Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan xakiyi sai kin ta fama, anya kuwa ba a sa maki hannu ba imaan?" Imaan ta xamo daga kan gadon tace "Wayyo ni dai ki kira min yaya " Inna tace "Waye kuma yaya?" Hawaye na sakko mata tace "Ni dai ki kirasa" Inna tace "Toh su wa encan tsofaffin duk tsami sun cika min parlor kamar ni xan aurar da 'ya sun ki tafiya, ni dai na gaji wllh ana damuna, wata ma ni nafi shekara talatin ban gan ta ba, ni dai gaskiya sun isheni suje can bangaren da ake biki kuma sun ki, duk parlona ya gauraye da warin tsofaffi, wannan fitina da mai yayi kama" Imaan na son yi dariya amma ciwo yaki barin ta tayi, Inna ta fita fuska daure ta kashe TV da ke aiki tace "Kada TV ya buga in ja ma Ahmadu asara gwara a bar shi haka nan ya huta" daga haka ta dau wayarta ta fita don neman me kira mata Mujaheed, wata ta samu a tsakar gida ta nufeta tana kallon mata yan gayu xaune tsakar gidan, tace "Toh dai gida ba na bitilman bane duk wanda ya xubda ko kwayar shinkafa yyi hakuri ya share fisabillahi, kar a tafi a bar mu cikin wari cuta ta kama mu" mika ma matar wayar tayi tace "Gashi Idan kin iya karatu ki duba lambobi xa ki ga ansa Dakta, lambar Mujaheed ne shi ya sa mun shi a haka, sai ki kira min idan kuma baki iya ba don Allah kar ki rikita min wayar in shiga uku" murmushi matar tayi ta nemo number tayi dialing ta mika ma inna, ta amsa ta kai kunne, sai da yayi ringing sau uku sannan Mujaheed ya daga, inna tace "Mujaheed??" Mujaheed yace "Ina ji, ya aka yi?" Inna tace "Toh ga yar uwar ka nan dai rai a hannun Allah, duk inda kake ka rufa mana asiri ka juyo ka dawo, ni sae in iya cewa a daga bikin ma wllh don idan ta mutu ni nayi asara...." Da mamaki yace "Wacece?" Inna tace "Wacece banda Imaan, tun safe Ashe tana dakina babu inda bata mirgina ba don ciwo, tun daga kan gadon har kasan tass, wai yanxu na shiga dakin don kulle bandakina saboda marasu hankali masu shiga bayin mutum suyi kaca kaca da shi kawai naga yarinya duk ta hada xufa a kan gado kai kana ganin ta kasan...." Mujaheed ya katse ta yace "Ina hanya" daga haka ya katse wayar, Inna tace "Atoh haka kawai, bikin banxa bikin hofi..." Daga haka ta nufi part dinta, tana durkushe bakin kofa tana watsi da takalman jama'a can gefe ganin duk ya cika mata bakin kofar ta ji muryar Mujaheed a bayan ta ta mike, tace "Wannan uban sauri haka kamar wanda ya biyo jirgi, to ka shiga tana can ciki ban san isilinta ba" Shiga parlon yayi ganin mutane ya sunkuyar da kansa ya gaishe su ya wuce dakin Inna, karasawa kan gadon yayi yana kallonta yace "Me ya faru?" Ta fashe da kuka sosai tace "Yaya cikina" hannu ya kai cikin yace "Tun yaushe?" Ta cire hannunsa tace "Ni ba cikin bane ke min ciwo, period ne" ya daure fuska yace "Toh me xan maki, ba kin sha magani ba" da kyar tace "Bai yi ba, doctor Habib allura yake min" yace "Toh me ya hanaki kiransa?" Tace "Yana Lagos" yace "Toh bani da allura a nan sai na koma asibiti" ta kamo hannunsa cikin rawar murya tace "Toh ka tafi da ni asibitin plss" tana fadin haka ta fara kokarin sauka kan gadon, bude baki yyi ganin yanda tayi ma inna stain din kan gado, bai san lkcn da ya dauke kai yana murmushi ba don har ya hango inna, ita ma xaro ido tayi tace "Na shiga uku yaya" yace "Aa sai ta gani xaki ki shiga ukun ai, yanxu kina daya ne" ji tayi gaba daya ba ciwon ta sauko kasa da sauri jikinta na rawa tace "Wayyo yaya ya xan yi" Tana fadin haka ta nufi bathroom ta murda ta ji a rufe, tsayawa kallonsa tayi kamar xata yi kuka tace "Yaya ta sa makulli" parlor ya koma gun inna yace "Inna xata shiga bayi ina makullin" inna ta mike da sauri tace "Auzubillahi, wani bayin? Aa ta fito ta tafi nasu idan ma baxata iya tafiya ba ka goyata, haka kawai bayina fess ta shiga ta sa min k'arnin jini" Kunya ma yasa Mujaheed ya kasa cewa komai don mutanen dake parlon sun kai shidda, ganin inna xata shiga dakin ya rigata shiga da sauri, ya dau dankwalinta ya rufe saman gadon da shi, Imaan ta marairaice tana kallon inna da ta shigo tace "Don Allah ki ban makulli wllh xan wanke maki bayin" Inna tace "Ai uwata bata ce min je ki kya gani ba, don haka ba bayina xa a shiga a min kazanta da jini ba, ki daure ki tafi can bangaren ku idan ma tafiyar ne baxa ki iya ba sai Mujaheed ya goya ki" Kuka Imaan ta fara yi tace "Na fa ce xan wanke maki wllh" a fusace Inna tace "Kai ku fita ma ku bar min dakina kuje can bangaren ku karata, da na bar ki ma kika kwanta min saman gado duk da ban san al'ada kike ba" Mujaheed yace "Toh ki bata xan wanke maki bayin da kai na" Inna kamar xata rushe masu da kuka tace "Yau naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, wai ana dole ne, hypo uku na xuba bayin nan daxu da safe da nake wankewa, a kan wani dalilin xa aje a bata min da karni...." Ya katse ta yace "Ni kuma xan xuba maki hypo biyar" da kyar da kyar da sidin goshi inna ta bada makullin shi ma sai da aka yi yarjejeniyar baxa a bude mata drum din ruwa ba kada a xuba kazanta, Mujaheed ya dau buckets biyu ya fita debo ruwa a waje, Ita dai imaan na tsaye sai satan kallon saman gado take, Mujaheed na ajiye ruwan a bayin ta bi sa ciki tace "Wayyo yaya pant da pad da xan canxa fa?" Ya kalleta da mamaki yace "Ni ma kike tambaya?" Ta marairaice tace "Plss ko xaka je dakina...." Ya jefa mata wani kallo yace "You are stupid" fitowa bayin tayi ta bude gun kayanta a wardrobe din inna, ai ko taga panties dinta na nan, tace "Yaya toh saura pad" Yace "Bari in xama pad din ki sa" Bata ce komai ba ta turo baki ta shiga bandakin ta rufe, juyawa yayi ya fita, ya tafi gun mai kiosk dake layin ya amso always daya ya dawo, inna dai na xaune ta daura kafa daya kan daya tace "Allah ni dai ya dubeni ya rabani da k'arni, komin xuba hypo da xa ayi a bandakin nan" Mujaheed bai ko kalleta ba ya shiga dakin, yana ta tsaye har Imaan ta fito daure da towel din inna, ya jefa mata pad din kan gado, ta turo baki tace "Thank you" komawa bandakin tayi ba a dau lkci ba ta fito, yace "Sai ki cire xanin gadon ki wanke" ta xaro ido tace "Yaya ya min nauyi fa" bude baki yyi yace "Toh ki bar shi haka nan" kamar xata yi kuka ta isa kan gadon ta shiga cire xanin gadon bayan ya dauke pillows din kai, Muryar inna suka ji tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, jinin ta xuba min a kan gado ni Asabe????" Inna ta fashe da kuka tace "Me na maki xaki saka min da haka Imaan" Mujaheed ya dauke kai yana kokarin danne dariyarsa, imaan duk ta gigice, inna tace "Toh sai ki Kwashi xanin gadon don ubanki ki Bukar kai ma Aisha ta wanke min, kai kuma ka fitar min da katifar waje ka sa min shi a setin rana, Allah ubangiji ya saka min, daga taimako sai ta xuba min al'adarta a xanin gado k'arni ya kashe ni" Inna ta kara rushewa da matsanancin kuka tace "Sannan d'an walakanci tana yoyon xata dau tawul dina ta daura salon ta goga min gaibu, ni dai na shiga uku da wannan 'ya ta Bukar, tana cutata a gidan nan" Imaan ta wani hade rai kamar xata yi kuka, Mujaheed ya cire xanin gadon ya wuce bathroom da shi, Inna na matsar kwalla ta daga hannu biyu sama tace "Allah kaga xuciya daya nake xaune da kowa gidan nan, duk mai nufina da sharri ka min iyaka da shi" Tana fadin haka ta share idonta ta fita tace "Bari xanje inji ko Aishar ce ta sa ki xo ki cuce ni yau" Imaan ta murguda baki ta fiddo kayanta a press ta saka, bude kofar bathroom din tayi ta ga Mujaheed yana aikin wanke xanin gadon.Imaan dai na tsaye har ya gama wankin bedsheet din tana rike da kayan da ta cire, ya saka xanin gadon a bucket ya fito, a hankali tace "Yaya to wankin bayin fa?" Wani mugun kallo ya watsa mata ya dau wayarsa da makullin mota da ya ajiye kan gado zai fita ta xaro ido tace "Yaya don Allah ka tsaya, baxan iya shanya bedsheet din ni kadai ba ai" ko juyowa bai yi ba balle ya tanka ta, a bakin kofar parlor ya hadu da Inna, Inna ta gwalo ido tace "Har an wanke min bayin?" Yace "A'a xan fita in amso Hypo ne" yana magana ne yana kokarin fita, inna ta cakumosa tace "Sai dai ka raina ma Bukar ko Ahmadu hankali, ce maka nayi bani da hypon?" tana fadin haka ta ja sa xuwa bedroom din fuskarta daure, yace "Toh ki sakeni mana" ko saurarensa bata yi ba har suka shiga dakin, Imaan dake labe bayan kofar dakin tana jin sun shigo dama ta fito da sauri ta fice a dakin, Har bandakin Inna ta turasa ta dauko Hypo biyu ta jefa masa, yace "Biyar fa kika ce Inna" a fusace tace "Toh ai ni ba asararriya bace Mujaheed, Ko sisin Bukar da Ahmadu babu a Hypon, Isuhu ne na roka ya siyo min" tana fadin haka ta dau ledan omo babba ta jefa masa tace "Har jikin tiles ni dai a gurje min ba ruwana, kuma daga yau gaskiya idan Imaan ta sake shigo min daki xa a ga bala'i, wato kawai fasa bomb din bala'i xanyi a gidan nan, naje yanxu uwar bata nan, da sai in ji ko ita ta turo min ita ta cuce ni ta xuba min al'adarta, banda ma kazanta irin na yaran ynxu duk sai sun bari kowa ya san suna al'ada, gantalalliyar duk ta tashi ta kazance min kan gado da bandaki, to hirrr dinta kada ko da wasa ta sake leko min daki ta tsaya iya falo, idan kuwa dama bata da tsarki kar ta yo min nan xan koreta don parlona na tsarkakakku ne" Mujaheed dai bai tanka ta ba ya nade sleeve din shirt dinsa ya fara wanke bayin bayan ya kada kumfa da hypo, inna tace "A'a bana son aikin al'gus malam, ka kara barbade bandakin da omo lungu da sako sai ka juye dayan hypon" ya jefa mata wani kallo yace "Toh wai ni na bata maki bandakin daga taimako kawai" Inna tace "A'a ba ruwana saboda kai na bude, in don ta wancan matar ce ai sai dai ta tafi bangarensu jage jage da jini don wllh baxan bude ba, haka kawai" ko kallonta bai yi ba ya ci gaba da wankin bayin da babu abinda ya samesa, haka inna ta dinga basa wahala tana tsaye daga bakin kofa tace can tace nan, har daga karshe aka gama wanke bayin, ya wanke hannunsa ya fito fuska daure, tace "Toh don Allah ni dai kar in kwana cikin k'arni yau ka taimakeni ka fidda min katifar can ka ajiye dai dai idon rana" yace "Wannan kuma sai dai ki kira Yusuf baxan iya ba gaskiya" Tace "Toh wllh baxa ka fita dakin nan ba sai tare da katifar nan, haka kawai in kwana cikin najasa, kafar ka kafar katifan" tana fadin haka ta sa makulli a dakin ta tsaya bakin kofa, kallonta ya dinga yi fuska daure, inna tace "Oho dai duk kanwarka ta ja maka, ita yanxu ba gashi ta gudu ta bar ka da aikin jini ba, yarinya sai mugunta fal cikinta" Babu yanda ya iya haka ya cire katifar ta bude masa kofa tace "Saitin rana xaka ajiye duk ya kona abinda ya xuba kai" fita yyi da katifar ya ajiye inda tace, ya dawo dakin don daukan wayarsa da makulli, ganin babu su a inda ya ajiye ya kalli inna dake tsaye tana kallonsa kyarr, bucket din xanin gadon ta nuna masa tace "Idan ka shanya wnn sai ka dawo ka amshi wayar ka da makulli ba ruwana, yarinya dai ta cuce ka kawai, sae dai sakayyar Allah" tana fadin haka ta koma parlor, Mujaheed ya fi minti uku a tsaye, yasan ko me xai ce mata baxata basa ba, hakan ya sa ya ja tsaki ya dau bucket din fuska daure ya fice dakin, yana gama shanyawa a nan parlorn ya ajiye mata Bucket din yace "Bani wayana in wuce" ta jefa masa makullin siff dinta tace "Ka bude ka dauka ka rufe min kayana" daukan makullin yyi ya koma daki ya bude yana daukan wayarsa da car key ya bar mata siff din a wangale ya fice kamar xai tashi sama, inna tace "Oho dai....." Dab da Magrib Ammi ta shiga tada Imaan dake ta bacci tun bayan da ta kara shan magani, Ammi tace "Ya jikin?" A hankali tace "Da sauki, Ammi Daddy ya dawo?" Ammi tace "Ehh ya dawo" wara ido tayi ta sakko kan gado ta sa Hijab har ta isa kofa ta tsaya ta juyo tace "Ammi hope bak'in duk sun tafi?" Ammi tace "Ina kuwa xa su gobe biki?" Imaan tace "Toh daddy yana bedroom dinsa ne?" Ammi tace "Aa ina jin suna can tare da Abba" Imaan na sa takalminta bakin kofa aka bude kofar parlon, d'aga kai tayi taga Inna ce, Inna tace "Ya jikin, na ji shiru tun daxu baki leko ba shine nace bari in lallabo in xo in duba ki, kun je asibitin ne?" Imaan da ta hade rai ta ki kallonta tace "Ni na ji sauki" inna ta amsa gaisuwar masu gaisheta a parlon sannan ta kalli Imaan tace "Tohhh, Allah dai ya sauwake, amma wannan wahala ba gwara Bukar ya aurar da ke ba kowa ma ya huta kema ki huta" Ammi dake tsaye tana jin su ita ma ta gaida inna, inna tace "Lafiya lau Aisha, in ji mai gidan ya dawo lafiya?" Ammi tace "Alhmdllh" Inna tace "Toh da kyau, duk da dai ni ko tsinke ba a kawo min a tsarabar da yake yowa, sai dai ke da yar ki ku cinye, to duk ba wannan ba don bai dameni ba wanda Ahmadu ma ke bani Allah ya amfana, yanxu dai xuwa nayi in duba jikin Imaan, ta xo daxu tana ciwon mara ban kai ga jik'a mata ararra6i ba na nemeta na rasa" Ammi tace "Ta ji sauki yanxu, sai dai ko ta bi ki ta amsa ta sha a can" inna ta gwalo ido da sauri tace "Ta bi ni ina? A'a ta xauna xan lallaba in koma in jiko mata in kawo yanxu, ta bi ni kuma ana xaune kalau? Taje ta min me kuma ban da abun ki Aisha yarinya na fama da kanta, Aa bari inje in dawo yanxu, dama na bar sauran tsoffin da basu tafi ba kada a min barna" daga haka ta juya ta bar bakin kofa murya can kasa tace "Haka kawai ta sake koma min ta min wani aika aikan da kazantar ta a gida ta cuce ni, wa gareni da xai bi min hakkina ban da Allah" Imaan ta turo baki ta fita parlorn ko da wasa bata fadi ma Ammi abinda ya faru daxu ba, part din su Maimoon ta nufa, kasa shiga parlon tayi ganin mutane a ciki, ta fi minti biyar tsaye bakin kofar taji muryar Yusuf yace "Me kike yi nan Imaan" kallonsa tayi tace "Toh akwai mutane a parlon ta ya xan shiga" tana magana tana kallon Mujaheed da ya wani hade rai don tare da Yusuf suke, dauke kai tayi bata son tayi dariya, can ta turo baki ta bar bakin kofar ya shiga ciki, Yusuf yace "Toh ko in maki jagora?" Dariya tayi tace "Daddy na yana parlon Abba?" Yusuf yace "Eh mana" tace "Toh oya ka shiga gaba sai in bi ka a baya" a haka suka shiga parlon tana boyewa a bayansa wanda hakan yasa few kawayen Umma dake parlon suka dinga kallonta har suka shiga parlon Abba. Da gudu ta tafi ta rungume daddy tace "Daddy sannu da dawowa" Daddy yace "Baki gaida Abba ba" kallon Abba dake kallonta tayi, ta boye fuskarta tace "Ina yini abba" yyi murmushi yace "Lafiya lau daughter" Daddy yace "Toh baki gaida yayanki ba shi ma" ta kalli Mujaheed dake parlon tace "Ai mun hadu a waje" Daddy yace "Toh maa sha Allah" Tace "Daddy baxan je gombe Hutu ba tunda mun yi holiday?" Abba yace "Wajen wa a gombe" murmushi Daddy yayi yace "Kanwar mamarta" Abba yace "Ohk If I recalled well last holiday ma can kika je ko" Kai ta gyada masa, Abba yace "Kuma babu canji, ga gwaggon ku Suleja ma ba sai ki je can ba ko da su Maimoon, dama bata da lafiya" Daddy yace "Gaskiya ne ya kamata" Imaan ta xaro ido tace "Kauye?" Abba yace "Of course, you will have more experience.... Shi kauyen ba wuri bane" Ta dauke kai bata ce komai ba ta cinno baki gaba, Abba yace "Nasan inna xata ji dadi idan taji xa ku je, kinga sae Mujaheed ya kai ku a mota tunda ya sha xuwa tare da mu" Da sauri Mujaheed ya kallesa yace "Abba... ai ba lalle xan gane wajen ba fa" Abba ya kallesa yace "Last time ma ba kai ka kai mu a mota ba" da kyar yace "Abba kusan shekara daya fa" mikewa Imaan tayi ba tare da ta kallesu ba tace "Xan je ina taya Ammi aiki" bata jira cewarsa ba ta fice, Abba yayi dariya yace "On a serious note dole su je riga suyi hutu bari dai a gama bikin nan lafiya" mikewa Mujaheed yyi yace "Xan je ana kirana can waje" daga haka ya fice a parlon, Daddy ya gyada kai yana murmushi yace "Su masu wayo wai, gaskiya ne ya kamata su kai ma Hansatu ziyara tunda gashi bata samu xuwa biki ba ba lafiya" Abba yace "In sha Allah I will see to that on Tuesday if everything is settled" Daddy yace "Alhmdllh, Allah ya kai mu lafiya" Washegari Friday bayan an sakko juma'ah aka daura auren Seeyama da angonta Abdul, throughout shagalgulan da ake a gidan imaan na dakinta tana bacci ko ankon bikin bata sa ba, Ammi bata takurata ta shiga jama'a ba sanin cewar bata wani jin dadi, kuma dama bata son tayi stressing kanta ta jogana masu wani ciwon, sai dab da xa a tafi da Amarya Ammi ta tasheta don tun daxu Inna ke cigiyarta, sai a sannan imaan ta shiga bayi tayi wanka ta wanke baki ta fito ta shirya cikin daya daga ankon da suka yi, ta d'an shafa powder tasa eye pencil da chappette, sannan ta dau farin hijab har kasa ta saka ta dau wayarta, ganin missed call ta tsaya ta duba, Sadeeq ne ya kirata, komawa tayi ta xauna tayi dialing, katsewa yyi ya kirata, bayan sun gaisa yace "Ina kika shiga yau" tayi murmushi tace "Bacci" yace "Uhm baki da damuwa, ya su mama?" Tace "Alhmdllh" yace "Daxu Mariya tace min kuna biki gidanku" tace "Ehh haka ne" yace "Shine ba gayyata?" Tace "Uhmm" yace "Toh kin kyauta" a hankali tace "Kayi hakuri, next time" yace "Toh waye next din auren? Ko ke?" Ta xaro ido sai kuma tayi dariya tace "Ni kuma, yar yarinya da ni" yace "Haba?" Tace "Ehh mana" yace "How old are you?" Ta langwabar da kai tace "Na kusa 19 soon" dariya yayi yace "Ehh gaskiya ne, ke yarinya ce sosai ma" tace "Toh kaga" yace "Ko aure aka maki yanxu ma baxa ki haihu ba ai" ta xaro ido sai dai bata ce komai ba tayi murmushi, yace "Yeahh" tace "Xa mu je raka Aunt dina dakinta yanxu" yace "Wani anguwa ne?" Tace "Ban sani ba dai" yace "Toh idan kun je gidan ki kirani" tace "Toh in sha Allah" sallama yayi mata ya katse wayar. Inna ce tsaye tsakar gida ta cakare cikin atamfa England an mata dinkin su irin na tsoffi, ga katon gyalenta ta yafa, ga mutane duk ana ta shirin xa a wuce da seeyama gidanta, motocin dake compound din sun fi shidda duk na daukan yan kai amarya, tun daga nisa Imaan ke jiyo Inna ta tana cewa "Naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, duk an wani yi cirko cirko a gaban motoci ku ja baya mana kar ku gurje masu dukiya in shiga uku, ni wllh saboda bala'in mata ma duk xafi ya isheni abu kamar maita dai, ke Maimuna ba ca nayi ki dubo min Imaan ba ko har yanxu jinin bai dauke ba ne, duk yau ban ganta cikin jama'ah ba ko bakin ciki take ma yar uwartata ban sani ba" Imaan ta turo baki bayan sun hada ido da Innar, inna ta ja tsaki tace "Kai ni dai ko limamin babban masallacin Habuja ne Bukar yau dai baxai hanaki sa gyale ba, duk yan uwanki ga su fess cikin gyale ke ko kin maka hijabi uwa xamu je xaman makoki ba amarya xa mu kai ba haba imaan, ni dai na gaji da maganar ki a gidan nan" Imaan ta dauke kai har ta iso gun motar, wata kawar Umma ce ta xo tayi announcing wai Umma tace wasu su fara tafiya kafin a fito da amarya, nan aka fara kokarin shiga motoci, inna ta bude baki ta gwalo ido ganin wata katuwa cikin shiga ta alfarma da gwalagwalai na kokarin shiga daya daga motocin, cikin daga murya tace "Wayyo meye wannan kuma... Kee don Allah ki bar sirara su shiga, banda neman magana da tsokanar fada ina xa a dake a haka, kisa kike son yi cikin motar fisabillahi, wannan ai sai dai idan ke kadai xa aje a ajiye a dawo to ina kuma hakan xai yiwu tunda motar ba taki bace, fito don Allah mutane su shiga" Imaan ta boye fuskarta da Hijab kar tayi dariya, mutanen wajen wasu sai dariya suke kasa kasa, matar ta fito kamar warce ruwa ya cinye kanta a kasa, inna ta karasa kusa da ita tana kallonta tace "Haba baiwar Allah... ke ba kya tsoron Allah ne wannan abu haka kinyi wani bake bake bayan motar mutane, ina kike son a xuba sauran jama'a, ko ke baki ga irin ki bane" Wata mata ta karaso kusa da Inna tayi kasa da murya tace "Hajiya babban kawar uwar amaryar ce fa" inna ta bude baki tace "Babban kawar uwar amarya kuma sai a sa mata ido ta latse hanjin 'ya yan mutane a bayan mota, dama kisan kai ya kawota ba biki ba, wannan abu kamar giwa kice ta shiga mota, amma bakya tsoron Allah wllh" sum sum matar ta bar wajen, Inna ta ja tsaki tace "Kai sirara su shiga a wuce, ba ruwana a aje a tatse hanjin mutane daga kai amarya ace bikin jikata ga abinda ya faru, to banda gwalagwalan ma duk karya ne ya xa ayi kamar ta ace bata da mota, ke kuma imaan ga motar da xa mu shiga can da Seeyama nace ban son tukin kowa sai na Mujaheed haka kawai mahaukatan abokan angon su ja mu su watsar da mu a rami" Bude motar Imaan tayi ta shiga back seat tana murmushi, Maimoon xata shiga inna tace "Toh ina kuma wancan figaggiyar xata shiga ni patuu, ba ga

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment