Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da hankalin cewa ka shigo ka gaisheni kai baxa ka yi tunani ka shigo ba, dubi fa yanda ta ji kunya ta kasa juyowa kamar warce ruwa ya cinye" Sadeeq dai sai murmushi yake yace "Dama ai xan shiga in gaida ki kaka, kiyi hakuri" inna tace "Ni dai ba ruwana a dinga abu saboda Allah, tunda dai na kama ka mu je ciki" Yana murmushi ya bi bayanta suka shiga compound din ta rufe gate, tana nuna masa bangaren su Mujaheed tace "Kaga wancan katon ginin?" Yace "Na gani kaka" tace "Toh na wan ubanta ne, barrister suke ce masa, a India yayi karatun lauyancin sa, matansa biyu sai 'ya ya bakwai, Mujaheed shine d'an sa na fari, ina tsaye bakin kofar asibiti aka haifesa, yana nan xaka gansa wani lafcece dogo, da yake ada yana daga wannan karafunan turawan, to da kyar dai Ahmadu ya raba sa da su, nima na dinga rokon Allah har ya daina, a gabana fa ya girma, tun yaye yake wajena iyayen suka bar min, yana gama sakandari dama babansa ya biya masa kudin karatun likita a turai, ai ko in gaya maka babu irin fitsarar da bai koyo a can ba gaskiya, ni dai lkcn da ya dawo ma tsoron sa nake ga wani uban gashi da ya tara, buduwar da xai aura ma yar hayi ce, to sai kaninsa Yusuf, xaka gansa shi kuma wani lagwai lagwai kamar ya karye malam, da ma muka samu ya d'an yi kauri yanxu, sai kaga yanda aka haifesa d'an fiyot, to sauran kuma duk mata ne" Murmushi kawai Sadeeq ke yi yana bin inna, inna ta nuna masa part din su Imaan tace "Toh kaga wannan bangaren na su Imaan ne, Ubanta a can Habuja wajen neman abincinsa yake, ita kadai Allah ya basa a duniya, to dai ya fi babu d'an agwai da bak'in da, uwarta na nan wata bafillatana sai kirki, toh ni kuma kaga akurkin da suka gina min nake rayuwa ciki" ta fadi haka tana nuna masa nata part din.




*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻‍♀️

It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group._23. Imaan














Am bringing this to the notice of my fans, idan xaku biya book din *Imaan* in dai ba digit din nan 👉🏻 07087865788 wato lambata kuka yi ma magana ba to Wllh ba ni kuka biya ma kudi ba, lambata guda daya ne kacal kuma gashi can a sama na rubuta, sannan ni bana amfani da wani kati idan ba Airtel ba, don haka duk wanda ya biya ta wani lamba daban wllh ya karanta hakkina without paying coz every page sai na sa number na da account number amma sai ku tsallake ku tafi kuna biya a gun wa enda ban sani ba ban san da su ba, ni kadai nake harkata a bangaren rubutu bni da wani xae ce ku tura masa xai turo min, talk to me directly through my WhatsApp digit 👉🏻 07087865788, su kuma masu siyar min da littafi har da hada document Billah na bar su da Allah, we shall surely meet in the hereafter in dai hakkina ne in sha Allah. Sannan masu *forwarding* ma su ci gaba there is power in the tongue_





Dariya Sadeeq yayi yace "Haba wannan ai ba laifi kaka" ta tabe baki tace "Mu je dai tukun" suna isa bakin kofa tace "To dai ka gani..." yana murmushi ya shafa kansa yace "Wannan ai ya fi duk sauran kyau kaka, ga shi ba hayaniya ba komai" Inna ta kara tabe baki ta bude kofar tace "Toh Allah ya masu albarka da suka gina min ai dai yafi babu" bin bayan ta yayi cikin parlon dake ta kamshin turaren wuta ta bude fridge ta dauko masa malt biyu da ruwan gora ta ajiye masa yace "Nagode sosai kaka" xaunawa tayi tana washe baki tace "Madallah, to ya sunan jik'an nawa?" Yyi kasa da kai yace "Sunana Abubukar Sadeeq" Inna ta gwalo ido ta saki wani kabbara da ya sa ya dago da sauri yana kallonta, tace "Yo ai sunan mahaifinta kenan Bukar, wllh shi ya haifeta, ai ko baka gansa ba mutumin kirki mai dattako da sanin ya kamata, sam yaron bai son 6acin raina, yo Ashe ma d'a na ne kai, to ka sha kurumin ka in dai wannan yarinya Imaan ce to wllh ka sameta ka gama ko taki ko ta so in dai ina numfashi kai ne mijin ba ruwana, don gaskiya ka kwanta min sosai, naga kana da hankali da nutsuwa" murmushi kawai Sadeeq yake, yace "Toh kaka idan ita bata ra'ayi fa?" Inna ta xaro ido tace "Wannan kuma ita ta jiyo ni dai ba ruwana, sunan ubanta fa gare ka kuma duk masu sunan an sansu da rikon aure, dubi fa yanda ubanta ya rike uwarta duk da rashin haifa masa yara da yawa da bata yi ba, to ni ko ina xan yarda ka kubce mata, A'a baxai sa6u ba wai bindiga a ruwa" Sadeeq yace "Toh nagode kaka naji dadi sosai" Tace "A'a ba xancen godiya, sunan d'a na fa gareka, ni dai ko yau kace xaka turo magabatanka kofa a wangale yake, to me xa mu ci da ita?? duk da dai ko sati ba ayi da aurar da yar uwarta ba amma idan ma iyayen nata sunce baxa su iya ba ni xan mata gado da kambodi da dirowa, Ina ce suna kenan kayan auren dai?" Sadeeq couldn't help it but laugh, tace "Kai ba xancen dariya bane, ni wlh sai in sa a siyar da filina guda daya in mata kayan daki, dama ni tsinannen bokon nan da ake yi yanxu ba d'ad'a ni da kasa yyi ba" Sadeeq ya sakko kasa yace "Da xa a ban ixinin turo magabatan nawa ba da jimawa ba da naji dadi sosai kaka" Inna tace "Wannan ai ba wata matsala bace bari Ahmadu ya dawo tunda kaga shi uban nata na Habuja" yace "Toh naji dadi sosai kaka" Inna tace "Kai don Allah... ai kuma an xama daya godiya ta me kuma, in ji iyayen ka a nan garin suke su ma?" Yyi kasa dai kai yace "Ehh suna nan" Inna tace "Toh dan siyasa ne uban naka?" Yana murmushi ya girgixa kai yace "Aa d'an kasuwa ne, Alhaji Ahmad Bulasawa ne Abba na" Inna ta xaro ido tace "Bulasawa?? Bulasawa dai da na sani na garin nan?" Bai dago ba still yace "Ehh shi" Inna ta bude baki tana kallonsa da kyau, can tace "Ikon Allah, ashe d'an babban mutum ne gabana ni Asabe, waye bai san Bulasawa ba duk garin nan da ma duk kasashen arewa, ba ance gidansa na nan nan GRA ba?" Yayi murmushi yace "Ehh" inna ta rike ha6a tana kallonsa tace "Ehh lallai ga kamanni kawai hanci ka fisa wllh, amma matansa aka ce biyu, to wacece uwarka a ciki, ko uwargidan? Don dai Bulasawa bai wuce Ahmadu na ba" Yace "Ehh ita" Inna tace "Atoh Alhmdllh, Allah na gode maka, kai abu sharr... bari Ahmadu ya dawo ko cikin watan nan ma ni gaskiya sai ka turo su Bulasawan, wa xai xauna" shi dai bai ce komai ba, Inna tace "Kai.... Allah mai iko, amma xan so kada wannan abun arxikin ya dau lkci gaskiya, ai aure abun arxiki ne" a hankali yace "Toh Allah ya sa haka kaka" tace "In sha Allah ya ma sa, ai abun arxikin xa a hada" Mikewa tayi tace "Bari in debo maka dambun namar da na ajiye ma Mujaheed" Da sauri yace "A'a xan koma ne kaka" Tace "Da wuri haka? Ni dai ka tsaya ko a leda ne sai in kulle maka" bata jira cewarsa ba ta shiga daki ba a dau lkci ba ta fito da gaba daya dambun naman a leda ta juye, ya xaro ido yace "Kaka wannan ai yayi yawa" tace "A'a ba ruwana ka amsa, dama Mujaheed da Imaan na ajiye ma to gaskiya ba rabonsu bane ynxu" dariya yyi ya karba yace "Toh ngd kaka, Allah ya kara girma" tace "Don ma dai duk sun cinye min cin cin din, kuma nasan ba kowa ya aikata min haka ba sai Maimoon da Ummi, ita Imaan bata daukan abu ba a bata ba sam ba halinta bane, gashi yarinyar bata da fitina tun tana jaririyarta, ga rashin yarda da kowa, lkcn ma ni har fargaba nake kada a kawota wajena don idan ta fara tsala ihu duk sai ta tara min munafukan anguwa an shigo min ana tambayar lafiya, me ya sameta?? dama Mujaheed kadai ne bata yi ma kiwa ba lkcn da take tashan kiwan, idan kuwa ta makalkalesa a lkcn bbu mai banbareta sai uwarta Aisha, ita ce ma ta makala masa yaya tun bata da wayo, in ko ba shi ya bata abinci ba dama abincin sai dai yyi ta galantoyi ba ci xata yi ba, in gaya maka lkcn Bukar na siyo mata wani runtumemen alawa idan ta saka a baki bata yrda ta ba kowa don rowa sai dai Mujaheed, shima din d'an dangwala masa xata yi a baki tana makale jikinsa, kai har goyata Mujaheed ya sha yi fa ta saki fitsari jikinsa sai dai ya canxa kaya, gaskiya ta takura ma Mujaheed ba kadan ba tana karama, shi sa in har yana gida uwar ta kawo ta bani da fargaba in kyalesu can su karata inyi ta kaina, to idan ban kyaleta ba ya xan mata tunda bata yarda da ni ta sa iyayenta su fara wani mugun tunani a kai na in shiga uku? A'a ba ruwana wllh" Murmushi kawai Sadeeq yake yana kallon inna, ta tabe baki tace "Toh gashi dai Imaan an girma kamar ba ayi ba, bari dai in bar ka haka naga kamar sauri kake, to sai yaushe kuma xaka sake shigowa??" yace "Ae ko da yaushe xan dinga shigowa gaida ki in sha Allah" Tace "Kai toh nagode yarona, Allah maka albarka, ya kare ka sharrin mahassada" ya mike ya ajiye mata dubu goma a gabanta yace "Ba yawa kaka a sa katin waya ayi xumunci" ta kauda kai da sauri tace "kai kai.... Ayi haka kuma Bukar??" Ya nufi kofa yana murmushi yace "Sai na kuma dawowa kaka" ta mike tana washe baki tace "Toh Allah maka albarka ka gaida min uwarka kaji?" Yace "In sha Allah xata ji" daga haka ya fita parlon just smiling, inna ta koma ta dau kudin tana kirgawa tana murmushi. Dama tunda inna ta shiga ciki da Sadeeq imaan ta wuce part din su ta fashe ma Ammi da kuka, Ammi ta mike tace "Lafiya?" Cikin kuka tace "Ko ba inna bace ta wani fito ta gan mu shine ta sa suka shiga ciki tare da shi, yanxu ban san dame dame xata fada masa ba, wayyo na shiga uku Ammi, nasan komai ma yau sai ta gaya masa" Ammi ta sake baki tana kallonta, ita kanta hango irin maganganun da inna xata juye ma Sadeeq yau ta dinga yi, can tace "Ae ko sai ki tashi ki tafi bangaren nata, idan ta ganki xata kama bakin ta" Imaan na girgixa kai tace "Ammi baxan iya ba, tun fa a gate ta fara basa labari" Ammi tayi jigum, can tace "Toh Allah ya kiyaye, ban san kuma me xan ce ba" daga haka ta bar parlon, Imaan ta dinga hawaye duk jikinta yyi sanyi babban damuwarta ma kada inna tace masa ai gashinta na nan bata son a gyara mata shi. Sadeeq na fita compound din yayi dialing number imaan yana murmushi, da sauri ta mike xaune tana kallon wayar, ta fashe da kuka a hankali ganin shi ne, da kyar ta daga kafin ya katse ta kai kunne, yace "Toh ai xaki fito mu yi sallama amma?" Tayi gathering courage tace "Me grandma dita ta gaya maka?" Yayi yar dariya yana wara ido yace "Ai babu abinda bata gaya min ba, she told me everything" Ta xaro ido kawai ta katse wayar ta fashe da kukan takaici, duk kiran da ya dinga yi kin dagawa tayi daga karshe ta shige daki ta kwanta kan gado bata fasa kuka ba. Bayan Isha jin ana knocking Ammi ta sa Hijab ta nufi kofar ta bude, Abba ta gani tsaye da Mujaheed ta ba su hanya tace "Ina yini Alhaji?" Ya shiga parlon Mujaheed na biye da shi ya xauna yace "Lafiya lau Aisha, ya mai jikin?" Xaunawa tayi ita ma tace "Da sauki Alhmdllh tana daki" Mujaheed bai yarda ya kalleta ba yace "Ina yini" tace "Lafiya" Abba yace "Ko bacci take?" Ammi ta mike tace "Anya kuwa...." Mujaheed dake tsaye dama bai xauna ba yace "Bari in dubata" Har xata dakatar da shi sai ta ji kunyar Abba, ta dai bi sa da hararan gefen ido don ko kadan bata so tafiyarsa dakin ba, murda kofar bedroom din yyi ya shiga ciki, tana xaune gaban mirror daga ita sai towel tana shafa lotion a duk jikinta, duk tunaninta Ammi ce ta bude kofar don bata ko kalli direction din kofar ba, jin shiru ta daga kai tana kallon kofar ta madubi, tsaye yake yana kallonta, suna hada ido yayi saurin dauke kansa, ta xaro ido tana gyara daurin towel din tace "Yayaaa" Mikewa tsaye tayi ta juyo tana kallonsa kafin tace komai calmly yace "Abba na jiran ki a parlor" bai jira cewarta ba ya fita dakin ta bi sa da kallo tana turo baki, Mujaheed na duban Abba yace "Tana xuwa abba" Abba yace "Ohk" Hijab ta sa har kasa ta fito parlon, ta gaida abba da murmushi fuskarta yace "Ya jikin mamana" tace "Abba ai na ji sauki" yace "Toh Alhmdllh, Allah kara lafiya" tace "Ameen" Abba yace "Ga watermelon nan you take much of it kin ji" a hankali tace "Toh nagode Abba, but...." Sai kuma tayi shiru, yace "But what?" Ta boye fuskarta tace "Abba ina son cin suya" Abba yace "Toh Mujaheed xai siyo maki yanxu" Mujaheed ya kalleta ta gefen ido irin kallon harara, Tana murmushi tace "Toh nagode Abba" daga haka Abba yyi ma Ammi sallama Mujaheed ma yyi mata suka fita. Abba yace "Idan mun fito part din inna sai ka tafi ka siyo mata, there is still time ai" Mujaheed yyi kasa da murya yace "Abba yanxu tare xa mu gun innan?" Yace "Of course, ban san urgent kiran da take min ba, it might even be something that isn't worth the call" Mujaheed yyi yar dariya yace "Dama xaka ga it's nothing that important...." Abba yyi murmushi yace "But we still have to listen, gudun matsala" Suna shiga parlon Inna ta shafe addu'ar da take kan darduma tace "Har ka iso kenan Bukar, to shi kuma wannan jelan da ya biyo ka fa?" Dariya Abba yyi ya xauna yace "Aa mun shiga duba mamana ne shine muka karaso nan din tare" tace "Atoh na gansa wani sandan sandan kamar basamude a bayanka" Mujaheed dai sae hararanta yake k'asa k'asa, tayi kasa da murya tace "Kana ji na Ahmadu?" Abba yace "Ina jin ki" tace "Kaga kujeran can da Mujaheed ya xauna?" Kai ya gyada mata yace "Na gani" tace "To wllh tllh a kai Bulasawa ya xauna" da mamaki Abba yace "Bulasawa kuma?" Tace "Eh, amma d'an sa ba shi din ba" Abba yace "Tohhhh.... a ina ya san ki?" Ta daga hannu da sauri tace "A'a ni bai san ni ba, a titi muka hadu yau kuma muka fahimci juna kwarai da gaske..." daga Abba har Mujaheed kallonta suka tsaya yi without blinking, can Mujaheed ya girgixa kai planning to get up and leave the parlor yaji tace "Ashe wai saurayin 'yar ka ce Imaan, amma algungumar bata ta6a sanar da ni ko da wasa ba, a wajen na gansu tsaye jikin santalelen motarsa, in gaya maka taji kunya tsamo tsamo da ta gan ni, ni dai ban kulata ba bakina a leko na taso keyarsa muka shigo cikin gida, d'an wajen Amadi Bulasawa mai gidajen man fetur sun fi dubu a arewa fa Ahmadu" dakatawa Mujaheed yyi da sauri ya juya yana kallonta, Abba na gyada kai yace "Tohh da kyau hakan" Inna tace "Kai fa kasan da kyau yaro, wato idan Allah yyi auren har kasan waje fa sai an fitar da ita an juye duk gurbatattun jinin jikinta dake ja mata lalura a sauya mata sabo, sannan kasussukan jikinta su ma duk sai an ce xa a sauya su ta rabu da ciwace ciwace na har abada, kasan fa bbu abinda turawan nan basa iyawa in dai da naira, to ga naira dai faca faca ta samu, ae ni bayan fitarsa sai da nayi ya ma ake kiran sujjadar nan na godiya ga Allah?? To ni dai nayi wllh kuma na dade goshina a kasa" Dariya kawai Abba yake yana kallon mahaifiyar tasa, Mujaheed dae sai juya counter din hannunsa yake, inna ta marairaice tace "Ahmadu ka rufa min asiri ba abun dariya bane wannan, sannan yaron fa duk ya damu wai xai turo magabatan sa nan ba da dadewa ba ayi xancen aure, kasan su kuma manyan mutane basa son kwalo kwalo kada a bari wannan yaron ya kubce ma jikata in shiga uku gaskiya" Juyawa Mujaheed yyi ya dinga kallonta, Abba yace "Haba maganar aure kuma Inna, ko secondary fa bata gama ba" Inna ta wani tsuke fuska cikin d'aga murya tace "Allah ya tsine ma sakandarin, sakandarin banxa ga abun arxiki kana xancen sakandari, ko a gidansa wllh xai bari ta karasa, baka gansa ba dogo yanda kaga wannan mutumin dake kusa da kai a xaune, shi ma da kyar idan baya daga karafunan nan na turawa don kirjinsa duk a tale, kana ganinsa kaga d'an boko don gilashi ne ma a idonsa, toh irin wannan ne baxai bari ta karasa sakandarin jaraban ba idan anyi aure, gaskiya Ahmadu ku maida hankalin ku sosai a kan maganar nan da nake gaya maka, wllh kullu yaumin fargabana mijin da Imaan xata aura tunda ga yanda Allah ya halitto ta, mai rufin asiri kadai baxai iya da lalurorinta ba sai hamshakin mai kudi, da yau ace Bukar ya tara yara kamar yanda ka tara to fa da imaan bata kai labari ba don nasan ba xai tara uban kudin da xai dinga kashewa kan ciwonta ba, to astagfirullah kaga amfanin haihuwan kadan ba da yawa ba, to yanxu dai ga yaro matashi kyakkyawa d'an masu kudi ya fito, bari ma kaga abinda ya ban Ahmadu"



*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻‍♀️

It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment grouAbba na kallon Daddy yace "Kada kayi ma Imaan magana tukun, I want to confirm who the guy is from Yusuf, Mujaheed yace baxai rasa sanin sa ba" Daddy yace "Toh shikenan, amma I will so deal with her, ita har nawa take xata fara kula samari can you imagine?" Abba yace "Nace kar kace mata komai tukun, ni nasan abinda xan yi" Daddy bai iya yace komai ba, don gaba daya ransa ya gama baci, suna isa part dinsa ya shiga, Abba kuma ya karasa nasa part din. Direct bedroom din Mujaheed Abba ya tafi ya bude kofar, Mujaheed na xaune tare da Umma a dakin ya sunkuyar da kai yana saurarenta, Umma na ganin Abba tayi shiru daga abinda take cewa, Abba yace "Ka sameni parlor Muhd" a hankali Mujaheed yace "Toh Abba" daga haka ya rufe kofar, Umma tace "Wai me ke faruwa, jiya naga mood dinsa gaba daya sai a hankali, halan tsohuwarsu ce ta tada wani fitinar?" Murmushi Mujaheed yyi yace "Ehh.." Umma ta buda ido sosai tace "Wai me take so?" Kamar Mujaheed baxai ce komai ba sai kuma yace "So take ayi ma Imaan aure" Umma ta xauna da kyau da mamaki tace "Aure kuma? imaan din saurayi gareta da xa a mata aure? Ko tana da yaron da xata hada ta da shi ne?" Mujaheed ya d'an yi shiru sannan yace "Ban sani ba Umma" Umma ta hade rai tace "Baka sani ba duk kusancin ka da inna, ko dai gaya min ne baxa ka yi ba??" Ya girgixa kai yace "Umma ni bata gaya min komai a kai ba" Tuni mood din Umma ya canxa, Mujaheed dai kallonta kawai yake, Tabe baki tayi tace "To ma gani ai, yanxu dai xaka yi transfer din ne ko Safeenar xaka ma?" A hankali yace "Anjima xan maki Umma" ta mike tace "Toh ina jira" daga haka ta nufi kofa ta fice dakin, Dafe kansa yyi na kusan minti daya, can dai ya tashi ya tafi parlon Abba. Abba na kallonsa yace "Mun gama magana da Yusuf yanxu a waya yace bai san yaron ba, so what I want you to do now is ka samo min number sa a wajen Imaan, but ita kanta bana son ta san ka dau number yaron, do it wisely" Shiru Mujaheed yyi, Abba yace "Yea just get his digit by any means without her knowledge" Yace "Toh Abba" Abba yace "I want it before the end of today" yace "I will do that in sha Allah" Abba yace "Xaka iya tafiya if u have anything doing" mikewa yyi ya fita, Umma ya gani sanye da Hijab ta rike purse ta nufi kofa, ko lura da shi bata yi ba har ta fita, ya bi ta da kallo sannan ya wuce sama . Imaan na xaune kitchen tana kallon Ammi dake kwashe girkin da tayi a warmer, Ammi tace "Kafin Magrib idan ban dawo ba sai ki kai mata" Imaan dai bata ce komai ba, bayan Ammi ta gama tana kallonta ta marairaice tace "Ammi amma me yasa baxan bi ki ba plss" Ammi tace "Nace ki bari lahadi idan kin dawo islamiyya kije, yanxu akwai mutane da yawa a gidan you will be uncomfortable" a hankali tace "Toh Ammi" Ammi ta fita kitchen din ta mike ta bi bayanta, Hijab Ammi ta sa ta shiga parlor gun daddy tace "Yallabai xan je xa mu amshi lefen Halima" Daddy yace "Ohk xan je cikin gari dama, let me drop you" Imaan ta turo baki ganin ita kadai xa a bari gida, kamar xata yi kuka tace "Daddy in raka ka?" Wani kallo da ya tsorata ta ya maka mata yace "You are stupid" sunkuyar da kanta tayi ta juya ta wuce daki, Ammi ta hade rai tace "Ni ban gane haushinta da kake ji ba tun daxu, ka kuma ki gaya min me ke faruwa" Yace "Madam dauko min makulli a daki and stop questioning me" daga haka ya fita parlon, tabe baki tayi ta tafi ta dauko masa makullin, dakin Imaan ta leka ta ganta xaune gefen gado tace "Ki tashi kiyi sllh sai ki sa kallo ko a daki ne kiyi" daga haka ta rufe mata dakin, kusan tare suka Isa parking space da Mujaheed, kansa a kasa ya gaida Daddy, daddy ya amsa yace "Ya aikin?" Yace "Alhmdllh, xa ku fita ne Abba" Daddy yace "Ehh xan je cikin gari ne" Ammi ta hade rai ta bude front seat ta shiga, Mujaheed dai bai yarda ya kalleta ba dama, daddy yace "Toh sai na dawo" Mujaheed yace "Toh a dawo lafiya Abba" daga haka ya bar wajen yana d'an murmushi, dama tun safe yake tunanin yanda xai hadu da Imaan har ya dau lambar Sadeeq, kan farin kujera ya tafi ya xauna har Daddy ya fita gidan, bayan kusan minti biyar ya mike ya nufi part din nasu, murda kofar yyi a hankali ya shiga ciki yana kallon parlon ya ga bata ciki, ya jawo kofar ya rufe ya nufi bedroom dinta, tsaye yyi bakin kofar kafin ya murda gently ya tura kofar, bai ganta dakin ba ya d'an yi jim, running tap ya ji a bathroom ya gyada kai, ya tafi gaban madubi ya dau

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment