Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aisha baki taka mata burki, a kan me xata dinga rainata, I don't like that, and I am going to teach her manners soon" Ammi ta tabe baki ta mike ta dauke abincin da ta bari ta kai kitchen ta rufe, ta tsaya kitchen din tana wanke plates da ke sink. Washegari wajen karfe bakwai da rabi Imaan ta fito sanye da uniform din islamiyya, kanta a kasa ta gaida Ammi dake jera breakfast a dinning, Ammi dake kallonta tace "Wato ke ba isa a maki fada ba shine kika kwana kuka ido ya kumbura koh?" Ta fashe da kuka tace "Ni Ammi don Allah kar ki sake ce min in kai mata abinci kullum sai tayi ta ma mutum sharri alhalin ba abinda nayi mata" Ammi tace "Ko ban baki abinci kin kai ba ma da kanki naga kike kwasan kafafuwanki kije can din ko da kuwa koranki tayi" Imaan ta hade rai tace "Yesterday was the last day da xan je part dinta, har abada baxan sake xuwa ba" Ammi tace "Toh bari dai ya ji ki gashi can ya fito, ni ba ruwana" shiru Imaan tayi tana juya shayin da Ammi ta hada mata, Daddy dake tsaye parlon yace "Madam me yasa ba a kai ma Inna breakfast ne wai?" Ammi tace "Breakfast kuma?" Yace "Ehh ai ya kama ta ne" tace "A'a don Allah yallabai kar ka hada ni da ita, kullum sai Abba ya tura mata bread, tana da kayan shayi kuma tana da heater ta iya amfani da shi, meye breakfast din dama idan ba shayi da bread ba sai kwai wani lkcn, lunch da kanta tace bata so a daina kai mata wai jagwalgwalon yara ne" Tuni Daddy ya xauna ya sa news channel, Ammi ta shiga kitchen ta ci gaba da abinda take, Imaan ta gama breakfast din ta mike ta iso cikin parlor ta durkusa ta gaida Daddyn nata, sau daya ya kalleta ya amsa ya ci gaba da kallonsa, ta mike ta tafi kitchen ta amshi kudin makarantar ta gun Ammi ta fito ta dau jakarta bayan ta sa takalmi da safa tayi ma daddy sallama ba tare da ta kallesa ba ta fice daga parlon, kiranta daddy yyi ta juyo ta dawo ta sunkuyar da kanta tace "Ga ni" room freshener har biyu ya nuna mata dake ajiye yace "Dauka ki kai ma Inna kafin ku wuce" shiru tayi tana kallonsa kamar xata yi kuka, bata dai ce komai ba ta durkusa ta dauka sannan ta fita xuwa part din inna, Inna na ta goge goge bayan ta gama share ko ina fesss, banda kamshin turaren wuta babu abinda ke tashi a parlon, imaan bata kalleta ba ta ajiye abun hannunta fuska daure tace "Ina kwana" xata fita inna tace "Me ya sami idonki ni Asabe? An umaki wani abun ne" Imaan da har ta kai kofa ta juyo lkci daya ta fara kuka tace "Kawai sai kije kice ma daddy ina maki rashin kunya yaushe rabon da in xo nan...." Tana fadin haka ta fashe da matsanancin kuka, Inna da ta saki baki tace "Shine ya maki me?" Cikin kuka tace "Fada ya dinga min mana yace zai yi magani na" Inna ta dau dankwalinta ta fita parlon imaan ta bi ta da kallo tana share idonta, Ko sallama babu inna ta bude kofar parlon, daga daddy har Ammi suka daga kai suna kallonta, tace "Bukar dama yaro ba lallabasa ake yi ba a rayuwar nan, daga mun yi magana tsakanina da kai sai ka taho ka far ma yarinya da bala'i, to ae gwara ita sau dubu a kan sauran, Imaan bar ta da son jikinta amma wllh wllh bata da matsala, haka kawai ka ja mata wani cutan dama gata mai cuta iri iri kamar ta kashe d'an mutum, yanxu da kasa ta kwana tana kuka idan wani abun ya sameta me xa ka gaya ma Allah, kai dai wllh ka cika bala'i, ba haka yayanka Ahmadu yake ba, ba ruwansa da irin wannan hali, to wai ma me ta min da xafi haka da xaka sa ta kuka haka, ga abun duka can Mujaheed me nuna ni da yatsa, mai ce min Hajiya, ni tunda nake wllh xan iya kirga sau nawa Imaan ta mayar min magana shima kuma duk laifina ne....." Ammi dai tuni ta shige kitchen, Daddy kuma ya kasa cewa komai, Inna ta juya ta nufi kofa tana cewa "Wannan dai ba yi bane, kamar ba kai ka haifeta, yar gata daga ita sai ita amma kuma ka takurata, da wanne xata ji da rashin karo mata kanni da ba ayi ba har yau ko kuma da fitinar mahaifinta, kuma ka tashi ka kawo min turaren bature da ko kamshi babu wai in fesa a daki, to uwata bata ce min je ki kya gani ba turaren wuta tsadadde mai kamshi nake nufi, sai ka ba matarka mai kumewa a daki kamar matar liman ta fita kasuwa ta siyo min" daga haka ta fice ta kulle masu kofa. Dama imaan direct gun mota ta nufa bata yarda ta ma bi ta part dinsu ba. Yusuf ne ya ajiye su islamiyyar, karfe sha biyu Anty ta dauko su, A hankali Imaan ta bude kofar parlonsu tana lekan ciki, babu kowa hakan yasa ta shiga ta rufe kofar ta nufi bedroom dinta da sauri, tana kokarin cire Uniform dinta Ammi ta bude kofar, Imaan ta gaisheta kanta a kasa, Ammi tace "Amso min card waje kafin ki cire uniform din" Imaan ta amsa tana kallonta tace "Ammi daddy fa?" Ammi tace "Yana daki" Imaan ta marairaice tace "Ni fa ban gaya ma inna ya min fada ba, kawai taga idona ne haka" Ammi tace "Wannan ya rage naku ke da shi, ni kiyi sauri ki amso min card din" imaan ta maida Hijab dinta ta fita, kiosk din is just a house from theirs, ta amso card din ta juyo ta shigo gida, Umma ta gani tsaye parking space alamar xata fita, Mujaheed ya iso wajen ya bude mata back seat, sannan ya shiga driver seat, Imaan na hada ido da Umma dama ta dauke kai tayi wucewarta, Mujaheed ya bi ta da kallo ta madubi, Umma ta shiga cikin motar tace "Wllh duk ranan da ka gaida uwar yarinyar nn ko da mistake a gidan nan ban yafe maka ba Mujaheed, duk kanninka ma na karanta masu haka nasan kuma sun dauka...." Yana kallonta ta madubi yace "Haba Umma kema kin san....." Ta karasa masa da sauri tace "Baxa ka iya ba ko? tunda ga ta kanwar Ahmad ko kanwata, Mara tunani kawai da bai san ciwon uwarsa ba, to mu xuba da kai wllh, ba dai makiyana su ne mutanen arxikin ka ba a gidan nan, ka ci gaba, a ta dalilin munafukar uwar yarinyar nan na bar gidan ubanka for good 5 years, ta hade kai da kishiyata suka yi ta kulla min makirci har ubanka ya sakeni, da yake akwai sauran xamana a gidan na dawo few years back na tarar baka da masoya da ya wuce makiyana, ka maida Aisha uwarka, ka nuna duk gidan nan baka da kanwa da ya wuce yarinyar Aisha, yarinyar da bata gaisheni a ynxu ko idona xai makale a nata saboda uwar ta hanata, da kyar da siddin goshi da rokan Allah na rabaka da su, ni da ba a kan idona na haifeka ba kuma ina haihuwar ka aka ajiye min kai a gefe na da wllh bbu abinda zai sa baxan ce canjen ka aka min a asibiti ba, sam baka san mutunci na ba, ace makiyana su ne masoyan ka Mujaheed? Anya kana son gamawa lfya kuwa?" Shi dai ya kasa cewa komai, ta gyada kai ta bude motar ta fice tana cewa "Ga ka ga su ai, daga ynxu ma ka tatttara yanaka yanaka ka koma bangaren nasu" a hankali yace "Umma I have avoid a lot of things a gidan nan kema kin sani, wllh ko kadan bani son abinda xai bata maki rai, don Allah kiyi hakuri...." Ko saurarensa bata yi ba ta fice daga compound din ya sauka ya bi bayanta da sauri. Washegari har Ammi ta gama hada breakfast ta fito daga kitchen imaan bata fito daki ba, ta kalli agogo ganin bakwai da quarter ta nufi dakin ta bude ta shiga, kwance ta ganta ta dukunkune cikin bargo, Ammi ta karasa da sauri ta cire bargon tace "Are you okay Imaan?" Ta bude ido kamar xata yi kuka, Ammi ta dinga kallonta don jikinta ya dau xafi sosai, a hankali tace "Ina ke maki ciwo kuma?" Kafafuwanta ta nuna mata da kai, hawaye cike idonta tace "Ammi duka jikina ciwo, jiya ban yi bacci ba" Ammi ta kamo hannunta cikin sanyin murya tace "Ba ki sha magani ba jiya da daddare ko daughter" ta nuna ma Ammi magungunanta a side drawer tace "Na sha Ammi" saketa Ammi tayi ta mike ta shiga bathroom ta hada mata ruwan wanka ta fito tace "Toh shiga kiyi wanka sai ki kara shan maganin" da taimakon Ammi ta sauka kan gadon, Ammi na rike da ita suka shiga bathroom, bayan ta wanke baki Ammi ta taimaketa tayi wanka ta fito, barin ta tayi ta sa kaya ta tafi hado mata shayi, Daddy na xaune parlor yana dube dube a laptop, ta tsaya bayan kujerar tace "Yallabai jikin imaan fa kar ya rikice mana ko xa aje asibiti tunda likitan ma baya nan" daddy ya mike yace "Bata jin dadi ne" Ammi tace "Nima yanxu na shiga ganin bata fito ba, her temperature is high tace bata yi bacci ba" daddy ya d'an yi shiru, Ammi tace "Kwanakin baya ciwon ya lafa sosai, as from some weeks ago yanxu duk sai ya tasar mata ga xaxxabi da ciwon kai kuma tana shan drugs dinta" Daddy yace "Toh ta shirya mu tafi asibiti" Ammi tace "Toh" komawa yayi ya xauna, ita kuma ta wuce dinning don hada mata shayi. Kwance ta sameta bayan ta sa abayar da ta fiddo mata, da kyar Imaan ta sha shayin, Ammi ta fesa mata turarrukan ta ta bata veil din abayar sannan suka fito parlor, kwanciya tayi kan kujera tana gaida daddy dake rike da makullin mota yana jiransu, ya amsa yace "Sannu mamana, tashi mu je to" mikewa tayi ya kama hannunta suka nufi kofa Ammi na masu Allah ya kiyaye hanya, A hanya daddy ya hadu da Abba ya taho daga part din Inna, gaisawa suka yi, Imaan ma ta gaishesa a hankali, Abba yace "Jikin ne ya tasar mata?" Daddy yace "Wllh kuwa, xa mu je asibiti ne yanxu" Abba yace "Subhanallah tana shan magunguna kuwa" Daddy yace "I think so" Abba yace "Toh likitan ta fa?" Daddy yace "Yayi tafiya ne" Abba yace "Toh tunda Muhammad na nan ba sai ya dinga dubata ba kafin likitan nata ya dawo, ko gwara a tafi asibitin?" Daddy yace "Noo in xai dubata shikenan, dama don likitan baya nan ne xa mu je asibitin" Abba yace "Let me give him a call, na barsa sashin inna, idan ma asibitin xa a sai ya kai ta kawai" Yana kokarin kiran Mujaheed suka hangosa yana tahowa, Abba ya maida wayarsa, har Mujaheed ya isa parking space da suke tsaye kallonsu kawai yake, Ya risina ya gaida Daddy, ya amsa masa da fara'a, Abba yace "Imaan xaka duba Mujaheed, bata jin dadi" Sosai gabansa ya fadi ya kalli Imaan dake jingine da mota duk ta wani langwabe.

I appreciate my fan's love always, ina yinku fisabilillah😘😍
[6/11, 12:34 PM] +234 703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟




_By khaleesat Haiydar_✍🏻





5.....

Gaba daya Mujaheed ya daburce ya rasa abin cewa, Abba yace "Ko in kai ta asibitin kawai" da sauri yace "Noo Abba, naga bani da kayan aiki a gida ne, sai dai in kai ta asibitin in duba ta a can" Abba yace "Toh hakan na da kyau" Magana yake amma gaba daya rabin attention dinsa na kan window din dakin Umma duk da baya hango komai, amma fatansa yanxu ace bata tashi bacci ba duk da yasan da wuya, Ya sunkuyar da kansa yace "Toh xan dauko makullin mota a ciki" Daddy ya mika masa nasa makullin motar yace "You use my car, duk yanda ake ciki you let me know" Mujaheed ya risina ya amsa makullin motar yace "Toh Abba" daddy yayi ma yayan nasa sallama ya wuce ba tare da ya kalli imaan da ta cika saura kiris ta fashe ba, bayan ya tafi Abba ya kalleta yace "Sannu Mamana" Ganin hawaye idonta yace "Baki son bin Muhammad din kenan?" Da sauri ta gyada masa kai hawayen na sakkowa idonta, yace "Kuma baki son daddyn naki ya huta koh, am sure kila xuwa anjima ko gobe xai koma bakin aiki, shi Mujaheed din ba yayanki bane?" Ta fashe da kuka tace "Abba ihu xai ta min a hanya fa" Abba yyi murmushi mai sauti sai dai bai ce komai ba, Mujaheed dai sai kallonta yake ta gefen ido, Back seat Abba ya bude mata yace "Shiga" a hankali ta shiga ta jinginar da kanta jikin motar, Abba na kallon Mujaheed yace "You take very good care of her, ko kallon banxa ban yarda kayi mata ba" Ya sauke idonsa yace "Toh Abba" Abba ya daga mata hannu ta mayar masa tana goge idonta, ya juya ya wuce ciki, Mujaheed ya gama warming motar yayi horn ana bude masa gate ya fita gidan, sai da suka hau saman titi yace "Saboda baki son xuwa schl shine kika fake da ciwon karya salon ki ba mutane wahala koh?" Jin bata ce komai ba ya kalleta ta madubin motar, murguda masa baki take, suna hada ido ta turo bakin kamar xata yi kuka sai dai bata ce komai ba, ya gyada kai yace "Xaki gwammace schl kika yi tafiyar ki yau" ta fashe da kuka tace "Dama dai Abba yace duk abinda ka min in gaya masa" Bai tanka ta ba har suka iso asibitin da yake aiki, yana gama parking ya bude motar ya fita ita ma ta fita, ya rufe motarsa ya dau hanyar entrance din shiga hospital din, a sauri ta bi bayansa, tsaye ta gansa reception suna gaisawa da nurses dake wajen da fara'a, Wata nurse tace "Doctor I heard an sake transferring dinka xuwa nan, kuma shiru ba mu ganka ba" Yace "Sure da yau xan yi resuming, but due to some reasons sai Wednesday in sha Allah" duk nurses din suka amsa masa da Allah ya kai mu, juyawa yyi yaga Imaan ta nemi kujera tayi xamanta, wata nurse tace "Dr sister dinka ce?" Yace "Sure bata da lafiya ne" daga haka ya wuce sama, duk sai da ya shiga office din doctors dake duty safiyar, Dr Mukhtar na ganinsa ya mike yace "Kaga mara kirki dama yau xaka yi resuming shine babu sanarwa" Mujaheed ya karasa yana murmushi suka gaisa yace "Sai Wednesday in sha Allah, na kawo sister na ne bata da lafiya" Mukhtar yace "Subhanallah Ummi ko Rahma?" Yace "None, cousin dita ce wannan" Dr Mukhtar ya koma ya xauna yace "Ohk tana ina" Yace "Tana reception" Dr Mukhtar ya buga waya downstairs ba a dau lkci ba wata nurse ta shigo office dinsa, gaida Mujaheed tayi da fara'a ya amsa yace "Ya aikin Zainab" tace "Alhmdllh Dr" Dr Mukhtar yace "Ki taho da patient dake reception" tace "Wanne they are almost 7 patients downstairs" Mujaheed yace "Imaan sunanta" tace "Ohk" daga haka ta fita, tare suka dawo da Imaan da ta wani yi laushi da kyar take jan kafar, Dr Mukhtar ya nuna mata kujeran dake kallon wanda Mujaheed ya xauna, ta xauna xata kwantar da kanta kan table Mujaheed ya mata wani kallo yace "Tashi" kamar xata yi kuka ta dago kanta, likitan yace "Sannu Imaan, ya kike jin jikinki, like ina ke maki ciwo?" A hankali tace "Jiya da daddare bayana ya dinga min ciwo har da kai na kuma ina jin sanyi, ban ma yi bacci ba" likitan yyi murmushi yace "Yau da safe fa" Ta kallesa murya can kasa tace "Kafafuwana suka fara min ciwo da na tashi, anjima kuma duk jikina ya fara min ciwo" Ya langwabar da kai yace "Ikon Allah, suna maki haka ne?" Kai ta gyada masa, yace "Toh kina shan wasu magunguna ne?" Kai ta gyada masa, yace "Kin san sunan su?" Ta gyada masa kai, yace "Can you write them down for me now?" Tace "Sure" farar takarda ya ajiye mata da pen, nan ta rubuta masa gaba daya drugs dinta har da na shafawa ta mika masa takardan ya amsa yana dubawa, bayan few seconds ya daga kai yana kallon Mujaheed dake kallonsa shi ma, kafin yace komai Mujaheed yace "Rubuta mata injections taje ayi mata" Likitan yyi yanda Mujaheed yace, Mujaheed ya amshi takardan yana kallon alluran da ya rubuta mata sannan ya mika ma Imaan da ta kife kanta da table yace "Karba kije nurses su maki alluran" ta dago da sauri tace "Yaya allura kuma, ni doctor na baya min allura magani kawai yake ban" ya jefa mata wani kallo yace "Sai ki jira ya dawo ya ci gaba da baki maganin, nan kam allura xa a maki, get up my friend" a d'an tsawace ya karasa maganan, Ta amsa lkci daya hawaye ya cika idonta ta juya ta fita office din, a hankali Dr Mukhtar yace "Is she a sickled cell patient Mujaheed?" Mujaheed ya girgixa kai yace "Not at all, She is only carrying the trait, a carrier" da mamaki Likitan yace "But it's almost mimicking the disease" Mujaheed ya buda hannu yace "Mu ma haka muka gani" Dr Mukhtar yace "Subhanallah, this is kind of rare, Allah ya bata lafiya" Mujaheed yace "Ameen" Dr Mukhtar yace "Kasan alluran are strong, ta ci abinci kuwa?" Mujaheed ya mike da sauri yace "I don't know, bari in tambayeta, kafin in dawo plss kayi prescribing drugs in addition to hers" daga haka ya fita, injection room ya shiga bayan nurses din sun sanar masa suna ciki xa a mata alluran, tsaye take tana hawaye nurse din ma na tsaye rike da alluran sai kallonta take, tana ganin Mujaheed tace "Yauwa Dr ta ki fa" Mujaheed ya hade rai yace "Are you a baby? Waye kike son ba wahala, xan maida ki gida da ciwon ki ne idan baki yi respecting kan ki ba" ta fashe da kuka bata ce komai ba, Yace "Kin ci abinci?" Cikin rawar murya tace "Na sha shayi kadan amma yunwa nake ji" wani kallo ya dinga mata, can ya kalli nurse din yace "Nurse let me get her something to take plss" nurse din tace "Ba damuwa Dr" daga haka ya fita, nurse din ta nuna mata kujera ta xauna. Rike da malt Mujaheed ya dawo injection room din, ya bude sannan ya mika mata, Kadan ta sha xata ajiye yace "Wa za ki ajiye ma" ta hadiye na bakinta da kyar tace "Xan sha idan an gama min" nurse din tace "Aa ki kara kadan" da kyar Imaan ta kara malt din sannan nurse din tasa ta tashi, ta mike ta fashe da kuka tana kallon Mujaheed tace "Wllh tsoro nake ji xai min xafi" nurse din tace "Baxai maki ba kuwa" Mujaheed yace "Xan fa tafi in bar ki a asibitin nan kina bata min lkci" tace "Don Allah kai ka min plsss" yace "Baxan yi ba, kin tsaya ko inyi tafiyata" da kyar ta isa kusa da nurse din, ta kallesa ta mika masa hannu jikin rawar murya tace "Don Allah ka rike min hannu Yaya" bai san lkcn da yyi murmushi ba ya karasa inda suke, ta kama hannunsa ta runtse ido, nurse din tace "Me yasa baki sa under skirt ba?" Ta turo baki tace "Ni bana so" nurse din tayi murmushi, ta daga mata abayar jikinta, rungume Mujaheed tayi ta kwantar da kanta kirjinsa, cikin rawar murya tace "Wayyo Yaya don Allah kace ta min a hankali, kar ta min da xafi" Mujaheed ya amshi alluran hannun nurse din yayi mata, xaro ido tayi tana cewa "Yaya ta sa alluran? Don Allah tayi a hankali, tuni ya amshi dayan alluran yyi mata shi ma, sae da ya cire syringe din ta sakar masu ihu duk tunaninta lkcn xa ayi alluran, ya turata daga jikinsa, ta dinga xaro ido, nurse din tayi dariya tace "Toh ba gashi har an gama ba" Imaan ta zaro ido tace "Da gaske? To ban ji sanda aka cire ba" Mujaheed dai ko kallonta bai yi ba yyi disposing syringe din ya nufi kofa, nurse din tace "Ki fa danna wajen sosai idan kun koma gida" Imaan ta gyada mata kai tana goge idonta har sannan tana mamakin wai har an mata allura don bata ji zafin da take ta jira ba, ta dau sauran malt dinta ta fita, xaunawa tayi reception ganin bata gansa ba, bayan kusan minti goma sai gashi ya sakko, yana kallonta ya nufi kofa, da kyar ta mike tace "Yaya na fara jin jiri" yace "Toh ko in bar ki a nan" da sauri ta girgixa masa kai ta isa gunsa, saura kadan ta fadi gun fita, ya kalleta sau daya yyi gaba, back seat ta shiga ta kwanta tana maida numfashi, ya shiga motar ya tada suka bar asibitin, wani pharmacy ya tsaya xai fita tace "Yaya wllh idona juya min yake" nan ma dai bai tanka ta ba, drugs dinta da sabbin da Dr Mukhtar yyi prescribing ya siya mata sae lucozade boost babba biyu, duk ya ajiye bayan motar, har suka isa gida yyi parking a parking lot din daddy bacci Imaan take, daga cikin motar ya dinga lekan apartment dinsu gabansa na faduwa, ya juya ya kalleta, sannan ya fito daga motar, ya bude back seat yace "kee" bude ido tayi da sauri, yace "Sakko" ba musu ta fito daga motar da kyar, ya dau magungunan da drinks din ya rufe motar, da sauri ya juya ganin kiris ya rage ta fadi ya kara kallon apartment dinsu, kamo hannunta yyi ta jingina jikinsa. Har suka isa bangarensu, ya bude kofar ya shiga parlon hade sallama, Imaan ta kwanta saman kujera ya ajiye drugs din hannunsa da lucozade boost ya kalleta kafin yace komai daddy ya fito parlon, yace "Har kun dawo kenan?" Mujaheed yayi kasa da kai yace "Eh mun dawo Abba" dukawa yyi ya dau ledan maganin ya fiddo gaba daya, ya bude wanda xata sha a lkcn yana kallonta yace "Tashi ki sha magani" Daddy ya tafi kitchen don dauko table water da cup, Mujaheed daure fuska kamar tana ganinsa yace "Baxa ki tashi ba?" A hankali ta bude ido ta mike xaune kamar xata yi kuka, daddy ya iso parlon ya ajiye ruwan da glass cup yace "So how much is the bill doctor" kallonsa Mujaheed yyi, sai kuma yyi murmushi yace "Bill kuma Abba" Daddy yace "Eh ba asibiti ku ka je ba, ga kuma drugs ka siyo" ya girgixa kai yace "A'a Abba, I have settled everything, Allah ya bata lafiya" daddy yace "Toh madalla, Allah ya yi albarka" Mujaheed ya debi ruwan ya mika mata tare da drugs din ta amsa, tana runtse ido ta kai baki sannan ta sha ruwan, mikewa Mujaheed yyi yace "Xan koma daddy Allah ya bata lafiya" Daddy yace "Ameen thanks Son" daga haka ya fita parlon, daddy na kallonta yace "Toh tashi ki shiga ciki ki kwanta" ba musu ta mike ta wuce bedroom dinta. Mujaheed na shiga parlonsu ya kalli mahaifiyarsa dake sakkowa downstairs, kai kana ganin shirin da tayi kasan fita xata yi, Anty dake parlor tana kokarin sa turaren wuta a burner ta kalli Mujaheed tace "Har kun dawo kenan, ya jikin nata?" Gabansa ya fadi sosai, ya hadiye abu da kyar yace "Eh na dawo" Anty tace "Daxu Abban ku ke gaya min ka kai Imaan asibiti, da naga breakfast dinka baka yi ba" kasa cewa komai Mujaheed yyi, ya d'an saci kallon Umma da ta tsaya stairs tana kallonsa baki bude, Anty tace

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment