Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

itama kukan take saboda jikinta na bata diyarta na cikin damuwa ,ta mike daga zaune da take ta shiga zagaye d'akinta zuwa babban parlou'n gidan  ta wuce matar danuwan mijinta  da suka kawo musu ziyara tare da yarinyar su zuwa   haraban gidan tana baza idanunta gani take kamar zata ga diyarta daga sama matar danuwan Alh Abubakar da suke uwa daya uba daya ta biyo bayanta ta rungumeta ajikinta  "kiyi hakuri inshallahu za'a ganta "jikina na bani tanweer tana cikin damuwa Allah kasa basu ma yarinyata wani abu me suke bukata daga garemu su kira mu su tambayi duk abinda suke so wallahi a shirye nake zan mallaka musu duk abinda nake dashi muddin zasu dawo min da farincikina ..."

Tunda Hajiya zainab ta fito  hankalin minister ya rabu gida biyu  wani bangaren ya koma gurinta yayinda wani bangaren ke gurin d'an'uwansa  da suke tare "Haba Abubakar taya irin wannan babban abun zaifaru ace bazaku sanar damu ba 'yan uwa? Wannan wace irin rayuwace ta rashin zumunci kuka zab'a kai da zainab ?". Matashin Dattijon yayi maganar cike da b'acin rai yana binsu da kallo,
kallo d'aya zaka ma dattijon matashin kaga kamanni sosai da suke da Alh.Abubakar sai dai Ko a fuska zaka fahimci ya girmemishi.
"Kayi hakuri yaya Walh tallahi kaga dagani har zainab bama cikin hayyacinmu tunda wannan  tashi hankalin ya faru, gaba d'aya Zainab bataci baresha ni kaina Walh bazan iya cema when last nasa abu a cikin nan nawa ba" Alh.Abubakar yayi maganar cike da damuwa wacce kallo d'aya zaka fahimci damuwa a kan fuskarshi me tsanani dan duk yayi baki ya rame kamar ba Minister of Health ba.
"Allah sarki Ubangiji Allah ya fito mana da ita lafiya dan walh tashin hankali ya zama dole. To wai basu Kuma kiranku Ko suna buk'atar k'arin kud'iba?". Yayi maganar cike da tausayin d'an uwansa.
Girgiza mishi kai Alh.Abubakar yayi. "Kod'aya walh! Ni da zasu kira Ko duka dukiyata ce saina had'a daita su dawo da munda Tanweer". Ya k'arasa maganar cikin rawar murya wacce ke k'ara fitar da damuwar shi. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un". Alh.Usman yayi maganar cike da tausayawa nan ya shiga lallashin Kanin nasa tilo musamman ya jima bai ganshi ba kasancewar shi a Arewa yake da zama kaduna State da iyalansa hakan yasa bai sama labari ba sai da aka kwana biyu, yaji ciwo amma yanzu jin zantukan d'an uwansa yasa yaji jikinsa ya mai sanyi gaba d'aya a tare suka koma cikin parlou'n inda diyar Alh Usman rukkaya ke kwance akan kujera mai zaman mutun uku .

Numfashi  jaguwa ya furzar ya mike tsaye zai bar daki  "ka maidani gidanmu plz yaji sautin muryarta cikin sanyi  ya doki dodon kunnenshi  "nasan ka taimaka min ,ka karasa taimakon  ta hanyar maidani ga iyayena "idan kina bukatar zuwa gida ki ci abinci kina gama ci ko second biyu ba zaki kara a cikin gidan nan  ba zan maidake gaban iyayenki "yana gama fadar haka yaga ta matso da kujera da take zaune  ta bude kwanon abinci daya fara yin sanyi ta soma tsukura  ...." wayarsa ce ta dauki qara sauti ya ciro wayar daga cikin aljihunsa yana duba screen din wayar sunan Alh Tahir ya gani yana yawo ya  lumshe idanunshi sannan ya dauka batare da yayi magana ba "cike da in inna alh Tahir ya soma magana "har yanzu baka dawo da yarinyar nan ba gashi akwai next taget dina akanta ya kamata zuwa yanzu kasan yadda zakayi ka dawo daita plz "doka ce ko iko kake son min ? ya furta  masa haka a natse wanda zaka ɗauka maganar ba daga bakinsa ya fito ba sai agurin alhaji Tahir kamar saukar aradu yaji maganar .

saurin girgiza kai Alh Tahir yayi kamar yana gabansa "no babu ko daya naga dai ya kamata ne a dawo daita haka nan "to baza'a dawo daita ba kayi duk  abinda zakayi ya ja tsaki yayi disconneting din kiran ya maida wayar cikin aljihunsa tare da zura hannunwansa ciki ya juya "ki tabbatar da kin ciye abinci nan  tass kin shanye  driks da ruwa ke everything dake gurin make sure kin gama dashi idan kina son barin gidan nan  ", Allah bazan iya cinyewa ba yanzu ma da kyar nake tura wa ",Karki yi kiga abinda zai faru "ya karasa maganar yana barin dakin kai tsaye bangaren daya tanada domin shakatawa ya nufa a can ya iske abokansa da yaransa suna shaye shaye , masu shan wiwi nayi masu shan win nayi, duk sun cika gurin da hayaniya da hayaki suna  ganinsa suka hau sara masa suna masa  kirari gutun wiwin dake rike a hannun jubi ya amsa ya ɗan zuka yana fitar da hayaki ta hancinsa da bakinsa sannan ya  fita ta kofar baya yana tunanin mugun hali irin na Alh Tahir ko me zai yiwa ƙaramar yarinya kamar wannan gashi kuma shi din aminin mahaifinta ne?
Kusan minti goma yana tunanin agurin "

*****

"Wai Ibrahim kana so ka kashe kanka ne akan mace". Momynsa tayi maganar cike b'acin rai wanda ke had'e da tsantsar damuwar halin da d'anta ke ciki. "Momy I can't live without Tan, ta riga ta zama rayuwa ta, inda abunda nakeso bai wuce Tanweer ba Mo...". "Dakata!". Ta katse shi ta hanyar daga masa hannu da tare da mai tsawa. "Ibrahim bazan taba son ka rasa ranka akanta  ba duk da nima ina matukar kaunarta saboda irin son da kake mata ,but at least ka duba lamarina  kai kad'ane d'ana taya zanso akan wata 'ya mace wani abu ya sameka ?".
Tayi maganar tana kallon Ibrahim wanda tunda ta soma maganar idanunsa ke runtse.
"Ibrahim!". Ta kira sunansa cikin wani irin yanayi wanda bai taba saninta dashi a rayuwarsa ba" gaba daya Inaso kayi hakuri da Tanweer!". Ta karashe maganar cikin dakiya tana kallonsa ganin yadda har ya samu courage d'in tashi zaune shida tun b'atan Tanweer bata ganshi a zaune ba.

"Mom!". Ya fada cikin daga murya tare da gyara zamansa yana binta da wani irin  kallo idanunsa ko kiftawa ba yayi, already ya gama zazzarosu waje gaba daya what !". Yayi maganar  yana kallonta kamar bai fahimci abunda yake faruwa ba musamman furucinta. "Mom!". Ya Kuma fad'a yana kallonta cike da mamakin furucinta."Haba Momy, taya zakiyi wannan furucin na rabu  da Tanweer bacin kinfi kowa sanin irin son da nake mata? How could you utter such words uhm?!". Ya jero mata tambayoyin cike da damuwa lumshe idanu tayi tare da fadad'a murmushinta tana shafa sumar kanshi.

"Ibrahim kenan,". Ta fada tana kad'a kanta ,sannan ta  tashi ta soma taku yana binta da koda'dd'un idanunsa da suka sha wahala saboda rashin ganin abincin su  Tan, har ta Kai k'ofa sai Kuma ta juyo tayi murmushi me sauti tana kallonsa  lokaci guda Kuma fara'a dake tattare da fuskarta ya d'auke nan take bacin rai ya maye gurbinshi."Hmm! Yaro yarone nan gaba zaka gane da kanka nasan dalilin da yasa nace ka hakura da yarinyar nan ". Tana fad'in haka ta fice ta barshi zaune zuciyarsa cike da tunanin zantukan ta musamman bacin rai daya hango cikin idannun Momyn nasa wanda kusan ya jima baiga hakan tattare da fuskarta ba. Wayarsa da ta soma ruri ne ya katse mishi tunanin daya shiga ya soma zurfi, hannunsa na rawa ya kai hannunsa ganin me kiran, da sauri ya manna wayar a kunnensa banajin me ake fada masa a can d'aya bangaren naga ya tashi da sauri. "What?!". Ya furta da d'an k'arfi tare da runtse jajayen idanunsa  ya bude su tuni suka k'ara rinewa tare da k'ara tiruwa zuwa ja sosai kamar jan gauta. "Alright I am coming". Ya fad'a da sauri tare da wullar da wayar kan bed d'insa.
Yunku'rin k'arasawa wardrobe yayi amma me wani irin jirine ya kwasheshi da sauri yasa hannayensa akansa saboda wani irin nauyi da rada'dd'i da suke masa, yana ciza pink lips d'insa kanana wanda suka sauya colour saboda azabar ciwo a d'an bushe   "Ya Salam I.B!". Dadynsa ya furta wanda ya bud'e ko'farsa kenan a daidai lokacin da I.B ke ko'k'arin k'arasawa k'as, cike da matsanancin tashin hankali Alh.Tahir ya k'arasa ya tallafoshi zuwa jikinsa inda yak'arasa sauke su kan bed d'in. "Ta...Ta...Tan! Da....". Karasa kulle idanunsa yayi hankalin Alh.Tahir ya tashi a wannan lokacin banda ihun kiran sunan matarsa cikin tashin hankali babu abinda yake  dan ya fara tsorata da yanayin dan nasa .."

Darling's

💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

 WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686
alert  domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu  a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️12

......Cike  da   dakiyar    zuciya   alqali   ya   cigaba  da   bin  bayan motar   jaguwa    land  cruiser   prador   yana sake   neman   layin  IB  domin  bashi  direction  din  Inda  yake a daidai wannan   lokacin   sai  dai  Kiran  na   shiga   ba'a  d'auka   ,ya   kira  ya  kai sau   goma    bai    d'auka   ba  wanda a  wannan    lokacin   nazifi  da  alhj  Tahir  da    hjy    baseera    ne  tsaye a kanshi     nazifi   na  qakokarin   bashi  taimakon   gaugauwa ,   haushi  ya  kama   alqali   ya   ciza   gefen  lips dinsa   yana    dukan    sitiyarin  motarsa  "oh  my goodness   ko   me  yasa  yaki  d'aukar  Kiran yanzu bayan  bamu  gama  wayar  ba ya  ajiye   ? yayiwa   kanshi   tambaya  yana  d'an  rage  gudun  motarsa   dan  kar  jaguwa  ya  fahimci su yake  bi  ."

yayinda   a hankali  motar  jaguwa  ke  sharara  gudu  akan  titin  onipan a natse    ya  d'an  juyo  gefen  da  tanweer   ke   zaune   shiru   sanye  da   doguwar   riga   pinky  colour  ta  yane kanta   da  mayafi   baki   haka ka'fafunta   sanye  suke cikin   baby  shoe  baki  masu  matukar   kyau  tsintsiyar  hannunta  d'aure da agogo fata   baki   duk  jaguwa ne  ya  bata  su a  wannin da  suka  gaba tare da yi mata  albishir  din  maidata  gidan iyayenta   ,  kayan  sun   amshi   jikinta  sosai    kamar  dan ita aka  yisu .
a hankali itama  ta  juyo  cike da  natsuwa  fuskarta  d'auke da  murmushin  jin dadi zata  gida  taga iyayenta  cikin  sa'a shima ya Kalli Inda  take  idanunsu ya tsarke   cikin  juna  wani  irin  bugawa  qirjinsu yayi , alokaci  d'aya  sukai  shiru tare  da  tsurawa  juna idanu   gbdy  suka  kasa  d'auke   idanunsu .
a cikin  zuciyarsa yake  yabawa kyawunta   "hakika   tsarki  ya tabbata  ga ubangiji  daya halicci   wannan  yarinyar ,  kallo   d'aya  zaka mata kasan  kyakkyawa ce ajin  farko  ."

a natse   ya d'auke kyawawan  idanunshi  acikin  nata sakamakon ganin  yadda ta kafe shi da nata  idanunta da suka  wadatu da zararan gashi  Ido  gashi  ko kifta su  bata yi  shi  kuma mutun  ne  da  bai fiyye son  kallo  ba  bare kallo irin  nata  dake saukar  masa  da kasala tare da  sha'awa  me  tsayawa arai  , dan  nan take   kallonta  kesa   yanayin  mutun   ya   sauya  batare daya  shiryawa hakan ba." kasa  d'auke idanunta tayi   daga  kallonsa saboda  baiwar  kyau da  Allah   yayi   masa ta sha jin mutane na yabawa kyawunta haka zalika  idan ta Kalli kanta a  mirrow tana  tabbatar da abinda mutane ke  yawon  fad'a  akan  tsarin jiki da  kyawunta  sai dai  ko kusa bata kai shi komai  ba ,  dan  idan  tana  gabansa  raina  komai  nata take domin gani take  ya  fita  komai  bama za'a a had'a  ba .

muryarsa  a  kasalance ta  fito kmr baya  son  yin  magana  "ki  daina yiwa  namiji  irin wannan kallon  domin  duk  macen dake  kallon  nmj  haka   yana  nuna alamun bata da  cikakken   tarbiya  ,mace  da  kunya da kauda Kai   aka  santa  " ya  qarasa maganar   yana   jan  dogon  tsaki  dake   'batawa   duk   wanda  akayi dominsa  rai , runtse  idanunta tayi gam  tana  zance zuci  "nice  mara tarbiya  sannan mara kunya ?"tayiwa kanta  tambayar  ranta na quna da tuttukin   bakincikin  daya  maye gurbin  farincikin  dake  kwance a fuskarta ,  idan  akwai abinda ta tsana a rayuwarta  bai  wuce wulakanci irin wannan  ba  , kusan    second  biyu  tayi  idanunta na runtse  kamar  bataji abinda  yace   ba  , cikin  natsuwa taje  d'aura   laulausan  tafin hannunta saman   kushin  din  kujera  domin gyara   zamanta  taji  ya sauka  akan  laulausan  hannunshi   nan  take  yaji  qirjinsa  ya  cigaba da  bugawar da yake , itama  qirjinta ya  shiga dukan uku  uku  dan  wani irin zirrrrrrrrr taji lokacin da hannunta ya sauka a nasa  .

ya  sauke  wani zazzafan   ajiyar  zuciya da  numfashi alokaci d'aya ,
a hankali tayi karfin halin d'auke hannunta  dake saman nashi  a dalilin  jikinta  dake  kyarma  ta soma magana  cikin  fushi da bacin rai   "karka  sake  furta  min  wannan kalmar  domin  kuwa kallon  nmj    bashi  ke  nuna  rashin tarbiya ko  rashin  kunya   ba dan haka bana son sake jin   kalmar  gareni  domin ni din macece  me tarbiya da kima  idan Kai baka  ganin kimata akwai dayawa masu gani  ta  k'arasa  maganar hawaye  na  gangarowa akan quncinta ,ta sake kawar da idanunta sosai  tana goge hawayenta dake tsiyaya  "wani kallon banza ya watsa  mata mai  hade da harara  " lallai yarinyar  nan  ma  ta sameshi  yadda ya  kamata  ,shi take maidawa  magana ?ai duk  laifinka  ne da baka gyara mata zama ba  ka  tsaya  kana  tattalinta,  yarinyar da yaka mata ka  wulakantata   ta hanyar keta  mata  haddi  tunda abinda yasa ka d'aukota kenan "  zuciyarsa ta fad'a masa
haka  numfashi  ya  fesar yana jin  zafin  acikin zuciyarsa , sam bai ji  d'acin  Kalmar  daya   fad'a mata  ba, dan  haka  yayi tunani sake musguna  mata   jikinsa a sanyaye ya Kai  bakinsa   daidai saitin  kunnenta yana sake watsa mata kallon  bazan    tayi  saurin   gocewa   tana  furzar   da  numfashi  tare da  hura  hanci  sannan taki waigowa  ta Kalli Inda yake bare taga kallon banzar da yake mata zafin da zuciyar ke yi yasa wasu hawaye masu zafi da ciwon  sake zubo mata ita daya kamata ya farantawa adalilin zata tafi ta  barshi  tafiyar da ba lallai su Kara haduwa ba kamar yadda  ya  sha fad'a mata  ."

ya matso  kusa  daita Sosai yana busa mata iskar  bakinsa , bakinciki da takaici yasa   tayi  saurin  janye jikinta  daga nashi  tana  kallon  gefen  titi ,shiru  yayi  yana kallon  gefen  fuskarta  numfashi   ma  da kyar take   fesarwa  bai san yadda akayi ba  ya sake matsowa  sosai  ya d'aura kanshi a saman  kafad'arta  ,shiru  tayi taki   motsi   sannan taki waigowa, jin  shiru  taki  motsawa  ya tabbatar masa da lallai  fushi  tayi dashi  tsintar Kansa  yayi da rashin  jin   dadin yanayinta can Kuma ya furzar da iska had'e da jan dogon tsaki    "me  yasa   zan ji babu dadi  araina  dan  tayi fushi dani  ?ya  jefawa kwakwaluwarsa  tambayar  " Kiran  daya  shigo  wayarsa ya  katse masa zance zucin da yake bare ya samu amsa daga  wankakkiyar zuciyarsa , ya lalu'bo wayarsa daga cikin aljihun  wandonsa   ya mannata a kunnensa  batare  daya duba me Kiran ba.
jin sautin muryar  amminsa ce yasa shi  barin   jikinta  da hanzarinsa dan yana expecting  jin dadd'adan labari  daga  bakinta dan  jiya   da  sukayi  waya yake  sheida  mata ya kamata ace  yaron dake son  shefiqa  ya  turo iyayensa  ayi maganar aure  ,a lokacin ammi  ta  tabbatar  masa da zatayiwa shafiqa  din  magana   ,  ai kuwa abinda  yake expecting ji  shi  ta fara fad'a  masa  yasa wayar a hands free ya d'aura wayar a  kafad'arsa  ya  jingina jikinsa sosai a kujera."

  "yaron   nan gali  wai  zai  turo  iyayensa  ranar   lahadi  tare da saka rana   gbdy "  murmushi   jaguwa  ya saki  na  farinciki   yana cewa  " Allah ya  nuna mana  ranar  lafiya so nake na  aurar dasu gbdy kafin nawa auren . "a'a ban yarda da wannan  tsarin  ba ,idan ma  son samu ne a had'a  auren  da naka ba qaramin  farinciki zanyi ba "shinkenan ammina yadda  kikace  haka za'a yi  bani da za'bin da ya wuce naki  zanyi   k'okari naga anyi auren da nawa sai dai  ki qara  addua akan wanda kike  min     Allah  yasa  na samu me sona tsakani da  Allah  "zaka  samu da iKon allah dan  baka  da  makusar da wata diya mace   zata  kika  ni dai  fatana kayi kokari  ka  cika min alkawarina  Ina  son kyakkyawar  suruka me nagarta   idan   son samu ne   wacce  ta  fika kyau". wani  narkakken  murmushi    ya   saki  kamar  yana gabanta  kana yace "kin samu kin gama  ammina  dan sai na  kawo   miki  irin matan  hurul'ain  dan irinta  kike  bukata ta zama  surukarki   ya k'arasa  maganar yana dariya    tare da  matsowa  ya kamo  yatsun  hannun  tanweer  ya rike gam  cikin  nashi yana massaging a hankali  ,   itama ammi dariya take sosai tana sake tabbatar masa da hakan  take  so  , ita Kuwa tanweer  gbdy  ranta  a dagule  yake  sbd haushin   abinda yayi mata da Kuma haushin maganarsa da mahaifiyarsa  dan  duk  tana ji abinda mahaifiyarsa ke fada masa   sannan tana   Jin amsar da yake  Bata    cike da  fushi ta  soma k'okarin zare  hannunta  cikin  nashi  tana sauke wahalalle numfashi  sai dai ta kasa  kwatar hannunta dan haka tayita jan  tsaki babu kaukautawa ganin  hk  yasa yayi  sallama  da ammi  tun  kafin  ta  tunhumeshi  ,ya  katse Kiran yana  cewa   "ki  daina wahalar da  kanki  bake  ba ko namiji dan'uwana na rike bai Isa  ya kwace ba bare ke    " ko   kina tunani ni din irin  lusaran  samarinkanki ne da zaki gwada  karfi  dani   ..?"ya karasa  tmyr  yana furzar da  iska mai zafi daga bakinsa."

danne abinda taji ya tsaya mata arai tayi  tana zance zuci" shi take  mutuwar so amman shi burinsa kullum ya cusguna mata tare da nuna mata ita din ba kowa bace ,  tunda suka  had'u  yake kyautata mata  ta hanyar  bata  kulawa  sai dai a fahimtarta bashi da burin daya wuce   ya 'bata  mata  rai  ta hanyar fada  mata  baqaqen  maganganu . tasan  ba lallai ta zamo test dinsa ba amman at least itama tana da daidai nata  kyau sama  sama ta dinga fidda numfashi  tana danne damuwarta  "dan  Allah  direba ka taka  motar nan da sauri  Ina son d'aura kwayar idanuna  akan  iyayena wad'anda   suka zamo min bango abun ma jingina  kuma  farincikina   nasan suma  nice farincikinsu rashina baqaramin  babban  tashin hankali bane  garesu  suna can suna mararina"

  "shiiiii......." munafurcin  banza kawai   kina dai  son kije kiga wad'an can  rubabbun  samarin naki   barin wancan  me murya  gangarin da bata  dadin  saurara "ya Allah ta furta dan sai  lokacin ta fahimci  a fili tayi maganar , muryarta qasa qasa tace "kafa  san  irin maganar da zaka dinga fad'a  min dan ni din ba motar haya bace bare  kayi tunanin Ina tara kwashe  kwashen  samari Ko da yake yau ne final  kasancewata    da  kai zaka  mayardani  gidanmu  na  gode da  taimako  ta k'arasa maganar tana murgad'a masa  'karamin bakinta "karki gode min ki godewa Allah sannan  na fiki jin dadin zan rabu dake na huta da ganin wannan fuskartaki .
muryarta a raunane tace " aikin banza  kawai  Nima daga yau ai  bazaka sake ganin ko me kama dani bane tayi mgnr tana jan  dogon   tsaki shiru yayi yana ciza gefen lips dinsa can kuma ya murtuke   fuskarsa    yace "wannan shine Karonki na farko Kuma Ina son ya zamo Karo na karshe karki yarda ki sake min tsaki a rayuwarki , ko ni sa'anki ne da zaki dinga ja  min tsaki yayi tmbyr  yana murd'e mata hannu qara ta saki mara sauti tare da cewa "a'a kayi hakuri hannuna zafi  bai mata  magana ba ya sausauta rikon da yayiwa hannun  tare da bud'e tafin  hannun  ya tsurawa tsakiyar hannunta   kyawar Idanunshi yana kallo , a hankali ya d'aura dayan hannunsa ciki  ya fara  mata tafiyar tsutsa wani  irin tsalle hade da bugawa zuciyar tanweer yayi  take tsigar jikinta suka mike kasa cewa komai tayi illa numfashin  da take saukewa  da kyar  tare da jin wani sauyi na dabam  a sansar jikinta.  Shima  wani  irin abu  yake ji yana masa yawo a gbdy ilahirin jikinsa wanda ya haddasawa qirjinsa tsananta bugawa wani tunani yayi gara ya sake musguna mata kafin su rabu   ,wayarsa  ya d'auka ya soma danne  danne bayan kmr second biyu ya kira sunan eku remo dake  tukasu  ."eku ka duba wayarka na  tura maka sako  eku yace "noted  boss ya  tura wa su anas  dake   bayansa  Sako  kamar yadda ya turawa eku sannan ya  koma ya jingina bayansa ya runtse  idanunshi .."

motar    bata  tsaya a koina  ba  sai   gaban   katon    get   din  Rita Lori hotel   dake  onipan  , get  din   already a bud'e yake kamar Koda yaushe security's  ne  tam ciki da wajen  hotel din saboda manya  masu kudi da kusoshin  gwanati  dake zuwa  da manya manyan yan fashi da makami , gurin  fitowa daga ciki hotel  din  dabam haka zalika  gurin shiga dabam , eku ya  sanya  hancin  motarsa  cikin Rita Lori,  d'aya daga  cikin security's din gurin  ya mike da sauri  ya  zare karfen da sakale  Wanda  ke  bawa  mutun damar shiga,   eku  ya   samu  guri ya soma k'okarin  parking  adaidai   lokacin  da motar  alqali  danasu anas   ya shigo
haraban    hotel  ne  dake da  bangare dabam  dabam  dan  shakatawa sam  tanweer  bata fahimci  Inda suke ba saboda ranta dake 'bace .
a natse jaguwa ya fito ya zagayo bangaren da take zaune  ya bud' mata   kofa "fito ko ".ya fad'a  yana furzar da iska mai  zafi  daga bakinsa
ta  yunkura a hankali ta fito  tana  jiran ta ganta a haraban  gidansu kawai ta  ganta a Rita Lori hotel a hankali ta dinga bin gurin da kallo qirjinta na dokawa da matsanacin karfi  tana son gano Inda take bata Ankara ba taji ya riko tsintsiyar  hannunta  ya fara tafiya daita  zuwa cikin had'ad'd'en  club din dake ciki,   banda sautin kidi da waka  baka Jin sautin  komai "Ina ne nan ka kawoni  ? tayi masa  tambayar muryarta a tsarke  "gurin  shakatawa yayi  maganar a dake  yana cigaba  da tafiya daita  yayinda har lokacin  hannunta  na cikin nashi jikinta  na rawa taja ta tsaya  qirjinta na wani irin  bugu fiyye da kaida   juyowa  yayi  ya tsaida  idanunshi  a kanta  take ya fahimci damuwar data shiga adalilin ganinta a Inda suke  "gida  mukayi  da  Kai zaka Kai ni me yasa zaka kawoni nan ?shiru yayi kawai yana bin qaramin bakinta da kallo yana jin kmr ya rungumota jikinsa ya hau  sotsan  lips  dinta  ." ni gaskiya gida nake son  zuwa  ba nan ba ka Kai   gidanmu  tayi maganar  kamar zatayi kuka  dan  tuni hawaye sun gama cika mata Ido kafin kace me hawaye sun shiga turereniyar zubowa har da shesheka  hankalinsa ya tashi dan hk cikin tsarkewar murya yace  "Kinga  dan  Allah ki kwantar  da hankalinki bazan cutar dake ba Kuma bazan bar kowa ya cutar dake ba domin ba haka yasa na d'aukoki ba dan haka ki natsu ki kwantar da hankalinki ya dan yi shiru dan jin me zatace itama shiru tayi saboda jin  maganrsa  " kennan idan ta fahimci maganarsa shine d'an fashin daya d'aukota daga gaban iyayenta  ? wani irin bugu gabanta ya sake yi  da karfi kafin daga bisani qirjinta ya shiga dukan uku uku da numfashinta dake k'okarin  tsayawa hankalinta  yayi matukar tashi ta  dinga maimaita kalmarsa  ta karshe daya furta ."

a hankali ta shiga girgiza Kai "no no impossible bashi  bane sam bai yi kama da irin wad'an nan mutane ba dukkanin  alamun sun nuna shi din mutumin kirki ne ya dai taimaketa daga hannun yan fashi ne   zuciyarta ta  tsayu akan haka ,cikin natsuwa ya juya ya cigaba  da tafiya  cikin Isa da  izza ya barta tsaye adaidai lokacin da alqali ya fito daga cikin motarsa  wani  yawu ta hadeye   tana  qoqarin daidaita  numfashinta da  natsuwarta  ta biyo hanyar da ta ga yabi tana waige waige karaf idanunta ya sauka akan alqali da hannunsa  yayi mata alamar ta tsaya amman dake a tsorace take cikin sauri ta  shiga d'aga ka'fafunta  kmr walkiya ya nemeta  ya rasa Yana nan tsaye su anas  suka fito daya bayan daya suka wuce ta gabansa  kowanne ya kama gabansa kasancewar  kowannensu akwai bangaren  da  yafi so  ."

*******
Tsaye   tanweer    tayi  aguri d'aya  kamar wacce aka dasa tsabar tashin hankali Inda  ta tsinci kanta a yau din nan ,  ta rungume hannuwanta duka aqirji har loakcin sauti ne ke tashi  akoina acikin Rita Lori yayinda jaguwa tuni ya

Please Login or Register in order to submit comment