Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai zai tabbatar mana da abinda muke bukata "lallai muna bukatar mu san ta yadda aka san  fitar sconpio  daga gidan nan da kuma inda zashi domin byn mu goma da muka tautauna babu wanda yasan da fitarsa kuma na tabbatar acikinmu babu wanda zai fitar da sirrinmu tunda ba yau muke tare ba dole sai mun yi bincike sosai akansa musan waye shi dan leke asiri ne ko kuwa shi din namu ne ?.


"Wannnan gsky ne na yarda da kai dari bisa dari Ana's to yanzu me ya kamata muyi? Anas yayi shiru kawai yana sake zurfafa tunaninsa domin nemo mafuta."ka fada min abinda ya kamata muyi mana kayi shiru kana kallona  ?" ban san me zamuyi ba wallahi kaina ya kulle  ,kayi tunani  adnan dan ka fini kaifin basera da hangen nesa akan komai kayi tunani me kyau abokina."gyada kai jaguwa yayi sannnan ya cigaba da tafiya yana kallon yatsun kafafunsa yana zurfafa tunaninsa "da fari muna bukatar kwakwarar hujjar da zai tabbatar mana da aliyu ya shigo gidan nan acikin kwanakin ko bai shigo ba ",

"Eh mu samu wannnan hujjar  mu fara duba naurorin gidan nan tukun , duba nau'rori kawai  bazai bamu wannnan hujar da muke  nema ba saboda a wannnan falon mukayi tautaunarwa fitar sconpio kuma har muka gama babu wanda ya shigo duk wanda ma ya  fitar da maganar to yayi ne ta hanyar lebe ,amman bazan ki ta taka ba muje  mu duba tukun mu san next abinda zamuyi ."
Duk da hankalinsu a tashe yake amman a natse  suka jera  har dakin na musamman da na'urorin suke  .”jaguwa ya samu guri ya zauna ya daura kafarsa daya akan daya   tare da rike habarsa da hannu daya yana kallon anas dake kokarin  kunna  makaken tv  dake manne  da bangon dakin , nan take ya kunnu bangaren  dake daukar haraban gidan har inda mai gadi yake  zama  suka maida hankali kai ."

a hankali suke kallo duk abinda ke faruwa har suka kawo wani guri inda suka ga yana nuna musu dishi dishi alamun an rufe idon camerar kuma daga waje can kuma komai ya daidaita suka cigaba da ganin komai har zuwa fitar scorpion a jiya  da shigowar bakinsu na dazu da shigowar anas ."jaguwa ya mike tsam  ya hade hannunwansa guri daya yana tura lips dinsa na kasa cikin bakinsa cike da zafin rai ya soma magana "anan aka samu matsala "a wannan gurin aka samu matsala ya sake maimaitawa yana furzar da iska  mai zafi daga bakinsa,idan ma aliyu ne lallai suna da hadin baki da wannan tsohon dake mana gadi ".

A dan firgice anas ya dubesa zuciyarsa na rawa kafin daga baya ya soma magana cikin tsananin tashin hankali "gaskiya bana tuanin tsohon nan zai yi mana haka, za dai mu tambayesa amman mutamin nan  yana da kirki  bazai zama da hadin bakinsa ba,idan kuma har ya zamo da hadin bakinsa lallai wayo aliyu yayi masa dan wannan tsohon bana tunanin zai iya shirya wannan kimurmura kuma na tabbatar bazai boye mana komai ba tabbas idan aliyu ya shigo gidan  nan zai fada mana idan ma aliyu ya yaudaresa ne ya bashi wani abu dan ya ida nufinsa akanmu zai fad'a mana ."

jaguwa bai ce komai ba ya fito zuwa babban parlour'nsa ya karasa inda fridge yake ya bude ya dauki goran ruwan mai sanyi ya kafa a bakinsa dan  tashin hankalin da yake ciki yasa makoshinsa ya bushe ,har cikin zuciyarsa bai yarda aliyu zai masa haka , zuciyarsa tafi amince masa da me gadi ne
idan kuwa hakan ya tabbata zai bashi mamaki ,zai masa abinda mutane zasu tsaneshi sai daya shanye ruwan tas sannan yayi wurgi da goron ruwan yana sauke numfashi ,ya rike kugunsa da hannunsa daya ya fara tafiya babu shiri shima anas ya biyosa a baya ,yana cikin damuwa da tashin hankali amman idan ka kallesa bazaka fahimci  komai ba sakamakon dakiyar zuciyar da allah ya bashi ."

Kafafunsa basu tsaya akoina ba sai inda mai gadinsa yake zaune yana cin dafaffiyar kyada ya tsaya a gabansa kyam bayan ya zuba hannuwansa duka  cikin aljihun wandonsa tare da zuba masa rikitattun idanusnhi yana kallonsa,shi kansa mai gadi sai daya tsargu da irin kallon da jaguwa yake masa dan bai taba masa kallo irin haka ba har tsakiyar idanu,babu shiri ya ajiye ledar gyadar hannunsa yana cewa "yallabai barka da fitowa?jaguwa ya daidaita kansa yana sake boye tashin hankalinsa ya gyada masa kai kawai .” sai da anas yayi masa alamar yayi magana sannan ya bude bakinsa da kyar yace “baba ya aiki "?
“alhamdulillah mun godewa allah ina ta son ma na shigo nayi maka magana akan Jama’arka sun dade yau a kofar gida suna jiran fitowarka ,wasu sun gaji sun wuce wasu kuwa suna  nan  har yanzu sunki tafiya “.

Shiru jaguwa yayi daga maganar farko da yayi bai sake cewa komai illa idanu daya zuba masa ganin bashi da niyyar sake yin magana yasa ana's ya shafa sumar kanshi shima yaso yayi masa magana dan lokacin da zai shigo ya mutane dayawa a kofar gida sai dai tashin hankalin da ya taho dashi ya mantar dashi ."Allah sarki bari yanzu idan ya koma ciki zai sa azo a sallamesu inji cewar Ana's .shi dai jaguwa bai sake cewa  uffan ba sai idanu daya zuba ma mai gadi yana karantar yanayinsa gabadaya yanayinsa ya nuna masa rashin gsky Ana's ya cigaba da magana "daman baba mun zo mu tambayeka wani abu ne ? allah yasa na sani yallabai yayi maganar  da sauri zuciyarsa na rawa "nace ko aliyu yazo gidan nan acikin kwanankin nan  da suka wuce ?shiru mai gadi yayi yana tunanin amsar da zai bashi   "baba
ana tambayarka kayi shiru ."eh yazo ko bai zo ba that's all ?

"uhm bai zo ba ".

stil jaguwa cigaba da kallon bakin  mai gadi yayi yana  hura hanci  batare da yace komai ba so yake ya gano wani abu atattare da mai gadi   Kuma ya gano dan haka ya juya cikin tsananin fushi da zuciya ya soma daga kakafunsa bai yi magana ba sai daya shiga cikin dakinsa "wannan tsohon na fara tantama akansa."  anas ya fuskancesa sosai "kamar ya  ka fara tantama akanshi ?"wannan tsohon fa bazai yi haka ba , zai yi Ana's yanzu nan fa ka gama cewa mutane sun zama abun tsoro cin amana ne qarara ke zagayedamu bamu sani ba, idan ma zargi zamuyi wannan tsohon zamu zarga ba aliyu ba domin ya riga aliyu zama tare damu kuma shine ke yini a gidan nan 24 hour's sabanin aliyu amman nasan me zanyi zan d'ana masa tarko lallai sai na san wani abu akansa ,idan shine yake bibiyata acikin gidan nan zan sani idan ma wani dabam zan sani wannan karon bazan bar kowaye yake da sa hannu cikin bibiyar rayuwata   ba yana gama fadar haka ya shige bedroom dinsa shima Ana's ya biyosa ."

Anas na tare da jaguwa har sanda ya dauki karamar wayarsa daya saka sabon sim  ya boye number ya soma neman layin  dcp bayan an dauka  yaji ba muryarsa bace dan haka  yace "Ina son nayi magana da dcp ,"ko zamu iya sanin me yasa kake son kayi magana dashi ?masaniya gareni game da mutuwar honorable abdulaziz ,anas najin haka ya tattara hankalinsa gbdy zuwa kansa dan sam bai yi tunanin ta nan zai bullo da tsarinsa ba  , daga can office din jami'an tsaro aka tambaya sunansa yace "Amir ali."
Wanda ya dauki wayar yace ka  bada minti biyar zaa hadaka dashi  ."

  bayan wasu mintuna aka hadashi da dcp  "hello ko zan iya sani da wa nake magana?ba lallai kasani ba amman  ni nasanka da dade wa na kira ne na  nasar maka cewar "mutuwar honorable abdulaziz abokansa guda biyar ne suka hadu suka kashesa suka binne gawarsa a gidan dayan daga cikinsu ."
shiru dcp  yayi domin dai yasan da labarin a halin yanzu ma ana kan bincikensu akan haka sai dai ba'a rigada ansan inda gawarsa take ba "to shi yanzu me zai yi da wannan case din ? shi da yake son ganin bayan jaguwa da tawargarsa me zai sa ya sanya kanshi cikin binciken akan matacce ? dan haka a matukar a fusace yace "shshan banza ni me zanyi to akai da ka kirani ? "Me yasa bazaka kira babban headquarters na abuja ka sanar dasu ba  tunda case ya koma hannunsu idan ka samu labarin inda babban dan fashi da makamin nan  mai suna jaguwa yake ka gaugauta kirana zamu baka lokacin mu har ma mu hada maka da makudan kudade amman akan matsalar mataccen karka sake kiran mu a waya kit ya katse kiran yana gama fadar haka ."

Shiru jaguwa yayi yana tunani abun yi yana duban anas  daya tasa shi gaba da kallo kamar shine dcp din kafin daga baya ya sake Kiran  layin  aka dauka tare da cewa "da me zan iya taimaka maka ?amir ali ne yake magana wanda ya kira yanzu ka sake hadani  da dcp  ,okay ka dan rike waya ya mike cikin hanzari ya sake shiga office din dcp alokacin yana tare da yaronsa suna tautaunawa akan scorpion"yallabai  mutumin dazu ne yake son magana da kai "batare daya dago ya kallesa ba yace "kace masa bana nan okay sir ."ya  dawo yana cewa kayi hakuri a she baya nan" shin ka san ..."kafin jaguwa  yace wani abu dansanda ya katse kiran ya koma mazauninsa  ya cigaba da ayyukan gabansa ."

Dcp kuwa sai faman tsaki yake ja "aikin banza
kawai ko ina ruwana da batun mutuwar honorable abdulaziz, kaje can ka kai rahontonka ga masu bukatar bincike akan mutuwa , ni nan labarin yadda zan kama jaguwa nake nema ba wani mutuwa ba , yaronsa asp isa dake zaune a gabansa  yace "yallabai me yasa zakayi haka ai da ka tsaya kaji a ina yasan batun inda aka binne gawarsa "kai bazan tsaya naji komai ba , da jin wannan maganartasa  kasan wata qullaliya ce akasa ,amman kuma idan gaskiya ce zai yi matukar mana amfani "dan allah ka rufe mana baki babu ruwanka kaji da karamin matsayinka idan ka kai wannan matsayin sai kayi aiki fiyye da wanda mukeyi a yanzu ."

tsit asp isa yayi saboda ya fuskanci mai gidan nasa ya dau zafi da maganarsa dcp ya cigaba da Magana "wani bayani kuka samu a bakin yaron jaguwa "?har yanzu  dai shiru sir yaki  yace  komai "kun matse shi sosai kuwa ? sosai kuwa yallabai daga jiya zuwa yau din nan  ba karamin izaya muka masa ba gbdy mun canza masa kamani amman yaki bamu cikakken bayanai akan jaguwa sai ihun azaba yake ."
"Baku matse shi da kyau ba ,ku matseshi sosai karku masa da wasa idan yaki magana zuwa gobe kusashi  a under ground idan shima yaki magana ku sanar min zan masa izayar da bakinsa zai bayyana mana sirrin komai na gidan jaguwa ai tunda ya shigo hannun magana ta kare sai munga bayansu daya bayan ".
"Okay sir !
Ya fada tare da mikewa tsaye cike da girmamawa
har ya kai bakin kofa dcp ya dakatar dashi ta hanyar  kiran sunansa" Asp isa!"Yes sir ya fad'a tare da juyowa ya Kame agabansa "Kusa ido sosai akan scorpion domin su din barayi ne masu  matukar wayo da dabaru kala kala da zasu iya komai domin kubatar da kansu  dan haka ku maida hankali sosai ku qara matakan tsoro mai karfi yanzu harinmu na gaba cikin manya abokansa ne dama wannann yaron nasa yace wani abu ne da yanzu mun san ta inda zamu fara aiki lallai sai mun kama jaguwa da gbdy yaransa a mace ko araye inshaallahu ma a raye zasu zo hannu sir ya juya ya bar office din ."



Jaguwa  ya furzar da iska yana cizan lip's dinsa da karfi "wannan itace damar da nake son nayi amfani daita, idan  bata samu karbuwa ba bansan me zan  yi ba kuma?  yayi maganar a fili ya zagaye dakin .
anas ya matso shi yana cewa "karka damu zaka yi nasara ka sake yin wani tunani akai  ko kuma ka kira  number office din commissioner kai tsaye  nasan shi bazaiki amsar maganarka ba ,take zuciyar jaguwa ta amince masa da hakan,ya  kira da wani layi ya nemi yayi magana da  commissioner ai kuwa kai tsaye aka hadashi da commissioner wanda shima alokacin yana tare da mataimakinsa A kwantagora ya soma magana  a natse  "ko zan iya sani dawa nake magana"?

"Kana magana da Amir ali ne batun mutuwar honorable abdulaziz ba hatsari yayi ba kashesa akayi
"taya akayi kai  kasan ba hatsari yayi ba kashessa akayi "? shikenan idan zaka bani dama sai mu hadu zan baka bayanan komai domin ina da hujoji a hannuna commissioner yay shiru yana sauraronsa tare danna record acikin wayarsa "duk naji bayaninka yanzu daga ina kake magana ?"
"daga kano !

"to me zai hana ka sanar da jami'an dake aiki a kano ko  abuja ?"ai gani nayi anan lagos honorable abdulaziz din yake daga nan aka fara bincike kafin case ya koma abuja kuma ni yanzu haka ina airport zan taho lagos daga lagos Australia zan tafi jirgina karfe bakwai zai tashi "to shikenan ka bani  numbarka zan nemeka idan ka shigo ,"Aa yallabai ni ne zan kiraka ka bani number wayarka ,to shikenan ka rabuta commissioner ya karanto ma jaguwa numbersa yana maimatawa anas kuma  na rubutawa  sannna ya katse wayar ."

commissioner ya kalli mataimakinsa yana sake yi masa bayani abinda jaguwa ya fada masa "ya kake gani zamu yi yanzu "kwanta kwata yallabai ni ban yarda da wannna mutamin ba "taya yasan labarin mutuwar honorable abdulaziz da mutanen da suka kashesa da inda aka binne gawarsa byn har yanzu ana kan bincike ne   baa gano inda gawar take ba su kansu abokansa sunki amsa laifin su suka kashesa dan haka ni ban yarda dashi ba karka sauraresa."
“amman kuma gaskiya ya fad'a mana tunda duk abinda ya fada haka ne kuma da alamun zai yi matukar yi mana amfani," nan dai suka cigaba da tautaunawa shi dai commissioner ya yarda da maganar jaguwa kuma idan dai har ya kirasa zai bari su hadu ya bashi bayanai akan komai bayan mataimakinsa ya tashi ya koma office dinsa kira ya shigo wayar hannu ta commissioner yana dauka ya fahimci mai magana "me kuma kake  so daga gareni ?

"so nake idan na shigo mu hadu da kai kai kadai na baka sheidu masu matukar mahimanci idan kuma hakan  bazai yiwu ka  hadu dani kai   kadai ba shikenan  sai na tattara sheidun na watsasu a ruwa daman yanzu adalci yayi wuya ayi sharia a lahira  a inda babu wanda ya isa sai allah ,ya tunhumeku akan abinda kukayi ,ni da zaku fahimceni ma bayan wannan mahiman bayanan akwai wasu akan  masu safar miyagun kwayoyi wanda dayansu polisawa ne duk zan baka amman kai kadai ,dan da kai kadai kawai na yarda ."To shikenan ai kuwa daka taimaka mana yanzu dai  ka  sake kirana nan da awa uku  zan fada maka inda zamu hadu jaguwa najin haka ya dunkule hannunsa yana jin dadi ya katse kiran  ya zauna  yana cewa "shikenan tarkona bai kama dcp ya kama commissioner  ,sai yanzu hankalina ya kwanta"ya karasa maganar yana sakin murmushi.

“ya  yarda zaku hadu kenan ?da alama tunda yace na kirasa byn awa uku zai fada min inda zamu hadu kasan  fa  shi wannnan commissioner din rikitaccen tsoho ne ina ganin ma a karshen shekara nan zai yi  ritiya ,zan bika muje tare ."baka da hankali  bakaji nace babu inda zakabini  ba , ance maka haduwa da commissioner abu ne me sauki ? ka barni kawai naje ni kadai idan ma matsala ce ta tsaya iya kaina ban da kai  ya karasa maganar tare da mikewa ya nufi bathroom dan lokacin sallah laasar yayi ."

Bayan jaguwa ya fito Ana's  ya tashi ya shiga bai bata lokaci ba ya fito alokacin jaguwa ya tada sallah ya karaso ya bishi jim'i byn sun idar  suka sake zama sai lokacin jaguwa ya tuna da jama'arsa dake kofar gida gashi ya soma jin alamun hadari ya kuma san muddin bai bada sakonsu ba anan zasu wuni har sai sun ga fitowarsa "anas kira sky kace ya sallama mutanen dake waje ,numfashi ya sauke "gsky kam dan wasu da wannan kudin daake raba musu kullum suke cin abinci batare da bata lokaci ba ya kira layin sky ya bashi umarnin ."
Suna hira suna duba lokaci a hankali har akaci awa daya acikin awa  ukun  da commissioner ya bayar dan haka  suka cigaba da hirar yadda jaguwa zai hadu da commissioner "tunanina idan na kira shi  zai ce mu hadu dashi  a hotel ko gurin shakatawa ba lallai mu hadu dashi a gidansa ba , nima gaskiya bazan so ku hadu a gidansa ba akwai hatsari gara ku hadu a waje  zai fi ,muna haduwa a yau ina tabbatar maka a yau scorpion zai fito domin bazan sausauta masa ba."

suna cikin  hirar wata awa daya tazo ta wuce karfe shida daidai kenan cikin haka  hally ta kira layin anas ya zaro wayarsa yana dubawa "my princess ."
Ya fada yana dauka "wa'alaikis salam matata fatan kina Lfy?alhamdulillahi kinji shiru ban kiraba ko ?sorry my princess inshaallahu bazan jima ba zan shigo  sukai sallama ya maida hankalinsa ga jaguwa wanda ya dauki sigari ya kai bakinsa "kasan yanzu hatta sigari ina kyamar shanta saboda banason matata taji warinsa ajikinsa ".
Wannan kuma damuwarka ce ni dai ko zan rabu da komai ban da sigari ina mugun qaunarta murmushi Ana's yayi  "wallahi adnan ina maka kwadayin aure da zarar kayi aure gbdy rayuwarka zata canza zaka rage wasu abubuwa tunda ga zahiri na gani akaina idan akace zan daina shan giya da neman mata zan karyata sai gashi hatta sigari ina neman barin ta "kai dan allah tashi  mune garin ma ya sake hadewa da hadari nasan muna kan hanya lokaci zai yi na ajiyeka agida na kara gaba da motarka ."

Mikewa yayi ya shirya kansa sosai tare suka jera har suka karaso haraban gidan babu kowa acikin abokan aikinsu sai mai gadi kadai zaune  akan farar kujera mai zaman mutun daya  dakin ajiye makamansu ya wuce ya dauki bindiga masu lafiya guda hudu da harsashi ya zuba cikin karamar jaka ya fito  inda motar anas take fake ya  nufa Ana's ya ciro keyn mota a aljihunsa ya mika masa sannan kowannensu ya bude murfin bangaren da zai zauna ya shiga ya zauna jaguwa ya waiga ya ajiye jakar abaya ya sanya key ya tayar da mota suka bar gidan ."
Suna barin gidan cid  ya soma kai kawo a haraban gidan bashi wannan lungu bashi wancan lugun wanda a garin leke lekensa yasan adadin mutanen dake rufe acikin gidan  babu wanda ya bashi tausayi kamar alqali  mutumin dake kan aikinsa shima fa da asirinsa zai tono wannan ne hukuncinsa agurin jaguwa tunda ya fahimci basa kisa sai izaya suka iya ."

A halin yanzu shi kansa ya matsu wa'adinsa ya cika ya tattara ya bar gidan domin yana matukar jin tsoro yana cikin tafiya yana dube dube kamar ance ya daga idanunshi sama ya hangi wata tukunyar kasa yar karama acikin tsakankanin fulawas din dake shuke a gurin ,bai yi sanya ba ya juya zuwa daki ya kira number dcp ya sheida masa ,"okay to shikenan amman ban zan samu damar fita ba  yau dana zo da tukunyar  ,no bai nan yanzu ya  fita tare  da amininsa ."
"Gaskiya bana tunanin suna  zargina ,"okay to shikenan sai dai nayi haka ya fito yana waige waige  babu kowa ata bangaren da yake dan haka ya dauki  kujera  ya kai daidai inda yaga tukunyar ya lallaba ya ajiye ya kara tsayi daita yayi bismillah ya dauko tukunyar ya ajiye yana kallon tukunyar babu komai acikinta sai kahon rago da madubi aciki  sosai tsoro ya kamashi ." amman hakan bai hanashi yayi fitsari acikinta ba  kamar yadda dcp ya fad'a masa ai gama fitsarinsa ke da wuya wani bakin hayaki ya tashi yayi sama ya dauki tukunyar ya mayar inda ya ganta ya lallaba  ya bar gurin  ."


Jaguwa kuwa tunda da suka shiga mota hirar yadda haduwarsa da commissioner zai kasance suke har suka hau kan babban titi ilu peju a lokacin garin ya sake hadewa da hadari "idan ruwan sama ya sauko allah kadai yasan lokacin da zai tsaya ,nima tunanina kenan ga aiki mai girma agabana fatana na samu nasara haduwa da commissioner suna tafiya ruwan sama ya tsinke kamar da bakin kwarya gbdy jikin anas yayi sanyi dan haka ya dif ya daina magana  yana kallon motocin dake falla gudu akan titi ."
wata mota kirar farari baka wuluk ta wucesu da mugun gudu   akan titi ilu peju tafiya kadan motar tai ta tsaya a gefen titi direban dake tuka motar ya waigo alokacin da matan daya tuko suke kokarin tmyrsa   dalilin tsayuwarsa a halin yaga ana ruwan sama  "tayar motar ce ta samu matsala bari na fita na duba na gani ya fad'a yana kokarin fita cikin ruwa ,  acikinsu babu wacce tayi kokarin hanashi fita sai hirarsu da suka cigaba da yi gashi mutumin ya dan manyata ,tsohon  direbansu  ne  minister ma ya so kwarai ya ajiye aiki amman tsohon yaki a cewarsa zai iya kuma tabbas yana kokari idan gurin tuki ne  ."

Boot din motar ya bude ya dauko wani karamin akwati dake dauke kayan gyara ya bude  sannan ya duba tayar  tan take ya gano matsalarta notikan tayar ne suka dan sake abun  daure taya ya dauka ya tsugunna ga ruwan sama na dukansa amman bai damu ba  ya fara aiki."cikin haka motarsu jaguwa ta karaso har ta gotasu kadan ya dawo baya yayi parking yana cewa"Ana's "bari na taimakawa tsohon can ya gyada masa kai kawai ,ya fito yana tare ruwa dake dukan fuskarsa da hannunsa har ya karaso gurin tsohon ya tsaya tsayuwa irinta ingarman namiji mai tattare da natsuwa da Kamala, a hankali ya motsa lips dinsa yana cewa "baba kawo na taimaka maka ka koma cikin mota ,tsohon ya dago yana yarfe ruwan dake dukan fuskarsa ya tsurawa jaguwa ido yana kallonsa yana ji dadi acikin ranshi  yace  "yaro na gode Kwarai da gaske allah yayi maka albarka amman  kayi tafiyar zanyi da kaina ."

"karka damu baba ka kawo ya kai hannu ya karbi karfen hannunsa shi kuma tsohon ya shiga cikin mota ya zauna "har ka gama baba ?Aa wani dan albarka na samu zai taimaka min ban taba tunanin har yanzu akwai mutane masu kirki haka a cikin wannan duniyar tamu  ba ,shiru tayi hakan nan taji gabanta ya shiga duka uku uku  bata sake cewa komai ba ,"Jaguwa ya  tsugunna a inda tsohon ya tashi ya kwance tayar motar kadan  ya sake daureta tanwer dake zaune bangaren da tayar ta samu matsala kamar tayi warning din glass  amman ta kasa aiwatar da hakan sai dai ta kasa dauke idanunta daga kallon gurin ga wani faduwar gaba daya dabaibeyeta ."

Bayan ya gama  ya tattara kayan aikin  da yayi amfani dashi ya nufi byn boot nan ma zuciyarta ta bishi da kallo sai dai bata dago ba  ya bude boot din   motar ya mayar masa da akwatin kayan aikinsa ya maida murfin ya rufe yana dagawa tsohon hannu dake kallonsa ta cikin mota sai  alokacin tanwer ta waigo  sosai  ta bayan motar domin taga wanda ya taimaka masu ana tsaka da tsuga ruwan sama byn ga motaci nata falla gudu akan titi karaf idanunta ya sauka akan jaguwa ,gbdy kayan jikinsa ya jike sharkaf  har sun bayyana tsayayyun nipples dinsa."
ta kasa dauke idanunta akanshi shima idanunshi
ya tsaida akanta cike da mamaki yake kallonta dan  tsantsar mugunta da zalumci shine ta bar tsohon mutane cikin ruwa ita tana hakikce abayan  mota lunshe idanunta tayi tana kokarin fitowa daga cikin mota sai dai kafin ta fito har ya juya bata damu ba ta fito cikin ruwan tana kiran sunansa da sauri ruky tabi  bayanta da kallo  ."

Cikin sauri  tanwer tasha gabansa  tana sauke numfashi "haba adnan ka

Please Login or Register in order to submit comment