya talks a lot...." Dariya kawai Aunty tayi ta xauna tace "Ikon Allah, Toh Allah ubangiji ya sanya alkhairi, yayi xabi na gari..." Yace "Ameen" Mikewa yayi yana kallon Imaan yace "Let me drop you" da sauri ta girgixa kai sai dai bata ce komai ba, Aunty tayi dariya tace "Aa ki je dai ya ajiye ki gida Imaan, ki gaida mutanen gidan kin ji, Allah maki albarka..." Sadeeq na murmushi ya nufi kofa ya fita, Aunty na kallon Imaan tace "Imaan idan ma kina da doubt a kan Abubakar a da, tohh stop that now kinji daughter, Sadeeq na son ki fiye da yanda kike tunani, I was so surprise da naji yace min ya sami yarinyar da yake so da aure yar Nigeria, coz ni nasan waye Sadeeq, I know him fiye da uwar da ta haifesa ma, kuma wllh duk jinsa nake ba wai na yarda ba, har gajiya nake da jin labarin ki a bakinsa, But plss kiyi kokarin kame kanki ki kare martabar ki na 'ya mace, am not saying this bcos Sadeeq is bad or anything of such, A'a Ina gaya maki haka ne a matsayina na uwa, ko Mariya iyakar shawarar da xan bata kenan...." Imaan dai ta kasa dago kanta, fitowar Mariya yasa Aunty tayi shiru, Aunty na kallonta tace "Ki rakata compound Sadeeq xai ajiyeta gida yanxu, he is waiting for her" Imaan ta mike tayi ma Aunty godiya cikin sanyin murya ta fita, Mariya ta dau ledan da Aunty ta ajiye mata tace "Mun gode Aunty" daga haka ta bi bayan Imaan da sauri, Mariya ta bata fuska ganin bata ga Sadeeq a bangarensu ba, tace "Kai ya Sadeeq maimakon ya dau motar dake nan yanxu sai mun bi sa har can" ita dai Imaan bata ce komai ba, haka suka dinga tafiya a lafcecen compound din xuwa bangarensu Sadeeq, Building din ya kusa biyun nasu Mariya, Kai kana gani kasan an rasa yanda xa ayi da Naira kuma, Motocin dake parking spaces din wajen sun yi goma ko wanne kuma ya wuce a kirasa mota sai dai Ride, ni kam nace don ma Inna bata xo taga gidan ba... Ai da gobe gobe xata sa Bukar da Ahmadu gaba ta tada bala'i a daura auren Imaan da Bulasawa... Lol, Sadeeq na xaune cikin daya daga motocin parking space din idonsa a kan Imaan dake tahowa tare da Mariya, irin kallon da yake mata yasa Mariya ta kalli Imaan sai dai bata ce komai ba, ana haka aka bude gate din gidan wani ride ya shigo compound din, Mariya tayi ma motar kallo daya ta dauke kai, Drivern yyi parking aka bude back seat, wata da baxata wuce shekaru hamsin ba ta sakko motar cikin shiga ta alfarma, tun daga kunnenta, wuyarta, finger, da wrist duk gold ne, tun da Imaan ta kalleta sau daya ta gane Mahaifiyar Sadeeq ce, Mariya tace "Sannu da dawowa Mami..." Sama sama matar ta amsa, Imaan ma ta gaisheta, ba tare da ta kalli Imaan ba ta amsa, tana kallon Sadeeq tace "Fita xaka yi yanxu Abba..." Ya fito daga motar yace "Welcome back Mami" tace "Yauwa..." Yana shafa kansa yace "Aunty tace in ajiye bakuwarta a gida..." Daga sama har kasa ta kallesa bata dai ce komai ba ta nufi entrance din babban gidan, ya bi ta da kallo, can yace "Mami xa a maki wani abun ne?" ba tare da ta juyo ba tace "Noo ka tafi inda aka aike ka, ka sameni parlona dai idan ka dawo, is Annur back?" yace "I don't think so" Front seat ya xaga ya bude ma Imaan yana kallonta, Mariya ta ajiye ledan hannunta a bayan motar ta xaga gun imaan tace "Plss kice ma Ammi ina gaisheta kin ji" Imaan ta shiga motar tana murmushi tace "Toh xan gaya mata" Sadeeq ya tada motar suka fita compound din Mariya na daga masu hannu, Sai da suka hau saman titi murya can kasa yace "Nayi missing din beautiful face din ki two days Imaan" Murmushi kawai tayi, yace "ke ko naga ma baki damu da rashin xuwa na ba koh? You won't even understand what I am going through now" Ta kallesa a hankali tace "I thought you are busy this days ne shi yasa" girgixa kai kawai yayi, bayan kusan minti biyar yace "My birthday is coming soon...." Ta kallesa tace "When" yace "7 days from today in sha Allah" shiru tayi don ranan daurin auren Mujaheed kenan, can tace "Toh Allah ya kai mu lafiya" yace "Anything for me?" Murmushi tayi tace "Me kake so?" Murya can kasa yace "Ke nake so Imaan" ta wara ido tace "Ni kuma" ya gyada kai yace "I don't know... i just have this urge of wanting to be with you, sai yanxu nake ganin nisan kwanakin da suka rage... I want you by my side as my wife" kasa kallonsa tayi ta kuma kasa cewa komai, ya kamo hannunta yace "Kin yi shiru" kwace hannunta tayi a hankali still ta ki cewa komai, parking taga yayi ta juya tana kallonsa, yayi kasa da murya yace "I am thinking of meeting grandmum, ko xata kara yi ma su Abba magana" Imaan ta kallesa da sauri tace "Maganan me?" Yana kallonta yace "Su yi hakuri su bani ke any time from now, wllh har professor xan iya barinki ki xama a gidana" Imaan ta girgixa kai kamar xata yi kuka tace "A'a ni dai, bayan ga abinda daddy na yace" Shiru yyi yana kallonta, cikin sanyin murya yace "Toh shikenan i will continue waiting and having patient in sha Allah" Driving ya ci gaba da yi, sai da suka kusa layinsu yace "My frnds are throwing a birthday party for me, kuma ke ce babban guess a wajen ranan" ta wani xaro ido tana kallonsa yace "Yea, don't turn down my offer baxan ji dadi ba....." Kasa cewa komai tayi yana shigowa layinsu gabanta yyi mugun faduwa, what if Mujaheed na waje yanxu haka, kafin ya isa kusa da gate dinsu da sauri tace "Kawai ma ka ajiye ni a nan ba sai ka karasa can ba" ya kalleta yace "Why?" Ta hadiye abu da kyar tace "Nothing" Bai ce komai ba ya kai ta har bakin gate din ta fara kalle kalle kamar munafuka ta bude motar ta fita yace "Wait Imaan" tsayawa tayi ya juya ya dauko ledan da Mariya ta ajiye mata, Mika mata yayi ta amsa tace "Nagode sai anjima" daga haka ta shige cikin gidan da sauri har hakan ya basa mamaki ya bi ta da kallo, tana shiga kuwa ta kulle gate din, sai da xuciyarta ya kusa shigewa cikinta ganin Mujaheed da Yusuf a compound din, Yusuf na xaune kan farin kujera Mujaheed kuma da alama gate xai fita amma sai kallonta yake, bata tsaya wani tunani ba ta fasa wani ihu ta sake ledan hannunta ta durkushe wajen tana yarfe hannu tana kiran Ammi, Mujaheed ya karasa inda take da sauri yana kallon kafarta yace "Me ya faru??" Ta kamo hannunsa tace "Wayyo Yaya kafana ban me ya same shi ba..." durkusawa yyi ya daga dogon hijab din jikinta yana kallon kafar, ta gefen ido ta dinga satan kallon kasan gate taga ko Sadeeq ya gama reverse.


*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788[7/19, 5:15 PM] +234 803 603 7561: Imaan ta kwace kafarta a hannunsa bayan ta ga Sadeeq ya wuce tana turo baki a hankali tace "Ni ya ma daina, dama gurdewa kawai nayi" bata jira cewarsa ba ta mike da kyar, Yusuf dake tsaye shi ma ya iso wajen yyi murmushi yace "Dama ba wani ciwo, ke dai kika san abinda kike boyewa a waje" Mujaheed ya kalleta ya kalli gate da sauri, ledan da ta jefar ya dauka ya bude yana kallon abinda ke ciki, sai kuma ya nufi gate din.... Tana ganin haka ta dau ledarta da takalmanta ta wuce apartment dinsu da sauri tana waigan Mujaheed, Yusuf yyi murmushi ya koma ya xauna, Parlor ta tadda Ammi xaune, Ammi ta amsa sallamarta tace "Meye kuma kike sa min makulli a kofa" ta xaro ido tace "Ohh na manta, nayi xaton dare yyi..." Still dai bata bude kofar ba tana murmushi ta karasa cikin parlon ta xauna tace "Ammi Sannu da gida" Ammi tace "Yauwa, ya mai jikin?" Imaan tace "Da sauki, Mum dinta tace in gaishe ki, ta ma bani wannan" tana fadin haka ta ajiye ledan a kusa da Ammi, Ammi tace "Toh Allah ya amfana" mikewa Imaan tayi ta wuce daki har sannan xuciyarta bai daina bugawa ba, yanxu da Mujaheed ya ga Sadeeq ya xata yi yau. Tun bayan da ta idar da sllhn magrib Ammi ta ce ta dau abincin Inna ta kai mata gabanta ke faduwa, har claiming ciwon kafa tayi duk don Ammi ta kira Maimoon ta kai ma Inna abincin amma Ammi tace ita dai xata daure ta kai a hakan, tana goge guntun hawayenta ta dau abincin ta fita a sanyaye, ita kanta bata gane wani sabon tsoron Mujaheed da ya diran mata yanxu ba, a hankali ta bude kofar parlon Inna ganin takalmin da bata dai san ko na waye ba bakin kofar, ta ajiye abincin a nan bakin kofa Inna na tambayar wani munafukin ne amma tuni ta juya da sauri har tana tuntube ta koma part din su. Washegari Saturday karfe takwas saura Imaan ta fito bangarensu cikin shirin islamiyya, duk gaba daya a tsorace take har Ammi ta lura da hakan amma da ta tambayeta damuwarta sai cewa tayi ita bayanta ke mata ciwo, Ammi ta sa ta sha magani sannan ta fita, parking space ta dinga lekawa ko xata hango motar Mujaheed, ganin motar tasa yasa ta ki jiran su Maimoon ta nufi gate da sauri, ta gwammace ta tafi bakin titi ta samu adai daitan da xai kai ta islamiyyar. Suna jiran drivernsu bayan an tashi islamiyya Maimoon tace "Imaan wai me yasa kika ki jiran mu daxu?" Imaan ta tabe baki tace "Salon kawai ku 6ata ma mutum lkci mu yi ta yin latti ana xane mu, naga baku fito ba ni kuma bana son inyi latti shi sa nayi wucewata" Rahma tace "Har akwai wanda ya kai ki saka mutum yin latti? Kullum sai mun yi ta jiran ki bakin mota kafin ki fito, daga ace bayan ki ya rike sai ace kafar ki ya rike, to daga yau ma kar ki sake jiranmu kiyi wucewar ki" Imaan ta kalli Maimoon tace "Kin ga dai ba da wannan matar nake magana ba ko, ki gaya mata ba ruwanta da harkata tayi ta kanta ta kyaleni..." Rahma tayi dariya tace "Ehh gwara in kyaleki kiji da ciwace ciwacen ki kam....." Maimoon ta kalli Rahma tace "Haba meye haka Rahma?" Rahma ta watsa mata wani kallo tace "Sai dai ki tambayeta meye haka, ko ni sa'arta ce aka gaya mata??" Tsaki tayi ta wuce gun motar gidan su da yyi parking dai dai lkcn, Ummi ta ja tsaki tace "Mutum sai neman fitina kawai, ana taba ta kuma lalura ya tashi a shiga uku, to dama wa xai taba sauran ciwo idan ba tsautsayi ba ma" tana fadin haka ta wuce ta shiga mota ita ma, Maimoon ta kalli Imaan dake kallonsu tace "Ki rabu da su kiyi hakuri" Imaan bata ce komai ba ta bude front seat ta shiga Maimoon ma ta shiga back seat... Suna isa gida driver yyi parking Imaan ta bude motar ta fita bata xame ko Ina ba sai part din Inna, Inna na xaune parlon tana hada kwadon rama Imaan ta shigo ta xube nan kan kujera ta fashe da matsanancin kuka, Inna ta tura roban gabanta tace "Auzubillahi, me ya sami Aishar?" Cikin kuka Imaan tace "Ko ba su Rahma da Ummi bane daga Ina magana da Maimoon suka fara xagina har da ce min sauran ciwo...." Mikewa Inna tayi ta rufe roban kwadonta ta dau gyalenta ta nufi kofa ta fice,

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment