Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"to yanzu kana ganin idan an canza masa  za'a samu me karfin  na farko ?"sosai  kuwa  za'a samu  zan duba  me karfi  wanda yafi na farko  zuwa gobe  sai nazo   dashi  "to shikenan na gode son Allah yayi maka albarka ya Kai hannu ya zagaye kafad'an  nazifi yana tafiya dashi  acikin falonsa" ka cigaba da bin umarninna ni Kuma bazan gaji da tura maka   sakona ba "nazifi ya gyada masa Kai tare cewa "babu komai dady ai ko baka biyani ba ya zama dole nabi duk wani umarninka nasan kana da wata munafa me kyau akan ib  shiyasa kake bukatar ganinsa akwance  ?".

"yauwa  nazifi  a she kana da fahimta ?" shi yasa kullum  kake kara burgeni  saboda kaifin  baseerarka"  cike  da  girmamawa nazifi yayi sallama da alhj Tahir ya fito zuwa babban  falon gidan   Inda ya iske  hajiya baseera zaune kusa da Ibrahim  dake zaune akan wheelchair tana bashi  abinci a baki tausayinta dana Ibrahim ya kamashi ,mace har mace me tausayi  da biyayya  amman batayi  sa'ar miji ba  "har ka  fito nazifi ? "eh  mumy  na fito  "to sannu da kokari  Allah  yayi muku albarka  gbdy , yadda kake kula da abokinka  baka gajiya Allah ya kula da lamarinka  "Ameen mumy ai kula da ib ya zama dole ,  Ibrahim ya  dubesa  wuyansa a karye  magana yake son yiwa  amininsa   amman ya kasa furta Komai  so yake ya sheida masa Kiran daya samu daga bakin  alqali a kwanakin  da  suka  gabata  .

 sai  da nazifi ya sake duba jikin  Ibrahim sannan ya fito zuwa haraban gidan ya  shiga motarsa  ya zauna ya bata wuta,  tafiya kad'an yayi ya  gangara gefen titi yayi parking ya Kasa cire hannunwansa akan stearing motar   ya  shiga  kogin tunani ta yarda alhj Tahir  yake wa  dan lelensa wanda shi kad'ai ya haifa a duniya  mugunta.ji yake kamar ya tattara ib da komai nashi ya turasa zuwa kasar    england  domin ya samu kulawa daga manya  likitoci ,  dan  allurar da mahaifinsa  yake sa shi yayi  masa bata da maraba  da  poising   me karya garkuwar jiki gashi sanadiyyar haka an tsaida komai nashi  bayan shi din mutum ne mai qulafucin  akan aikinsa"gbdy  zuwa yanzu ya soma zargin manufar alhj Tahir akan d'ansa   Ibrahim, idan kuwa haka ne babu shakka akwai  lauje cikin nadi wato akwai saka hannun alhj Tahir  cikin kidnappin  din tanweer da yan fashi suka yi  .
"haka ne ma  zuciyarsa ta tabbatar masa da hakan , wannan dalilin yasa  alhj  Tahir baya son Ibrahim ya tashi  bisa kafafunsa ya nemi tanweer da karfin da iKon da Allah ya  bashi, tabbas Ibrahim nada gogewa da  jajircewa da qulafici   akan aikinsa da  duk wasu masu laifi a kasar nan.
" idan ya gangara ta bangaren aikin sirri shine kan  gaba   saboda kwarewarsa  ya iya  binciken sirri tamkar aljani  tare da abokan aikinsa  har su  gano me laifi  yanzu abinda zai yi zai    cigaba da boyewa alhj  tahir tare da biye masa har sanda zai kammala komai  akan  abinda yake zarginsa akanshi tare da nemo  sheidu  masu   karfi  ta yadda za'a samu nasarar  kamashi a sikwane , yana da tabbacin muddin aka kamashi za'a kama ragowar  abokan sana'ar tasa dukkaninsu su girbi abunda suka shuka ya kusan awa d'aya  agurin yana  saka da warwara har hawayen tausayin Ibrahim ya zubar saboda rashin dacen mahaifi da yayi   sannan ya tada motarsa zuwa office dinsa har ya  Isa office tunanin aminisa  yake .."

*******

Tanweer  bata  farka ba  sai gurin  karfe d'aya  na rana ta farka cike da matsanacin azaban ciwo  dan   ta sha  wahala sosai  jikinta na rawa koina ciwo yake mata sai numfashin wahala take fitarwa  , wani abu ya hadiye  sannan ya matso kusa daita  sosai  ta  bud'e idanunta  da suka mata nauyi ta ga shine zaune a kusa daita wani marayan kuka ta fashe dashi tana shesheka, muryarsa a kasalance yace "lafiya kike kuka me ya  sameki ? ya fad'i  haka ne dan ya sake tabbatar da tana sane da abinda ya faru a daren  jiya   duk da baya   doubt   akan  gaskiyar abinda baba  ya fad'a masa .ta fashe da wani sabon kuka tana cewa  "nima bansani ba amman duk ilahirin  jikina ciwo yake  min tunda nake ban ta'ba Jin irin wannan ciwon ba dan Allah ka taimakeni ka  maidani gida ....." ta k'arasa maganar  tana sheshekar kuka  bai sake  yin  magana ba ya ɗauketa cak ya nufi bayi daita  ya had'a  mata ruwan zafi ya Kai hannu zai  riko hannunta ta goce ya bita da wani kallo.
ta zabga masa harara tana hura masa hanci ,shiru yayi yana cigaba da  kallonta yayinda  kukanta yaki tsayawa   ganin    ko ya  rarrasheta 'bata   bakinsa zai yi yasa  a hankali ya Isa  Inda  take jingine acikin  bayin  ,batayi  expecting ba taji ya rungumeta  ajikinsa  tsam , ajiyar zuciya ta saki  ta had'e  rai sosai  .

rarrashinta yake son yi amman yasan halinta ba lallai ta bashi had'in Kai ba zata iya butsare masa  "tanweer ! ya kira sunanta muryarsa a sanyaye tana jinsa taki amsawa ta cigaba da kukanta "tanweer !" ya sake kiranta cike da rauni Yana shafa sumar kanta zuwa  gadon bayanta " Kince jikinki na ciwo ? ta gyada masa Kai  kawai " ki d'aure please  ki shiga ruwan zafi zaki daina jin ciwon  kinji "tayi  masa  banza tamkar ba da ita yake ba bare   ta  nuna  alamun zata yi abinda ya bukata ,a hankali  ta soma k'okarin kwace kanta daga jikinsa  har ta  zare  ta tsura masa idanunta fuskarta babu annuri   a kallon da take masa  taga goshinsa ya dan kubura ta Kai  hannunta ta shafa gurin  batare da tace masa  Komai ba duk da tmbyrsa bakinta yake son yi  amman ta kasa sarrafa harshenta , hannunta ya kamo cikin nashi ya matse gam   "ki  shiga ruwan zafi  zan gasa miki jiki ta yadda zaki daina jin ciwon komai ajikinki" girgiza  masa kai tayi  sannan ta motsa labbanta " ka fita  kawai  zanyi da kaina ba sai ka tsaya ba dan bazan iya tubewa agaban wani katon banza ba  ta  fad'a  Kai tsaye taja ka'fafunta  ta  jingina jikinta da bango bayin ."

 yayi  shiru kawai yana kallonta maganarta ta sosa masa rai sosai azahiri ake iya hango hakan  "idan Kuma bazaka fita ba bari ni na fita ta juya tana d'aga  ka'fafunta da kyar  ya nad'e hannun rigarsa ya kamo kafadarta bai tsaya wata wata ba ya d'auketa ya dannata cikin ruwan zafi wani qara ta saki mai sauti ta zabura zata mike ya sake  dannata  ta zaro idanuwanta gbdy  hawaye na zubo mata , kallon juna suke wanda ita nata kallon na fita haiyaci ne shi kuwa na mugunta ne  "muryarta a tsarke tace "Allah ya Isa ban yafe ba  mugu azalumin  kawai Allah ya Saka min nace maka zan gasa jikina dole  ne  da zaka wani  sundumani cikin ruwan zafi dan mu...." ? bata k'arasa mgnrta  ba ya dalle mata baki da yatsansa  "har yaushe zaki daina yiwa mutane  rashin kunya ?ya fad'a yana sake dannata cikin ruwan zafi  har sai da ta sake sakin qara me sauti tana cewa  " har sanda mahdi zai bayyana ta bashi  amsa da haka tana marairaice fuska .
tausayinta yaji yana  yawo a sansar jikinsa  shiyasa ya rabu daita dan inya biyewa rashin kunyarta komai zai iya faruwa a tsakaninsu   "ni ka barni haka zafi na ratsani dayawa "ta fada tana kallonsa "abinda kika fad'a nayi aiki dashi  "to ni me na fada ?ta tambayesa  muryarta cike da shagwa'ba tana turo  masa  karamin bakinta  "muryarsa can kasa yace "kince jikinki na ciwo har kasanki  ko ba haka ba ?tai masa banza tana bata fuska tare da d'aga kanta sama alamun tunanin tana son ta tuna  lokacin da tace masa  har da kasanta ke mata ciwo  ita dai tasan tace masa  jikinta "ko  zan iya sanin abinda yasa kike jin ciwon jiki da  kasanki? ya tambayeta  yana k'okarin zare rigar  jikinta , idanunta ta tsura masa tana kallonsa cike da mamaki  hannunsa ya Kai yana shafa bakinta kafin daga baya ya maida bakinsa ya fara kissing dinta in a romantic way tun tana turjewa har dai ta hakura ta barshi bayan ya gama romancing dinta ya zare hannuwansa   yana cewa "kiyi  wanka ki had'a dana tsarki ".

zaro Ido tayi waje cike da mamaki  tana maimaita  abinda yace a zuciyarta " ki maida wadan nan  idanun naki  kiyi abinda nace  yana gama fad'ar haka ya juya zai fita ya jiyo sautin muryarta tana cewa  "akan wani dalili zan had'a da wankan  tsarki ni ba janaba  ba ?"ya juyo a natse  yana kallonta tai saurin kare  qirjinta da hannuwanta , ya kwa'be baki yana kashe idonsa d'aya  a ransa yace" abinda na kwashe rabin dare Ina sarrafasu  shine dan  manufarci  kike wani  boyewa  ,numfashi ya furzar ya sake juyawa yana cewa"kiyi k'okari  kiyi wankan dana tsarki idan Kuma kin Isa karki yi zan gane "baza'a yi  ba , babu  janaba  ajikina  dan hk babu wani wankan tsarkin  da  zan yi  daf da zai bar d'akin yaji ta fad'i haka "kwa'be fuska yayi " yarinyar nan da alamun sai na baki tarbiya kafin na maidake  gidan ubanki  dan kanki na  mugun rawa."

d'akinsa ya koma ya shiga wanka sai daya d'auki minti ashirin yana bayi  sannan ya fito yana  goge jikinsa da karamin towel fari tasss yana tunanin  tanweer,  hakan nan  yake qara Jin qaunar yarinyar na mamaye  ilahirin jikinsa sai dai yayi ta k'okarin yakice hakan yana karyatawa , ya shirya kanshi cikin wasu  Kanana kaya wando da riga  farare  sol  ya feshe ilahirin jikinsa da turare , ya  zauna a bakin gadansa  ya d'auki d'aya  daga cikin wayoyinsa   ya kira number aliyu number  bai shiga  ba da alamun akwai matsalar  network ya mike tsaye ya fito yana neman layin eku kira d'aya ya d'auka tare da cewa "boss Ina yini  ?"Lafiya ya fad'a atakaice , yana tafiya yana  bashi umarnin  ya d'auki  kudi yaje adidas ya siyo  masa  abinci  ya k'arasa maganar yana  tura  kofar d'akin da tanweer take ,Koda ya shiga d'akin  tana kwance ta lullu'be jikinta da blanket  kanta ne kawai a waje tana rawa sanyi .
gashin kanta yabi da Kallo bai ga alamun ruwa ba  ya had'e fuska sosai ya k'arasa ya Kai hannunsa  cikin sumar kanta ya cusa har yana ta'ba fatan kanta  bai ji alamun ruwa  ba ya cire hannunsa  yana cewa  "ke........" !
ta d'ago kod'ad'un idanunta ta zuba masa batare data amsa ba " wasa nake dake Koni sa'anki ne ?to ni me nayi Kuma nifa wallahi bana son takura tunda Kai ba sa'ana  bane  ka mayar dani Inda ka d'aukoni mana "tayi maganar jikinta na karkarwa ta janyo blanket ta sake rufe jikinta har kanta a zuciye ya fixge bargon yayi filinging dashi yana jan tsaki  "ki tashi kije kiyi wankan  tsarkin da nace  ko na 'bata miki rai yanzu  "kamkame jikinta tayi guri d'aya  ta lafe akan katifa  bata da alamun tashi ."

wata razananniyar tsawa ya buga mata wanda yasa tayi  zumbur  ta mike tsaye har hantar cikinta na  kad'awa  ta kwa'be masa  fuska tana kallonsa, da yatsansa ya nuna mata hanyar bayi simi simi ta juya tana d'aga ka'fafunta da kyar dan kwata kwata bata ga al'amun wasa atattare dashi ba a yadda take kallonsa zai iya marinta har ma ya had'a da duka  yabi  tafiyarta  da kallo gbdy yanayin tafiyarta ta canza kallo d'aya me hankali zai mata ya fahimci halin da take ciki ,bai  d'auke  idanunshi ba har  sai daya shiga bayi ta bugo  kofar  da karfi .
numfashi ya sauke ya koma bakin   gado ya zauna yana neman layin amminsa suna waya ta fito d'aure da towel tana rawar sanyi   ya tashi ya rungumota  jikinsa ya zaunar  daita a gefensa  ta rakube  ajikinsa tana karkarwa  ya janyo blanket ya lullu'beta tare da yi mata alamar ta kama kanta waya yake  sun dade suna waya da amminsa tana sauransu  Kuma duk akan maganar  abinda za'a yiwa baqinsu masu zuwa neman auren shafiqa ne  acikin satin  ...
Lokacin da suka gama wayar tuni bacci ya  d'auke tan  ya kwantar daita  ya tashi ya d'auko mata wata rigar ya dawo har zai Saka mata ya tuna da magani dan haka ya  fita ko second biyu bai yi ba ya dawo rike da roba da gayen magariya yayi adduoi aciki  ya shafa mata sannan ya  Saka mata  kaya ya lullu'beta ya kashe  ac d'akin gbdy ya fita daga d'akin zuwa nashi  ya kwanta a falonsa akan  doguwar kujera."

Bai jima da kwanciya ba aka  soma  knocking kofar  falonsa , yana  daga kwance ya bawa mai yin knocking ɗin izinin shigowa eku  ne ya shigo cikin falon hanunsa  riƙe da farar leda, cike da girmamawa ya rusunawa  ogan nasa a natse Jaguwa ya mike zaune ya zura silifas ya amsa  ledar    yana masa  godiya  eku  ya juya ya  fice daga  falon.mikewa tsaye  yayi ya  fito ya shiga   ɗakin  tan batare da yayi knocking ba  kamar yadda  ya saba  koda yaushe zai shiga Kai tsaye ne , sai kawai ya tura  ƙofar  ya shiga ciki, tun sanda ya kawota  gidan yake jin   haushi Kansa da bautan da yake mata  amman a yau din jin zuciyarsa yake fessss  akanta zai iya mata komai ciki kuwa har da zama bawanta .
Tana kwance akan gado ta  kwanta  ruf da ciki, bacci ta keyi har lokacin  hankalinta a kwance,  murmushin gefen baki yayi   kamar tana ganinsa  haɗe da aje ledar  hannunsa" sarkin rigima da rashin kunya  ya fad'a a ransa , har ya juya zai fita daga ɗakin kuma sai ya tsaya yana  kallonta   tun daga yatsun kafaunta har zuwa  kanta komai nata abun burgewa ne ,   ahankali ya taka zuwa inda take kwance,  tafin kafansa d'aya  yasa ya ɗan  shafa  tsakiyar kafarta .
azabure ta farka ta zauna tana murza   idanunta dan  har lokacin Jan da sukayi  bai baje  ba , sake kallonta  yayi, "Ki tashi kije kiyi wanka kiyi alwala kiyi  sallah , ke fa na lura sallah bata dameki ba  dan  zaki iya  wuni  bakiyi sallah ba  ki kuma kwana bakya damuwa"  yayi mgnr yana mai  tsareta da sexy eye's dinsa."

Tsura masa idanunta tayi tana kallonsa  tana Jin haushin abinda yake mata sai ya fad'awa  mutun mgn yayi kmr bashi  yayi maganar ba, saboda yanda yake fizgo mgnr da kyar Kallon agogon d'akin tayi yanzu ne ma hud'u   ta wuce muryarta a raunane tace "gara ni ko banyi sallahr akan lokaci ba zan rama Kai fa ?meye amfanin sallahrka akan lokacin tunda kana aikata aikin  haram, wad'amuhu haramun ,washarabahu haramun wa guziya bil haramun wa'anna ....."ki min shiru anan  stupid  " ya fad'a a tsawace , ana tausayinki bakya tausayawa kanki "nace ka tausaya min ne? ko nace ka cigaba da rikeni dole ? Ko  nace dole sai ka zau....."Idan kin   sake furta wata kalma  anan sai na tattakaki idan km  kin mutsa bismillah  kiyi  "  yana gama faɗan haka ya fice daga cikin ɗakin ransa a bace, gsky yayi mugun  sakewa yarinyar dayawa shiyasa ta rainashi .

Saukowa tayi ta shiga bayi tai alwala ta fito tayi sallah  tana idarwa ta mike ta Isa gaban mirrow  ledan da ya aje mata ta ɗauka haɗe da buɗewa, robobin take away ne acikin  har guda  uku,  ɗaukan ɗaya tayi haɗe da buɗewa ta soma ci, kad'an taci dan zazzzabi take ji sosai bata jin dadin  bakinta   ta sha ruwa kad'an  .
 kamar ta koma ta kwanta   ta tsinci kanta da fitowa, kanta babu dankwali  ta fito zuwa falo da kyar take taka ka'fafunta , yana tsaye agaban tv  ya bawa cikin falon baya yana ƙoƙarin danna code din bude wayarsa ,  jin motsin mutun  a falon yasa  batare da ya juyoba yace.   "waye ? "Waye byn wacce ka sato ka ajiye a gidanka  ita ce ta fito  ta sha iska tayi mgnr da kyar tana kokarin zama akan kujera "shekaru sun ja wallahi ya kamata ka tuba ka daina harkar fashi ,nasan da mahaifiyarka tasan wannan aikin kake yi da bata yi alfahari da Kai ba a karshe  kashe kanta zatayi dan bakinciki  ."

A matukar fusace ya nufo Inda take  tamkar wani mayunwanci zaki ya damki wuyanta yana Shirin danne makoshinta ya fasa saboda zafin daya ratsa tafin hannunsa ya tsura mata Ido kawai yana kallonta  "ka shaki ne mana ai ni yanzu a shirye nake da mutuwa gara min mutuwa akan cigaba da zama da Kai ,a farkon had'uwa ta da Kai naji duk duniya Kai  mutumin kirki ne  ,Kai ne  mutumin da zuciya da gangar jikina suka mace akansa saboda a  tunanin zuciyarka me kyau ce a she ba haka bane mugun  ciwo ne daskare  a zuciyarka wannan mummunar sana'artaka yafi min komai zafi acikin zuciyata wanda adalilin haka  yanzu  babu kyakkyawan zaton da soyayyarka   acikin zuciyata  sai zallar tsana  ,na tsaneka tsanar da zan iya ganin bayanka ka rubuta ka ajiye muddin na bar gidan  nan sai nasa  ka shiga ha......."

"karya ne " ya fad'a  a tsawace yana  nuna ta da yatsansa  "karya ne baki Isa ba , baki Isa kisa akamani ba how could you tell someone  tanweer ?"  you can't  do that , bazaki iya ba  sannan  jaguwa ba zai kamu ba cikin sauki ba  sai dai wani mutun dabam,  da zan kamu da ban Kai iyanzu ba" yayi mgnr yana furza mata iska a fuskarta  tayi saurin runtse idanunta gabanta na faduwa , ya juya mata baya tare da rike kugunsa da hannu d'aya ya fara zagaye falon zuciyarsa na tafarfasa can ya juyo a matukar fusace  "and     kikace me  byn zaki sa na shiga hannu ?" Kin tsaneni  tsanar da zaki iya ganin bayana Shima karya ne   zuciyarki  bazata  iya rabuwa da soyayyata ba  yadda  kika furta cewar kina sona haka zaki tabbata da sona  a karshe ciwon sona ne zai kasheki  saboda Ina ranki ,na  shigeki shigar  da bazaki iya cireni a ranki  ba ,zaki je gidan wani da tarin soyayyata gangar jikinki za'a Kai gidan wani zuciyarki kuwa tana nan  ....."ya nuna qirjinta daidai saitin zuciyarta .

wani  irin  sarawa kanta ya dinga yi da  karfi  kmr zai ra'be gida biyu  tayi matukar firgita da  Jin mgnr shi , ta d'auka zai tsorata da maganarta  sai dai taga sa'banin haka atattare dashi sam shi din ba matsoraci bane zuciyarsa  a dake take ,kallonsa tayi tare da ciza lips dinta  batare data sake yunkurin cewa komai ba "ki tashi ki 'bace min da gani  banason ganin wannan banzar   fuskarki, karki qara kuskuren zuwa  Inda nake sannan   duk abinda kikaga  Ina yi miki karki d'auka so ne , ba so bane tanweer  dan ko digo d'aya na sonki babu shi acikin  zuciyata  bakya cikin  irin tsarin matan da zan  so , idan Kuma kin koma gaban iyayenki  dan  Allah karki fasa idar da nufinki  akaina  kiyi  Ina jiranki  wani irin zafi da ciwo kai ne me karfi   yayi mata diran makiya gbdy  jikinta ya sake d'aukar zafi tayi karfin halin dafe kanta cike da sanyi jiki ta mike  ta nufi hanyar komawa d'aki  sai da tayi da tasanin fitowarta ."

da kyar ta  dinga d'aga ka'fafunta da
idanu ya bi  bayanta  yana kallonta  rai a 'bace  har ta bace wa  ganinsa sannan ya d'auke idanunshi  yana   fesar da iska zuciyarsa ban da zafi babu abinda  take sai  faman  tsaki yake ja da karfi  ya fad'a kan kujera  ya runtse idanunshi tare dafe goshinsa cikin haka abokansa suka shigo suka samu guri suka zauna   ganinsa haka yasa  suka fara tmbyrsa abinda ke damunsa shiru yayi yaki cewa komai  sai tsaki yake ja anas ya dafa kafadarsa "meye damuwarka  Kuma ? Still shiru yayi yana ciza lip's dinsa jabir da jubi suka tashi suka fita  dan sun San  tunda yayi haka ba magana zai yi ba "ya kamata ka rage  damuwar nan  jaguwa nasan duk damuwarka  bata wuce akan yarinyar nan ba "Ina matukar tausayin yarinyar nan  anas amman ita  burinta bai wuce taga bayana ba
yayi mgnr a fusace idanunshi sun yi jajur "kayi hakuri nasan da haka nasan kana tausayinta da qau...." wani irin   kallo yayi masa wanda yasa anas ya hadiye abinda zai fad'a "na sha fad'a maka ka daina cewa Ina son yarinyar nan amman tunda haka kake tunani ka zuba Ido zan baka mamaki"

"yauwa haka nake so Ji  abokina Ka bani  mamaki  ka rabu daita mu hutu tunda baka sonta banga amfanin   zamanta damu ba  dan kasancewarta damu matsala ne mu sallameta kawai  anas ya fad'a yana cigaba da   bashi shawara  akan tanweer ..."
Ita Kuwa tanweer tana shiga d'akin ta shiga har  gitsa d'akin tamkar mahaukaciya  a karshe ta fad'a kan gado hawaye na zubo mata sharrrrr akan quncinta  tasan hawayenta nada halaka da bakaken maganganun daya fad'a mata , zuciyarta ta karye madadin  soyayyarsa ta bar zuciyarta kamar yadda take buri sai ta  dawo mata sabo fil tunda take baa ta'ba kallon idanunta aka furta ba'a sonta ba sai Adnan shine mutun na farko jikinta ya sake d'aukar zafi sosai  wuni ranar bai shigo Inda take ba har dare  ita Kuwa zazzabi da  dacin maganarsa  da ciwon gajiyar sex din  jiya suka hade  mata  guri d'aya tayi kuka har hawayenta suka kafe bai shigo  Inda take ba ya kama kanshi dan yasan koya shiga gurinta  wani rashin mutunci zata masa shi Kuma bazai dauka ba ."

washegari  tun karfe goma suka bar gidan batare daya lekata ba , dan har lokacin haushin abinda tayi masa bai bar zuciyarsa ba  Kowani titi jami'an tsaro ne over fiyye da duk wani abun hawa, duk motar  data  zo wucewa sai an tsaresa an bincika ciki da wajenta  tun daga nesa suka hango motar jaguwa tun kafin  motar ya gama karasowa garesu suka daga ma eku  hannu alamar ya tsaya a hankali motar ta rage gudu  tare da k'okarin yin gefen titi ,a hankali  eku yayi waning  glass din motar  yana mazurai  ,daya daga cikin police officer ya dan leko cikin motar, cikinsa ne ya duri  ruwa  sakamakon ganin pesto a hannun jubi ,  ya ware Idanunsa sosai yaga ak 47  akan cinyar eku  dake tuki ya Kai Idanunsa baya nan yaga sabon tashin hankali domin kuwa manya  bindigu  ya gani akan cinyar anas da  jaguwa wanda ya kawar da fuskarsa gefe yana kallon titi da sauri Police office's  din  da suke  zagaye  da motar suka yi baya jiki na rawa .
daya daga cikin police yace "sorry ban San ku bane you can be on your way " a hankali glass din motar ya fara yin sama motar ta fara move  police sukayi sauri  suka tsaida wani me adaidaita suka duba cikin motarsa kana suka bashi hannu ya wuce direct   to Ogun state suka nufa   basu  suka dawo gidan ba  sai daf da sallar magriba  wanka ya fad'a tare da alwala ya fito ya soma k'okarin gabatar da sallah  byn ya  idar da sallah magrib ya nufo d'akinta    hannuwansa duka zube cikin aljihun wandonsa   ya  hangota   kwance tayi ruf da ciki   ko motsi kirki bata iyawa , ganin yanayinta  yasa qirjinsa bugawa da sauri  sai dai bai nuna hakan ba a fili   tun kayan jiya ne sanye  ajikinta, harara ya wurga mata  sakamakon tuno abinda tayi masa   a natse ya qaraso Inda take ya Kai hannunsa wuyanta nan yaji wani zafi ya ratsa tafin hannunsa  kmr ta buge masa hannu sai dai bazata iya ba dan jikinta babu karfi "baki da lfy ne ?ya tambayeta  banza  tai masa taki motsa labbanta  "raguwa banza kawai  ya fad'a acikin zuciyarsa ."

"Kinyi  sallah ma kuwa  ?
Still shiru tayi masa bai damu ba ya cigaba da mgn "idan kinyi sallah  ki canza kaya ki sameni a falon dan naga alamun tun kayan jiya ne ajikinki  yana gama  fad'ar hk ya juya har ya kai  tsakiyar daki yaja ya tsaya yana cewa  "na sanki da shegen  d'aurin Kan tsiya   ,minti goma kawai  na baki ki sauya kaya ki  fito dan Allah karkiyi abinda nace ya cigaba da tafiya ya  fice daga daki .
Babu yadda ta iya ta mike ta shiga bayi alwala tayi ta fito ta tada sallah  byn ta idar taki sauya kaya  kmr yadda ya bukata ta fito , yana tsaye tare da friends dinsa  ta fito duk suka tsura mata Ido suna kallonta  maganar jaguwa ta jiya ce ta fad'o musu sosai suka qura mata Ido
suna yabawa da kyawunta .
yaji motsin fitowarta amman yaki juyawa "muje  ko yace

Please Login or Register in order to submit comment