Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Rukayya ta xama abinda ta xama sai me xai dameni ni patuu? ga dai Amina na bina sau da kafa ga Aisha, ni dai abinda na sani shine Mujaheed ai xai yi auren, to nan xata d'an dana ko da dadi ko babu, abinda duk abinda ka shuka shi xa ka girba, tsaf xan karance ma yarinyar xaman da xata yi da ita, muna nan da ku sai an dinga xuwa daukata shari'a a mota...." Imaan har wani kwanciya tayi kan kujera tana dariya amma ba mai sauti ba, Umma da ta makale jikin kofa ta fita ta sa takalmanta, inna ta tabe baki tace "Wllh Mujaheed da gwiwowinsa bibbiyu ya durkusa ya dinga ban hakuri tun ban kai ga gaya ma ubansa ba, to tunda naga yyi nadama kawai sai na yafe masa don ba halinsa bane gaskiya bai taba juye ni a tsakiyar titi ba tunda mu ke" Imaan ta fashe da dariya tace "Jiya dai ya juye ki ai"


*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻‍♀️

It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.19. Imaan









Umma na komawa bangarensu kallo daya tayi ma Mujaheed dake xaune dinning yana shan coffee tace "Ka sameni daki yanxu" sosai gabansa ya fadi ya bi ta da kallo har ta haura sama, bai iya ya karasa shanye coffee din ba ya mike ya bi bayan ta, tsaye ya ganta tana safa da marwa a dakin, Yace "Gani Umma" ta juya tana kallonsa fuska daure tace "Mujaheed ina son sanin meye matsalar ka don kaga shegiyar yarinyar nan da mai mota jiya har kake ikirarin hukuntata" ya xaro ido yace "Ban gane ba Umma" Ta masa wani mugun kallo tace "Bana son ka gane dama ai, warce kaje ka ba sakon take fadi yanxu naji, dama baka raba kanka da makiyan nan nawa ba har ynxu Mujaheed? Mujaheed ka gaya min meye hadin ka da yarinyar nan Imaan?" Yace "Haba Umma, ke yanxu maganar inna kike dauka, kila ma don ta ganki yasa ta kirkiri haka, ni a ina na ganta har muka yi wannan xancen da ita?" Shiru Umma tayi tana kallonsa, a ranta kuwa tunani take kila hakan ne ma, ganin Umma tayi surrender, Mujaheed yace "Kawai ta fada haka ne don ki sa a rai, ni yaushe nake da wannan lokacin ma a gidan nan yanxu" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Sae ma kaga rashin mutuncin da ta min kayan da na kai mata, ni na ma ji dadin da ta gane cewar in don ta nine baxan bata ko tsinke na ba, basirar Abban ku ne kamar yanda ta fada" Mujaheed yyi murmushi bai ce komai ba, Umma tace "Gobe xan baka sako ka kai ma Hajiya Mansura ta marafa, bata samu xuwa bikin ba amma ta bada gudunmawarta dubu dari, cin cin da su alkaki xaka kai mata daga nan nasan xa ku hadu da Safeenah, tana nan ba ta koma makaranta ba, ni so nake nan da 'yan watanni a fara xancen naka bikin" shi dai Mujaheed bai ce komai ba banda kallonta da yake, ta xauna gefen gado tace "Kar fa kace min ka manta gobe kayi ficewarka, xuwa sha biyu in sha Allah xaka kai masu, tunda gobe lahadi" ya shafa kai yace "Allah ya kai mu" daga haka ya nufi kofa ya fita. Imaan ta kara leka samirar dake cike da cin cin da dubulan da alkaki da inna ta basu su kai ma ta rasulu aminiyarta, ta tabe baki tace "Wllh duk kin kwashe ma tsohuwar, mu fa har ynxu ba mu ci ba" inna ta tsuke fuska tace "To ina ruwana da rashin cin ku, ni na aurar da 'ya ko ko? Kaji min dai, Dubu talatin ta rasulu ta bada a kawo min gudunmawa, kuma ace baxan cika mata samira da kayan flawa ba, ni ta ma fi min Aisha kiji in gaya maki" Imaan tace "Kice ma ta fi maki har daddy mana" Maimoon tace "Toh ina dubu talatin din?" Inna ta kalleta da sauri tace "Amina aka ce in ba wa da xaki tambayeni dubu talatin Maimuna? Ko ko kin ban ajiya ne? Ni dai ku daina sa min ido a gidan nan, idan ba haka ba mugun alkaba'i ba shi da kyau amma to xance kowa ya ci kansa gaskiya" Imaan ta kalli Maimoon tace "Maimoon karbo kudin motar mu wuce" Inna ta kunce ha6ar xaninta ta fiddo naira dari ta ajiye masu tace "Hamsin xai kai ku ya dawo da ku, nan nan kabala dai" Imaan ta ajiye samirar ta xauna tace "Tabdi ko naira dari dari ma baxa a yarda a kai mu ba balle hamsin" Inna tace "Barawo ne mai adaidaitan da baxai kai ku a hamsin ba, ko ya sha wiwi ne, wllh kullum a hamsin ake kai ni a dawo da ni" Maimoon tace "Saboda ke tsohuwa ce ai" A fusace inna tace "Oh oh Allah, idan baxa ku ba ku ajiye min kayana ku fita, Xan kira Bukar ko Ahmadu cikinsu wani ya kai mun, ku fitar min a parlor" Kin fita suka yi jin abinda tace wai xata kira daddy ko Abba, Maimoon tace "Toh wai don Allah mu muka siya masu adaidaitan da xasu kai mu a hamsin su dawo da mu a haka, ki kara mana kudin mu tafi mana" Inna ta jefa masu wani hamsin tace "Aniyar ku ta bi ku dai" Maimoon ta dau kudin tana gunguni tace "Ae sai dai mu cika da kudin mu" Imaan ta tabe baki ta dau samirar tace "Sai dai ke ki cika, sisina baxan kara a kai ba tunda ba ni xan ci cin cin ba" daga haka ta fice parlon, inna tace "Shi sa har yau aka kasa gano cutar da ta sa ki gaba, saboda mugun xuciyar ki da rashin kunya, ni dai Allah ya saka ma d'ana, Allah ya saka masa kan kudaden da yake kashewa a kan tsadadden ciwon nan naki, Allah kuma ya raba shi dake lafiya, ya aurar dake ya huta ma ransa mijin ma ya d'and'ana ukubar, ba a taba jin alkhairi ya fito bakin ki sai sharri, to meye kuma don kin cika kudin mota" Maimoon ta bi bayan imaan ta kullo mata kofarta tana turo baki. Suna tsaye bakin titi suna jiran adai daita da xai je kabala, Imaan tace "Ko da yake nasan tsohuwar da xa mu kai ma baxa ta bar mu haka nan ba, kila ta ba mu kudin mota" Maimoon tace "Wllh da ba dan Abba da tace xata kira ya kai ba ba inda xanje ni dai, kullum fa idan xata aiki mutum sai ta raba kudin motar xuwa wajen kashi uku ta baka daya" Imaan tayi dariya tace "Kawai so take ayi ta mana fada shi sa tace xata aiki daddy ko Abba" motar Mujaheed da suka gani yasa suka yi shiru suna kallon motar, shi ma daga gida ya fito, ya sauke glass yana kallon Maimoon, Maimoon ta marairaice tace "Ya M.A inna ce ta aike mu kabala kuma ba mu samu adai daita ba har ynxu..." Ya gyada kai yace "Toh Allah ya kawo adai daitan" xai dage glass da sauri tace "Wait... Kai ina xaka plss?" Yace "Marafa" tace "Toh ka rage mana hanya mana don Allah" ya mata wani kallo yace "Me ya hada Marafa da kabala?" Tace "Yaya ai duk hanya ce mu dai ko ina ma ka ajiye mu nasan xa mu samu a can gaba" yace "Toh shiga" Imaan ta bude back seat ta shiga ya dinga hararanta ta madubi fuska daure, dama tun da suka hada ido taga kallon da yake mata bata sake yarda ta kalli madubin ba, Maimoon na kallon fancy nylon dake gaban motar ta dauka tace "Ya M.A wa xaka kai ma cin cin da dubulan?" Yace "Anty" dariya tayi bata sake cewa komai ba, sai da suka yi nisa yace "Gidan Baaba ta rasulu xa ki kenan?" Tace "Xa mu dai, ai ba ni kadai bace, ni da Imaan ce" ya watsa mata wani kallo ta xaro ido tana yar dariya ta rufe bakinta, har kofar gidan aminiyar inna ya kai su, Maimoon sai murna take tace "Ya M.A mun gode, ko mu raka ka marafan mu ma?" Shiru ya d'an yi da farko yana shafa kansa a hankali, lkci daya yace "Toh kar ki dade a ciki idan ba haka ba inyi wucewata" bude motar tayi ta fita tana kallon Imaan da ta fita tuntuni tana cinno baki suka shiga gidan, dari biyar ta rasulu dake ta sa masu albarka ta basu kudin mota, tace "Ina gaida Hajiya Asaben, kuyi mata godiya sosai, ita kuma amarya Allah ya basu xaman lafiya da mijinta, ku kuma Allah ya maku albarka ya fiddo maku maxaje na gari" suka amsa mata da Ameen, sannan suka mata sallama suka fita da samirar don juye kayan ciki tayi a nata samiran. Maimoon na kallon imaan tace "Wai Imaan me yasa baki gaida ya Mujaheed yanxu?" Imaan tace "Saboda baya gaida Ammi na sai ya ga Daddy" Maimoon ta xaro ido tace "Da gaske?" Imaan tace "Ehh mana" Maimoon tace "Toh saboda me" imaan tace "Oho" bude back seat tayi ta shiga Maimoon ta shiga gaba ya tada motar yayi reverse ya bar anguwar. Tafiyar kusan minti sha biyar suka yi suka iso gidan Hajiyan Marafa, Dai dai gidan yayi parking daga kusa da flowers yana kallon Maimoon yace "Xan yi sllh kafin in shigo" ya mika mata ledan yace "You take this in with you" tace "Amma yaya bamu san kowa a gidan ba fa" yace "Sai ki ce Hajiya ce ta aiko ki, ina nan shigowa nace idan nayi sllh" daga haka ya fita motar, Imaan dai na tsaye ta rungume hannu jikin motar bayan ta fita, Maimoon ta fito ya kulle motarsa da lock, ya wuce masallacin da ya gani a layin, Maimoon ta kalli Imaan tace "Mu je" bin bayan ta Imaan tayi suka shiga gidan, bayan sun sanar da mai gadi gun Hajiya suka xo, duk girman gidansu haka suka saki suke kallon gidan, Maimoon tace "Ni dai baxan shiga ba gwara mu jira sa a nan, kawai mutum yaje yana ta introduction ana masa wani kallo" Imaan ta yi dariya tace "Sai kice Hajiya Rukayya ce ta aiko mu" Maimoon ta buda ido tace "Bari ya Mujaheed ya jiki, wai Hajiya Rukayya" Imaan ta tabe baki suka shiga babban balcony din dake dauke da kujeru sannan ga babban rug a shimfide kasa, kan rug din suka xauna suna kara k'are ma gidan kallo, sai bayan da aka idar da sallah Mujaheed ya shigo gidan, kallonsu ya tsaya yi ya hade rai yace "What did I tell you Maimoon?" Ta marairaice tace "Yayanmu mun yi sallama kamar basa parlor" hararanta ya dinga yi kafin ya danna bell, ko minti daya ba ayi ba mai aiki ta bude kofar, ta gaishesa ya amsa yace "Hajiya tana nan?" Tace "Wa xa ace mata" Yace "Dr Muhd, Kice Hajiya Rukayya ce ta bada sako a kai mata" Murya can kasa Imaan tace "Toh ba gashi shi ma cewa yayi Hajiya Rukayya ba" Maimoon ta yi murmushi bata dai ce komai ba, Mai aikin tace "Toh ka shigo" bin bayan ta yayi xuwa cikin parlon da sauri imaan ta mike ta bi bayansa, Maimoon na yar dariya ta tashi ita ma ta shiga parlon, wata yarinya da baxata wuce ashirin da daya bace ta shigo parlon daga dinning kallo daya tayi masu ta wuce sama, tsaki imaan ta ja Mujaheed ya kalleta ta cinno baki ta dauke kai, mai aikin ta kawo masu drinks da bottle water ta ajiye, bayan wani lkci sai ga Hajiyar ta sakko cikin shiga ta alfarma ganin Mujaheed tace "A'a ashe kai ne doctor" yyi kasa da kai yace "Ina yini Hajiya" tace "Lafiya Alhmdllh, ya Hajiya Rukayyar, fatan an watse taro lafiya" yace "Alhmdllh" xaunawa tayi tana kallo su Maimoon da Imaan dake gasiheta tace "Wannan kamar kanwar khadijah da tayi aure Us koh?" Ta fadi haka tana nuna Maimoon, Mujaheed yace "Ehh kanwarta ce" tace "Maa sha Allah ga kamanni na gani, to ita wannan fa" Mujaheed ya kalli Imaan da ta nuna, da sauri yace "Yar uwarsu ce" tace "Allah sarki shi sa ban santa ba" Maimoon ta mike ta ajiye abun hannunta kusa da ita tace "Gashi Hajiya tace a kawo maki" Hajiyar tace "To maa sha Allah, nagode kwarai Allah ya basu xaman lafiya" Bude kofar parlon aka yi, wata yarinya ta shigo parlon cikin English wear bata ko kalli wa enda ke xaune parlon ba xata wuce sama Hajiya tace "Safeenah lafiya na ga ranki a bace" Jin sunan da Hajiyar ta kira Mujaheed ya daga kai yana kallon yarinyar, ita ba doguwa ba kuma ba gajera ba, farin ta har yayi yawa and she is beautiful, lkci daya ya dauke kansa, Maimoon da Imaan kuwa kamar sun samu TV imaan har da juyawa gaba daya tana facing dinta, rai bace Safeenar tace "Wai ki ji mum ashe birthday din ma wani local waje xa ayi, sai kinga yanda raina ya bace bayan duk shirin da nayi, wllh Saleema koluwa ce I don't know what's wrong with her, ni ko gaya masu na tafi ma ban yi ba" Mujaheed dai sai danna wayarsa yake, Hajiya tace "Atoh gaskiya basu kyauta ba, to why not baki ce masu a canxa hall din ba, ko ke ba sai ki biya kudin hall din ba" Tsaki Safeenah tayi tace "Ni duk raina ya baci wllh Mumy" xata wuce sama Hajiya tace "Toh ga doctor ku gaisa" Juyowa tayi tana kallon cikin parlon taga Mujaheed da ya ki dago kansa, ta fi second goma tana kallonsa, kafin ta karasa cikin parlon ta xauna hannun armchair da uwarta ke xaune cikin sanyayyen murya tace "Ina yini" sai a sannan ya daga kai yace "Lafiya lau, ya kike?" Tayi wani sanyayyen murmushi tace "Lafiya lau" Ta kalli su Imaan tace "Sannun ku" Imaan dai tace "Yauwa" Maimoon kuma ta gaisheta, Hajiya ta kwalo ma mai aiki kira ta fito da sauri, Tana kallonta tace "Pepper chicken da ku ka yi daxu xa ki kawo masu tun da ba ku gama lunch ba" Mujaheed yace "Daga gida muke yanxu Hajiya, we ate before leaving, so we are okay" tun da ya fara magana Safeenah ke kallonsa ko kiftawa babu har ya dasa aya, Hajiya tace "Wannan ae is more or less a dessert, daxu yara suka ce suna son pepper chicken, shine nasa su yi, kuma da yawa sosai suka yi don nasan baxa a cinye gaba daya yau ba sai dai a ba masu gadi da almajirai" Mujaheed ya d'an yi murmushi yace "Ni dai I am okay" Imaan tace "Ni dai xan ci" kallonta yyi da sauri, Hajiya tace "Yauwa, bar sa yayi ta fulako dama yayi kama da fulanawan, ke ma ai xa ki ci ko" Hajiya ta fadi tana kallon Maimoon, Murmushi kawai Maimoon tayi ta sunkuyar da kanta, mai aiki ta dawo rike da tray da plates uku a kai, ko wanne dauke da kaxa da aka yi garnishing sai kamshi da turiri yake, Mikewa Safeenah tayi ta dau plate daya ta karasa kusa da Mujaheed ta ajiye masa, hada ido suka yi yace "I said I am okay baxan ci ba" tace "Kaci ko kadan ne pls" Daga haka ta koma ta xauna, a hankali Imaan ta xamo kasa ta fara cin kazar, sai kallonta Mujaheed yake ta gefen ido, Maimoon ta dau tsoka daya daga kan kujerar tana ci a kunyace, Hajiya tace "To ya aikin doctor, Hajiya Rukayya tace min ka dawo Kaduna da aiki gaba daya yanxu koh?" Yace "Ehh" tace "To da kyau, Allah yayi albarka" yace "Ameen" idonsa na kan wayarsa amma da ya dago sai yaga kallonsa Safeenah take, Hajiya ta mike tace "Toh bari in d'an shiga ciki...." Mikewa yyi da sauri yace "Wucewa xa mu yi ai, xan je gun aiki" tace "Da wuri wuri haka, ka dai ki shan ko ruwa ne kuma ban ji ddi ba" yace "Am sorry bana jin cin komai ne yanxu" Tace "Toh ai sai ka jira kanninka su gama tukun na ko?" Yace "Bana son in makara xuwa gun aiki ne Hajiya" tace "Toh shikenan, bari a masu take away da shi" Imaan tace "Toh" wani kallo Mujaheed ya dinga mata, Hajiya ta kwalo ma mai aiki kira ta sanar da ita tayi masu takeaway din kajin, Imaan ta mike tace "Ina xan wanke hannu" Safeenah ta nuna mata hanyar dinning ko kitchen, tare suka tafi da Maimoon suka wanke hannu suka dawo, Hajiya ta basu dubu biyar Maimoon ta amsa da kyar, tuni Mujaheed ya fice gidan suka bi bayansa, Hajiya ta kalli Safeenah tace "Baxa ki raka su ba" bin bayan su tayi ita ma. Mujaheed har ya shiga mota sai ga ta tare da su Maimoon, tana kallonsa tace "I don't even know ur name" ba tare da ya kalleta ba yace "I am Mujaheed" tace "That's nyc, I am Safeenah" kai kawai ya gyada mata, Tace "Toh sai yaushe?" Yace "Watarana" yar siririyar dariya tayi tace "Do you mind sharing your digit with me pls?" Yace "Ohk" mika masa wayar hannunta tayi ya amsa ya sa mata lambarsa da bai fiye amfani da ba ya mika mata, tace "Thank you" yace "You are welcm" Daga haka ya tada motarsa ya wuce, haka ta bi motar da kallo har ya fita layin, da sauri ta koma ciki tana kallon uwarta tace "Wllh Mum naji ina son sa sosai" Uwar tace "Haba, to ai shine wanda na maki magana a kai kwanaki kika ce ke ba ruwan ki da hade hade in rabu da ke, uwarsa ce dama ta kawo shawarar ba ni ba tunda nasan kina da samari iri iri" ta marairace tace "Mum ai ban san haka yake ba, ni wllh mum ina son sa har raina" Hajiya tace "To ai shikenan, bari anjima sai in kira mahaifiyar tasa dama kwanaki duk ta dameni da kira a kan hakan bana daukan kiranta" Safeenah ta sauke ajiyar xuciya ta xauna tace "kaiii... Ya hadu wllh, his beards are damn cute, his lips so sexy with those catlike eye, gashi dogooo, I guess he have got six packs daga ganinsa yana workout, dama kuma ni bana son namiji fari pau, wllh Mum gayen ya hadu sosai, kuma naga sai wani basarwa yake yana shan kamshi, to ai irinsu nake so" Tun da Imaan taga irin kallon da Mujaheed ke mata bayan sun dau hanya ta kagu su isa gida ta fice daga motarsa tayi ta kanta, gashi dama so take suna komawa gida ta dau Atm card ta tafi supermarket siyo ma Sadeeq abinda ta masa alkawari jiya, a kofar gida Mujaheed yayi parking tana jin ya bude lock din motar ta bude ta fita da sauri, fitowa yayi shi ma bai kai ga bin ta ba tayi tuntunbe bakin gate sai ga ta a kasa, d'agata yyi ta fashe da wani matsanancin kuka tana cewa "Wayyo yaya kafana ya gurde wllh" maidata gun motar yayi fuska daure ya daga kanta yace "Waye kika fita wajensa shekaranjiya da daddare" k'in cewa komai tayi sai kukan da take tana kiran daddy a tsorace, ya wani hade rai cikin tsawa yace "Ba tambayar ki nake ba?" Still taki cewa komai xuciyar ta Sai bugawa yake, murda kunnenta yyi da karfi yace "Are you daft" ta kara rushewa da kuka tace "Don Allah kayi hakuri" yace "Waye shi" cikin kuka tace "Nima ban san shi ba yaya" Ji yake kamar ya sauke mata mari ya dinga mata wani kallo xuciyarsa na tafarfasa, he is just trying hard to control his temper, strictly yace "Toh daga yau Imaan, I mean daga yau.... na sake ganin ki da wani a tsaye wllh sai na kusa sumar dake a gidan nan I promise you that, ba ciwon jiki ko Asthma ba, idan ma jini ke xuba ko ina na jikin ki wllh sai nayi abinda na maki alkawari, ke har guda nawa kike xaki ke tsayawa da namiji jikin mota? How old are you??" Kuka kawai take tana kallonsa duk jikinta na rawa don ta dade bata gansa cikin yanayin nan ba, ya mata tsawa yace "Baxa ki bani amsa ba sai na gaura maki mari?" Cikin rawar murya tace "Ba na kusa 18 ba...." Rankwashi ya kai mata ta dafa wajen tana kiran inna a rikice, yace "In sake ganin ki da wani a waje, sai kin raina kanki wllh" daga haka ya saketa ya rufe motarsa, ta wuce ciki da sauri bata xame ko ina ba sai part din inna, xubewa tayi kan kujera tana rusa kuka, Inna ta fito daki da gudu tace "Na shiga uku me ya same ku a hanya, ko hatsari ku ka yi??" Imaan ta mike xaune cikin kuka tace "Yaya ne ya rankwashe ni kuma ya ja min kunne ni ban masa komai ba innaa" Inna ta xauna kan kujera tayi tagumi a hankali tace "Naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, Wannan yaro dai ya isheni a gidan nan wllh, innalillahi wa inna ilaihi raji'un, A kan wani dalilin kuma ya cuce ki, me kika masa?" Xata yi magana sai ga shi ya shigo, kin cewa komai tayi sai shessheka take hawaye na bin kuncinta, inna tayi mitsi mitsi da ido tace "Mujaheed kana manta cewar akwai hisabi koh, kana mance akwai lahira koh, ni ina jiye maka kada wataran ka karasa gawar da ba taka ba a gidan nan, idan abu ya sami yarinyar nan gaskiya xan rufe ido in mance ni na haifi Ahmadu in maka tijara kotu ta raba mu Mujaheed," Yace "Toh yanxu ma ki tashi a tafi kotun mana, duk ke ke karanta mata tsayawa da samari tun bata kai ko ina ba a titi, idan aure take so ae sai ta sanar da Abbanta ayi mata ba ta dinga tsayuwa da maxaje ba tare da saninsa ba, ita har nawa take, ni nasan wlh Abbanta bai sani ba, halan Ummi bata bata labarin abinda na mata kwanaki ba" Inna ta saki baki tana kallon imaan dake shessheka a hankali, can tace "Amma gaskiya ke munafuka ce Imaan, samm baki da hali, banda munafurci ya xa ayi kiyi sabon saurayi amma kiyi ta nuku nuku kina boye min?? me xai bani da Allah bai ban ba, shi kuma gantalallen bai san kakarki na da rai bane da bai taba cewa xai shigo gaisheni ba? Ko uwar ki ce tace ki boye min ban sani ba" Mujaheed ya dinga kallonta da mamaki, rai bace inna tace "Toh ni dai ba ruwana, dama ana boye abun arxiki irin wannan Ashe, me na maki da xaki boye min sabon saurayin ki Imaan?"Juyawa Mujaheed yyi ya fice daga parlon, Imaan ta kyabe baki tana share idonta tace "Shi fa bai san ko waye ba xai wani dinga ce wa saurayina, ni dai wllh inna ku ce masa ba ruwansa da ni a gidan nan" inna tace "Atoh dama meye hadin ki da shi, kawai ni dai nasan ubansa wan ubanki ne kuma duk ni na haifesu, to bayan wannan bbu abinda ya hada ki da Mujaheed ba dangin iya balle na baba, ke dai kawai ki rabu da shi ya ji da wawancin sa kiyi ta kan ki, banda fitina ma ina ruwansa da lamarin rayuwarki, idan ma saurayin kika yi baki isa ba ne, ko idan kin rasa mijin aure astaghfirullah shi xai aure ki ne?? kar ki sake saurarensa duk saurayi ya kira ki shirya ki fesa turare ki tafi, wa xai xauna biye ta Ahmadu da Bukar ga d'an su ma ya dauko hanya, bokon jaraba kawai ni wllh kina gama sakandari aurar da ke xance

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment