Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma ba turo su kake ba balle yaranka, yau da Hurera na da rai xaka mata haka, Allah dai ya mata Rahama ya gafarta mata bata min komai ba, lafiya muka xauna da ita...." Mikewa daddy yyi ya fice a parlon, Inna ta bi sa da kallo tace "Wannan Bukar din dai ba shi da kirki wato ga mahaukaciya na magana shine ya fita, Wai... Ai da Bukar ne ke xaune a kaduna wllh baxan sha ruwa a gidan nan ba, mulkata kawai xai dinga yi da bafillatanar nan da figaggiyar Yar su, Toh sae Allah ya rufa min asiri Ahmadu ne, kwata kwata Ahmadu dama bai son abinda xai ta6a ni a duniyar nan shi da yaransa, kaga inda ya fi Bukar kenan, to meye kuma daga magana dai ta fahimta xai kwashi jiki ya fita" murmushi kawai Abba ke yi da kawu Bala da yyi hamdala a xuciyarsa da ta katse tsigesan da tafara yi ta koma kan daddy, Abba yace "Toh shikenan dai Inna, Allah ya kiyaye hanya sai kun dawo" Inna tace "Toh dama mota daya xa a ware mana da imaan da kawata ta rasulu, tace min tana hanya" Abba ya buda ido da mamaki yana kallonta, kawu bala yace "Toh madallah Allah kawota lafiya" daga haka ya fita Abba ya bi bayansa, Kawu Bala na ta murmushi yace "Ayi ta hakuri Barrister tsufa ne" murmushi kawai Abba yyi yace "Ana ta yi, sai dai Allah ya kara mana hakurin" Kuka umma ta xauna kan gado ta dinga rusawa jin da Inna xa a je kai lefe tana kallon kawayenta tace "Babu abun kirki idan aka tafi da matar nan wllh, xuwa xata yi ta mana tonon asiri, tayi ta sakin xance a gidan"

*The book Imaan isn't free* it's 300
Via

Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence of payment via my WhatsApp digit
07087865788 subscribe and read without been judge by ur conscience.
[7/16, 7:46 AM] +234 807 505 4566: 🌟⭐Imaan⭐🌟

39...


Mujaheed dai na tsaye kitchen sae kallon Umma yake har ta kai aya, jin yyi shiru a fusace tace "Wae ba da Mujaheed nake magana bane??" Ya d'an shafa kai yace "Ina ji Umma, Toh ni ya xan mata, kinsan tunda tace sai taje, ba wanda ya isa hanata xuwa ne" Umma ta hade rai tace "Yanxu baxa ka samo dubara da xaka hana xuwan nata ba, wllh idan taje gidan nan tsaf xata iya sa su fasa baka mata, tun da uwata ta haifeni ban taba ganin mutum sakakka irin tsohuwar nan ba, ni dai duk yanda xa ka yi ka rufa min asiri kayi ka hanata xuwa Marafan nan don Allah, ga ta can bakin motoci tsaye sai nuna hali take" Mujaheed yyi murmushin karfin hali yace "Toh..." Juyawa Umma tayi ta fice daga kitchen din rai bace, Inna dai na tsaye an sha super da mayafi da yar jakarta sae xuba kamshi take, duk mutan wajen dama sun bar jikin motar an bar ta ita kadai barin kawayen Umma, ta aika Maimoon ya fi sau uku ta kira mata Imaan amma shiru, ganin Maimoon ta dawo for the 4th time Inna tace "Yau naga abinda ya isheni ni patuu, Ina Imaan din ta shiga ne wai??" Maimoon tace "Inna ni fa ban ganta ba" Part dinsu Imaan Inna ta nufa fuska daure tana cewa "Ni ai xan ganta idan naje" Daddy ne xaune parlorn yana operating laptop dinsa, ta shigo parlon ko sallama babu tana kallonsa tace "Bukar Ina Imaan ta shiga ne wai, ko bata san duk jama'ah sun taru ita ake jira bane?" Daddy ya kalleta yaci gaba da abinda yake yace "Tana daki...." Inna tace "Kaga walakanci ko, wllh tarbiyar 'yar ka kalilan ne Bukar, ce mata nayi fa ta shirya ta fito mu tafi amma don wlknci ta shanya ni a rana ina ta jiran fitowarta, gafara xata min ne ko menene haka??" Daddy ya kalleta yace "Ku je Ina wai?" A fusace Inna tace "Kai lefen mana, ko gwari nake maka" girgixa kai yayi yace "Don Allah ki bari Inna, me xata je yi gidan... cikin manya kuma, kai lefe dai tun daxu ana ta abu daya ya ki ci yaki cinyewa, Ni nace mata baxa ta je ba don babu sa'anta a masu kai kayan, kema kawai don kince sai kin je ne babu yanda muka iya..." Inna ta saki baki tana kallonsa, can tayi kasa da murya tace "Meye laifina don nace xanje kai kayan jikana da nayi wahala da tun yana tsumma, me yasa baka da fahimta d'an uwanka ya fi ka fahimta Bukar...." Sai kuma ta fara matsar kwalla tace "Toh ai shikenan sai in fasa xuwa a kira ta Rasulu ace tayi xamanta, ai ba aikin Allah bane kai lefen na hakura" Daddy yace "A'a ni bance kar ki je ba tun da kinyi niyya kiyi tafiyar ki amma Imaan baxata je ba gaskiya" Inna tace "A'a su tafi, haka kawai in bata maku rai kan tsinannen lefe, dama ai babu sa'a na a masu kai kayan sai ta Rasulu ita ma xan sa a kirata ince tayi xamanta kawai, ae gaskiya ku ka fada, duk wanda kuma ya rasa mai gaya masa gaskiya a duniya yyi asara, ni dai na hakura da in bata maku rai sbda kayan mutane" Daddy dai bai ce mata komai ba har ta fita, Ammi da har ta gama shiryawa ta fito daga daki tana kallon Daddy tace "Kai me ya kai ka yin haka yallabai, maimakon ka barta tayi tafiyarta tunda ta sa rai" Daddy yace "Gwara ana yi ai ana mata gyara, ba gashi yanxu tace ta fasa ba, Amma komai tace be it right or wrong sae barrister ya biye mata" Ammi dai bata sake cewa komai ba. Inna na xaune parlonta bayan Yan kai lefe sun tafi kai lefen, Umma kam kamar ta xuba ruwa kasa ta sha duk tunaninta Mujaheed ne yyi mata magana ta fasa xuwa farin ciki gunta ba a cewa komai sai murmushi take bayan an tafi kai kayan. Mujaheed ne ya shigo parlon Inna da sallama ta dalilin sawa da Innar tayi a kirasa a waya, ita kadai ce parlon xaune kan kujera fuskarta shabe shabe da hawaye har da majina, Kallonta Mujaheed ya dinga yi da mamaki yace "Mai ya faru kuma?" Ta rushe da sabon kuka tace "Babu abinda Bukar ya mance bai gaya min ba Mujaheed wai daga nace xan je kai kayanka don Allah ya albarkaci kayan, shine ya tsitstsige ni ya gaggaya min ba dadi, yayi ta min bala'i kamar xai ari baki wai xan je cikin yara tsofe tsofe da ni, inda Bukar yake shiga ba nan yake fita ba, yayi min tatasss...." Wani kukan ta kara fashewa da, Mujaheed ya xauna yana murmushi yace "Shine kike kuka?" Cikin rawar murya tace "Baxan yi kuka ba Mujaheed, Bukar ya lalace, yau har nuna min yayi bani da iko da figaggiyar 'yar nan tasa mai ciwace ciwace iri iri kamar warce ta kashe d'an mutum, Ni dai ba Ruwana ba haka Bukar dina yake ba da, duk Aisha ta lalata sa da halinsu na fulani, ta sa ya xama jarababbe ya xama fitinanne, ga bakar xuciya.... Ni dai ban tanka sa ba nayi shiru Ina ta kallonsa don gani nayi abun ba na lafiya bane, Ni Ahmadu baya min haka komai nace sai dai yace min to, kwata kwata bai son bacin raina, Bukar dai ya lalace kuma ni ba ruwana da shi da 'yar sa.... su je can su karata idan Bala ma xai tafi ni bin sa xan yi kawai, duk kwana biyu sai in dinga kiran Ahmadu muna gaisawa" Murmushi kawai Mujaheed yake yace "Kece fa baki fahimci daddy ba ba fada yake maki ba kawai dai gyara ne" Inna ta daga hannu sama tace "A'a wllh fada ya dinga min kamar xai ari baki, ni ba ruwana kar ka xo nan ka karesa.... lalacewa ne dai ta riga ta samesa, har ni xai bude baki yace ma babu inda yar sa xata bi ni" Sai kuma ta fara kuka tace "A karkashin akwati fa na fiddo kayan nan ko sa su ban taba yi ba gashi yanxu babu inda naje sai na wanke su kar su yi warin jiki, kasan mutum ba komai bane facce datti" Mujaheed ya tabe baki yace "Kiran kenan?" Tace "Eh wllh, na rasa wanda xan gaya ma ne na kira ka, gashi har naji sanyi, to wa gareni dama banda Allah sai kai din, sai kuma Ahmadu" mikewa yayi yace "Toh ki shirya sai in kai ki gidan nawa ki gani...." Tace "Gidan da xa mu xauna?" Ta gefen ido ya kalleta bai tanka ta ba ya fita tace "Toh ai kawai bari in fito tunda ban tu6e kayan ba...." Mujaheed na isa part din su Imaan ya shiga da sallama, har sannan Daddy na parlorn a xaune, ya xauna saman kujera ya gaishesa with respect, daddy ya amsa da murmushi yace "Ya gajiya" murmushi kawai Mujaheed yyi yace "Abba dama wai Inna ce..." Sai kuma yyi shiru yayi yar dariya yana kallon daddy, daddy yace "Kiran ka tayi kenan" Kai ya gyada masa, Daddy ya girgixa kai bai ce komai ba, nan Mujaheed ya fada masa duk yanda suka yi da ita, daddy murmushi kawai yake yace "Dama xan je yanxu in sameta" Mujaheed yace "Amma kuma xan fita da ita xuwa can gidan ta gani, xaka sameta yanxu ko sai mun dawo?" Daddy yace "Toh shikenan ku tafi kawai, anjima xan je idan kun dawo, Ku tafi tare da imaan din..." Mujaheed yace "Toh" Daddy ya kira Imaan dake dakinta, fitowa tayi parlor, ganin Mujaheed ta xaro ido ta koma da sauri ta dauko Hijab dinta tasa, shi dai Mujaheed dauke kansa kawai yyi, Bayan ta sake fitowa daddy yace "Ki shirya xa ku fita tare da Inna yanxu" a hankali tace "Toh" daga haka ta juya ta koma daki, Mujaheed ya mike yace "Toh sai mun dawo Abba" Daddy yace "Toh Allah ya tsare, thank you son" murmushi kawai yyi ya fita parlon. Back seat ya bude ma Inna ta shiga tana cewa "Allah dai ya shiryi Bukar, Ni dai inaga bakin cikin 'yar kazar da xa a ban in ci a can yake min, to ni kuwa wani irin nama ne ban ci ba a rayuwar nan, ni wllh ya ma fara bani tsoro, sam ba haka yake ba da, yasan wahalan da nayi da shi yana karami kuwa, kamar fa baxai yi rai ba mayu suka kama min shi, kasan lkcn yana da kyau tsantsaa ga shiga rai yanda dai kaga wannan figaggiyar yar tasa da ya haifa, haka nayi ta wahala in gaya maka Mujaheed, Ni ce can nice nan cikin kishiyoyi gantalallu lkcn Ahmadu na da shekara hudu shi kuma ba shi da aiki sai shegen kiriniya yyi ta kwaso min kayan bola...." Rufe motar Mujaheed yyi bayan ta shiga ya juya suka yi ido hudu da imaan dake tahowa sanye da hijab dinta har kasa hannunta rike da wayarta.... Ya dauke kai ya xaga ya bude driver seat ya shiga, Imaan ta bude back seat xata shiga ya juya ya jefa mata wani mugun kallo yace "Do I look like ur driver?" Turo baki tayi bata shiga ba kuma bata ce komai ba, Inna tace "Oh oh Allah, kaga jaraba ko Mujaheed, yanxu wa ya gayyatota nan, ba Uban cewa yayi kar ta bi ni ba, meye kuma ta wani xo mana nan salalo salalo" Imaan ta hade rai tana kallonta, Inna tace "Ni dai ba ruwana, ki shiga gaba ki xauna tunda ubanki ba son tarayyar mu yake ba, ni ki daina ma xuwa min sashina nunawa yake a fakaice wai ina koya maki bakin hali" Imaan taji kamar ta juya ta koma bangarensu amma sanin Daddy na parlor kuma kafin ta fito ta ce masa ita baxata bi su ba yayi insisting sai taje, tasan tana komawa yanxu fada xai mata yace ta koma, haka nan babu yanda ta iya ta shiga front seat din fuskarta a daure. Tafiyar kusan minti ashirin suka yi xuwa gidan Mujaheed dake Unguwan sarki, throughout journey din Inna bata yi shiru ba, Daga Mujaheed har Imaan babu mai ce mata komai, wayarta dake hannunta ya fara vibrate ta kalla taga Sadeeq ke kiranta, silencing wayar tayi gaba daya ta saci kallon Mujaheed suka hada ido don shi ma kallon nata yake a sace, da sauri ta dauke kai bata sake kallon gefenta ba, Mai gadin gidan ne ya bude gate ya shiga ciki da motar yyi parking a space din mota uku dake cikin babban compound din da ya kawatu da shuke shuke masu kyau da daukar hankali, Kashe motar yyi ya fito, Inna ma ta bude motar ta fito tana kallon babban duplex din tace "Lahhh, toh ai wannan ya ma fi na ubanka kyau da haduwa, kasan lkcn da ka kawoni ba a gama ginin gidan ba duk sai na raina gidan...." Imaan ta bude motar ta fito fuska daure, Inna na kallonta tana washe baki tace "Kema dai Allah yasa wanda Bulasawa xai saka ki ya fi wannan komai da komai...." Tana fadin haka ta bi bayan Mujaheed da ya nufi main entrance din gidan, imaan ta bi bayansu tana tabe baki, da makulli ya bude kofar shiga gidan inna ta riga sa shiga tana rafka uban sallama, the parlor was well furnished, babu abinda babu a ciki na xamani, Inna ta rike ha6a tana kallon Mujaheed tace "Mujaheed duk kai ka xuba wa enannan kayan a parlon nan, kar fa kaje bashi ya hau kanka mu shiga uku..." Bai tanka ta ba ya wuce sama ta bi bayansa da sauri, imaan ta kyabe baki ta dinga bin hadadden parlon da kallo, wani kofa da ta gani a parlon ta bude ta ga daki ne babba da bathroom a ciki, ta kara bude wani taga makeken well furnished kitchen sai dai babu kaya a ciki, ta karasa cikin kitchen din ta bude wani kofa dake ciki taga store ne na ajiye kayan abinci, sai kuma wani kofa da xai yi leading dinka xuwa bayan gidan, rufe store din tayi ta fito ta rufe kitchen din ma sannan ta wuce sama, dakuna hudu ne a jere amma da distance mai d'an dama tsakaninsu, sannan corridor din na da fadi da tsayi sosai, wani kofa ta bude taga daki ne da bathroom a ciki, babu komai dakin sai Ac da curtains sai fitilu, ta rufe ta bude wani taga irin wancan ne, kin bude Wanda taga alamar suna ciki tayi don muryar Inna kamar speaker a dakin, ta bude last door din dake corridor din, well furnished parlor madaidaici ta gani ta shiga tana kare ma hadadden parlon kallo, can ta bude wani kofa da ta gani a parlon taga bedroom ne, shiga ciki tayi ta rufe kofar tana kalle kalle ta karasa ta bude wani kofar taga bathroom babba, ta d'an tabe baki ta juya ta nufi kofa ta bude suka ci karo da Mujaheed, juya masa baya tayi da sauri tana xaro ido, taji kamar ta nutse a wajen, jin yana sa makulli a kofar ta juyo da sauri tana kallonsa....


*Imaan isn't for free* it's 300 viaJa baya Imaan ta dinga yi ganin kallon da yake mata fuskarsa a daure, ta 6ata fuska kamar xata yi kuka, a hankali tace "Yaya fita fa xan yi...." Bai tanka ta ba kuma bai fasa bin ta ba tana komawa baya, ganin kiris ya rage ya risketa ta koma can kusa da window din dakin ta tsaya xuciyarta na bugawa tace "Wayyo ni dai ka kyaleni in fita, me na maka" dab da ita ya tsaya, xata durkusa ya dago ta yace "Training da Ammi ta maki kenan na ba ma namiji hannun ki yayi kissing a bakin mota kina washe baki koh?" Ta wani xaro ido tana kallonsa, tsawa ya mata yace "Baxa ki bani amsa ba sai na baki dirty slap?" Tsorata tayi ganin babu wasa fuskarsa, kamar xata fashe masa da kuka tace "Ni fa Yaya...." Fixgota yayi lkci daya idanuwansa suka canxa yace "Ke fa me?" Kasa cewa komai tayi, ta hadiye abu da kyar tace "Don Allah kayi hakuri, ni bani na basa hannun...." Bai jira ta karasa ba ya buge mata baki da karfi, Ta kai hannunta da sauri bakinta, lkci daya hawaye ya kawo idanuwanta, cikin husky voice yace "I am making you this promise... babu abinda xai hanani gaya ma Abban ki sooner or later...." ta wani gwalo ido a rikice tace "Don Allah Yaya kayi hakuri wllh ba da gangan yayi ba shi ma bai sani ba" Bai san lkcn da ya kara buge bakinta ba, tayi tsit hawaye na sauka idonta, yace "Wato ke yanxu kina ganin kin girma kin isa tadi da maxa, har wani rawan jiki kike ki fita idan ya xo, har da jan sa xuwa parlon ku ki ajiye masa nama a gaba Saboda kinga Inna na goya maki baya, to bari ki ji abinda baki sani ba, as far as I Muhammad is concerned babu aure tsakanin ki da mutumin nan, you had better stop wasting ur time and face ur study, kamar yanda na xa6a ma Seeyama miji ke ma haka da kai na xan xaba maki mijin da ya dace da ke, duk ki gama rawan kanki xaki sha mamaki na, wannan mutumin da kike gani is just here to spoil and use you, ba so na tsakani da Allah yake maki ba, ki bar ganin yana kashe maki kudi ki xata wai son Allah yake maki, lalata maki rayuwa xai yi which I will neva allow, and let me give you this warning....." Ita dai hawaye kawai take xuciyarta na bugawa tana kallonsa, "Daga yau kika sake tsayawa kusa da motarsa sai na kusa sumar da ke wllh, duk karyar da xai maki ya maki a waya ba sai ya sake xuwa kofar gida ba, idan kuwa ba haka ba a gaban daddyn ki xan xane ki sai dai duk abinda Inna xata yi tayi..." Kuka kawai imaan take bata ce masa komai ba, strictly yace "Am I clear?" Ta gyada masa kai da sauri, muryar Inna suka ji tana cewa "Naga abinda ya isheni ni patuu na 6ata a gidan Mujaheed" sai kuma ta kwalo masa kira, bude kofar Mujaheed yyi ya fita ya jawo kofar, Imaan ta durkushe a dakin tana kuka a hankali, Inna na ganin Mujaheed tace "Alhmdllh, ni na xata 6ata nayi, Toh ita kuma matar ina ta shiga, har kasa fa na sauka ban ganta ba, kada ta shiga wani waje in shiga uku dama ga Bukar ya xama abun tsoro, ba da xuciya daya ya yarda ta biyo mu ba" Mujaheed yace "Tana waje, muje ki ga dakin dake kasa" Inna tace "Na waye dakin?" Yace "Baki" inna tace "Irin su Hansai da 'ya yanta knn idan sun xo" murmushi yyi ya bude kofar parlon yace "Har ke ai" Bai jira cewarta ba ya fice. Har garden sai da Mujaheed ya kai Inna ya xaga duk gidan da ita, tana kallonsa tace "Toh ai tun yanxu ya kamata mu shiga gun makota a san juna kafin mu tare, ko ya kaga?" Kallonta yyi ya dauke kai, tace "A'a ba xancen dauke kai ba yana da kyau in san su su san ni, ko haka mutum xai ta xama ba jama'ah a gida, ai mutane Rahama ne" Mujaheed yace "Sai ki jira idan kin ga dawowarki gidan" Inna tace "Wannan gaskiya ne, to ni na shiga uku ban fa yi la'asar ba Mujaheed" yace "Toh mu je ciki kiyi" parlon suka koma ya nuna mata dakin dake downstairs yace "Sai kiyi alwala a bayin ciki kiyi sllhn" tace "Toh dakin su Hansai kenan" shi dai bai ce mata komai ba ta wuce ciki, kallon agogo yyi sannan ya wuce sama, parlonsa ya shiga ya bude kofar dakin, durkushe ya ganta inda ya bar ta har sannan tana kuka, tana ganinsa ta mike tsaye, karasawa cikin dakin yyi, ta hadiye kukan da take ta sunkuyar da kanta, takawa yayi har gabanta ya tsaya ta ki yarda ta daga kai balle ta kallesa, ya dago kanta a hankali, ta kallesa sai kuma ta fashe da kuka ta juya masa baya, xagawa yayi gabanta ta rufe fuskarta tana shessheka, d'an murmushi yyi, kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "ki dinga jin magana ta idan baki son na dinga sa ki kuka" ta kara juya masa baya cikin kuka tace "Ni bana soo" xagawa ya kara yi gabanta ya jawo ta kusa da shi, ta kuma fashewa da kuka, ya d'an hade rai yace "Toh baxa ki yi shiru ba" kin cewa komai tayi, ya ja ta xuwa bathroom, ruwa ya bude yana kallonta ta madubi a hankali yace "Wash ur face now" ta turo baki ta ki cewa komai, tara hannunsa yayi ya debi ruwan ya dukar da ita ya shiga wanke mata fuskar, yana gamawa ya ciro handkerchief dake aljihunsa ya fara goge mata ruwan fuskar, yana kallonta ta madubi yace "Promise me xaki fara jin magana ta daga yanxu...." Kin cewa komai tayi ya hade rai yace "I am talking to you" da kyar tace "Na ji" yace "Kin ji me?" A hankali tace "Abinda ka ce" mayar da handkerchief din yyi aljihunsa ya juya ya fita bathroom din, murguda baki tayi ta juya tana kallon kofar bayin. Parlor Mujaheed ya xauna yana danna wayarsa har Inna ta fito dakin da ta shiga yin sllh, tace "Wai Mujaheed ni fa ban ji motsin Imaan ba.... A rufa min asiri mu dubota" Mujaheed yace "Tana sama ai" Inna tace "Toh ni dai mu je in ganta" bata jira cewarsa ba ta nufi stairs ya mike ya bi bayanta, dakinsa ya shiga da ita suka ganta tsaye jikin window waya kare a kunnenta, tana jin an bude kofa tayi saurin dauke wayar daga kunnenta tayi tsuru tsuru, kallonta Mujaheed ya dinga yi, Inna tace "Toh ke daga ganin gida sai ki shige dakin matar mutane ki xauna, jira xa ki yi Allah ya kawo lkcn naki da Bulasawa ae" Juyawa Mujaheed yyi ya bar bakin kofar, Inna tace "Toh fito masu a daki yi hakuri haka" imaan bata tanka ta ba ta nufi kofa gabanta na faduwa ta fita, Inna ta bi bayanta, balcony suka tadda Mujaheed suna fitowa ya kulle gidan da makulli ya tafi gun motarsa, imaan bata yrda ta kallesa ba ta bude front seat ta shiga kamar munafuka Bayan Inna ta shiga baya, ya ja motar ya fita compound din yyi ma Mai gadi sallama. Suna hawa saman titi Inna tace "Ni dai Mujaheed da dai in samu kaza in siya, naji raina na so sosai" Mujaheed yayi parking dai dai gun masu gashin kazan da ta gani ya sa tayi magana, tana washe baki tace "Allah dai ya maka albarka" Bai ce komai ba sai ma jinginar da kai da yayi da kujeran motar ya lumshe ido, Inna tace "Toh ko ta fita ta amso?" Ba tare da ya bude idon ba yace "Ehh" inna tace "Toh guda nawa?" Jin bai ce komai ba Inna ta gyara xama tace "Ko guda uku ai yyi, Ni daya ita daya, yan sa ido kuma sai in kacalcala masu daya" Mujaheed yace "Ohkk" Inna tace "Yi maxa ki sauka imaan, kice masu su xabo manya don Allah na tsohuwa ce kuma ba miji gareni ba" Imaan ta bata fuska ta juya tana kallon Inna, inna tace "Naga Ikon Allah, ko in sauka da kaina ne? Me mutanen xa su maki ko ina ruwanki da su" bude motar Imaan tayi ta fita ta tafi gun masu gashin, Mujaheed ya bude ido ya bi ta da kallo daga cikin motar, ba laifi akwai maxa a gun, imaan na sunkuyar da kai ta amsa tambayar da masu wajen ke mata tace "Guda uku" tana ta tsaye har aka gama packaging kajin a leda

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment