Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shegen Bulasawa da har xai bata hakuri ta hakura? Bayan abinda tsinanniyar matar nan Rukayya ta mana, Kai Asabe Allah ya baki lafiya, ya kuma shirye ki, ni dai kin ga tafiyata nan...." Inna ta tsuke fuska tace "Toh ai ni ba gantalalliya bace da xa ayi ta ba ma hakuri in ki hakura kamar kafurar Bayan tsauni, ehe... Bulasawa kuma ni ya fi min kowaaa, yaro mai hankali da natsuwa mai magana irin ta manya, duk sai da ya fada min maganganu masu dadi da kwantar da xuciya wanda su Amadu suka kasa, toh ni ko me xance ma yaron Banda Allah ya masa albarka, ai in dai bai auri Imaan ba to sai dai in ni Asabe bana numfashi, Imaan ta sa ce in sha Allah, Bai fi min wasu 'yan uwan nawa ba ma ni Allah na tuba, Rukayya kuma ai tuni tana akurkin gidan da ta gina ma iyayenta sai kace ba ni ta ma rashin mutunci ba da xa a bar ta ta kwana gidan nan...." Ta Rasulu ta mike tace "Ni dai tunda kika kunya ta ni, kika kunyata Hadiza Allah sai ya saka mana ya bi mana hakkin mu, Rukayya kuma mu dai je xuwa muna nan dake xata dawo gidan nan...." Inna tace "Ke ni fa ban hakura da abinda Rukayya ta min balle ta dawo, ai Rukayya yar iska ce, aure ne dai nace aje a daura kada 'ya yana su ji kunya" Ta Rasulu tace "Oho dai ni kin ga tafiyata sai ki saka Bukar gaba ya bada kudin nan na laluran Imaan a san abun yi...." Daga haka ta fice daga parlon, Inna tace "Toh Allah bar xumunci ta Rasulu, Allah ji kan mai salati da jikan shehu, Allah ya saka da alkhairi ai ni kin gama min komai a duniya wllh kin fi min kowa ma, Allah ya bar mu tare sai kuma kin dawo bikin Imaan da Maimoon in sha Allah, Kai ae xan taho har gida maki ban gajiya, Bari dai 'yan kauyen nan su koma kauyukansu xa ki gan ni" Mikewa Mama Hadiza tayi ta fice daga parlon rai ba dadi, Inna ta bi ta da kallon gefen ido tace "Toh meye kuma axumi uku da xa ki yi, sai kace warce bata axumin Ramadan, Ni dai ba ruwana dama ban aike ki kiyi ta rantse rantse ba...." A ranan Mama Hadiza bata kwana gidan ba ta tafi gidan wata yayar Mai gidanta dake nan garin kadunan. Imaan na parlon Inna bayan isha tare da Maryam suna cin abinci aka bude kofa, kallon kofar suka yi Mujaheed ya shigo da sallama murya can kasa, wani daddadan kamshi ya gauraye parlon, yayi wani kyau na daban cikin milk shaddar jikinsa dake ta talli, Maryam na murmushi tace "Groom dama har yanxu baka tafi ba?" shi dai bai ce mata komai ba ya xauna, Imaan dai bata kalli inda yake ba tun bayan da suka hada ido shigowarsa, ta dinga cin abincinta a hankali, daga cikin dakin Inna tace "Mujaheed ne?" Maryam tace "Ehh" da sauri Inna ta fito ta marairaice tace "Tun daxu nake cigiyar ka Mujaheed, nace to ko har ka tafi wajen amaryar ne ba sallama ni patuu...." Kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Yanxu xan tafi" Xaunawa Inna tayi ta fashe da kuka a hankali tace "Shikenan yanxu Mujaheed sai dai ka xo ka gaishe mu ka tafi?? Shikenan ba kai ba kwana cikin gidan nan yanxu balle ka xo da sassafe ka gaisheni, wa xai dinga shigo min nan muna hira? Shikenan tafiya xaka yi ka bar ni yanxu, dama ba kowa gare ni ba sai Allah sai kai, kaine me debe min kewo gashi yanxu kayi aure xaka tafi gidanka ka barni ni kadai raina..." Mujaheed bai san lkcn da yyi murmushi ba sai dai bai ce komai ba yana danna wayarsa, Inna na share hawayenta cikin rawar murya tace "Rayuwa kenan, lallai sabo turken wawa, Allah ubangiji ya ba ku xaman lafiya da matar, in sha Allah xuwa nan da kwana biyu imaan xata rakoni don baxan gane gidan ba in xo ganin daki in sa albarka kuma in maku nasiha da amaryar, Allah ya sanya alkhairi... Ni dai baka taba min komai ba Allah maka albarka" Mujaheed na murmushi a hankali yace "Ameen" Mikewa yayi yace "Toh sai da safe" Inna ta kara rushewa da kuka har da rike kai, Maryam ta kasa ci gaba da danne dariyar da ke cinta, Imaan kam kin dago kanta tayi tana juya shinkafar gabanta, Cikin kuka sosai Inna tace "Shikenan kuma, wayyo rayuwa kenan...." Maryam na murmushi tace "Allah ya bada xaman lafiya Ya M.A, sai mun xo ganin dakin Aunty amarya" Mujaheed ya d'an yi murmushin karfin hali ya gyada mata kai ya juya ya nufi kofa, Inna na kallon Imaan da ta sunkuyar da kai tace "Toh ke baxa ki ma yayan naki fatan xaman lafiya da matarsa ba Imaan" Shi dai Mujaheed bai tsaya ba har ya fita, bin sa da kallo imaan tayi sai kuma ta mike ta bi bayansa da sauri, Maryam ta xaro ido tana kallon Inna tace "Wai kuka fa take yi..." Inna ta kara rushewa da kuka tace "Ka ji ki da wata magana, baxa ta yi kuka ba?? ke kinsan wahalan da Mujaheed yyi da ita tun tana tsumma, ke kinsan irin fadi tashin da yayi a kanta tana karama, to ko ubanta bai yi wahalar da Mujaheed yyi a kanta ba, kullum a makale da shi xa ki ganta duk ta takura bawan Allahn duk inda xa shi tana hannunsa, tayi ta basa wahala, har goyata ya sha yi, ta xo ta fara ciwace ciwacen da ba a san kansa ba nan ma babu irin wahalan da bai yi da ita na ganin ya nema mata lafiya ba, ai shakuwar dake tsakaninsu ko d'a da uwa sai haka, kuma kice baxata yi kuka ba yau xa su rabu na har abada" tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka ta xamo daga kan kujera tayi xaman dirshan a kasa, Maryam dai sai dariya take kasa kasa. Imaan na fita parlon Inna taga har yayi nisa, ta bi bayansa da sauri tace "Yaya" tsayawa yayi ya juya yana kallonta, Bata san lokacin da ta fashe da kuka ba ta nufesa da gudu ta rungume sa cikin rawar murya tace "Xan yi missing din ka Yaya" kasa cewa komai yayi, lkci daya idonsa ya canxa launi, rungume ta yyi shi ma yyi ya lumshe ido, kuka ta dinga yi a kirjinsa, cike da karfin hali yace "Ae xa ki dinga xuwa gidana in sha Allah..." Ta gyada masa kai kawai hawaye na sauka idonta, cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri da abinda nayi daxu, ban san it's wrong ba I wouldn't have done that, kayi hakuri plss...." A hankali yace "Na hakura" gently ya janyeta jikinsa ganin hawaye take har sannan yace "Toh ya isa haka mu je ki rakani gun mota" Bata iya ta ce komai ba ya kama hannunta suka nufi gate. Tafiya kawai suke kamar ba su son tafiyar har suka fita gate din gidan, suna isa motarsa ya juya yana kallonta har idanuwanta sun yi jajir, sunkuyar da kanta tayi a hankali tace "Sai da safe, I am wishing you a happy married life...." Yayi murmushin karfin hali yace "Thanks imaan" Juyawa tayi ta fara tafiya yace "Imaan" ta tsaya sannan ta juyo jin bai ce komai ba ta dawo inda yake tana kallonsa, yace "Shiga mu je xan siyo ma Inna abu ki kawo mata ynxu" a hankali tace "Toh" sannan ta xaga ta bude front seat ta shiga, ya shiga driver seat ya tada motar, the journey was silent har suka iso gun masu gashin kaji, yayi parking ya kashe motar, ya sauka, ba a dau lkci sosai ba ya dawo rike da leda uku na kaji da fresh milk, ya bude back seat ya ajiye leda guda sannan ya bude side dinta ya mika mata leda biyu ta amsa ya xaga ya shiga driver seat, gida ya koma bayan yyi parking ya juya yana kallonta yace "Sai da safe" ta sauke idonta kasa tace "Allah ya kai mu..." Yace "Ameen, ki dau daya sai ki kai ma Inna daya" D'an murmushi tayi ta bude motar ta fita, ta nufi gate ya bi ta da kallo har ta shiga sannan yayi reverse ya bar layin. Washegari asabar tun da wayewar gari Ammi da Aunty, Mama Hansai da matan kawu Bala suka dinga aiki a gidan trying to make sure everywhere was neat, masu kujeru dama su ma sun xo sun dau kayansu, su Maimoon, Ummi da Maryam kadai ke taya su aikin, Imaan kuwa na kwance dakinta wai kai na ciwo, Rahma dama tare da ita Umma ta bar gidan da yammacin jiya.... Bayan azahar Imaan na part din Inna tare da Maryam, Inna na kan darduma tana bada labarin nan dai na irin yanda aka haifi Mujaheed tana tsaye bakin kofar asibiti tun safe har dare, wahalan da tayi da shi tun yana tsumma, yanda ya girma a wajenta da fadan da yasa ta dinga yi da jama'ah a anguwa, har lkcn da ya tafi kasar waje karatu.... Imaan dai na kwance sai game take a wayarta tana tabe baki don ita dai har ta haddace labarin nan layi layi, Maryam sai dariya take ita da ba a ta6a ba ma labarin ba, Inna na matsar kwalla tace "Har xuwa jiya da aka daura masa aure, Allah sarki Mujaheed dina" Dariya kawai Maryam take har da kwanciya, Inna dai sai matsar kwalla take tace "Duk cikin 'ya yan Ahmadu babu ya shi, gashi duk ya fi su kyau wllh, ga tsafta ga mutunta na gaba da shi, sam Mujaheed bai san wani abu wai rashin kunya ba, bai taba mayar min da magana ba, wllh jiya ban yi baccin kirki ba da tunaninsa na kwana..." Sai kuma ta fashe da kuka sosai, sai a sannan Imaan tayi murmushi bata dai ce komai ba, cikin rawar murya Inna tace "Da dakunan bangaren nan nawa sun kai uku sai in ce su dawo nan da matar kawai ni dai in dinga ganin sa kullum" Maryam dai sai dariya take, Imaan ta mike ta wuce daki ta dalilin kiranta da ake a waya, Daga kiran tayi ta xauna gefen gado ta kai kunne hade da yin sallama, ya amsa yace "How are you dear?" Tace "Alhmdllh" yace "Hope kin ji sauki sosai" tana murmushi tace "Sure, sosai" yace "Ohk to ki dan fito ki amshi sako" ta xaro ido tace "Na me?" A hankali yace "C'mon dear" tana murmushi tace "Toh bari in fito" daga haka ta katse wayar ta fito parlor tana kallon Maryam tace "Mu je ki rakani" Inna na goge hawayen idonta tace "Ina??" Imaan ta turo baki tace "Ae yanxu xa mu dawo" Inna ta marairaice tace "Tou ni dai kar ku dade, mai tayani xaman gashi yayi aure ya tafi..." Dariya imaan tayi ta fita Maryam ta bi bayanta, har suka isa gate Maryam tambayarta inda xa su take yi amma ta ki gaya mata, suna fita gate din Maryam tayi shiru ganin Sadeeq tsaye kusa da motarsa, murmushi yayi ganinsu, Maryam tace "Hi...." Yace "Hello Maryam" tana murmushi tace "Happy Belated birthday Sadeeq" yace "Thanks much... Hope an gama biki lafiya?" Tace "alhmdllh" yace "Maa Sha Allah, Allah ya basu xaman lafiya" Maryam tace "Ameen" kallon Imaan da ta jingina da motar ta rungume hannu yayi a hankali yace "Hello princess..." Ta d'an yi murmushi tace "Ya gida" yace "Alhmdllh, ya Kaka?" Imaan ta langwabar da kai tace "tana ciki tana ta missing ya Mujaheed" Yace "Allah sarki, ta kwantar da hankalinta after a month sai ta koma gidan gaba daya koh" Yar dariya kawai imaan tayi tace "Gaskiya ne" yyi murmushi ya bude back seat ya fiddo da wani kwali dake a rufe amma ko bai fadi meye a ciki ba kowa ya sani, yana kallonta yace "Here..." Ta xaro ido tace "Haba wannan ai yayi yawa" yace "Ni ma sun min yawa, take plss baby" Imaan tayi murmushi ta d'an risina ta amsa tace "Toh Allah saka da alkhairi" hararanta yyi tayi dariya bata ce komai ba, wani box mai kyau ya fiddo ya mika mata ta make kafada tace "Bana so" hade rai yayi ya kalli Maryam dake murmushi yace "Kin ganta koh?" Maryam tayi dariya ta mika masa hannunta tace "Bani in rike mata" Mika ma Maryam box din yyi, Maryam tace "Allah ya saka da alkhairi" Yana murmushi yace "And ban mance promise da na maki ba, kin bar min xabi or you want anything?" Yar dariya Maryam tayi tace "Ehh na bar maka" yace "Toh shikenan, thank you" Kallon imaan yayi yace "Dear, we will talk later ki gaida kaka" Imaan tace "Toh xata ji nagode" Sallama yayi ma Maryam ma suka nufi gate, ya bude maxaunin driver ya shiga ya tada motar, suna shiga gida Maryam ta kashe ma imaan ido tace "Yau xa mu ci cake mu yi dam, amma me xa ki ce ma Ammi?" Imaan ta xaro ido tace "Part din Inna xan kai ai" Maryam tace "That will save u long explanation" Washegari Sunday tun da sassafe Inna ta gama shiryawa wai xa su gidan Mujaheed da Imaan, Daddy dake parlor xaune yana kallon news yace "Toh ai kila ma basu tashi ba da sassafe xa ki je masu Inna" Inna ta xaro ido tace "Sai kace rubabbu Bukar kace min basu tashi ba, Toh ni dai gaskiya na shirya kuma yanxu xan tafi ina imaan din?" Daddy yace "Bata tashi ba" Inna ta xauna saman kujera tayi tagumi tace "Naga abinda ya isheni.... baccin safe ko baccin asara ni Asabe, karfe takwas ace mutum mai rai bai tashi yyi wanka ya kintsa ya karya ya gyara gidansa ba? Kuma tun jiya nace mata ta shirya da safe xa mu tafi tare tunda wannan yarinya Maryam dangin ubanta sun xo sun tafi da ita jiya da magariba... Kai ku dai baku da tsari gaskiya... Meye kuma baccin safe??" Shi dai Daddy bai ce komai ba, Ammi ta fito daga kitchen ta gaida Inna sannan ta tafi dakin Imaan ta tasheta... Inna na ta xaune parlor ta tsuke fuska har imaan ta fito bayan kusan minti talatin cikin atamfa riga da skirt na biki da aka masu bata sa ba, sosai kayan suka amsheta, Inna tace "Ki dauko mayafi mu tafi idan munje can kya karya gaskiya...." Ammi da Daddy suka kalleta, can Ammi tace "A'a inna da dai ta karya ai bata da 6ata lkci wajen cin abinci, ta je gidan mutane da sassafe...." A fusace Inna tace "Ke dai Aisha ki daina haka, ki dinga jin tsoron Allah, Gidan Mujaheed din ne gidan mutane idan ba walakanci ba, gidan Mujaheed ne fa, ni dai ku dinga tsoron Allah sai kace wanda xata gidan 6are? Ke dauko hijabinki mu tafi, shi gidan yayan nata xaki ce ma gidan mutane saboda baki da mutunci..." Tana fadin haka ta nufi kofa a fusace, Daddy ya tabe baki bai dai ce komai ba, Imaan ta sa hijab ta dauko takalminta da wayarta tana kallon parent din nata a hankali tace "Sai mun dawo" Daddy kadai ne yace "Allah ya kiyaye" Ammi kam bata ce komai ba sai aikin gabanta take.


*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
[7/19, 5:15 PM] +234 803 603 7561: Suna fitowa compound Inna ta kalli Imaan tace "Toh ko dai in je inyi ma Ahmadu magana ya sa direba ya kai mu?" Imaan dai bata ce komai ba, Inna tayi tsaki tace "Ayi ta maki magana kina ma mutane shiru idan ma baccin ne bai isheki ba idan munje gidan Mujaheed din ba sai a baki daki daya ki kwanta kiyi ta yi ba, ai can ma gida ne" Daga haka ta nufi part din Abba imaan na biye da ita, Aunty ce parlor tana goge goge da su Maimoon, Aunty ta xauna ta gaida Inna, su Maimoon ma suka gaisheta, Inna ta amsa tace "Gidan shiru ba wannan mata Rukayya koh" Ita dai Aunty bata ce komai ba, Inna tace "Toh Ahmadu nake nema ya kira wannan mutumi me jan mota ya kai mu gidan Mujaheed, tun asuba na gama shiryawa Imaan ta bata min lkci" Aunty tace "Toh xauna Inna ki jira driver din an aike sa yanxu" Inna ta xauna tace "So dai ake in makara kawai, Banda haka ni fa tun Asuba nayi wanka na" Imaan ta xauna a parlon bayan ta gaida Aunty tana kallon series din da akeyi, ba a dau lkci ba driver ya dawo, Aunty na kallon Inna dake xuba gyangyadi tace "Toh ya dawo fa inna..." Inna ta bude ido da sauri ta mike tace "Toh tashi mu je imaan, shi Ahmadun baya nan ne?" Aunty tace "Bacci yake" Inna tace "Ni dai ba wajena suka gaji baccin safe kamar rubabbu ba gaskiya" daga haka ta fita imaan na biye da ita, a waje suka tadda driver da mota, imaan ta bude ma Inna motar ta shiga tana amsa gaisuwar driver din sannan imaan ma ta shiga, sai da suka hau saman titi Inna na kallon Imaan tace "Toh kin gaya masa anguwar ne" Drivern na murmushi yace "Ae na san gidan kaka" Inna ta washe baki tace "Ashe har ku kunje kun sa ma gidan albarka ku ma" Shi dai bai ce komai ba yana murmushi, tafiyar kusan minti ashirin suka yi suka iso gidan Mujaheed, Inna na kallon driver da yayi parking a waje tace "Kai ya haka ka danna han a bude maka gate ka shiga mana, gidan jikana ne fa" Horn driver yyi mai gadi ya fito yana kallonsa, can ya karaso gun motar yace "Daga ina?" Rike baki Inna tayi da mamaki tana kallonsa tace "Naga abinda ya isheni, kai gidan jikana ne fa kake tambayar daga ina? Na shiga uku wai ni yake tambaya daga Ina, ko in sauko in bude get din da kai na ne" Mai gadin yyi kasa da kai yace "Yi hakuri Baaba" daga haka ya tafi da sauri ya bude gate din, Inna ta ja tsaki tace "Mutane dai ba tsoron Allah... wai daga Ina, ke ki ji fa gantalalle amma ba laifinsa bane na Mujaheed ne da bai sanar masa kakarsa na da rai ba" Ita dai Imaan bata ce komai ba driver ne ke bata hakuri, yana gama parking imaan ta bude motar ta fito, Inna na kallon driver din tace "Toh yi wucewar ka yaro, mu da gida kuma sai bayan isha in sha Allah" Yace "Toh baaba ku dawo lafiya" Inna ta nufi entrance din shiga gidan tana washe baki, Imaan dai na biye da ita, Bubbuga kofa Inna ta shiga yi da karfi tana cewa "Salama alaikum" Imaan tace "Kai inna kiyi a hankali mana..." Matsawa Inna tayi ta bude baki tana kallonta, Imaan ta turo baki ta danna bell tace "Kawai kiyi ta bubbuga ma mutane kofa da karfi" Inna xata yi magana aka bude kofar, Inna ta washe baki tana kallonsa tace "Mujaheed...." Kallonsu kawai yake yana tsaye bakin kofar sanye da jallabiya, Inna ta rike haba tace "Ashe da gaske ba ku tashi ba kenan" rabawa tayi ta gefensa kamar yar yarinya ta shige parlon, Imaan ta juya tana murmushi, can dai ta juyo a hankali, kallonta taga yana yi, ta sunkuyar da kai tace "Ina kwana Yaya" Muryar Inna suka ji a parlor tace "Ina amaryar??" Mujaheed ya juya ya koma parlon, Imaan ta bi bayansa, Xaunawa yyi yana kallon Inna yace "Ina kwana?" ta washe baki tace "Lafiya lau Mujaheed, tun asuba da na tashi nayi wanka wllh, Banda imaan da ta bata min lkci da tun gari bai gama wayewa ba xa ku gan ni" shafa kansa yyi bai dai ce komai ba, Inna na kallon pillow da aka ajiye kan lallausan sabon rug din parlon tace "Cewa nayi ina amaryar" Mujaheed yace "Tana sama...." Yana fadin haka ya tashi ya wuce sama, Inna ta kara kallon pillow dake parlor murya can kasa tace "Toh waye kuma ya kwana a parlor ni patuu" Imaan tayi murmushi tace "Toh ke ina ruwan ki" Inna tace "Atohhh, ba ruwana kuwa" Cire Hijab Inna tayi ta linke tana kallon parlon tana murmushi tace "Sabon gida ba dai sha'awa ba" Mikewa tayi ta nufi wani kofa ta bude tana lekan ciki ta karasa ta ajiye hijab din nata a ciki ta fito ta rufe tace "Dakinsu Hansai ne, shi ma sun xuba lafiyayyun kaya a ciki wllh masu tsada...." tabe baki tayi ta tafi ta bude kofar kitchen tana lekan ciki ta xaro ido tace "Waiii.... Ai kitchen din ma ba masaka tsinke da kayan kitchen na xamani, Ashe dai ba gwalagwalan karya aka dinga yawo da shi ranan casu ba" Imaan dai ta hade rai sai kallonta take... Mujaheed na haurawa sama ya bude dakin da Safeenah ke ciki, bacci ya sameta tana yi, ya shiga ya kulle kofar ya karasa kan gadon ya d'an bugi gadon yana kallonta, sai da ya buga gadon da karfi for d second time sannan ta bude ido ta mike xaune tana kallonsa da wani expression, yace "Kin ma yi sllhn kuwa?" D'an tsaki tayi tace "Haba don Allah sai ka wani buga gado ka tsorata ni kamar xaka tada kato??" Daga head har toes yake kallonta, ta tabe baki ta kalli agogo tace "Sllh dai dole inyi ko karfe nawa ne" da mamaki yake kallonta yace "A gidan ku haka kike kai wa har karfe tara baki yi sllh ba Safeenah?" A fusace tace "Toh gajiyan bikin fa? Plss Mujaheed that's not how to treat a new bride you are not romantic, haba don Allah sai kace mun ta6a rayuwa gida daya...." Wani kallo kawai Mujaheed yake mata, strictly yace "Look Safeenah I won't tolerate this, gidana ba na kafurai bane, tun asuba na shigo na tashe ki kiyi sllh shine har yanxu baki yi ba, is this ur home training?" Yar dariya tayi tana kallonsa daga sama har kasa tace "Kai ko kunya baka ji ba don Allah??" tana kwaikwayonsa tace "Wai wani tun asuba na shigo na tashe ki.. ban taba jin labarin ango irin ka ba sai yau da nake gani a xahiri a gidana, wai ka shigo min da asuba, ain't you ashame of ur self plss" murguda baki tayi ta sauka daga saman gadon da yar figigiyar rigar baccinta ta nufi bathroom, ya bi da kallo kafin ta shiga bayin yace "Ki sameni downstairs yanxu idan kin yi sllhn" daga haka ya juya ya fice daga dakin, Tv ya tarar Inna na kokarin kunnawa tana cewa "Toh sai me idan Baki kunna min ba kamar yau na saba hada kayan kallo kuma... Gidan Mujaheed kuma baxa ki saki jiki kiyi yanda kike so, ban da shi wa gare ki da xa ki je gidansa ki sake jiki dama, ni dai ba ruwana, ki dinga abu domin Allah Banda munafurci" Imaan dai sai kallonta take fuska daure, Inna na ganin Mujaheed ta mike tace "Wai ka ji daga nace ta hada min kayan kallo shine xata ce min daga xuwa gidan mutane, su waye kuma mutane, Mujaheed din koko Amaryar da bata fito gaisheni ba har yanxu, ni dai ba ruwana, idan ma xa ki cire Hijabin nan na jikinki ki linke ki ajiye ki tsayar da ranki waje daya ki saki jiki kamar kina gidan Bukar to gwara ki cire don da kyar ma ba kwana xamu yi a nan ba gaskiya, ga dai dakuna na kirga har hudu ranan" Mujaheed ya karasa ya kunna mata tv din yace "Xata sakko yanxu ta gaishe ki ai" Inna ta koma kan kujera ta xauna ta tsuke fuska tana kallon Tv, Xaunawa Mujaheed yayi kan kujera ya kalli Imaan ta gefen ido, Sai turo baki take, Mujaheed ya kalli Inna yace "Amma kuma sai ki

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment