Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

xa su faru gun birthday din nan da kika kwallafa rai sai kin je, why all of a sudden kika canxa from the decent Imaan da muka sani kika dawo mara ji?" Fuska daure yayi mata tambayar, kamar xata yi kuka tace "Ni fa ba birthday nace xan je ba, ai ba yau bane birthday din, kuma I only want to get him a gift now coz I know I might not get it tomorrow, ban ce lallai sai na je birthday ba" Kallonta ya dinga yi ta sunkuyar da kai a sanyaye, wayarsa da yyi vibrate ya kalla yyi replying text din da ya shigo sannan ya tafi gun motarsa ta bi sa da kallo, Maryam ta langwabar da kai tana kallonsa, yace "Ke ce ke xugata koh Maryam?" Xaro ido tayi tace "I don't get you" yace "Idan ke baxa ki gaya mata gaskiya ba why encourage her??" Maryam tace "Is there anything wrong with her getting her bf a birthday gift, we are in a civilized world Yaya Yousuf...." Yana mata wani kallo yace "Bani makulli na" Mika masa makullin sa tayi ta fito daga motar, Imaan dai sai kallonsu take ta gefen ido, ya juya ya koma inda take yace "Koma ciki..." A hankali tace "Toh ni gida xan tafi..." Ya daure fuska yace "Koma ciki nace" turo baki tayi ta juya ta koma cikin hall din, Maryam ta wucesa rai bace ta koma cikin hall din ita ma, Imaan na shiga ta tafi inda suke xaune tana kallon Mujaheed dake kallonta ta xauna, Maryam ma ta xauna a fusace tace "Gaskiya guys din nan sun fiye takura mutane, haka suke da sa ido dama, I won't tolerate this shit assuming we are staying together with them" Imaan ta tabe baki tace "I don't even know what's their business with me, sun dameni wllh" Maryam tace "Kece kike nuna kina tsoronsu ai" Imaan kamar xata yi kuka tace "Toh ni yanxu ya xanyi plss?" Shiru Maryam tayi tana kokarin nema masu wani option din, Yusuf dai na xaune d'an nesa da su yana kallonsu lkci lkci, ana fara cin abinci Maryam ta mike ta tafi ta debo masu yar fried rice ta cika nama ta dawo tana kallon Imaan tace "Let eat" Imaan ta girgixa kai tace "Am not eating" Har aka tashi dinner din Imaan bata da walwala, gashi da ta kalli Mujaheed sai ta ga kallonta yake, Tasowa Yusuf yyi ya taho inda suke ya ajiye ma Maryam makulli yace "You two should wait for me..." Daga haka ya wuce, Maryam tayi tagumi murya can kasa tace "Amma gaskiya wa ennan mutanen mayu ne, may be they know what we are up to" Ita dai Imaan bata ce komai ba idonta na kan Safeenah dake tahowa tare da Mujaheed kawayenta na biye da su a baya, hada ido suka yi da ita Safeenah ta wani daure fuska, Imaan ta dauke kai hade da tabe baki, sai da taga sun fita hall din sannan ta mike Maryam ma ta mike tace "Kinga hararan da yarinyar ke maki kuwa, did you know her b4?" Imaan tace "I don't know her fa" fita waje suka yi xuwa gun motar ya Yusuf, Aunty na kallon Yusuf a haraba hall din tace "Ka ajiye Mama Hadiza da su Hajiya Lailah a gida Yusuf..." Yusuf ya d'an bude ido amma bai ce komai ba, da sauri Imaan ta dauke kai tana wani murmushi, xagawa yyi ya budu front seat yana kallonta yace "Xo ki shiga nan" ta d'an xaro ido tace "Ya Yusuf Maryam fa?" Yace "Xata shiga wani motar, bana son musu ki xo ki shiga" Maryam ta hararesa ta dauke kai, A hankali Imaan ta taka ta isa front seat din ta shiga, Mama Hadiza da kawayen Aunty biyu suka shiga back seat, ya shiga motar ya bar haraban hall din. Yana parking a compound Imaan bata ko kallesa ba ta bude motar ta fice xata wuce apartment dinsu ta ji muryar Inna bakin gate tana cewa "Iliya Ahmadun bai dawo ba har yanxu??" Mai gadi da ya bar gate bude ganin motoci har uku dake bin bayan motar Yusuf yace "Ehh bai dawo ba Baaba" Inna na hango Yusuf da ya fito daga mota da Mama Hadiza da kawayen Aunty ta fashe da matsanancin kuka, da sauri Mama Hadiza ta nufeta tace "Me ya faru Inna" cikin kuka tace "Me na ma Rukayya a duniyar nan xata saka min da haka, ni fa na yarje ma Ahmadu aurenta tun tana yar jagaliya, yar yagalgal tana yawo da kodadden zani da yagaggen Hijabi" Mama Hadiza tace "me ya faru" Inna ta sharen hawayenta bata tanka ta ba tana kallon ta rasulu tace "Mu je kawai" ta rasulu tace "Idan ma kika yarda Rukayya ta kwana gidan nan yau Allah ma sai yayi fushi da mu da bamu dau mataki ba, irin wannan cin mutunci da raini haka? Oh oh tun da uwata Mai salati ta haifeni ban taba gani ko jin labarin irinsa ba, waiii.... Ai wannan babban magana ce wllh, ko kotu aka kai kara ba karamin muhimmanci xa su ba maganar nan ba, kuma da kyar idan ba sai an yanke mata hukuncin kare rayuwarta a gidan yari ba" Inna tace "Toh kun ji dai, ke dai mu je kawai wanda ya ajiyeta a gidan xai dawo duk gidan uban da yaje ya same mu, casun kuma da bamu samu ganin yanda xa a kare ba Allah ya isa xa mu hadu gaban ubangiji...." Ta rasulu na biye da ita tace "Ke ma dai wllh, sai ma kin fada?? Ae wannan a rubuce yake Asabe, abinda ba yafewa xa mu yi ba" Mama Hadiza da su Hajiya Lailah dai suka bi su da kallo. Imaan na kokarin saka kayan baccinta bayan ta fito wanka aka bude kofar dakinta, Maryam ce ta shigo ta tsaya tana kallonta tana murmushi, da mamaki Imaan tace "Ina kika je tun daxu kowa ya dawo banda ke??" Maryam tace "Close ur eyes please" Imaan tayi shiru tana kallonta, Maryam ta hade rai tace "Toh ko inyi wucewata" Murmushi Imaan tayi don sai sannan ta lura da hannunta dake boye a bayanta, a hankali Imaan ta lumshe idonta tace "Toh na rufe" Maryam ta isa kusa da ita ta tsaya tace "Bude ki ga gift da xa ki ba Sadeeq din ki" da sauri Imaan ta bude idon taga wani flower mai kyan bala'i da cards Maryam na mika mata tana jujjuya eye balls dinta, Imaan ta saki baki tace "What's this?" Maryam tace "Gift din da xa ki ba sa mana" Dariya Imaan tayi tace "You are very funny wllh, me xai yi da wannan din" Maryam ta xaro ido tace "Me xai yi da shi fa kika ce?matsalar ku kenan yan Nigeria wllh, ke kinsan Value din abun nan dake hannuna kuwa, kin san mu a turai wannan ya fiye mana kudi da wasu abubuwan rayuwa idan aka xo fannin kyautatawa, wllh I am telling you this sai ya fi son wannan akan kudin da xaki basa ko abinda xa ki siya masa, idan kin basa kudi me xai yi da shi bayan yana da fiye da wanda xaki basa, sai dai ma ya bada kudin kyauta tun bai shiga gida ba, idan kika ce xaki siya masa abu me xai yi da shi bayan bai fi karfinsa ba?? Wannan kam kina basa am telling you xa ki ga reaction dinsa..." Tana murmushi ta kare maganar, Imaan dai sai kallonta take nan kuwa a xuciyarta tunani take kuma fa gaskiyan Maryam tunda shi ma a turan ya taso xai so gift din sosai, Maryam ta kai mata flower din hancinta tace "Smell it" lumshe ido Imaan tayi jin wani cool scent da flower din yake, ta amsa tana murmushi tace "It smells nice, I love you Maryam" ajiye flowers din da card tayi gefen gado ta rungume ta. Umma na dawowa daga hall din dinner tare da kawayenta bayan sun sallami mutane gaba daya dama bata yarda ta shiga gidan ba, kawayenta su Hajiya Saude ne kadai suka shiga cikin gidan tunda haka dama suka shirya tun a hanya, Umma ta dau wayarta ta nemo lambar daddy tayi dialing, ba a dau lkci ba ya daga, tayi kasa da murya ta gaishesa ya amsa yace "Lafiya dai koh Hajiya Rukayya" Tana yake tace "Lafiya Baban Imaan, nace kana gida kuwa?" Daddy yace "Ehh na kusa gidan yanxu, driving nake" Umma tace "Toh Ina ma kofar gida, xan jira ka iso" yace "Ohk" daga haka ya katse wayar, Daddy na shigowa layin ya hangota tsaye d'an nesa da gate din gidan, parking yayi kusa da gidan ya fito yana kallonta yace "Lafiya kuwa?" Tace "Toh lafiyar kenan dai..." Yace "Mu shiga ciki toh" da sauri tace "A'a bari dai in maka bayanin a nan" Ya rungume hannunsa yana kallonta yace "Toh ina ji" Tace "Wllh Baban Imaan daxu ne Inna taje wajen da ake dinner...." Da mamaki Daddy yace "Yanxu sai da taje dinner din nan duk abinda muka gaya mata??" Umma ta bude hannu alamar ai shine, tace "Kuma da aminyar nan tata Baaba ta rasulu, wllh Abban Imaan sai kaga abinda taje ta dinga yi" Daddy ya girgixa kai yana kallonta, Umma tace "Wata kawar amarya na tsaye gaban jama'ah tana bada tarihin amarya in gaya maka sai Inna ta tafi ta sami yarinyar ya amshe microphone ta fara xaginta wai wani tsinannen tela ta ba kudi ya mata dinki, Kai maganganu dai babu dadin ji Abban imaan, ai su Mama Hadiza da Hajiya Aisha na wajen ni ba sharri na mata ba, wllh kunya kamar in nutse, dama imu imu ne abun xai xo da sauki amma fa ga dangin amarya sun cika wajen kuma Yan babban gida, bayan ta gama da yarinya mai bada tarihi ta tafi ta kwashe duk abinda aka ajiye ma amarya da ango a gabansu ta wuce ta bar wajen sirara, haka ta dinga ma mutane fada wai kada a xubda datti sun xo cin shinkafa da miya da kaza mayunwata kawai, maganganu dai ga su nan xar kayan kunya xar takaici Abban Imaan, yanxu fisabilillahi hakan ya dace?" Girgixa kai kawai daddy ya dinga yi yana salati, Umma tace "Toh ganin abun sai gaba yake sai naje na sameta nace toh fa ga ruwa can ya cike parlonta ta bar pampon bandaki a bude, shine Inna ta bar wajen ba shiri da kawarta Baaba ta rasulu, yanxu nayi laifi a nan Abban Imaan?" Daddy yace "Aa dai dai kenan" Umma tace "Toh nasan yanxu suna can kila ma ta tara jama'ah ana jirana, kuma ko me xata gaya ma Abbansu Mujaheed wllh yarda xai yi ya xauna a kai, shi sa ma nace bari in maka bayani tukun" daddy ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh Allah ya kyauta, kuma hakan da kika yi shine dai dai, don da ba don haka ba baxa su bar wajen ba, kada ki damu nasan abinda xan yi, kiyi wucewar ki ciki" Umma ta d'an yi murmushi tace "Toh ngd Abban Imaan da ka fahimce ni" cikin gidan ya nufa ta bi bayansa bayan ta sauke boyayyen ajiyar xuciya. Inna ce xaune parlonta kan tabarma ta daura kafa daya kan daya fuskarta shabe shabe da hawaye tana fyace majina da hankicin hannunta, ta rasulu dake xaune kan darduma ta girgixa kai kamar xata saki kuka tace "Ni Ahmadu babu abinda ya fi min ciwo irin yanda muka dinga yawo muna xaga garin kaduna a adaidaita sahu muna neman wajen casu bayan mun dawo mun ga karya Rukayya take, daga karshe sai dawowa gida muka yi bamu gane wajen ba, mai adaidaita na bala'i mu ma muna bala'i, haka muka yi asaran dari biyun mu don da kyar mai adaidaitan ya amshi dari biyun wai sai dari shidda xa mu basa, wllh mune har sabon kawo neman wajen casu, babu wajen casu babu labarinsa" Mujaheed dai na xaune parlon sai kallonsu yake, Yusuf ma haka, Aunty da Ammi da Mama Hadiza ma duk suna xaune, Abba dai kansa na sunkuye yana sauraronsu, Cikin kuka Inna tace "Duk a kanmu sanyin daren yau ya kare muna yawo a daidaita neman wajen casu kaman yan iska, kuma ace inyi hakuri saboda ba a san ciwo na ba, ni wllh yau duk sai mu tattara mu tafi Police station, wacece kuma Rukayya da xata min wannan toxarcin, me aka yi aka yi ta, Rukayyar banxa Rukayyar hofi, ni dai wllh Ahmadu na xuba ido yanxun nan in ga matakin da xaka dauka kan katuwar nan, bikin ma ni sai in iya cewa a dage sai an bi min hakkina da na Aminiyata ta rasulu tukun, shkkn haka aka kare casun yau banda mu, ba mu ci Yar shinkafa da kazar da aka raba ba" sai kuma ta fashe da matsanancin kuka, Yusuf ya sunkuyar da kai yana murmushi, Ta rasulu na matsar kwallan da ya cika idonta tace "Ni wllh Asiya bata isa ta min haka ba, don sai dai in sa Muhammadu ya xabi ko ni ko ita...." Sallama aka yi bakin kofa, Inna ta amsa cikin rawar murya tace "Bukar yau dai bamu samu casun bikin Mujaheed ba, Rukayya dai yar iska ce wllh"

*Thanks for the prayers via phone calls and WhatsApp messages fans, Allah bar xumunci, nagode sosai, am feeling a little better in sha Allah*



*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
[7/19, 5:15 PM] +234 803 603 7561: Shigowa Daddy yayi parlon yana bin dukansu da kallo, Mujaheed ya mike ya koma kusa da Yusuf, Daddy ya xauna yana kallon Inna yace "Lafiya? Me ke faruwa?" Inna ta fyace majina a hankali tace "Kana ji Bukar? Bayan fitar ku daxu da yamma shine kawai na yanke shawarar tafiya wajen da ake casun ko minti sha biyar ne in yi in juyo duk da dai kun hanani, Toh ya xa ace bikin Mujaheed guda baxan je wajen casu ba, wllh Bukar mun shiga wajen da ake abun kenan mun xauna ko kayan kwalaman ba a fara rabawa ba sai ga Matar nan Rukayya tana haki wai in maxa in koma gida ance ruwa ya cika min daki da parlor, shine fa muka taho kamar mahaukata tare da Ta rasulu, muna shigowa gida in gaya maka sai muka ga bandaki a bushe tass babu ko digon ruwa balle ambaliyar ruwa, shine dai muka ta fada rai bace tare da Ta Rasulu nace mu koma wajen mu ji dalilin da ya sa xata gilla mana irin wannan karyar me tsada ko mu sa'annin uwarta ne, to fa muka dau adaidaita xa mu koma amma neman duniya mun wa wajen casun nan bamu gane ba haka muka ta walagigi a adaidaita sahu sanyin daren nan duk ya kare mana daga karshe muka dawo gida, yanxu fisabilillahi me na ma Rukayya xata min haka?" Daddy ya girgixa kai yace "Amma ba nace maki kada ki tafi wajen ba daxu da yamma Inna?" Inna tace "Bukar cewa fa nayi minti goma sha biyar kawai xan yi, ai da ban leka wajen ba wllh kullatata Mujaheed xai yi shi sa nace bari kawai in je a tsatstsaye in dawo, kuma meye laifina" Daddy yace "Haba Inna, yanxu fisabilillahi ki shirya ki shiga cikin yara ki xauna kice kin tafi wajen casu, me yasa kike mana haka don Allah?" Inna tace "Haba Bukar don dai minti sha biyar in juyo, wa ma xai san naje wajen banda mai sa ido? a baya fa muka xauna don ma kada a lura da mu" Daddy yace "Kwata kwata bai kamata, ban ga amfanin shiga cikin jikokin ki wai kinje casu ba, mu dai idan mun gaya maki magana baki ji baki amfani da shi, bamu san ko kina da wasu masu gaya maki bane bayan mu, ni bana jin dadin hakan da kike yi, kullum ayi ta magana amma baki gyarawa Inna, abinda baki sani ba a nan shine har mu kina xubar mana da mutunci a idon duniya...." Shiru Inna tayi sai 'yan idanuwa, a hankali ta Rasulu tace "Wllh Bukar sai da nace mata mu hakura kar mu je amma Asabe taki saurarata....." Juyawa Inna tayi tana kallonta baki sake, can ta kalli Daddy tace "Kaga xata gilla min sharri da rai na ko Bukar, to wllh ta ma riga ni shiryawa har tana cewa xata tafi ta bar ni ina bata mata lokaci, ni dai a dinga jin tsoron Allah ba ruwana" Ta rasulu tace "Yo idan ban ji tsoron Allah ba tsoron ki xan ji Asabe? Ke dai ki dinga bin 'ya yan ki sau da kafa baki da kamarsu, da Muhammadu ne yace min kada in tsallake ko nan da kofa wllh baxan tsallake ba, kawai ki sa mu shiga cikin jikokinmu mu xauna kamar wasu gantalallu har ana gilla mana karya don a kora mu...." Inna tace "Ni dai nace a dinga jin tsoron Allah ba ruwana, biki kuma gashi nan dai an gama sai kowa ya san na yi..." Ta Rasulu tace "Ina nan sai na raka Mujaheed gidansa na sa albarka...." Inna ta tabe baki tace "Toh naji na tafi casu ba da izinin ku ba Bukar, walakanta ni da Rukayya tayi fa??" Daddy yace "Ae ni na kirata nace ta fada maki haka saboda hakan kadai ke iya sawa ki dawo gida, don xuwan ki wajen bashi da fa'ida" Salati Inna ta saki tana kallonsa a hankali tace "Allah ya fi annabi sani...." Ta Rasulu tace "Toh ai da sauki tunda kai ne ka sa ta, kuma gaskiya da ba haka aka yi ma Asabe ba bata da ranan baro gun" Inna ta kalleta ta gefen ido ta rike ha6a tace "Ohh.. Naga abinda ya isheni, mutane dai basa tsoron Allah, da ranka ma sai an dinga bin ka da sharri" Mikewa Daddy yayi yace "Mu dai muna neman alfarmar ki dinga daukar maganar mu kina aiki da shi ba don mu ba don Allah..." Inna tayi kasa da murya tace "Toh ni dai kayi hakuri kuskure ne na riga nayi, sai dai Allah ya kyauta na gaba" Bai tanka ta ba ya fita parlon, Inna ta bi sa da kallo, Mikewa Abba yayi yace "Toh a dai yi hakuri inna" daga haka ya fita parlon shi ma ta bi sa da kallo, Mujaheed ya mike yace "Tsofe tsofe kice sai kin je casu..." Bai jira cewarta ba ya fice parlon yana murmushi ta bi sa da kallo, Yusuf ya mike ya fita parlon shi ma ta bi sa da kallo, Aunty dake kokarin danne dariyarta ta mike tace "Toh don Allah kuyi hakuri Inna" Inna ta tabe baki bata dai ce komai ba, Aunty tace "Bari in je Inna, muna aiki ne" daga haka ta fita, Ammi ma tayi mata sai da safe ta fita, tagumi inna tayi bayan duk sun fita tace "Lallai Bukar ya xama abun tsoro Ta Rasulu, ni da ba don a kan idona na haifosa ba ma sai ince canjin sa aka min a tsinannen asibitin turawan da na haifesa, ke kiji ashe shi yasa katuwar mata ta kirani ta gilla min karya, duniya ta lalace ni patuu" Ta Rasulu tace "Ai yanxu darajar sa Rukayya xata ci baxa mu daukaka kara ba, amma wllh bata ci bulus ba, ki kyale Yar iska Allah ya kai mu wayewan garin gobe lafiya" Inna tace "Shi kuma Bukar dama kada ya sake tako min nan tunda haka ya xama, ba ruwana ya je yyi ta kansa" Ta Rasulu tace "Atoh, ni da ace Salihu ne da na masa barbadin bala'i ynxu...." Mama Hadiza dai sai kallonsu take daga inda take xaune, Inna tace "A'a ni dai gwara da na bar figaggen da halinsa ba ruwana ace naje ina cecekuce da shi, gwara kawai da na masa shiru ya gama bambaminsa ya fita, ae shi Ahmadu baya haka, dama ni ban so ya shigo ba sai Ahmadu ya gama yanke hukunci, Toh sai gashi Allah ya jefo mana shi, haka kawai inje inyi magana bafillatanar matar sa ta ji haushi na ta kullace ni, A'a ba ruwana" Ta Rasulu tace "Dama shirun ya fi ina xaki tsaya cecekuce da d'an cikin ki?" Inna ta tabe baki tace "Ni dai ba ruwana, Allah ya shirye sa, amma Bukar gaskiya ba shi da hali duk cikin 'ya yana"
Washegari tun da imaan ta tashi take jin xaxxabi da ciwon kafa, har karfe tara bata fito ba don ko Ina a gidan cike yake da jama'ah, Maryam dai tun da ta kawo mata breakfast dakin bata sake ganinta ba, Ammi ce ta shigo dakin karfe goma saura ganinta kwance ta karasa kusa da gadon tana kallonta tace "Lafiya?" Mikewa xaune tayi da kyar tace "Ammi kamar xanyi xaxxabi kuma kafana ciwo suke min" Ammi ta kai hannu jikinta ta ji da xafi, Juyawa tayi ta fita ta wuce kitchen ta hado mata wani shayin ta dawo tace "Kin ma yi wanka?" Kai ta gyada ma Ammi, Ammi ta mika mata shayin tace "Ki sha shayin sai ki sha drugs din ki" karba Imaan tayi ta fara Shan shayin Ammi ta dauko drugs dinta inda suke ta ballar mata bayan ta sha kusan rabin shayin Ammi ta mika mata maganin, Karba tayi ta sha Ammi tace "Ki tafi can bangaren Inna ki kwanta baki xa su sauka nan xuwa anjima kadan" Imaan ta xaro ido tace "Ammi bandakina fa?" Ammi tace "Ku dai ba ku da hali mai kyau abu dai na kwana daya, to sai ki kinkimi bandakin ki tafi da shi bangaren Inna ki ajiye" Imaan kamar xata yi kuka tace "Wllh bata ma mutum fa xa su yi, ni dai gwara in kulle in boye makullin" Ammi tace "Toh ki kulle tunda baki da hankali" Imaan bata ce komai ba Ammi ta juya ta fita, Mikewa tayi da kyar ta kwashe gaba daya kayan cosmetics dinta dake gaban madubi ta xuba su drawer, ta cire farin bedsheet dinta ta dau mai duhu ta shimfida tana turo baki, ta shiga bandaki ta dauke sabulu da sponge dinta sai brush da toothpaste ta dawo daki ta adana, hijab ta saka bayan ta dau sabbin kayanta na biki da xata saka a cikin leda ta fita dakin tana dingishi, babu yanda ta iya haka tayi ta gaida mutane har ta isa part din Inna, Ta Rasulu ce tsaye bakin kofa tana kallon tsofaffin da ke xaune cikin parlon tace "Don Allah ba don mu ba idan kun cire takalma a dinga ajiyewa a gefe guda kar su bata bakin kofar, bikin fa na yan gayu ne, haba takalma sai kace na masu talla" Imaan ta raba ta gefenta ta shiga parlon, daga kitchen Inna ya fito rike da cooler da plate ta duka tace "Toh ni dai basu gama girkin ba ina ji, wannan dai 'yar wainar da aka xubo min ne da safe sai in manna ma kowa guda biyu, ga miyar taushen mai kyau da nama...." Kallon Imaan dake gaida mutanen parlon xata wuce daki Inna tayi da sauri tace "Waye wannan kuma?" Juyowa Imaan tayi ta hade rai tana kallonta, Inna ta mike tace "Me xaki je ki min a daki??" Imaan ta marairaice tace "Inna baki suna dakina ne kuma bacci nake son yi" Inna tace "Naga abinda ya isheni, to Ina ruwanki da bakin Imaan? Gaskiya ni dai kiyi hakuri ki xo ki wuce na saka ma dakina turaren wuta kuma ma wannan mutumin...." Ko sauraranta Imaan bata yi ba ta shige dakin da sauri tana turo baki ta kulle, juyawa tayi, tayi still ganin Mujaheed kwance saman gado... Ta xaro ido tana kallonsa, A hankali Imaan ta bude kofar xata fita sai kuma ta juya tana kallonsa, Bude ido yyi yana kallonta shi ma, ta turo baki ta fita da sauri ta kulle kofar. Inna dake ta xuba waina a plate tana diga miya kamar xa a ba jarirai ta kalleta tace "Har kin fito knn, toh

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment