Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fito kitchen, ganin Mujaheed xai fita masallaci tace "Dr idan ka dawo mosque ka sameni bedroom" Yace "Toh" daga haka ya fita parlon, tare suka dawo masallacin da Yusuf, bayan sun haura sama Mujaheed ya shiga dakin Anty, Yusuf ya shiga dakinsa, Anty na xaune kan darduma ta shafe addu'o'in da take ta mike ta dauke pray mat din ta linke tana kallonsa tace "Toh ka tsaya min kamar soja a kai ka xauna" murmushi yayi yana shafa kansa ya xauna gefen gadon, tace "Yanxu M.A idan kowa ya guji inna kai ma sai ka gujeta" ya d'an buda ido yace "Inna kuma?" Tace "Eh mana" yace "Ban gane ba Anty" tace "Kirana tayi daxu wai kwana shidda rabon da kaje bangarenta kai da Imaan" Mujaheed yyi murmushi bai ce komai ba, Anty tace "Toh ka gama murmushin ka tashi ka ta fi ka gaisheta" mikewa yayi yace "Wa?? Ai har abada ni da xuwa apartment dinta, beside irin warning da Abba ya min ma is not funny don haka..." Anty ta karasa masa tace "Baxa kaje ba koh?" Yace "Allah Anty kinga kwana biyu shiru bata ce an mata komai ba hakan bai fi ba?" Anty tace "Toh ni dai nace ka tashi ka je" ya mike xaune yace "Anty ki bari kawai ba inda xanje" Anty tace "Wato ban isa da kai ba kenan, idan Hajiya ce tace kaje xaka ce mata ba xa ka ba?" Yayi murmushi yace "Anty Hajiyan ma hanani xuwa bangaren tayi gaba daya" Anty tace "Toh tashi ka fita ka ban waje" ya marairaice mata yace "Wllh Anty ina iya xuwa yanxu tace nayi mata wani abun" Anty ta hade rai tace "Cewa nayi ka gaisheta kawai ka juyo" Ya lumshe ido ya bude yace "Wllh da ba don ke bace ni ba inda xanje Anty" Anty tace "Naji din tashi ka fita, idan ka dawo kuma ka xo ka gaya min, gobe da safe kuma xan je in ji ko ka je" Murmushi yyi ya mike ya fita dakin. Tun da Imaan ta fito parlonsu rike da warmer din abinci take tsaye jikin wani flower taki tafiya, kiris ya rage ta fashe Inda take tsaye, daga nisa ta hango Mujaheed yana tahowa waya kare kunnensa, labewa tayi ta koma bayan flower din ta tsaya da sauri, sai da ya d'an wuce inda take ta fito tayi wani kara a bayansa, still yyi na few seconds, ta fashe da dariya ya juya yana kallonta, ya wani hade rai yace "Kee" Ta wara manyan idonta tace "Toh ai baka ji tsoron ba ma" Wani kallo ya dinga mata, ta turo baki ta wuce sa, sai da ya ga tayi nisa sannan ya bi bayan ta, tsaye ya ganta tana lekan parlon inna don kofar ba duka aka rufe ba, ya cire takalmansa outside the balcony yayi tiptoeing har bayan ta, fingers dinsa ya kai gefen cikinta yayi tingling dinta, ihu ta fasa ta sake abincin hannunta, tuni ya janyeta wajen don gaba daya tuwo da miyar dake warmer din ya tarwatse a kasa, ta xaro ido a rikice tace "Innalillahi yaya ka xubar" daga cikin parlor inna ta dinga cewa "Me aka 6arar??" Ummi ta bude kofar, Imaan dai sai kallon abincin take kamar xata yi kuka, Inna ta mike ta taho wajen tace "Meye hakan?" Kamar xata yi kuka tace "Yaya ne ya xubar da abincin da na kawo maki" Inna tace "Toh sai ki kwashe ki mayar mata ta canxa min wani ba ruwana" Imaan ta shige parlon ta xauna ta rungume hannu tace "Salon Ammi ta doke ni ba ga abinci nan Ummi ta kawo maki ba" Inna tace "Aa wllh kinga ina cin wani abu banda tuwo, Ummi maxa kwashe ki kai ma Aisha kice yar ta ta xubar ta xubo min wani" Ummi tace "Mu ma fa tuwo muka yi" A fusace Inna tace "To ni ina ruwana da tuwon ku? Ku tuwon ku har wani dadi garesa miya kamar an wanke kai, ki min abinda nace kada ran kowa ya baci a gidan nan" Ummi ta mike a fusace ta kwashe tuwon ta mayar cikin warmer din, Imaan tace "Dama kice yaya ne ya xubar na ni ba" Inna tace "Haba dai, dama ina xa ki iya xubar da wannan abincin ai sai dai shi" Tsallake miyar Mujaheed yyi ya shiga parlon ya xauna, Ummi ta tafi da abincin da ta kwashe part din su Imaan, gyaran wajen inna ta dinga yi duk suna xaune, bata gama ba Ummi ta dawo da wani abincin ta ajiye ma inna tace "Imaan Ammin ki tace xa ki dawo ki sameta" Inna tace "Sai me xai faruwa idan ta sameta, bakin cikin kara min abinci take komai, ina laifin ma tace xata gamu da Mujaheed din, Imaan ce ta wani san xubar da abincin mutane, bata ta6a ba tunda take, lafiya take kawo min abinci ta koma to yau da yake ta hadu da wnn mutumi a hanya" tana kai wa nan ta shiga parlon tana kallon Ummi tace "Don Allah ki rufa min asiri ki taimakeni ki karasa goge wajen baki ji bayana ba kamar xae cire" Ummi tace "Toh su da suka xubar...." Kallon da Mujaheed ke mata yasa tayi shiru ta mike rai ba dadi ta fita ta ci gaba da gyaran wajen. Inna ta shiga daki sai ga ta ta fito da bowl na dambun nama, tace "Tun ranan litinin nake ta ajiya amma ban gan ku ba na nace to ko lafiya, na ba kowa nasa...." Mujaheed ya amsa yace "Na waye wannan din?" Tace "Na kai da takwara ta" Ya saci kallon Imaan, da sauri Imaan tace "Inna ni dai ki raba mana da kanki" Mujaheed yace "Toh samo leda sai ki raba mana" komawa daki Inna ta yi, Mujaheed ya mike kafin Imaan ta ankara har ya fice parlon, kwalo ma inna kira ta yi, ya saka takalminsa ya kara gaba, inna ta leko parlon tace "Lafiya!" Imaan ta fara kuka tace "Ya tafi da naman gaba daya" inna tace "Maxa tashi ki bisa in ya kama ki je parlon Ahmadu ki tafi" Imaan ta mike ta fita parlon, bata son gudu saboda laluranta, hakan yasa kafin ta iske sa har ya shige part din su, ta goge hawayen da ya cika idonta a ranta tace "Allah ya isa" daga haka ta wuce apartment dinsu kawai, Sai da ta tsaya Ammi ta gama fadanta na xubar da abinci da tayi sannan ta shiga bedroom dinta. Bayan isha tana saka kayan baccinta wayar ta ya fara ring, duk tunaninta Sadeeq ne don kullum sai ya kira ta da daddare sun gaisa duk da basa waya mai tsawo iyaka gaisuwa shikenan amma har wani murna take idan ya kirata, Daddy ta ga ke kiranta, ta daga a hankali tace "Ina yini daddy" yace "Lafiya lau Mamana, ya gida?" Tace "Alhmdlh ya aiki?" Yace "Da godiya, kina karatu sosai dai koh?" Tace "Ehh ina yi" yace "Maa sha Allah, daxu kafin magrib inna ta kirani wai sati daya kenan baki je gaisheta ba, why is that?" Imaan tace "Daddy na fa je yau" Daddy yace "All those days me ya hanaki xuwa?" Tace "Cewa tayi kar mu sake xuwa ni da yaya fa" yace "That's because kuna mata rashin kunya ke da shi, wato warning da na maki kafin in tafi went in vain koh?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Toh kar ki sake skipping one day baki je gaisheta ba, idan Ammin ki ce don ta maki fada xa ki k'i xuwa gaisheta, she is my mother Imaan you have to respect her much, shi ma Mujaheed na kirasa ban samesa ba ki kai masa waya yanxu" Kamar xata yi kuka tace "Toh" daga haka ya katse wayarsa, Hijab ta sa har kasa ta fita, Ammi dake parlor tana kallo ta bi ta da ido, Imaan tace "Daddy yace in kai ma yaya waya" Ammi tace "Shi me ya samu wayarsa?" Bude hannu tayi alamar bata sani ba, Ammi ta ci gaba da kallonta, hakan yasa ta nufi kofa ta fita. Babu kowa babban parlon nasu don hatta kayan kallo ma a kashe suke, ta haura sama ta na kallon direction din dakinsa don har ta manta rabon da ta je wajen, takawa tayi har bakin kofar sannan ta bude tana lekan cikin bedroom din, wani sanyayyen kamshi me hade da sanyi ya doki hancinta da fuskarta, shiga dakin tayi ta kulle kofar, ko ina fes har kan gadon dake dauke da farin bedsheet, Ko ba a fada mata ba tasan wanka yake jin saukan ruwa da kamshin sabulu da ya hadu da kamshin dakin, xaro ido tayi tana kallon sketches dinta dake bangon dakin kusan gudu hudu, tun tana Jss3 tayi drawing din mai kyau coz she is more than perfect a zane, turo baki tayi ta dau kujeran dake gaban mirror ta kai jikin bangon ta hau ta dinga cire hard carbon paper din a hankali kar ya yage. Bude kofar bathroom Mujaheed yyi ya fito da short yana goge gashin kansa da karamin towel, xaro ido yyi yana kallonta da mamaki, ta juya jin an bude kofa suna hada ido ta turo baki tace "Yaya daddyna yace in kawo maka waya" Tana magana wayarta da ta ajiye kan gado ya fara ring, sakkowa tayi da sauri ta dau wayar tace "Ga shi nan ya kara kira" daga haka ta nufesa ta daga kiran ta kai kunne tace "Daddy ga shi nan" mika masa wayar tayi ya amsa ya kai kunne hade da sallama, Kamar ance ta juya taga bowl din dambun naman da ya dauke ajiye a gaban mirror dinsa, yana magana da daddy amma duk hankalinsa na kanta kuma yana lura da ita, ganin ta nufi gun mirror din ya fixgota, xaro ido tayi xata yi magana ya rufe bakin, sai ce ma daddy yake toh don ya kagu ya katse wayar, kamar kuwa daddy ya shiga ransa yace "Shikenan we will talk tomorrow sae da safe" da sauri yace "Allah ya tashe mu lafiya Abba, mun gode, sae da safe" daga haka ya katse wayar ya juyota yana mata wani irin kallo yace "Drawings din da kika cire nake so ki hau kujeran ki maida su yanxu kafin ki fada min sanda na fara wasa da ke da xaki shigo min daki kai tsaye" ta 6ata fuska tace "Toh ba waya na kawo maka ba" Jan kunnenta yayi yace "Baxa kiyi knocking idan kinji ba a amsa ba kiyi wucewar ki" muryar Umma suka ji a corridor tana ma Maimoon masifa wai ta share datti ta kai bakin kofarta lkci daya kuma tana tambayarta ko Mujaheed na dakinsa, Maimoon da ta hade rai tace "Yana ciki" Mujaheed ya xaro ido ya ja Imaan ya bude kofar bathroom dinsa suka shiga ya kulle kofar, dai dai nan kuma Umma ta shigo dakin tana kiran sunansa, Irin tsoratan da imaan tayi ba a cewa komai, Mujaheed ya dukar da ita kasan bayin murya can kasa yace "Kee you better relax now kar in mare ki, ance maki xata shigo nan ne" kai kawai take gyada masa numfashinta na sama, ya cire Hijab din jikinta yace "Nace maki ba fa shigowa xata yi ba, breath in and out gently now" jingina take son yi da bango ya jawota jikinsa ya rungumeta yana shafa bayan ta a hankali to calm her down, tuni Umma ta fice dakin ganin Mujaheed bai ciki, bayan kusan minti biyar jin tana fitar da numfashin a hankali kuma a nutse ya dago kanta yana kallonta, hawaye ne makale idonta, ya daure fuska yace "What?" A hankali ta nuna masa kirjinta, ya mike ya fita bathroom din ya sa makulli kofar dakin sannan ya dawo ya fito da ita dakin, wajen da yake ajiye drugs da allura ya bude yana dube dube, can kasa ya hango inhaler dinta da take bari a dakinsa a da idan ta xo, ya juya ya kalleta ya ga kwanciya tayi kan gadonsa ta takure waje daya, ya mayar da inhaler din ya mike, ya dau gogaggen jallabiyarsa ya saka don tuni jikinsa ya bushe, ya feshe jikin sa da turare, ya dau drawings da ta ciro ya fara maidawa jikin Bangon, Imaan ta mike xaune tana turo baki xata ce masa don me idonta ya kara sauka kan dambun dake gaban mirror, tashi tayi a hankali har sannan hannunta na kirjinta ta isa gaban mirror din ta dau bowl din, karan bude kofar da yaji ya sa ya juya, xata fita da gudu ya bi bayanta da sauri yana cewa "ke har kin manta abinda ya same ki a bathroom ynxu koh, ba ruwana fa idan...." Tuni ta fara sauka stairs, sai da ya tabbatar ba kowa corridor sannan ya bi bayan ta da sauri, amma har ta fita gidan, can ya hangota a durkushe kusa da apartment dinsu, karasawa yyi kusa da ita a hanxarce, ya durkusa kusa da ita yace "Ba nace kar kiyi gudu ba..." Dagata yyi ganin Asthman ne ya tashi ya amshi bowl din, ya wuce da ita cikin apartment dinsu, Ammi ta tabe baki ta mike ta dauko inhaler ta jefa masu, sai da ya ga numfashinta ya dawo dai dai sannan ya mike ya dau bowl din naman ya ajiye a kafarta yana mata wani kallo ya fita parlon, a hankali take sauke numfashi ta bude bowl din ta fara cin naman.


*The book Imaan is not free, it's for sale, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻‍♀️

It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.


Kindly patronize ur writer for continuation, tnx 07087865788.Ranan Friday Imaan suka gama exams din first term ss2, suna tsaye tare da Mariya a bakin gate din makarantar tasu ko wannensu na jiran driver, Ummi da Rahma ko fitowa cikin schl din ma basu yi ba, Maimoon dai na tare da wata Kawarta a waje ita ma, Mariya na ganin motar Sadeeq tace "Lahh ya Sadeeq ne ma ashe shi sa ya bata mana lokaci" Imaan dai bata ce komai ba, tunda yayi parking idonsa ke kan Imaan, suna had a ido gabanta ya fadi, siblings din sa duk suka shiga motar, Mariya bata taba sanin Yayan nata na interacting da Imaan ba don Imaan din bata gaya mata ba, Mariya tace "Mu je ku gaisa da shi, shine ya ta6a ajiye ki gida ko baki gane sa ba" Imaan ta d'an yi murmushi kawai, Mariya ta kama hannunta suka nufi gun motar, Mariya tace "Ya Sadeeq frnd dita da ka taba ajiyewa a gida..." Ya cire glass din idonsa Yace "Yea na gane ta" Imaan ta sauke idonta kasa tace "Ina yini?" yace lafiya lau, fatan an gama exams lafiya" tace "Alhmdllh" yace "Toh Allah bada result mai kyau" ta daga kai tana kallonsa tace "Ameen" lallausan murmushi ya sakar mata ta dauke kai da sauri gabanta na faduwa, yace "Let drop u mana" ta girgixa kai tace "Aa yanxu driver din mu xai xo" Yace "Ohk then" ta saci kallonsa ya kashe mata ido daya, ta daga ma Mariya hannu ta juya da sauri ta tafi gun Maimoon, Sadeeq ya tada motar ya bar wajen, Ya Yusuf ne ya xo daukansu bayan tafiyar su Sadeeq da kusan minti bakwai, Maimoon na turo baki tace "Ya Yusuf driver din fa?" Yusuf yace "Ya kai su Umma kasuwa, M.A aka ce ya dauko ku tun daxu ya ki, ni kuma ynxu na dawo aiki" Maimoon ta kyabe baki tace "Da dai Anty Farida aka ce yaje ya dauko, jiya fa da yamma har Hayin d'an bushiya muka je daukota taje gidan aunt dinta, baka ga uwar wahalan da muka sha ba ga hold up sai kusan shidda da rabi muka dawo gida" Yusuf yace "Au suna tare har yanxu kenan?" Maimoon tace "Tab, sosai ma, gobe xata koma schl sai kaga tulin shopping da yayi mata" Yusuf ya sake baki yana kallonta, Maimoon ta kyalkyale da dariya tace "Amma fa wllh ya Yusuf kar ka ce masa komai, dama yace kar in fadawa kowa" Yusuf yace "Ae ko kin fada ma kowa tunda kika fada gaban Imaan da Ummi" Imaan ta hade rai tana kallonsa ta madubi tace "Ya Yousuf kamar ya?" Ya wara ido yace "Ke sai ki kwasa ki kai ma inna, Ummi kuma ta gaya ma Umma, saukin abun dai idan magana ya fita an san it's either Imaan or Ummi sae M.A ya ji dadin jibgarku da kyau" Imaan ta xumburo baki tace "Naji dai" Ummi kuwa yi tayi kamar bata ji sa ba dama, suna isa gida Maimoon tace "Dama ya Yusuf ka ja masu kunne ba ruwana idan suka fada ma kowa" wani kallo Imaan ta watsa mata ta fice daga cikin motar tana turo baki ta kara gaba. Satin da aka shiga banda shirye shiryen bikin Seeyamah babu abinda ake a gidan, tun ranan lahadi yan uwa suka fara xuwa daga nesa gida ya fara cika da jama'a, kowa ya xama busy a gidan barin Umma da Anty, Ammi kam baya baya ta dinga yi, tun a ranan lahadin dama ta kai nata gudunmawarta na tsadaddun manyan bedsheets biyu, da set din food warmer shi ma biyu masu kyau sosai, a walakance Umma ta dubi kayan aka bar su a nan parlorn. Ranan laraba Abba ya ba su Maimoon kudin gyaran gashi da lalli a kai su Saloon, Har xa su fita ya dakatar da su ya ciro wani dubu biyar din yace "Na mance ban bada na mamana ba, gashi nan ta shirya ita ma ta je" Fita suka yi su hudu Ummi na cewa su yi wucewansu kawai don Imaan ba xuwa xata yi ba, Maimoon tace "Ba ruwana Abba cewa yyi mu je mu kira ta" A balcony suka tadda Anty tana magana da wa enda xa su yi girkin biki a biya su, Mujaheed ma na xaune balcony din sai Yusuf dake tsaye, Anty tace "Saloon din xa ku yanxu" Maimoon tace "Anty Abba yace mu je da imaan" Anty tayi wani dariya tace "Wace Imaan din tab, amma ku je dai ku ji abinda xata ce" Imaan na dakinta Maimoon ta shigo parlor, nan ta sanar ma Ammi abinda Abba yace Ammi ta kira Imaan, tana fitowa Ammi tace "sai ki dau Hijab ku wuce saloon" sosai gabanta ya fadi ta marairaice tace "Saloon kuma Ammi, aa ni dai xan wanke gashina da kai na" Ammi tace "Kee! dau Hijab ki fice min parlona, dama idan baki gyara gashin nan ba yau kar ki dawo min gidan nan" Imaan fa fashe da matsanancin kuka tana kallon uwar tata, ganin Ammi ta mike ta shiga daki da sauri ta dau Hijab dinta ta fita, Maimoon ta bi bayan ta tana dariya kasa kasa, Anty na ganinta tace "Subhanallahi me ya faru Imaan" cikin kuka tace "Anty ni fa gashina bashi da wani datti kawai combing dinsa ne bana yi" Anty tace "Toh mu ga gashin" tana shesshekar kuka ta cire Hijab din ta cire hulan kanta, Yusuf ya dauke kai bai son dariya ta fara wani sabon kukan, ga dai gashi har gashi amma duk an cukuikuye shi waje daya, Anty tace "When last kika wanke gashin" a hankali tace "Ranan nan" Anty tayi murmushi kafin ta ce komai Mujaheed ya mike fuska daure yace "Mu je in kai ku saloon din" Ta fashe da sabon kuka xata koma bayan Anty ya ja ta sai gun motarsa, Yusuf yayi murmushi yace "Da yake Umma bata nan ba" Su Maimoon duk suka shiga motar bayan ya tura Imaan ciki, Suna isa saloon din Imaan ta hadiye kukan da take barin da taga yan mata kala kala cikin saloon din, Ita Mujaheed yasa a fara gyara ma gashin, da ruwa mai dumi sosai yace a wanke mata gashin nata bayan an sa mai, banda turo baki bbu abinda take tana runtse ido don ba daman kuka ga yan mata kar su mata dariya, lkci daya gashinta ya dawo sak na Indians sai sheki yake, ganin an kusa gama mata ya kalli kannin nasa yace "Sai ku samu napep da xai maida ku gida, coz I am a driver to none of you" daga haka ya fice saloon din, duk suka bi sa da kallo. Sai bayan magrib suka shigo gidan don har da lalle suka yi, dama Imaan direct part din inna ta nufa tun daga bakin kofa ta cire Hijab din jikinta ta shiga tana murmushi tace "Inna..." Inna tayi mitsi mitsi da ido tana kallon gashin nata tace "Ikon Allah kin ganki kin fito sak mace ko?" Imaan ta xaro ido tace "Toh da ni na miji ne?" Inna tace "Idan ba kallon isuhu nake maki wani lkcn ba shegiya nake" Imaan ta fashe da dariya har da kwanciya kan kujera, Inna ta kalli Mujaheed dake cin abinci tace "Ko kai baka gani ba Mujaheed?" Imaan ta hararesa ta gefen ido ta mike xata shiga daki Inna tace "Dawo nan ana ma yar uwar ki gyaran jiki tunda can bangarensu ya dawo kamar wajen cin kasuwar laraba" Imaan tace "Anty Seeyama" Inna tace "Ehh kema da dai Allah ya fiddo maki da mijin nan kiyi aurenki da wuri ki haifi kanninki da uwarki taki haifo maki" Imaan ta hade rai tace "Yar karama da ni xaki ce min aure?" Inna ta kalli Mujaheed tace "Don Allah Mujaheed Imaan bata isa aure ba yarinyar da ke al'ada? Ga kirjinta cike da dukiyar fulani" Murmushi Mujaheed yyi kansa a kasa yana cin abincinsa, Imaan ta harari Inna ta juya ta nufi kofa inna tace "Ke kika sani, ni ba ruwana wllh, Allah na tuba lalurorin ki na duniya ma ai tsaye yake da kafafuwansa gun d'a na, ba gwara kiyi auren ko Bukar xai huta da kashe kashen kudi kije can kuma mijin shi ma ya d'an dana ukubar" Washegari alhamis Imaan ta tashi da ciwon ciki ga bak'i a part dinsu balle tayi raki yanda ranta ke so, duk magungunan da ta sha ba wanda taji ya mata, ta lallaba da kyar ta tafi bangaren inna, ita din ma dai parlon nata duk tsofaffin kawayenta ne a xaune, imaan ta gaishesu da kyar ta shige bedroom dinta ta kwanta, lkcn Azahar nayi dama inna ta lallabo ta shigo dakin ta sa ma bandakinta makulli don ba wanda xai shiga balle ya mata kazanta duk me son yin alwala ga pampo can ta bude, idan kuwa xai kama ruwa ne to yaje sashin masu biki, ganin juye juyen da Imaan take duk ta hada xufa duk da iskan fankan dake dakin ta wani xaro ido tace "Ke lafiya meye hakan, ni fa ba ruwana idan baki da lafiya ne ki tafi bangarenku kada a gigitani a nan, meye wani juye juye kamar macijiya a kan gado na" Imaan ta fashe mata da kuka tace "Wayyo cikina ke min ciwo" Inna tace "Auzubillahi, to rufa min asiri ki sakko ki tafi gun uwarki ba ruwana" Cikin kuka tace "Akwai mutane a can" a fusace Inna tace "Mutanen banxa ina ruwanki da su, idan wani abu ya sameki maganin me mutanen xa su yi banda su cika mu da surutu, dama ba komai ya kawo su ba sai kwadayin d'an shinkafar da xa a raba a kwano da kaji banda haka wani ma anyi shekara goma ba a gansa ba, ki tashi ki tafi tasan yanda xata yi dake idan ma asibiti ne ta kai ki, idan ko ba haka ba idan ban sa an dage bikin ba ace bani ba, biki ya fi rai ne" da kyar Imaan tace "Ni fa marana ke min ciwo" Inna tace "Wai jini?" Imaan ta gyada mata kai, Inna tace "Toh shi kuma wanda kika yi ko sati ba ayi ba fa?" Tace "Ba shi bane kawai alama ne" Inna ta xabga tagumi tace "Ke kam kina ganin jarabawa iri iri a rayuwa na lalura, banda haka jinin ma

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment