Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faffadan qirjinsa yana furzar da hucin numfashi  ,  sama yayi kaɗan da fuskarsa daidai saitin fuskarta  suna shakar numfashin juna   hancinsa na kan nata sun dauki minti biyar suna shaƙar numfashi juna batare da sun kalli kwayar idanunsu ba , cike da jarumta ya hade bakinsu guri daya dan abinda zuciyarsa tafi bukata kenan a wannan lokaci  jin teast din miyon  bakinta yana jin muddin bai tsotsa ba wani mumnunar abu zai iya faruwa dashi,  soma tsotsa ya soma yi yana lumlumshe idanu, a sanyaye ya kamo hannuta cikin nashi ya tsarke   yana murzawa a hankali, gbdy ya kanainayeta ya hanata sauke wadataccen numfashi saboda  kunyarta data masa diran makiya  , tana rungume ajikinsa bacci ya soma fixgarta ta dinga   lumshe idanunta  tana sauke numfashi  dan  haka   ya barta ,ta godewa Allah daya bar abinda yake mata   dan kwakwaluwarta bazata iya daukar abinda yake mata ba,  jin yanayin numfashinta ya sauya ya zareta ajikinsa ya kwantar  daita idanushi na kanta kallo ɗaya yayi mata ya fahimciceta  ya gyara mata kwanciya ya lullube mata  jiki  da bargo mai taushi saboda rashin kayan dake jikinta ya tattara sumar kanta daya sauko  fuskarta gefe ,  sannan ya juya mata baya yana matse kafafunsa jin muryarsa tayi a kasalance   " bari na hada miki ruwan zafi ki tashi kiyi wanka  zanje na dawo kafin na dawo kiyi wanka kiyi sallah  yanayin yadda yayi maganar ya bugar mata da zuciya sosai taso saita natsuwarta dan   ji take kamar  ita dashi ma'aurata ne ina ma su  kasance ma'aurata , ya Allah ka fini sanin dalilin da yasa ka had'ani da wannan bawa naka da ko sunansa bansani ba , Allah  idan alkhairi ne haduwata dashi ka gaugauta saka masa soyayyata tayi addu'ar   a kasan ranta   ...

Jiki a mace ya mike ya fita daga bangaren zuwa dayan bangarensa  jikinsa na sake kwad'aituwa daita ,tsayawa yayi a tsakiyar dakin yana bin jikinsa da kallo duk yanayin jikinsa ya sauya , tsaki ya ja yana mai tsananin jin kunyar abinda ya aikata,  tabbas wannan mafi munin abu kunyar daya  aikata "shi da mata ke kawowa hari kamar zasu cinyesa  yau shine ya ........
Iska ya furzar daga bakinsa ya kai hannun  ya shafa sumar kanshi yana ciza gefen lips dinsa kasa , wani tunani ne  yazo masa har lokacin fa bata sanyawa cikin komai ba , ya karasa gaban madaidaicin table din da yake ajiye mahiman abubuwansa ,   ya ɗauki daya daga cikin wayoyinsa ya soma neman daya daga cikin yaransa  Kira daya ya dauka yana furta "boss.......
katse shi yayi yana  bashi umarnin siyo  masa  abinci  tare da ruwan  zafi yana gama fadar hk ya  katse kiran ya shiga bathorrom domin tsarkake jikinsa  .

Bangaren mahaifiyar tanweer kuwa tunda aka tafi da tilon diyarta take cikin tashin hankali  taki ci taki sha taki wanka ta dawo kamar wata zautacciya mahaifin tanweer ne zaune a gefen ta rike da hannunta daya yana rarrashinta  "dan Allah zainab kiyi hakuri  kida'n sa wani abu a cikin ki dan Allah". ya fada yana kallon hajiya zainab wacce ke zaune kamar wacce bata da rai a tattare da ita, duk tayi wani iri  kamar wacce ta jima cikin wahala ta zabge a cikin kwana  ɗaya  ganinta hakan bak'aramun da'gama Alh.Abubakar hankali yake yiba"Yanzu Zainab kina ganin abunda kike  yana da kyau kenan ?  "nasan irin zafin da kike ji nima ina jin fiyye da naki sai dai idan kika bari wani abu ya sameki baki min adalci ba ,babu diyata a kusa dani ke kuma kinki kwantar da hankalinki ,ki kwantar da hankalinki dan Allah  yanzu haka  ana kan binciken gano inda suke ita kanta  tanweer   idan ta   dawo  ta taddake a wannan yanayin  kinsan she will not feel   bad,  what  if something happened to you me kike so na fada ma 'yarmu Tanweer?"tana jinsa duk waɗan nan zantukan amma sam taki tanka mishi.

Kallonta yayi cike da jin  wani irin matsanancin damuwa, tunda yake a rayuwarsa basu tab'a fuskantar irin wannan tashin hankalin ba , wayarsa ce ta soma sowa alamun kira ya shigo, jikinsa na rawa haka hannunsa ya tashi daga gefen gadon ya tura hannu ya shiga laluben wayarsa, lokaci guda ya ciro yasa ta a kunne. "Waalkassalam"ya fada da alama daga can bangaren an mai sallama.
"Owk gani nan gangarowa k'asa yanzu" Yana fad'a ya kashe wayar ya maida cikin aljihu. "Anganta?!"hajiya zainab  ta mai tambayar tare da d'ago idannunta wadanda sukai rau-rau kamar na wacce ta jima tana jinya.
Wannan shine iya abunda take iya fad'a tun a lokacin da aka fita da Tanweer bata iya cewa kowa komai, haka duk wanda yazo jaje 'yan uwa da abokan arziki bata iya saurarsu  kusan ma  bata gane mutane saboda tsananin tashin hankali da take ciki.

Girgiza mata Kai yayi alamun a'a  "Ki jira naje na  dawo Insha Allahu za'a ganta zainab, amma dan Allah ki daure kisa wani abu a cikin ki  plz"ya karashe maganar cikin rarrashi yana kallon kwayar idonta.

   Dauke idannunta tayi  wad'an da suka cika taf da ruwan  hawaye. "Dan Allah kutaimaka ku dawo mun da 'yata Tanweer, please ka taimaka mun dan Allah Alhaji nasan ba abunda yafi k'arfinka kune governatin na...".
"Shhhhh! Nace kiyi shiru za'a ganta ki kara hakuri yanzu kiyi ko'kari kici abincin da'aka kawo  kan ya huce plz, I will be back soon". Yana rufe baki ya fice yana k'ada Kai cike da takaicin abunda yake faruwa dasu.
Bin kulolin da Salamatu ta shigo ta ajiye mata d'azu na abinci tayi, tana Jin yunwar sai dai bazata iya ciba a yanzu inba ganin tillon 'yar'ta tayi ba.

Suna zaune a babban falon Alh.Abubakar ya shiga da sauri wanda hakan yasa dukkansu tashi ciki hanzari, k'arasawa yayi inda suke tsaye cikin hanzari ya soma mika musu hannu  cikin sauri suke gaisuwa  fuskarshi ba yabo babu fallasa ya koma ya zauna tare da musu alamu da hannunsa da su zauna.
"Tuntuni nake sa idon ganin ku Inspector ina fatan  ansama wani information kan yarinyar nan?". Yayi tambayar yana kallon Inspector hassan wanda kansa ke kallon k'asa batare da ya dago yace komai ba.
Ganin haka yasa Alh.Abubakar dan tsuke fuska tare da gyara zamansa kamar zai tashi , ya cigaba da fad'in. "Lafiya Inspector naga kunyi shiru dukkanku don't tell me ba wani improvement"ya k'arasa maganar fuskarsa cike da damuwa q'irjinsa na wani irin bugu kamar zai fita ba k'aramun dauriya yake ba yana jin rad'ad'in rashin tilon 'yar tasa, tabbas ya fahimci shirun nasu ba alkairi bane d'an runtse idannunsa yayi inda ya soma tsinkayar maganar Inspector.

"I am very sorry sir, gabad'aya investigation d'inmu  ya  nuna an bugar da wasu daga cikin ma'aikatan  dake aiki a cikin gidan  kafin a samu nasarar  shigowa gashi duk wata na'ura da CCTV Footage an datse kamar yadda muka sheida maka a tun farko da...".

"Dakata Inspector! Ni damuwa ta a yanzu 'yata dan haka ina rok'onku dan Allah ku hanzarta nemo min yarinyata kafin su cutar min daita, How comes za'ace ansace 'yata tilo a wannan k'asar da nake da babban matsayi? ya zama dole a binciko   ta  cikin kankanin lokaci, taya muna  ba da tsaro ga al'umma  ace gunmu da iyalanmu  babu?" Alh. Abubakar ke jero wad'an nan tambayoyi wad'anda kana  saurara  zaka fahimci  'bacin  rai da damuwa  a   tattare  dashi  , Inspector  kansa shi da  SP sun tsorata da yanayinsa, d'ago jajayen idannunsa yayi wad'anda da ba ja bane amma yanzu sun rikid'e zuwa ja ya kallesu.
"Zan k'ara baka second chance wajen nemo mun farin cikina, zan kira minister da commissioner of police na sanar dasu if you fail this time I will make sure to disqualify you from all duties dan hakan zai nuna baka iya aikin ka ba sam"ya karasa maganar lokacin daya tashi.

"Insha Allahu we will do our best bazan taba kasa yin aikina ba ka...".
"Inspector kuje kawai, banson jin promises just fulfill your duties kawai, As you all know bazan iya rayuwa ba muddin wani abu ya sameta I need to act quickly yarinyata karamace tayi kankanta da kasancewa a hannun waɗan mutanen, she can't be around such people I won't let her stay long in there Insha Allahu goodbye and good luck for  all Inspector". Yana gama  fad'in haka bai sauraresu ba ya sa kai ya barsu .

Kallon  juna  su kai cike da damuwa "muje" Inspector ya musu magana suka wuce dukansu ukun cikin hanzari Ko drink din da lokacin aka shigo musu dashi basu iya tsayawa sun sha ba .

"I.B why?".
Nazifi yayi tambayar yana kallon Ibrahim wanda yake cike da matsanancin damuwa duk   jikinsa yayi zafi rau saboda zazzabi , tunda aka d'auke Tanweer yake kwance yana fama da zazzabi sosai.
"Amma kasan abunda kake ma kanka ba zaisa aga yarinyar nan bako?". Ya Kuma fad'a yana kallon Ibarahim wanda idonsa ke runtse wasu hawaye masu d'umi ke faman bin k'uncin sa yana tsananin son Tanweer.
"I thought you are strong police officer but a yanzu ganin yanayin ka got me thinking otherwise why? Abune da yakamata ace ka bishi da k'arfin ka like a real man haunt them like lion that you are but...ya Rabbi". Ya fada tare da kad'a kansa.

Shigowar Mahaifiyarsa Haj.bassera ne ya katse Nazifi dake zaune gefensa da Kayan gwaje-gawajensa na hospital kasancewarsa likita kwarare. "Yaci abincin kuwa?". Ta tambaya lokacin data k'arasa shigowa idonta na kan Ibrahim.
Gigirza mata kai Nazifi yayi. "A'a Umma har yanzu dai yaki infact yaki mun magana tunda na shigo". Cike da damuwa ummansa ta  girgiza kanta
"Haka yake ae tunda abun nan ya faru yak'i magana yaki cin abinci gaba daya, lamarin dai sai addu'a kawai" ta k'arasa maganar lokacin data kai hannunta jikinsa runtse ido yayi, yanzu ba zafi jikin normal sai dai damuwar ta abincin. "Umma Ki cigaba da bashi abincin may be zai ci, ni zan koma gun aiki". Ya fada lokacin da yake had'a shirginsa.

"Owk a dawo Lafiya Allah Ubangiji ya tsare". Ta fada tare da mai murmushi.
"Ameen Umma bye". Ya fada lokacin daya dau suitcase din nashi ya fita ya barta zaune tana cigaba da k'okarin yadda  Ibrahim zai yarda yaci abinci tare da kwantar masa da hankali .
Yana fita babban falo ya tunkara jin muryar Abban Ibrahim a falon da alama waya yake, da sallama ya shiga cikin falon. Kallonsa Alh.Tahir yayi tare da saurin magana. " can I call you later?". Ya fada cikin sauri tare da ajiye wayar yana kallon Nazifi.
"Abb...".
"Muje muje waje Nazifi we need to talk ". Alh.Tahir Ya fada lokacin da yayi gaba nazifi na binsa a baya cike da matsanancin damuwa. "Yauwa a nan zamu iya magana". Alh.Tahir yayi maganar yana kallon fuskar nazifi wacce ke nuna damuwa.
"Haba Nazifi, Me yasa kake damun kanka bayan na fad'a maka so nake kawai ka keeping dinshi na d'an day's har na samu abunda nake kallo ya yu...". "Amma Abba me kake nema wanda zaisa kasa nayi ta kashe ma Ibrahim jiki da samai zazzabi haka bayan kafi kowa sanin yanzu ne yake buk'atar jarumtarsa wajen nemo Tan....".
"Dakata Nazifi!". Alh. Tahir ya fad'a cikin b'acin rai tare da d'aga mishi hannu.

"Who is Ibrahim to you? In tambayeka ma". Yayi maganar cikin bacin rai. Cikin girmamawa Nazifi yayi k'asa da kansa.
"Tambayarka nake!". Ya fad'a da d'an k'arfi saboda damuwa.
"Abokina ne". Ya bashi amsa batare da ya kallesa ba. "Good naji dad'i da kasan wannan, so stay within your limits kaima you are like a son to me karkayi abunda zai b'ata zumuncina da kai da iyayen ka, I know
What is good and bad for Ibrahim karka damu bazan cutar da d'ana ba shi kad'ai gareni nima kamar yadda Tanweer take gun iyayen ta na tabbatar babu abunda zai sameta she will be back kaji?"ya karasa maganar cikin sanyin murya .
"To Abba, ni zan tafi aiki". Ya fad'a lokacin daya d'au hanya.
"Owk sai ka dawo my son god bless you for me zaka ji alert kaji ko". "To". Abunda Nazifi Ya fada kenan ya fice cike da mamakin halin Alh.Tahir ya rasa dalilinsa na sa d'ansa a wannan halin gaba d'aya da harara Alh.Tahir yabi bayan Nazifi daga bisani ya koma cikin gida abunsa ya cigaba da wayarsa ...

***
ba'a dauki  cikakken minti shabiyar   ba  eku  ya  karaso yana knwoking din kofar a daidai lokacin daya fito daga bathroom kugunsa daure da towel ya amsa da" Yes yana  dakatar dashi sai daya goge jikinsa ya karasa jikin wordrobe dinsa ya zaro jallabiya  milk colour  design  mai shegen kyau da santsi ya zira ajikinsa ya fesa turare mai sanyin kanshi  sannan  ya karaso bakin kofar ya bude ,ya  amshi farar  laida  da flaks din dake rike a hanun eku ya sallameahi ya murd'a kofar dakin da take  ya  shiga bakinsa ɗauke da sallama ,tana tsaye a   lokacin sanye   da daya daga cikin  dogayen rugunan da yasa aka siyo mata, kallo daya yayi mata ya dauke kanshi daga gareta  saboda wani irin abu daya ji ya tsinkari ilahirin jikinsa mai kama da sukar allura   , ya karasa shigowa  tamkar  bashi ne   ya dawo mata  tamkar  bawa ba a dazu ko wani mayunwacin zaki ,ya balain hade ransa kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa tun daya shigo hankalinta da idanunta tatare da natsuwarta suka koma  kansa ta kasa dauke idanunta akanshi  ina ma zai aureta ....
tayi kewar iyayenta sosai sai dai bata son rabuwa dashi, tuna sauran awani kadan ya rage ya sadata da gidansu kamar yadda yace  yasa hankalinta ya sake tashi  "why will you disturb yourself over him? Uhm! kika sani ko yana da mata shiyasa yaki amincewa dake, why bother your mind? Why?!".  zuciyarta ta jiho mata wannan tmbyr take idanunta yayi raurau ya cicciko da ruwan hawaye , sosai take kallonsa tana jin wani irin sonshi nabin lugu da sako na gangar jikinta  ,ta bala'in kafeshi da  idanunta , ya ɗan dago ya kalli inda take batare da yayi magana ba ya ajiye flaks da laidar hannunsa "menene kuma kika  wani tsareni da idanu?  yayi maganar cikin rashin damuwa "a ranta tace kaji da munafurci kana wani ciccin magani like he is not the person that try to...". Da sauri ta katse tunanin. " ga abincin nan ki tabbatar da kin ci nan da awa biyu zaki koma hannun iyayenki ta yatsin fuska tana turo masa karamin bakinta cike da shagwa'ba tace "ni ni babu abinda zanci sannan babu inda zani, I won't go anywhere I will stay here!".
niyyar fita yake Jin abinda tace yasa  dole ya dawo ya zauna wanda zuwa  lokacin itama ta zauna a gefen gado tana fuskantarshi ya kafeta da kyawawan idanunshi yana kallonta a tsanake, bata fuska tayi tace "meye na wani tsareni da ido kamar zaka cinyeni kana tunanin maidani batare da nasan matsayina ba, ni dole sai ka fada min matsayina kafin! Are you marrying me or not?!".
"ba ke kike da wannan ikon ba ganin damana ne ko akasin haka yayi maganar a dake yana mikewa  ya karasa ya dauko cup da spoon  ya dauraye wannan tsarin na cikin tsarinsa da  dokokinsa tun bai san zai taka matsayin da yake a yanzu ba ,ya dawo inda take tamkar an dasata ya hada mata coffer ya tsiyaya zuma a ciki ya juya ya  mika mata "ki sha karki 'bata min lokaci dan lokacin sallah ya karato dole ta Kai hannu ta amsa  saboda  yadda ya  hade rai ta soma kurba kadan kadan tana kallonsa , ya janyo farar laida ya buɗe ya ciro takeway ya buɗe ya janyo karamar stood gabanta ya ajiye tayi murmushin karfin hali tace " laila kamar wata matarka gsky i will love to be tha...". "shut up I don't want hear ....
Sai kuma yayi shiru ya kasa karasa maganar  "ki daina kusanta kanki dani zaki sa zuciyarki cikin rudani  da wahala  dan I can't be that person".

shiru ne ya biyo baya kafin daga baya yaja numfashi ya  cigaba da motsa lip's dinsa  "ina ke ina ni  ? "da kinsan koni waye na tabbatar da ba zaki yi kwadayin kasancewa dani ba har kiyi muradin son zamowa mata agareni , nasan kyawuna ne ya rudeki ko ?".

tayi saurin hadiye ruwan shayin data kurba tana girgiza masa kai  "no just like that I fa...".
"Shiii! karki bata bakinki duk abinda zaki fada bazan taɓa yarda ba dan dubunki sun fada Kuma ta nan yake bi  ya fita ta nan ya nuna kunnenshi ,  ta narkar da fuska kamar zata yi kuka " ka fahimceni dan Allah give me chance to sho...". "nace bamu dace ba sam! Let's this be the first and last" ya kasara mgnr yana tsura mata idanunsa dake bugar mata da zuciya"Anyway daga yau basai kin Kuma ganina ba".
yayi mgnr  a fusace "ki ci abinci kawai , girgiza masa  kai tayi "ka kwantar da hankalinka wallahi da zuciya daya nake son zama abokiyar rayuwarka ,zan zauna da Kai tsakani da Allah, baxan damu da wani abu naka ba idan kuma kana da mata ne yasa kaki   amincewa dani ka fada min bazan so na shiga tsakanin ma'aurata ba? ".  ta karasa maganar kmr zatayi kuka cike da hassala ya katseta  "just eat!

yana zaune ta soma tsakuran abinci kamar bata son ci  har sanda aka soma Kiran  sallah  magrib ,ya  mike tsam ya shiga bayin dake manne da dakin bai wani dauki lokaci ba ya sake bayyana a parlour a kallon da yayi mata ya fahimci gbdy attention dinta yana garesa "ki tabbatar da kin cinye abincin da shirin barin gidan  nan  kafin na dawo daga masallaci". ya  fita daga d'akin yana taku cikin isa da izza kamar wani jinin sarauta tabi bayansa da kallo har ya bacewa idanunta "ya rabbi Allah ! You alone knows that I am not attracted to him for his handsome face, haka kawai  na tsinci kaina Allah ka kawo min ɗauki ya fahimceni before is too late".   ta lumshe idanunta wasu siraran hawaye suka gangaro mata  yana fita ta saki spoon din hannunta  ..

Kai  tsaye matsallaci ya nufa da kafafunsa yana tafiya kamar baya son taka kasa yayinda mutane unguwan suke gaisheshi cike da girkamawa yana amsa musu a mutunce  lokacin daya karaso cikin matsallacin tuni sawun gaba dana biyu ya cika bai ji dadin haka ba  yabi sawu na uku cike da ladabi ga ubangijinsa yake tada kabbara  bashi ya fito daga massalacin ba  sai da akayi isha'i yana fitowa daga masallaci Kai tsaye gida ya dawo ya sameta kwance cikin bargo  idanunta a lumshe "ke ki tashi muje kou gabanta ne yayi mummunar faduwa  har ga Allah tana son komawa gida  ga iyayenta dan tasan suna can cikin tashin hankali most especially mum  dinta sai dai  bata son barinsa dan tasan ba lallai ta sake had'uwa dashi ba kamar yadda ya furta , akwana  daya datayi dashi ta fahimci shi din mutukin kirki ne wanda samun irinsu ke da wuya "ki tashi muje there is no time to waste".
tana jinsa tayi shiru ta sake  lafewa  haɗe da kamkame jikinta ....

DARLING'S


💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

    WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

https://my.w.tt/lcJskJdtpbb

🅿️07

......Kusa daita ya ɗan duka  yana  kallonta ,a hankali yaji ta kamo yatsun  hannunsa cikin nata tana murzawa bai san sanda   ya  zauna a gefenta yana sauke numfashi tare  da tankwashe ƙafarsa  ɗaya yayinda d'ayar kafar ke kan tayis yana jijigawa , matso da kanta tayi ta d'aura  a saman  cinyarsa, idanunta a lumshe take jin yadda idanunshi ke yawo a fuskarta ,motsa hannunsa yayi da niyyar zarewa daga cikin nata saboda yanayinsa daya ji yana sauyawa, ta bud'e idanunta  tar akanshi Ido cikin ido suke kallon juna lumshe idanunshi yayi na second biyu sannan ya bud'esu akanta ya mik'e  dan baya son kusancinsu tare "me yasa baki jin magana ?"

  cikin sanyi murya tace " me nayi maka ?" tana janyo hannusa ya rankwafo jikinta bakinsa ya sauka a daidai kunnenta hucin numfashinsa  yasa ta runtse idanunta da sauri.  "Ki tashi muje na maidake gidan ku" yayi mgnr yana sakin numfashi haɗe da ciza gefen kunnenta  ta saki qara mara sauti tana jin wani iri a gabad'aya ilahirin  jikinta ."No! bance maka bazan tafi gida  ba but atleast na.....
"Shiii!". ya katseta ta hanyar d'aura yatsansa a kan lip's d'inta,  shiru sukayi gbdy zuciyarsu na bugawa da karfi  "ka hanzarta maida yarinyar nan  tun bata zame maka kaska ba'. zuciyarsa ta faɗa masa haka, mik'ewa ya sake yi  yana kamo hannunta "Ke! tashi muje Karki bata min lokaci ". banza tayi masa tana  yatsina fuska "bana son Ki sake min mutsu  akan komai " yayi maganar yana matse yatsun  hannunta cikin nashi yana ko'k'arin sauko dai ta, Cikin rashin sani ta fad'o jikinsa tare dan sakin  k'ara  "Ahm!". Idannunta rufe, yadda ta runtse su yasa ya k'ura mata idanunsa masu matukar  kyan gaske, dan kanne d'aya idon tayi ta bud'e sai tayi saurin mayarwa  ta rufe hakan ya bashi murmushin da  bai shirya yiba me sauti jin haka yasa  tayi saurin bud'e idannunta akansa.

Murmushin  ya k'ara mishi kyau sosai kamar kar ya daina  , d'an k'ara ware idanunta tayi tana kallonsa wanda har lokacin fuskarsa na d'auke da murmushin. Ko'k'arin gyara tsayuwarta ya soma yi , Tanweer kuwa da sauri ta kai ma bakinsa cafka tamai peck a lips d'insa , ware idannunsa yayi sosai  yana kallonta cike da mamaki  'Do want to kill me wannan yarinya'. Ya furta a ransa Tan kuwa murmushi take masa, sake kai mai Cafka tayi a karo na biyu sai dai wannan karon taji ya bude 'yan lip's dinsa inda ya soma kokarin kissing d'inta,ya  cafko laulausan harshenta cikin nasa kamshi sweet taji mai kamshi lemun ,ware idannunta tayi ganin kallon da yake mata yasa tayi saurin runtse idanunta jikinta na dan rawa saboda wannan shine karo na farko a rayuwa  data yi  kokarin shan bakin wani nmj .

Tsura mata idanunshi yayi tare da d'an murmushi, yana jin yadda take jujjuya harshenta da sweet din dake  cikin bakinsa take zuciyarsa ta dasa masa  ayar tambaya akanta. 'anya kuwa yarinyar nan  cikakkiyar buduwar ce ? anya kuwa ba watsatsiba ce take neman kawowa zuciyarsa farmaki? to idan itace kai meye ?Me ye marabinka daita? " wata killa ma ta fika tunda bata aikata abinda kake .......
Kasa k'arasa zancen zucin nasa yayi saboda yadda take bin kunnensa da lallausan yatsunta tuni ya kasa jure abinda take masa a hankali ya cafko harshenta yana tsotsa a tare suka shanye sweet din sai ji sukayi sweet din ya kare aiko ta saka masa kukan shagwa'ba. "Wayo! Why?"
Tsura mata ido yayi yana kallonta tare da d'an janyewa, Tanweer banda tab'e baki ba abunda take tana kallonsa. "Ba...ka..kaine ka shanye sweet din byn bai isheni ba". Tayi maganar a shagwab'e kamar zatai kuka. 'bata face  yayi wannan karon ba alamun wasa  yanzu a fuskarsa. "okay tashi muje idan ma dubunsu kike so zan miki guzurinsa ta sauko tana gama saukowa ta rungumeshi a jikinta "i love you Mr.No Name!" I will miss you no name   tsintar kanshi yayi da kasa rabata da jikinsa "Just one day with you but ina jinka tamkar kar mu rabu, is it necessary sai mun rabu?". bakinsa ya kai cikin kunneta yana busa mata  hucin  numfashinsa, lumshe ido tayi "ka barni zuwa gobe plz ban gaji da kasancewa tare da kai ba"ta furta cikin sanyin murya kamar zatai kuka, dan ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta. "ta kowani bangare mahaifinki ya baza mataken tsoro ya damu sosai da rashinki me yasa zaki so zama dani fiye da iyayenki why?"
yay  mata tambayar tare da ko'karin kaucewa.

"I know zasu damu sosai hatta I.B ma zai damu da rashina mutumin da muryata kadai idan bai ji ba a rana  babban tashin hankaline gareshi "
take qirjinsa ya buga zuciyarsa ta shiga rawa  shiru yayi yana ƙoƙarin 'ban'bareta a jikinsa idan bai manta ba shine mutumin da suke waya daita a wancan ranar da tayi accindent "wannan kuma damuwarki ce yayi maganar cike da rashin damuwa , murmushin karfin hali tayi wanda yafi kuka ciwo "mutum mai dakakkiyar zuciya kamarka bai dace ya damu da lamuran mutane ba sai dai acikin kwayar idanunka kadai za'a iya hango tarin tausayi mutane bila'adadin". "Ki daina wasa da zuciyarki da tunaninki  muje kawai". Yayi yunkurin sake  bambareta a jikinsa ,sake   manne masa tayi tana gyara tsayuwarta a jikinsa gabansa na bugawa da matsanancin karfi

Please Login or Register in order to submit comment