Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadda ka taimaka ka ceci rayuwar diyarmu kai ma allah ceci rayuwarka tana gama fadar hk ta juyawa ta nufi hanyar fita kunneta manne da waya tana magana da dady “.

rukayya ta karaso inda yake “please ya dace ka wuce gida haka kafin dady ya karaso wani irin dagowa yayi yana mata wani kallo da yasa kayan cikinta juyawa kafin a hankali ya mike ya sake komawa dakin da tanwer take kwance ya tsaya agabanta kallonta kawai yake cike da tausayawa har baya qaunar ya dauke idanunshi akanta wanda ita sam batasan yana yi ba ,ahankali ya matso kusa da fuskarta yana hura mata iskar bakinsa at the same time yana shakar nunfaahinta sai kusan goma saura ya fito daga dakin jiki a sanyaye ya shiga mota zuciyarsa na bugawa da karfi eku ya jashi suka fita daga hospital tafiyar mintuna talatin ta kawo su gida eku yayi parking ya kashe motar ya fito yana tafiya yana balbale botiran gaban rigarsa kai tsaye hanyar bedroom ya nufa yana karasa cire rigar gbdy ya shiga bathroom zuciyarsa cike da tunanin halin daya baro tanwer.
Shima dady agigice ya shigo dakin “Me ya samu tanwer?” inna lillahi me ya faru da ita please dady ke tambaya rukayya dake rarrashin mumy muryarta a raunane tace “ tsautsayi ne dady ku mata addua inshaallahu zata samu lafiya dady ya kalli mumy yana shafa kan tanwer “please karki kuka zainaba babu abinda zai samu tanwer dinmu zata samu lfy zata dawo daidai muyi wasa muyi dariya kamar yadda muka saba bazamu rasata ba , duk da zuciyarta na cike da jin haushin laifin da yayi mata amman sai daya bata tausayi ta matso ta rungumeshi tana kuka “ina son tanwer bana son na rasata “bazamu rasata ba inshaallahu sai munga yayanta “.

Jaguwa ya jima a bathroom cikin halin tunanin kafin yay wanka ,ya nemi rigar towel tare da towel dinta ya lullube koina ajikinsa ya fito ya dan leko yana dube dube yayi saa ganin fitowa anas daga dakinsa cikin sauri ya nufosa alokacin da ya juyo ya koma cikin dakin,anas ya murda kofar ya shiga yana kiran sunansa, ya kallesa cike da manaki “adnan yaushe ka dawo gidan nan ? .
“Ban jima ba ya fada ,shiru anas yayi yana sake kallon jaguwa fuskarsa cike da zullumi da fargaba yace “ka samu natsuwa please kai kasan rashin samun kwanciyar hankalinka daidai yake da nawa rashin kwanciyar hankali , jin haka yasa jaguwa ya sakar masa murmushin karfin hali,”Na kasa jurar ganin tanwer da ciwon nan , da mutun na cirewa wani ciwo wallahi dana cire mata na dauki nauyinsa. “ba cire ciwon yafi dacewa kayi ba ka aureta shine kawai abinda zaka mata ka samar mata kwanciyar hankali”bai sake cewa komai ba dan yasan ba abu ne me sauki da yuwu ba agaresa .
“Me zakaci naje na siyo maka?jaguwa ya kallesa sannan ya kalli agogon dake manne a parlaur’sa karfe shadaya ta wuce muryarsa a kasalance yace “karka damu “haba adnan duk wunin yau fa ina lura da kai baka sakawa cikinka komai ba ka daure kaci wani abu,bazan iya ci bane anas“okay bari na hada maka coffee first ka fara sha ya juya da sauri bai dade ba ya dawo ya mika masa cup din tangaram “ka dan sha please cikinka zai warware har ka iya cin wani ba ,zanje checking republic yanzu zan dawo ya juya da sauri ya sake fita .
jaguwa ya fesar da numfashi yana jin wani irin faduwar gaba mai tsanani ya samu guri akan kujera mai zaman mutun uku ya zauna yana kurban coffee ahankali, hoton fuskarta ya shiga gani acikin kwayar idanunshi yana jin wata irin tsantsar soyayyarta na ratsashi shi fa duk daukan da yake zai iya cigaba da rayuwa ko babu ita a she babban kuskure ya tafka bazai iya ba,tabbas bazai iya cigaba da rayuwa babu ita ba dan yana mata soyayyar da bazata misaltu ba zuciyarsa bata bugawa in har babu tunaninta sai dai kash aurenta kuskure zai yi akan *KUSKUREN BAY*

cikin mintuna da basu wuce talatin ba anas yayi knowking ya shigo hannunsa rike da farar leda ya iske jaguwa zaune a falonsa ya daura kafa daya akan daya yayi zurfi cikin tunani ya ajiye ledar ya dafa shi nan ya sauke numfashi da karfi sannan ya maida kallonsa ga ledar dake ajiye “sorry my friend ka rage damuwar nan ka bar tuna abinda ya faru daita,ya zan iya mantawa byn ni ne sanadi ya fada fuskarsa da tsantsar damuwa ,da kyar anas ya lalllabashi yaci arsh da soyayyar kaza ranar sam jaguwa bai yi bacci ba ga tsananin bacci yana ji amman ya kasa saboda so da tausayin tanwer dake nukurkusan zuciyarsa sai faman juyi yake,shima anas bai yi bacci ba duk motsin da jaguwa zai yi zai motsa ya rarrashesa jaguwa karshe ya mike zaune ya kunna wutar dakin yana cewa “anas ina ganin zan koma hospital gara kawai na zauna tare daita hankalina zai fi kwanciya ya fada yana durowa daga Kan gado dariya ce ta kusan subucewa anas amman yayi saurin dannewa dan yasan yana Kuskuren yinta zai janyo wa kansa matsala dan zuciyar maza zata matso.
“kajika da wata mgn kafin iyayenta sonta ne ko me ? ”kaji dan iska nace maka ina sonta ne na damu ne kawai saboda ni ne silar accident din da tayi.”wai kai har yanzu bazaka daina yaudarar kanka ba?wallahi ka guji ranar da zuciyarka zata gaza hakuri akanta,ka guji ranar da nadamarka bazata maka amfani ba , sannan ka guji ranar da hakin yarinyar nan zai kamaka wannan fa zalinci ne qarara kake yi ,jaguwa yayi tsuru yana kallonsa qirjinsa na dokawa ,”eh mana kana zalintar yarinyar nan over “.
.please anas ka bar maganar nan karka min baki ,wallahi babu wani batun baki sai gskyar da kake ki ce nake fada maka kai kafi kowa sani muna fadawa juna gaskiya koda kuwa zamu samu matsala da juna”ya sake yi shiru dan yasan gsky ya fada masa ka koma ka kwanta babu inda kazaje adaren nan dan ko ka koma bazaka samu natsuwar da kake bukata ba saboda iyayenta na tare daita anas ya fada tare da komawa ya kwanta ya juya masa baya .
jiki a sanyaye jaguwa ya kashe wuta ya koma kan gadon sai dai ya kasa kwanciya ya jingina bayansa da abun gado ya janyo pillow har guda biyu ya matse aqirjinsa ,hhhhhh kadan ma kagani jaguwa ba dai taurin kai ba.Bangaren tanwer har safiya tayi bata san inda kanta yake ba duk ta galabaita ciki ciki take fidda nunfashi .”

Tunda sassafe ya tashi ya shirya ya bar gidan sai daya tsaya yayi mata siyayya kayan amfani sannan ya nufi asibitin,ahankali yayi parking din motarsa a haraban hospital ya kashe ya fito zuwa ciki jikinsa sanye da blue black din riga da dogon wondo baki, hannunsa daya daure da agogon fata baki yayinda dayan hannun ke daure da band baki .
Kai tsaye hanyar dakin da take kwance ya nufa qirjinsa na wani irin bugawa da matsanancin karfin gaske dan bai san su wa zai tarar a dakin ba ,
adduarsa kada ya iske kowa ,cike da natsuwa ya tura kofar dakin ya shiga bakinsa dauke da sallama aiko ya taki saa babu kowa adakin sai ita kadai .
naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfi sannan ya cigaba da taku a natse kamar bai son taka kasa har ya karaso bakin gadon da take kwance ya tsaya idanunshi na kanta ,jikinsa a matukar sanyaye ya samu guri ya ajiye ledar hannunsa ya zauna still kwayar idanunshi na kallon kyakkyawar fuskarta yayinda take sauke numfashi a hankali a hankali ,
hannunta daya na saman ruwan cikinta kusan 20 minutes yana zaune yana kallon kafin daga baya ya mike a hankali ya soma zagaye gadon da take kwance yana cigaba da kallonta zuciyarsa na narkewa akanta bashi da ja ya rigada ya kamu da matsanancin soyayyarta sai wani ikon allah ne kadai zai fitar dashi amman zai yi iya yinsa ya bawa zuciyarsa hakura domin kuwa samunta ba abune mai sauki da yuwu agaresa ba.
Sama da awa daya yana zariya a cikin dakin amman duk bata motsa ba ya juya ya fita zuwa office din doctor ya cike wasu takardu ya sake dawowa dakin ya jingina jikknsa da bango dakin hade da rungume duka hannuwansa a qirjinsa yana dubanta cike da tsananin tausayawa ,hawayen tausayin kansa suka cika idanunshi ya kai hannunsa ya goge sannan ya dawo kusa daita ya zauna .Ahankali ta fara motsa jikknta yayi saurin mikewa ya tashi ya nufi kofar fita domin kiran doctor ...
"Adnan dina .....!"
Ta kira sunansa muryarta a raunane ,ya juyo da sauri ya dawo ya tsaya a gabanta ta sakar masa murmushinta mai bugar masa da zuciya tana cewa "ya kake?"
Ya matsota sosai Kmr zai shige jikinta tare da riko laulausan tafin hannunta cikin nashi wani irin yanayi suka tsinci kansu mai wuyar misaltuwa "ni ya kamata nayi miki wannan tamvayar ".Ta lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya tare da jin wani sanyi dadi na ratsa sansar jikinta .
a hankali ta canza fuska zuwa ta shagwaba kamar zatayi kuka " ya ka hade fuska haka ?"Idan bana ganin murmushi akan fuskarka bana jin dadi tayi mgnr idanunta na cikin nashi .
Ya tsuke bakinsa yana duban cikin kwayar idanunta batare da yace uffan ba "zafi nake ji sosai a goshina tayi mgnr cike da shagwaba tana matse hannunshi dake cikin nata."Karki damu zaki samu lafiya bari na kira doctor yayi kokarin zare hannunsa ta rike gam "in da ka amince munje gurin shakatawa da kai da yanzu kaima kana kwance a gadon asibiti kamar ni"karki damu haka allah ya qaddara kema zaki samu lafiya "kai ma ka kwantar da hankalinka lafiyata lau ,na tsaya ina kallonka ne ban san mota ta taho ba .
Murmushin jin dadin yadda take sonshi ya bayyana akan fuskarsa ya dawo daidai kanta ya daura hannunsa a kanta ,yayinda dayan hannun ke cikin nata yace "is okay zaki samu lafiya amman ki rage wannan son tanwer yayi yawa adnan fa da kike mutuwar so ba kowa bane kamar yadda kika dauka dayan hannunta ta daura akan hannunsa tana shafawa "kaine kake ganin haka amman ni nasan kowa ne kai , kai din mutumin kirki ne mai tausayi inshallah rayuwarka zata canza bazaka kare rayuwarka a wannan sana’ar ba..."
“Ya girgiza kai me yasa kike irin wannan maganar ?ta bude baki zata sake mgn ya katseta “ba wannan tunanin ne agabana ba ni dai ki samu lafiya sannan kiyi min alkawarin bazaki sake min wannan ganganci ba da wani abu ya faru dake fa? “inshaallahu karka damu zan dinga kiyayewa bai ce komai ba ya gyara mata kwanciya ya jingina bayanta tare da sa mata pillow yana mata sannu sannan ya ciro toothpaste peppermint ya matsa akan brush ya dauko farantin silver ya bude goran ruwa roba daya zo dashi ya dawo kusa daita ya kai brush bakinta “ki wanke baki kafin su kawo miki abinci kici sai ki huta dan kina bukatar hutu tayi murmshi tace “bazan gaji da yi maka adduar shirya ba allah ya kawo karshen damuwarka ,ta fada hawaye na cika idanunta .
“na gode ya fada atakaice zuciyarta tayi sanyi da jin abinda yace numfashi ya sauke lokacin daya gama wanke mata baki “allah sarki tanwer kwanciyar hankalinsa shine nata haka tashin hankalinsa shine nata bata son ganinsa cikin damuwa .”

suna zaune suna kallon juna aka turo kofar dakin da teburin abinci baa tsaya dashi akoina ba sai gefenta “adnan !Ta kira sunansa bai ce uffan ba ya maida abun wanke baki ya dawo ya bude plet din farko white rice sai dayan plet din shi kuma stew ne sai dan karamin jug dake dauke da ruwan zafi “adnan !”
Ta sake kiran sunansa bai amsa ba ya tsura mata ido kawai yana sauraranta “ni cikakkiyar masoyiyarka ce shiyasa kaga ina kyamatar aikinka ka yarda dani amatsayin masoyiya zan tsaya maka akowani hali bazan taba cutar da kai ba amman ka mika kanka ga hukuma saboda zan shiga ciki bazasu cutar da kai ba wallahi muddin baka daina wannan sanar ba zaka cigaba da rayuwa ne cikin dar dar, “ har yaushe zaka daina rayuwa atakure? kowa so yake yasan fuskarka ta ainihi “Dan allah ka amince da shawarata bazan gujeka ba zan rayu da kai akowani hali please kace ka amince.
Kansa ya kawar gefe”yana jin kamar ya amince da maganarta sai dai zuciyarsa tace “no karka yarda bakasan a wani hali zaka tsinci kanka ba dan haka ya furta mata “aa ! amman a ranshi yace
inshaallahu zanyi kokarin na rage wasu abubuwa ko dan hankalinki ya kwanta .ya tsiyaya mata ruwan tea a cup ya bata ta sha kadan kana ahankali ya kai spoon din abinci bakinta taki bude baki , ya sake kai bakinta “no bana ci ta fada tana hade fuskar “ya kamo yatsun hannunta da dayan hannunsa yana murzawa ahankali yana sake kai spoon bakinta yadda ya dinga mata ko bata da niyyar ci dole sai yasa ta fara ci a natse ya dinga bata abinci yana kallon kyakkyawar fuskarta yana cigaba da murza yatsun hannunta itama din shi take kallo taci abinci sosai sannan ta kawar da kanta alamun ta koshi ta lura hakan yasa shi farinciki matuka sannan ya ciro hanky a gaban Aljihun rigarsa ya goge mata baki sannan ya dinga kokarin sata dariya bai wani dade ba yace mata zai wuce har ya mike ta tsaidashi ya tsura mata ido kawai suna kallon kwayar idanun juna dady ya shigo tare da rukkaya rike da basket din abinci motsin shigowarsu yasa ta maida hankalinta ga kofar dady ganin dan haka tayi saurin sunkuyar da kanta kasa shima jaguwa kasa yayi da idanunshi kirjinsa na bugawa kamar zai fashe “oh my god tanwer me yasa kika saidani?Cikin yanayi na tashin hankali dady ya karaso ciki sosai yana cewa “waye wannan “?ta dago kanta agigice jin tmbyr dady “da….dady ad…ad….”sai kuma ta kasa karasa maganar “ad…ad “me ya kawoshi ?muryarta na rawa cike da in ..inna tace” shi shine ya kawoni hospital.”

You’re very stupid da shine ya kawoki hospital “wai tanwer me zakiyi dashi ? wallahi kinji na ratsen muddin baki fita hanyar wannan ba zan mugun saba mki,ganin idanunki zan shayar dake mamaki ,jaguwa ya juya da sauri cikin tsananin tashin hankali ya bar dakin “wallahi bazan hakura na bar masa ke ba sai dai shi hakura ya bar min ke,idan na sake jin yazo hospital dina ko na sake ganinsa sai na sa an kamamun keda shi nafiki iya wulakaci tunda ke bakisan rarrashi ba,muna lallabaki ne ba dan muna jin tsoronki ba amman tunda baki san rarasshi ba zanyi maganinki yana gama fadar haka ya juya fuuuuuu ya bar daki.
Tanwer ta sauke naunayen ajiyar zuciya sannan tace “rukayya ina wayata ta ciro acikin Jakarta ta mka mata number jaguwa ta kira kira daya ya dauka yana cewa “tanwer yaakayi ne? muryarta a sanyayye tace “kayi hakuri please,daakayi me kuma?abinda dady yayi maka,no karki damu komai zai wuce inshaallahu nine fa nayi laifi ina janyo miki bacin rai ga fushin da iyayenki suke dake inshaallahu sai rabaki da wannan ciwon ki zauna lfy ki daina samu matsala da iyayenki .
qasa tayi da murya tana cewa “no karka min haka please “dole zan miki domin duk uba na gari bazai so diyarsa tayi soyayya da mutun irina ba bare har takaisu ga yin aure “zanyi comfuse dinsu,no ke kike daukar hakan da sauki alhalin babu sauki domin wannan shine dabiyar mutane babu uban da yana ji kuma yana gani ya bada auren diyatsa ga irinmu zan rikeki a matsayin kanwa kema kuma ki rikeni amatsayin yaya sai nazo gobe yana karasa maganar ya katse kiran yana jin wani irin ciwo mai tsananin acikin kanshi dan dole na raba zuciyata da tunaninki ta kowani hali.
Rukayya ta matso kusa daita “na zuba miki abinci?no adnan ya bani,gsky shima da alamun yana sonki sosai kinga yadda ya rikice ya shiga tashin hankali lokacin da motar nan ta bugeki har da hawayensa intakaita miki dashi aka shiga emergency room a gabansa akayi miki komai ina ma su dady da mumy zasu yarda da ba karamin sa’ar miji kikayi ba.
dadi ya lullube tanwer nan take taji kashi hamsin daga cikin damuwarta ta kau ta dinga jin sanyi dadi na bin jijiyoyin jikinta “gashi kyakkyawa gsky yana da kyau sosai a yanzu bana ganin laifinki gashi da ganin zai yi tausayi da bawa mace kulawa girgiza kai kawai tanwer tayi lokacin dataji mgnr ruky ta karshe sai dai aranta tace “allah sarki ruky ai kyaun dan maciji garesa suna tare har mumy tazo tanwer bata boyewa mumy komai ba akan zuwan adnan da abinda dady masa “allah mumy ina son shi matuka zafa ku rasani akanshi “rukayya ta daura da nata”gsky mumy yana da kirki ga natsuwa uwa uba kyau shine fa wanda na nuna miki jiya zaune a koridoor dana ce ya taimaka ya kawota hospital mumy kisa baki dady ya barta ta auresa ni sam banga ilarsa nan tashiga koro mata dalilin accident din “
Naunayen ajiyar zuciya mumy ta sauke batare data ce komai “dan allah mumy ki dan samu lokaci ki gansa ki kare masa kallo na musamman na san zaki fahimci wani abu attare dashi domin kina da tunani mai tattare da kaifin baseera ta karasa maganar tana kamo hannunta “naji zanyi wani abu.cike da farinciki tan ta kwanto jikin mumy tare kamo hannunta ta matse cikin nata “na gode mumy .
Mumy ta kai hannunta tana shafa bayanta ita daman ta mika wuya fatanta allah ya tabbatar musu da alkhairi za dai tasan hanyar dazaa bi domin komai yazo da sauki “ta mike ta bar rukayya ta dawo gida.

"Kai tsaye jaguwa gidan mlm mudi ya nufa Kansa na ci gaba da sarawa ,a hankali ya zauna akan kujerar kushion dake falo ya daura kafarsa daya akan daya yana shafa kwantaccen sumar dake kwance a fuskarsa yana cigaba da tunanin tanwer “Oh my godness wai meyake faruwa da nine komai ya zama worst a gareni?shine tambayar da yayiwa zuciyarsa.yana zaune malam mudi ya shigo ya zauna cike da girmamawa ya gyara zamansa ya gaishesa “ya dai adnan fatan dai lafiya naga duk kayi wani iri ?lafiya ya bashi amsa yna shafa sumar kansa,to allah yasa mu dace jaguwa yace “ameen yana dan ciza gefen lips dinsa ya numfasa kana ya soma mgana a natse “akwai wasu baynai né malam mudi da kace nazo ?”
“Eh akan dai batun koken din da nayi maka mgn ne har yanzu raina nason kayi aiki akansa karkayi tunani manyan kasar nan dake da hannu ciki kayi dan allah da kuma alumna ,iyayen yara bilaadadin zasu ji dadi “tô shikenan zanga abinda zan iya yi akai .”Yauwa kayi kokari kayi wani abu nasan dakatar dasu ba komai bane agurinka ai baka manta da dukkanin bayanan dana baka ba?”eh ban mata ba nima kabani lokaci zan sake zurfafa bincike idan lokacin fara aikin yayi zan nasar maka nan suka cigaba da tautaunawa mlm mudi yasa yarinyar safna ta kawo masa abinci.”


mumy na komawa gida ta zubewa kasa tana zubar da hawaye a gaban dady a matukar tsorace yake kallonta “ka daina mamakin ganina a durkushe agabanka ba dan kai na durkusa ba saboda rayuwar diyata nayi domin zan iya komai akanta kasani nasani diyarmu ta fada iftilain soyayya “kasa hannu mu san abunyi akan lamarin tanwer , rayuwar diyarmu is very very important agurinmu , kayi hakuri bazan juri ganin mutuwar tanwer ba gara na mutu na barta.
Dady dake zaune yana kallonta da karanta yanayinta ya numfasa yace “ karna sake jin kin zo min da makamanciyar magana irin wannan .“ka duba irin damuwar da zan shiga idan na rasata “kin dade baki shiga damuwa ba indai akan tanwer da wannan tsinannan yaron ne ya fada a matukar fusace cikin muryar kuka tace “tanwer ta tabbatar min da zamu iya rasata akanshi “wallahi zainba dana aurawa dan fashi diyata gara na barta ta jaraba mutuwa ,bari na fada miki wani abu tanwer ta fada miki haka ne dan ki amince ta auresa amman ko kadan bazata taba gwada mutuwa ba , da ta daukemu da mahimmanci a rayuwarta da tabi umarninmu don haka muma yana da kyau muyi duk yadda zamuyi ta ciresa azuciyarta batare da mun cika mata burinta ba ,Ko kuma ta zaba ko mu ko shi amman muddin ina raye bazan amince da wannnan auren ba idan ke mahaukaciya ce nida hankalina idan kuma taji ta gani lallai sai shi ki barta ta mutu mu huta”.A firgice mumy ta tsura masa ido tana kallonsa tace “yanzu kana ganin wannan maganar daka fada babu wani gyara a ciki?taya zamu haifi yarinya da cikinmu ace kuma mu barta ta mutu ?kafin ta karasa maganar har dady ya mike ya fita daga dakin...fashewa tai da kuka …

*****
A hankali anas ke taku acikin haraban gidan jaguwa dake magodo hannunsa rike da goran band energy drink yayinda kamil ke gefensa "shikenan nan aikin da muka fita jiya dominsa ya rushe?"
"Bakaga uban gayyan baya cikin haiyacinsa ba inji cewar anas ?
kamil ya numfasa kana ya cigaba da magana "yanzu yana ina dan tun safe ban sanyashi acikin kwayar idanuna ba?"ya tafi zuwa hospital duba lafiyarta anas ya bashi amsa tare da kai goran bang bakinsa ya kurba yana lumshe idanunshi .
kamil yaja ya tsaya yaki cigaba da tafiya yana dan dukan kafadan anas shima anas din tsayawa yayi yana dubansa "naji ance kaima ka fara batun ajiya iyali ga kuma jaguwa shima da alamun zai auri yarinyar nan zakuyi aure ku barmu abaya muna yawon akan titi ?".
"Kuma kuyi kokari ku ajiya dayawa masu irin alqallarmu suna da iyali wasu kuma basu dashi basa ma son su ajiye saboda yanayin kasar dake tattare da tashin hankali zasu iya riskar kansu a hannun hukuma amman ni dai gsky zan yi aure ban san dalili ba hakan nan nake jin araina gara nayi aure shiyasa ma kaga na rage wasu abubuwa ".
"A ina ka samo matar ne ?"
"Kuma yarinyar tana sonka?"kamil yayi masa tamvayar ajere yana tsaresa da idanunsa murmushi anas yayi masa sannan ya cilar da goran hannunsa ya dafa kafadan kamil "anan garin kuma yarinyar tana sona sosai nima ina sonta ina jiran jaguwa ne idan ya gama ruwan idonsa sai ayi magana domin ina son muyi aure rana daya ."ya karasa maganar yana dariyar karyar da yayi masa .”
kamil ya masa gyada "duk kun zama yan soyayya dai shima jaguwa na lura yana qaunar yarinyar nan sosai ka gansa lokacin da tayi accendent ya dauketa kmr jinjira yasata a mota yana kuka ya kaita hospital sannan yaki barinta yana tare daita har dare har sai da iyayenta suka zo gashi tun sassafe ya sake fita zuwa gurinta "wannan shi ake kira soyayya sai dai shi yallabai din bai yarda yana cikin soyayya ba da aka tsareshi zai ce maka ba soyayya bace tausayi ne ".lallai kuwa ai duk inda tausayi yake soyayya tana makale daita a natse suka cigaba da takawa har zuwa cikin babban parlour gidan .


Tsaye yake sanye da riga dark blue da wondo ash colour hannunsa rike da fari glass cup yayinda anas ,kamil ,jubi jabir ke zaune ,shiru jaguwa yana kurban coffee a hankali yana tunanin tanwer kamil ya mike tsaye sanye da

Please Login or Register in order to submit comment