Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani tuggu zai sake had'a  mata ba  Ina tausayinta Ina Jin kamar zai cutar daita ne Idan na mayar daita  ",saboda zunzurutun qaunar da kake  mata  ba  shiyasa kake Jin tausayinta ",oh my god jubril wai ya kuke min haka ne ?"idan Ina son yarinyar nan wallahi zan fad'a muku dan bamu Saba boyewa juna komai ba , ku yarda bana son yarinyar nan " shiru sukayi  suka cigaba da kallonsa  ba dan sun yarda dashi ba  har ya juya  ya kusan kofar fitar  sannan yace " eku   Scorpio  "zaman munafurcin  me kukeyi  dan Allah ku tashe kuje kuyi abinda na sakaku bamu da lokaci "  da sauri suka mike suna shafa kansu  ."

       
Cikin  takun  Isa  da Jin shi wani ne  ya nufi  haraban   gidan  hannunsa d'aya soke  cikin  aljihun  wandonsa   eku da Scorpio   suka  fice da  sauri  suka nufi Inda  ya aikesu , yana  nan tsaye yaga fitowar   tanweer   tana  karewa haraban   gidan   kallo  fuskarta d'auke da   murmushin  jin dadi ba kamar   d'azu   ba ,  a kallon   da  yake   mata    ya   lura   hankalinta   na   kan   shukokin     gidan    ne  ,yana  kallonta  ta   cigaba    da    takawa    a hankali   har   ta  Isa   Inda   shukokin suke  tana  shafawa   a hankali  tana lumshe idanu , a  natse   ta  karya  kwana  tabi hannunta  na   hagu  ,cike  da natsuwa ya biyo bayanta , bata tsaya koina ba sai  gurin   fararen   fure  dake shuke   cikin  ruwa  har  lokacin  fuskarta da murmushi , ya  k'araso  ya  tsaya  a bayanta   yana  sauke numfashi, saukar  numfashinsa  yasa ta juyo  a  tsorace  har qirjinta na ta'ba  nashi  saurin  d'auke numfashi yayi qirjinsa  na tsananta  bugu ,  ganin  shine  tsaye  yasa  ta sauke  naunauyen  ajiyar zuciya  sannan  ta juya ta cigaba da kallon fararen  fure  muryarta a sanyaye  tace " ina son fararen fure ko zaka tsinko  min? ta fad'a tana duban Inda yake  tsaye  har lokacin  hannunsa na  soke cikin aljihunsa " kina son fure ne haka ? ya tmbyeta  yana  kare  mata kallo  tsab " sosai Ina qaunar fararen  fure arayuwata  ya  qara taku biyu  yayi kusa  daita sosai yana cewa   "yarinyar da nake so itama  tana matukar son fure " qirjinta ne yayi wani irin bugawa da karfi , taji saukar maganarsa  kamar  saukar aradu ,zafi ta dinga ji a qirjinta tamkar ana diga mata ruwan dalma  nan take ta nemi natsuwarta ta rasa    idanunta na kan furen tace "wacece ita yarinyar da kake so ? ta tambayesa  kwayar idanunta cikin nashi ,bai  bata  amsa  ba duk da ya lura da canzawar da tayi a lokaci  daya  sakamakon  jin yana son wata  dariya taso  subuce  masa dan  yadda  ta had'e rai abun babu sauki kace shi din mijinta ne .

ranta a  'bace ta soma tafiya zuwa wani  bangaren "ke   Ina   zaki  ?itama banza  tayi masa kamar yadda yayi mata  "ba dake nake magana ba kina jina ? still banza ta masa " ki   koma  ciki  kar  na   sake  ganin  kafafunki  kin fito  haraban  gidan nan bare nan. "dan   me  yasa bazan fito ba ? ta fad'a a fusace  tana Jin wani irin zafi mara misaltuwa sannan   ta juyo ta fuskancesa  fuskarta a had'e tamakr ba itace take murmushi a sakwanin da suka wuce  ba , ta rasa dalilin wannan so da take masa  , soyayyarsa me  karfi ce  agareta  ,bata ta'ba sanin  tana  da  kishin irin haka ba sai yanzu daya  furta  yana  son wata ba ita ba  yace baya son zahra sannan baya sonta to wacece wannan daya furta da bakinsa ?   Ido  cikin Ido suke kallon cikin kwayar idanun  juna  kamar ta rufesa da duka ko zata samu sausauci ,k'okarin danne kishin tayi ta sanyawa jikinta  jarumta   "ko bazanje koina ba ka barni na dinga  fitowa Ina ganin fararen  fure tayi mgnr kmr zatayi kuka ,bai ce mata Komai ba   ya riko tsintsiyar hannunta ya soma tafiya daita bai tsaya a koina ba sai d'akinta ya bud'e kofar ya turata "iya nan na yarda kiyi rayuwa aciki ko falon gidan nan ban yarda ki fito  ba  idan Kuma kikayi kuskuren fitowa zaki  ga abinda zan miki ya k'arasa maganar tare da  ya janye kofar ya rufe garam , ita duk wannan abun  da yayi  bai dameta ba akan zance budurwa da  yayi  mata shi yafi komai ta'ba zuciyarta  da d'aga mata hankali, tsaki taja yafi sau goma ajere  " Allah! Allah !! ka tsi ...." shiru tayi ta kasa tsine masa shi da budurwar da yake so  ta koma karshen gado ta zauna tare da zuba  tagumi  ."

ya  shiga d'akinsa  ya cire kayan jikinsa ya shiga  wanka ya tsaya  shiru cikin bathtube ruwa na tsiyaya a sansar jikinsa  yana tunanin maganar abokansa  akan yarinyar "duk suna min kallon d'an soyayya alhalin ba haka bane acikin zuciyarsa ," taimako ai  ba soyayya ce?  ya tambayi kanshi  ya  d'an dade ruwa na sauka ajikinsa sannan ya fito kugunsa d'aure da farin towel wanda bai wuce cinyoyarsa ba   byn ya goge jikinsa
ya shafa body lotion yayi cumb din sumar kanshi ya soma shirya kansa cikin Kanana kaya  riga blue wanda a gabansa  aka rubuta  polo  1967  yayinda wondon  da canvers din kafafunsa suka kasance ja ,kansa sanye da facing cap ja kmr yadda rigar jikinsa  yake , tsintsiyar hannunsa  d'aure da agogon  rolex   ya rufe idanunshi da  glass baki  ya feshe ilahirin jikinsa da turare mai sanyi kamshi, sosai  kyawunsa ya bayyana ya soke hannunsa daya cikin aljihun wandonsa kamar Koda yaushe ya nufi kofar fita,  falon ya dawo Inda ya iske scopio ya dawo bai tsaya bata lokaci ba ya karbi farar ledar hannunsa ya juya zuwa d'akin da tanweer  take ."

 tana Jin shigowarsa amman  taki  d'agowa daga kwance da take  dan wani irin haushinsa take ji ,ya ajiye ledar akan bedside yana cewa  "ga abinci nan ki tashi kici sannan zanje  wani aiki me mahimmanci  zan dan dade kafin na dawo batare data d'ago ba tace "a dawo Lafiya amman dan Allah ka bani waya ". "ki  daina  damun kanki ba waya ba gidan ma zaki bari gbdy  idan lokaci yayi  ya juya ya fara tafiya  cikin hanzarin wannan karon d'akin dake gefen  d'akinsa ya shiga ya jima sosai dan kusan awa d'aya  yayi sautin muryar scopio ya fito dashi "boss komai ya kammala "okay kana iya tafiya   ya fad'a d'akin tanweer  yana cewa "   nasa a kawo  komai na kayan abinci muje kiga kitchen  din ". banza tayi masa taki cewa komai hakazalika taki tashi hatta abincin da ya kawo bata ci ba   ya zuba mata Ido har kusan minti biyar  kome ta tuna tayi zumbur ta mike tsaye tana dubansa  yayi gaba ta biyosa a baya har cikin had'ad'd'en kitchen din ."

a hankali ya dinga nuna mata komai daki daki kitchen  din  very Niet  kamar mace ce ke amfani dashi  babu abinda babu na kayan abinci  komai gashin nan  ajiye   yasa  an  kawo," ki duba ko akwai abinda bai miki ba a canza akawo miki wanda kike so ".  idanunta  da suka canza kala sukayi jazir  tsabar kishi ta d'ago ta sauke su akan fuskar  jaguwa dake tsaye a gabanta  yana kare mata kallo ,Shep dinta yafi komai daukar hankalinsa irin  matan nan ne masu  shep din cocakola   "dan tani da baka tanadin wad'an nan abubuwa ba dan ba sune abinda nafi bukata ba bukatata na .." ".shiiiii ya d'aura yatsansa akan lips dinta yayi kusa kusa daita har suna iya jiyo numfashin juna wani irin tsalle zuciyoyinsu yayi  wanda har sai da hakan ya haifar musu da tsayuwar numfashi , take jikinta ya soma kyarma   rungumeta   ajikinsa  yayi tsam yana busa mata numfashinsa .
 tuni zuciyarta ta karye hawayen kishinsa da kewar gida   ya soma zuba bisa kuncinta ya rungumeta  sosai ajikinsa kamar zai mata numfashi yana shafa gadon bayanta .

wani irin haushi  ne  da bata ta'ba  jin irinsa  ba  ya diran mata a kahon zuciya  ,kullum yana ikararin baya sonta amman ya iya nesanta kanshi daita yana son maidata yar  iskar karfi da  yaji   ta soma mutsu mutsun kwatar  jikinta domin zuwa wannan lokacin   zuciyarta  ban da zafin  kishinsa babu komai aciki ,ganin yaki sakinta yasa ta soma dukan qirjinsa da iyakacin  karfinta amman yaki sakinta  ya kamkameta tsam  yana son yaga karshen karfinta   "Kai dai wallahi mugu ne Kuma azalumi inshallahu yadda kake quntata min wallahi Kai ma sai Allah ya  quntatawa  kannenka ".  cak  ya saketa   yana furzar da numfashin mai zafi  daga bakinsa   idan  akwai abinda ya tsana bai wuce a ta'ba kannensa ko aibantasu da mugun abu ba . ta zube kasa bisa gwiwowinta tana wani irin kuka tare da Kiran sunan iyayenta , muryarsa  a tsarke yace"tan ...."bata d'ago  ta kallesa ba "karki sake sako kannena cikin shirmenki   idan kina son ki zageni kiyi amman kannena karki sake ."
"Dan Allah malam ka min shiru daga yanzu  muddin  baka maidani ga iyayena ba  wallahi na dinga ma kannenka  mugayen fata kenan , ada na dauka ka taimakeni  ne sai dai a yanzu taunina ya  Kashi dabam dabam tare da tambayoyi masu wuyar amsawa "waye Kai Adnan ? Ka fad'a min waye Kai Ina son sani kai din  waye ?cikin sauri ya juya ya bar kitchen din   zuciyarsa na rawa bai ta'ba Jin tsoron wani yasan sana'arsa ba ko sanin ko shi waye  sai yau , bazai iya sheida mata shi din waye ba , zai barta a matsayinsa na me taimakonta  bazai ta'ba yarda tasan ko shi waye ba yana tafiya yana jan tsaki ji yake kmr zuciyarsa zata buga .
ya rufe kofar falon ya fita zuwa  haraban gidan , tuni su  kamil ,anas, jubi, da jabir  da sauran yaransa sun hallara har wasu ma sun shiga mota sun zauna  shi kadai suke jira yana daf da karasowa eku ya  bud'e masa gidan baya ya shiga yana  cewa "hope  kowannenku  yayi shiri  me  kyau? "  sosai  suka bashi amsa  motarsu na kokarin fita daga gidan Idanunsa  ya sauka  akan wani dattijo  zaune a gindin bishiyar dake gefen gidansa nan take yace wa eku "stop ! ".eku  ya tsaya   nan take mutumin ya mike tsaye yana kallon motocin  jaguwa masu shegen kyau da  daukar hankali da hannu ya yafito  me gadi  ya k'araso  da d'an saurinsa  ya   tsaya yana rusunwa  "wacan mutumin fa me yake yi  anan ? "wallahi oga gurinka yazo wai yana son ganinka tun jiya byn fitarka yazo nace baka nan shine dazu byn dawowarka sai gashi ya dawo  na  shiga domin nasar maka sky  yace Kuna meeting shine na dawo na sheida masa ya dawo Koda karshen sati ne amman yace lallai sai ya ganka ."

shiru  jaguwa yayi  yana nazari sannan ya dan Kalli Inda dattijon  mutumin yake tsaye cikin kod'ad'un kaya marasa fasali  yana cigaba da nazarinsa ,a hankali ya fito ya soma tafiya   har ya k'araso garesa , dattijon na ganinsa ya shiga rawar jikin "barka da fitowa ranka ya dade  "barkanmu  baba ya kwanan iyalin ?" Alhamdulillah duk muna Lafiya  ,
jaguwa ya kad'a Kai sannan yace  " baba fatan  dai lfy kake son ganina ?"dattijon ya marairaice murya  kmr zai yi kuka sannan ya fara mgn muryarsa na rawa gwanin tausayi "daman matsalace ke tafe dani gareka a wajen mutane na samu labarin irin taimakon da kake yiwa mutane ".  jaguwa na jin haka ya sauke numfashi yana dubansa a tsanake  " Ina Jinka baba wacce irin matsalar ce ?"daman akan yarona ne  shekararsa biyar kenan da kammala karatunsa  na  degree sai dai  yadda kasar nan tamu ta  dawo yasa  har yanzu yake gida zaune, duk Inda yaje apply din aiki sai ace sai ya biya kamin dubu dari biyar kudin office kafin a daukeshi  gashi  bashi da hanyar da zai samu kudin,  ni ya kamata na biya  masa ya samun aikin  to ni din ma babu dan na abinci ma da kyar muke samu, dan Allah ka taimakeni kamar yadda Allah ya taimakeka  ka samo masa aiki ko Kuma  ka yarda ya kasance a karkashinka ya karasa maganar yana zubar da hawaye ."

jaguwa yayi shiru yana sauraronsa har sanda ya dasa aya "karkayi kuka baba    inshallahu zan yi iyakar kokarina  yanzu dai Ina kan hanya ne zani wani  aiki amman ka dawo zuwa  karshen sati da yaron   inshallahu matsalarka  tazo karshe dattijon ya soma k'okarin durkusawa jaguwa domin yi masa godiya, jaguwa  yay saurin sa duka hannuwansa ya taresa "haba baba karka min haka  mana " na gode  d'ana Allah ya albarkaci rayuwarka , Allah yasa ka gama da duniya lafiya ,Allah ya jikan iyayenka  idan sun rigamu gidan gsky, idan Kuma suna raye Allah ya Kara musu Lafiya mai amfani na gode na gode  daman da gaske ana samun mutane irinka  ?karka damu baba ya k'arasa maganar yana tsaida dattijon bisa kafafunsa ya Ciro  dubu goma  a  aljihun wandonsa ya mika masa "ga wannan kayi kudin  mota  yana gama mikasa ya juya ya shiga mota suka bawa motacinsu wuta suka bar unguwar ,da sauri dattijon ya Ciro  wata rubabbiyar   wayarsa ya shiga neman  number d'ansa  domin yi masa albishiri  ."

******

Bangaren  minister of health  kuwa  gbdy  hankalinsa yaki kwanciya   kullum yana manne da hjy zainab yana rarrashi wacce kuka ya zame mata abincin ruhinta , yanzu ma zaune yake kusa daita  yana aikin daya  saba tare da babban  amininsa alhj Tahir  dake k'okarin shawo kanta   "kada kiyi fushi  da hukuncin  Allah  zainab  wannan  abu daya faru gbdy bai mana dadi ba sai dai  bawa  baya wuce qaddararsa  Allah ya rigada ya  qaddaro surayya zata fad'a cikin wannan tashin hankali bamu Isa mu canza mata qaddararta ba,  fatan mu  dai Allah yasa bata cikin tsanani cikin muryar kuka tace "na kasa  jurewa   dady  dake hk take kiransa kmr yadda Ib ke kiransa "  yau  da mutuwa tanweer tayi na binneta da  zan fi samun natsuwar zuciya  amman Ina raye tanweer  tana hannun  'yan fashin da ko labarinsu ba'a samu ba , taya kuke tunanin hankalina zai kwanta ?".  Suma kiramu muji me suke  bukata daga garemu sunki  ta k'arasa maganar tana kallon saman falon hawaye masu zafin gaske na gangaro mata wanda zafinsu da rad'ad'insu ya wuce tunanin mai karatu .
"wannan haka ne  amman duk da haka  addua zamu  taru muyi allah ya bayyanata cikin koshin lfy "amen ta furta a kasan makoshi tana cewa ya jikin Ib kuwa?   kullum Ina sa ranar zanzo na dubasa   mutanen dake shige da fice agidan nan  zuwa jaje ke hanani  fita ammn inshallahu zan samu lokaci na  leko na dubashi  .
"to jikinsa dai da sauki zamu ce Allah dai ya iya mana  da iyawarsa dan rayuwar Ibrahim na daf da fuskantar matsala da Kuma qalubalin rayuwa ya kasa jurewa rashin tanweer  "Allah  sarki ib yana qaunar  tanweer  kmr yadda yake qaunar rayuwarsa  inshallahu zata dawo har ma suyi aure  ta k'arasa maganar tana sake matso ruwan  hawaye sun dade suna tautauna wa akarshe  minister ya  kira  cp  yaji halin da'a ake ciki  ,byn  cp   ya d'auki Kiran  suka gaisa "wai ya ake ciki ne da batun yarinyata  shirun fa yayi yawa zuciyata ta fara tsinkewa Ina Jin kamar Allah ya d'auki raina  na huta ? na kasa jurewa rashin diyata da rashin kwanciyar hankalin matata ".naunayen ajiyar zuciya cp  ya sauke sannan ya fara magana a natse"mun baza mutanen mu  cikin   gari    yanzu haka mun  fara  samun improvement akan lamarin   "to alhamdulillah   Allah ya taimaka   yasa aga  yarinyata  cikin koshin lfy "karka damu inshallahu komai yazo karshe ka kara mana lokaci kad'an "na gode na gode "  sukayi  sallama minister ya  fuskanci  hjy zainab tare da yi mata albashiri da abinda cp ya fad'a masa  nan take farinciki ya mamaye zuciyarta  shi kuwa alhj Tahir  cikinsa ne  ya duri ruwa gabansa ya  shiga  fad'uwa hankalinsa yayi kololuwar  tashi .
babu shiri yayi musu sallama   ya  shiga motarsa direbansa ya ja suka  kama hanyar zuwa gida ,yasan ya taro wa kanshi  match tunda yayi sanadin da'aka d'auke tanweer  wayarsa ya Ciro yanata  Kiran number jaguwa  ana ce masa akashe  take har ya k'araso gida bai samesa ba ,  ya rasa yadda zaiyi da rayuwarsa  yasan muddin  su jaguwa sukazo  hannu   kashinsa ya  bushe domin asirinsa ya tono ."

fitowa yayi da sauri daga cikin motar bai tsaya jiran direbansa ya fito ya bude masa ba  kmr zai tuntsura ya shiga cikin gidansa gumi na karyo masa ta koina a sansar jikinsa  kai tsaye bedroom dinsa ya shiga ya rage kayan jikinsa ya shiga zariya  yana neman mafuta , yana tsaye hjy baseera ta shigo tana binsa da kallon mamaki dan ta kwana biyu bata gansa cikin yanayi irin haka ba  "wai Lafiya ka shigo kamar wani kububuwa me km ya faru ? tsaki yaja   yace "babu  komai . "To daga Ina kake yanzu "?. daga  gidan minister nake ya bata amsa yana fifita da hannunsa dan wani irin  azababben zafi yake  ji ta koina    tana Jin  haka na gane komai   ta  kama  gabanta  zata fita ya d'auki remut din ac yana kokarin  qara karfinta tare da cewa  "ya kuma zaki wuce ki barni ga dan iska kin samu  kin tmbyeni na baki amsa kawai zaki juya ki kama gabanki  "oh to ni me  zanyi  maka ?"   zata sake magana ya d'aga mata hannu"jeki kawai bananason jin komai tunda babu abinda zakiyi shasha kawai  ya  fad'a a matukar fusace  yana juya mata baya.
tabe baki tayi a ranta tace  "ai Kai ne Sha Sha ,mutumin banza kawai  da bai san ciwon kanshi ba aurenka ko hasara duk a tunaninka ban San halin da kake ciki bane  byn na san komai  a juri zuwa rafi dai wata rana tulun zai fashe  juya tayi ta barshi tsaye  yaji da damuwarsa .ta nufi gurin  d'anta ta bashi maganin karfin jiki  dan ta sha alwashin bazata sake yarda da tsarin mijinta  ba   hk kawai  ta rasa tilon d'anta a banza, gbdy magungunan da yasa  nazifi ya rubuta masa an siyo sai dai bata bashi ya sha ba  wasu dabam ta bashi  jikin ne dai nashi yaki daidai saboda an rigada an karya masa garkuwar jiki " .

*******

Sannu a hankali motarsu  jaguwa   ta d'auki  titin airport  suna  gama  Isa kowace  mota  ta samu guri  ta  tsaya a Inda jaguwa  yayi  umarni tare da saka fuskokin roba , motar  da  jaguwa yake ciki  ne kawai  ta  Kai cikin  mutane sosai. shiru yayi yana nazari da karewa gurin  kallon da  tarin mutane dake bin mutane  ko suna bukatar canza kudi .facing cap dinsa ya cire ya juya ta baya ya cire glass din  dake manne da idanunshi ya makala a goshinsa   bayan kamar minti   talatin  ya  ciza lip's dinsa na kasa da karfi  ya  fito  rike da bindigarsa  ak 47  yana gama  fitowa  ya fara sakin  harbi kamar ruwa  domin  Kore  mutane dake safa da marwa agurin , kafin  kace me mutane sun rud'e tare da neman gurin 'buya  bayan kmr minti biyar sai ga anas shima  ya fito had'e da   harbi   nan  ma sauran  mutanen da  suka rage suka  tarwatse ya tsaya yana huci "iam  bally  the deadly one, mutun ya kama kanshi idan baya son ya bukunci lahira ."ya fad'a yana sauke numfashi .

jubi ya fito ya saita bindigarsa wani lungu Inda ya hango wasu mutane suna likensu  sai dai  bai  yi harbi ba bisa umarni  jaguwa dake duk suna Jin  maganarsa  sakamakon connecting din da yayi da wayoyinsu  ya sauke numfashi yana cewa  "as you can  see am gentle man to the core , I don't take what's beyond my capacity disprit  that iam not the one to be taking for granted , go and ask those how have done such before ya k'arasa maganar yana numfasawa  tare da gyara  tsayuwarsa eku remo ya k'araso ya tsaya gefen jaguwa rike da bindigarsa yana cewa ""Jaguwa ne da kanshi  d'an   mutuwa  Kuma mutuwa  ta dade da kar'basa  amatsayin d'anta  so everyone should run for his life "yana gama fad'ar haka ya koma gurin tsayuwarsa ya had'e da sauran  yan'uwansa suka tsaita bakin bindiga ."

Shiru jaguwa yayi ya  fuskanci office din da aka kwatanta masa jubi ya matso kusa dashi  yana cewa  " jaguwa let's move to his office  jaguwa yace "da alamun bai nan jikina ya bani  amman Kuma wannan lokacin anamdi ya bamu "to mu juya mana mu koma  girgiza masa Kai yayi yana ciza lips dinsa na kasa "to ko zamu shiga office office ne muyi operation  ?"no ya bashi amsa atakaice "okay ya fad'a yana gyara bindigarsa .gbdy gurin ya d'auki shiru  ciki kuwa har da jami'an tsaro dake aiki agurin kowa nason rayuwarsa dan da ganinsu an san ba kananun yan fashi bane ."

Loakaci zuwa lokaci yake duba agogo dake d'aure a tsintsiyar hannunsa Bayan  kamar minti talatin sai ga wata  mota   fara sol  ta  shigo  gurin. tun da suka shigo tsoro ya kama na cikin motar  sakamakon ganin gurin shiru babu motsin mutane  jaguwa ya gyra bluetooth din dake manne da kunnensa  "eku  ga mutumin da muka zo dominsa nan ya shigo  "okay   boss I will do my duty .cike da matsanacin tsoro   direban motar yaja burki yana k'okarin juyawa  sakamakon ganinsu take eku  ya harbi tayar motar .
tsayawar motar ke da wuya yaga  mutane sun zagaye motar  kamar almara sai ga jaguwa ya  bayyana a tsakiyarsu  direban yayi saurin kife kanshi akan stearing motar yana rawar jiki , jubi ya bude murfin site din baya Inda alhj  aminu ke zaune    ya fito dashi  yayi cilli dashi  gaban jaguwa ya tsaita kanshi da bakin bindiga  "where's the money jikin mutumin na rawa yace "it's inside the car ya fad'a yana nuna motar "cheek !  inji cewar jaguwa".Anas  da kamil suka nufi motar suka duba can byn  second biyu anas yace "comform it's there "okay fine ,move move kamil ya fad'a yana ture alhj aminu " face the grand if you do nonsense i will kill you ,nan take alhji aminu yay sujjada gbdy ilahirin jikinsa na kyarma .

Suka jefa jakar kudin byn motarsu  jaguwa ya shiga byn mota sauran dake shirin shiga  sai ga jiniyar motacin police suna harbi ,ai nan take qarar  harbi ya karad'e gurin police na harbi Suma suna yi  kowa ya shiga mota har sun fara ja  ya saura  kamil  ne bai samu damar shiga ba  ya biyo motar aguje yayinda sauran yan'
uwansa ke harbin yansanda suna Kiran sunansa "km run kayi gudu mana  suna miko masa hannu shi kuwa gudu yake da iyakar karfinsa yana k'okarin Isa ga motar gabad'aya suka mika masa hannuwansu suka  had'a baki "zo kamil zo  gamu maza mana kamil ka kara  gudu  suka fad'a hankalinsu a tashe .ganin   halin da ake ciki  yasa  hankalin jaguwa yayi matukar tashi nan fa ya shiga bud'ewa police wuta daf da kamil zai shiga mota wani police yayi nasarar harbinsa a kafa wata razananniyar qara ya saki ya durkushe kasa cikin azaban ciwo tare da rike kafarsa  "...

Mmn sudas


💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

 WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686 alert  domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu  a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️14

.....Cike   da  zafin  rai  da zafin  zuciya  jaguwa   ya  soma   k'okarin   fitowa daga  cikin  motar  yana gyara   bindigar   hannunsa   nan  fa hankalinsu   anas  yayi  kololuwar   tashi , anas  ya rud'e    yay   saurin dakatar  dashi  ta hanyar Kai   hannunsa  qirjinsa  "karka   fita  jaguwa , kaucewa  yayi  yana cewa    "ku   wuce  kawai   zanji   da  komai "dan  Allah   jaguwa  karkayi wannan  kasadar ".  bai  sake    saurararsa   ba ya  soma  harbi  gumi  na  karyo   masa  ,  hakan  yasa   da   sauri  kowannensu   ya  cigaba   harbi  da  iyakacin kwarewarsa ."
da  mugun   gudu   jaguwa  ya  isa inda  kamil   yake  durkushe  rike   da  kafarsa  yana  cewa "km    bani hannunka " ,  cikin  tsananin  tashi hankali   kamil  ya d'ago kai  sai dai bashi  da kuzarin da  zai mika masa hannunsa  " nace  ka bani hannunka ya  sake  mika  masa hannu  shima  kamil ya mika  masa  ya  rike 

Please Login or Register in order to submit comment