Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jaraba duk sai ta tsiyace su muna nan muna gani, kee duk wanda xata ra6a ma wllh sai ya tsiyace, haka nan kuma xata yi ta xama ba mashinshini.... to ubanwa xai iya da ita ta kassara tattalin arxikinsa, ni fa duk duniya billahil azim bani da makiyiya da ya wuce Aisha, wllh xan iya yin komai don in toxarta ta da yarta, ni ko kishiyata ban jinta yanda nake jin Aisha, kuma yanda tasa aka toxarta ni aka min kishiya sai na toxarta ta ita ma ko ba jima ko ba dade, ina nan dai kan bakana lokaci kawai nake jira" Hajiya Salaha tace "Ae ko kar ki yarda wllh, ki mata fiye da wanda ta maki ma" Umma tace "Yanxu gobe ma akwai inda xa ni tare da magajiya da sai ki fito mu je tare, wani take take na fara gani nake son taka ma abun burki tun wuri" Hajiya Salaha tace "Haba na me kuma?" Umma tace "Ki ji fa don walakanci yanxu sai su yi ta makala ma Mujaheed ita ya kai ta asibiti, ga uban kudaden da xai kashe wanda nasan ko ance xa a basa baxai amsa ba to akan wani dalili? Shi ya dauro mata ciwon? Na samu na rabasa da shegiyar yarinyar suna kara lika masa ita to gwara in kara xage damtse, ba wani ke nemo masa kudin ba kuma kudinsa ba na banxa bane, su je can su da suka haifeta su karata da cutan ta" Hajiya Salaha tace "Gaskiya kam Allah ya kai mu goben idan kin fito ki kirani" Tunda Imaan ta fito Yusuf dake xaune tare da mai gadi da sabon drivernsu ke kallonta, yyi murmushi yace "Ina xuwa Imaan din daddy?" Rufe fuska tayi tace "Shopping mana" Ya wara ido yace "Kaji Hajiya Imaan, in taso mu je ki min shopping din nima" dariya tayi ta make kafada tace "mu je dai ka biya min" yyi murmushi yace "abun yar haka ne kenan, to wa xai kai ki?" Ta buda hannu tace "Napep xan shiga" ya bude ido yace "Salon ki kwaso k'ura ki dawo mana da asthma?" Turo baki tayi yace "A'a bari driver ya kai ki ya dawo dake kawai" Ta wara ido tace "Da na ji dadi" Ya kalli sabon drivern dake murmushi yace "Toh driver xa a ajiye mana ita a supermarket" ya mike yace "In sha Allah, bari in fiddo motar" daga haka ya shiga cikin compound din, Sai a sannan Imaan ta ga Mujaheed dake xaune kan farin kujera nesa da su yana danna wayarsa, tana kallonsa ya jefa mata wani harara, ta turo baki ta dawo kusa da Yusuf tace "Ya Yusuf jiya da na fita inna ta debar maka dambun koh?" Dariya yyi yace "Aa bata ban ba" ta tabe baki tace "Ba wani nan nasan dama jira take in tafi sai ta xuba maka ita ma ta ci, ni da ba ma cin dambu nake sosai ba" yace "Ae ko sai kin ji dadin da dambun yyi, cewa tayi ita ma ta rama abinda kika mata" bata fuska tayi tace "Ai nasan sae ta baka nice dai baxata ba" Driver na shiga compound din ya gaida su Hajiya da ladabi yana rike da makullin motar ba ta amsa gaisuwar ba tace "Ina xaka?" Yayi kasa da kai yace "Hajiya karama xa a ajiye a supermarket" Umma na masa wani kallo tace "Anya kasan wanda ya dauke ka aiki gidan nan kuwa?" Shiru yyi yana kallonta, tace "Toh ita warcan da kake gani ubanta daban a gidan nan, kuma ba shi ya dauke ka aiki ba, mai nan bangaren ne ke biyanka don haka ka maida hankalin ka, ka wuce ka ban wuri nan da 'yan mintuna xaka ajiye kawata gida" kansa a kasa ya risina yace "Ayi hakuri Hajiya ban sani bane" tace "Ehh ka sani yanxu ai" hakuri ya kara bata ya juya ya fita compound din, Yusuf na kallonsa yace "Ya aka yi?" Yayi kasa da kai yace "Hajiya ce tace xa a ajiye bakuwarta yanxu" Tsaki Yusuf yyi ya mike Mujaheed ya daga kai yana kallonsa, Yusuf na kallon Imaan yace "jira in dauko mota in ajiye ki" a hankali tace "Toh nagode" banda hararansa babu abinda Hajiya take don tasan shi xai sa driver ya fita da imaan, ta ja tsaki bayan ya fita da motarsa waje, Imaan ta bude front seat ta shiga ya bar layin, sai bayan sun hau saman titi yace "Amma dai baxa ki shanya ni a mota idan kin shiga shopping din ba" yar dariya tayi tace "Kasan me ya Yusuf kawai idan ka kai ni ka wuce ba gida xan dawo ba" Yace "Ina xa ki?" Tace "Xanje duba kawata bata da lafiya" yace "Wani anguwa?" Ta fada masa tana kallonsa yace "Su Imaan an fara hankali xa a je duba Mara lafiya" dariya ta fara yi, har suka isa Supermarket din Yusuf na tsokanarta, Bayan yyi parking yace "Kar ki shanya ni Imaan, in har kika dde to baxa ki same ni nan ba, ga ATM dina kiyi amfani da shi ai kinsan pin din" tace "Ya Yusuf ka wuce kawai ba gida fa xan koma ba nace, kuma Daddy ya turo min kudin shopping din" yace "Anya gidan kawarki kadai xaki je kuwa Imaan" ta turo baki tana kallonsa, yyi murmushi yace "Toh yi hakuri, napep xaki hau xuwa gidan kenan?" Ta gyada masa kai yace "In ji kin fito da nose mask din ki?" Tace "Ehh yana jaka" yace "Toh kar dai ki jima gidan kawar don ni baxan iya ba ammi hakuri ba" tayi dariya tace "Sae ka bata ni dai idan xata dokeni" dubu daya ya mika mata yace "Sai ki hau napep din tunda Daddy ya baki kudin shopping" ta amsa tace "Nagode" daga haka ta daga masa hannu ta nufi entrance din supermarket din. Tun a bakin entrance din yake kallonta har ta shiga mall din yana biye da ita a baya, gun turarurruka ta nufa, bayan ta dau wa enda take so har shidda, ta tafi gun pad, ta duka ta dau pad manya biyu kenan sai gashi yana xuwa toward her, suna hada ido gabanta yyi mugun faduwa don rass ta ganesa, da sauri ta ajiye pads din hannunta ta dau dettol dake wajen guda biyu, har ya iso kusa da ita kallonta yake daga cikin bakin spec dake idonsa, ta dauke kai ta dau wani sabulun ma ta sa a basket din hannunta xata wuxe, yace "Assalamu alaikum" ba tare da ta kallesa ba ta amsa, yace "Good evening" Tace "Same" yace "Kin gane ni kuwa?" Kallonsa tayi bata ce komai ba tayi saurin sunkuyar da kanta ta shiga jera kayan basket din hannunta, yyi murmushi yana kallonta yace "Dama saboda kina tare da yayanki ne kika kafe ni da ido jiya a airport, yanxu kuma gashi kin kasa" juyawa tayi xata wuce yace "Wait" juyowa ta kuma yi, ya duka ya dau pads din da ta ajiye ya sa mata cikin basket din, still tayi a tsaye, ya wuce shi kuma gun counter, turo baki tayi ta bi sa da kallo ta gefen ido, bayan wasu sakwanni ta bi bayansa, bata yadda ta tsaya gun da xai biya nasa kudin wines din da ya siya ba a mall din, duk da mutanen da suka fi yawa a next counter din can ta tafi ta tsaya, ana xuwa kanta ta bude jaka xata fiddo atm card dinta taga ya mika masu nasa, juyawa tayi tana kallonsa ya saka masu pin dinsa a pos din, imaan dai ta kasa cewa komai, suka cire kudinsu suka mayar masa card dinsa ya nufi kofar fita, ledan kayanta ta amsa bayan an mata packaging, gabanta ya dinga faduwa har ta fita bata fatan ganinsa a waje, ai ko tsaye ta gansa jikin ride dinsa, da sauri ta dauke kai ta nufi bakin titi, ya bi bayanta har ya isa Inda take yace "In ji yau yaya bai ce ki taho shopping da kafa ba" bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, yyi murmushi yace "Toh muje in ajiye ki a gida?" Kamar jira take tace "Nooo" daga haka ta tsayar da adaidaita fuskarta daure ta shiga, mai napep na tambayarta inda xata je tace "Mu je gaba" bin su yyi da kallo yana murmushi, sai bayan da suka yi nisa Imaan ta fada ma mai adaidaitan anguwar da xa ta. Suna isa ta kasa gane gidan, mai napep din yace "Toh kiyi tambaya mana" a hankali tace "To wa enda ban sani ba xan tambaya? Kamar fa wancan layin ne" ya juya yana kallonta yace "Duk fa kin sa na xagaye anguwar nan" Shiru tayi tana kallon layin da suke tsaye ciki banda haushin karnuka baka jin komai ko ina silent" mai napep din yace "Duk na kona mai na" yana fadin haka ya sakko don samun wanda xai ma tambaya duk da ba kowa silent layin sai mota daya dake tahowa, kana ganin layin kasan na manyan mutane ne sosai, ya kalleta yace "Ya kika ce sunan layin?" Fada masa tayi, mai motar na isowa inda suke ya tsaya ta dalilin tsaida shi da mai adai daitan yayi, Ya sauke glass mai adai daitan ya kalleta yace "Ya layin ma?" Ta hade rai don ta gaji da gaya masa sunan layin ta sakko daga napep din tana sake nanata masa, shiru tayi tana kallon mai motan kamar yanda shi ma ke kallonta, ya d'an yi murmushi yace "Ashe anguwar mu xa ki xo dama" bata ce komai ba ta wani hade rai, yace "Gidansu wa kike nema?" Ta sauke kanta kasa tace "Mariya Ahmad" Yace "I think wancan gidan ne" ya nuna mata gate din gidan, sae a sannan ta gane wajen, ta kallesa da kyar tace "Nagode" daga haka ta ciro dubu daya ta mika ma mai adai daitan ya bata dari biyar ta wuce xuwa gate din. Sosai Mariya taji ddin ganin Imaan ta rungumeta tace "Imaan a gidanmu, lallai yau za ayi ruwa da kankara, taya kika gane nan" imaan tayi murmushi tace "i just came to check on ur health daga shopping mall nake" Mariya tace "wllh naji sauki sosai, gobe in sha Allah xan je schl" Imaan tace "Toh Allah ya kara lafiya" Mariya zata dauko mata drinks a fridge tace "Aa ni fa baxan sha ba bana shan abu mai sanyi" Mariya tace "Ehh akwai mara sanyi ai" murmushi kawai imaan tayi Mariya ta tafi dauko mata mara sanyi, sosai Mariya ke son Imaan sai dai Imaan bata da saurin sabo kuma bata sakewa da mutane duk da kowa yasan mahaifin Mariya mai kudi ne sosai kuma sananne, har kawance ake son yi da ita, yawanci Mariyar ce ke xuwa gidansu Imaan dubata idan ta kwana biyu bata je schl ba, ita ko Imaan tun da suka je gidansu Mariyan duba yayarta da aka ma aiki tare da classmates dinsu bata sake komawa gidan ba sai yanxu, bayan boko islamiyyarsu ma daya kuma Mariya ma na da haxaka both schl da islamiyya tamkar Imaan din, Duk yanda imaan ta so tafiya Mariya ta ki yarda wai sai mamarta ta dawo sun gaisa, mahaifiyarta na dawowa kuwa ta kai Imaan har parlonta, Imaan ta duka kasa ta gaisheta da fara, matar mai kirki ta tarbe ta tana tambayarta mamarta, Imaan tayi murmushi tace "Tana gida" Aunty tace "Ya karatun fa" imaan tace "Alhmdllh" Aunty tace "Maa sha Allah sai ku yi ta dagewa, Allah ya bada sa'a kin ji" bude kofar dakin aka yi duk suka kalli kofar, xaro ido Imaan tayi tana kallonsa gabanta na faduwa, ya mata kallo daya kafin yace komai Aunty tace "Har ka dawo Sadeeq" yace "Ehh na dawo, ina yini" tace "Lafiya lau" Mariya tace "ina yini ya Sadeeq" yace "Lafiya lau" Imaan ta sunkuyar da kanta, yana kallon Mariya yace "Bakuwa kika yi" Mariya tace "Eh yaya, classmate dita ce Imaan" Yace "Oh I see, sannu da xuwa bakuwa...." Imaan ta kasa dago kanta tace "Ina yini" yace "Lafiya lau" Daga haka ya juya ya fita, Imaan na kallon Mariya tace "Xan tafi Mariya" Turaren Humra mai yawa Aunty ta dibar ma Imaan da smart collections, Mariya ta amsar mata tana godiya, Imaan tayi mata godiya ta mike suka fita tare da Mariya Aunty na cewa ta gaida ummanta, Bedroom din Mariya Imaan ta shiga daukan jakarta da ledan shopping dinta, bayan ta dauka tana facing Mariya tace "Waye wannan da ya shigo Mariya?" Mariya tace "Wai ya Sadeeq? Yayana ne shi" Imaan ta xaro ido da sauri tace "Da gaske?" Mariya tace "Kin san sa ne?" Da sauri Imaan ta girgixa kai tace "A'a tambaya kawai nake" Mariya tace "He is my stepbrother, ga bangarensu can, kina shigowa compound part dinsu xa ki fara gani" Imaan tace "Ayya, ni dai xan wuce kar Ammi ta fara kirana" daga haka ta fita Mariya na biye da ita, a parlor suka tadda Aunty da Sadeeq, da fillanci Mama ke ce ma Sadeeq tunda fita xai yi ya daure ya ajiye Imaan ko bai kai ta har gida ba, Imaan tayi murmushi tace "Aunty ya bar shi xan hau napep" Mariya ta fashe da dariya, Aunty tayi murmushi tace "Ashe dai kina ji, kin bar kawar ki a baya, ba abinda ta iya sai shashanci" Imaan ta kalli Mariya da ta cinno baki tana murmushi, Sadeeq ya mike yace "Toh bari in ajiye ta" Imaan ta d'an xaro ido, Babu yanda ta iya, bata kuma yi ma mahaifiyar Mariya musu ba, suka fita tare da Mariya dake rike da ledan ta bayan Sadeeq ya fita parlorn, Aunty ta bi su har bakin kofa tana ce mata ta gaida ummanta, cikin motar suka tadda Sadeeq, Mariya ta bude mata front seat Imaan ta sunkuyar da kanta ta shiga ba don ta so ba, Mariya tace "Byee Friend sai mun hadu schl gobe, nagode sosai" murmushin karfin hali Imaan ta mata bata ce komai ba, Mariya na kallon Sadeeq da ya tada mota tace "Ya Siddiq drive my friend carefully fa" wani kallo yyi mata bai dai ce komai ba yyi horn, Mariya ta koma ciki tana dariya, har suka hau saman titi babu wanda yace komai cikinsu, bayan wani lkci yace "Wani anguwar xa ki?" Tana wasa da fingers din ta tace "Malali" bai ce komai ba, sai da suka kusa bayan kusan minti sha biyar sannan yace "Wani layin?" Ta gaya masa, daga nan kuma ta dinga nuna masa Inda xai bi har suka shigo gate din layinsu, dai dai gidan ta nuna masa yayi parking ya juya yana kallonta, bata yarda ta kallesa ba tana daukan ledanta dake kan kafarta tace "Nagode" yace "Welcm" daga haka ta bude motar ta fita ta rufe masa motarsa ya bi ta da kallo, Tsaye taga Mujaheed bakin gate da alamar fita xai yi don makullin motarsa na hannunsa, ya kalleta ya kalli motar ya sake kallonta da wani expression, ta wani daure fuska duk da faduwan da gabanta ke yi abinda yayi ma Maimoon ranan don an ajiye ta a mota ya fado mata a rai, turo baki tayi ganin ya ki matsawa daga gate din sai kallonta yake, ta raba ta gefen sa har tana bugesa ta shige gidan da sauri, juyowa yyi yana ci gaba da kallonta, tana ganin haka ta kwasa a guje xuwa part dinsu, sai da ta isa entrance din parlonsu ta tsaya ta juya tana kallonsa, har sannan kallonta yake, ta turo baki ta bude kofa ta shige ta kulle.🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟





_By khaleesat Haiydar_✍🏻





9.....

Bayan magrib Imaan ta je kai ma inna abinci ta hadu da Yusuf a hanya yana dawowa daga bangaren innan, gaishesa tayi ya amsa yace "Wai ina tsaraban shopping dina ne Imaan?" Tace "Body spray da turare na siya fa, ka xo sai in baka daya idan yyi rabi sai ka maido min, rabi kawai xan baka dama" yayi murmushi yace "Toh an gama, yaushe xaki fito part din inna?" Tace "Ina kai mata xan dawo" yace "Toh idan na dawo masallaci xan shigo sai ki fiddo min su in xabi wanda nake so" tace "Tohmm ina jiranka" daga haka ta wuce, Mujaheed ta gani bakin tap din inna yana alwala, taji muryar innar tana cewa "Mujaheed ka tabbatar ka datse min pampo wllh cutata kawai Imaan take ta debe min ruwa ta kai ma uwarta" Imaan ta murguda baki tace "Tunda Imaan kadai ce a gidan ba" Ta gefen Ido Mujaheed ya kalleta daga durkushen da yake, ta yi watsi da takalmanta nan bakin kofa ta shiga parlon ta dungure mata warmer din hannunta, inna ta daga murya tace "Har gwara Ita Mujaheed a kan su Ummi da Maimoon tunda ita tana tambayata kafin ta diba, su dai diba kawai suke da hakkina" Juyawa Imaan tayi ta fice mata a parlonta, bata ga Mujaheed din a bakin tap din ba kuma bai kulle mata ba da kwadon da tace Ga, ta yi wucewarta, tayi nisa sosai daga part din inna xata dauki hanyar part dinsu ta ga Mujaheed a tsaye, xaro ido tayi ta juya xata gudu ya cafkota, a tsorace tace "Wayyo me nayi maka" yana mata wani kallo yace "Uban wa ya ajiye ki a mota daxu? Ta 6ata fuska tace "Ni yaushe kaga an saukeni a mota, kawai fa...." wani wawan mari ya xabga mata, ta dafe kuncinta a rude ta fara kwala ma Inna kira, yana mata mugun kallo yace "Baxa ki gaya min waye shi ba" Kuka kawai take tana bubbuga kafa har sannan hannunta na dafe a kuncinta, strictly yace "Gobe na sake ganin haka wllh sai na faffasa maki jiki, duk gidan nan wa kika ga ana ajiyewa a mota, yar mitsitsiya dake xaki shiga mota a sauke ki a gida baki tsoron kowa ke gaki kwai da ake lallabawa" yana kai wa nan ya turata yyi wucewarsa, da gudu ta koma sashin inna ta shige parlon ta xube kasa tana rusa kuka, Inna ta mike tace "Ae fa an kwan biyu ba ayi ba, to uban waye ya ta6a min ke?" Cikin kuka sosai tace "Yaya ne" Inna tace "Waye haka? waye kuma wani yaya?" Imaan ta ki cewa komai sai kuka, Inna tayi fici fici da ido tace "Shi Mujaheed din ya sha wiwi ne da xai kai hannunsa jikin ki?" Imaan na shessheka tace "Mari na yayi ya tura ni" inna ta gwalo ido tace "Mari? Kika sakar masa fuskar ya mara baki ciccijesa kin gudu ba, uban me kika mashi? Toh ya tara kuma ya samu, ba a ta6a ki ba ma ya aka kare da ciwace ciwacen ki balle an mareki a fuska, to mu je ki nuna ma ubansa fuskar" tana fadin haka ta daga Imaan suka fice parlon, inna na tafe tana kunduma masa duk xagin da ya xo bakinta, Imaan dai sai ajiyar xuciya ta ke saukewa tana biye da ita, inna ta tura kofar parlon Abba bayan ta shiga main parlor, Umma ce duke tana sa turaren wuta a parlon, Inna ta wani hade rai tace "Ke ina mijin ki?" Umma ta dauke kai tana ci gaba da abinda take tace "Bai dawo masallaci ba, ina wuni" inna ta xauna saman kujera tace "Ina wuni kuma, dama da ban wuni ba kya gan ni Rukayya" Umma dai bata ce komai ba, Inna na kallon Imaan dake tsaye tace "Toh ai sai ki xauna mu jira ubansa koh" Imaan ta xauna kasa tana goge hawayen idonta, Abba ne ya fara shigowa parlon, yayi still ganin Inna, ta kafesa da ido tana girgixa kafa, yace "Lafiya kuwa inna?" Mujaheed dake bayan Abba har ya sako kai jin abinda Abba yace xai koma baya da sauri suka yi ido hudu da inna, da sauri cikin daga murya inna tace "Rikosa Ahmadu rikosa, abu ya lalace idan ya gudu kar ka bari ya fita, xamansa muke a nan" Abba ya juya yana kallon Mujaheed da ya wani hade rai ya fasa komawan, Abba ya karasa cikin parlon ya xauna yana kallon Imaan da ta hade kai da gwiwa sannan ya kalli Inna, Mujaheed na satan kallon Umma ya shigo ya nemi waje ya xauna a kasa, duk ya fi jin ummar tasa a kan inna, banda faduwa babu abinda gabansa ya ke, Abba yace "Me ya faru kuma inna" Inna ta kalli Umma dake tsaye tace "Toh Malama xa ki iya ba mu waje in yi sirri da d'a na koko mu koma daya parlon" Umma bata ce komai ba, Inna tace "Atoh ke kadai ce bare, nan d'a na ne da jikokina" Umma ta nufi kofa fuskar nan nata a murtuke, Mujaheed ya sauke ajiyar xuciyan samun relieve daya wato fitar Ummarsa, Inna ta mike da kanta ta rufe kofar har da sa makulli ta dawo, Abba dai sai kallonta yake, ta xauna tayi kicin kicin da fuska tace "Ahmadu daxu Imaan taje kai min abinci bayan ta ajiye ta fita ba sai wannan yaro Mujaheed ya kamata a hanya ya daddage ya kwada mata wani mahaukacin mari a fuskarta ba" tana fadin haka ta dago kan Imaan tana nuna ma Abba fuskar tace "Yanxu fisabilillahi meye wannan Ahmadu, yau ko dabba Mujaheed ya samu xai maresa haka balle d'an mutum, d'an mutum din ma 'yar kanin ubansa, to wllh ka dau mataki yanxun nan, Sam baxai yiwu ba, yarinyar da ake kaffa kaffa da ita saboda lalurorin da Allah ya saukar mata, yanxu gobe ba abun mamaki bane a ga fuskar ya salu6e wannan irin bugun da yaji, tunda ga irin yanda Allah yayi ta ko ina ba kwari sae laushi, to wllh ka san abun yi Ahmadu, shegiya nake idan na yadda" Mujaheed dai ya kasa dago kai sai kallonsa Abba yake, fuska daure Abba yace "Kai..." Ya dago da kyar, Abba yace "Uban me tayi maka ka kai hannu fuskarta?" Inna ta gyara xama ta hade girar sama da ta kasa tana kallonsa, Mujaheed yyi kasa da murya yace "Abba gani nayi an sauketa a mota daxu...." Abba ya kalli Imaan yace "Mota kuma?" Inna ta buda ido sosai tace "Mota?? Ina kika samo mota Imaan?" Imaan ta ki cewa komai ta fara hawaye, Abba yace "Baxa ki bude baki ki ma mutane magana ba, wa ya sauke ki mota Imaan?" Inna tace "A'a dakata Ahmadu kada a wani fake da an sauketa a mota a shashantar da xancen mari, kai ko daukanta aka yi a hannu aka sauketa a kofar gida bai kai katon d'an ka ya xabga mata mari har haka ba, a kan me? To an sauketa a motar, ita yarinya ce ko ba ta isa a ajiyeta a mota bane? Idan sabon saurayi tayi fa, ko dama haka xata yi ta xama ba saurayi?" Daga Abba har Mujaheed kallon inna kawai suke, ta ja tsaki tace "Wannan ai abun farin ciki ne ni dai a gu na, to da a mashin roba roba ku ka so a sauketa idan ba a mota ba, ko kuma idan tayi ta xama ba saurayi Mujaheed din ne xai aureta? Yau naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, kawai yaro ka tattakure ka kama yar mutane ka falle da mari ga ka mugun tantiri ko? sannan na taso takanas na kawo kara gun ubanka ya wani fake da wa ya sauketa a mota salon maganar marin ya bi iska, To Allah ya Isar mata" daga haka ta mike tana kallon Imaan tace "Tashi mu je, Allah dai ya isa" Tashi Imaan tayi ba tare da ta yarda ta kalli Abba ba inna ta ja hannunta ta nufi kofa tana cewa "Ka ci gaba da daure masa kugu wllh duk randa xuciya ya kwasheni idan ban sa k'attin anguwar nan sun tare sa a lungu sun nakada masa shegen duka na biya su ba kace ba uwata ta haifeni ba" da karfi ta rufo masu kofar bayan sun fita, Abba ya sauke ajiyar xuciya yana kallon Mujaheed, lkci daya ya hade rai yace "Does that warrant you to slap her Muhammad?" Mujaheed

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment