Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ba" Inna tace "Auuu" kara bude ledan tayi ta fiddo tsoka daya ta manna masa kan plate din, Ta kalli Imaan tace "Naga kina son albasa da kabeji dauko kwanon can da kika ci abinci in kwashe maki in hada maki da tsoka daya" Imaan tace "Ni nace maki xan ci kaza?" Inna tace "Toh na sani? Gani nayi kin xabura kin tashi kamar Bukar ya siyo min" Daga haka ta kai cinya baki tana ci tace "Allah maka albarka Mujaheed duk cikin jikokina kafi jin k'aina wllh, shi sa ma kana aure zan tattara yanawa yanawa in koma gidan ka na rantse" ya xaro ido yace "Gidan wa?" Ta kallesa tana washe baki tace "Gidan ka" yace "A'a wllh ga yar gaban goshin ki nan kice kuma gidana" tace "Waye yar gaban goshi na?" Yace "Gata nan xaune" inna tace "Oh oh ni gidan ka xan xauna xai fi min kwanciyar hankali, idan matar ka xata rainani nasan xajka taka mata burki kai da baka son abinda xai ta6a ni, wannan salubabbiyar kuma ai yunwa ma kadai ya isa ya koro ni, ni fa ban jin imaan ta iya girki tunda take ko tafasasshen ruwan xafinta ban taba d'andanawa ba" dariya Mujaheed yyi, Imaan ta wani hade rai tana kallon inna, Mujaheed yace "Kinga idan tayi aure xaki d'an dana idan kin koma gidan ta da xama" Inna tace "Ni fa baxan xauna gidan imaan ba gidan ka xan xauna wllh" yace "Wllh baxa ki xaunar min gida ba sai dai nata" Inna tace "Toh me yayi xafi haka, wannan satin idan nayi gidan ka wani satin sai inyi a gidan ta duk da nasan a rame dai xan dawo daga gidan nata amma dole naka naka ne, idan na koma gidan ka sai in murmure" Mujaheed yyi dariya yace "Inaaa ba wannan xancen gidan mijinta ko gidan Yusuf xai fi maki kwanciyar hankali amma gida na kam sai dai ki hangesa daga nisa shi ma kuma a photo, Kinga duk sanda mijin nata ya gaji sai ya koro ki da ita" Inna tace "Wai tsaya Mujaheed da kake wannan xancen da kudin asibiti mijin xai ji ko da nawa dawainiyar ka fa san irin cimar da nake ci bana banxa bane, gwara dai a bar sa ya ji da jinyarta, ni kuma in xauna gidan ka ko Yusuf koh Maimoon, amma ina ni ina xaman gidan imaan ga yunwa dai kiri kiri tunda ba girki take ba sai a wani fake da ciwon numfashi kamar yanda uwarta ke cewa" fuu imaan ta mike xata fita cikin rashin sani plate din da ta ci abinci ta bari wajen ya xamar da ita sai ga ta rijib a kasa, wani ihu ta fasa da karfi tana cewa wayyo kafarta, Inna ta xaro ido ta mike da sauri ta bude kofa tace "Ni dai na shiga uku da jaraba, yi maxa fita da ita Mujaheed, fitar min da ita kar ma ace a parlo na ta fadi" Mikewa Mujaheed yayi yana mata wani kallo yace "Baxa ki tashi ba" cikin kuka tace "Wayyo yaya kafana ya rike baxan iya tashi ba" Inna ta gwalo ido tace "Ka ji ko? Mujaheed ka fitar min da ita kada a sani a bakin duniya" Ganin da gaske ta kasa tashi Mujaheed ya daga ta, ta zaro ido tana yarfe hannu tana cewa wayyo kafarta, inna duk ta rude tana ce ma Mujaheed ya fitar da ita, ko fita basu gama yi ba ta tura su gaba daya, ta kulle kofarta tasa makulli tace "Dama kada a kuskura ace a parlo na ta fadi wllh don ba ruwana" Mujaheed ya xabga ma imaan harara yace "Baxa ki tsaya da kyau ba" cikin kuka tace "Wllh ba karya nake ba yaya kafar ya rike min" kalle kallen wajen ya fara yi, can yayi tsaki ya dauketa kamar yar baby ya nufi bangarensu da ita, gam ta rikesa tana rera kuka.🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟🌟⭐ *Imaan*⭐🌟





_By khaleesat Haiydar_✍🏻





7.....

Ajiyeta yyi a balcony ta durkushe wajen yace "Baxa ki shiga ciki ba" cikin rawar murya tace "Baxan iya ba ka kira min Ammi" ya kalli kofar parlon sannan ya daga ta yyi knocking, daddy ne ya bude kofar, Mujaheed yyi kasa da kai, daddy yace "Subhanallah me ya faru?" Mujaheed yace "Faduwa tayi parlon inna" daddy bai ce komai ba ya basu hanya, Mujaheed na rike da ita suka shiga parlon, xata kwanta kan kujera Daddy yace "Take her to her room" Mujaheed ya wuce bedroom dinta daddy ya karasa ya bude masu kofar, kan gado ya kwantar da ita, Daddy na kallonta yace "Ina maganin shafan ki?" Kamar xata yi kuka tace "Yana kan dinning table" juyawa daddy yyi ya fita sai gashi ya dawo rike da methylated cream din dake cikin tube, Mujaheed ya amsa yace "Bari in shafa mata daddy" daga haka ya durkusa yana kallon kafar, daddy ya juya ya fita ya rufo masu kofar, cire Hijab din jikinta tayi ta daga rigar baccin jikinta xuwa gwiwa ta marairaice tace "Yaya ka min a hankali plss" ya mata wani kallo xae shafa mata bayan ya matso cream din ta rike hannunsa da sauri tace "Wayyo Ammina" buge hannun yyi ya mike ya turata ta fada kan gadon ya koma ya durkusa ya fara shafa mata cream din tun daga saman gwiwanta har xuwa fararen toes dinta, runtse ido tayi tana yarfe hannu, ya fi minti biyar yana shafa mata daga karshe taji ya daina, a hankali ta bude idonta, taga ya mike yana kokarin rufe tube din, da sauri ta tashi xaune ta bude zip din yar rigar jikinta tace "Yaya saura bayana" xata sauke rigar kamar warce ta tuna abu ta wani xaro ido ta mike tace "ina xuwa" bathroom ta shiga ta dau towel dinta ta sauke rigar jikinta ta cire sannan ta daura towel din ta fito, ta hau saman gado yace "Kee meye haka?" Ta xaro ido tace "Wayyo to ya xanyi ina son ka shafa min a bayana ne, ciwo yake min da daddare" tana fadin haka ta rungume pillow ta sauke towel din, ya second goma yana kallonta, girgixa kai yyi ya bude man ya matso ya hau saman gadon ya shiga shafa mata daga shoulder dinta har xuwa bayanta, ya kusa minti biyar yana hka, can ya leka fuskarta Bayan ya cire hannunsa ya ga idonta a rufe, har ya rufe tube din bata juyo ba bata bude ido ba, duka ya kai mata a kafarta ta mike xaune a firgice tace "Ammi ba bacci fa nake ba" dauke idonsa yyi, ta wani xaro ido tace "Yaya" ya mike ya ajiye tube din gaban mirror ya fita dakin ya kulle mata kofa, daddy na parlor har sannan, yyi masa sae da safe sannan ya fita parlon. Washegari da safe Imaan ta fito sanye da kayan islamiyya ta shiga kitchen sanin Ammi na can, gaida Ammi tayi, Ammi tace "Kin tashi lafiya?" Ta langwabar da kai tace "Bayan Ammi jiya baki shiga kin duba ni ba nasan kuma ba bacci kike ba, faduwa fa nayi a parlorn inna" Ammi tace "Ehh ban shiga ba, ina jin cikin mafarki kika dauko duvet a closet kika rufe jikin ki" Ta xaro ido tana kallon Ammi, sai kuma tayi dariya tace "Ashe ke kika lullube ni" Ammi tace "Ke da kika kwanta zindir" dariya kawai Imaan tayi, Ammi tace "Garin yaya kika fadi jiya" Imaan tace "Plate ne a hanya, shine Inna ta dinga korana wai kar ace a parlonta na fadi, yaya ne fa ya dawo da ni ko tashi bana iyawa, Allah inna ta iya mugunta" Ammi tace "Toh yyi kyau, amma kina kallon agogo dai ko?" Da sauri Imaan ta leka parlor don ganin agogo, cup ta dauka ta koma parlor ta wuce dinning don hada shayi, takwas saura minti biyar ta fita gidan bayan tayi ma Ammi sallama. Tun da ta dawo karfe sha biyu bayan tayi azahar take ta bacci har karfe uku da mintuna, Fitowa parlor tayi don xuba abinci ta ci, ganin jakar Daddy a parlorn ta kalli Ammi dake tattara masa takardunsa tace "Ammi daddy wucewa xai yi?" Ammi tace "Ko xa ki bi sa" shiru tayi lkci daya mood dinta ya canxa, ta dawo kusa da Ammi ta xauna cikin sanyin murya tace "Ammi me yasa mu ma baxa mu koma Abuja gun daddy ba, bana son yana tafiya ya na barin mu" Ammi tayi dariya tace "Toh ai sai ki gaya masa" dai dai nan Daddy ya fito yana waya, ta mike tana kallonsa kamar xata yi kuka, yana gama wayar ya kalleta yana murmushi yace "Ya aka yi mamana" hawaye ya cika idonta tace "Daddy mu ma mu koma Abuja mana, sai kayi ta zama kai kadai" yace "Wataran xa ku koma my dear, kinyi azahar ma kuwa?" a hankali tace "Nayi" yace "Good" tace "Daddy airport xaka je?" Yace "Ehh, flight xan bi" ta marairaice tace "Toh xan raka ka airport plss daddy" Ammi ta jefa mata wani kallo tace "islamiyyar fa?" Ta marairaice tana kallon Ammi, Daddy yace "Ba sai ta shirya ba mu fita gaba daya, idan ya so sai a ajiyeta a makarantar idan sun dawo airport" da sauri Imaan ta shige dakinta don fara shirin islamiyya , da kyar ta ci abinci bayan Ammi ta tilasta sanin bata wani ci abincin ba daxu da ta dawo, ganin daddy ya fita da jakarsa ta kai plate din kitchen da sauri ta fito ta xura hijab din islamiyyarta ta sa safa da takalmi ta dau jakarta xata fita Ammi tace "Ki tafi da jakar laptop din" dawowa tayi ta dau jakar ta fice da sauri ba tare da ta bi ta kan kudin da Ammi ke cewa taje daki ta dauka ba, Mujaheed ne tsaye kusa da motor daddy rike da makullin mota yana jiran dawowansa daga part din inna da yaje sallama, Maimoon ce ta kwalo ma Imaan kira tana tambayarta inda xata, Imaan tace "Ni motar daddy xan bi ku wuce kawai idan kun shirya kar ku jirani" Mujaheed ya hade rai yace "Ina zaki?" tace "Daddyna xan raka airport idan ya so idan muna dawowa sai a ajiye ni a islamiyyar" yana girgixa kai yace "kama gaban ki.... uban wa xai ajiye ki islamiyya ni na maki kama da driver din ki, daina kallona ki bar nan wajen my friend" Hawaye ya fara kawowa idonta ta tsaya tana kallonsa har sannan, strictly yace "Baxa ki daina kallona ki bace min a nan ba?" Juyawa tayi ta nufi sashinsu da sauri, lkci daya ta fashe da kuka, yana ganin haka ya xaro ido yace "Imaan" kin juyowa tayi, ya fara dube duben babban compound din kafin ya bi bayanta da sauri, har ta kusa shiga balcony dinsu ya fixgota ta juyo ta kara fashewa da kukan shagwaba, rikicewa yyi hango daddy da yyi yana tahowa daga part din inna, yace "Toh me nayi maki, kina son kiyi lattin islamiyya ne?" Cikin rawar murya tace "Toh bayan lkci bai yi ba" yana Satan kallon direction din da daddy ke tahowa yace "Toh naji goge idonki mu je" ta turo baki tace "Saboda kaga daddy na koh?"Wani kallo ya dinga mata kafin ya kama hannunta suka koma gun motar, bude back seat tayi ta ajiye laptop dake hannunta ta shiga tana kallonsa ganin irin kallon da yake mata tace "Yaya ka tuna watarana da za mu je gidan Mama fa'ixa abinda ya faru?" Bai tanka ta ba ya dauke kai, sai da daddy ya fara shiga yyi ma Ammi sallama sannan ya fito ya nufo parking space, yana kallon Mujaheed dake tsaye yace "Sorry for keeping you waiting son" murmushi kawai Mujaheed yyi, daddy ya bude back seat ganin Imaan ciki yace "Mamana why not seat at the front" tace "Noo, I am more comfortable here" yace "A'a dawo gaba" Mujaheed yace "Abba tace ta fi son nan ne" Daddy yyi murmushi ya shiga motar shi ma, Mujaheed ya shiga maxaunin driver, mai gadi ya bude masa gate ya ja motar. Sae da suka hau saman titi Daddy yace "Mujaheed pls ku dinga hakuri da grandma dinku, ita haka Allah yayi ta, mu wa enda ta haifa ma muka iya xama da ita balle ku grandchildren, ya kamata kafi kowa sanin halinta tunda ka xauna gunta, kasan abinda take so kasan abinda bata so, plss bana son in ji kun sake samun matsala kaji?" Yana murmushi yace "In sha Allah Abba" Daddy ya kalli Imaan da ta dauke kai yace "Ke kuma kar ki yarda ta kirani tace kin mata wani abu, wllh zan sa6a maki, tsakanin ki da ita respect babu wasan grandma and grandchild tunda bata so, I repeat respect her ynda xa ki respecting Ammin ki" Imaan tace "Ni dama na daina xuwa part dinta.... Kullum sai tace an mata rashin kunya" daddy yace "Don't try dat, you make sure kinje gaisheta everyday, kinsan Allah duk kika yrda ta kirani ta kawo karan ki xan bar duk abinda nake in dawo in ci kaniyar ki" kamar zata yi kuka tace "Toh yaya fa? Ae shima yana mata rashin kunya, Rahma da Ummi ma haka" Ta madubi Mujaheed ya mata wani kallo ta murguda masa baki, daddy yace "Ae duk na ja masu kunne kuma suna jin maganata ke ce dai mai kunnen k'ashi" Imaan ta bata fuska xata yi kuka, the remaining journey to d airport was silent, Imaan dai sai kumbure kumbure take. Suna isa airport din wajen karfe hudu da rabi, suka raka daddy har ciki, daddy na rike da jakarsa yace "Thanks much sai mun yi waya Muhd" Mujaheed ya dukar da kansa yace "Allah ya tsare Abba" Daddy yace "Ameen" yana kallon Imaan dake goge hawayen idonta, murmushi kawai yyi ya mata side hug yace "Sai mun yi waya anjima daughter, na maki transfer ta account din ki" daga haka ya sake ta ya juya ya wuce, Imaan ta fashe da kuka, Mujaheed dai na tsaye har sai da ya tabbatar baya ganin daddy sannan ya kalleta ya hade rai yace "Toh ki bi sa mana" ta gefen ido ta kallesa bata ce komai ba tana kuka, ya ja tsaki ya juya ya fara tafiya, sai da taga yyi nisa ta bi sa da sauri tana goge idonta...A haraban airport din ta tadda Mujaheed suna gaisawa da wata, Imaan ta ja gefe ta tsaya kamar ance ta waiga taga wani tsaye jikin ride dinsa ya rungume hannu yana kallon saitinta ta cikin black glasses dake idonsa, she couldn't tell ko ita yake kallo, ta dai dauke kai da sauri, bayan few seconds ta kara satan kallonsa taga saitin ta yake kallo still, tayi saurin dauke kai, again ta sake kallonsa, cire glass din idonsa yyi yana kallonta da kyau, a hanxarce ta kauda kai tana son tuna ina ta ta6a ganinsa, bata hakura ba ta kara satan kallonsa ganin bai daina kallonta ba ta juya tana kallonsa directly ita ma, murmushi yyi da har sai da dimples dinsa ya lotsa, ya xura hannunsa aljihunsa ya langwabar da kai yana kallonta dai, Mujaheed ya juya yana kallon Imaan bayan sun gama gaisawa da friend dinsa, ya ga sai kallon mutumi kamar ta samu television take, takawa yyi har kusa da ita yace "Do you have any business with him?" Ta turo baki tace "Toh shi ma ai kallona yake" Mujaheed yace "Wuce mu je kar in kwada maki mari" ta gefen ido ta hararesa ta nufi gun motarsa ya bi bayanta, bude front seat tayi ta juya tana kallon mutumin da bai fasa kallonta ba, Mujaheed yace "Wai kina hauka ne" ta turo baki ta shiga cikin motar, tada motar yayi bayan ya shiga suka bar haraban airport din, sun yi nisa sosai kamar ance ta dago kanta ta ga wani waje da ake gashin kaji, ta kallesa da sauri tace "Yaya" kallonta yayi, ta marairaice masa tace "Don Allah ka siya min kaza plss" yace "In siya maki kaza?" Shiru tayi tana kallonsa, yace "To kudi kika bani?" Ta turo baki, bai sake ce mata komai ba, ganin xa su wuce gun masu kajin tace "Wayyoo yaya plss" kara gudun motar yyi ya wuce wajen, kallonsa ta dinga yi kafin ta dauke kanta, ganin hanyar da ya dauka tace "To islamiyyar fa?" Yace "Sai dai in ajiye ki ki ta fi da kafa daga nan, ni ba drivern ki bane" yana shiga anguwarsu yyi parking gidaje uku kafin nasu ba tare da ya kalleta ba yace "Sauka" bude motar tayi ta fice fuuu ta nufi gate dinsu sai da ya ga ta shiga sannan ya karasa da mota gate din mai gadi ya bude ya shigar da motar. Ko kallonsa Imaan da har ta kusa part dinsu bata yi ba har ta shiga parlornsu, Kallonta Ammi ta dinga yi bayan ta shigo parlon tace "Dawowa kika yi baki tafi islamiyyar ba Imaan?" A hankali tace "Yaya ne yaki kai ni" Ammi tace "Ba har dadin fashi kike ba, ki ci gaba" Shiru Imaan tayi bata ce komai ba, Ammi ta wuce daki ta bar ta parlon. Bayan magrib Imaan na kwance parlor tana kallo, Ammi ta kirata daga kitchen, ajiye remote din hannunta tayi ta mike ta wuce kitchen din, Ammi ta nuna mata abincin Inna tace "Ki kai ma inna" Imaan tace "Ammi da xa mu kai Daddy airport fa sai da ya sake min warning a kan xuwa wajen inna" Ammi tace "So?" Ta marairaice tace "Toh ni kar inje in sake mata wani abu ta kira daddy" Ammi tace "Ni xan dinga kai mata abincin kenan" Kamar xata yi kuka tace "Ni wlh Ammi nace fa baxan sake xuwa part dinta ba har abada" Ammi tace "Toh kar ki je ki bar abincin a wajen" Imaan ta dau abincin rai ba dadi ta fita, Yusuf da Ummi na xaune parlorn Imaan ta shiga ta ajiye abincin, tana kallon Yusuf tace "Ina yini ya Yusuf?" Yace "Lafiya lau Imaan yau ba ciwon kafa kenan" Inna ta kallesa da sauri tace "Kaji wata mugun alkaba'i, kai fata kake kafar su yi ta ciwo kenan? Shi kenan ita kuma sae ta k'are a ciwo kamar warce ta kashe d'an mutum, ku dai 'ya yan Ahmadu baku da kirki, ku dinga sa ma bakin ku linzami don Allah" Yusuf yyi dariya yace "Daga tambaya kuma Hajiya inna?" Inna ta sharesa ta jawo wani leda tana kallon Imaan tace "Gashi nan Mujaheed ya kawo maki daxu, sai ki xauna a nan ki bude ki tsamma kowa don kema haka kike da sa ido, ni wllh ban ma ji dadin zuwanki ba tunanina baxa ki xo ba in cinye inyi nak" Imaan ta bude ledan da sauri, kaza ce babba guda daya sai kamshi da turiri yake, Imaan ta saci kallon kofa sannan ta saci kallon Inna dake goge plate din da xa a dibar mata ta fice parlon a dari da sittin, sake baki inna tayi da plate din hannunta, Yusuf ya kyalkyale da dariya, inna tace "Kaji daya daga dalilin da xa ku ji ance ta tashi kafa ya rike gobe saboda mugun halinta, toh meye kuma nama ni fatima? Halin fulanawan kenan fa rowa da mugunta, shi naman da xata d'an yaga ma kowa shine xata kwasa a guje kamar k'arya?" Dariya kawai Yusuf yake, inna da har hawaye ya kawo idonta tace "Don ubanta ta yi kiba kafin gobe idan ta cinye kaza daya, kuma Allah ya isa rai da aka sa min" Yusuf ya mike ya fice parlon yana ta dariya, mikewa inna tayi tana share idonta ta nufi dakinta tana cewa "Me aka yi aka yi nama kuma don Allah, wani irin nama kuma?? wani irin nama ne ban ci ba a rayuwar nan, kuma shima Mujaheed din da gangan ne, ai yasan shegen rowa gareta da na tambayesa na wa sai ce min yayi xata dibar min, babu yanda ban yi kokarin fahimtar da shi kan cewar da kamar wuya fa shegiyar ta dibar min, to ga karshenta nan ta gudu, a dinga abu ba tsoron Allah" Ummi tace "Toh shi me ye ma na siya mata kaza bayan ko gaishe shi bata yi wlh a gidan nan" Inna tace "Ohon masu, kya bar ni budurwa, ni dai Allah ya isa" Ranan litinin sabon driver da Abba ya daukar masu ne ya kai su schl....

_By khaleesat Haiydar_✍🏻

8.....

Yau Thursday Imaan na dawowa schl bayan tayi wanka ta ci abinci ta fito parlor ta xauna kusa da Ammi dake xaune, ta langwabar da kai tace "Ammi ina son xan je supermarket in siya pad da turarurruka" Ammi ta kalleta tace "Duk uban turarrukan da kika kwaso ranan sun kare kenan Imaan?" Yar dariya tayi tace "A'a ba su kare ba amma sun kai rabi" Ammi tace "Toh sai ki kira babanki bani da kudin da xan baki ki karo turare" Imaan ta bude ido tace "Ya min transfer din 30k ranan da xai tafi ai" Ammi tace "Tohhhh har 30k, lallai kam Allah ya taimaka" dariya Imaan tayi ta mike ta koma daki, Hijab dinta gogagge har kasa ta fiddo ta saka sannan ta dau karamar jakarta ta sa atm card ta feshe jikinta da turare ta fito parlor, ta durkusa kusa da Ammi tace "Toh Ammi ba ni kudin transport don Allah" Ammi tace "Ki duba gaban mirror a daki" tashi tayi ta shiga ta dauko sannan ta dawo parlon, tace "Yauwa Ammi ina son xan biya ta gidansu Mariya, tun Tuesday bata xo schl ba bata da lafiya" Ammi tace "Waye kuma Mariya?" Imaan tace "Lahh wannan da ke xuwa dubani wani lkcn idan bani da lafiya" Ammi tace "Kice min dai gidansu xa ki je ba supermarket ba" Imaan tace "A'a fa Ammi, kawai tunawa nayi, Ban ma san ko xan gane gidan ba fa tunda sau daya muka taba xuwa da Maimoon, idan ban gane ba kawai sai in dawo gida" Ammi tace "Gwara dai ki gane don ki dubota tunda tana yawan xuwa duba ki" Imaan tace "Toh Ammi" daga haka tayi ma Ammi sallama ta fita Ammi na tunatar da ita tayi addu'an fita gida, tana isowa part din su Yusuf taga Umma da wata kawarta xaune a waje kan fararen kujeru, Imaan ta dauke kai duk da sun hada ido har ta wuce su ta nufi gate, Hajiya Salaha tana kallon Umma tace "Wace fitsararriya ce wannan kuma" Wani murmushi Umma tayi tace "Yar wajen Aisha" Hajiya salaha tace "Ikon Allah ita ce ta girma haka?" Tabe baki Umma tayi, Hajiya Salaha tace "Ita Aishar ta sa kar ta gaishe ki gidan nan kenan?" Umma tayi yar dariya tace "Ga dahir kin gani, ai fa ko idona xai makale cikin nata shegiyar baxata gaida ni ba uwar ta hanata" Hajiya Salaha tace "Tabdi ita wannan yar ficicciyar yar?" Umma tace "Ba shine bayan na dawo gidan nan naga ita da Mujaheed da bai san ciwon kansa ba bai san ciwon mahaifiyarsa ba tamkar su yi 6ude, ya maida Aisha kanwar uwarsa bashi da tamkar ta gidan, ita kuma yar mai ciwo yau mai ciwo gobe tunda sickler ce idan kin ga abinda yake mata ko kanninsa su Ummi bai masu, in takaice maki duk dai Aisha ta bi ta shanye min shi yanda ta shanye kanin ubansa, yanda kika san xai mata sujjada" Hajiya Salaha tace "Ikon Allah" Umma tace "Ae tuni na tashi tsaye, nice can nice nan, da taimkon Allah da taimakon Magajiya na kwato d'a na da karfi da yaji, yanxu ko ga maciji basa yi a gidan bangaren ma ya daina xuwa, I can't risk that, uban waye bai san tsafi Aisha take ba, gashi dai ta hana kanin babansa karo matar da xata haifo masa 'ya yansa duniya ta rufe masa baki ta hada sa da 'ya sickler kullum ana hanyar asibiti ana kashe Dan banxan kudade, Allah kenan, kuma in dai ina numfashi a haka yarinyar nan xata kare yau lafiya gobe babu, in Allah ya yarda sai yar nan sai ta xame masu
DOWNLOAD
DOWNLOAD

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

1 year ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

4 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment