Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Inna tayi tace "Ka karyata ubanka isuhu Bukar.... Kuma a kira Mujaheed din" babu Wanda yace mata komai a parlon, Umma dai tuni yan hanjinta suka kada ta fara matsar kwalla, idan aka ce an fasa auren nan da gaske ai an kasheta kenan balle ta san in sha Allahu sai anyi, cikin tsawa Inna tace "A kira Mujaheed din mana tun da karya nake" Mama Hadiza ce ta kira layin Mujaheed, yana dagawa tace "Ka taho parlon Inna yanxu" daga haka ta katse wayar, Inna dai sai girgixa kafa take, ba a dau lkci ba Mujaheed ya shigo parlon da sallama kansa a kasa, nan kusa da imaan dake xaune jikin kujera ya duka don babu waje parlon bai kuma son xama kan kujera, Inna na kallonsa tace "Tsakanin ka da Allah Mujaheed kana son auren yarinyar nan da Rukayya ke son hada ka da?" Shiru Mujaheed yyi yana kallonta, can ya saci kallon Umma dake kallonsa tana matsar kwalla, sunkuyar da kansa yayi, Inna tace "Kun ga munafuki koh??" Abba ya hade rai yace "Don't waste our time Mr Man" d'an murmushi yyi yana kallon Inna yace "Toh Inna da bana sonta ai baxan yarda da auren ba" Sake baki Mama Hadiza tayi tana kallonsa, Umma ta sauke boyayyen ajiyar xuciya, Inna ta saki salati tace "Jini ba wasa ba ni Asabe, Allah sarki Ahmadu kana cikin jarabawar ubangiji 'ya ya duk sun kwaso halin uwa...." Wani kallo Mujaheed ya dinga mata, Inna tace "Toh oho dai, da ka so yarinya da kar ka so ta duk uwasu daya ubansu daya, aure dai tunda aka xageni aka ci ma ni da aminiyata mutunci babu xancensa an fasa, sai dai duk abinda xai faru ya faru Babu kuma wanda ya isa ya canxa min ra'ayi ko waye shi kuwa, idan baku son a maku kallon kananun mutane kamar yanda ku ka ce sai a samu wata yarinyar a aura masa amma ba xabin Rukayya ba, xan nuna ma kowa ni jarababbiya ce yau" daga haka ta mike ta shige daki tana goge guntun hawayenta, Abba ya jinginar da kansa da kujera yana salati a ransa, Daddy kam sai girgixa kai yake ya rungume hannayensa, a hankali Imaan ta mike ta fita parlon Mujaheed ya bi ta da ido haka ma Abba da Daddy.



*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
[7/19, 5:15 PM] +234 803 603 7561: Daddy na kallon ta Rasulu a hankali yace "Yanxu Baaba don Allah baxa ki bata hakuri a daura auren nan ba saboda mutanen da aka tara??" Ta Rasulu ta xaro ido ta mike tace "Toh Asabe ga Bukar nan wai in baki hakuri a daura auren... da yake dama cikin 'ya ya ma akwai mai gudun bacin ranka akwai kuma wanda bai san ciwon ka ba kwata kwata, toh Bukar dai bai san ciwon ki ba, don da ya sani sai in da karfinsa ya kare a shakiyancin da Rukayya ta mana yau" Daga haka ta shige daki murya can kasa tana cewa "Ba ruwana.... Haka kawai ince Asabe ta hakura ta ji haushi na..." Mama Hadiza na kallon su Abba on a serious note tace "Wllh Yaya tun da Inna tace baxa ayi auren nan ba fa baxa ayi ba, nima kuma dama nace baxa ayi din ba, ba kuma abinda xai sa ayi, sai an nuna ma Rukayya duk fitinar uwar mu a haka muke sonta kuma babu shegen da ya isa ya taka mana ita ya xauna lafiya, babu shi a duniya wllh, tun wuri ku kira dangin amaryar ku sanar masu an fasa don su san nayi, tunda uwata tace baxa ayi ba baxa ayi ba, ni nayi Imani da Allah da kun ji irin cin mutuncin da tayi ma Inna yau baxa ma ku tsaya kuna bin maganar a sanyi sanyi ba, kuna shakku a ran ku, me aka yi aka yi Rukayya xata raina mana uwa mu kasa daukan mataki?? to wllh yau sai ta ga iyakarta sai dai idan ban haifu ba...." Tana kai wa nan ta mike a fusace ta fice a parlon, Umma ta tabe baki ta dauke kai, Mikewa Daddy yayi ya fice daga parlon shi ma, a hankali Mujaheed ya mike ya bi bayansa, Abba ya kalli umma da kyau yace "Ki bar gidan nan as soon as possible Rukayya bana son ganin ki..." tace "Toh xan tafi ai dama ba sai ka maimaita ba yallabai, amma dai kar ka manta yar gidan wacece Mujaheed xai aura, tsaf xa ku xubar da mutuncin ku da kimar ku a idonsu, da ma duniya gaba daya, barin kai da kake sanannen Barrister" tana magana tana matsar kwalla, har xata fita sai kuma ta tafi kofar dakin Inna, Bude kofar tayi ta durkusa tana goge kwallan idonta tace "Ina neman gafaran ku inna, ku yafe ni ku yi hakuri sharrin shaidan ne..." Inna ta mike a rikice tace "Auzubillahi, garin yaya aka bar ta taxo min nan ni Asabe, don Allah ki rufa min asiri ki fita ba don hali na ba, ki tafi don Allah Rukayya" Mikewa Umma tayi ta fita parlon....
Abba da Daddy ne xaune parlon Abba duk sun rasa abun yi gashi har sha biyun rana ya kusa, fasa aure gaskiya is out of the point yanxu, bai kamata bane kwata kwata amma basu san ta inda xa su billo ma al'amarin ba, Mama Hadiza ce ta shigo parlon da sallama ta dalilin kiranta da Abba yyi, Ta nemi kujera ta xauna tana kallon yayyin nata, Murya can kasa Daddy yace "Yanxu Khadija baxa ki taimaka ki ma Inna magana ta janye wannan batu na fasa aure ba, da dai ace daga wajen mu aka fasa daurin auren nan gwara hakan ya faru daga bangaren iyayen amaryar.... Ki dubi irin mutunta gidan nan da ake amma aga irin haka ya billo daga gidan, ga mahaifin yarinyar dattijon kirki ga kuma irin manyan mutanen da xai gayyato daurin auren nan, kaninsa kuwa wajen aikinsu daya da Sadeeq kuma suna mutunci....." Mama Hadiza ta katse sa tace "Toh ko in ja Innar mu tafi gidansu amaryar tayi abinda xai sa daga wajen su suce sun fasa daurin auren tunda dama kowa kallo masifaffiya mara hakuri yake mata?" A fusace Abba yace "Ji wata maganar banxa, kina ma da hankali kuwa Hadiza?" Mama Hadiza ta mike tsam tace "Ehh kwarai Ina da hankali Yaya, dama naga take taken ku, wato ku baku ma wani ji haushin abinda aka ma mahaifiyar ku ba saboda fitinarta ko, infact ba ku ma yarda cewar ita ke da gaskiya ba, to wllh bari ku ji in har baxa ku bi abinda tace ba toh ku xa ku yi ta ganin ba dai dai ba, ba ruwana, sannan duk fitinarta xan dauketa daga gidan mu tafi sai ku xauna da matanku ku ci karanku ba babbaka, ita ma Rukayyar sai ka ce ta dawo masifaffiya ta tafi" daga haka Mama Hadiza ta fice daga parlon a fusace, Daddy ya girgiza kai yace "Bata da hankali kwata kwata" Abba ya sauke ajiyar xuciya yace "Ni fa nasan duk abinda Inna ta fada Rukayya xata iya aikatawa, kuma ko wani hukunci tace in yanke mata yayi dai dai, amma not to the extent da xata ce a fasa daurin aure ranan daurin aure, meye laifin iyayen amaryar? Ina ce Rukayya ce ta mata laifi ba su, gaskiya Inna tana son ta samu cikin wani yanayi ne, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..." Daddy da yyi shiru yana sauraren yayan nasa yace "Ko xaka kira Bala da su Jibril su mata magana?" Abba yace "Sai kace baka santa ba ai ni har yanxu ban ga wanda ya isa ya sa Inna ta canxa ra'ayin nan ba sai dai wani Ikon Allah" Abba ya jinginar da kansa jikin kujera yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, where are we to start from coz gaskiya babu xancen fasa aure, duk hukuncin da tace ayi ma Rukayya xa ayi amma banda fasa aure don iyayen yarinya basu san hawa ba basu san sauka ba xa mu kunya ta su a idon duniya" Daddy ya tallabi chin dinsa thinking of a way out also. Karfe sha biyu Abba da Daddy da su kawu Bala da Jibril da wani kanin Inna da suke uba daya suka kara komawa bangaren Inna don su bata hakuri ta janye batun fasa auren Mujaheed da Safeenah, kora irin ta kare Inna ta masu da maficin hannunta, har kawu Bala na neman faduwa saboda saurin ya fita a parlonta, Inna ta rakosu har bakin pamponta tana huci tace "Munafukai kawai" Su dai basu juyo ba, amma daddy gaba daya ransa ya gama baci, Abba dai ne ke murmushin karfin hali, su Bala da Jibril ba bakin magana sai yan idanuwa, kanin Inna Alhaji Audu ne ya dinga cewa "Tun da muka fito lafiya Alhmdllh, Asabe ba kyau" Daddy na isa part dinsa ya shiga ko sallama bai masu ba, Imaan da Maryam na dinning xaune Imaan na bata labarin abinda ya faru parlon Inna kasa kasa, Mama Hadiza na daki tare da Ammi, Ammi ta fito jin an bude kofa ganin daddy ne tana kallonsa ta xauna saman kujera bata dai ce komai ba don Mama Hadiza fa na kan bakanta na cewa babu xancen daurin aure ranan har ta gama hada kayanta, Daddy ya jinginar da kansa da kujera yace "Inna na son bata sunan gidan nan ta kunyata mu a idon duniya ne kawai, ta mance cewa bayan Mujaheed akwai yan baya da xa su yi aure, ta mance gaba daya akwai Yan baya.... wani interpretation take son mutane suyi ma gidan nan, auren namiji ma ga abinda ya faru balle mace?? This is very serious...." Ammi dai ta kasa cewa komai sbda Mama Hadiza, Imaan ta taso ta dawo parlor don a rayuwarta na duniya bata son abinda xai 6ata ma Daddynta rai, Durkusawa tayi gefensa a hankali tace "Daddy ku yi hakuri" Daddy bai iya yace Komai ba.... Can Ya kalli agogon wrist dinsa yace "Ya Allah, just an hour remaining, Me xa mu ce ma mutanen nan fisabilillahi??" Ammi dai ba bakin magana, Mikewa Daddy yyi ya fita parlon, duk suka bi sa da kallo, Ammi ta sauke ajiyar xuciya, imaan ta mike a sanyaye ta wuce daki. Hijab dinta ta saka ta tafi part din Inna, suna xaune tare da ta Rasulu sun cika faranti da shinkafa jollof ga kaji kusan goma ana ta ci, turo baki tayi ta xauna tana kallon Inna a hankali tace "Inna don Allah ku yi hakuri ku bari ayi auren nan, kuna son a dinga ma su Abba kallon kananun mutane ne a garin nan?" Inna ta ajiye cinyar kazar dake hannunta tana kallonta baki bude tace "Shi Uban naki ne ya aiko ki in tafi in samesa yanxu?" Imaan tace "Ni ba wanda ya aiko ni" Inna na nuna mata kofa tace "Toh maxa kiyi ta kanki, tunda ba uwar ki aka xaga ba dama me xai dameki, gantalalliya ki ma je ki ji da lalurorin ki xa ki dinga tsoma baki a xancen manya kina yar yarinyar ki da ke...." A fusace Imaan ta mike ta fice a parlon, part dinsu ta koma ta shiga dakinta ta tadda Maryam a dakin, Maryam tace "Ina kika je?" Imaan ta xauna gefen gado tace "Wajen Inna mana, naje na mata magana ta xageni" Maryam tace "ke me ya kai ki, ni fa am happy gwara a fasa auren gaba daya... yarinyar da ta walakanta ni ranan farkon da muka hadu, I sooo hate her with passion" Imaan tace "Toh reputation din su Abba da Daddyna fa? Ae shine abun dubawan ba fasa auren ba" Maryam tace "It's just for sometimes dear, ke kina ga akwai wanda ya isa ya sa Inna ta canxa ra'ayin ta?" Shiru Imaan tayi, can a hankali tace "Na san me xan yi, I pray it works" Inna na bakin tap tana wanke kwanukan da suka ci abinci da ta Rasulu tana yan wakeken su shata na tale tale ta daga kai jin tafiya, Mikewa tsaye tayi tana washe baki tace "A'ahhhh sannu da xuwa Bukar, Sannu da xuwa...." Sadeeq dake sanye da tsadadden Gezna fari kal sai walkiya yake ya iso inda take yana murmushi yace "Sannu kaka, ke kam baki gajiya da aiki...." Inna ta xaro ido ta rike ha6a tace "Huuuu in gaji da aiki in mutu cikin wari Bukar, Allah ya tsareni... maxa shiga ciki gani nan tahowa na ma gama ae" Sadeeq ya cire takalmansa ya shiga parlon dake ta kamshin turaren wuta ya xauna saman lallausan rug din, Inna ta shigo tace "Bari in kawo maka abincin bikin da aka fasa, ai ko yayi dadi har da na fitina, yana nan ta Rasulu ta jido mana har da nama ba iyaka, ni dai hakorana har ciwo suka fara yi saboda cin kaji, yanxu ma ta Rasulun ta shiga wanka ne..." Yana murmushin sa mai kyau yace "Kaka ni a koshe nake wllh kuma lkcn Juma'ah ya kusa sauran yan mintuna..." Inna tace "Toh yi maxa ka tafi idan an sakko sai ka dawo" Yana shafa kansa yace "Ehh xan tafi yanxu kaka...." Tace "Toh ko in dauko maka darduma, jiya na wanke sa tasss nasa Maimoon ta goge min na feshe sa da turare" yar dariya yyi yace "A'a kaka Ina da darduma a mota, xauna mu yi magana" Inna ta dawo da sauri ta xauna tace "Toh gani Bukar, in ji lafiya dai???" Yayi sunkuyar da kai yace "Na ji abinda ya faru ne daxu...." Bai kai aya ba Inna ta fashe da kuka tana kunce ha6ar xaninta cikin rawar murya tace "Wllh abinda ya faru kenan Bukar shine yasa nace baxa a daura auren ba, ba ruwana, yanxu haka an fasa duk nasa a sallami bakin da suka xo" Sadeeq yyi kasa da murya a hankali yace "Don Allah kaka kiyi hakuri, kinga su Abba da Daddy baxa su ji dadin kallon da jama'ah xa su masu ba, gashi ana ganin mutuncin gidan nan, babba dama shi da hakuri aka san sa, kuma wanda aka cuta shi ake ba hakuri dama..." da sauri Inna tace "Inaaa Bukar ai tuni an fasa daurin auren...." Yace "A'a na fa ce kiyi hakuri kaka, kuma ni dai na san ki da hakuri... Ke babba ce fa Kaka" shiru Inna tayi tana matsar kwalla, can tace "Wllh ni dai kunyar ka nake ji Bukar" Yana murmushi yace "Toh don Allah ki janye batun fasa auren" Inna ta d'an yi shiru, can tace "Toh ai shikenan, sun ma kansu ni dai ba ruwana, kuma na hakura aje a daura auren" Murmushi sosai Sadeeq yayi yace "Yauwa Kaka Allah ya kara girma, na ji dadi sosai da kika dau shawarata, Allah ya kara girma" Inna tace "Toh ai dama meye amfanin babban da bai daukan shawara, hakuri kuma ai Allahn da ya halicce mu ma hakuri yake da mu balle ni, na hakura wllh, ga waya sai ka kira min Bukar uban Imaan dama ya fi saka abun a kai uwa kanwar uwarsa ce amaryar, oho dai kirasa ince masa su je su daura auren hankalin su ya kwanta" Yana murmushi ya amshi wayar yayi searching sunan da tace anyi mata Saving lambar daddy da shi ya kira sannan ya mika mata, Daddy na dauka tace "Toh ni dai ba ruwana Allah ma hakuri yake damu, ku je ku daura auren ni na hakura Allah ya saka min da alkhairi" bata jira cewar daddy ba ta katse wayar, Inna ta kalli Sadeeq tace "Ni Rukayyar ma bata taba min irin haka ba gaskiya, ban dai san shaidanin da ya makale a xuciyarta ba yau, amma dai gaskiya tatattce ne d'an iska, ya cuceta ba kadan ba yau, nace to ko radion da suka kunna ya cika gida ne yasa shaidanin ya samu nasarar rudar ta, amma gaskiya ni bata tanka ni kwata kwata a gidan nan, kuma har xaunawa take idan xata gaisheni, shi kuma Ahmadu sarkin xuciya har ya yanke hukuncin ta tafi gida, ni sai ta ban tausayi ma wllh...." Sadeeq dai sai kallonta yake yana murmushi yace "A dai yi hakuri kaka" tace "Atohh, biyayya iya biyayya dai suna min ni baxan masu sharri ba...." Daddy ne ya shigo parlon tare da Abba da kawu Bala, Inna na washe baki tace "Sannun ku da xuwa" Sadeeq ya gaishe su gaba daya da ladabi, Inna tace "Toh gaskiya duk babban da yace baxai dinga daukan shawaran yaro ba yayi asara, me yyi min xafi da xan bari inyi asara, wannan yaro Sadeeq dai ya shigo ya ban baki kuma wllh na hakura aje a daura auren Allah ya sa albarka, kamar daga sama ya fado min yanxun nan, wato har labarin ya baxu duniya Kai jama'ah.... Kuma da kun san ta yanda xa ku bi da ni da xancen bai yi tsayi ba haka ba duk baku da wayo, ni dai na yafe, aje a daura auren" Abba ya d'an yi murmushi yace "Toh madallah mun gode Inna, Allah ya kara girma, xa mu je masallaci ynxu lkci ya kusa" Inna tace "Toh ku tafi Allah maku albarka, Bukari kai ka dawo in xuba maka abinci don Allah har da kaji xuka xuka" Sadeeq na murmushi ya mike yace "Toh in sha Allah xan dawo" Bin bayan su Daddy yyi ya fita, Abba na kallon Sadeeq yace "Maa Sha Allah, I am very happy at ur contribution Allah ya saka" Sadeeq yyi murmushi bai ce komai ba, a haka suka fita gidan Abba na kiran wayar Mujaheed, Mujaheed was so shock da ya ji wai ai Inna ta hakura, kuma wai Sadeeq Bulasawa ne ya bata hakuri, har reaction dinsa ya ba Abbansa da Daddy mamaki, haka dai suka wuce mosque ana sakkowa masallaci kuma aka daura auren Mujaheed Ahmad da Safeenah Usman, ko jira Mujaheed bai yi su gaisa da abokansa da suka taho daga nisa ba ya koma gida, direct part din Inna ya nufa, Imaan na tahowa daga part din innar rike da warmer xata sha corner suka kusa cin karo da shi, fixgota yyi wanda hakan yasa ta saki abincin hannunta a tsorace, yana mata wani mugun kallo da idanuwansa da suka rine cikin tsawan da ya raxana ta yace "Uban wa ya aikeki ki sa saurayin ki yaje ya ma Inna magana? Uban wa ya sa ki????"


*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788[7/19, 5:15 PM] +234 803 603 7561: Kasa cewa komai Imaan tayi tana kallonsa don ba karamin tsorata tayi ba, cikin tsawa yace "Ba tambayar ki nake ba sai na baki dirty slap?? Who sent you, waye ya aike ki??" Hawaye ya cika idonta ta sunkuyar da kanta bata dai ce komai ba, saketa yyi ya jingina da bango xuciyarsa na bugawa, ta tsallake abincin da ya xube ta wuce da sauri tana goge idonta ya bi ta da kallo har sannan kirjinsa bai daina bugawa ba, hade kai yyi da bango yana Kiran Allah a ransa, ya fi minti biyu a haka sannan ya juya da kyar ya nufi bangarensu yana jin idanuwansa na juya masa. Imaan na kwance daki da yamma idonta a lumshe duk da ba bacci take ba, wayarta dake kusa da ita ya fara vibrate, bude ido tayi tana kallon wayar, tun abinda Mujaheed yyi mata daxu take daki taki fitowa duk nacin da Maryam tayi da ita ta fito, gaba daya she is moody, a hankali ta dau wayar tayi picking ganin Sadeeq ne ke kiranta, sallama yayi mata daga daya barin, murya can kasa ta amsa, yace "Are you okay dear?" Shiru ta d'an yi sai kuma tace "Bana jin dadi" yace "Subhanallah baki jin dadi kuma, kin yi stressing kan ki da yawa kenan, what's wrong? I mean me kike ji ke damun ki?" Cikin sanyin bemurya tace "Ache all over" yace "Subhanallah, kin sha drugs din ki?" Ta gyada kai kamar yana ganinta yace "Ohk toh xan kawo maki wani yanxu sai ki sha shi da daddare, you will feel much better" tace "Toh" yace "Xan kira ki idan na iso" daga haka yyi mata sallama ta katse wayar ta ajiye ta rufe idonta. Biyar saura ya sake kiranta yana waje, Hijab ta saka har kasa, xata fito ta tuna birthday gift dinsa ta koma ta dauko flower din da cards ta saka cikin hijab ta fito, Few visitors ne a parlon nasu, ta tafi dakin Ammi ganin bata ciki ta fito, a balcony ta tadda Ammi da Mama Hansai, Ammi na kallonta tace "Ina xa ki?" Ta sunkuyar da kai tace "Ammi ba dadewa xan yi ba ana kirana a waje ne" Ammi na kallon hannunta dake cikin Hijab tace "Meye wannan kike boyewa a hijab?" Murmushi tayi kanta a kasa tace "Ammi ba komai bane, sako ne fa" Mama Hansai na dariya tace "Yi wucewar ki kinji" wucewa imaan tayi tana murmushi, Yana tsaye jikin motarsa idonsa sanye da glass ya sa kananun kaya, sunkuyar da kai tayi ta isa kusa da shi, da damuwa yace "Ya jikin" tana d'an murmushi tace "Da sauki" ya dauko wani leda a gaban motar ya mika mata yace "ki sha tablets daya each each kafin ki kwanta" Bata amsa ba ta fiddo hannunta dake cikin hijab ta mika masa flower din hannunta cikin sanyin murya tace "Happy birthday dear" still yyi yana kallon flower din ko kiftawa babu" lkci daya ya karba yana wara ido so happy yace "Waowww Thanks soo much baby I love it...." Ita dai murmushi kawai tayi, a hankali tace "i am happy u love it...." Ko bai fada ba she can see how happy he is, yana wara manyan idanuwansa yace "But baby how did you know I love flowers plss?" Ta langwabar da kai tace "I only guess" lumshe ido yyi murya can kasa yace "I feel like hugging you sweetheart" d'an murmushi kawai tayi ta dauke kai tace "Ni xan koma ciki, and I am sorry I won't be able to attend ur party saboda bana jin dadi" a sanyaye ta kare maganar, cike da damuwa yace "Ai na maki uxuri dear, Allah baki lafiya thanks a lot, I will give you a call later" a hankali tace "Ameen ngd" daga haka ta juya ta koma cikin gida ya bi ta da kallo still smiling. Mama Hadiza ce xaune parlon Inna tare da Ta Rasulu, cikin rashin jin dadi Mama Hadiza tace "Yanxu fisabilillahi kin kyauta min Inna, duk yanda na takarkare a kan an ci maki mutunci sai ki watsa min kasa a ido??" Inna tayi kasa da murya tace "Toh Hadiza shikenan ana ta bani hakuri ana hada ni da Allah sai in botsare kamar shaidaniya? Babba fa dama da hakuri aka san sa, baki ga yanda aka cika min parlon nan ba daxu ana bani hakuri har da su Audu d'an tsut, daga karshe sai kuma ga Bulasawa da kansa shi ma ya tako har parlon nan ya ce inyi hakuri, to idan dai ni ba tsohuwar banxa bace mai kunnen kashi mara jin magana Hadiza ai ya ci ace na yayyafa ma raina ruwan sanyi in hakura, kuma ni dai gaskiya Rukayya bata ta6a min irin haka ba, hau ne ya fada mata...." Ta Rasulu na nuna Inna ta kankance ido tace "Ke dai Asabe ki dinga jin tsoron Allah, nan kika maida mu mahaukata muna bambami daga karshe kika watsa mana kasa a ido wai kin hakura, Toh ai ina gida xa ki sa a kirani ki kawo min karar Rukayya, ba kuma ruwana wllh don baxan saurare ki ba, ke kuma Hadiza me xai dame ki?? Ai kadan da aikin Asabe kenan baki biyu, ni ban yi mamaki ba, ni ba dai ruwana ban ce komai ba in yi magana ta kullace ni, amma banda haka me aka yi aka yi wani

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment