Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalleta ba ta nufi kitchen rike da plate din, Rahma ce kitchen din ta gama wanke wanke, sai Mujaheed dake tsaye yana xuba ruwan Lipton daga teapot a cikin mug, Imaan xata ajiye plate din, Rahma tace "Kinga plate mai datti a wajen ne malama" turo baki tayi ta dau morning fresh ta bude xata wanke plate din, Rahma tace "Ya M.A in debar maka abincin ne xan fita?" Ya harareta yace "Abincin da ku ka cika yaji ko wanda ba yaji?" Yar dariya tayi tace "Ya Mujaheed yajin fa ba yawa" tsaki yyi yace "Ance maki ban yi tasting abincin bne ku dinga cika ma mutane ya ji a abinci kamar mayyu" Tace "Toh in maka cous cous?" Yace "I will take tea" Imaan ta gama wanke plate din ta juya ta fita kitchen din. Kallonta Ammi ta dinga yi bayan ta shigo tace "Ya jikin Imaan" tayi murmushi tace "Na ji sauki Ammi" daga haka ta nufi dakinta Ammi ta bi ta da kallo. Karfe sha daya saura Ammi ta shiga dakin Imaan, ganin tayi bacci ta tasheta tana mika mata wayar hannunta tace "Me ya sa kika kashe wayar ki" Imaan na murxa ido tace "Kila mutuwa yyi ba charge" Ammi tace "Toh idan kin gama ki maido min wayata daki" Imaan tace "Toh" sannan ta kai wayar kunne tace "Daddy ina yini" Daga daya bangaren ya amsa yace "Why is ur phone switched off" ta langwabar da kai tace "Daddy ban sa a charge ba tun jiya" yace "Toh kiyi kokari ki sa ya jikin?" Tace "Naji sauki, daddy ina missing dinka yaushe xaka dawo?" Yace "Weekend in sha Allah" ta wara ido cike da jin ddi tace "Plss daddy ka dawo week end din kar ka daga, wllh ina son in ganka" kamar xata yi kuka ta kare, yyi murmushi yace "Sure dear, plss ki daina wasa da shan drugs din ki kinji" tace "Ina sha Allah daddy, har yanxu Dr ma bai xo ba" yace "Ehh mun yi waya daxu yace bai dawo ba" Imaan tace "Toh" yace "Sleep tight dear, banda kunna Ac" yar dariya tayi tace "Toh daddy byeee" katse wayar tayi ta mike ta kai ma Ammi daki sannan ta dawo dakinta ta shige duvet. Yau Friday Imaan na dawowa schl bayan tayi wanka tana kokarin saka kayanta taji k'aurin abincin da Ammi ta bar mata a kitchen kan gas don tana shigowa gidan Ammi ta fita kasuwa yin cefane, da gudu ta fita daure da towel don kashe gas din don dama sae da Ammi tayi mata kashedi kan cewar kada ta yarda abincin ta ya kone, muryar inna ta ji a balcony tana cewa "Aa kawai ni dai naga kwana biyu bata shigo bane shine nace in xo in duba ko jikin ne, tunda haka Allah yyi ta mai laulayi, ni jiya ma ko abinci basu kawo min ba wllh, in ma ba ta da lafiya ita Aishar baxata iya takowa ta kawo min abincin ba tunda ba uwarta Habiba bace, abu dai gashi ba tsari da ni fitinanniyar tsohuwa ce ba Bukar xan kira ince matarsa ta bar ni da yunwa ba?" muryar Yusuf imaan taji yana dariya yace "Toh ae an kai maki daga gidanmu naga" da sauri Imaan ta shige daki ta dau Hijab dinta ta fito ta shige kitchen ta kashe gas din sannan ta bude kofar kitchen din ta fice tana murguda baki ta sa Hijab dinta da iyakarsa gwiwa, ko takalmi bbu kafarta ta dinga tafiya har ta zagayo front din gidan, Mujaheed ne xaune kan farin kujera yana waya, ta turo baki ta wuce sa da sauri, ko minti biyar ba ayi da wucewarta ba shi ma ya ji muryar inna tana tahowa, mikewa yyi da sauri tun kan ya bar wajen ta gansa, da karfi ta kwalo masa kira tana murmushi, ya ki juyowa har ya sha corner, Yusuf sai danne dariyarsa yake, Inna ta bude baki tace "Wato ni Mujaheed xai walakanta ina kiransa ya min banxa kai shaida ne ko Isuhu" tana magana tana kunce ha6ar xanin xata goge kwalla, Yusuf ya kasa daurewa ya fara dariya yace "Ke fa kika ce kar ya sake xuwa bangaren ki..." A fusace tace "To shi mahaukaci ne bai san bacin rai ba" Karo Mujaheed ya kusa yi da Imaan dake kokarin lekowa taga ko inna ta taho bangaren, ya hade rai yace "Baki gani ne?" Tana shafa Inda ya bugeta tace "Ko ba inna bace, ta wani biyoni gidanmu anjima tace ina mata rashin kunya" tafiyarsa yyi ya bar ta wajen tsaye, ta turo baki ta bi bayansa, jin tafiyarta a bayansa ya tsaya ya juyo yace "Wai me yasa kike bi na ne" Tace "Ni ba bin ka nake ba tafiyata kawai nake" Tsayawa yyi ya daure fuska yace "To yi tafiyar ki, bana son ganin ki kusa da ni" ba ta ce komai ba ta fara tafiya kamar mai counting steps dinta, yana ta tsaye yana jiran tayi nisa ganin ynda take tafiyar ya girgixa kai ya wuce ta cikin lokaci kankani, sai a sannan ta kara saurinta har ta jera da shi, d'an murmushi yyi bai dai ce komai ba bai kuma kalleta ba, sai da suka kusa entrance din kitchen din part dinsu tace "Yaya ka mance promise da ka taba min 2 years back koh?" Kallonta yayi kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Na me?" Ta wara manyan idanuwanta tace "Idan nayi saukan al-quran, gashi mun kusa in few months time" tabe baki yyi xai bude kofar kitchen din yace "I can't recall...." Ta xaro ido ta rikosa da sauri tace "Wllh nasan baka mance ba" Buge hannunta yyi yana mata wani kallo yace "Keee" Ta turo baki tana kallonsa, yace "Sakeni kar in mare ki" sake sa tayi ya bude kofar kitchen din ya shiga ya kulle, tana ta tsaye wajen bayan few minutes ta murguda baki ta wuce, ta kitchen dinsu ta bi ta kulle kofar sannan ta wuce dakinta ta sa kayanta. Yau tunda Imaan ta tashi take ta murna, gaba daya farin cikin ta ya kasa boyuwa, Kitchen ta shiga tace "Ammi da yaushe daddy xai iso?" Bude baki Ammi tayi tace "Kina kallon agogo kuwa Imaan?" Imaan tace "Ammi wai yau ma da daddyna xai dawo sai naje islamiyya?" Ammi ta mata wani mugun kallo tace "Uwar me xa ki xauna ki min ko yace maki da safe xai taso, common kin 6ace min a nan kin je kin shirya ko sai na 6ata maki rai" a hankali Imaan ta juya a sanyaye ta koma bedroom dinta ta fiddo uniform dinta ta shiga sa wa, sai da Ammi tayi mata jan ido ta amince da yin breakfast da ta hada mata, tana xaune dinning tana shan shayin da kyar Maimoon ta shigo parlon sanye da uniform, Ammi dake goge goge a parlorn tace "Maimoon ku yi wucewar ku kar ta bata maku lkci ko da kafa ne sai ta je" dariya kawai Maimoon tayi ta fita, Imaan ta mike don kanta ganin takwas ya wuce ta dau jakarta ta fita tana matsar kwalla ko ta kan kudin makarantar bata bi, Ammi dai ko kallonta bata yi ba, Tsaye taga Mujaheed jikin motar banda masifa babu abinda yake ma kannin nasa, duk kallonsa kawai suke babu wanda yace komai, "Don samun waje nan nan da islamiyyar ma sai an kai ku a mota ku ga yan gayu ko, to wllh ni ba driver din kowa bane a cikin ku da xa a dinga cewa in ajiye ku a makaranta, Yusuf da ya ga xai iya sai yyi, I won't tolerate that shittt" A hankali Ummi tace "Amma ya Mujaheed kawai don kana nan ne yasa xaka kai mu ai ba kai ke kai mu ba dama, kuma Abba yace kila Monday xa mu samu sabon driver...." wani kallo ya dinga mata fuska daure, ta sunkuyar da kanta, Imaan da isowanta kenan ta bude motar xata shiga ya dakatar da ita yace "Kee, do I look like drivern gidanku da xaki ajiye ni for the past 15 mins a nan, to ke daga yanxu ma xa ki fara naki trekking din" yana fadin haka ya nuna mata makeken gate din gidan yace "Bi can ki kama hanyar makarantar" ta wani gwalo ido tana kallonsa, lkci daya ta juya kamar xata yi kuka xata koma part dinsu tace "Ni dai ban ta6a tafiya da kafa ba...." Wani tsawa yyi mata yace "Wllh ki ka yarda na takowa har Inda kike sai na sa ki kuka" tsayawa tayi tana hawaye don bata mance last abinda ya mata ba, ya nuna mata gate on a serious note yace "Bi can" Gate din ta nufa tana kuka ya jira ya ga fitar ta sannan ya shiga motar ya bar gidan har ya wuce ta. Tsaye tayi bakin titi ta rufe fuskarta da Hijab tana kuka, ta kusa minti sha biyar tsaye a haka taji cikin cool voice ance "Are you okay" xame hannunta tayi a hankali daga fuskarta tana lekan ko waye ta cikin hijab dinta, wani dogon matashi ne da baxai wuce thirty two ba, yana sanye cikin kananun kaya idonsa sanye da bakar spec, dogo ne shi din sosai, sannan shi ba baki ba kuma baxa a sa shi a jerin farare ba, kuka ya kara taho mata ta dinga rerawa, yace "Subhanallah, wani abu ya faru da ke ne? Talk to me plss" Cikin rawar murya tace "Yaya ne ya ce baxan shiga mota ba trekking xanyi kuma islamiyyar mu da nisa wllh" kallonta ya dinga yi da mamaki, ta sake lekosa ta cikin Hijab suka hada ido ta yi saurin rufe fuskar tana shessheka, ya d'an yi murmushi yace "Kin masa laifi kenan" girgixa masa kai tayi, yace "Toh mu je in ajiye ki ga ride dina can, while going inside the filling station na gan ki tsaye bayan nayi refilling tank na fito I still saw u the way you were so I decided to check if you are alright" shiru tayi bata ce komai ba yace "Mu je to" tace "A'a" yace "Ohk in samar maki adai daita?" Kai ta gyada masa, ya tsayar da adai daitan ta shiga ya basa kudin, a hankali tace "Nagode" ya mata murmushi kawai mai adai daitan ya ja suka bar wajen, Yusuf ne ya dauko su daga islamiyyar bayan sun tashi karfe sha biyu, tun a mota ya dinga tambayar Imaan me ya faru ganin yanda take yamutse fuska, da kyar tace "Kafana ke min ciwo" yace "Toh sannu, idan muka isa gida sai ki shafa maganin" a hankali tace "Toh" suna isa gidan da kyar ta fito motar, Yusuf ya kama hannunta ya rakata har sashin nasu sannan ya bude mata kofa ta shiga ciki, wanka kawai tayi ta saka doguwar riga Ammi ta shafa mata methylated lotion din da take shafawa a kafafuwanta sannan ta sa ta kwanta nan da nan kuma bacci ya dauketa, dab da la'asar Ammi ta tasheta, Ammi bata mata xancen islamiyya ba Imaan ta wara ido ganin irin girke girken da Ammi tayi tace "Ammi is all this for daddy?" Ammi tace "No it's for Imaan" murmushi Imaan tayi ta rungumeta ta baya tace "Thanks sweet mum" Ammi tace "Ki tafi kiyi sllh ko baki ga lokacin hr ya gota ba" da sauri ta koma daki, tana idar wa ta fito, Ammi tace "Daddy ya kira yana gate, ki fita ki shigo masa da kaya" da sauri Imaan ta nufi kofa Ammi na kiranta ta xo ta sa hajib don rigar jikinta karamin hannun garesa amma tuni ta fice, dai dai nan mai gadi ya bude gate sai ga motar Daddynta, da gudu ta nufi parking space ta tsaya cike da murna, Mujaheed dake kokarin bude motarsa suka yi ido hudu da daddy da ya fito Imaan ta rungumesa, Daddy ya sakar masa murmushi, hakan yasa ya nufe sa kamar mai kirgan steps dinsa, daddy na shafa kan Imaan yace "Ba kya girma koh Mamata" ta kara kankamesa tace "Don Allah daddy ka daina dadewa haka wllh ina Missing dinka" yyi murmushi yace "To xan daina mamana" Mujaheed ya risina yace "Sannu da hanya Abba" Wani hade rai Imaan tayi tana hararansa ta gefen ido, Daddy na murmushi yace "Thanks Son, ka bar mu a birnin tarayya ynxu koh" murmushi Mujaheed yyi yace "Ae kam daddy" daddy yace "Toh Allah yayi jagora, ya aikin fa?" Yace "Ae ban fara ba sai Monday Abba" Daddy yace "Allah ya kai mu" Daddy ya mika ma Imaan da ta turo baki ledan apples dinta da chocolates don a ko da yaushe tsaraban ta kenan, Mujaheed dai ko kallonta bai yi ba ya dau jakar laptop din daddy da wasu files ya nufi part dinsu, Murguda baki Imaan tayi ta jera da daddynta tana ci gaba da gaya masa yanda tayi kewarsa, Mujaheed ya sunkuyar da kai ya gaida Ammi bayan ya ajiye jakar hannunsa da files, ta amsa ta dau jakar ta wuce daki, Daddy ya xauna yace "Barrister bai dawo ba ko Mujaheed?" Mujaheed yace "Ehh bai dawo ba" Daddy yace "Ohk mun yi magana daxu ma" Mujaheed ya dukar da kai yace "Toh Allah ya huta gajiya Abba" daddy yace "Madalla nagode son" har ya fara tafiya Daddy ya kalli ledan apples da chocolates da Imaan ta sa gaba tana dubawa yace "Son baxa ka Debi apples ba" Da sauri Imaan ta jawo ledan jikinta tana kallon daddy, Mujaheed da har xai ce A'a don he isn't a fan of Apple ganin abinda tayi yayi kasa da kai yana shafa gashinsa yace "Toh Abba" daga haka ya nufeta, bude baki tayi tana kallon daddy lkci daya hawaye ya kawo fararen idonta, Mujaheed ya jawo ledan yana kallonta da kyau ya cire spare leda ya debi apples har hudu a cikin guda takwas da Daddy ya siya ya xuba a wani ledan yana kallonta har sannan, ya kara bude ledan chocolates din ma ya debi mai yawa ya xuba a ledan hannunsa, har ya mike ya sake dawowa ya dau Apple daya ya sa ka a ledan, daddy ya dauke kai yana murmushi, Mujaheed bai yarda ya kallesa ba yace "Nagode Abba" daga haka ya fice parlon.
[6/11, 12:34 PM] +234 703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan*⭐🌟





_By Khaleesat Haiydar_✍🏻





4.....

Daddy ya kalli Imaan dake goge hawayen idonta yace "Don yayanki ya debi apples kike kuka Imaan?" Ta marairaice tace "Toh daddy ai ba shi ka siyo ma ba gashi ya kwashe min gaba daya kuma wllh baya cin apple" Daddy yyi murmushi yace "Shi yace maki bai ci" cikin rawar murya tace "Ae nasan baya ci tun da can" Daddy yace "Toh anjima idan na fita xan karo maki" a hankali tace "Toh nagode" yace "Wai amma me ya hada ku da yayan naki all of a sudden Imaan" Ammi da ta fito parlon tace "I am still wondering also, lkci daya aka yi parting" Daddy yace "Ko kin masa wani abun ne dai" ta turo baki ta dawo kusa da daddy tace "Kawai dai naga ya xama mugu ne shi sa na daina kulasa" Dariya kawai daddy yayi, Ammi tace "Har nan ma ai baya shigowa yanxu" Daddy yace "Toh Allah ya kyauta" Imaan tace "Daddy ni dai ka daukan min personal driver dina plss" daddy yace "Ba Abbanku xai daukar maku driver ba, ai mun yi magana da shi bayan tsohon drivern ya wuce" Tace "A'a daddy ni dai nawa daban nake so, kilan ba yanxu driver din ma xai xo ba, yau fa Yaya bai bari na shiga motar ba don na bata masu lkci da kafata na tafi islamiyya shi sa tun da na dawo duk jikina ke ciwo sai da Ammi ta shafa min magani na kwanta da na tashi shine naji sauki"' Murmushi kawai Daddy yayi ya mike yace " Bari in yi wanka daughter " daga haka ya wuce bedroom dinsa, Ammi tace "Sai ki tashi ki kai ma Inna abinci ko yau ma baxa ki ba" Ta kalli Ammi da sauri tace "Ammi ca tayi bata son sake ganin kafata a part dinta fa, kuma in je yanxu ta gaya ma daddy" Ammi tace "Tashi ki dauki abinci ki kai mata nace" Daga haka Ammi ta bar parlon, mikewa Imaan tayi ba don ta so ba ta shiga kitchen, kusan duk abinda Ammi tayi ma daddy sai da ta dibar ma inna duk ta ajiye a basket, Imaan ta dau basket din me dauke da abincin ta fita, har ta isa part din Inna fuskarta a daure yake irin ko kulata din nan baxata yi ba, ta dinga kallon takalman dake bakin kofa kafin ta bude kofar ta shiga, Mujaheed na xaune yana kallon inna dake bada labari tayi mitsi mitsi da ido, banda murmushi babu abinda yake don da wuya yake dariya, su Maimoon da Rahma kuwa dariya har da kyakyatawa, Inna ta saita hannu sama tace "Ji kawai muka yi ratatatata.... Ba sai kakan ku ya shige karkashin gado ya bar ni da halina da 'ya yana ba, lkcn Bukar na bayana sai tsala ihu yake, Ahmadu kuwa fitsari ya dinga saki yayi sau uku a wando...." Ganin Imaan Inna tayi shiru ta jawo daya daga apples biyar dake cikin leda a gabanta ta kai baki, Har sannan su Maimoon dariya kawai suke, imaan ta ajiye basket din hannunta tana kallo chocolates din da Daddy ya kawo mata a hannunsu Maimoon, ta saci kallon Mujaheed ta juya xata fita Inna ta tabe baki tace "Ga dambun naman ki can a daki ni dai na ajiye maki bana bi ta halin ki ba" ba tare da ta juyo ba tace "Bana ci" inna na ci gaba da cin apple dinta tace "To wa yayi asara?" Mujaheed yace "Yana ina a dakin?" Da sauri Imaan ta juyo ta shige dakin, Inna tace "Ya xaka ce yana ina bayan ka ci rabon ka da wanda ma ka dauka ban baka ba" yace "Haba" tayi tsaki tace "Yana nan cikin roba xa ki gansa a rufe, duk naki ma ya fi yawa" Imaan ta fito rike da uban dambun naman da inna ta ajiye mata a bowl mai murfi ta nufi kofa, inna tace "Wannan liyafar hala Bukar ne ya dawo?" Imaan tace "Bai dawo ba" daga haka ta fita, Inna tace "Duk ta ma fige kamar bata cin abinci" Rahma tace "Mu dai ci gaba da ba mu labarin da kike yi don Allah inna" inna ta gyara xama xata ci gaba, mikewa Mujaheed yyi ya fita parlon. Imaan na komawa bangarensu ta tadda Yusuf ya shigo gaida Daddy, Ya bi ta da kallo ta boye bowl din hannunta tana wara masa manyan idanuwanta tace "Nasan ka ci naka dai" fitowar Daddy parlon yasa Yusuf bai ce mata komai ba, daddy yace "Engnr ashe kana gari" Yayi murmushi yace "Ina nan daddy, da fatan kun iso lafiya" yace "Alhmdllh My son, ya aikin fa" Yace "Mun gode Allah Daddy" daddy ya xauna kujera yace "Madalla, kowa dai lafiya koh?" Yusuf yace "Duk lafiya" Yusuf bai wani dade ba ya mike yace xai wuce, daddy yace "Baxa ka tsaya mu ci abinci ba" Yace "Alhmdllh daddy na ci abinci" Ammi dake dinning tana jera abincin tace "Anya Yaya Yusuf" dariya yayi yace "Ammi wllh na koshi" tace "Toh shikenan" sallama yyi ma daddy ya fita. Bayan magrib daddy xai je gaida inna babu yanda bai yi da Imaan su je ba ta ki, har hakan ya basa mamaki ya tafi shi kadai, inna na goge tiles din parlonta daddy ya shiga da sallama, ta mike tace "Amma dai gaskiya Bukar ka dinga kwa6a ma yar ka ta daina karya, ce min fa tayi baka dawo ba" Ya xauna yana murmushi yace "Sannu inna, ina yini" ta shimfida tabarma ta xauna tace "Lafiya lau, amma ai karya ba shi da amfani kuma a gaskiya Imaan ta iya karya" Shi dai bai ce komai ba, tace "Toh ya hanyan?" Yace "Alhmdllh mun baro hanya" tace "Wannan karan kuma kamar baxa ka sake dawowa ba" yace "Aiki ne yyi yawa Inna" tace "Toh Allah ya bada sa'a ya tsare mana ku a duk Inda kuke, ya maka albarka" yace "Ameeen inna" Tace "Toh ya xa ayi, Allah ya kaddara a can abincin ka yake, banda haka na tabbata da kana gidan nan da ka dinga share min hawaye daga bakin cikin da nake fuskanta" Daddy na kallonta da mamaki yace "Bakin ciki kuma Inna?" Inna tace "Yo bakin ciki mana Habu... Kaga yayanka baxai fito daga masallaci ya tako nan tun asuban ba ya gaisheni sai ina jin wajen karfe tara xai taho da safe ya duka can bakin kofar ya gaida ni a gurguje ya kara gaba, bana sake ganinsa Bukar sai ina kokarin kulle kofa ta da daddare shi ma Allah yasa ya yi minti biyu xaka ga yace sai da safe daga haka ya wuce, Kaga matar nan tasa Rukayya take ko wa? Uwarsu Mujaheed dai wllh kaji rantsuwar musulmi tafi wata biyu ina ga bata tako ta xo nan ta gaisheni ba sai ta gan ni a tsakar gida ko a can bangaren, ita kuma dayar mai kama da fulanin Bararoji wato Amina da suke ce ma Anty sai ta bushi iskarta xata kwaso kafafuwa ta xo gaisheni, ita wnn farar wa take da suna? Uwar wannan yarinya Imaan d'an wankin da take min da duk ta watsar sun xugeta, in kuwa wannan 'ya taka Imaan borinta ya tashi ta ki kawo min abinci to ranan fa da yunwa xan kwanta a gidan nan, Aisha ta fi karfin ta taso takanas ta kawo min da kanta, to me yafi wannan bakin ciki Yaro? Gashi gaba daya 'ya yanku sun rainani sun maida ni ba bakin komai ba, sun maida ni kakarsu tun ma ba wannan katon Mujaheed ba da ramammiyar 'yar ka, sai wannan kazamar Ummi, ni nasan da sun ga ido wllh taka ni xasu dinga yi suna wucewa, isuhu kadai ke raga min a gidan nan sai wannan yarinya Seeyama, Imaan idan ta fara balbale ni wlh shiru nake, haka ma Mujaheed yaron da aka haifa a gabana, to ina dalili ina da gata na ta ko ina don dai d'an abincin da ake yarfa min a kwano sai a maida ni bola" Daddy dake ta saurarenta ya dago kansa a karo na farko yace "Kiyi hakuri don Allah inna" a fusace tace "Na gaji da jin wnn axxalumin kalman, ayi ta baka hakuri ana cutan ka, ni dai a fita harkata, don idan tsiyata ta debeni wllh sai an fita har kasashen waje ana nemana" Daddy yace "Xa a gyara Inna, duk ki yafe masu, ita Imaan xan sameta yanxu, shi ma Mujaheed din xan gamu da shi" Tace "Atoh, sai ka xaunar da su ka tambayesu kaji ko xaman gidan ne basa son inyi, ka tambayesu dalilin da yasa basa fitsaran su a waje sai a cikin gida cikin gidan ma a kan uwarka, kayi masu jan ido ka nuna masu bacin ranka Yaro" Daddy yana murmushi yace "In sha Allah" nan suka ta6a hira amma kusan hiran gaba daya na complain ne daga karshe daddy yace mata xai wuce masallaci don an kira isha. Daddy na dawowa masallaci ya dinga kallon Imaan dake xaune parlor tana cin abinci, ya xauna yace "Imaan yanxu ita innar kika mayar abar wasar ki a gidan nan?" Kallonsa ta dinga yi kamar zata yi kuka, ya hade rai yace "would you take ur eyes off me silly girl, haka kike ma uwar ki? I warned you the last time a kan haka shine kika sake repeating foolishness din yanxu ko?" Ta sunkuyar da kanta, ya gyada kai yace "Nasan maganin ki, tashi ki bar min parlor" tashi tayi da sauri ba tare da ta bi ta kan abincin ba ta shige bedroom dinta ta kulle, ita dai Ammi bata ce komai ba, Daddy yace "I don't like this nonsense character of her, ita innar abokiyar wasanta ce, ke kuma

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment