Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

motoci can ba" Maimoon ta sauka da sauri, Imaan ta dinga dariya har da kyakyatawa, Kamar yanda inna tace Mujaheed ne ya ja su, ita, Seeyama da kawayenta biyu sai Imaan, suna hawa main road inna tace "Toh yau dai Seeyama gashi xa mu kai ki dakin ki, duk da dai mijin naki wani ga6o ga6o ne kiyi masa biyayya iya yanda xa ki iya, ni baxan ce kiyi hakuri yaje ya kashe mana ke ba gaskiya, bbu xancen xaman hakuri, mu dai da aka cuta da hakan aje a haka, amma duk kika ga abinda baxa ki iya dauka ba yafa gyalenki ki dawo gida, ko ki tafi sashin ubanki ko ki tafi sashin kaninsa ko kuma ki yo sashina sai iya Inda karfin mu ya kare na kwatar maki hakkin ki, ni fa tun daga lefen da ya hada maki dama na raina masa aji...." Mujaheed da takaici ya ishesa yace "Haba inna yanxu fada kike mata ko hudubar tsiya?" Inna ta hade rai tace "Ka ji min yaro da aka haifa ina tsaye bakin kofar asibiti daga safe har dare, kai xaka koya min xaman duniya Mujaheed, ko ance maka ban san abinda nake bane, to bari kaji ko kai yau aka daura ma aure iyakar abinda xan gaya ma matar kenan don ni yar gaskiya ce, akan me xa ayi ta wani ce ma mace tayi hakuri gidan miji ana cutarta ana musguna mata, Allah kadai yasan me yasa ya halitto ni a mutan da ba na yanxu ba, kuma ai bance kada tayi masa biyayya ba kawai idan taga xai takata ta gudo gida, ina laifin wannan shawara tawa??" Kawayen Seeyama dai sai kallon inna suke k'asa k'asa, inna ta ja tsaki tace "Tun da shaidan duk na makale gefen xuciyar ku ba dole kaji haushin abinda na fada ba, maxa dai sun xama masifa yanxu, duk halinku daya dama, yo banda halinku daya ya wuce idan yace xai walakanta maka kanwa ka matse gantalalle ka nakada masa duka tunda ga irin sa kamar tsinken sakace, wllh xaka iya dukansa" Seeyama dake hawaye cikin gyalenta ta fashe da dariya, imaan na taya ta, shi dai Mujaheed bai ce komai ba yana mamakin warce Allah ya basu matsayin kaka.....


*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee wllh*🤷🏻‍♀️

It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello JiddahSuna isa gidan bakin inna ya mutu murus sai 'yan idanuwa ganin gida ne ba na wasa ba, ni ko nace dama Umma ce xata yarda 'yar ta ta auri mai rufin asiri kawai?? Inna ta fito cikin motar tana cewa "Fito da kafar ki ta dama in sha Allah gidan xama ne, yi nayi bari na bari, aure kuma da kike gani d'an xaman hakuri ne duk shi muka yi muka kawo yanxu da rai da lafiya, Allah ya maki albarka yasa gidan ki ne ke kadai don na xauna da kishiyoyi ban ji da dadi ba, kishiya masifa ce" Wani kallo Mujaheed ya dinga mata, inna na washe hakora tana kara kallon katon gidan tace "Toh kai Mujaheed baka da abinda xaka ce mata ne ka tsaya wani sandandan kana kallonmu, wannan ai ya ma fi gidanka girma wllh" Yace "Kece baki mata nasihar tun a gida ba amma ni nayi tun a can" Kuka kawai Seeyama take, inna ta hade rau tace "Ji shashanci don Allah, to ki bude ido ki ga gidan mana idan ba sae kin daina shegen kukan nan ba" Mujaheed ya karasa kusa da ita yana kallonta yace "Be the best wife you can be lil sis, wishing you a peaceful married life" rungumesa tayi tana kuka, shi ko ya dinga kallon imaan da ta ja can gefe tana 6a66aka dariya har da rike ciki, ganin kallon da yake mata ta shige cikin gidan da sauri bata kuma fasa dariyar ba, cike da damuwa Inna tace "Ni dai wllh wannan 'ya ta Bukar gani nake kamar ciwace ciwacen ta ya shafi kwakwalwarta, to banda haka taya xa a kawo yar uwarki dakinta tana kuka, ke baki bata hakuri ba kina dariyar mugunta, to Allah dai ya kai mu naki kiga iskanci wllh" tana fadin haka ta janye seeyama tace "Mu shiga ciki kiyi kukan a tsanake kin ji jikalle, kai kuma Mujaheed bayan isha ka xo ka daukeni, idan kuma ya kama a nan xan kwana to shikenan" daga haka suka wuce ciki shi kuma ya fita compound din da motarsa yana girgixa kai. Bayan Magrib da rashin arxiki inna ta sallami duk kawayen Umma yan kawo amarya, Aunty da Ammi dama basu dade ba suka bar gidan, tsaye inna tayi bakin kofa rai bace tana cewa "Wannan ai ba yi bane, sai kace baku da maxaje baku da mafada, amarya dai ga ta an kawota lafiya har ta hakura ta daina kuka, to ai kuma sai kowa ya kama hanyar gidansa sai kuma wata shekarar idan ta haihu, amma duk kun wani ja6e ba niyyar tafiya, a dai dinga jin tsoron, ni ma nan da ku ka ga ban tafi ba kakar ta ce, ni na haifi ubanta Ahmadu, bai baci ba ko da cewa nayi xan kwana, amma mutane karere kawai ku cika gidan yarinya kun ki tafiya, ko ita Rukayyar ce tace ku kwana tare da su bani da labari? To ni dai ba ruwana" Wa enda suka fita iskanci yi suka yi kamar basu ji abinda take cewa ba, wasu kuma haushi yasa duk suka bar gidan, a fusace inna tace "Mata wasu katangala kawai rai ba ga ta sun xaune ma yarinya a gida, ni ban taba ganin haka ba tunda uwata ta haifeni, ku barta daga ita sai kawayenta su ma a xo a sallamesu su kama gabansu mana" Inna na kallon imaan dake kokarin fita ta gefenta tace "Ke kuma ina xaki sanyi ya kare maki ki cuci d'a na da kashe kudi?" Imaan ta turo baki tace "Ina xuwa ni dai" inna tace "Toh kar dai kiyi nisa don Mujaheed ya kusa xuwa yanxu, ba ruwana in kwana su Ahmadu su min fada" imaan bata ce komai ba ta fita, tana ganin motarsa ta gane don layin tamkar rana saboda hasken fitilu, ta karasa gun motar ya bude ya fito yana kallonta, Ta sunkuyar da kai tace "Ina yini" yace "Lafiya lau Imaan, nan ne gidan sistern naki?" Kai ta gyada masa, yace "Maa sha Allah, Allah ya basu zaman lafiya" tace "Ameen" yace "Amma ba nan xaki kwana ba dai koh?" Ta xaro ido tace "In kwana kuma?" Murmushi yyi ya rungume hannu sa yace "Shi na gani ai, Idan kika kwana ai xaki yi inconveniencing amarya da angon" turo baki tayi tace "Toh ni dama ta ya xan kwana" yar dariya yayi yace "Gaskiya ne, yaushe xa ku koma gida?" Tace "Muna jiran yaya ne, xai maida ni da Maimoon da Grandma dinmu" yace "Ohk yayanku kenan" ta gyada masa kai, yace "Idan bai taho ba let me drop you people mana" ta xaro ido tace "Bayan ma yana hanya yanxu, ai shi ya kawo mu" Yace "Ohk then...." Bata kuma cewa komai ba, shi kam yyi shiru yana kallonta, a hankali yace "Kin yi kyau" Dauke kai tayi tana murmushi, shi dai bai fasa kallonta ba, murya can ciki tace "Kai kuma baka sa glasses dinka yau ba" wara ido yyi yace "Ya 6ata.... sai dai ki siya min wani" ta kallesa tace "Da gaske?" Yana murmushin sa mai kyau yace "Yea" Sunkuyar da kanta tayi, yace "Ko baxa ki siya min ba" Ta d'an kallesa tace "Xan siya" yace "Toh yaushe xan xo amsa?" Tace "Idan na siya" yace "Toh gobe nake so, I can't do without it" da sauri ta kallesa sai kuma ta dauke kai tana murmushi tace "Toh Allah ya kai mu" yace "Ameen... Da yamma xan xo amsa" ta girgixa kai tace "A'a kawai ka bar shi next tomorrow" Shiru yyi yana kallon bayanta.... Can yace "Or wancan ne yayan naku?" Imaan ta juya da sauri taga motar Mujaheed yayi parking, ta gyada masa kai a hankali, tunda Mujaheed yyi parking d'an nesa da su dama yake kallonsu, Sadeeq yace "Tunda ya gan mu bari in je mu gaisa" shiru tayi da farko, ganin yanda yake kallonta a hankali tace "Is it necessary?" Yayi murmushi yace "Baki son yan gidanku su san ni kenan?" D'an bude ido tayi tace "Toh kaje ku gaisa ni xan shiga ciki in kira su Maimoon" yace "Ohk" gate ta nufa tana satan kallon Mujaheed da ya bi ta da kallo gabanta na faduwa, Sadeeq kuma ya nufesa, sauke glass Mujaheed yyi ya bude motar ganin sadeeq, ya fito yana kallonsa directly cikin ido, sadeeq ya masa sallama hade da mika masa hannu, sai bayan kusan seconds biyar Mujaheed ya mika masa nasa yana d'an murmushi wanda iyakarsa lips, nan suka gaisa... Cikin cool voice Sadeeq yace "I am Dr Abubakar Ahmad" Mujaheed ya gyada masa kai kamar baxae ce komai ba, sai kuma yace "Muhammad Ahmad" Sadeeq yace "Maa sha Allah it's nice meeting you" Mujaheed yace "Same" Sadeeq yace "Alryt xan koma, sae da safe" Mujaheed yace "Ohk... kun yi sallama ne" Sadeeq yace "Sure" daga haka ya nufi motarsa ya shiga ya wuce. Inna bata fito parlon Seeyama ba sai da ta kada kan sauran mutanen dake parlorn, har Mujaheed ya gaji da jira cikin mota, Inna ta fito gate tare da Maimoon da Imaan ta shiga bayan mota tana cewa "Mujaheed kaga Gantalallu kila da so suka yi su kwana a gidan, don da ban masu jan ido ba baxa su tafi ba, ni dai ba ruwana" Maimoon ta bude front seat ta shiga, imaan ta shiga back seat gun inna, Mujaheed dai bai kulata ba yyi reverse, Inna tace "Ni bikin Imaan da na Maimoon ma gaskiya sae na xabi wa enda xa su raka su daki, iyaka kawai in xauna bayan mota ni da su don ina fatan ya xamo rana daya, Mujaheed ya ja mu in kai su dakunan su ya maida ni gida idan Allah ya yarda, ba katuwar da xata bi mu" Mujaheed dai driving yake har ya bar layin ya hau saman titi, lkci lkci ta madubi yana kallon imaan da ta ki yarda ta kalli gaban motar, inna tace "Mujaheed kaga kawayen uwar ka kamar mayu kuwa, wllh da kyar na kora su, duk sun ban wahala, ita ina ta samo su haka wasu lafta laftan mata ba kyan gani kamar aladu? kaii Rukayya dai shahararriyar mahaukaciya ce wllh" taka brake Mujaheed yyi bayan ya tabbatar bbu motar dake bayansa ya gangara gefen titi, inna ta saki salati tace "Lafiya Mujaheed, me ya sami motar" ya bude motar ya fita ya bude side dinta yana kallonta yace "Ita uwar tawa ce mahaukaciya?" inna ta bude baki tana kallonsa, sai kuma ta kalli Imaan tace "Ga reshen bishiya can, sauka ki karyo ki kawo masa...." Imaan ta hade kai da kafarta tana dariya kasa kasa, a fusace inna ta kunduma masa xagi tace "Na ce mata mahaukaciyar sharri na mata, da hankalinta ina ita ina gunduma gunduman matan da ta ajiye matsayin kawaye, wasun su idan suka xaune kanta shegiya nake idan bata suma ba bayan sun latse ta" yace "Ku saukar min a mota ku samu wanda xai kai ku gida Hajiya" kamar jira Inna take ta sauka da sauri tana kallon Imaan tace "In dai kin san motar ba ta Bukar bace ki sakko ki bar masa tsiyar sa" Imaan ta hade rai tace "Inna bai ce har da mu ba fa" Irin kallon da Mujaheed yyi mata yasa ta sauka da sauri don ya dade bai mata irin kallon ba, Inna ta kalli Maimoon tace "Ke kuma idan ba ta Amina bace motar ki sakko kema" Maimoon ta bude front seat ta sakko, inna ta fara matsar kwalla tace "Ku sama min Adaidaita sahu" ko kallonta Mujaheed bai yi ba ya rufe back seat dinsa ya shige motarsa ya kara gaba, inna ta bi motar da kallo tace "Allah dai ya isa, kuma sai Ahmadu ya min iyaka da Mujaheed yau, ni xai toxarta ya walakanta a bakin titi a kan Rukayya" Imaan ta tsayar da adaidaita ta fada masa inda xai kai su, Mai adaidaita yace "Ba can xan yi ba" bai gama rufe baki ba inna ta shige adaidaitan ta xauna, Imaan da Maimoon suka saki baki suna kallonta, Mai napep din ya juya yana kallonta yace "Baaba nace ba can nayi ba" a fusace tace "Dalla can mu je d'an nan, ko baka ganin dare yyi ne xaka ce min ba can kayi ba, jika na ne fa ya watsar da mu a titi yanxun nan yyi wucewarsa daga nayi ma katuwar uwarsa gyara, banda haka yaushe xaka gan ni bakin titi tsaye da gata na, motocin 'ya yana sun fi biyar wllh, ko da yake in mun je gidan ma xaka gane abinda nake nufi, ko kai so kake inyi ta tsayuwa kamar yar iska bakin titi?" Shiru yyi bai ce komai ba, Inna ta kalli su Imaan sannan ta kallesa tace "Yaro idan baxa su shiga ba ja ni ka kai ni gida, su kuma Allah ya kawo masu mafita, mu je ni dai" murmushi mai napep din yyi, Imaan ta turo baki ta shiga Maimoon ma ta shiga, inna tace "Atoh da kun tsaya jiran d'an sahun da xai je ku kwana a wajen" suna isa gida dama inna ta sauka napep din ta nufi gate tana gyara yafin mayafinta, Maimoon ta kalli Imaan dake dariya ta ja tsaki ta bude jakarta ta fiddo dubu daya ta basa ya bata canji ta wuce ciki, can suka ga inna har ta shige parlon su Maimoon, Imaan ta nufi part din su Maimoon ta bi bayan Inna, babu kowa parlon Abba hakan yasa inna ta dawo main parlor tana kallon mutanen da ta wuce da farko tace "Ahmadu baya nan ne" Daga kitchen Aunty ta leko tace "Bai shigo ba inna, kun dawo lafiya?" inna bata tanka ta ba ta fice parlon, bata tsaya ko ina ba sai part din su Imaan, ba kowa parlon sai kamshi dake ta tashi, cikin daga murya inna tace "Salama alaikum" Imaan ta bude kofar bedroom dinta tana lekowa, Inna tace "Ina Bukar din?" Daddy ya fito daga daki yace "Har kun dawo inna" karasawa cikin parlon tayi ko takalmanta bata cire ba ta xauna saman kujera tana share guntun hawayen idonta, Ammi dama na jin irin sallamar da inna tayi tasan ba lafiya don haka bata fito ba, duk xaton ta k'aran imaan ta kawo, Imaan da har ta cire kayanta ta sa Hijab kawai ta fito da sauri, Daddy na kallon inna a hankali yace "In ji dai lafiya inna" a fusace tace "Ina fa lafiya Bukar, shegen d'an ku ya watsar da ni tsakiyar titi gefen jaji yayi wucewarsa, daga nayi ma Rukayya gyara" Shiru Daddy yyi yana kallonta da mamaki, ta fashe da kuka tace "Gaskiya Bukar idan ba a bi min hakkina ba yau duk a station xa mu kwana gwara in kai karar can a bi min hakkina, da girmana da matsayina da martabata Mujaheed xai juye ni tsakar titi yyi wucewarsa?? Ae wannan babban magana ce wllh" Daddy ya sauke ajiyar xuciya yace "Subhanallah me ke damun Mujaheed haka" Inna ta tsaida kukan da take tace "Toh ai ba ni xaka ma tambayar ba, waya xaka dauka yanxu ka kirasa, kada ma ka nuna masa ina nan, kawai ce masa xaka yi ya xo xaka aikesa yanxun nan, daga nan sai kaji me ke damunsa ko wiwi ya fara sha bamu sani ba" Daddy ya kara sauke ajiyar xuciya, inna tace "Sae wani sauke sauken ajiyar xuciya kake Bukar, ko tsoron sa kake ne inyi ta kai na?" Yar dariya kawai daddy yayi ya dau wayarsa, inna ta tsuke fuska tace "Wllh yanda ya min tijara a kan uwarsa kai ma haka xaka masa tijara akan taka uwar, kuma idan baka ce masa aikensa xaka yi ba wllh baxai xo ba nan kuma xa mu kwasa mu tafi police station " Daddy dai bai ce komai ba yayi dialing number Mujaheed ba a dau lkci yana ringing ba ya daga, Daddy yace "Muhammad kana kusa ne?" Daga daya bangaren Mujaheed yace "Eh Abba" daddy yace "Toh ka xo parlor na yanxu" Mujaheed ya d'an yi shiru, kafin yace "Toh Abba" Daddy yace "Don't keep me waiting fa naji kayi shiru ko baka kusa ne?" Yace "Ina nan" Daddy yace "To ina xaune ina jiranka yanxu" Mujaheed yace "Toh" daga haka daddy ya katse wayar, inna tace "Kai xaka kwana a ciki wllh idan yaron nan bai xo ba Bukar" Daddy dai bai ce komai ba, Mujaheed ba don yanda yake jin kunyar daddy ba da fa ba xai je ba don yasan sarai inna na can, kuma da Abbansa ne ma ya kirasa ba lallai yaje ba, jallabiyarsa kawai ya xura ya fita dakinsa, banda girgixa kafa babu abinda inna take, da sallama ya shiga parlon, ba tare da ya kalli Daddy ko ita ba ya tafi ya xauna kasan lallausan carpet din parlon yace "Barka da dare Abba" Daddy yace "What happened between you and ur grandma yanxu?" Mujaheed ya daga kai yana kallonta yaga yanda ta wani tsuke fuska tana kallon sa, ya maida kansa kasa, inna na nuna Imaan dake kwance kan kujera tana kallonsu tace "Idan sharri na masa ga 'yar ka kwance kusa da kai ka tambayeta ka ji ko ba tsakiyar titi ya juye mu ba" Daddy ya juya ya kalli Imaan, a fusace Inna tace "Ke tashi xaune ki basa labarin abinda ya faru, ba tsakiyar titi Mujaheed ya sauke mu ba, naga kamar tantama Bukar yake" Imaan ta mike xaune tace "A'a ba fa tsakiyar titi bane inna, gefen hanya ne....." Rai bace Inna tace "Amma wannan anyi shegiyar 'ya... Dama akwai bambanci tsakanin gefen titi da tsakar titi, ke dai munafuka ce wllh" Imaan ta harareta ta gefen ido tana turo baki ta koma ta kwanta, Inna tace "Wllh Bukar gefen hanya yayi watsi damu, kuma kafin ya sauke ni don Allah mai yace min Imaan" da sauri Imaan ta daga hannu tace "A'a ba ruwana nima ban sani ba" Bude baki inna tayi tana kallonta, daddy yace "Yanxu dai ki tashi ki tafi ki bar ni da shi inna" inna tace "In tashi in tafi ka basa hakuri shima ya tafi xaka ce min" Tana fadin haka ta mike tace "Tun farko ma ban san me ya kawo ni gun Bukar ba, duk inda Ubansa ya tafi ai ya ci ace ya dawo yanxu" daga haka ta fice parlon fuska daure. Daddy ya hade rai yana kallon Mujaheed yace "Saboda baka da kirki xaka ajiye su bakin hanya Muhammad?" Mujaheed yyi kasa da kai bai ce komai ba, Daddy yace "Yanxu ka kyauta kenan, idan Hajiyar ka ce ko min abinda tayi maka xaka mata haka?" Yace "Kayi hakuri Abba" Daddy yace "Haba Muhammad, I am highly disappointed at you, this is very rude and stupid of you, she is our mother fa, no matter how she behaves baxa mu canxa ta ba" Mujaheed bai iya cewa komai ba, daddy yace "Ka tashi ka bi ta ka bata hakuri yanxu" yace "Toh, ayi hakuri Abba" Daddy ya kalli imaan yace "Ke kuma I've warned you times without number ki daina fada mata magana anyhow amma baki ji ko, xan fara sa6a maki soon wllh idan baxa ki canxa naughty attitude din nan ba, will you dare talk to ur mother that way?" mikewa xaune tayi kamar xata yi kuka, Mujaheed ya tashi yace "Xan je in sameta yanxu Abba" daga haka ya fita parlon. Washegari da safe da kyar imaan ta tashi tayi wanka tayi breakfast da Ammi ta ajiye mata a dinning, Ammi tace "Idan kin gama ki dau magungunanki ki sha kada in tuna maki, kuma da Ac kika kwana ko?" Ta xaro ido tace "Ammi wllh A'a" Ammi tace "Toh ga mura nan na shirin kama ki" Ta langwabar da kai tace "Jiya fa da daddare a napep muka dawo, kin ji sanyi kamar xanyi freeze a hanya" Ammi ta fiddo kindirmo a fridge yayi sanyi sosai ta ajiye mata a dinning din tace "Gashi ki kai ma inna inji daddyn ki, you make sure kin goge min dinning table idan yayi stain" Ta marairaice tace "Ammi my legs are aching me fa" Ammi ta harareta ta wuce dakin ta, Imaan na gama breakfast ta tashi ta dau kindirmon ta tafi kai ma inna, Tana shiga parlon bayan ta ajiye tana kallon inna dake ta kukkula dubulan da cin cin a leda sai ga Umma ta shigo parlon da sallama, Inna ta kalleta ta ci gaba da abinda take ta amsa sallaman ba yabo ba fallasa, Umma ta dafa kujera tace "Ina kwana inna" inna tace "Lafiya lau" Umma tace "Ya gajiyan taro" inna tace "Bana tare da gajiya duk ya bi lafiyar gado" Umma tace "Toh Alhmdllh Allah ya saka da alkhairi yaji k'an mahaifa" inna tace "Ameen" karasawa tayi kusa da inna ta ajiye ledan hannunta tace "Ga wannan dai ba yawa" inna na kallon ledan tace "Meye wannan din? Ke imaan xo ki bude" imaan dake xaune ta mike ta karasa kusa da Inna, Umma ta bi ta da kallon gefen ido, durkusawa tayi ta bude ledan ta ciro atamfa da pack din sabulu guda biyu da turare mai tsada" Inna ta bude atamfar tana kallo da kyau, tace "Holland ce wannan din?" Umma tace "Ehh" inna ta tabe baki tace "Toh, da dai basirar ki ce hakan da sai ince Allah yyi albarka, amma wannan ko kaffara baxan yi ba Ahmadu ya sa ki, Allah ya masa albarka ya kare min shi duk inda xai shiga, Allah ya ci gaba da hada kansu da d'an uwansa Bukar ya raya mai 'ya yansa yayi masu albarka, ita kuma wannan da ya aurar Allah xaunar da ita da mijinta lfya, ke kuma nagode da isar da sako" Umma ta dinga kallonta ko kiftawa babu, Imaan sai danne dariyarta take, Inna ta ci gaba da kulla dubulan dinta a leda, Umma tace "Sai anjima" inna tace "Mu jima da yawa" daga haka ta nufi kofa, inna na kallon Imaan tace "To ke sai kiyi ta kanki, don wllh jiya Mujaheed ce min yyi xai kakkarya ki ya xane ki, wai ya ganki da wani mai mota a tsaye a kofar gidan seeyama, imaan ina kuma kika samo mai mota kike ta boye min ban sani ba ni Asabe??" Umma ta d'an dakata bakin kofa jin abinda inna ke cewa, Imaan ta turo baki tace "Shi sa ma xan tashi in tafi yanxu kar ya xo nan, to har kun shirya ne inna?" Inna tace "Haba dai sai kace wata yarinya, to me yyi min da baxa mu shirya ba, wai na ce ma Rukayya mahaukaciya, ke ki ji fa? to me ta min xan xageta banda abunsa ma dai, kawai daga ina mata gyara? Ni fa na yarje ma Ahmadu ya aureta wllh, baki ganta ba a lkcn yar siririya yanda kika ganki, kamar iska xai hure 'yar banxa ta fadi, gashi iyayenta basu da komai basu kuma ba wani ajiya ba, wani d'an akurkin gida fa gare ubanta a lkcn, to ni ban masu bakin ciki ba don xuciya ta fess mai kyau ne na yarda Ahmadu ya auro mana ita a haka, ke kinga wahalar da nayi da ita kuwa? Wllh kare baxai ci ba, gashi ba abinda ta iya a lkcn, har girki ni ke sa ta kan hanya ina koya mata, kishiyoyina su yi ta jin haushi yanda nake ji da ita bana son ko k'uda ya ta6ata har dai ta samu cikin wannan yaro Mujaheed, sai kin ga wahalar da nayi mata sbda laulayin da ta dinga yi ba kakkautawa, to ni duk ba wannan ba don nasan sakayya ta dai na gun Allah, to don kuma yanxu
DOWNLOAD
DOWNLOAD

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

1 year ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

4 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment