Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

don gaskiya ko ni bana cin abincin gidan hansai, to idan na ci na tsuge da xawo ya za ayi da ni???" Mujaheed ya juya a mugun fusace xai fita jin dariyar da Imaan take ya juyo ya haureta da karfi ya fice, wani ihu ta fasa ta rike kafar, inna ta mike da sauri tace "Fita ki bisa ni ba ruwana kada a dameni ya xa mu dinga magana ki mayar da mu mahaukata kina dariya" Imaan ta mike tana kuka sosai ta fita parlon tana dingishi ta wuce part din su, Ammi ta fito kitchen da sauri, Tace "Lafiya, me ya faru?" Cikin kuka tace "Yaya ne ya haure min kafar dake min ciwo da karfi gashi yanxu ya rike Ammi, Wllh ban masa komai ba" tana fadin haka ta xube kan kujera tana kuka sosai, Ammi ta karaso tana kallon kafar, har gun ya tashi yyi ja, Hijab dinta ta dauka ta sa ta fita parlon bata xame ko ina ba sai bangarensu, Yana xaune dinning takaici ya ishesa Anty kuma na kitchen da su Maimoon. Nan parlon Ammi ta tsaya tace "Mujaheed me Imaan tayi maka ka haureta a kafa?" Kallonta yyi ya dauke kai bai ce komai ba, ta karasa dinning din fuska daure tace "Tambayar ka nake malam, ka fara hauka ne xaka haureta a kafa, to Wllh even by mistake kada ka sake don zan dau mummunan mataki a kanka" Anty ta fito kitchen da sauri tace "Lafiya Hajiya Aisha?" A fusace Ammi tace "Wllh ku ja masa kunne ya fita harkar Imaan a gidan nan, duk ranan da ya sake gangancin ta6a lafiyarta xa ayi tashin hankali a gidan nan, haka kwanaki ya mareta na kai xuciya nesa ban ce komai ba, to this shud be the last, kada ya sake idan ba haka ba wllh sai na rama mata" Hakuri Anty ta dinga bata, Mujaheed ya mike ya wuce sama ba tare da ya sake kallonta ba, Ammi ta nufi kofa xata fita suka kusa cin karo da Umma xata shigo sun dawo anguwa da Rahma, ko kallonsu bata yi ba ta fice, tana komawa dama daki ta shiga ta dauko man xafi ta fito ta shiga shafa mata a gun, Imaan ta dinga yarfe hannu tana kiran daddy, bayan Ammi ta daina shafa wa a hankali tace "Ammi xuwa kika yi gun yaya?" Ammi tace "Baxan je ba ko shi ya haifa min ke?" Imaan na kallonta tace "Fada kika masa" Ammi tace "Abinda ya fi fada ma" imaan ta zaro ido tana kallonta, can tace "Ni da baki je ba Ammi ni ne fa nake ta masa dariya...." Da gudu ta mike bayan ta kauce marin da Ammi tayi niyyar sauke mata, ta wuce daki tana turo baki ta kulle kofar ta sa key, tana jin Ammi na cewa "Xaki fada min ko kanin ubanki ne yayan, daga yau ma kika sake xaunawa inda yake wllh sai na kakkarya ki a gidan nan" Inna ta saki baki tana kallon Mujaheed har ya gama, tura tuwon gabanta tayi tace "Ba lafiya, ita Aishar? To yaushe ta xama haka, atoh gaskiya imaan dai ta zama yar jaraba tunda akan ta uwarta taje tana maka bala'i, wato Allah kadai yasan abinda yarinyar ta tsara ma uwar, saboda irin wannan halayyar tata yasa aka rasa gane kan ciwonta fa har yau, to meye kuma yarinya karama da hada gurmi a gida, ae da sai kace ma Aishar A'a ni ba ruwana baxan yi fada da ke ba don kin haifeni, ai ke kusan sa'ar uwata ce, to kawai kuma sai ka tsaya kallonta kayi shiru" Mujaheed yace "Ni baxan ce mata komai ba ko sbda daddy, amma ta sake min haka a gidan nan gaskiya sae dai duk abinda xae faru ya faru" Inna tace "Ni ko sai naje na sameta wllh" da sauri Mujaheed yace "A'a kar ki ce mata komai" Inna ta ja tsaki tace "Ba dole in sameta ba xata sa ka gaba tana jaraba a kan figaggiyar yarinya mai hada gurmi" tana fadin haka ta fice parlon, Ammi na shafa ma Imaan man xafinta a kafa Inna ta shigo ba ko sallama, Ammi ta mike tace "Sannu da xuwa inna" inna tace "Aa ba wani sannu da xuwa, yanxu Aisha a kan yar ki xa ki sa Mujaheed gaba kina masifa inda kike shiga ba nan kike fita ba kamar xa ki make sa, to ma ina ruwanki kina 6are xa ki shiga harkan 'yan uwa, ubansa fa wan ubanta ne uwa daya uba daya, to ke kuma a wa Allah na tuba, Ba kunya ba tsoron Allah xaki shiga fadan 'yan uwa, abinda ma ina xaune parlon d'an shafa kafar nata yyi ya fita shine munafukar nan ta dinga ihu tana min birgima ni kuma na koreta, ni dai ba ruwana kar ki lalata mana xumunci gaskiya, ko xane Imaan Mujaheed yyi yau kanwarsa ce kuma yana da ikon yin haka, to banda shi da ya tsaya mata kan lalurorinta shekarun baya da ba sai dai ta mutu ba, ni dai a dinga jin tsoron Allah, gashi nan dai albarkacin Bukar bai kula ki ba, toh ni dai kada a sake sa min jika a baki ba ruwana, banda ma bifillatani agwai da wauta ina shi ina shiga sha'anin family" tana kai wa nan ta fice a parlon, Ammi ta rufe man hannunta tana kallon Imaan tace "Wllh na sake ganin ki xaune inda Mujaheed yake a gidan nan sai na kusa sumar da ke" Imaan dai ba ta ce komai ba. Misalin sha daya Imaan ta mike daga kwancen da take da kyar xata shiga daki ta kwanta, duk jikinta ciwo yake mata ga wani xafi da jikin yayi, Ammi dake xaune parlon tace "Kina ji na" imaan ta juyo tana kallonta, Ammi tace "Dama gobe kice masu baki jin dadi baxa ki iya tafiyar ba, don babu inda xa a dake, ina xaman xamana a kwaso min wahala a bar ni da jiyya" Imaan tayi shiru tana kallonta, can tace "Toh" daga haka ta wuce cikin daki ta kwanta. Washegari karfe tara su Maimoon, Ummi da Rahma suka gama shirin su na tafiya, kaya kala biyu ko wannensu ya dauka Abba duk ya basu kudin kashewa, Yana kallon Ummi yace "Tafi ki duba ko mamana ta gama shirya wa" Ummi ta fita parlon xuwa part din su Imaan, Ammi ta fito daga bedroom din Imaan kenan rike da cup din shayi don da mugun xaxxabi ta tashi safiyar ranan, Ummi ta shigo parlon da sallama, gaisheta tayi tace "Abba yace Imaan ta fito" Ammi tace "Ae kam yau ta tashi babu lafiya" Ummi na komawa ta fada ma Abba haka, Abba yace "Subhanallah ba lafiya kuma" mikewa yayi ya fita, a dai dai part din su Imaan ya hadu da Mujaheed ya dawo daga bangaren inna, Abba yace "Imaan wai bata da lafiya yau" Mujaheed yace "Subhanallah" Abba yace "Let me check on her" Mujaheed bai ce komai ba kamar ya juya yayi tafiyarsa sai kuma dai ya bi bayan Abba, Ammi suka gaisa da Abba, Mujaheed yayi kasa da kai ya gaisheta, Ita ma ba tare da ta kallesa ba ta amsa bbu yabo bbu fallasa, Abba yace "Toh ya jikin nata?" Ammi tace "Toh da sauki, tun jiya dama bata jin dadi" Abba yace "Ikon Allah" Ammi tace "Tana ciki" Abba ya nufi dakin nata, Mujaheed ya bi bayansa kansa a kasa, kwance suka sameta cikin duvet amma still sai shivering take, Abba ya cire duvet din yace "Sannu mamana" Bude idanuwanta da suka rina tayi a hankali, Abba yace "Ina ke maki ciwo" girgixa masa kai kawai tayi, Mujaheed ya duka kusa da ita a hankali ya kai hannunsa jikinta, Abba na kallonsa yace "Ko dai a tafi asibiti" Mujaheed xai yi magana aka bude kofar dakin inna ta shigo a rikice tace "Ahaf, ni dama nasan xa a rina, ba ayi hauri ba ma ya aka kare balle anyi, wllh Ahmadu da ya tattakure ya tattakure kawai sai gani nayi ya haureta"




*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻‍♀️

It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.22.

Imaan






















Abba ya juya ya kalli Mujaheed jin abinda inna tace, Imaan ta mike xaune da kyar tace "Ba fa kafana ke ciwo ba" Inna tace "Toh ina ke maki ciwo" Komawa tayi ta kwanta bata tanka ta ba, Ammi dake tsaye bakin kofar dakin sai kallonta take, Abba na kallon Mujaheed da ya kasa cewa komai yace "Amma me yasa xaka haureta jiya?" Ya sunkuyar da kai yace "It wasn't intentional" Abba ya gyada kai yace "It wasn't intentional, OK that's good kayi kokari" Daga haka ya juya ya kalli Ammi yace "Ta shirya ta fito mu je asibiti" daga haka ya fita dakin, Mujaheed ya harari Inna fuska daure xai fita tace "Oho dai ta rufa ma ka asiri amma ko tantama babu haurin da ka mata ne ya ja mata wannan ciwo" Ammi ta basa hanya fuska daure, kansa a kasa ya fita dakin, Inna tace "Kyansa duk inda imaan xata ga Mujaheed daga yanxu ta gudu tayi ta kanta, ni dama tun da naga yanda yake laftar 'ya yan jama'ah a anguwa yana d'an yaye bai fi shekara 3 ba nasan akwai bala'i a gaba wllh, duk ya bi ya addabi 'ya yan mutane da cizo da yakushi a anguwa, kowa ya gansa sai ya adana d'an sa, lkcn d'an Hansai Garba na kamarsa kullum sai ya ciji garba yakushesa, Hansai tayi ta jin haushi don ta xo jegon Huraira a gida, in takaice maki kafin Hansai ta bar gidan idan aka bude jikin garba duk ta6on cixon Mujaheed ne, to kuma meye baxai yi ba yanxu?" Imaan na daga kwance sai dariya take da kyar, Ammi dai ko kallon Inna bata yi ba tana fiddo ma imaan kayan da xata sa, inna tace "Toh Allah dai ya kiyaye gaba yyi maki tsari da shi, amma gaskiya imaan ki guji duk inda Mujaheed yake, idan kun dawo asibitin xan xo dubaki idan Allah ya yarda, tafiya dai ta sha ruwa" daga haka ta fita dakin, Ammi tace "Kin tashi kin shirya ko xaki kwanta nan kina dariyar walakanci ne?" Imaan ta tashi ta saka kayan da Ammi ta fiddo mata, Inna na fita taga Abba tsaye a waje, tace "Ahmadu tafiya dai ta sha ruwa koh?" Yace "A'a xa su wuce tare da Yusuf yanxu, shi Mujaheed xa su je asibiti da Imaan" inna tace "Toh madallah, hakan ma yayi, to ko in bisu asibitin ne" Ta gefen ido Mujaheed ya kalleta da sauri, Abba yace "Ehh to xa ki iya bin su" Tace "Toh bari in kulle dakina kada a barsa a bude gaskiya" daga haka ta wuce sashin ta, Mujaheed ya nufi motarsa don fitar da motar waje, Abba ya bi sa da kallo har ya isa parking space ya shiga motar, Imaan ta fito sanye da Hijab har kasa, da kyar take tafiyar, Abba yace "Sannu mamana, Allah ya sauwake" a hankali yace "Ameen" yace "Mu je can kofar gidan, ban gane fita da motar da yayi ba" tare suka fita compound din, Ya bude ma Imaan front seat ta shiga, Abba na kallonsa yace "Inna na tahowa yanxu, tare xa ku tafi" yace "Ehh na sani" Daga haka Abba ya koma cikin gida, Mujaheed na ta kallon gate har sai da yaga inna ta fito tana washe baki sannan ya ja motarsa yayi zooming off, Imaan ta xaro ido tana kallonsa, yana isa titi ya kashe wayarsa ya ajiye ya dau hanyar asibitin da yake aiki, Sai da suka yi nisa fuska daure yace "Ni kika je kika hada da mamarki koh?" Tace "Ko dai ita taga ina kuka" ya gyada kai yace "Xa ki gane kuran ki" Ta turo baki ta jinginar da kanta da kujera, Suna isa asibitin bayan yayi parking ya juya yana kallonta yace "Sauko min a mota" Bude ido tayi da sauri, ya bude door din motar ya fita, a hankali ta ta bude side dinta ta saukar da kafafuwanta kasa, xagayowa yyi ganin bata fito ba yace "Baxa ki sauka ba" kamar xata yi kuka tace "Wllh jiri nake ji yaya" Wani harara ya watsa mata yace "To daukan ki xan yi?" Bata ce komai ba ta sauko motar, ya rufe ya kama hannunta suka shiga cikin asibitin. Yana xaune office misalin sha daya bayan ya kunna wayarsa kiran Abba ya shigo wayar, murmushi yyi ya daga ya kai kunne, Abba yace "What's taking you people too long Mujaheed" yace "Drip aka sa mata Abba, jikin da sauki sosai, she is fast asleep now" Abba yace "Toh Allah ya sauwake, why did u left inna behind?" Yace "Abba Kasan yanda take abinta, xuwa xata yi tayi ta fada every slight mistake" Abba yace "Haka ne, da yaushe xa ku dawo kenan" yace "Nan da azahar in sha Allah" yace "Toh Allah ya kai mu" Mujaheed yace "Ameen" daga haka Abba ya katse wayar, Mujaheed ya juya yana kallon Imaan dake kwance kan gadon duba pregnant women tana bacci, mikewa yyi ya isa kusa da ita yana kallon ruwan da ya kusa rabi, Hannu ya kai forehead dinta yaji da dumi har sannan, ta bude ido a hankali, daure fuska yyi yace "How are you feeling now?" Yamutse fuska tayi tana son mikewa xaune yace "Lie still and answer my question" murya can kasa tace "Kai na yana min ciwo" yace "Shi kadai?" Tace "And am hungry" ya kalli abincin da ta ki ci da yawa daxu kafin a mata alluran a sa mata drip ya dauka ya bude ya ajiye kusa da ita ya daga ta xaune, xaro ido tayi tace "Yaya abincin daxu kuma??" yace "Kin taho da abinci daga gida ne" ta hade rai tace "Ni dai baxan iya ci ba bayan ya huce kuma an ajiye k'ura ya gama shiga ciki" wani kallo ya mata yace "Toh sai ki tsaya da yunwar ki ai, wannan abincin dake rufe meye ya samesa da baxa ki ci ba, Bayan har ynxu ma da dumi abincin" yana fadin haka ya dau cokalin ya debi abincin ya kai baki, ta tabe baki ta dauke kai tace "A'a ni dai bana so, tun da safe fa, ko ta gefe gefe ai dust xai iya bi ya shiga, sai dai kai ka cinye a kawo min wani" Yace "Toh xaki ga wani kuwa" daga haka ya kai abincin table dinsa ya xauna ya fara ci, ta dinga kallonsa kamar xata fashe da kuka, ganin ko kallonta bai yi ba tace "Ni dai ka bani waya in kira Ammina ta kawo min abinci" yace "Baxan bayar ba" komawa tayi ta kwanta ta fara kuka har bacci ya sake xuwa mata, mikewa yyi ya rufe sauran abincin da bai cinye ba ya fita office din. Wani takeaway din ya fita ya siyo mata na abinci, yana dawowa ya tasheta ya ajiye mata abincin a gabanta sannan ya juya ya fita, ta mike xaune ta bude abincin ta fara ci a hankali, har ya dawo dakin bata gama cin abincin ba, ya xauna kan office chair dinsa, tana kallonsa tace "Yaya ni baxan iya cinyewa ba" bai tanka ta ba hankalinsa na kan laptop din gabansa, ya gama abinda yake sannan ya juya yana kallonta ya ga ta ajiye abincin ta kwanta, mikewa yyi ya karasa kusa da ita ya dauke abincin ya ajiye ta bude ido tana kallonsa tace "Yaya ina son xan yi magana da Ammina" yace "Baxa kiyi ba" yana fadin haka ya koma table dinsa, ta turo baki ta juya masa baya. Karfe biyu Imaan ta bude ido jin an kama hannunta, ya karasa cire mata drip din yace "How are you feeling?" Ta mike xaune da kyar tace "Da sauki, I want to go home" Yyi disposing roban ruwan ta sakko saman gadon, da sauri ya rikota ganin xata fadi duk da ita ma ta kama gadon, kamar xata yi kuka tace "Wllh jiri nake ji yaya" Ya saketa yace "Toh ni nace ki sakko?" Komawa saman gadon tayi ya fita dakin, ba a dau lkci ba ya dawo ya dau wayarsa da car key yace "Mu je" ta xaro ido tace "Idan na fadi fa?" Yace "Sai ki tashi" daga haka ya nufi kofa, sauka tayi saman gadon ta tsaya na kusan minti daya har ta ji ba jirin kuma sannan ta nufi kofa a hankali kamar mai counting steps dinta ta bude kofa ta fita, tsaye ta gansa yana jiranta, ya mata wani kallo yace "Da kin bari na sake shiga office din ki gani" daga haka ya wuce ta bi bayansa, sallama yyi da co workers dinsa suka fita asibitin, a Wani pharmacy ya tsaya ya sauka ya siyo mata drugs da aka mata prescribing sannan ya dawo ya shiga motar suka bar wajen, sai da suka kusa gida a hankali tace "Yaya baxa ka siya min kaza ba plss" yace "A'a sai dai in siya maki akuya" murmushi tayi tace "Toh siya min" A waje yyi parking yace "Sauka..." Ta bude motar ta fita sai da ta shiga gate ya ga ledan maganin da ya siya mata" fitowa yyi motar rike da ledan ya wuce ciki da sauri, ganin har ta kusa apartment dinsu ya wuce nasu bangaren kawai, Babu kowa parlon, ya haura sama dai dai fitowar Anty dakinta tace "Ya jikin Imaan din?" Ya saci kallon kofar Umma kafin yace "Da sauki, Umma bata nan ne?" Anty tace "Ehh tun da ta ji kai ka kai Imaan asibiti ta fice gidan tun safe bayan ta gama bambaminta" Mujaheed ya xaro ido ya jingina da bango yace "Wa ya gaya mata Anty?" Anty tace "Abban ku, tunda ba tsoron ta yake ba" Ji yayi xufa na keto masa, Anty ta wuce ta bar sa wajen tsaye, da kyar ya ja kafafuwansa ya wuce dakinsa. Ammi ta hada ma imaan ruwan xafi a bayinta ta fito tace "Ga ruwan ki shiga, saura ki salance ruwan" Tashi Imaan tayi ta wuce dakin nata. Wanka Mujaheed yayi ya shirya jin lkcn Asr yyi yayi alwala ya fita gidan, yana dawowa masallaci dama part din inna ya nufa don Allah yasan yana tsoron haduwarsa da mahaifiyar tasa Inna ta fito daga daki jin an bude kofar parlor ganinsa tace "oyaa Alale, fitar min parlor kada in tara maka jama'ah, uban me ka xo min??" Mujaheed yayi dariya yace "Haba dai mai gidan kuma kike kora yau inna?" A fusace tace "Yana kabari, tun raina bai baci ba Mujaheed ka fita" Mujaheed yace "Abba ne fa yace kada mu tafi dake Inna" ta buda baki tana kallonsa tace "Kai haba?" Yace "Xan maki karya ne" xauna wa tayi tace "Ikon Allah, shi Ahmadun yace ku tafi ku bar ni kenan, to ya ma kansa kuwa, shine har da shi a bani hakuri da masu gadi a tsakar gida daxu, har hawaye fa sai da na xubar" Mujaheed yyi murmushi ya kwanta kan kujera, Inna tace "Toh ae shikenan, ya jikin Imaan din?" Yace "Da sauki" inna tace "Kuma da gasken bata da lafiya Mujaheed? Naga kamar don kar aje kauyen da ita yasa ta langwabe fa" Mujaheed yace "Ni dai akwai abinci?" Tace "Gashi can wanda Aisha ta kawo min ne daxu, bai wuce shinkafa da miya ba, Idan kuma biskit xa ka ci ga su can iri iri a daki wanda aka kawo ma Imaan, Kazan ma daxu na dumama na karasa cinyewa..." Mikewa xaune Mujaheed yyi yana kallonta na kusan second goma, can yace "Wa ya kawo mata?" shiru Inna tayi kanta a kasa, can ta saci kallonsa suna hada ido tace "Yo wa gareta banda Bukar??" tana fadin haka ta mike ta shige daki.... Imaan ta fi minti biyu tsaye bakin kofar bedroom din Ammi ta kasa shiga don bata san me xata ce mata ba, bude kofar dakin aka yi ta ja baya da sauri, Ammi ta dinga kallonta tace "Meye haka kike yi a bakin kofa ta?" Ta fara kame kame ba tare da ta kalli Ammi ba, Ammi tace "Imaan" daga kai tayi ta kalleta kamar xata yi kuka, Ammi tayi kasa da murya tace "Tell me what you want" tana jan fingers dinta a hankali tace "Ammi dama... Dama Sadeeq ne yace min yana waje ya xo gaisheni" Ammi ta dinga kallonta tace "Waye Sadeeq" ta sunkuyar da kai tace "Abokin ya Muhsin" Ammi ta yi shiru, can tace "Toh kar ki dade" Ta d'an yi murmushi tace "Toh nagode Ammi" daga haka ta saka Hijab dinta ta fito don tun da aka yi la'asar Sadeeq ke waje amma ta rasa yanda xata sanar ma Ammi ta fita, sosai hankalinta ya kwanta ganin ba motar Mujaheed a parking space, kamar mai tausayin kasa ta fita kofar gida, Tsaye ta ga Sadeeq jikin motarsa ya rungume hannunsa, as usual sanye da spec dinsa, dogon hancinsa da cute millionaires belt dinsa shine first abinda xaka fara noticing a fuskarsa daga nisa, Ta sunkuyar da kanta har ta isa inda yake tsaye, kallonta yake daga cikin glass din idonsa ko kiftawa babu, murya can kasa tace "Ina yini?" Yyi murmushin da ya bayyan dimples dinsa ya cire glass dinsa yace "Lafiya lau Imaan ya jikin?" A hankali tace "Na ji sauki" yace "Sure??" Ta gyada masa kai, yace "Toh Allah ya kara lafiya, hope kin sha dosage na afternoon, I mean ur drugs?" Ta gyada masa kai tace "Na sha" yace "Good, ya mama fa?" Tace "She's inside" ya langwabar da kai yace "Yaushe xan xo gaisheta pls" ta xaro ido tace "A'a xan ce kana gaisheta" cikin sanyin murya yace "Ke dai baki son yan gidanku su san ni koh?" xata yi magana aka bude gate, Inna ce tsaye bakin gate din tana kallon mai gadi tace "Kai iliya kake ko ilu, Kasan kan waya kuwa? Hadiza xa a kira min duk ba kowa gidan sai mai laluran can kuma nasan tana can tana bacci yanxu haka, yaran duk sun tafi kauye sai gobe xa su dawo" Imaan tayi stiff inda take bayan gabanta yayi mugun faduwa jin muryar inna, Mai gadin ya mike da sauri ya amshi wayar yace "Toh Hajiya...." Buda baki inna tayi tana kallonsa tace "Eh lallai baka da da'a, banda barbada kace ma matan gidan Hajiya nima kace min Hajiya, to bari kaji ko wa enda suka dauke ka aiki ma inna suke ce min balle kai, bar gani na haka xuciya mai kyau da rikon gaskiya da amana yasa ka gan ni har yanxu da kyau na, amma wllh da kyar idan ban girmi wanda ya haifi kakanka ba ma" yayi kasa da kai yana murmushi sosai yace "Yi hakuri Baaba tuba nake" inna tace "Kaji min yaro dai" Imaan dai ta kasa tsaye waje daya tayi backing din inna xuciyarta sai bugawa yake, murya can kasa Sadeeq yace "Ur grandmum?" ta gyada masa kai a hankali, kamar ance inna ta daga kai ta gan su, sake baki tayi ta kalli mai gadin tace "Kai wancan ba Imaan bace nake gani a tsaye?" Yace "Ita ce Baaba" Sadeeq yace "Let me go and greet her tunda ta gan mu" imaan dai kasa cewa komai tayi, ta ji kamar ta fashe da kuka, ae kuma shikenan.... Sadeeq na isa gun Inna dake ta kallonsa ya risina ya gaidata da ladabi, tace "Kai ne sabon saurayin nata?" Murmushi Sadeeq yyi ya kasa cewa komai, Inna tace "Ikon Allah, Kai ni fa na haifi ubanta Bukar, jikata ce fa, ita kenan Allah ya ba Bukar fa, a hannuna fa aka haifeta wllh, yanxu d'an nan da ban fito na gan ku ba shikenan, kai a garin ku haka ake yi?? ko bata ce maka kakarta na da rai bane, ita tunda bata

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment