Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace "Kinga walakanci ko, wannan wace irin yarinya ce don Allah, ta san daga inda maganin nan ya fito?" Imaan tace "Ni nace maki na sha magani fa a gida, ya xa ayi in hada magani iri biyu" Inna ta ajiye spoon dina hannunta tayi tagumi tace "Oh waannan 'ya ta Bukar dai jarababbiya ce wllh, Toh meye da maganin da baxata sha ba? Ba daci, ba 6auri, ba hamami, ba galmi sai ma gyara mata bakin ta da xai yi, ta ji dadi kuma a jikinta, to ni dai ba ruwana gashi can uwar ki da ubanki sun fara laka maki ciwon da ba a san ki da shi ba ba a san kansa ba, wai dama idan lkcn gabatar da yaro ya kusa ba duk iccen da aka jika ma yaron aka basa sai ya amsa ya sha ba sbda a kauda ikon makiya, Ni dai ba ruwana Ina taimakon ki kina min wlknci, idan ta uwarki ce sai dai fa ki mutu ba abinda xata maki, shi kuma Bukar na can na neman na abinci a Habuja, to wa gare ki banda Allah sai ni din, to ni ba ruwana, ki tashi ki amshi maganin nan ki sha ni ba asararriya bace, uwata bata ce min jeki kya gani ba da xan dinga maki bauta baki gani, ko ubanki bai samu haka a guna ba" Maimoon ta ajiye cup din hannunta ganin imaan ta ki amsa tace "Inna ni dai xan je inci abinci" Inna tace "Toh idan kin gama ki dawo kema ga naku da su fitsararrun can Ummi, ba dai don halinsu ba, ya xanyi tunda ni na haifi Ahmadun" Maimoon dai bata ce komai ba xata fita sai ga Mujaheed ya shigo parlon, gaishesa Maimoon tayi ta fita, Inna tace "Mujaheed waya dai ko sama ko kasa, an dai rasa wanda ya sace, ni na ma fi xaton hauro kantangar aka yi, ai daga yanxu ni kaca ma xan dinga sawa in rufe kofar da kwado idan xan fita, Ina dalili? Ai ko ya daukan ma kansa fitinar duniya" Mujaheed ya gaisheta sannan yace "Za a xo daukan akwatunan nan" Inna ta kallesa sannan tace "Ita da ta turo ka ba sai ta xo ta kwasa ba in ga, Rukayya dai tayi hankali da ni ba ruwana.... Wannan yarinya kuma kayi mata magana ta rufa min asiri ta dau nonon nan ta sha ba sato kudin nake yi ba, dubu goma kenan cikin kofin a kwance ta rasulu ta sa aka amso min" Mujaheed bai ko kalli imaan ba yace "Kaya xa a karasa xubawa cikin akwatunan shi sa xa a dauka" Inna tace "Sai kuma ka yi ai, ko Ahmadu bai isa yace xa a dau akwatunan nan ba balle kai" Kallonta ya dinga yi fuska daure, can ya juya ya fita. Washegari da safe Mujaheed ya shigo parlon Abba da sallama ta dalilin kiransa da yayi a waya, Abba na kallonsa yace "Jikin Imaan ya matsanta mata, yanxu Hajiya Aisha ta kirani..." Mujaheed yace "Toh a tafi asibiti kawai" Abba yace "Toh xa ka kai ta ne?" Girgixa kai yyi yace "Zaria xan tafi Abba, kuma likitan ta na gari ai" kallonsa kawai Abba yayi bai ce komai ba, Mujaheed yace "Xan je in shirya yanxu" Abba yace "Ohk then" Juyawa yayi ya fita parlon. Sai kusan la'asar Ammi da Aunty suka dawo asibiti da Imaan, nan parlor Imaan ta kwanta Ammi ta shiga kitchen don girka mata light food ta ci, Imaan ta jawo wayar Ammi dake vibrate kusa da ita ta kalli screen din, Sadeeq ta ga ke kira, sai da ya kusa katsewa ta daga da kyar ta kai kunne tayi masa sallama, ya amsa yace "Kun dawo gida ne?" Tace "Um..." yace "Ohk before magrib xan kawo maki drug din, but I have to see wanda aka baki a asibiti" tace "Toh" yace "Allah ya kara lafiya" a hankali tace "Ameen" yace "Do you need anything" tace "A'a" yace "Sure?" Ta gyada kai kamar yana ganinta, yace "Ohk sai na xo" daga haka ya katse wayar. Karfe shidda saura Yusuf ya shigo parlon da sallama, Imaan na xaune bayan tayi wanka ta shirya tana cin farfesun kayan ciki da Ammi ta mata, xaunawa yyi ya sakar mata murmushi yace "Sannu, ya jikin?" Ta mayar masa murmushin tace "Da sauki ya Yusuf" yace "Toh Allah ya kara lafiya, Ammi fa?" Imaan tace "Ta shiga daki" Yace "Ohk, me xa a kawo maki na marasa lafiya" ta kallesa ta marairaice tace "Kawai awara nake son ci" ya d'an buda ido yace "Awara?" Ta gyada masa kai a hankali, yyi murmushi yace "Toh bari a nemo maki" mikewa yayi yace "Anjima xan taho maki da shi, ki gaida Ammi idan ta fito" tace "Toh" daga haka ya nufi kofa ya fita, ko minti biyar ba ayi da fitansa ba sai ga kiran Sadeeq, sanar mata yyi yana waje tace "Toh ka shigo" Sadeeq ya d'an buda ido yace "Ni fa Ina jin kunyar Ammi" Murmushi tayi tace "Ae tana daki" Yace "Uhn toh gani nan shigowa" ajiye wayar tayi bayan ta katse, ta mike ta wuce dakin Ammi ta sanar mata Sadeeq xai shigo, Ammi tace "Toh haka xaki tsaya babu hijab" ta girgixa kai tace "A'a xan dauko a daki yanxu" Ammi tace "Ohk" daga haka Imaan ta fita ta shiga dakinta ta dauko hijab ta sa ta dawo ta xauna xata rufe farfesun gabanta yayi sallama bakin kofa, ta kalli kofar ta amsa sallaman sa, ya shigo parlon, sunkuyar da kanta tayi ya xauna saman kujera ya ajiye ledan hannunsa a kasa yana kallonta yace "Sannu Imaan, ya jikin?" d'an murmushi tayi tace "Ina yini" yace "Lafiya lau, Ina drugs din da suka baki a asibiti" mikewa tayi ta nufi daki ya bi ta da ido, ta dawo rike da ledan drugs din, ajiye masa tayi a kusa da shi, sannan ta koma ta xauna, yayi murmushi ya dau ledan ya fiddo Magungunan yana dubawa, can ya mayar da su, ya dau karamin ledan da ya shigo da ya ciro drugs biyu yace "You can take this also ba komai, na rubuta prescription din a jiki" ta gyada masa kai ya ajiye maganin, ya ciro wani na tube yace "Wannan ma ki dinga shafawa a duk inda kike jin pain" Imaan tace "Toh..." Ya d'an bude ido murya can kasa yace "Ko in shafa maki dear?" Xaro ido tayi ta kallesa sai kuma ta boye fuskarta a kujera, murmushi kawai yake yana kallonta, ganin ta ki dagowa yace "Toh baki cinye pepper soup dinki ba" a hankali ta dago tace "Ko xaka ci ne?" Yayi murmushi yana shafa beard dinsa yace "Ai baki bani ba" daukan bowl din tayi ta kai gabansa ta ajiye, ya xaro ido yace "I am only joking" tace "Ae sai ka ci" yace "Plss ki dauke, wllh wasa nake maki I am okay" ta make kafada tace "Ai kace ban baka ba to gashi ynxu na baka" ya wani xaro ido yace "Kar Ammi ta fito ki dauka plss" cike da shagwaba tace "Sai ka ci" yace "Ohk ohk idan na ci xaki dauke" tana murmushi tace "Ehh" yace "Toh dago min" daukan bowl din tayi ta rike da hannu biyu ta durkusa gabansa tana kallonsa har sannan tana murmushi, ya lumshe ido ya bude ya dau spoon din ya dau nama guda daya yayi kamar xai bata a baki ta koma baya da sauri, bakinsa ya kai spoon din ya ci, ta wara ido tana kallonsa, ya lumshe ido yace "It's sweet" dariya ta fara yi kasa kasa tace "Ashe kai ma ka iya kwadayi" da sauri ya bude ido, ta koma ta xauna still tana dariya, murmushi yyi yace "Ai xan rama" ta buda masa hannuwanta tace "Ko dai ka rame" kallonta kawai yake affectionately, ta turo baki tace "Ni dai ka daina kallona haka" dauke idonsa yyi yana murmushi yace "Watarana xaki yi bayanin me yasa xan daina kallonki" bude kofar parlon aka yi duk suka juya, daddy ne ya shigo parlon da jakar laptop dinsa Mujaheed na bayansa rike da traveling bag dinsa, imaan ta wara ido ta mike da sauri tace "Daddy" murmushi ya sakar mata, tana son xuwa ta rungumesa amma ta kasa saboda Sadeeq, ta isa gabansa cike da farin ciki, a hankali tace "Sannu da dawowa Daddy, baka ce min yau xaka dawo ba" Daddy ya shafa kanta yace "I just decided to come back and check on you daughter, how are you feeling now" tace "Da sauki sosai Daddy, har na ci abinci ma" amsan ledan hannunsa tayi, ya karasa parlon yana kallon Sadeeq kamar yanda Mujaheed ma ke kallonsa, Daddy na murmushi yace "Sadeeq" Sadeeq yyi kasa da kai yace "Sannu da dawowa Abba" Daddy yace "Thanks son, ya aiki" Sadeeq yace "Alhmdllh" Daddy yace "Ya Mai jikin?" Sadeeq yace "Alhmdllh she's getting better" Daddy yace "Maa sha Allah" Kallon Mujaheed Sadeeq yayi yace "Barka da yamma...." Mujaheed yace "Thank you" Ajiye jakar hannunsa yayi yana kallon daddy yace "Allah huta gajiya Abba" Daddy yace "Ameen son" imaan dai ko kallonsa bata yi ba kamar yanda shi ma bai ko kalleta ba ya juya ya nufi kofa, Daddy ya wuce bedroom dinsa, mikewa Sadeeq yayi yana kallonta yace "Kin ga kunyar da naji" dariya imaan tayi tace "Kunyar me? Sadeeq na shafa kai a hankali yace "Kunyar Abba mana" Imaan tayi murmushi bata ce komai ba, yace "Ki gaida min da Ammi, let me get going now" a hankali imaan tace "Toh nagode, Allah ya tsare" yace "Ameen dear, Allah ya kara lafiya, and plss kar kiyi wasa da drugs din ki" Ta d'an yi murmushi tace "In sha Allah" yace "Toh baxa ki rakani ba" tace "Toh xan raka ka bakin kofa" yace "Noo bakin mota dai plss my dear" tace "Toh idan na fadi a hanya fa" yace "Sai in daga ki sweet" boye fuskarta tayi ya nufi kofa yana murmushi ta xaro ido tace "Ka manta ledan ka" ba tare da ya juyo ba yace "Na ki dai" shiru tayi tabi sa da ido sannan ta bi bayansa, kamar mai tausayin kasa ta isa kusa da shi don tsaye yyi yana jiranta, a jere suka dinga tafiyar yana kallonta ita ko ta ki yarda ta kallesa, Ni kam nace waow perfect couples they will make... Lol, A dai dai bangarensu Maimoon Umma ta fito ta nufi parking space kana ganinta kasan fita xata yi, Sadeeq ya kalleta yace "Ina yini" tace "Lafiya lau" Imaan tayi kasa da kai a hankali tace "Ina yini?" Banxa Umma tayi mata ta bude back seat xata shiga, Imaan dai bata kalleta ba suka fita tare da Sadeeq, ido hudu tayi da Mujaheed dake xaune gun Mai kiosk dake kusa da gate din su, Dauke kai tayi da sauri, Sadeeq bai ma lura da shi ba, ya isa gun motarsa tana biye da shi, Yana kallonta yace "Keep on greeting her xata amsa wataran, you will loose nothing don kina gaisheta...." murmushi kawai Imaan tayi, ya kafeta da manyan idanuwansa, murya can kasa yace "Plss ki dinga cin abinci da yawa sweet, kin rame fa" ta wara ido tace "A'a ni dai haka nake" kallonta kawai yake bai ce komai ba, ta sunkuyar da kai tana wasa da fingers dinta, underneath his breathe yace "I have always loved you from day 1 imaan..." kasa kallonsa tayi gabanta ya dinga faduwa, kamo hannunta yyi a hankali ya lumshe ido xai kai lips dinsa ta kwace hannun da sauri tana satan kallon inda Mujaheed yake, kallonsu taga yana yi, Sadeeq ya kalli inda ta kalla suka yi ido hudu da Mujaheed, dauke kai yyi a hankali yace "We will talk later dear" daga haka ya shiga motar ta juya ta nufi gate gabanta na faduwa tana satan kallon Mujaheed da ya bi ta da ido fuskarsa dauke da wani expression, rufe gate din tayi tana kara kallonsa sannan ta wuce part din su da sauri. Mujaheed na gama parking ya juya yana kallon ummansa dake Bayan motar sai danna waya take, ta daga kai da sauri tace "Au, har an kawo ashe" bude motar tayi bayan ta ajiye wayar tace "Ka jira ni ba dadewa xan yi ba" yace "Umma aiki nake son wucewa don Allah kar ki dade" tace "Na sani baxan dade ba Mujaheed" daga haka ta fito motar ta shiga gidan Hajiya Balaraba, ita kadai ce babban gidan duk kishiyoyinta dama ta rabasu da gida, Hajiya Balaraba dake parlor xaune tace "Daga Ina haka Hajiya Rukayya" Umma tace "Daga gida Ina son kai ma Hajiya Saude kudin da ta ranta min na ba mutumi, sannan ku dai xauna da shiri sati mai xuwa xa a kai lefe gidansu Safeenah" Hajiya Balaraba tace "Toh Allah dai ya kai mu lafiya, amma ya ku ka kare jiya ina ta son in kira ki ko inje gida in sameki" Umma ta tabe baki tace "ya dai sa in rubuta masa abinda nake so ya faru, na kuma rubuta yace min in sha Allahu an gama, abu ne mai matukar sauki.... Kar ki so ki ga irin farin cikin da nake wllh Hajiya, idan hakan ya faru ae har Aisha ta mutu baxata rabu da ciwon xuciya ba" Hajiya Balaraba ta xaro ido tace "Toh me kika rubuta halan?" Umma ta rike ha6a tace "Cewa yyi kar in gaya ma kowa, ki sha kurumin ki aminiya, komai xai fito fili xa ki gani" Hajiya Balaraba tace "Amma xa su yi auren kuwa" Umma tayi dariya tace "Ehh to yace yaga da auren, amma ban jin abinda xai faru xai sa ayi auren nan... Kinga bari inje na bar Mujaheed yana jirana a waje" sallama tayi mata ta fita tana murmushi.

*imaan isn't free* the subscription is 300 via

Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
[7/16, 7:46 AM] +234 807 505 4566: Imaan na kitchen tana yanka ma Ammi pumpkin leaves ta ji an danna bell, barin ganyen tayi a chopping board ta dauraye hannunta ta fito, bedroom dinta ta shiga ta dauko hijab ta sa sannan ta nufi kofar ta bude, Mariya ta gani tsaye bakin kofar ta xaro ido tace "Mariya Ahmad" Mariya na murmushi tace "Am I not welcm?" Sai a sannan Imaan ta kara ganin mugun kamar da suke da Sadeeq har dimples din, ta kamo hannunta cike da murnar ganinta tace "Sosai ma besty, daga Ina kike haka? Come in plss" Mariya ta shiga parlon tace "Mumy ce ta aiko ni wancan layin dake gaba da naku shine nace let me branch and say hi, ni da yayanmu ne ma" Imaan ta wara ido tace "Wanne?" Mariya tace "Wannan da ya taba maido ki gida da kika xo gidanmu" Dariya kawai Imaan tayi bata ce komai, har yau kuma tana mamakin me yasa Mariya bata ta6a nuna mata ta san suna tare da Sadeeq ba, ko bata sani bane?? She still can't tell, Imaan tace "Toh xauna plss in kawo maki ruwa mana" Mariya ta xaro manyan idanuwanta tace "Ya Sadeeq xai wuce kenan ya bar ni, dama kawai shigowa nayi mu gaisa ai daga gida muke, am okay dear" Imaan tace "Toh shkkn nagode kuma naji dadi" Mariya tace "Mum fa?" Imaan tace "Taje kasuwa tare da mamansu Maimoon" Mariya tace "Toh ki gaishe min ita idan ta dawo, mu je ki rakani, baya son jira wllh" imaan na murmushi tace "Toh shikenan mu tafi in raka ki" a tare suka nufi gate bayan sun fito parlon, Mariya tace "Ya shirin Sauka fa?" Imaan tace "Ina ta yi" Mariya tace "Ae kam gashi lkci sai matsowa yake..." Imaan tayi murmushi bata ce komai ba har suka fita gate, ta dinga kallon lafiyayyen ride dinsa dake parke a waje ba wanda ya saba xuwa da shi wajenta ba, tun da suka fito Sadeeq ke kallonta ta cikin glasses din idonsa ko kiftawa babu, har suka iso kusa da motar ya sauke glass din motar yana kallonta murmushi dauke fuskarsa, imaan ta sunkuyar da kanta tana fidgeting fingers dinta tace "Ina yini?" Cikin cool voice dinsa yace "Lafiya lau" Mariyata kallesa tace "Yaya ka tuna ta? Frnd dita din nan..." Sadeeq yyi murmushi ya girgixa kai yace "Ni kuma sbda mantuwa na yyi yawa kullum sai anyi min introducing dinta koh?" Dariya Mariya tayi tace "Eh mana Yaya frnds dina kullum ba ganesu kake ba sai kace ka manta, to ita ma nasan ka manta ta" Ya shafa kansa yana kallon Imaan har sannan yana murmushin sa mai kyau yace "Ita ai baxan manta ta ba" Imaan dai bata yrda ta kallesa ba, Mariya ta juya ido tace "Toh ya sunanta?" Yar dariyarsa yyi mai kyau yace "Kin fini sanin sunanta ai" Mariya tace "Na kamaka a nan, you are just pretending amma ka mance ta yaya" Sadeeq ya daga kafada yace "Ohk then, let leave it that way, na manta" Mariya tace "Tohm gwara dai" kallon Imaan tayi tace "Bye frnd ki gaida mum idan ta dawo plss" Imaan tace "In sha Allah, nagode da ziyara" Sadeeq ya d'an kalleta yace "Toh kawar Mariya sai anjima" Imaan ta hararesa ta gefen ido ta wuce ciki da sauri, ya bi ta da kallo yana murmushi, Mariya ta rungume hannayenta tace "Hmmm Yaya wannan kallon fa?" Da sauri ya kalli step sis din tasa, sai kuma yyi murmushi yace "Kallon gate din gidan?" Dariya tayi sosai ta xaga ta shiga gaban motar ya tada motar ya bar layin. Mamaki Imaan ta dinga yi na me yasa Sadeeq ke boye ma yan gidansu gashi dai ajinsu daya da Mariya both islamiyya da Schl amma bai gaya mata ba, tabe baki tayi ta cire hijab dinta ta shiga kitchen ta ci gaba da aikin da take. Bayan ta gama duk abinda xata yi bayan la'asar ta wuce part din Inna don su Ammi basu dawo ba har sannan, Mujaheed ta tarar bakin tap yana alwala, tun da ya kalleta sau daya bai sake kallonta ba ya ci gaba da performing ablution dinsa, ta wucesa ta shiga parlon Inna, Inna ta mika mata abun kwashe sharan hannunta wanda ba komai ciki sai few dirt tace "Xubar min wannan a bola, dubi fa parlon kamar ba komai amma ji yanda datti suka cuceni suka makale, kamar na sani nace bari dai in share in gani, ilai kuwa ga shi har da guntun kasa, kila ma wannan mutumin ne ya shigo min da su, sam datti bai da masugunni a parlona gaskiya" amsa imaan tayi ta fita ta kakkabe abun kwashe sharan ta dawo, ta bi Mujaheed da kallo ganin wucewarsa yyi ta shiga parlon, Inna ta shimfida tabarma ta xauna tace "Ke ki ji ya xo min nan ya kwanta salon ya fara wannan xaxxabin nasa a ce a parlon Inna haka ya faru" Imaan ta xauna saman kujera tace "Ba shi da lafiya ne?" Inna tace "Wai daga anje an kai kudin gaisuwa shine har ya fara tunanin rabuwa da ni bai san tare xa mu tare a can gidan nasa ba" Imaan ta xaro ido tace "Shi yace maki haka?" Inna tace "To sai ya fada?? ko bai fada ba nasan hakan ne ma, ke kinsan shakuwar da Mujaheed yyi da ni kuwa? Nima har na fara jin xaxxabin xai rufe ni" Imaan tayi dariya tace "Yaushe aka kai gaisuwan?" Inna tace "Daxu da safe su Ahmadu da Bukar da Bala da abokan Ahmadun suka kai... jibi kuma xa mu je kai lefe ki shirya tare xa mu dake" Imaan ta xaro ido tace "Har da ke?" Inna ta saki baki tana kallonta tace "Oh oh Allah, ban gane har da ni ba, to dama su waye masu kai lefen idan ban da ni... Ni ana bani mamaki wllh haka Ahmadu da Bukar wai bai dace ba inyi xamana a gida, to a kan me? Ni fa nayi wahala da shi Mujaheed din, sannan ba shi da wata kaka da ta wuce ni a duniya, in har baxan je ba dama sai dai iyayen yarinyar so su dau lefen da kansu ba ruwana" Imaan dai bata ce komai ba, Inna ta mike ta shiga daki sai ga ta ta fito rike da wani takarda, tana kallon imaan tace "Duk cikin jikokina kece kadai xan ce tayi abu tayi, da kyar kiyi min musu, sauran kuwa dama baxa su yi ba, to wannan ba wani damu na yayi ba don kansu suke ma, ga wannan wanka xa ki yi da shi ni dama baxan ba su Ummi su xubar min dukiya ba ba ruwana ba sato kudin nake ba, ke kadai ma amsowa" Imaan ta turo baki tace "Meye shi din?" Inna tayi kasa da murya tace "Wllh garin magani ne, sai kamshi ma yake, ko uwarki kada ki gaya ma ba hankali gareta isasshe ba sai ta hanaki amfani da shi, ki xuba a cikin bokitinki ki tara ruwa bakin ki a leko ki yi ki fito kin ji takwarata" Imaan tace "Ni wllh kaikayi xai dinga min a jiki fa" cike da fada Inna tace "Yau naga jaraba sai kace warce xan ba karara? Meye kuma wani kaikaiyi ni patuu? Garin magani ne fa ba wani abu ba" Imaan ta hade rai tace "Toh bana so baxan yi ba" Inna tayi kasa da murya tace "Toh yi hakuri takwara, abinda ma idan kika yi yau kika yi gobe shkkn, wllh dubu goma kenan kar ki ja min asara ba ramin kudi gareni a dakina ba, ba komai sai tarkacen kwallaye da tsoffin akwatuna" imaan ta turo baki ta amsa tace "Toh wai na meye?" Inna tace "Kaikayi koma kan mashekiya" Imaan ta xaro ido tace "Meye hakan?" Inna tace "Duk wanda xai sa maki ido a duniyar nan idonsa xai tsiyaye tass barsa da jakar idon, idan kuma mugun abu xai maki to fa sai dai ya koma kansa ne ni ruwana, babu wanda ya san ta yanda Bukar ya sameki" Murmushi kawai Imaan tayi, Inna tace "Su Maimoon ma ga nasu can na ajiye masu ba don halinsu ba" Imaan tace "Toh" Inna tace "Ni kwana biyu banji Bulasawa ya kirani ba, ko dai lambar ta bace a wayana ne shi sa baya iya kirana" daukar wayar tayi ta mika ma imaan dake dariya tace "Ke duba min, ba halinsa bane rashin kiran duk kwana biyu kya ga ya kirani mun gaisa har in fada masa damuwata" imaan ta gama danne dannenta ta mayar mata wayar tace "Network ne ya dauke sai bayan sati daya xai dawo" Inna ta saki baki tace "Saboda me toh?" Imaan ta mike tace "Ae haka yake yi" daga haka ta fice parlon tace "Na tafi" Inna ta ajiye wayar tace "Toh Allah ya mana tsari da su masu wayan" Ranan Friday da yamma babu yanda Abba da Daddy basu yi da Inna kan cewar tayi hakuri ta bar yan uwan umma, Matan kawu Bala, Ammi da Aunty sai kanwar umma da kawayenta biyu su kai lefe gidansu Safeenah ba inna tace samm bata san xance ba da ita xa a kai kayan, Daddy dake ta kallonta yace "Yawanci ynxu fa iyaye maxa ne ma ke kai kayan ba mata ba Inna, ke me xaki je kiyi cikin yara don Allah" Inna ta masa wani kallo tace "Toh ko a baka kayan ka kai ne Bukar?" Daddy bai ce komai ba, Inna tace "Yau naga jaraba, to wai ina ruwan Bukar a maganan nan fisabilillahi, Wai xanje cikin yara, A'a gyambo ce ni karewar girma, kawai ayi ta laka ma mutum tsufa, ni din nawa nake gaba daya tukunna ma dai, kamar warce dai ta haifi duniya??" kawu Bala yyi kasa da murya yace "Hajiya Inna da dai kiyi hakuri ki bari su kai kawai, ke fa babba ce...." Inna ta dakatar da shi a fusace tace "Kai rabu da ni Balalau, Ina ruwanka?? Ka san da xamana a kaduna ko ka taba xuwa takanas ka gaisheni? Ko gantalallun matan ka

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment