Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maganr daga bakinta ba akan just common criminal take data sanin aurensa ? to ma me yayi zafi akan gsky dan haka shima ransa ya qara baci sai dai bai ce daita komai ba dan yasan idan ya cigaba da magana babu mamaki a kokarinsa na ganin ta fahimcesa abun zai zamo rikici da zai kaisu ga jin zafin juna .”

“Idan ma baka bashi aurenta a matsayinsa na dan fashi ba ai ka bawa d’an wanda ya zamo shugaba agaresu?still shiru yayi yana kallonta da sauraronta “me ye bambamcinsu da Ibrahim ?akwai bamba ci sosai a tsakaninsu domin kuwa shi Ibrahim rayayye ne da’aka fitar daga cikin matacce dan shi ba gurbatacce bane ,shi din mutumin kirki ne kuma kema ki sani sai dai yanzu idanunki sun rufe akan cikar burin diyarki kiki fadar gsky ,idan Ibrahim ya zamo siriki agareki zakiyi Alfahari dashi da alfaharin hada zuria dashi ,shi fa wannan gurbataccen ? da wani ido zaki kalli kawaye da mutane gari dashi ?“Wannan tabo ne da har abada bazai gogu ba ,wallahi wannan abun kunya kike yi zainba ke da ya kamata mu hada karfi da karfi mu yake tanwer shine zaki goya mata baya dan kuga bayana to wallahi baku isa ba , kuma ba kece zakiyi da kinsanin aurena ba nine ya dace nayi danasani dana aureki kika zamo silar haifar min diyar da take kokarin kunnawa zuciyata wuta “. yana gama fadar haka ya fita fuuuuuuu ya bar mata dakin ..”

Fashewa tayi da kuka zuciyarta na zafi kamar zata fito waje ,a hankali ta mike ta fito ta nufi dakinta ta kwanta akan gado amman har karfe biyun dare mumy bata runtsa ba tana tunanin wulakamcin da dady yayi mata gbdy damuwa tayi mata yawa but halin da Tanwer take ciki shine worst da yafi damunta dan tasan idan har dady yaki amincewa ta auri adnan zata iya rasa rayuwarta.”
Mumy tayi kuka har taji babu dadi duk sanda ta tuna bakaken maganganun minister sai sabon kuka ya kufce mata ,tana kwance tana matso ruwan hawaye daga cikin idanunta ya shigo dakin yyi kokarin tabata don ya rarrasheta ya kuma sake fahimtar daita illa abinda take son biyewa tan su aikata ta goce ya numfasa sannan ya hade hannunwansa guri daya ya fara magana “zainba ki yafe min maganganuna nayi kuskure amman lokaci yayi daya dace ki fahimceni nasan kina da right akan tanwer amman ta wannan bangaren sam bai dace ki goya mata ba da wannan hadin ba ,wallahi babban ciwo ne atare damu ,duk yadda dady yaso mumy ta fahimcesa amman ina hakan bai samu ba dan kuwa bata sauraresa ba sai ma wani mugun kallo take masa cike da tsana da bacin rai “me kuma zaka fada min nida ba uwar arziki bace ?har kana dauting ina da hankali bare aje batun hangen nesa ,ni da bani da cikakkiyar hankalin da ciwo acikin kwalkwaluwata ta yaya kake son na fahimceka yanzu ?.Yayi shiru yana cigaba da dubanta domin yasan wadan nan maganganun sun fi sauran tsaya mata arai da mata ciwo “am sorry zainab kiyi hakuri amman duk kece sila kina tunanin wani abu zai samu tanwer ne akan rashin aurensa ? “ wallahi babu abinda zai sameta idan ta gaji da kanta zata ma kanta nasiha ta hakura dashi .”

“Ba abinda zaka ce min insaurareka ko in fahimceka tun tuni ya kamata na fahimci cewar yanzu kai baka damu damu ba sai kanka da Ibrahim kake tunani,ka daina damuwa dani da diyata tun randa adnan ya shigo rayuwar tanwer yanzu baka damu da rayuwar kowa ba baka damu da farincikinmu ba ,baka damu da lafiyarmu ba sai kanka data Ibrahim , yarinya tana fama da ciwo acikin zuciyarta amman baka damu ka tausaya mata ka nemo mata magani ba bayan duk kai ne silar faruwar komai ka shuka abinda sakaya ta koma kanta bata ji bata gani ba , alhj tahir yaci amanarka amman duk da haka ka lashi takobin sai ka hada zuria dashi mutumin da yana nan baa nemeshi an rasa ba da zai iya kawo karshen numfashinka at any moment tunda ya iya turo maka yan fashi ai komai ma zai iya yi yaga bayanka,wallahi abubakar kaci amanarta da diyar cikinka …”
“Ki fahimceni zainab Ibrahim dabam mahaifinsa dabam idan kuma kema bakya son Ibrahim ki fad’a mata ta kawo min wani amman banda wannnan mutumin dan …”nima bance Ibrahim bashi da karki ba yana da daidai nashi amman ka duba ciwon da diyarmu take dauke dashi tanwer na dauke da ciwon soyayya wanda at any moment zata iya rasa ranta nidai tunda tace bata so Ibrahim ga wanda take so mu bata mu taimaka mu sa hannuwanmu
mu janyosa jikinmu mu inganta rayuwarsa ya bar sanaar “kina ganin idan shi ya bari sauran abokan sana’arsa zasu bari ne ko kuwa dukkanin su zamu taru mu inganta rayuwarsu dan son rai irin naki?
“Nice ma nake da son rai ?
“Kwarai kuwa zainba kina dashi ke nifa na soma tunanin ba kece kika haifi tanwer ba ina bukatar gwada jinina da nata domin na tabbatar da cewar tanwer diyata ce wacce na diga ko kuma akasin haka kawo min ita a matsayin diyata ban sani ba .”ya karasa maganar a fusace yana dafe goshinsa daya ji yayi masa mugun sara da karfi ,a matukar firgice take kallonsa kafin daga bisani ta fara magana cikin zafin rai da zuciya “gsky ne tunaninka yayi daidai , tanwer ba diyarka bace nima ba diya bace kaga sai ka daina takamar banza akan diyar da bata ka ba ,
kuma kasa ido ka gani zan tsaya mata ta auri adnan inshaallahu kuma zai zama mutun kirki har ma kayi alfahari dashi wata rana.”

jikinsa da hannunsa rawa suka kama ya kasa cigaba da tsayuwa adakin ya fito waje yana kai kawo tausayinkansa dana matarsa dana diyarsa ya kamashi ya kife kansa a bangon falon yana kuka yayinda yake ganin laifinsa ne domin dai yasan shine silar komai shine ya kawo alhj tahir gidansa da har yasan sirrinsa , sannna alhji tahir shine silar da dan fashi ya dasa mugun ciwo azuciyar diyarsa har adalilin haka ake shegenta masa diya ,ya sake fashewa da wani kuka “ya allah kawowa tanwer saukin abinda take ji akan yaron nan ,tanwer ko ba diyar cikina bace ta zama tawa har abada bazan iya rabuwa daita ba bare ma nasan karya ne babu wanda zai kalli yatsun kafafunta yace masa ba diyarsa bace fuska da tsarin jiki ne kawai na mahaifiyarta amman hatta hakoranta irin nashi ne .”
Ranar dai a gidan minister babu wanda ya runtsa daga mumy har dady da tanwer.”

Washegari gidan ya kasance tamkar anyi mutuwa babu wani jin dadi gabdayansu suna daki ,ruky ce kawai ke kai kawo a tsakanin masu aiki ,ta shiga dakin mumy bakinta dauke da sallama yayinda hannunta ke rike da flaks din abincinta ,ta ajiye akan center table ta karaso ta tsaya gabanta “sannu mumy ga abincikinki dan allah ki daure kici wani abu “.kai kawai ta daga mata sannan ruky ta fito ta shiga dakin tanwer ita kanta ta shiga damuwa sosai sakamakon ganin yanayin mumy “sister karki damu inshaallahu komai zai daidaita amman karki yarda ki bata da iyayenki akan wani nmj can wanda zai iya juya miki baya .” tana zaune a dakin tanwee tana kwantar mata da hankali dady ya shigo dakin bakinsa dauke da sallama ya tsaya akan tanwer rukayya ta gaishesa ya amsa mata sannan ta fita ya kalli tanwer ya girgiza kai ita kanta tanwer din sai data sha jinin jikinta da irin kallon da yake mata sai daya numfasa sannan yace “Shikenan tanwer kin hadani fada da matata ? ta girgiza masa kai alamun”a’a !
“Wallahi da Kinsan tarihin haduwarmu da zainba har zuwa lokacin da muka sameki da bakiyi abinda zai kawo tashin hankali a tsakaninmu da zainab ba ,bamu taba samun matsala da zainba sai akanki ya fada yana furzar da iska sannan ya cigaba da magana na fada mata ta fada miki idan baki son Ibrahim ki kawo min wani zan baki shi amman banda wannan dan Iskan yaron ai tana jin haka “tasa masa kuka da karfin gaske “dady ya zanyi wallahi bani da karfin zuciyar da ina da karfin zuciya da zan iya kawar da komai a zuciyata na hakura dashi “
“Dan allah ki ka min dan iskan baki wallhi matsawar kika auri yaron nan tanwer babu ni babu ke sai dai ki nemi wani uban bani ba, “to ai dady bana halaka da kowa bare batun soyayya ko Ibrahim ma ni a mutunci na daukesa daga baya kamai ya sauya ni adnan kawai nake so bayan shi bazan iya rayuwa da kowani nmj ba , da dashi na yarda na amince in zauna in mutu a gidansa sai dai bazan só naga kun samu sabani a tsakaninku ba “ karki ce bakya son mu samu sabani mana kina so dan gashi kin janyo uwar ki tana jin haushina bayan bamu taba samun sabani daita ba sai akanki “ina sonku iyayena bazan so naga kun samu sabani akaina ba kune farincikina kune garkuwa,bangon jingina agareni ,wallahi ina sonku domin kunyi matuqar kokari akan kuga tarbiyyarta ta gyaru wallahi dady nasani ban maka adalci ba amman ban san yadda zanyi bane dady ka min addua ko zan daina jin abinda nake ji akansa ta karasa mgnr tana fashewa da kuka “wallahi da akwai abinda zanyi na daina son shi dady zanyi dan nima na gaji da wannan wahalar sai kuma jikin dady yayi sanyi , jiki a sanyaye ya fito daga dakin dan bazai iya jurar ganinta tana kuka ba ya shiga dakin mumy tana zaune ya karaso ya bude kular abincin daaka kawo mata bata ci ba ya kalleta ta kawar da kai alamun bata son ganinsa ya kai hannu ya shafa gefen fuskarta “kiyi hakuri uwar gidana na fahimci halin da kike ciki ,na fahimci son da kikewa diyarmu ne yasa kike son biye mata amman kisani baa rayuwar aure a haka zainba wallahi aurawa tanwer yaron nan bashine karshen matsalarmu ba .”

“ kiyi hakuri banason ganin tanwer cikin wahala ne duk abinda zai sameta dole ya sameni nan hawaye ya soma gangaro mata ba kakkautawa murya kasa kasa tace “kayi musu fatan alkhairi babu abinda ya gagari allah wannan auren idan ba alkhairi bane allah ya dakatar dashi idan kuma alkhairi ne fa ?
”inshaallahu ma bazai tabbata ba kawai ni abinda nake so dake ki tsaya a bazaa yi ba, Kiyi min wannan alkwarin “gaskiya bazanyi ba tana gama fadar haka ta mike ta dauki wayarta ta fito ta bar masa dakin babu kowa a falon sai tv dake aiki da ac ta soma tafiya a hankali tana karewa falon kallo har ta isa kofar dakin dake kallon nata wanda suke saukar baki ciki ta soma neman layin uncle bashir kira daya ya dauka cike da girmamawa tace ya hau online haka ma uncle jamil shi daman soja kullum yana online da wahala ka hau baka sameshi ba conference ta hadasu a vedio call kowannensu yana kallon danuwansa “na kiraku ne akan matsalar tanwer da wannan yaron adnan ,bashir ina ganin lokaci yayi da zan dauki shawararka na amince tanwer ta aure shi amman kai jamil da Aliyu me kuka gani akai ?”nan take uncle jamil yace “minister ya yarda da hakan ne ? ta sauke numfashi da karfi “bai yarda ba gskiya.
Yayi min daidai gsky nima ban goyo baya ba kai yaya saboda me zaka bata wannan shawarar ?” Wannan ai abun kunya ne da torzarci gsky karki amince aunty sam sam wannan shawarar batay ba mu dai san yadda zamu nisanta tsakaninsu idan garin zaa mu bari daita zuwa wata kasar to adai san yadda zaayi.”
“Shikenan kai Aliyu fa me zaka ce ?
“Ni dai gsky na yarda ta auresa idan dai har adnan din dana sani ne lallai zai rike miki ita da gaskiya wallahi adnan din danasani me kirki ne dasanin yakamata…”kai dan allah malam ka rufewa mutane baki maganar riko akeyi ko sanin yakamata ?” ya katse shi ta hanyar fadar haka “ana magana ne akan sana’arsa duk kirkinsa tunda bashi da hali ai na banza ne “ni kaina banason auren nan jamil amman da ta dinga binsa suna aikata zina suna ciki ana cirewa me zai hana mu taimaka masa tunda muna da halin yin haka “ kayi hakuri kaji kanina nasani abun akwai ciwo amman ya zamuyi da qaddara?ta karasa maganar tana zubar da hawaye nan fa duk suka rude suka shiga rarrashinta “ban taba tsamanin rayuwarta zata dawo haka ba tanwer da kanta ke binsa kuma nasan da wahala su hadu wani abu bai shiga tsakaninsu ba ,nasan tanwer nasan yanayinta sai dai kawai na share dan yin maganar bashi da amfani sun dan dade suna tautaunawa a karshe dai dole jamil ya sadaukar ya hakura suka amince akan ta auresa wannan yasa mumy taji kwarin gwiwa suka sallama ta fito ta nufi dakin tnwer ta murda handle ta kusa cikin dakin alokacin tanwer tayi zurfi cikin tunani .”

ta zauna kusa daita tana shafa sumar kanta a dan firgice ta waigo suka hada ido daita mumy ta sakar mata murmushi itama tanwer murmushi ta sakar mata mai hade da kuka "na amince da zabinki tanweer ,na amince ki auri adnan kice masa ya turo iyayensa ..”tanweer tayi tsuru tana duban mumy tana jin mgnrta kmr a mafarki  kafin daga baya ta mintsini fatan jikinta  domin ta tabbatar da mafarki take ko kuwa gaske ne abinda taji mumy ta  fada .
"tunda kin amince kina son Adnan kice masa ya turo magabantansa suyi magana da mahaifinki karasa mgnr hawaye na zubawa daga kwarnin idanunta .”allah yasa yayi miki adalci tanwer amman kiyi min alkawari zaki yaki sanarsa kafin aurenku “nayi miki alkwari mumy .”
zuciyarta  tanweer sol da jin abinda mumy tace nan take ta sauko ta durkusa kasa gabanta  tana kwalla tace "na gode mumy Kuma Ina Kara baku hakuri dan Allah ku yafe min  Mumy ta share hawaye tana cewa  "ai ya wuce tanweer amman kibi a hankali banason ki Kara zuwa inda  yake  kice masa ya dinga zuwa , hawayen farinciki ta dinga zubawa muryarta a sanyaye tace “mumy dady ya amince ne ?
Naunayen ajiyar zuciya mumy ta sauke tare da cewa “eh yanzu nayi masa magana ya kuma amince tana gama fadar haka ta mike ta fita  .”
Tana fita tanweer ta soma neman layin jaguwa amman wayarsa bata shiga ,  dole ta hakura ta fito da gudu ta  nufi d'akin rukayya tana shiga ta kamo hannunwata duka cikin nata ta  fara juyi daita acikin d'akin tana cewa"yau dai naga amfani addua ruky mumy da dady sun amince na auri Adnan rukayya ta kamota ta zaunar  daita  "Kai amman na tayaki  murna Allah ya tabbatar da alkhairi rukayya tasan tanweer nason adnan sosai amman batasan dan fashi bane daga mahaifinta sai mahaifiyarta da kannenata da alhj Usman ne suka san da wannan maganar washegari da farinciki ta tashi ta tafi aiki hatta maaikatanta sun fahimci halin da take ciki na samun sukuni sai dai babu wanda yasan abinda ya jefata cikin farinciki a office dinta ma a qalla ta kusan minti talatin tana neman layinsa ko dan tayi masa albishiri amman bata samu ba haka har washegari numbersa kawai take kira but no answer a lokacin shi jaguwa yana kan wani aiki daman kuma idan yana kan aiki bai kunna wayoyinsa har  sai ya kammala abinda dake gabansa sannan ya kunna waya .”
*******

Karfe goma na safiya anas bai yi shirin fita ba kamar yadda ya saba sai kallon dayasa gaba yanayi sosai hankalinsa yana kan film din dan ko motsin kirki bayayi hally wacce ta fito ta zauna kusa dashi more than 30 minutes ta rasa mai yake gani aciki har ya dauki hankalinsa ta dai kara arawa kanta lokaci ta cigaba da zama tana bin katuwar flazma din da kallo tana karanta translation din tana fuskantar film din amman sam bata gano wata maana da zata saka mutun ya dauke hankalinsa kacokan akan film din ba .”
Ya dan gyara zamansa lokacin da yarinyar cikin film din ta fito daga cikin ruwa kayan jikinta sun manne ajikinta surarta ta bayyana sosai ta dan saci kallonsa cikin kunyar data shigeta na ganin wannan yarinyar wani murmushi tagani a fuskarshi ji tayi zuciyarta ta buga nan take ta hade rai “wai meye amfanin wannan kallon da kake ina ganin gara kayi abinda ya dace ?” .ya waigo ya kalleta ya kawar da kanshi yana karantar abinda ya bata mata rai ya dauki remut yayi rewarning ya dawo baya kadan daidai inda yarinyar ta fito daga ruwa ya tsaya ya cigaba da kalla har aka dauke gurin sannan ya dawo da idanunshi kanta bai damu da cikar da take tana batsewa ba dan daman da biyu ya sako film din ya cigaba da kallonsa ganin haka ta tashi tsam ta koma dakinta ta kwanta wani takaici ya ziyarceta damuwar da batayi zato akan anas ba ta dabaibayeta wannan shine kishi itama ta fuskanci hakan amman bata san hanyar da zata kawar da kishin nashi ba .”

Bata jima da kwanciya ba ta tashi da niyyar ta leka domin ganin ko har lokaci yana zaune a hankali ta bude kofar ta turo da kanta waje nan ta fara jiyo tahowarsa sosai suka hada ido dashi kuma tasan ya ganta da sauri ta koma cikin dakin shiru bai shigo ba kunya kuma sai ta hanata sake yunkurin fitowa amman a yanzu kunyarsa da take ji bazata kaita ga hanata kawo abinda zai kawo masa farincikiba .
Dan haka ta daure ta fito parlour alokacin ya gama kallon ya mike akan doguwar kujera da “alamun yau dai babu inda zashi domin ko wanka baiyi ba ta zauna kusa da kujerar da yake kwance ta dube shi anatse “amman dai yau babu inda zaka ?ta fada tana kallonsa kamar ba zai yi magana ba daga bisani ya dago kai “me kikagani? Ya dawo mata da tmbyr ta dan dauke kanta daga kallonsa saboda kasa jure hada ido dashi tace” aa kawai dai na ganka ne kwance baka da alamun fita “mai zai hanani fita tunda zaman gidan ba wani abu zai amfanar min dashi ba kiran yayanki kawai nake jira na kama gabana “.

Magana ya fada mata d’an haka ta maida kanta ga kallon kofa fuskarta ta sauya launi sai taji batayi masa tambayar abinda shima ya lura dashi kenan ya dai dan samata ido yana kallonta ganin ta juya tana kallonsa ya dauke idanu shi ya cigaba da yin shiru kamar mai bacci ta mike a hankali ta nufi kitchen dan rana ta fara shadaya da rabi tayi zuciyarta babu dadi duk abinda yayi mata bata bashi laifi ba kanta ta bawa domin kuwa ita ta masa laifi T unanin yadda zata shawo kanshi ta nuna mishi qaunar da yake muradi daga gareta itace halalinsa halaka malak dole yana da bukatarta, ita kanta zuwa yanzu tana da bukatarsa amman bata jin zata iya kai masa kanta bazata iya wannan rashin kunyar ba sai daga yanzu a shirye take duk lokacin dayazo zata faranta masa rai ta nuna masa itama tana kwadayinsa domin ta tabbatar hakan zai dawo masa da walwalarsa .”
da damuwarsa bata wuce nuna koinkuka da take masa ba har ta isa bakin barandar da zata kaita kitchen ta dan juyo ta dan saci kallon fuskarsa,
idanuwanshi tsaye kyam abayanta ita yake kallon ,suna hada ido ya kawar da kai cikin nuna rashin kallonta .
Ta tsaya tana kare masa kallo ta tuna maganarsa kuma ta gasgantashi laifinta kunya tabbas ba karya yayi ba dole akwai muradina a tattare dashi ya zama dole ta cire kunya da tsoro ta bashi hakinsa sai dai ita kunyar ba zata barta ta kai masa kanta ba koda kuwa rike hannunsa ne tayi murmushi ta fice ta shiga kitchen tana tunani rayuwarsu da suka gudanar , to abu ne duk an hada da yarinyata sai hakuri dan ita din duka shekarunta basu wuce sha bakwai ba dole daman a samu irin haka bugu da kari bata da waye wa irin na matan daya saba muamula dasu .
Tana tsaka da aiki taji alamun tsayuwar mutun ta juyo bayanta shi ta gani tsaye yana kallonta ta juya sosai ta kallesa sai taga ya shafa sumar kanshi tare da kiran sunanta “hally !
Ta amsa hade da bashi duka hankalinta tana tsamanin akwai abinda zai sanar mata ya tsura mata idanunshi yana kallonta “jikina yana bani kamar kina fushi dani ?
“Fushi kuma da kai da akai yi me zanyi fushi da kai ?ya dan tsotsa kai kawai ya juya tayi murmushi kafin yayi nisa tace “am mai kake son a girka maka ?bai juyo ba yace “komai ma .”
Ta dan yi turus amsar shi bata mata dadi ba dan tun da ta soma girki abinda yake so take girka masa ta share ta cigaba da aiki ta taliya ta zaba ta girka domin ta fahimci yafi sonta ta hada komai sannan ta fita dan bata d’an lokaci baya falon amman da zamanta bai fi minti uku ba sai gashi ya fito daga dakinsa tana son ta faranta masa rai amamn ta rasa ta ina zata fara da me ma zata fara wani abu yazo mata rai dan haka tayi hanzarin daidaita natsuwarta “tun dana tare ko sai daya banga an gyara dakinka ba ko baka bukatar a gyara maka ne ?
Ya dan dubi kofar dakin ya kawar da kai yace “shi dakin ne baya bukatar a gyara shi ba mai shi na amsar daya bata sam bata mata dadi ba amman kuma saboda me bai bata amsar data dace daita ba“?
“Ko me yasa dakin baya bukata ?
Saboda babu wani abu da akeyi ajikinsa komai daidai ne very nit .”
Ta rausayar masa da kwayar idanuwanta cikin tsigar harara tace “ to amman dai naki ko baa komai acikinsa bai kamata a wayi gari batare da an gyara shi ba “shi dai wannnan dakin baya bukata gyara ya fada cikin son abar maganar dan tunda ta nuna bata bukatarsa shima zai barta bazai dameta ba yadda ya share ya bar maganar haka itama ta share a ranta tace wannan dabarar bata yi ba uhm wane ma zatayi duk wanda ta dauko zatayi baya karbarta yadda ya kamata tsam ta mike ta koma kitchen ta sauke abinci ta shirya yadda ya kamata a food flaks ta fito dashi akan faranti ta ajiye shi a table ,duk da tasan ba yanzu zai bukata ba amman sai data tsokano magana “ga abinci fa har yayi .
Bai bata amsa ba jaguwa ya shigo sai dai ya zube akan kujera kamar bai ganta ba ya dauke kanshi suna gaisawa dashi ta mike ta koma dakinta ta dauko mayafi ta yafa tazo suka gaisa kallo daya yayi mata da amsa war ma ba a wadace ba, ganin haka taji gabanta ya fadi tasan ba haka ya saba mata ba duk yadda akayi tayi laifi tunda ba yau tasan shi ba shekara d shekaru tasan halinsa muddin ba wani laifi tayi ba bazai mata haka ba ko Ada can idan suna son su gane ammi ta fada masa sunyi laifi daga amsa gaisuwarsa suke fahimtar ta fad’a masa .
Hira ce ta barka a tsakninsu ita dai tana jinsu sai dai tabi duk wanda yayi magana da kallo gbdy ta rasa abinda tayiwa yayanta da yau yayi mata

Please Login or Register in order to submit comment