Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wayarta dake ajiye xai yi silencing wayar yaga ma a silent yake, ya xura a aljihu sannan ya karasa kofar bayin ya makale jikin bango, Imaan ta gama alwalan da take ta bude kofar bathroom din ta fito, ji tayi an cafketa ta baya, ta fasa wani ihu a raxane ya jawo ta jikinsa ya riketa gam, kafin ma ya kai ga cewa komai ta gane shine saboda scent dinsa, k'asa cewa komai tayi ta dinga numfashi a tsorace don tayi mugun tsorata, bayan few seconds numfashinta ya dawo dai dai, juyo da ita yyi yana kallonta yace "Anjima Abba xai kira ki, kin dai ji abinda nace maki daxu koh?" Kin cewa komai tayi, ya hade rai yace "Ba magana nake maki ba" tace "Naji mana" Saketa yyi ya nufi kofa, ta murguda baki tace "After all he is just a frnd, and he is...." juyowa yyi da sauri yana kallonta, tayi maza ta shige bathroom ta sa key.
Mujaheed ya koma inda yake xaune ya fiddo wayar nata a aljihu ya shiga call log, bai ga wasu calls ba sai na Daddy sai wani number da bata yi saving ba, ya dinga kallon Number kafin yyi dialing, katsewa aka yi sai gashi an kira, ya daga ya kai kunne yyi shiru, daga daya bangaren Sadeeq yayi sallama, Mujaheed ya cire wayar a kunnensa ya katse kiran ya ciro wayarsa ya kwashe number sannan ya danna ma number block ya goge log din kiran a wayar gaba daya. Imaan na idar da sllh ta debo chocolates ta xuba su kan gadon ta sannan ta kunna kallo ta kwanta tana shan chocolates tana yi, ta fi minti talatin tana kallo ta tuna Sadeeq ya kira ta tun daxu bata dauka ba, mikewa tayi xaune da sauri tana kallon gaban madubinta don nan ta ajiye wayar, da mamaki ta karasa wajen mirror din idonta a kan inda ta bar wayar ganin babu shi, lkci daya Mujaheed ya fado mata, ta xaro ido tana fatan ba shi ya dauka ba, duba dakin ta shiga yi amma ba alamar waya, kamar xata yi kuka ta dau Hijab ta sa ta fita, bata tsaya ko ina ba sai part din su, Babu kowa parlon gidan tsit don har sannan su maimoon basu dawo ba duk da ta ji alamar akwai mutane a kitchen, ta wuce sama cikin sanda tana waige waige, tana ta tsaye corridor tana kallon kofar dakinsa, karasawa tayi ta murda kofar a hankali ta tura, ba kowa dakin sai kamshi me dadi dake tashi, ta karasa ciki da sauri tana kalle kallen dakin, wayarsa ta gani gefen gado amma bata ga nata ba, dauke wayar tayi ta boye cikin Hijab ta fita da sauri, da gudu ta karasa part dinsu ta shige parlor ta sa makulli tana turo baki, xaunawa tayi tana kallon wayar ta bude taga ba lock, gallery ta shiga ta ci karo da hotan Farida a WhatsApp images, ta shiga wajen, duk yawanci hotunan farida ne ta ajiye wayar ta kunna TV nan parlor ta kwanta kan kujera ta ci gaba da kallonta. Mujaheed na kallon agogon wrist dinsa yace "Aunty xan wuce aiki yanxu..." Aunty dake hada stew tace "Toh Allah ya kiyaye" fita yyi daga kitchen din ya wuce sama ya shiga dakinsa, makullin mota ya dauka ya kara feshe jikinsa da turare, ya juya xuwa saman gado xai dau waya yaga babu, da mamaki ya dinga kallon inda ya ajiye wayar, ya fito ya duba dakin Aunty ko ya mancesa a ciki ne yaga babu, fitowa yyi daga dakin yana sauka stairs yyi still a zuciyarsa yace Imaan, to yaushe ta shigo?? karasa sauka yyi ya fita parlon dai dai shigowar daddy compound din da mota, a hankali yace "Shit" Ya tsaya har Daddy ya fito daga motar, ganin leda a hannunsa ya karasa da sauri ya amsa yana masa sannu da dawowa, daddy yace "Thanks Muhammad, Barrister ya dawo?" Mujaheed yace "A'a bai dawo ba" a tare suka karasa apartment din Daddy dake amsa call da ya shigo wayarsa, Daddy yyi knocking, Imaan dake kwance ta mike xaune da sauri tana xaro ido tace "Waye wannan?" Daddy yace "Open the door" tashi tayi ta bude kofar, Daddy ya ci gaba da wayar da yake, ta wani xaro ido ganin Mujaheed ta juya da sauri ta koma ciki, Mujaheed ya saci kallon Daddy sannan ya shiga, Har ta dauke wayar nasa da ke ajiye kan kujera xata gudu ya fixgota, ba daman tayi ihu hakan yasa ta gatsa masa cixo a hannu da duk strength dinta, ba shiri ya saketa, da gudu ta nufi dakinta, sai a kan idon Daddy da ya shigo ya dinga kallonta da mamaki yace "Zo nan Imaan, whats wrong with you?" Kamar xata yi kuka tace "Daddy yaya ne" Mujaheed ya kasa daga kai ya ji kamar ya nutse a wajen, Yyi saurin ajiye ledan hannunsa yace "Abba xan wuce gun aiki" bai jira cewar daddy ba ya nufi kofa ya fita. Da Magrib imaan ta tafi kai ma inna abinci bayan ta sake boye wayar Mujaheed da kyau, duk kiran da aka dinga masa na Farida kawai ta daga, tun da ta fito compound dama gabanta ke faduwa, da sauri sauri ta karasa part din Inna, Yusuf ta gani xaune, ta wara ido ta ajiye abincin hannunta tace "Lahh ya Yusuf yaushe ku ka dawo?" Ya kalleta ya d'an yi murmushi yace "Daxu..." Inna tace "Baki ga da ya shigo ba daxu duk a kode wllh, ai yanxu ya washe a haka, Allah ya rufa ma ke da Mujaheed asiri ba ku je ba, baku da rabon wahala, amma wannan garin ae ba wajen xuwa bane tirr" Imaan ta duka kusa da shi tana dariya tace "Toh me ka kawo min ya Yusuf" ya shafa kansa bai ce komai ba, Inna tace "Yauwa ina maka xancen kirki kafin wannan mata ta shigo..." Ya sauke ajiyar xuciya a hankali yace "Ae ina ji" tace "Ko kai ya ka gani, wannan ba shawara mai kyau bace na kawo?" Da kamar baxae ce komai ba sai kuma yace "Da dai kiyi hakuri a bar xancen inna...." Ta katse sa da sauri tana gwalo ido tace "Xancen auren?" Calmly yace "Ehh" inna ta saki baki tace "Ehh lallai kai da Mujaheed kun xama abun tsoro, yanxu har kai isuhu bakin ciki kake ma yar uwar taka? Anya 'ya yan Ahmadu xa ku ga annabi kuwa? Ba kunya ba tsoron Allah ku fito kiri kiri kuna nuna ma yar uwar ku bakin ciki" Shi dai kallonta kawai yake, imaan ma sai kallonta take don bata gane kan xancen ba, Inna na tabe baki tana girgixa kai tace "Har abada in dai ni yar halas ce ba ni ba shawara da gantalallu irin ku, tun da haka ku ka xama gwara in yi ta kaina, to wai tsaya idan aka ki gabatar da ita jika ta xa mu yi mu baku ku shanye?" Nan ma dai bai ce mata komai ba, ta rike ha6a tace "Ai ni na shiga uku, lallai 'ya yan Ahmadu mugaye ne, sam ba alheri a ranku, to wai tsaya... ku xa ku aureta idan aka bar xancen?" Ya kalleta yace "Kika sani?" Imaan da ta fara dago xancen ta wani hade rai xata mike ta bar parlon Inna ta riga ta, tana kallon Yusuf cikin rashin hankali tace "Ku har kuna da kudin da xa ku rike min jikata? Ku a su wa kuma Allah na tuba, lallai kun cika marasa tsoron Allah, me kuma Imaan xata yi da kai ko Mujaheed Idan ba sa6o kake son yi ba, ka ja mana fushin ubangiji...." Murmushi kawai Yusuf yake, imaan ta nufi kofa xata fita, still tayi jin kamshin Mujaheed, juyawa tayi da sauri ta nufi dakin inna tana cewa "Kar ku ce masa ina nan" Mujaheed ya shigo parlon bayan few seconds, inna ta xauna tace "Imaan dai bata nan idan ma ita ka xo nema" Mikewa Yusuf yyi ya nufi kofa ya fita. Bedroom dinta Mujaheed ya nufa direct, inna tace "Da dai ka kinkimota ku fito don na share dakina tasss ba ko kwayar datti, kada a bata min a cuce ni ba uban wani ke min gyaran ba" Imaan na jin dama inna tace masa bata nan tasan dole xai shigo dakin, ta shige bayi da sauri ta sa makulli, Mujaheed ya murda kofar bathroom ya ji a kulle, juyawa yyi ya dawo parlor yana kallon inna yace "Kiyi mata magana ta ban wayata kada in sa ta kuka" Inna tace "Ikon Allah ya fi gaban haka, lkcn da wayar ya fita hannun ka ya shiga nata sani nayi Mujaheed? Kaji min raini dai, ni dai ta fito min daki gaskiya don ba Aisha bace ta share min" ya gyada kai ya juya ya fita parlon, Da kyar Imaan ta yarda ta fito bayan tafiyarsa da kusan minti goma, Inna dake tsaye bakin kofar bathroom din tace "To uwar me kike masa da wayar sa ya taba ki ya taba alakakai ya taba jaraba, ke dai ki daina tsokanan mutane kiyi ma kanki fada Imaan" Imaan ta fice a dakin, inna tace "Da dai ya kama ki ya nakada maki shegen duka da xai gigitaki in ga me ce masa don me a gidan nan, yarinya kawai kamar yar aljanu, wannan iri ta Bukar Allah ka raba mu da ita lafiya, duk da dai lkci ya kusa" A hankali Imaan ta bude kofar parlorn inna ta fita, ta gwammace tayi xagaye da ta bi normal route, da gudu ta shige parlon su ta sa makulli tana murmushi. Karfe tara da wani abu Ammi ta shigo dakin Imaan, Imaan dake xaune gaban madubi ta fito wanka kenan tace "Na xaton fa kinyi bacci" Ammi tace "Ki ji da ni kwanciya xan je inyi" mikewa tayi ta hau saman gado Ammi na kallon wayar kan gadon tace "Wayar waye wannan?" Imaan tace "Na yaya ne" Ammi na mata wani kallo tace "Me wayarsa yake a nan?" Kamar xata yi kuka tace "Ammi to ya dauke min nawa wayar ya ki ya bani" Ammi na kallonta da kyau tace "Kin san Allah idan baki kame kanki gidan nan ba kin raba kanki da Mujaheed sai na sa6a maki Imaan, yaushe ke da shi ku ka fara shirin da har xa ki dauke masa waya?" Imaan dai bata ce komai ba, Ammi ta hade rai sosai tace "Let me make it brief, daga yau na datse sabon alakar ku na gulma da Mujaheed, duk kika kuskura naga sabanin abinda nace wllh sai kin sha mamaki na, ko dama kin hada wani abu da shi ne ban sani ba? Kuma maxa ki kai ma inna wayar ta basa kayansa, naki kuma idan ya ga daman baki toh, idan kuma bai baki ba ki bar sa, hope am clear?" Kai kawai Imaan ta daga mata a hankali, Ammi tace "Shegantaka kawai, wai wani yaya, A'a ba yaya ba yayo, in sake ganin kin kalli inda yake a gidan nan idan ban tsole maki idanuwa ba" daga haka ta shafa mata lotion din maganinta sannan tace "Ki rage fan din, sai da safe" daga haka Ammi ta fita ta kulle mata kofa, Imaan ta saka kayan baccinta ta koma mirror tana shafa lotion a kafarta taji ana bude window, mikewa tayi da sauri tana kallon window din, ido hudu suka yi da Mujaheed ta dauke kai, strictly taji yace "Bani wayata" Ta make kafada tace "Nima ka bani nawa first" Yace "Na fara maki wasa a gidan nan koh?" Ta ki cewa komai ta daura kafarta kan stool dake gaban mirror tana shafa lotion dinta, jin shiru ta juya, kallonta taga yana yi da lumsassun idanuwansa, ta hade rai tace "Yaya yanxu idan sauro ya cije ni na fara rashin lafiya fa? Dubi yanda ka bude min window fa, ni dai ba ruwana idan na fara ciwo" calmly yace "Kar ki bari in shigo gidan nan, wllh xan sa ki kuka, give me my phone I want to use it" yar dariya tayi ta dau turare tana fesawa, yace "OK kina xaton baxan iya shigowa bane?" Ta wara ido tace "Toh ai bance maka kar ka shigo ba" Tana fadin haka ta karasa saman gado ta kwanta ta rufe da duvet, rufe window din yyi yana gyada kai ya bar wajen. Mujaheed xai shiga parlon su suka hadu da Daddy, gaida sa yyi da ladabi daddy na tambayarsa ya aiki yace "Alhmdllh" yana tsaye har daddy ya shiga gun Abba, ya d'an yi jim, can ya tafi apartment din su imaan, ya fi second goma tsaye ya kasa bude kofar, A hankali ya murda kofar ya shiga yana kallon cikin parlon, babu kowa sai tv dake kunne, dakin Imaan ya nufa ya bude kofar, kwance ya ganta har ta yi bacci, ya dinga bin dakin da kallo ya karasa kusa da ita, daukar wayarsa da ta ajiye bedside drawer yyi yana kallonta, gaba daya ta takure waje daya saman gadon sleeping peacefully sai dai ta cire duvet din, dauka yyi ya rufa mata ya tafi gun switch din fan din dakin ya kashe fan din gaba daya ya juya xai fita yaga Ammi tsaye bakin kofa, still yyi ya kasa cewa komai, lkci daya ya sauke kansa ya fara kame kame yace "I... I came to take my phone"


*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻‍♀️

It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.p.Ammi ta dinga kallonsa kafin a nutse tace "I want to give u this warning Mujaheed, stay away from Imaan" shi dai bai yarda ya kalleta ba, bai kuma ce komai ba, juyawa tayi ta bar bakin kofar, Mujaheed ya fita xuwa kofar fita parlon. Washegari da safe Imaan ba inda bata duba ba a dakin tana neman wayar Mujaheed ganin bata gansa inda ta ajiye ba, kamar xata yi kuka ta fito parlor sanye da uniform din islamiyya, tana kallon Ammi a hankali tace "Ammi kin ga wayar nan na jiya?" Ammi ta mata wani kallo tace "Wanda kika bani ajiya?" Shiru tayi bata ce komai ba, Ganin ko kallonta Ammi bata sake yi ba ta juya ta wuce dinning don yin breakfast, mamaki ta dinga yi ta ya xata nemi wayar ta rasa a inda ta ajiye, daga karshe tayi concluding kawai Ammi ce ta boye, ta tura soyayyen dankalin gabanta ta mike ta dawo cikin parlor, safarta ta sa ta xura Hijab din makarantarta ta dau jaka tana kallon Ammi dake parlor kamar xata yi kuka tace "Ammi fa kila xai yi amfani da wayarsa don Allah ki bani in kai masa plss" Ammi ta daga kai tana kallonta, da sauri Imaan ta fice daga parlon don ta san sauran, parking space ta tafi ta tsaya tana jiran su Maimoon su fito, Mujaheed ne ya fito tare da Yusuf, Imaan ta dinga kallon hannunsa da mamaki ganin wayarsa, bai ko kalli inda take ba ya nufi gun motarsa ya bude ya shiga, Yusuf dake kallonta yyi murmushi yace "Why are you looking at him that way" kamar xata yi kuka tace "Ya Yusuf jiya ya dauke min wayata shine nima naje dakinsa na dauke nasa toh yanxu ga na sa a hannunsa ban san ya aka yi ya dauke ba, ni kuma nawa har yanxu ya ki bani" Yusuf yace "Toh me yasa ya dauke wayar ta ki?" Tace "Nima ban sani ba kuma har daki na ya shiga ya dauka, ni dai wllh ya bani waya ta xan je in gaya sa da inna" Yusuf ya kalli Mujaheed da har ya tada motarsa amma idonsa na kansu, dauke kai Yusuf yyi yace "Yaushe har ku ka fara shiri da Mujaheed da har ya shiga dakin ki ya dauke waya?" Ta turo baki tace "Ni ba wani shirin da mu ke, kawai ganinsa nayi a dakina bayan Ammi da daddy sun fita" Yusuf ya sake kallon Mujaheed da yaki driving din motarsa, ya dauke kai, Imaan tace "Ya Yusuf ka yi masa magana plss kuma fa ana kirana a wayar" Yusuf yace "Wa ke kiran ki?" Boye fuskarta tayi ta fara dariya, Yusuf ya dinga kallonta, ta xame Hijab din da ta rufe fuskarta a hankali, sai a sannan ya sauke idonsa yace "Baxa ki gaya min ba" ta wara ido tace "Ya Yusuf wani ne, he is my friend" jin Yusuf bai ce komai ba tace "Ni dai kafin su fito bari in je in gaya ma inna" daga haka ta wuce ya bi ta da ido kamar yanda Mujaheed ma ya bi ta da kallo, waje ta ga inna tana ta faman goge window with seriousness, Imaan tace "Ina kwana inna" Inna ta d'an kalleta kafin ta dauke kai tace "Aa ba wani inna ina kwana, ke din ce xa ki xo gaisheni takanas da safe, ke dai fadi abinda ya kawo ki ina ji" Imaan tace "Toh ko ba yaya bane ya dauke min wayata tun jiya ya ki bani" Kamar xata yi kuka ta kare maganar, Inna ta ajiye tsumman hannunta a bokiti da mamaki tace "Waye kuma yaya?" Imaan ta rungume hannunta xata yi kuka, inna tace "Lallai ba lafiya, shi Mujaheed din akwai wani alaka ne tsakanin ku wanda ni ban sani ba da har xai dauke maki waya? ko sata ya fara yi ba a sani ba a gidan, ni dai naga abinda ya isheni, gaskiya wannan d'a na Ahmadu yana cutar mu a gidan nan, to meye kuma xai dauke maki waya kamar shi ya siya? ko yana bin ki bashi ne? Toh a gaskiya ya kamata Mujaheed yyi aure ya kama gabansa na gaji da maganarsa kuma haka Allah ya gani nayi kokari, shekara kusan talatin da biyu ana abu daya, wannan ai fitinanne ne mara son xaman lafiya, mu je gun Ahmadu in ji ko shi ke koya masa ya dinga walakanta ni a gidan nan" daga haka inna tayi gaba imaan ta bi bayanta, Inna ta tsaya kamar warce taga mugun abu ta juyo da sauri tana kallon Imaan tace "Toh da ya dauke wayar ta ina Bulasawan ke kiran ki?" Imaan tace "Toh ba wayar na wajensa ba, kila ma ana ta kirana ya daga" Inna ta saki salati tace "Ashe yau xa a ga barbadin fitina a gidan nan, mu je gun Ahmadun" Yusuf na nan tsaye inda yake, Mujaheed kuma ya wuce kenan inna ta iso kamar xata tashi sama, Yusuf na kallonta yace "Ina kwana Inna" a fusace ta juya tana kallonsa tace "Da ban kwana ba xaka gan ni, ko a titi kake gaida uwarka Amina, to hirr dinka... Dama duk gantalallen da yace jikata xai sa ma ido ya dinga yi ma bakin ciki to yyi ta kansa inyi nawa a gidan nan, ba ruwana, kada ma ka sake gaisheni bana so, ko kuma in tsine ma gaisuwar...." Kallonta kawai Yusuf yake bai ce komai ba, Inna ta wuce kamar xata tashi sama, imaan da ta ki yarda ta kallesa ta bi bayanta, Anty na goge goge parlon Abba inna ta shiga imaan na biye da ita, Anty tana kallonta tace "Ina kwana Inna?" Inna tace "Ke ba xancen ina kwana, Amina ashe kema jaraban kika haifa ban sani ba sai jiya, ashe Isuhu ma ba mutumin kirki bane na banxa ne ni ban sani ba, ashe halinsa daya da tijararren nan Mujaheed, to Ahmadu ya ga ta kansa kuwa don wannan ba yaran nunawa bane, banda haka ta ya xa su nuna bakin ciki da hassadansu a fili kan jikata, daga Allah ya axurtata da mai kudi saurayi sabon jini sai hassada ya tashi? toh wllh su cire idanuwansu kan imaan, shi Isuhu tsabar shaharan da yayi a fannin bak'in ciki ce min yyi a bar xancen sabon saurayin ma gaba daya, ke ki ji min mugunta, kice min lalacewa bai xo duniya ba?? saboda mamakin abinda yace min sai nake tambayarsa ko idan aka bar batun sabon saurayin su xa su aureta?? Budan bakin katon sai ce min yyi to na sani ko su xa su auretan? Ke ki ji wani sa6o fa, kawai ya ja gida ya rushe da ni a ciki" Inna ta fara matsar kwalla tace "Yanxu Isuhu bai ji kunyar gaya min haka ba, idan ba ta6ewar basira ba dama ina su ina Imaan daga shi har Mujaheed din, wllh ta fi karfinsu, me garesu da har xa su rike min ita salon wataran in xo daukar gawarta ina kuka suna bani hakuri, haka kawai su kai ni su baro, yanxu fisabilillahi Allah ya dubeni ya fiddo mata dai dai ita kuma sai bakin cikin yan uwa ya tashi, to Allah ya so ni dama ba abinda na hada da su, ba dangin iya balle na baba, kawai ni dai nasan na haifi Ahmadu shi kuma ya haifesu, ni sai ince Bukar ya tattara ya bar gidan ma...." Shigowar Abba yasa ta dakata, Abba na kallonta yace "Lafiya inna?" A fusace tace "Ina fa lafiya Ahmadu isuhu da Mujaheed sun fi karfina, kawai yaro ya dage ya kwace ma yarinya waya sai kace Rukayya ce ta siya wayar, to wllh kafata kafar wayar nan yau idan ba haka ba in bar kowa da Allah, kuma gaskiya a daina bata min rai gidan nan don duk ranan da xuciya ta debeni idan ban bi Bukar Abuja ba ace bani bace" Abba dai ya kasa cewa komai, Ajiyar xuciya Anty ta sauke tace "Toh ina Mujaheed din?" Inna tace "Sai ki tambayeni Mujaheed ba tare ku ka kwana gidan nan ba ke kuma" Abba ya dau wayarsa yyi dialing number Mujaheed, Mujaheed na driving ya daga wayar, Abba yace "Where did you drop imaan's phone?" A hankali Mujaheed yace "It's with me" Abba yace "Bring it back now" daga haka Abba ya katse wayar, inna ta xauna kan kujera tana kallon Imaan tace "Xauna mu ga ta inda wayar xai fito" Imaan da ta ki yarda ta kalli Abba ko Aunty ta karasa kusa da inna ta xauna, Inna tace "Ahmadu dai bai yi sa'an 'ya ya ba gaskiya, don Mujaheed da Isuhu sai su iya kashe mutum" Anty ta ci gaba da aikin da take yi, Inna sai girgixa kafa take bayan kusan minti goma sai ga Mujaheed ya shigo parlon, Inna tace "Huuuu an dai ji kunya, fito da wayar da ka dauke" Mujaheed dai bai ko kalleta ba ya mika ma Abba wayar, Abba ya mike ya ba inna, inna ta karbe ta mika ma imaan tace "Tashi mu je, daga yau dama duk inda kika ga Mujaheed ki canza hanya da gudu don ba mutumin kirki bane" Imaan ta mike ta bi bayan inna, inna ta bude kofa tana cewa "Sai kuma ka sace wayar Rukayya idan ta ajiye ba dai na imaan"
Karfe biyar saura na yamma Sadeeq yayi parking kofar gidan su Imaan ya kashe motarsa ya jinginar da kujeran motar, Muhsin dake kallonsa yace "Ya da gyara xama kuma Doctor" Sadeeq ya shafa kansa a hankali yace "Ni fa I told you ban taba xuwa gidansu yarinyar da nake nema gun iyayenta ba, I don't even know where to start from, to idan ma na shiga me xan ce masu? All that aside, ni ban ma san me yasa ake nemana ba" Muhsin yyi dariya yace "Toh dama kuwa ina xaka je gidan su yarinyar da kake nema bayan duk turawa ne Sadeeq, kaga kawai idan baxa ka iya shiga ba mu rabu da su mu koma kada mu je ka kunyata ni gaskiya" Sadeeq ya sauke glass din idonsa yana kallon Muhsin, can yyi murmushin sa mai kyau cikin cool voice dinsa yace "In koma fa kace" Bai jira cewar Muhsin ba ya mayar da glass dinsa ya bude motar ya fita, sanye yake da kananun kaya da suka yi matukar amsan jikinsa, Muhsin ya fito motar yana kallonsa yace "Ehh lallai Abokina ya xurma da yawa"

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment