Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inna kakar ka ce, amma gaskiya akwai matsala daga bangaren inna ka bar ni ma in ji da headache daya...." Yusuf ya girgixa kai yace "Kiyi hakuri Mum, I don't think all this u are saying is enough da xai sa ki hanani auren Imaan" Aunty ta bude baki tace "Ni nace xan hana ka aure Imaan Yusuf, idan Allah yyi Ita din matar ka ce ni na isa in hana? Don't quote me wrong plss, amma kai kasan kana son ta me yasa ko sau daya baka taba nuna alamar haka ba?" Yace "That's bcos she is still young, har yanxu Imaan bata san meye rayuwa ba, bata san kanta ba har ynxu, I was thinking idan ta fara jami'a ta d'an yi hankali sai in fito da intentions dina toward her" Aunty tace "Toh Allah ya kyauta, I think it's best ka je ka samu abbanku, amma ni nasan da kyar ne...." Yusuf yyi kasa da kai a hankali yace "Ni dai ki daina cewa haka plss mum, support me sannan ki min addu'a" a sanyaye tace "Toh na daina cewa haka, Allah yayi maku xabi mafi alkhairi Yusuf" yace "Nagode mum" daga haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, Tagumi tayi tana furta innalillahi.... A xuciyarta. Sake baki Abba yyi yana kallon Yusuf with surprise, shi dai Yusuf bai yarda ya kallesa ba, bayan few seconds Abba yace "Yusuf" Sai a sannan Yusuf ya daga kai da kyar yana kallon Abban nasa, Abba yace "Kana nufin Imaan kake so?" Yusuf ya sunkuyar da kai a sanyaye yace "Ehh Abba" Abba yace "Ikon Allah" Shiru ne ya biyo baya na kusan minti biyu, can Abba ya daga wayarsa yyi dialing number Mujaheed har ya gama ring ba a daga ba, Abba ya ajiye wayar sanin yana gun aiki, Abba yace "I am happy hearing this son, but at the same time I am disturbed coz I made a promise to someone earlier, all the same don't worry, Allah xai shige mana gaba, tashi ka tafi" Mikewa Yusuf yyi ya nufi kofa Abba ya bi sa da kallo yana murmushi. Ko minti goma ba ayi da fitar Yusuf ba sai ga Umma ta shigo parlon Abba cikin shirin fita, har sannan Abba was still pondering at what Yusuf told him, kuma har ransa yake jin xai fi kowa murna da wannan hadin, Auren d'an sa da tillon 'yar d'an uwansa, tunanin yanda xai fara billowa al'amarin yake, first ya fara kiran D'an uwan nasa ya sanar masa sannan su tafi gun Mahaifiyar su ita ma su sanar da ita, yasan Daddy xai yi farin ciki da hadin shi ma, don fargabarsa a ko da yaushe gidan da only child din tasa xata fada da sunan aure, yasan Daddy na son imaan fiye da tunanin me karatu, he can do anything bcos of his only child, Umma Ta karasa cikin parlon tace "Alhaji kasan Mujaheed ya tura min kudi xan fara hada masa lefe, to yau xan fara shiga kasuwa" Abba na kallonta da mamaki yace "What? Lefe kuma? But he told me nothing about that" Umma ta d'an bude ido tace "Toh ba sae an gama hadawa ba xa a kinkimo maka ka gani, kar ya fada maka kayi tunanin ko so yake ka basa wani abun, wllh ban son ya daura maka ko wani nauyi ne kaga ba a dade da hidimar seeyama ba, tunda Allah ya hore masa xai iya komai shi sa kawai nace kada ya gaya maka sai na gama hada kayan a kawo maka ka gani, ba laifinsa bane shi ma ya so sanar da kai na hanasa, amma idan hakan ya bata maka rai kayi hakuri don Allah" Abba yace "Toh Allah ya rufa asiri..." Umma tace "Ameen, tun jiya naga kamar abu na damun ka, shine nace to mai kuma ya faru, idan ma inna ce don Allah a dinga hakuri, uwa ce... Sai ayi ta fatan a gama lafiya da ita, ya ci ace duk abubuwan inna ya xame maka jiki yanxu..." Abba yace "Haka ne" Umma ta xauna ganin maganganunta sunyi tasiri xuciyar Abba, murya can kasa tace "Toh me kuma take so Alhaji?" Abba yace "A'a wannan mun shawo shi tare da Sadeeq, Yusuf ne dai ya xo min da wata magana yanxu da ya kulle min kai... Am still trying to find a way out ne har yanxu" Da mamaki Umma tace "In ji dai lafiya??" Abba yace "Lafiya lau, yar uwarsa Imaan yake so da aure wai" Mikewa Umma tayi da mugun mamaki baki bude tana kallon Abba, can tace "Aure kuma Alhaji??" Abba yace "Kwarai, yanxu ma ya bar parlon nan" Umma tace "Ikon Allah.... Aure fa???" Juyawa tayi ta nufi kofa tace "Toh Allah yayi mana mai kyau dai, ya xaba abinda ya fi alkhairi, ae imaan yar uwar sa ce, Imaan ta mu ce..." daga haka ta fice, direct sama ta wuce ta bude dakin Yusuf ganin baya ciki ta shiga dakin Aunty, xaune ta samesa tare da Aunty, Umma tace "Amma Yusuf kayi asara wllh, ka kuma samu tabin kwakwalwa mai wuyar ganowa balle ayi maka magani, yanxu ka rasa warce xaka je kace ma Ubanka kana so sai Imaan, Yusuf me ya same ka ni Rukayya?? ina ita Hafsar da kake nema take??" Yusuf dake kallonta yace "Umma ni Hafsat ba aurenta nace xan yi ba" Salati Umma ta saki tace "Amma Allah ya isa tsakaninmu da kai, mu xaka ka ma bakin ciki Yusuf?? ka bar 'yar attajiri ka dawo kace mai lalura iri iri kake so? Anya akwai lafiya kuwa, mu xaka kwaso wa mugun iri, irin ciwo a xuri'ar mu? Yarinya mutu kwakwai rai kwakwai?? Toh wllh tunda an asirce uwarka ta kasa cewa komai ni kam ba a asirce ni ba sai inda karfina ya kare in sha Allahu, yanda xan ma Mujaheed haka xan maka don duk daya ku ke a gu na, in sha Allahu sai naje na gano tushen abun nan... Ba wanda ya isa ya ci nasara a kanka kamar yanda aka ci a kan kanin Ubanka, uban kuturu yyi kadan wllh balle na makaho" daga haka ta fice a dakin kamar xa ta tashi sama, Aunty da ta bude baki tana ta kallonta tace "Ikon Allah ya fi gaban haka...."
Daddy couldn't help it but laugh bayan Abba ya xo har part dinsa ya sanar masa intention din Yusuf a kan Imaan, Daddy yace "Ikon Allah, nayi farin ciki sosai sai dai kar ka mance da alkawarin da kayi a baya barrister, ko ya xa mu yi?" Abba yace "Sure ina sane, shi ma ba wai xa a dakatar da shi bane Sadeeq din, abinda xai faru yanxu kawai mu fara xuwa gun Inna mu je ta bakin ta kafin a yanke ko wani decision" Daddy yace "Gaskiya ne wannan" Part din inna suka tafi a tare, Inna ta fito daki tace "Tun safe in gaya maku nake aiki ban xauna ba, ku leka bandakina ku ga ko tuwo ya xube kasa xa a iya xaunawa a cinye tass, ba ku ji bayana ba kamar ya balle ni dai in huta" Murmushi duk suka yi suka xauna, Daddy yace "Gwara dai ki dinga hutawa haka inna, gashi kince baki son mai aiki balle a samo maki ko yar dattijuwa ce" Inna tace "Ni ko ina xan so masu aiki mutane duk wari, sannan su cinye ma mutum abinci, A'a ba ruwana ni ko da rarrafe ne xan yi aikina, 'ya yanku ne sun xama abun tsoro banda haka Imaan ko Maimoon ko Ummi baxa su dinga xuwa min d'an share share ba banda karshen duniya da lalacewa ta xo" Abba yace "Inna ke fa kika ce baki so, ai da suna xuwa..." Inna tace "Ehh ni nace bana so, don ba abinda suka iya gaskiya, basa min yanda nake so, ni dai nace na yafe su daina xuwa" Duk suka yi shiru basu ce mata komai ba, ganin ta dauko tsintsiya Abba yace "Inna daxu Yusuf ya sameni kan wata magana da naga ya dace mu sanar maki kafin mu yanke hukunci...." Ajiye tsintsiyar tayi ta xauna kan kujera da sauri tace "Me ya faru kuma??" Abba ya d'an yi murmushi yace "Wai yar uwarsa Imaan yake so da aure...." Inna ta gwalo ido ta saki baki tana kallonsu, saukowa kasa ta yi a hankali ta xauna kan rug ta fashe da matsanancin kuka tana tafe hannu tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, LA haula wala kuwata illa billahil Aliyul Azeem, la ilaha ilallahu Muhammadurrasulillahi sallallahu alaihi wassalam, hasbunallahu wa ni'imal wakeel.... Na ga abinda ya isheni ni patuuu" Daga Abba har Daddy kallonta suka dinga yi da mamaki, inna ta dakatar da kukan da take tace "Toh da kyar idan Imaan bata ta6a shan nonon Amina ba ma, yo ta ma sha ne kawai... Idan xa kuyi ta kanku kuyi ta kanku"




*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻‍♀️

It's 300 via Fcmb 3276052019Mikewa Imaan tayi da sauri ta nufi cikin gidan tana waigan ko Mujaheed ya dawo har ta shiga ta kulle kofa, dakin gwaggwo ta wuce ta boye box din a cikin trolley dinta, tsoronta daya yanxu Ammi, bata san me xata ce ba idan ta ga dankunnen, bayan Magrib suna cin abinci tare da Anty Halima da wata kawarta, wayar Halima ya fara ring, dauka tayi bayan taga mai kiran ta kalli Imaan tace "Wai ina wayar ki?" A hankali Imaan tace "Yaya ya kwace min" Halima ta xaro ido tace "Saboda me?" Buda hannu Imaan tayi alamar bata sani ba, Halima ta mika mata wayar tace "Toh gama magana tukun" karba Imaan tayi ta kai kunne bayan ta daga hade da yin sallama, Sadeeq ya amsa mata daga daya barin yace "Har yanxu baki yi charge din wayar ki bane Imaan?" A hankali tace "Ehh" yace "But naga akwai wuta ai yanxu, ina ma anguwar" ta langwabar da kai tace "Wayar na gida fa" yace "Ohk after Isha xan kira ki, it's almost time now" tace "Allah ya kai mu" daga haka ya katse wayar, Imaan ta ajiye gefen gado, Halima tace "Haka kawai Mujaheed din ya amshe maki waya?" Tace "Ehh wai saboda abokin Muhsin na kirana" Bude baki Halima tayi tace "Toh shi ina ruwansa" Imaan ta buda hannu tace "Nima ban sani ba" Rabi'ah kawar Halima tace "Yayanki ne kuma?" Halima tace "Cousin dinta dai" Rabi'ah ta d'an bude ido tace "Toh ko son ki yake?" Still Imaan tayi tana kallonta da wani expression, can tace "Yaya ne fa... Yayana ne shi" Rabi'ah tayi dariya sosai tace "Wai yaya ne, to haka kawai baxai dinga hana ki waya da samari yana kwace maki wayar idan babu wani abu a kasa" Imaan ta ajiye cokalin hannunta a hankali tace "Abu kamar me?" Halima tace "Tukunna dae me yace maki da yaga Sadeeq din na kiran ki?" Imaan ta jingina da gado tace "Kawai ya hanani waya da shi ne, har blocking dinsa yyi ni kuma nayi unblocking dinsa, a gida ma da Abba ya kira ni xai tambayeni meye tsakaninmu da Sadeeq kafin in je ya sameni wai ince ban san sa ba" Dariya sosai Rabi'ah take, Halima tayi murmushi tace "Tabb, lallai Mujaheed" Imaan dai sai kallonsu take don bata san me ya basu dariya ba, Rabi'ah ta ajiye spoon din hannunta tana kallon Imaan da kyau tace "Toh wllh son ki yake...." Imaan ta xaro ido ta koma baya da sauri tace "Don Allah ki daina cewa haka plss, wllh yaya na ne fa, Anty Halima yaya fa ne" Halima tayi wani murmushi tace "As far as ba ciki daya ku ka fito da shi ba ki daina deceiving kanki Imaan Mujaheed son ki yake, so mai tsanani ma kuwa, ni dama tun lkcn da yake kawo ki nan few years back ina ganin irin kallon da yake maki nasan ba a banxa ba da abu a kasa, sannan kulawar da yake maki ko kanninsa basa samun haka, abinda Mujaheed ke maki a da ya wuce shakuwa ko so na 'yan uwantaka, ke dai ce ban san lkcn da xaki yi wayo har ki fahimci inda ya dosa, wai yaya ne... A'a ba yaya ba..." lkci daya hankalin Imaan ya tashi ta fashe da kuka sosai tace "Wllh ku daina cewa haka ba kyau, ni ba wani so na da yake yi, ina ce maku yayana ne fa, to taya xai so ni, ni kanwarsa ce fa..." Dariya kawai Rabi'ah take don imaan tayi mugun bata dariya nan kuma ta yarda har sannan Imaan na tare da yarinta ba kadan ba sannan ga ta only child shi sa abun ya taru ya mata yawa, Imaan ta mike da sauri ta fice daga dakin ta koma wani daki ta xauna kan gado maganganunsu na mata yawo a kai, fashewa tayi da matsanancin kuka ta fada kan gadon tace "Ni baxan ma kwana a gidan nan ba, ta ya xa a ce wai yaya na so na, wai yaya fa?? Allah ya kiyaye wllh" Imaan bata ta6a jin abu ya tsaya mata a rai irin abinda Halima da kawarta suka gaya mata ba, wai Mujaheed sonta yake, tabbb, ji tayi ita gaba daya duniyar ma babu wanda take jin haushi kamar Mujaheed din, duk da tasan baxai ma taba yiwuwa ace yana sonta ba, amma abinda suka gaya mata yasa ita taji bata ma son sa shi a ido, bata son ganinsa kwata kwata, lamo tayi kan gado very restless, aka bude kofar dakin ta juya da sauri, Halima ta shigo tace "Gashi Sadeeq ya kira" Imaan ta mike xaune a hankali ta amshi wayar ta kai kunne tare da masa sallama, ya amsa yace "I am outside Imaan" tace "Toh bari in fada ma gwaggo" daga haka ta katse wayar ta tafi ta nemo gwaggo ta gaya mata, Gwaggwo tace "Toh ya shigo mana ai ba kowa parlon ma, ce masa yayi shigowarsa kawai" Imaan bata ce komai ba ta sa Hijab dinta ta fita, tsaye ta gansa ya jingina da motarsa, ta karasa kanta a kasa ta tsaya keeping a enough distance tsakanin su, kallonta kawai yake, ita ko bata yarda ta kallesa ba, a hankali yace "What's wrong imaan you look disturbed" da sauri ta daga kai ta kirkiri murmushi tace "A'a ba komai fa, ya gida" yace "Lafiya lau" tace "Gwaggwo tace ka shigo ciki ba kowa a parlor" Yace "No ni baxan shiga ba kunyarta nake ji yanxu" murmushi Imaan tayi tace "Toh akwai kujeru a compound ai, shi ma baxa ka shiga ba?" Ya shafa kansa smiling sweetly yace "Ohk then mu je" ita ta shiga gaba ya bi bayanta har suka shiga cikin compound din. Sai da ta fara xama kan farin plastic chair sannan ya xauna shi ma yana kallonta, dauke kai tayi ganin kallon da yake mata yace "Amma ba dai kunyata kike ji ba" murmushi tayi tace "Shi nake ji mana" Yayi dariya yace "Aa kiyi hakuri kar ki ji plss" Ita dai bata ce komai ba, bayan few seconds yace "Did you know what imaan" ta daga kai ta d'an kallesa, cikin sanyin murya yace "I am hoping to spend the rest of my life with you" Imaan ta sauke idonta kasa, yace "I was born and bred in Uk, yawancin rayuwata duk can nayi sa, daga baya na dawo Nigeria gaba daya, I've neva for once thought xan hadu da mace yar Nigeria inji ina son rayuwa na har abada da ita sai kan ki Imaan, my ex was white ita ma it's not as if I have much feelings for her, it's just to while away time... Here in Nigeria frndship kadai ne tsakanina da yan mata, Ni ban san meye so ba, I don't even believe in it until I met you few months back, pls don't break my heart imaan, it's too fragile for something this big...." Imaan tayi murmushi a sanyaye bata dai ce komai ba, yace "Yea... I have been counting down tun yanxu xuwa ranan da xaku fara waec, but plss me yasa baxa kiyi waec din a ss2 ba" xaro ido tayi ta kallesa, yace "Sure, a lot a ss2 suke waec" tace "Aa nafi son inyi ss3" ya lumshe ido ya bude yace "almost a year to come in sha Allah kenan fa Imaan?" Imaan ta kallesa tace "Sure" yace "Toh Allah ya kai mu lafiya" Tace "Ameen" Yace "Promise me something plss...." Imaan tayi shiru tana kallonsa, yace "Ki min alkawarin baxa ki yi betraying din soyayyata gare ki ba, and I am also promising u same, I will and will neva leave u for any reason" lkci daya jikin Imaan yyi sanyi tace "Ae an riga an san ka gidanmu, so there is nothing to worry about" yace "Sure an san ni, but I am afraid of ur cousins" da mamaki tace "Cousins dina kuma?" Ya d'an yi murmushi yace "Yea kada su min fin karfi...." Imaan ta kasa daina masa kallon mamaki tace "Su ai yayyina ne ba so na suke ba" Sadeeq ya girgixa kai yace "I saw their reactions ranan da Abbansu ya kira ni, more especially the very fair one" Imaan gabanta ya shiga faduwa, Sadeeq yace "They might not tell you now amma kada watarana su xo su ce suna sonki ki mance alkawarin mu, kada ki min haka plss Imaan..." cike da damuwa ya fadi haka, imaan ta ji kamar ta fashe da kuka tace "Ni ka daina cewa haka, ba wanda ke so na cikinsu duk yayyina ne su wllh, they are only disturb sbda ban gama secondary schl ba" yace "Toh Allah ya sa haka, amma ba sai kin min kuka ba gimbiyata, reminder ne" Imaan ta boye fuskarta da Hijab, yyi murmushi yana kallonta, murya can kasa yace "Kin san inda xan kai ki for our honeymoon?" Kamr yace ta kara boye fuskarta da Hijab cike da shagwaba tace "Ni dai bana sooo" yyi dariyarsa mai dadin sauraro yace "Toh na bari baby, when the time comes xa ki ga, amma fa tare da kaka xa mu" da sauri Imaan ta bude fuskarta ta xaro ido tace "Aa ba inda xata bi mu" Sadeeq couldn't help it but laugh yace "Are you serious??" Ita kanta sai daga baya taji kunyar abinda ta fada ta mike da sauri xata wuce ciki yace "Noo plss wait dear, ki rakani first plss" da kyar ta yarda ta rakasa gate tana sinne kai, ya juya yana kallonta kafin yace komai, a hankali tace "Thanks much for the earrings na gode sosai" Ya mata wani kallo yace "Bana son ki min godiya idan na baki abu, ba don ki gode min bane na baki" murmushi kawai tayi bata ce komai ba, nan suka yi, sallama ta daga masa hannu ta koma cikin gida. Washegari gidan gwaggwo ya xamo ba masaka tsinke saboda yan uwa da abokan arxiki duk da gobe ne daurin auren, imaan dai na daki duk ta takura, ita dama haka Allah yayi ta bata da sakewa cikin mutane, babu yanda Halima bata yi da ita kan ta bi su gidan wata makociyarsu ba don can xata xauna har gobe sbda mutane amma taki, Har daki Ammi ta kawo mata abincin rana ganin ta ki fitowa, ganin yanda take yatsine yatsine Ammi tace "Ko dai xa ki wuce gida ne bana son matsala" girgixa kai tayi tace "A'a kawai kaina ke min ciwo amma idan na ci abincin xan sha magani" Ammi ta tabe baki ta fita dakin, imaan ta gama cin abinda xata ci a abincin ta dau maganin ta sha, mikewa tayi rike da plate din ta fita don kai wa wajen wanke wanke, tun da ta fito parlor taji numfashinta na tsarkewa ta dai dinga gyaran murya har ta fita compound, hayaki ne cike gidan saboda wutan icce da aka hura, ta rike numfashinta da sauri ta karasa ta ajiye plate din ta juya xata shiga parlor ta saki numfashin, tari ta fara sosai ta durkushe nan bakin kofa mutane suka taho kanta, Nan Asthma dinta ya tashi duk Gwaggwo ta rikice tana salati, Ammi ta wuce daki da sauri don duba inhaler dinta a jaka, Aunty da sauran mutanen wajen suka shigar da ita parlor. Har Imaan ta samu bacci dakin Gwaggwo bayan an rufe duk windows din an kunna mata fan Halima ta shigo sanye da Nikab a kan Hijab dinta ta durkusa kusa da ita tace "Sannu Imaan" bude ido tayi amma ta kasa cewa komai, ba kadan asthman yayi attacking dinta ba wnn lkcn don har sun yi niyyar tafiya asibiti sannan ya lafa, Kai kawai ta iya gyada mata, Halima ta dinga kallonta cike da tausayi, Can tace "Sadeeq ma ya kira har sau biyu, bari in kirasa ince baki da lafiya" Ita dai Imaan bata ce komai ba, Halima ta kirasa ya katse ya kira ta, tace "Ka kira daxu ina sllh, na taho gida yanxu na tarar ma Imaan din bata da lafiya" Yace "Subhanallah what's wrong with her?" Halima ta rasa me xata ce masa da farko don bata san ko yasan imaan na da Asthma ba, can tace "Gata nan dai a kwance bari in bata" mikewa Imaan tayi da kyar ta karbi wayar ta kai kunne cikin sanyin murya tayi masa sallama, cike da damuwa yace "What's wrong with you dear?" a hankali tace "Naji sauki" yace "But what happened, dama baki da lafiya ne?" D'an shiru tayi kafin tace "I had an attack..." Da mamaki yace "Are... you asthmatic?" Ta gyada kai kamar yana ganinta tace "Um" yace "Subhanallah, to Allah ya sauwake... is ur breathing now ohk?" Tace "Sure" yace "Xa ki iya fitowa yanxu?" Ta yi shiru, sai kuma a hankali tace "I will try" yace "Alryt gani nan xuwa" katse wayar yyi, ta koma ta kwanta, Halima na kallonta tace "Allah ya sauwake imaan" imaan ta d'an mata murmushi, Halima tace "ki rike wayar idan ya kira bari xan je ana jirana na sani" Imaan tace "Toh nagode" daga haka Halima ta mike ta fita, ba a dau lkci da fitar ta ba Gwaggwo ta shigo da cup din tea ta xauna gefen gadon tace "Sannu Fatima tashi ki sha shayi na hada maki" imaan ta mike xaune tace "Gwaggwo ai na ci abinci, a koshe nake" Gwaggwo xata yi magana sai ga Ammi ta shigo dakin tare da Aunty, aunty na kallonta tace "Sannu Imaan, ya jikin" imaan ta d'an yi murmushi tace "Na ji sauki Aunty" Aunty tace "Toh Allah ya kara lafiya" fita Aunty tayi don xuwa su ci gaba da aikin da su ke yi, Ammi na kallonta tace "Kirjin yyi sauki?" Imaan tace "Kadan kadan yake min" Ammi tace "Toh sannu, dama sai da daddy ya guji hakan, nima nasan kawai wahala xa ki xo ki kara min nan" Gwaggwo tace "Wani irin magana ce wannan Aisha, ita ta daura ma kanta ciwon ashe?" Ammi dai bata ce komai ba, imaan ta kalli wayar Halima da ya fara ring, Sannan ta daga a hankali ta kai kunne, satan kallon Ammi tayi, murya can kasa tace ma Sadeeq "Toh..." Daga haka ta katse wayar, Gwaggwo tace "Wa ye?" Imaan ta sunkuyar da kai tace "Ce min yyi yana waje" Gwaggwo tace "Sadeeq?" Imaan ta gyada mata kai, Gwaggwo ta kalli Ammi tace "Toh ko ya ajiye ta gida kawai... Ni xamanta nan bai kwanta min ba, ba a fara komai na girki ba fa ciwonta ya tashi, ina ga gobe da xa ayi girke girke" Ammi tace "Waye ya kira ki?" Imaan ta kasa cewa komai, Gwaggwo tace "D'an gidan Bulasawa ne..." Ammi tace "Bulasawa kuma?" Gwaggwo ta kalli Imaan tace "Ko bata san ki da shi bane??"Imaan tayi kasa da murya tace "ta san shi" Ammi tace "Na san sa a ina??" Imaan tace "Abokin ya Muhsin fa" da mamaki ammi tace "D'an Bulasawa ne dama?" Gwaggwo tace "D'an sa ne na cikinsa,

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment