Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fata mai kyau da tsada yayinda kwantaccen sumar Kansa ya sha gyara ya kwanta luf luf Hakan ya karawa fuskarsa kyau da annuri sai dai fuskar a hade take babu alamun fara'a ko kad'an ,key din motarsa ferari ne rike a hannunsa Kai tsaye d'akin da tanweer take ya kutsa ya shiga bakinsa d'auke da sallama sai da aciki yayi ,kamshin turarensa daya saba amfanin dashi ne ya doki hancinta ta d'ago a natse ta tsura masa idanunta kamar Koda yaushe fuskar nan tashi babu wadataccen fara'a, muryarta a sanyaye ta motsa labbanta"Ina yini ?"bai amsa mata ba sai ma wani kallon banza daya bita dashi kafin ya d'auke kanshi daga kallonta ya nufi Inda bedside yake ya bude.
bata damu ba dan tasan dole zuciyarsa ta d'auki fushi daita sakamakon abinda tayi masa jiya wasu file ya ciro yana dubawa ya d'auki minti biyar yana tsaye yana dubawa sannan ya mayar ya ajiye ya juya ya fita ya nufi parlour yana taku a hankali kamar bai son taka kasa har sanda ya fito parlour'nsa .
Gbdy abokansa suna zaune kamil nacin abinci ,yayinda jubi ke k'okarin nada tabar wiwi , kunnen anas manne da waya yana ganinsa ya mike tsaye da sauri yana binsa da kallo .
Shima jaguwa Tsura masa Ido yayi yana karanta yanayin wayar da yake , anas ya karasa sosai kusa dashi ya rike masa hannu yana cewa "tanko gote ne wai yana da alqalla me kyau da yake son muyi masa ya kira layinka ba baka d'auka ba shine ya kirani kayi magana dashi ya mika masa wayar . "bazan yi magana dashi ba kaima karka sake d'aukar wayarsa sanin kanka ne anas bama Kulla alqalla da irinsu tanko gote mutumin da nake fatan a karshen rayuwarsa ya zamo mabaraci akan titi ya numfasa sannan ya cigaba da magana a sanyaye " ka kula da kyau anas banason wani abu ya sameka idan wani abu ya sameka bazan yafe maka ba ".duk maganar jaguwa d'aya byn d'aya suke shiga kunnen tanko gote ya runtse idanunshi tare da disconnecting din kira."

" Inshallahu zan kular maka da kaina Ina zuwa haka ga abinci anyi order da Kai ? numfashi ya fesar yana yamutsa fuska kafin yace "zanje ganin ahlina idan naje can zanci zan dan d'auki lokaci ban dawo ba dan zan fara da biyawa gidan marayu akwai sakon da zan Kai musu yana gama fad'ar haka ya zare hannunsa ya juya ya fice daga parlour'n dan yasan yanzu raunin anas zai bayyana .
ilai kuwa hakan ce ta kasance gbdy yanayin anas ya canza rauninsa ya bayyana kamar zai yi kuka ,ya danne hawayensa suka koma, a duk sanda yaga jaguwa za shi ga ahlinsa sai yaji zuciyarsa tayi rauni saboda rasa nashi ahlin da yayi bashi da kowa a halin yanzu sai jaguwa shine komai nashi zama yayi ya shiga duniyar tunani .Kai tsaye Inda motarsa ferari yake ya nufa ya danna keyn hannunsa ya bud'e ya shiga ya zauna yana me kunna motar tare da yin hon me gadi ya wangalemasa get din gidan ya fice.

tafiyar awa d'aya ce ta kawoshi gidan marayu babus'salam dake ikeja gra yayi hon aka bud'e masa get ya shiga, yasa guri ya
yi parking din motarsa ya fito ya bud'e bayan boot dinsa ya ciro bakar jaka dake shake da kudi ya kulle motar Kai tsaye office din shugaban makarantar ya nufa .malam yusif na ganinsa ya fad'ad'a fuskarsa da murmushin jin dadi dan yawon zuwan jaguwa yasa sabo me karfi ya shiga tsakaninsu ,ya nuna masa gurin zama byn jaguwa ya zauna ya mika masa hannunsa suka gaisa "yalla'bai barka da zuwa ya aiki da k'okari ? "alhamdulillah ya naku k'okarin da fama da yara ? malam yusif yayi murmushi kawai ,sun dan ta'ba hirar duniya sannan jaguwa ya mika masa jakar kudin daya zo dashi "ga wadan nan kudaden ayi wa marayu hidima dasu.
"Kai masha Allah ,Allah yasa Saka da alkhairi ,Allah yasa maka ladan a mizani ,yadda kake faranta zukatan marayu Allah ya faranta naka , Allah ya kawo farinciki a rayuwarka data iyalinka, Allah ya tsareka". "Ameen na gode sosai da addua ni zan wuce har ya juya malam yasif yace "yalla'bai har yau baka fad'a min sunanka ba gashi za'a Saka cikin sunayen masu tallafawa marayu "ya juyo a natse yana cewa"bana bukatar a Saka suna , sukayi sallama ya wuce ya d'auki hanya zuwa unguwarsu ko gama daidaita parking din motarsa bai yi ba Jamar'sa na unguwar suka zagaye motarsa tare da Kawo masa gaisuwa.
a natse ya fito yana ƙoƙarin kulle motar byn ya kulle ya mika musu hannunsa d'aya bayan suka gaisa ya Ciro kudi masu yawa ya shiga raba musu me dubu biyar me dubu goma cike da murna suka dinga masa addua shi km yana amsawa da Ameen sannan ya sa Kai zuwa cikin gidansu.

yana shiga gidan ya hargitse da murnar ganinsa ya samu guri ya zauna akan kujera me zaman mutun biyu idanunshi na kan fuskar amminsa dake zaune fuskarta d'auke da annurin ganinsa duk cikin ya'yanta tafi qaunarsa saboda tausayin dake garesa, yana qaunarta da qaunar kannensa ,yana tausaya musu, duk abinda suke so zai musu batare da bata lokaci ba shine komai nasu ita da yaranta.
kannensa suka durkusa har
suka gaishesa ,bayan sun gaishesa kowacce ta samu guri ta zauna akan hannun kujerar da yake zaune.
yayi murmushi kana ya dan zamo ya gaishe da mahaifiyarsa "ammi Ina yini ?Lafiya lau ya gida ya fama da aiki ?
"alhamdulillah ammina ya fad'a tare da juyowa ya Kalli hally "Ina sadiq ko ya fita aiki ne ?bai fita ba father yana gida yanzu nan ya fita raka ya marwan bata qarasa rufe bakinta ba sai gashi ya shigo fuskarsa da murmushi dan tun daya ga motarsa a kofar gida yasan yazo ya gaishesa yana tmbyr me jiki jaguwa ya waske tamkar ba dashi yake magana ba.
ammi taso ta tambayesa abinda ya faru dashi jiya amman ganin Babu damuwa atare dashi sai zallar farinciki yasa ta kame bakinta sadiq ya samu guri ya zauna a gefen ammi yana sake tmbyrsa tanweer , ammi ta gyara zamanta tana cewa wacece babu Lafiya ne ?"budurwarsa ce ammi "ya fad'a cikin tsigar zolaya Jin haka yasa jaguwa ya waigo ya watsa masa katuwar harara "Kai haba sadiq yanzu daman yayanka yana da budurwa baka ta'ba fad'a min ba ? lallai kayi min laifi me girma zaka fuskanci hukunci ? Tayi mgnr kmr Adnan ba dan farinta bane, ta rasa dalilin da soyayyar dan nata yake hana kunyarta tasiri idan tagansa neman kunyar take ta rasa "Allah ammi Nima ban dade da sani ba "oh nace dai ta Kalli jaguwa banda abunka ai sai kayi magana a tura gidansu ba sai a had'a dana shafiqa ba a wuce gurin" .

jaguwa ya sake watsawa sadiq harara yana cewa "Allah ammi karki amince da maganarsa ba budurwata bace taimako nayi "taimako! ?ta tmbyesa tana tsura masa idanunta domin gano gaskiyar dake zuciyarsa ,ya gyada mata Kai alamun "eh ".
to ai shikenan idan dai har ka bata lokaci Allah auren dole zan maka na huta da wannan shan kamshin da kakewa aure ta k'arasa maganar tana cewa shafiqa "jeki zubowa yayanki abinci da sauri ta mike ta fita ko cikakken minti biyu batayi ba ta shigo rike da plet ,hally ta mike ta janyo karamin stood gabansa shafiqa ta ajiye abinci tare da bude masa cike da farinciki suka dinga Ina na Saka Ina ajiye da yayansu kowannensu na kokarin faranta masa, cike da matsanacin farinciki da soyayya jaguwa ya kai loman shikafa da miya bakinsa ya ajiye spoon shima sadiq ya matso ya d'auki spoon din da jaguwa yayi amfani dashi ya Kai bakinsa ,ya ajiye spoon jaguwa ya sake d'auka Sadiq yace "gsky father ya dace yadda kayi kyau din nan na rakaka gurin yarinyar nan zance Allah Kun dace ban ta'ba ganin mutanen da suka dace da junansu ba kmar ku ba ......"jaguwa ya wani kallesa shekeke yana cewa menene Kuma zance ? yayi mgnr tare da ajiye spoon din hannunsa ya d'auki tissue yana goge bakinsa "haba father karka waske mana ni dai dan Allah ka auri yarinyar nan wallahi tayi min "na fika sanin tayi aurenta ne dai bazan yi ba kwarya tabi kwarya ya fad'a a zuciyarsa .
"kasan Allah Sadiq yayanka Adnan yafi karfin zuwa wani zance ko menene kace sunansa Allah dai ya tsareni da ..."wani kallo da ammi tayi masa yasa shi katse abinda zai ce ya yamutsa fuska yana lumshewa ammi Idanunshi "duk kagama cika bakinka Muna nan zaka zo kayi auren ai duk dan sunan dole zai so aure "Allah ammi ko zanyi aure bazan je wani zance ba wannan zuwa zance fa kauyanci ne " agurinka ba me ra'ayin rikau amman meye na kauyanci aciki ?"
Allah ammin bayan kauyanci har da lalata Yara yake shi yasa kikaga bana son yaran nan nayi zance "a'a ban yarda da mgnrka ba zance baya wani lalata yaro sai dai can yaron dan iska ne Amman irin zance da shafiq ke yi taya yaro zai lalace a parlour'n nan suke zama gashi mutane ma na Kai kawo Kai dai ka Maida hankali ka tsaida matar aure ,
ni jikina ma ya fara bani lokaci yayi ".sadiq yayi tsigil yace "sosai ma kuwa ammi sai ma Kinga yarinyar dana ganshi daita Allah cewa zakiyi ya aureta kawai "Nan fa hirar ta juye zuwa ta aure jaguwa ya wani shagwa'be fuska kamar karamin yaro yace "ni dan Allah ka rabani da zance aure nan ,nifa auren nan ban ta'ba Jin zanyisa nan kusa ba Kuma ma idan zanyi zanyi ne dan ya zama sunnah da faranta ran ammi Kuma ko zanyi sai na nemo wacce zatayi hakurin zama dani ba wacce zan dinga rage murya ba Ina kaskantar da kaina ba, kasan fa mata idan suka ga ka damu dasu sai salo da iskanci ya tashi babu ma abinda ke bani takaici kmr kaga katon nmj a gaban karamar yarinya yana rage murya da kaskantar da Kai wai duk akan a amsa masa soyayyarsa Kai Allah bazan iya ba ni kawai idan ma ya zama dole Allah umarni kawai zan bata tunda ya fara mgn sadiq da kannensa mata har ma da ammi suke dariya.
Shi kuwa jaguwa yayi dip kmr anyi ruwa an d'auke ,duk yadda sadiq ya so acigaba da mgnr tanweer jaguwa yaki sai ma ya kawar da hirar ya shiga tmbyrsu abinda basu dashi a gida anan yayi sallahr magrib da isha'i
Hira sukayi sosai har lokaci yaja ya duba agogon hannuna karfe shadaya saura ya mike yayiwa ammi sallama byn ya ajiye mata bandir din kudi yan dari biyu biyu suka fita tare da sadiq domin yi masa rakiya ya shiga motarsa ya kunnata ya bata wuta sai da sadiq yaga tashinsa sannan ya koma gida ya rufe .
Koda ya koma gida bai bi ta kan kowa ba har ma tanweer ya shareta ,ita Kuwa idanunta shi suke son gani ta sake neman afuwansa amman yaki shigowa Inda take ranar da kyar ta runtsa kwana tayi juyi da kuka .

Washegari ta shigo d'akinsa bakinta d'auke da sallama yana kwance a akan doguwar kujera a falonsa dan tun bayan daya dawo sallah asuba yake kwance agurin ta ra'be gefe guda tana dubansa ,a hankali ta k'arasa ta tsugunna a gabansa tana kallon gefen fuskarsa Inda ta maresa ,saukar numfashinta akan fuskarsa yasa shi bude Ido eyes to eye's suke kallon juna "sorry for my active kayi hakuri nasan har yanzu kana fushi dani "ya juya mata baya yana jan tsaki ta sake matsowa sosai ta Kai hannunta jikinsa ya buge mata hannu da karfi ta rike hannunta tana runtse idanunta dan taji zafi sosai har cikin ranta taji dukan .
take gumi ya shiga tsatsafo mata a goshi da karan hancinta muryarta a shagwa'ba tace "yanzu bazaka yafe min ba ?banza yayi mata kamar bai san da wani halitta agurin ba "ki tashi ki bar d'akin nan tun kafin na tashi nayi miki abinda banyi niyya ba . "ka yarda nayi nadama "dan ubanki karkiyi nadama maza ki tashi ki bar d'aki ya fad'a yana mikewa tsaye da sauri itama ta mike tsaye"oya out of this room "dan murmushi gefen baki tayi tare da matsoshi sosai ta rungumeshi tsam ajikinta kamar za'a kwace mata shi, jinta ajikinsa yasa shi Jin wani iri muguwar kasala ,tayi lif a faffadan qirjinsa tana shakar numfashinsa da kamshi turarensa me d'aga hankali.
a hankali kowannensu ke sauke ajiyar zuciya muryarta a matukar sanyaye tace "karka sake zagin ubana ko zan d'auki komai ban da zagin mahaifina ka kiyaye harshenka " shiru tayi tana jiran abinda zai ce hannusa yasa ya zareta ajikinsa "tunda shine abinda kika fi tsana daga yau shi zan dinga fada miki "zan kuwa rama tunda uba bai fi ba "bar d'akin nan ya fada a fusace yana nuna mata kofa "karki sake shigo min daki "Kai ma haka karka sake zuwa Inda nake "wai ni sa'anki ne da ina fada kina fad'a?yayi mgnr a matukar hassale yana kokari damkota ta zame tayi baya da sauri tare da yi masa gwalo da karkad'a masa kunnuwanta.
tsura mata tsumammun idanunshi yayi kawai ya kasa cewa komai taku d'aya yayi ta kwasa da gudu ta bar d'akin ya ja dogon tsaki "zanyi maganinki ne ."Tun daga ranar bai sake shigowa Inda take ba hatta abinci ya daina kawo mata , lura da so yake yayi punishing dinta da yunwa yasa hankalinta ya tashi sosai ta shiga damuwar halin da zata shiga idan ta wuce kwana daya nan gaba batare data sakawa cikinta wani abu ba .

Sai da yayi kwana biyar yana fushi daita sannan ya sauko ya shigo domin kawo mata abinci ya ajiye mata farar leda zai fita tace "malam ka dawo ka d'auki abincinka bana ci duk kwanakin nan da baka kawo min abincin ba na mutu ne ?"ban mutu ba dan haka ka dauki kayanka ba zanci ba zan cigaba da zama haka har na bar gidan nan.
wani murmushin gefen baki yayi sannan ya juyo ya fuskanceta sosai yaga ta rame acikin kwanakin da yayi bata ci komai ba taku d'aya ya K'ara ya fara mgn cike da dakiyar zuciya "Kinga rashin cin abincinki ko rashin walwarki bazata dameni ba ,saboda bana sonki bakya cikin rayuwata bakya gabana ,kisan Allah ko nemanki na sake yi na rasa yanzu bazan damu ba saboda na lura baki da mutunci, bakida kirki ,baki da biyayya biki san komai ba sai zallar rashin kunya ,ada Ina matukar jin tausayinki da gudun abinda zai cutar dake amman a yanzu duk babu wannan , zan cigaba da rikeki ne dan na musguna miki dan fahimci kina qaunar komawa gida kamar yadda kike qaunar rayuwarki". yana dasa aya ta fashe da kuka tana cewa "Allah ya Saka min wallahi sai hakina ya bibiyi rayuwarka ni wallahi dama kasheni kayi na huta .
"bazan kasheki ba zaki zauna ki cigaba da ganin rayuwa a gidan nan , sannan babu abinda zai bibiye rayuwata bakinki bazai kamani ba danke ba uwata bace
yana gama fad'ar haka ya fice daga dakin ya barta tana kuka yana fita ta hau share hawayenta da hannuwanta duka ta Isa Inda ledar takeway yake ta bud'e ta fito da takeway jikinta har rawa yake ta soma cin abincin tana zubar da hawaye ."

jaguwa na fita daga d'akin gidan ya bari gbdy zuwa asibiti Kai ziyara sai dai tafiya kad'an yayi ya fahimci ana binsa abaya , ilai kuwa yana duba mirrow din motarsa dcp lawan numan ya gani zaune yana biye dashi nan take ya qara gudu shima ya biyosa a guje sunyi tafiya me nesa dcp na biye dashi daf da zai sha gaban jaguwa ya ciro bindigar ya harbi tayar motar dcp cak motar ta tsaya daga mugun gudun da take Allah ya taimakesa motar bata hantsila ba , yaja tsaki yana cewa zaku rasa ranku akaina idan baku daina bibiyata ba ya canza hanya ya cigaba da tafiya yana sauke numfashi ."
Cike da rashin kuzari dcp ya dawo office ya tara yaransa gbdy ya Kalli Inda babban yaronsa yake zaune "meye nazarinka akan wannan lamarin na kwamushe diyar minister da danfashin nan yayi yaki dawo daita sannan yaki bukatar komai daga hannun iyayenta ?"ni fa bansan abinda zance ba wannan lamari yafi karfin tunanina" kana ganin shigowar yan fashi gidan minister hakan bashi da halaka dana jikin minister ?
"Nima na fara tunanin akwai saka hannun wani dake tare da minister dan mutun abun tsoro ne zasu iya aikata komai amman Kuma bai zama lallai zarginka ya zamo gaskiya ba dan idan da saka hannun wasu zuwa yanzu zamuga alama" "haka ne Kuma nan suka shiga nazari akan abubuwan dake faruwa suna nan zaune har karfe shida kira ya shigo wayar dcp ya d'auka "Yana d'auka sautin jaguwa ya karad'e gurin dake a handsfree ya Saka wayar "barka da yammaci masoyina "masoyinka Kuma ?eh mana masoyina dake bbiyata a duk Inda na Saka kafa kaga dole na kiraka da masoyi yakamata ace kasan Koni wanene shiyasa ma na kiraka na sanar da Kai wani Abu da baka sani ba .

cike da zakuwa dcp yace "Ina jinka a she dai kana bukatar mu tautauna kenan ? ya mike cike da hanzari yana cewa "Ina saurareka me yasa kake aikata abinda kake aikatawa ?"so kake kasan dalilin da yasa nake aikata hakan? dcp ya gyada masa kai kmr yana gabansa " amman Kuma sanin dalilin ba fa shine me mahimmam ba sanin mahimmam aikina yafi ."
"yanzu har aikin fashi da garkuwar da mutane yana da wani mahimmanci ? Sannan Kai fa masheki ne "kwarai kuwa mahimmancinsa ne ma yasa nake aikata shi da kwarin gwaiwa ,kace masheki a karshen maganarka waye na sheke ?
"ban sani ba amman Kai ai kasan me laifi ne ? "Kenan har yanzu ana kan kirana da me laifi ? Idan ni an kirani da mai laifi su tanko gote da tawagarsa fa me za'a kirasu dashi ? gskiya Kai din mai baseera ne ya kamata na tayaka murna sosai amman meye laifina akan abinda nake aikatawa ?"
"shikenan na yarda baka da laifi amman Ina son na had'u da Kai mu tautaunawa abu me mahimmanci nima yanzu zan goyi banyanka dan nasan akwai jami'an tsaro da dama da suke aiki karkashin ikonka masu kawo maka rahoto akanmu' "dakata dcp har yanzu ba'a haifi uwar d'an da zai min wayo ba" dcp ya runtse idanunshi yana shafa goshinsa " ni nan da wayona aka haifeni idan kaga na bar mutun to naga dama ne , dcp ya furzar da iska sannan yace "Kai karka dauka wannan takamar da kake samun sauki ne ko mafuta ,karka manta har yanzu Kai din me laifi ne a kasar nan "na dauka yalla'bai dan ka kirani da me laifi amman kasani masu aikata laifin irin nawa basa ta'ba shiga hannun yansanda domin a idon alumma ba masu laifi bane idan da naso da Kai kanka bazaka iya bincike akaina ba sannan da na kawar da Kai a dazu dan ba tayar motarka zan harba kwakwaluwarka zan fasa .
"ya kamata ka taimaki rayuwarka data iyalinka ka hutar da kanka da tunaninka akaina dan bazaka iya komai ba."
"ka min shiru barawon banza kawai Kuma me garkuwa da mutane " yalla'bai ka dai kirani da kwararren d'an fashi wannan nasan Ina yi amman garkuwa da mutane wannan ba aikina bane gurinsu tanko gote zaku samu cikakken bayanai masu yi ,ku daina bibiyata dan ga dukkanin alamun Kuna sa Ina Kara yin suna a duniya kunsa koina acikin garin nan sunan jaguwa kawai ake kira .
"idan aiki kuke bukata karku manta akwai yaran da kullum ake musu fayde sannan akwai yaran da kullum ake maidasu marayu saboda basu da gata arayuwaarsu da talakawan da basu ji ba basu gani ba aka sakasu shiga tashin hankali ,
aikin ne da yakamata Kuna tsaye akansu amman duk kun kasa daukar mataki Kuna zaune a office sanye da uniform din sharri ?"bari Kuji Ina kan zuwa kan aikinsu domin na hukuntasu bisa laifinsu tunda ku cin hanci ya hanaku bawa kasarku tsaron daya dace ".
"Ina ruwanka da wannan bangaren ?baka da hurumin hukunta ko ma wanene dan Kai ba kowa bane tamkar matacce dan kana shigowa hannu mutuwa ce zata tarbeka .
"nasani yalla'bai ni ba kowa bane Kuma duk daren dadewa zan mutu ko baka fad'a ba,Amman kasan da cewa Ina kishin kasata ni d'an kasa ne me kishin Kai Kuma na zabi farinciki al'uma akan mutuwa da komai Kuma zan hukunta azzaluman sannan na kawo karshen rayuwarsu.
"wallahi Kai sheidan ne "kwarai kuwa ka kirani da abinda yafi haka indai akan gaskiyata ne na yarda ."me ! dcp ya fad'a a razane shine dansanda Amman yafi shi shiga tashin hankali.
"Eh tamkar mota haka zamu cigaba da karawa da Kai Amman kasani a koda yaushe Ina gabanka daga nan har izuwa lokacin da zaka gane ba kuskure nake aikatawa ba domin kuwa ko za'a fito da gaskiyar a yanzu bazai shafe *KUSKUREN BAYA BA* shiru dcp yayi da sauran mutane suna sauraronsa "da zaku gane da Kun daina bincike akaina Ina fatan ka fahimta masoyi "tur da Hali irin naka yanzu yaushe zaka dawo da diyar minis ...."ai kafin ya karasa mgnr yaji kit wayar ta mutu tsaki dcp yaja yace "yanzu kenan bazamu iya kamashi ba ?da alama kam inji cewar daya daga ciki police din dake gurin "aikin banza kama wannan dan fashin dole ne Koda zan rasa rayuwata dole mu cigaba da bibiyarsa tunda da alamun har yanzu bai fahimci mun tura masa jami'n sirri ba dole zai shigo hannunmu a lokacin zai gane kuskuren da yake aikatawa sai yayi dayasani mara amfani wai shi me hukunta masu laifi , nida Kai ba masoya bane makiyan juna ne yadda kake bibiyar komai namu muma hk muna bibiyar  komai naka ."

********
Tanweer zaune a bakin gado tayi shiru ta zuba uban tagumi tana tunanin shikenan ta sadaukar ita da iyayenta sai alahira idan da rabon zasu had'u dan bata ga al'amun zata koma garesu ba ta barwa Allah komai komai yayi zafi maganinsa Allah
a tsakanin wannan lokacin ta lura Kullum gidan cike yake da mutane da yammata kala dabam dabam , wasu masu fasali wasu marasa fali ga shaye shaye baka jin kamshi komai a gidan sai na wiwi da ta'ba da sauran kayan shaye shaye, wannan Abu na matukar daga mata hankali idan ta tuna da irin qaunar da take wa Adnan kullum kokari take taga ta yakicesa a rayuwata dan ingata nata rayuwar amman abun ya cutura kullum soyyarsa sake nunkuwa yake amman hakan bai hanata son komawa gida ba .
ganin yadda gidan ya rikice yasa take kulle kofar d'akinta dan bazata zauna akaita a baro ba .tun da jaguwa ya lura tana kulle kofar ya tsareta yayi mata gud warning "karki sake kulle kofar nan ko da kudin ubanki na gina gidan ?"
ranta a matukar bace tace " ba da kudin ubana ka gina ba hakazalika Kai ma bada kudin ubanka ka gina ba da kudin ubannen mutane ka gi... "bata k'arasa ba taji saukar mari akan quncinta "zaki sha wahala matuka a hannuna muddin zan dinga fada kina fad'a Kuma na rantse na sake ganin kin kulle kofar d'akin nan zaki ga yadda zanyi dake ."

Ya sake d'aukar fushi me tsanani daita bata damu ba duk sanda ya fad'a sai ta fad'a masa haka rayuwar tanweer ta cigaba a gidan jaguwa cikin rashin Jin dadi da kwanciyar hankali domin kuwa a maimakon abubuwansa yayi sauki sai yayi gaba tayi fushin tayi zagin tayi rashin kunya duk abanza dan bai canza ba sannan bai sauko daga fushin da yake daita ba dan haka ta sauko daga nata fushin tayi k'okarin shawo kansa amman ya faskara ta bishi har d'akinsa ta bashi hakuri amman yaki nan itama ta fita hanyarsa ko kallon kofar d'akinsa ta daina kullum cikin addua take Allah ya kawo mata d'auki ,adduar da batayi ada shi ya zamo abokin hirarta a yanzu ."
*****

Hajiya Zainab zaune cikin halin damuwar da take kawarta hjy saratu ta kawo mata ziyara tare da diyarta mardiyya

Please Login or Register in order to submit comment