Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Ji walakanci ba da Mujaheed nake magana ba" Da kyar yace "Anty ba fa ni na kai ta ba, Abbanta ne ya kai ta" Shiru Anty tayi ganin yanayinsa, can ta saci kallon inda yake kallo, d'an tabe baki tayi ta duka ta ci gaba da abinda take, Umma ta juya ta koma sama, da kyar Mujaheed ya ja kafarsa xuwa dinning, har Anty ta gama abinda take Mujaheed na xaune bai taba komai a dinning table din ba, tace "Idan baka ci ka kai min su kitchen a ba almajirai" ya marairaice yace "Anty da baki yi magana a gaban Hajiya ba" Anty ta maka masa wani kallo tace "tunda uwata ce ita ba" Bai ce komai ba, bayan wani lkci ya mike ya fita parlon ko a mafarki bai ma son haduwarsa da Umma, to me ma xai ce mata ta yadda, part din Inna ya nufa, ya sameta xaune kan tabarma rike da cazbi tana ta xuba gyangyadi, kwanciya yyi kan kujera ya lumshe ido, inna ta yi gyangyadin ta mai isarta sannan ta bude ido, a tsorace ta koma baya ganin sa tace "Meye wannan?" Shi dai bai tanka ta ba bai kuma bude ido ba, tace "Wannan dai ba yi bane ina Lazimi kato ya fado min parlor ba sallama" Ba tare da ya bude ido ba yace "Kina gyangyadi dai" rai bace tace "Ya xaka ce ina gyangyadi ga carbi hannuna, ai asararre ne xai yi gyangyadi a wannan lokacin walha fa na gama ina lazimi ka shigo sadaf sadaf ban sani ba" Mikewa xaune yyi yace "Akwai ruwan shayi?" Tace "Eh akwai wanda uwarka ta kawo min" ya kalleta bai ce komai ba, tace "Can din hanaka ruwan shayin suka yi?" Komawa yyi ya kwanta, tace "Sai dai in sa Aisha ta dafa maka don baxan iya ba, baka ji bayana ba tun safe nake aiki, ko kai baka ga ko ina fess ba, leka dakina ma kaga yanda yake talli" shi dai bai ce mata komai ba, tace "Duk na tattara ma yarinyar nan me shigo min daki ta kwanta ta bar min tsummokaran dankwalayenta idan ta tashi tafiya, suna can baranda na ajiye mata, sai kaga hasken da dakin yyi wllh, ni dai da xata taimaka ta daina shigar min daki don Allah, ni tsoron da nake jiye mata idan tayi aure, ko ina fa ta samu barin kayanta take kamar mahaukaciya, Bukar dai ya haifo abinda ya fi karfinsa" mikewa Mujaheed ya sake yi ya shiga kitchen, ba a dau lkci ba ya fito rike da cup din ruwan xafi yace "Ina kayan shayin?" Makulli ta kunce a habar xaninta ta mika masa tace "Saboda ire iren su Imaan nake adana kayana, ba ruwana" Ya tabe baki ya amshi makullin ya shiga dakinta, closet dinta ya bude yaga gwangwanin madara manya har biyu da milo biyu sai kwalin sugar uku, da kwalin lipton girgixa kai yyi ya sauke madaran da Milo, muryarta yaji a bayansa tace "Da dai ka bari in xuba maka Mujaheed kada ka min barna" Wani kallo ya mata, ya debi cokalin Madara har uku ya xuba, ta bude baki cikin tsawa tace "Kai ubanka ne ya siyo min xaka diba haka, Bukar ne dai mai siyo min kayan shayi, shi Ahmadu sai dai ya jibge min kayan abinci kamar mayunwaciya, kudin nan fa da wahala ake samun su" shi dai bai tanka ta ba har ya gama hada shayin sa ya fita, tayi kwafa ta kwashe kayanta ta maida closet din ta kulle da makullin tana cewa "Ae dai gobe rana ce" Daga haka ta fito parlor. Har kusan azahar Mujaheed na bangaren Inna, har ya gaji da jin muryarta gashi bai taho da earpiece balle ya toshe kunnensa ba. Yana kokarin tashi ya je yyi alwala jin an kira sllh aka bude kofar parlon ya kalli kofar da sauri, Imaan ta shigo parlon rike da warmer, har ta rame ciwon kwana daya sai manyan idanuwa, Inna ta saki baki tace "Wacece wannan kuma?" Imaan bata ko kalleta ba ta ajiye warmer din hannunta, inna ta rike ha6a tace "Ni dai naga abinda ya isheni bai ishi ubangijina ba, yanxu fa sai ace jikinta ne ya tashi, fisabillah dubi yanda yarinya ta zabge ta koma fiyot kamar kyanwa Mujaheed, anya iyayenki na son ki kuwa yar nan, haka xasu xuba ido suyi ta kallonki kina wahala ga magani kasadan na wani malami a Maiduguri ance min babu ciwon da baya warkarwa, dubu hamsin aka ce xa a basa Bukar ya maida ni ban san abinda nake ba kamar shi ya haifeni, ta rasulu kawata xata cuce ni ne ake tunani? ce min fa tayi xata min hanyar samun maganin don can bayan tsauni mutumin yake, kuma babu kalan iskan da bai warkarwa da ciwace ciwacen da ba na Allah da annabi ba irin na yarinyar nan, amma iyayenta sun ba tsinannun turawa karfi sun amince masu dari bisa dari ba saurarana xa su yi ba, dubi don Allah yanda ta fige, lafiya muka rabu jiya amma ga iskan har ya tashi tunda gashi bata je makaranta ba" Mujaheed yace "ina kika ce mai maganin yake" Inna ta gyara xama tayi kasa da murya tace "Wllh a bayan tsauni ta rasulu tace yake, sannan aikinsa yanda kasan yankan wuka, sha ynxu maganin ynxu, duk xata fitsare ciwon da iskan inji ta rasulu" yyi murmushi yace "Ikon Allah, boka ne kenan?" Buda baki tayi tace "Kaji salu6a66e ko, ni dai ka rufa min asiri kar ka ja min kasa Ahmadu ya kafa min sabon babin wa'axi, kai ynxu fata kake inje wajen boka d'an nan" yace "Atoh, mutumin kirki dai baxai je bayan tsauni ya xauna ba" tace "Yo ai ni ce gantalalliya ma da nake xancen nan da kai na mance ashe d'an aiken turawan ne kai ma, Allah wadaran naka ya lalace, ba damuwa ni da ya xame ma dole xanje samo mata magani kuma kada wani shege ya min maganan banxa, Allah kuma ya tsine ma turawan nan dai" Imaan dake tsaye bakin kofa har sannan ta tabe baki tace "Kar ma ki amso ni baxan sha ba, daddy yace min in daina hada na asibiti da gargajiya" a fusace Inna tace "Kya tsufa a gida ina kallonki kina kallona don wllh babu namijin da xai auri ciwo da kudinsa ki karar masa da tattalin arxiki a asibiti, wllh baxan bari a cucesa ba duk sai na xayyane masa lalurorin ki don ni ba yar cin amana bace, ni yar gaskiya ce, ke ce ciwon kafa, kece ciwon baya, ke ce ciwon kai, ke ce ciwon mara, kece sanyin k'ashi, kece xaxxabi, kece ciwon jiki, ga shegen son jiki sannan in rufe masa da cewa duk iska ne da ba a san kansa ba, ba ruwana wllh" murmushi Mujaheed yyi ya mike ya fita don yin alwala, Imaan ta mata wani kallo bata son magana saboda daddy ta juya kawai ta fice mata daga parlonta tana murguda baki.

I am soo grateful for the birthday wishes from families, friends, fans, and love ones, Allah bar xumunci ya kara mana shekaru masu albarka.
[6/11, 12:34 PM] +234 703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟





_By khaleesat Haiydar_✍🏻






6.....

Hatta islamiyya Imaan bata iya taje ba ranan banda bacci babu abinda take, xuwa lkcn jikin ya mata sauki sai dai rashin kwari, Daddy dake parlor a study area dinsa ya kalli Ammi dake parlon ita ma yace "It's almost six madam baxa ki tada Imaan ba?" Ta kallesa tace "Kafin magrib xan tasheta" yace "Amma jikin ba xafi koh?" Tace "Ehh ba xafi but she's weak" yace "Allah ya bata lafiya" a hankali Ammi tace "Ameen" bayan wani lkci ta kallesa tace "Am really disturbed with Imaans health ailment... She have suffered a lot but always claiming strong, and...." Sai kuma tayi shiru, a hankali ta ci gaba "I don't want to loose her" Daddy na kallonta yace "Allah plans best, ke dai ki ci gaba da yi mata addu'a a ko da yaushe wataran sai labari, Allah xai yaye mata" Ammi tace "In sha Allah" Bayan magrib Ammi na kitchen taji muryar inna a parlor, fitowa tayi ta gaida ta da ladabi tace "Sannu da xuwa inna" inna tace "Ina mijin naki?" Ammi tace "Ya fita masallaci" Inna tace "Daxu Imaan ta xo duk tayi wani fayau fayau da ita, jikin ne ya matsa mata koh?" Ammi tace "Ehh wllh, amma taji sauki ma yanxu, tana daki xata yi sllh" Inna tayi kasa da murya tace "Yanxu 'yar nan idan shi mijin nan naki boko ya gama cutarsa ya ratsa sa ta ko ina ke baxa ki maida hankali ki tashi tsaye kiyi ta kanki da 'yar ki ba? Fisabillilah meye laifin maganin gargajiya Aisha, komai sai ace sai asibiti ga na gargajiya kasadan?" Ammi tace "Gaskiya ne inna" Inna tace "Wllh malamin a bayan tsauni yake" Ammi ta d'an bude ido tana kallonta, tace "Ga aikinsa kamar yankar wuka, duk xata fitsare jaraban ta dawo kamar mutane, amma ni tsoron magana nake Bukar da Ahmadu ba kirki ne da su ba sai su karee min rashin mutunci suce boka ne alhalin ba boka bane kawai Allah ne yyi xamansa a bayan tsauni, ta rasulu ta sha xuwa can kuma ana kwana daya da rabi a hanya kafin a kai, tunda kika ji haka ai kinsan akwai kamshin nasara, tafiyar kwana daya har da rabi ai kuwa akwai nasara....." Shigowar Daddy ya sa tayi shiru, daddy ya gaida ta da ladabi ta amsa masa sama sama tana kallon Ammi tace "Kina ji 'yar nan bari in koma na bar kofa bude kada yaran gidan nan su min aika aika ga dambun nama ta can daki, dama Mujaheed sai xarya yake min tun safe, ko shi ya isa ya kwashe, yanxu dai yaushe mijin naki xai koma?" Ammi tace "Xuwa gobe in sha Allah" Ammi tace "Toh idan ya tafi ki taho sashina ki same ni mu karasa maganar a can don sirri ne" daga haka ta nufi kofa daddy na mata sai anjima ko tanka sa bata yi ba. Bangarensu Mujaheed inna ta nufa tana cewa "Ita kuma Amina bara inje inji ko lafiya ban ganta yau ba" Mujaheed ne xaune parlor sai Yusuf, Hajiya na dinning tana jera abinci Rahma na taya ta, gaba daya Mujaheed bai yarda sun hadu ranan ba sai yanxu da ta riskesa a parlor ta fito kitchen, Inna na kallon Yusuf tace "Kai ina uwar ka, lafiyarta yau bata xo gaisheni ba" Yusuf yace "Yanxu da daddaren nan xaki kamo hanyan xuwa nan inna" Hajiya ta karaso parlon tayi kasa da kai tana daga tsaye tace "An yini lafiya Inna" Inna tace "Rukayya idan Hadiza ce xa ki gaida ta a tsaye sandandan haka?" Juyawa Umma tayi ta koma ta ci gaba da abinda take ba tare da ta bata amsa ba, inna ta kara da cewa "Sannan kiyi min rai ki rufa min asiri ki daina gaisheni kwata kwata a gidan nan idan kin gan ni, don Allah bana bukata, wnn ae kanki kike munafurta, kuma Allah ya tsine ma gaisuwar" Wani kallo Mujaheed ke ma inna fuskarsa daure, inna tayi kwafa tace "Mu xuba dai, xamu ga mai kwashewa, ae kema ga naki d'an ya isa aure ba don ya tsaya shashanci ba xaki ji ko da dadi ko babu" mikewa Mujaheed yyi yace "Ke dai ba dai alkhairi ya kawo ki nan ba sai fitina da complaint, haba don Allah, gaba daya ba a ta6a maki dai dai...." Inna ta bude baki tace "Ni kake xagi Mujaheed?" A fusace yace "Mu bar sa a hakan" daga haka ya wuce ta kamar xai tashi sama, Yusuf ya bi sa da wani kallo, tuni Umma ta shige kitchen ranta fari fat duk da haushinsa da take ji, Yusuf ya mike yace "Yi hakuri muje in raka ki" Inna ta fara matsar kwalla tace "Isuhu kaga abinda Mujaheed ya min ko? Da ina kusa da shi babu mai hanasa make ni.... Ina mahaifin ku yake" Yusuf yace "Ke dai mu je, Abba bai dawo ba" Da kyar Yusuf ya lallabata suka fita parlon tace "Wllh in har Mujaheed zae ci gaba da xaman gidan nan sai dai ni in tafi" Yusuf ya danne dariyarsa suna isa part din su Imaan ta bude kofa, daddy dake xaune yana duba laptop ya mike ganinta tace "Bukar babu abinda Mujaheed ya mance bai gaya min ba yanxun nan daga nayi ma uwarsa gyara, sai ku xaba ko ni ko shi a gidan nan" daga haka ta rufe kofar. Yusuf dai tuni yyi gaba, suna isa part dinta ta rushe da kuka tace "Sai yanxu abun ke min ciwo isuhu, kai kaga wahalar da nayi da Mujaheed kare baxae ci ba wllh" Yusuf yace "Sai kiyi hakuri, Mujaheed din ki ne fa" a fusace tace "Mujaheed dinsu dai, bari dai mahaifin ku ya dawo xai gaya min ko shi ke koya masa ya min rashin arxiki" kiran Isha da ake yasa Yusuf ya bar part din inna, tare Daddy ya je gun Inna da Imaan bayan isha, Inna ta fito daga daki ta shimfida tabarma ta xauna tace "Wllh Bukar daga nace ma Rukayya ta daina gaisheni a gidan nan don na munafurci ne, shi kenan Mujaheed ya hayayyako min yana huci..." Daddy yace "Kiyi hakuri Inna, ina fita xan je in samesa yanxu" a fusace tace "Oh oh babu xancen samunsa, kawai ni ba na son ganinsa gidan ne ko kuma ni in tafi ai dama ya isa aure sai yyi ya koma gidansa baxan xauna tare da shi wataran ya mareni ba, wai ku me yasa baku san ciwon uwar ku ba, uwarsa fa na yi ma fada shine ya min rashin arxiki haka, kai ko ga ka xaune sandandan gabana kana bani hakuri, ya fi karfin ka ne mujaheed din ko kuma uwarsa ta fi naka ne, Ahmadu dai bai ba yaron tarbiyar da ya ratsa jikinsa ba wllh" Daddy ya mike yace "Xan dawo anjima inna" daga haka ya nufi kofa tace "Yauwa, ka titsiye sa sai ya gaya maka ko ni sa'arsa ce kafin ya bar gidan" shi dai bai ce mata komai ba har ya fita, Inna tayi kwafa tace "Xai san ya ta6a uwar su yau" Imaan dai na kwance kan kujera tana kallonta, Inna tace "Ni na ma fara tsoronsa tunda abinda ya zama kenan yanxu" Imaan tace "Toh ke me ya kai ki bangarensu" inna tace "Ya za ki ce min haka 'yar nan, ni da gidan d'a na kuma kice me ya kai ni?" Imaan dai bata ce komai ba, Inna tayi kwafa tace "Ke kin ga wahalar da nayi da Mujaheed?" Imaan tayi dariya tace "Ae ke dama kullum sai kice kin yi wahala da kowa" Inna tace "Kee na Mujaheed k'are baxai ci ba, ni nasan me nake cewa, ina fa tsaye bakin kofar dakin haihuwa daga safe har dare sannan aka haifesa, sai kin ga wahalar da ya ba uwar d'an banxan, ai ko aka haifosa lafcece ya kusa biyun wani jaririn, duk ya cika asibiti da kuka nyaaa ke kina gani kinsan sadauki aka haifo, gashi jajir da shi fari hulll, gashin kansa kuwa ga bak'i ga cika yanda kika san d'an balarabe, ke ki bari kawai, nan dai muka koma gida na wanke sa tass, baki ga uwarsa ba lkcn yar siririya kamar xata karye ba yanxu da ta ci kudin d'a na iya ci ba ta koma kamar buhun masara, kullum zanyi wanka da sassafe daga gidana in tafi gidan Ahmadu yi ma fitsararren yaron nan wanka, don babu abinda uwar ta iya wai tsoron jaririn ma take don bala'i, a haka har yayi wata uku ya koma yanda kika san bredi wato ya xama wani lukeke, ga kyau tsantsa, ba sai uwar tayi ta cika masa nono yayi ta tumbudi ba duk k'arni??" Imaan ta fashe da dariya har da kyakyatawa tace "Shi yayan?" Inna tace "Wllh shi, to ni ko ina xan iya kazanta da k'arni, oh oh nan na taka mata burki, ga uwar kazama dn har sannan tana tashen kuruciya ni fa ko abincin gidan bana iya ci da, ana haka har Mujaheed ya kai shekara biyu, ba sai naga ana neman hallaka yaron ba, ba shi da aiki sai kukan banxa, fitsari a tsaye kashi a tsaye, ga uban shan yogurt, to da yake ba yanda na raini ubansa ba kenan bakina a leko na daukesa, kin ji mafarin komawansa waje na kenan, kuma Mujaheed bai bar gu na ba sai da uban ya biya masa kudin karatun likita a kasashen turai bayan ya gama sakandari, to ace banyi wahala da d'an banxan yaron ba kuwa, tsakaninsa da iyayensa fa sai dai bayan kwana biyu yaje ya gaishesu ya dawo, ko k'uda bana yarda ya ta6a min shi balle shegun kishiyoyina da duk suka mace yanxu, Allah dai ya ji kansu amma shari'ar mu da su sai a lahira...." Imaan tace "Ni lokacin ma ba a haifeni ba koh?" Da mamaki Inna tace "Oh oh kaji wata magana kamar na ta6a66u, wa ke ta ke, ke da aka haifa jiya jiya, a hannuna fa kika fado, ai wannan labarin da nake baki a lkcn mu duk mun dauka uwar ki juya ce...." Imaan ta mike xaune ta hade rai tana kallon inna, inna ta gyara xama tace "An auro uwar Mujaheed da shekara uku fa Ubanki Bukar ya auri bafillatanar uwar ki tana tallan nono a lkcn, a gidan sa fa tayi wnn karatun da take takama da shi" Imaan ta daure fuska tana kallonta, inna tace "Bayan an auri Uwar ki Aisha da yan watanni na tursasa Ahmadu ya sake aure shine fa ya auro Uwarsu isuhu, don a lkcn Rukayya na tashen rashin kunya duk an hure mata kunne, ga kazanta duk ta bi ta ru6ar min da gidan d'a na, To ita kuma uwar isuhu lkcn kawar Mamarki ce, kin ji musabbabin rashin shirin Rukayya da mamanki har yau, Rukayya ta dinga jin haushin Aisha tunda kawarta ta aure mata miji, Uwar su isuhu na shigowa da wata goma sai gashi ta haifo wannan d'an albarkan isuhu shi ma dai a gabana aka haifesa ina tsaye, ke ko uwar ki shiru kamar malam ya ci shirwa, ke in takaice maki har bayan shekaru aru aru sai dai uwar ki ta ci ta sha tayi kashi duk tayi bake bake a gida babu haihuwa babu dalilinsa, babu yanda banyi da Bukar ya karo mata ba amma yaron nan ya bijire min to duk ta shanye min shi ta rarraba min sunansa inda bai kamata ba, ke kinga bafillatani? To wllh kiji tsoronsa mugwaye ne na kin karawa, ni dai na dage rokon Allah ba dare ba rana don Allah ya warware abinda tayi ma d'a na, to wllh karshe sai da Ahmadu yayi 'ya ya shidda sannan uwar ki ta haifo ki, murna gun mahaifinki kuwa ba a cewa komai, duk lkcn fa ba mu san ba lafiyayya bace ke din, nayi ta xuba idon xuwan kanninki amma shiru, astagfirullah wa ya sani ma ko sai a lahira idan ana haihuwar tunda gashi yanxu kin doshi ashirin, kuma tun da kika fara wayo Bukar ya kulla adashin da ba kwasa da asibiti, shine ake nan har yanxu jiya e yau, ni yanxu mai kwasan ki ma nake tausayi wllh kada ya kasa rike ki, wannan idan talaka kika aura ae sai dai mu xo wataran mu dau gawarki muna koke koke, to banda haka sata xai yi ya kai ki asibiti? abinda Bukar yace min a kalla magungunan ki suna yin kusan dubu hamsin duk wata, wa xai iya wannan idan ba mai kudi ba irinsu yaran d'an tata, mu dai Allah ga mu gare ka, ka yaye ma jikata wannan iska da ya sa ta gaba yake cutan ta, ita kenan gun d'a na" Imaan na hararanta tace "Daga labarin yaya kin wani dawo bada labarina kamar an tambayeki, har na gaji da jin labarin nan a gidan nan" inna tace "Toh wa ke ta wani yaya da barin gidan xai yi gaba daya, ai yau sai ya san ya ta6a uwar masu gida" Da sallama Abba ya shigo parlon, Inna ta daure fuska, Daddy ma ya shigo parlon Mujaheed na biye da shi a baya, inna na ganin Mujaheed tace "Ni dai n shiga uku, mutumin nan ya fitar min a parlo don ba ruwana" Mujaheed ya durkusa d'an nesa da ita ya sunkuyar da kansa yace "Kiyi hakuri inna" inna tace "Oh oh Allah, ni dai wllh sai naga kamar tsoron yaron nan ku ke Ahmadu, ni cewa nayi ku taso sa ya bani hakuri? Me xanyi da hakurinsa, idan da amana Mujaheed zae dinga fifita uwarsa a kai na kuwa? Ni da na ci fitsarinsa na ci kashinsa ba irin wahalar da ban yi da shi ba, wannan wani irin fitina ne, me yasa Isuhu baya min haka?" Shi dai Mujaheed bai dago ba, inna tace "Toh ni dai a bar min parlo na" Daddy yyi murmushi bai dai ce komai ba, Abba yace "Mu dai sai dai mu ce kiyi hakuri, shi kuma nasan maganinsa" inna ta wani tsuke fuska bata ce komai, Imaan dai na kwance sai murmushi take, Abba na kallon Mujaheed yace "On a serious note Mujaheed be careful... you had better respect yourself in this house, and mind you no matter how she does her things, how she behaves, how annoying she might be, she is still my motherr, yes she is my mother I can't change her from who she is, and you have got to respect her to the fullest, you keep that grandma and grandchild play aside since she doesn't cherish that, she have got all right to complain of ur mother, let her be entitled to her opinion, today shud be the last that she will complain of ur attitude toward her Muhammad am I clear" Mujaheed bai iya ya dago kansa ba yace "in sha Allah Abba" Daddy yace "Maa sha Allah" inna da sai tabe baki take tace "Oho dai duk a banxa tunda baxa ku iya koransa a gidan ba" Mujaheed yyi kasa da murya yace "Kiyi hakuri" tace "Tashi ka bani waje, ba dai aure xaka yi ba wataran, wllh duk sai matar ta rama min abinda uwarka tayi min a duniyar nan, takanas xan tattara kayana wllh in koma gidanka da xama duk ni xan dinga koya ma yarinyar, nan Rukayya xata ji ko da dadi ko babu" Mujaheed dai bai ce komai ba, Abba yace "Leave now" mikewa yyi yana hararanta ta gefen ido ya fice daga parlon, Imaan ta fara dariya kasa kasa. Ranan juma'ah da daddare Inna na xaune parlonta Imaan kuma na kwance kan kujera gaba daya ta gaji da labarin da inna ke bata, tana son tashi ta wuce amma ciwon da kafarta ke mata yasa ta kasa tashi, tun magrib take wajen bayan ta kawo mata abinci har wajen tara da rabi yanxu, Inna tace "To kin ji abinda ya raba ni da uwar d'an gwate kenan, kuma fa lkcn kakanku bai san ina xuwa ba, kai jama'a na xuba farin jini gun masu kudi wllh" Imaan dai bata tanka ta ba, bude kofar parlon aka yi Mujaheed ya shigo da sallama, Inna tace "Dama shi kadai ne me shigo min da sallama banda su oh oh" Ta gefen ido Imaan ta kalleta, ya ajiye ledan hannunsa yace "Gashi" ta jawo ledan tana budewa tace "Lahh kaza ce kamar yasan ina marmari wllh " Imaan ta mike xaune, inna ta hade rai ta rufe ledan, mikewa Mujaheed yyi ya dauko plate ya ajiye gabanta, ta mayar gefe tace "Ni dai wllh kuna takura ni gidan nan kai da Imaan ba haka isuhu da su maimoona ke min ba, su basu da sa ido" ta hade rai ta bude ledan ta dau cinya daya ta dungura masa a plate din, dariya yyi ya dauka yace "Ni fa na siya maki kazar ba Abba

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment