Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daita sannan ya fuskanci abokansa "zan dan fita amman bazan dade ba zan  dawo  ya karasa  maganar ya  nufi kofar fita .."Tabi bayansa tana adduar Allah yasa gidansu  zai kaita ta huta  ..

suka bisu da kallo kowannensu  na maganar zuci .yana gaba tana biye dashi abaya har suka ƙaraso inda motarsa ke fake eku na ganinsa ya taso  da  hannu  jaguwa ya dakatar dashi ya   buɗe  murfin motar ya shiga  itama ta shiga yayiwa motar  key ya tada motar  mai gadi  na ganinsa yayi hanzarin tashi ya bud'e masa yana daga masa hannu ya fice ya hau kan titi tafiya kad'an yayi ya waigo  gefen da take zaune   cike da takaici"sai nace kisa  seatbelt zaki sa kome  ?"  ya tambayeta cikin yanayi na ɗan jin haushi. Janyo belt tayi ta saka batare da tace umm ba bare Uhmmm sai  qirjinta dake bugawa  kamar zai fito waje.Sunyi tafiya me d'an nisa  akan titi bata  waigo ta kallesa ba,  sai faman  wasa take da yatsun hanunta tana addua acikin ranta  ."

Kai  tsaye   1829 plaza   ya shiga   har    ya  gama daidaita parking ɗin motar bata d'ago ba  ya ciro wayarsa ya lalu'bo number aliyu  yayi  dealing     ya manna a kunnensa maganar minti  biyu yayi ya katse ya kira sadiq shima bai dade ba yayi disconnect din Kiran ya  fito  ya barta ya kulle motar  gbdy, taja tsaki aranta  ,shiru tayi tana zance zuci da dube dube da  idanunta sai lokacin ta fahimci  inda ya kawota,  kallo d'aya tayiwa gurin ta fahimci gurin sun ta'ba zuwa da ib  ta cigaba da zance zuci kmr ance ta Kalli kan kujerar daya tashi idanunta suka sauka akan wayarsa ta d'auka da sauri ta shiga daddana code din data ga ya danna jiya tana addaur Allah yasa haka ne 2020 ta danna sai ga wayar ta bud'e  jikinta  na rawa tashiga dealing number dad dinta  kira  biyu ya d'auka bakinta na rawa tace "dad ..."!daga  can bangarensa a zaune yake amman sai daya mike tsaye cikin firgice yace"tan !!!  where are you ? dad ka zo  1829  plaza ...." ai bata Kai karshen maganrta ba taga yana tahowa da sauri ta sauke wayar a kunnenta tana kokarin goge number ta kashe waya gby da sauri ta ajiye wayar zuciyarta na bugawa da karfin gaske ta sunkuyar da kanta tana danne kukan dake kokarin fito mata ".

ya bude  murfin bayan motar ya jefa ledar hannunsa sannan ya bude   banagaren mazaunin  direba ya shiga yaja  Kai  tsaye fmc  hospital ya nufa a hankali ta d'ago idanunta nan ta fahimci asibiti ya kawota yayi parking Yana kokarin fitowa  yace "fito muje" ya faɗa yana ciccin magani .jiki a sanyaye ta fito daga cikin motar ya rike tsintsiyar hannunta gam  cikin nashi suka jera koina hasken fitilu ne  kowa ya gansu sai ya sake kallonsu dan bakaramin dacewa sukayi da juna ba  zaka d'auka su din mata da miji ne ,yayinda gabanta ya dinga  faɗuwa aranta  tace   "Allah Ka bani iKon tserewa yau daga hannunsa  ".
Tafiya   kad'an sukayi taga sun tsaya  a bakin wani  ƙofa  ya Kai hannu yana  knocking din kofar   daga ciki aka bashi izinin shigowa." shiga muje "babu yadda ta iya ta shiga kmr zatayi kuka  Sadiq  na ganinsu  ya miƙe  yana fad'ad'a fuskarsa da murmushin jin dadi  Dan bai taba ganin yayansa da wata  mace  ba sai yau shiyasa murnarsa a fili take da hannu ya nuna mata gurin zama ita Kuwa kallonsa take saboda tsananin kamaninsu zaka rantse tagwaye ne , babu shakka wannan mutumin dake gabanta  dan'uwansa ne km na jini dan kamar ta baci a natse muryarsa ta fito tmkr ta dan'uwansa   "father ya sunanta ne ?"ga tan a gabanka ta fad'a maka  sunanta tunda shishigi kake son yi ".

sadiq yayi murmushi  yana kallon tan  wacce ta dago ta kalli jaguwa sannan  ta d'auke kanta  ita dai addua take har lokacin ,shi kuwa sadiq ya kasa hakuri hakan ya tsinci kanshi da cewa "aunty nah  ya jikin naki?" ya sake  tambayeta cike da kulawa." da sauƙi!" ta basa amsa murya a sanyaye a natse sadiq ya soma haɗa kayan aikin da zai mata amfani dashi yana gama had'awa yace "miko hnnunki shiru tayi Taki mika masa sadiq ya    
kalli  yayansa,  jaguwa ya wani haɗe fuska yace "kiyi abinda yace mana karki batawa mutane lokaci  "
Hawayen dake makale a kwarnin idanunta suka zubo duk da kasancewarta likita amman   Allah yayita da tsananin tsoron allura muryarta na rawa tace "ni...ni banason allura a bani magani ".
"dole kiso allura  ko mutuwa zakiyi sai an Miki " cikin sanyin  jiki  sadiq yace ", father ka bita a hankali kasan mata akwai su da mugun tsoron allura "rabu daita munafurcin ne kawai  ita kanta likita ce  mutane nawa tayiwa allura?  murmushi sadiq  ya sake yi yana cewa " aha ai likitocin nan sun fi kowa shegen tsoron allura ganin tana ta bata musu lokaci  yasa jaguwa kamo hannunta tare da matseta gam  ajikinsa "bismillah sadiq kayi mata allura " sadiq ya soma k'okarin tsira mata ta makale  ajikin  jaguwa sosai  tare da sakin K'ara mara sauti ,wani irin harbawa jijiyar jaguwa  tayi da  karfi  take yanayinsa ya sauya   bayan hk  wani sanyi yaji yana taso masa tarayyarsu ta shekaranjiya ce ta dawo masa a hankali tsigar jikinsa suka dinga mkewa gbdy ya nemi natsuwarsa ya rasa    ana gama  mata allurar ya saketa dan idan suka cigaba da kasancewa haka komai zai iya faruwa dan  zai iya danneta a office din.
sadiq ya had'a mata  maganunguna  har dana zazzabi ya mika mata  yana sake mata Sannu  jaguwa yayi masa sallama  suka fito kmr farkon  da zasu shiga yanzu ma hakan ce ta kasance  taji kmr ta fixge daga hannunta ta kwasa da gudu ."

suka karaso Inda sukayi parking  suka tsaya abakin mota kamar ya sani ya bude mata sai data shiga ta zauna ya kulle sannan ya zagaya ya shiga bai   zauna  ba sai daya d'auke  wayarsa
ya zauna yana danna gefenta  yayi mamakin ganin wayar a kashe  ya kunna ya ajiye a ma'ajinta  tare da yiwa motar key ko cikakken minti biyar bayi da kunna wayar ba kira shigo da sauri zuciyar  tanweer ya shiga bugawa da karfi .
ta kame guri d'aya ya d'auki wayar da hannun d'aya yana dubawa yayinda hannunsa ke kan stearing  yana tuki sunan Abubakar Hamid ya gani yana yawo akan screen din wayar  da yake yana da truculler a wayarsa  ,bai gane ko waye ba ya dai d'auki wayar yana dauka yaji saitin muryar hade da Kiran sunan tanweer ...!wani wawon burki yaja a tsakiyar titi  ya waigo  yana kallonta "tanweer !!!  are you okay ? shiru cikin tsananin tashin hankali minister yace "Talk to dady  tan where are  you  ? "Inna lillahi ta furta a fili tare da  juyowa  da sauri Jin sautin muryar mahaifinta dake fita cikin tsananin tashin hankali  .
Kit jaguwa ya katse Kiran   tare da ɗauketa da barin  makauniyar  take hancinta ya balle da jini  ,wani kuka ta saki mai ban tausayi  ta bud'e baki zata yi  mgn ya sake yarfa mata wani  mari wannan karon gilmawar duhu ta gani acikin kwayar  idanunta ta sake fashewa da wani  sabon kuka tana neman d'auki tana kallonsa ya  bud'e  bayan  wayar ya cire sim din ciki  ya karya ya watsa a bakinsa  ...."

Mmn sudai


💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK
FREE PAGE
 WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686 alert  domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu  a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️17

A matukar  fusace ya bawa  motar  wuta  gabansa   banda  fad'uwa  babu  abinda  yake , ita Kuwa  kuka take  sosai  kamar  ranta zai fita   .
zuciyarsa  ke  wani   irin  ciwo  da  zafi  dan  idan akwai  abinda ya  tsani  gani  shine   zubar   hawayenta    sai  dai  a halin yanzu  baya jin  zai  iya  rarrasheta  ,zai  jure Jin  zafin  saukar hawayenta .hannunta  ta Kai  kan hannunsa  ta  rike  gam hawaye  shabe  shabe  kwance  a fuskarta ,
da  sauri ya waigo   fuskarsa   ya  kalleta   yana  zabga  mata katuwar harara  ,gashi  fuskarsa  gbdy  babu  annuri  , cikin muryar   kuka ta kira sunansa  "Adnan '!
Yana  jin ta yayi  mata banza   tare da d'auke  kanshi   ya maida kan  tukin da yake  yana jan dogon  tsaki   "me  yasa  Adnan  ? " me yasa  bazaka maidani   gidanmu  ba ?"
Shiru   yayi  yaki  ce mata Komai   dan ko  yace  zai yi magana muryarsa bazata  fito  ba saboda 'bacin rai  dake  daskare  a zuciyarsa  ,zubewa  tayi ajikinsa   ta  saki  wani  sabon   kuka  me  tsuma zuciya  tana cewa "kayiwa  Allah  da manzonsa  ka maidani gidanmu   nagaji ! nagaji !!  " .
bai ce  ta daina kukan  ba  haka  zalika  bai ce  ta  bar  jikinsa ba ya barta  tayi  kukanta , shi Kuma ya cigaba da  falfala gudu akan titi ."

Bangaren  minister  kuwa cikin   lokacin da  bai wuce minti  biyu 
 da   yaji  wayar  farko da sukayi da tanweer  ta mutu  ba   ya soma  neman   number     din  commissioner  batare  da  bata lokaci ba ya d'auka nan minister ya shiga  zayyano masa abinda  ke  faruwa .  cikin sauri  commissioner  ya  katse  Kiran  ya  kira  dcp   dake   rike da  halakin kula da  binciken  tanweer  kafin kace me  jimi'an  tsaro  sun hallara a gabansa ,cike da natsuwa ya soma magana "please  ku  maida  hankali sosai yanzu  nan  minster yace sun  gama waya da diyarsa  tana  1829 amman  ga  number data kirasa dashi  ya  turo  mana  ku tafi    kuna    tracking  din  number  ku samu location   Inda  gurin yake .
Nan   take  dcp   ya   amshi  number suka  fito  cikin  sauri suka shiga  motocinsu   suna tracking  din number   sai  dai yaki nuna musu location  saboda   number  bata shiga   gbdy  bare su  samu  location din da akayi  amfani da wayar  har  suka hau babban  titi  .
dcp  ya  kira commissioner  yana d'auka  yace "sir  layin  nan bai shiga ba bare  mu  samu locacin din Inda suke   amman zamu k'arasa 1829 plaza  dake igando  ko zamu dace a  nan  akayi amfani da layin yanzu dai    zamu cigaba da  Kiran layin har mu Isa  ."Allah  yasa  ba fahimta yayi ya kashe  wayar ba ? "Dan Allah kuyi aiki yadda ya  kamata  dan yarinyar ta kira  cikin mawuyacin hali  da  alamun tana cikin  tsaka  me  wuya, wannan  wata  dama ce me  kyau da muka samu  kada ku bari ta subuce mana  "okay  sir inshallahu zamuyi iyakacin  k'ok'arinmu ".
Commissioner  ya katse Kiran yana juyi     akan  kujera  gashi dai  shirin tafiya gida yake Kiran minister ya same shi Amman a yanzu ya zama dole  ya    fasa  tafiya  gida ya zauna zaman jiransu idan ta kama ya kwana ma a office zai yi ".

 gudu  motocinsu  suke  sosai akan titi tare da jiniya ,kowacce mota ta gansu  sai  ta  kauce ta basu  hanya  ,irin  gudun da  sukayi  yasa  cikin kankanin  lokaci suka k'araso 1829 suka  faka  motocinsu suka  firfito cikin sauri  wasu suka nufi   babban get  din   plaza  din , yayinda wasu suka  tsaya abakin kofar motocinsu  rike da  bindugu   suna mazurai kamar  wasu  zakuna ,mutane kuwa tuni suka fara bawa kafarsu iska kar tsautsayi   ya  rutsa dasu  .
a hankali  police  suka kusa cikin plaza din  ,bincike  suka  fara yi kafin  daga  baya suka bukaci  ganawa da manager   gurin  , Kai  tsaye  aka Kai su Inda yake , tun kafin su fito da Id card  dinsu ya  fahimce su din su waye ,  nan take ya rikice  yana  kallonsu .Jimi'an  tsaro  ne suka nuna masa I'd card  "akwai wani mai laifi daya shigo plaza dina a mintunan da suka gabanta ko zamu iya ganin cctv camera dinku ?muryarsa na rawa yace babu matsala yalla'bai  ya juya ya soma  lalu'bo daukar yau dan Daman a qunne yake , a hankali suke kallo har ya kawo zuwa sanda suka shigo babu wanda ya shigo  me irin  fuskar  da  suke  nema  tare da yarinyar dan haka suka juya  cikin sauri  suka shishiga motocinsu suka nufi wani  branch  din dake ikotun ."

Jaguwa  na isowa gida yayi parking yana ƙoƙarin bud'e mota  domin ya  fito  da sauri tanweer ta rike shi gam  ajikinta   "dan Allah kada ka sake shigar dani cikin  gidan  nan  "ya  waigo a natse  sai dai a fusace yake   kallota sai daya d'auki second biyar yana kallon  sannan  yace "wai meke damun tunaninki  ne ?"me ya samu  gidan  nan   da kike son barinsa bayan rayuwarki ake k'okarin karewa ?
Tayi shiru tana kallonsa  da nazarin maganarsa kullum maganarsa kenan rayuwarta yake son karewa "ka fad'a min waye wanda yake son d'aukar rayuwata da har kake k'okarin karewa  ?  tayi   masa tambayar jikinta na rawa tare da  sheshekan kuka."ganin  yadda ta rikice  yasa  ya kamo hannunta  ya  rike  cikin nashi  gam suna jin dumin juna   "ki  natsu zan  fad'a miki amman ba yanzu ba "ni dai ka fad'a min ko waye shine samun kwanciyar hankalina  da samun natsuwar zuciyata, Idan ma
ta kama  zan hakura da gidanmu  na cigaba da zama da Kai ,"ko Kuma ka siyo min sabon layi ka had'a min  waya sannan  ka fad'a  min ko waye  sai na fad'awa mahaifina  a d'auki  mataki   akansa , wallahi nayi  maka alkwarin  bazan  fad'awa  kowa ba ."

Yayi  d'an murmushin gefen baki  wanda  ya  bayyana  ainihin  sirrin kyawun  da Allah yayi masa "Ina  ce  kince  zaki  tona  min  asiri  byn kin bar gidan nan ? "tayi saurin  girgiza masa  Kai alamun a'a "bazan yi ba na maka wannan alkwarin duk runtsi duk wuya bazan aikata hakan gareka ba muddin ka fad'a min  ".
"kada ki damu idan kin shirya  fad'awa  duniya  kiyi   karki   fasa , idan kin koma  gida ki tara gbdy 'yan jaridan garin nan ki sheida  musu cewar Adnan dan fashi ne abinda nayi Imani dashi   Allah  bazai  basu  nasara akaina  ba ,  mahaifiyata tana tsaye  a  kaina da adduointa haka mutane  da dama suna min addua , duk da Ina  aikata  zunubai   Allah zai   tsareni   daga sharrin duk wani  jami'n  tsaron  albarkancin  adduar mahaifiya data mutanen kirki  ."
shiru tayi tana  kallonsa hawaye na gangaro mata cike da sanyin jiki  ta zare hannuwanta dake  cikin  nasa  ta soma k'okarin zare jikinta daga garesa  ,yana  kallonta tayi baya da kujeran da take zaune ta  maida jikinta ta kwanta  tana mai runtse idanunta ,  yatsun hannunta ya kamo  bai san yadda akayi ba ya tura cikin bakinsa  ya  fara tsotsa , wani iri ta dinga ji a sansar jikinta kmr ana zarar ranta , tayi k'okari cirewa ya rike yatsun  da  karfi  yana cigaba da tsotsa kamar ya samu sweet  sai daya tsotsa son ranshi sannan ya cire bakinsa ya ciro hanky ya goge mata hancinta dake digar  jini  yana cewa "ki kwantar da hankalinki zan  fad'a miki ko waye amman  ba yau ba   ". yana  gama fad'ar haka ya sakar  mata  hannu ya    bud'e  murfin motar ya   fito ya  zagayo  bangarenta da  take  ya  bud'e mata  ta fito  jiki a sanyaye,  ya d'auki ledar maganin  da aka  basu   ta dubeshi fuska da hawaye  .
bai tsaya bi ta kanta ba ya riko    hannunta  ta turje  alamun bazata ba ya juyo ya watsa mata  idanunshi fuskarsa a d'aure  "karki  min  taurin kai " ya  fada tare da sake  juyawa  suka shiga cikin  gidan bakinsa d'auke da  addua (bismillahi  walajna
wa  bismillahi  kharajna wa'allahi rabana tawakkalna ) tana jinjinawa  girman  iliminsa,  gashi tantiri  gashi  malami   ta  fad'a  acikin  ranta .

Kai tsaye d'akinta  ya shiga daita  ya  kamota ya  zaunar daita abakin gado ya janyo  kujerar  madubi ya zauna yana  bin  d'akin da Kallo duk ta hargitsa   d'akin ko d'azu daya shigo yaso yayi magana yanayinta yasa ya share    ya  girgiza Kansa  sannan ya  fuskanceta  ,baya  jin dadin yadda  take d'aga  hankalinta  akan gida ,
shi  bashi  da niyyar  cutar daita , ko abinda ya faru daren  shekaranjiya ma  ba yin  Kansa  bane itace sila ,  tillastawarta ce    ta  janyo  hakan ta faru   ban cin haka babu abinda zai kai shi aikata zina daita.
"tan ...!
Ya kira sunanta cikin kasalalliyar muryarsa yana  sake  kamo  hannunta tare  da kafeta da  tsumammun idanunshi  masu  kashe mata sansar  jiki , d'ago idanunta tayi ta zuba masa tana sauraronsa tare da jin wani iri a sansar  jikinta duk sanda zata kalleshi sai taji wannan yanayi wanda babu tantama na qunar da take masa ne . "wanda  ya  tura mu fashi gidanku  bashi da  hannun  cikin zamanki  tare damu , rikeki da nayi Kuma nayi amfani da maganar da mukayi  dashi  a  karshen maganarmu  cewa "yayi  yana da wasu  target  akanki  a dawo dake  ya aiwatar da nufinsa  wannan  shine dalilin da yasa  na rikeki  ba dan raina na so ba ".

"Dan  ranka  na so dai ka rikeni  idan ba haka ba meye aciki  ? tayi maganar a  matukar fusace  " ka mayar dani  Inda ka d'auko  ko ka fad'i  wanda ya turaku  gidanmu  kawai  a wuce gurin , ya runtse idanunshi  yana nazari wasu  abubuwa akanta .
ta dubeshi  idanunta cike da ruwan  hawaye "adnan ka d'auke ni a daren nan  ka mayardani  gidanmu   dukkanin  alamun  sun nuna min  iyayena na cikin tsananin damuwar rashina da.... ...."
"na  sani Kuma zan mayar dake amman ba yau ba ki bani lokaci wallahi zan mayar dake akwai binciken da nake da  zarar  na gama zamammu  tare  zai zama  tarihi  ".
ta  matso kusa dashi sosai har gwiwowinsu na gogan juna "naji amman dan Allah ka sanar dani Wanda ya tura ku gidanmu  fashi ?ya girgiza mata Kai  sannan yace "idan ma kika ji ko waye ba lallai ki yarda ba, Killa Kuma  ma kiji kin tsanani kanki  sannan tabbas wasu rigingimu zasu  faru  saboda kusancin dake tsakanin mahaifinki da wanda ya bamu  aikin ." ta kamo hannunsa  ta rike gam cikin wani yanayi "cikin   dangin dad dina ne  ko na mum dina ke son ganin bayan iyayena  da ni kaina ? ya girgiza mata Kai alamun "a'a"to sanar dani dan Allah zan barwa cikina bazan ta'ba fad'awa  kowa ba  ".

Shiru yayi yana nazari akan  lamarin ya fad'a mata ne ko ya shareta "abinda yasani  tabbas  idan batun
ya fito ya sa'bawa dokarsu domin a aikinsu babu wannan tsarin ,duk  runtsi duk wuya ba'a tonawa juna asiri tunda tun farko da wajewa ake tsara komai ba'a juyawa juna baya.
ta katse masa tunani ta hanyar cewa  "kana  ganin zan iya tona maka asiri ne ?"  Allah na  dai fad'a ne amman  bazan iya aikata hakan  ba. "na sani  dan  fad'awa soyayya  ba  abu  ne me sauki  ba  da  har   zaki tona asirin masoyinki I know  you  can't  do that to me tanweer    bazaki  iya fad'ar  komai akaina ba   saboda qaunar da  kike min."

ta lumshe tsumammun idanunta na second biyu tare da jan tsaki acikin zuciyarta dan muddin tayi a fili balai zai mata a hankali   ta bud'e idanunta  akan kyakkyawar  fuskarsa  "ba  wannan story din   na  tambayeka ba ,ka ajiye  batun wani soyayya dan a yanzu  babu ita acikin  raina buqatata   ka min bayani wanda yasakaka aikin  bana son jan  aji  da salo  tayi  mgnr tana murgud'a masa  k'aramin bakinta .yayi  murmushin gefen baki yace "to  da gaske zaki rufa min asiri agurin iyayenki ? da sauri tace "me zai hana in bukatar hakan  ya  taso ?"
"sannan  Ina fatan zaki fahimceni  ?" ta gyada masa  alamun zata fahimcesa, shiru tayi tana jiran ya faiyace mata  Komai  kawai taga ya zare hannunsa ya mike tsaye tare da zura hannuwansa duka cikin aljihunsa , a hankali ya juya mata baya yayi taku zuwa  daf da kofar  bayinta  ya tsaya tare da waigowa yace "ni zaki yaudara  ko ? ta girgiza masa Kai alamun "a'a  "karya  kike  tanweer yaudarata  zakiyi  dan  zuciyata  bata yarda dake ba   duk  da d'arurar soyayyata dake cikin kwayar idanunki da zuciyarki   kina son na fad'a  miki wanda ya tura mu fashi gidanku sai  ku taru  ke da jami'an tsaro ku  cutar  damu ko  ? 
yana rufe baki yaji ta rungumesa tsam  ta bayansa tana cewa  "wallahi kaji na rantse maka  bazan sheidawa kowa ba ,bazan zamo me Saka hannu gurin cutar da kai ba  ,ya juyo daita gabansa suka  fuskanci juna  "dame zaki gamsar  dani  bayan tun farko kice da bakinki kika fad'a min zaki tona min asiri ?" ta tsugunna gwiwowinta  biyu a kasa ",ka  yarda dani Adnan na rantse  maka bazan aikata  hakan  ba ".  ya tako  a hankali ya tsugunna a gabanta "na sani bazaki fad'a ba amman ni ba mahaukaci bane da zan fad'a miki wanda ya tura mu a aiki gidanku ,  babu wannan ajandar  acikin aikinmu  ko gaban alqali za'a Kai d'aya daga cikinmu da wahala ya fad'a  ,kada ki damu ki bar son jin komai  gida ne dai zan kaiki a duk sanda wa'adi ya kai   ya fad'a yana janyota jikinsa  ya makaleta tare da Kai bakinsa daidai kunnenta   "ki K'ara natsuwa  da  jin  dumin jikina ."

Tayi  shiru zuciyarta na quna  da  tuttukin bakinciki ,duk  abinda take  tana  yi  ne dan ya fad'a mata wanda ya bashi aikin amman shine zai  rainawa kansa hankali  yace ita ya rainawa  ?"   cike da matsanacin  bakinciki  fixge jikinta  tace " kar Allah yasa ka fad'a kuma Allah ya Isa da rungumata da kayi ban yafe maka ba  mugu kawai  me   zuciyar  dutse  duk  irin rantsuwar dana  yi maka bai sa ka  yarda dani ba  saboda muguwar zuciya irin taka  ." cikin  dariya ya sake  janyota jikinsa sosai ya  rungumeta tsam yana busa mata numfashinsa   tare da cewa "kada ki damu da irin zuciyata  dan babu abinda zai qareki dashi  Allah ya Isa  Kuma daman allah   isashe ne ko  baki ce  ba  , wayonki yayi  matukar  burgeni I love  it keep it  up  yayi  mata  kiss  a goshi sannan  yace "zaki cigaba da zama da Adnan har zuwa sanda yaga damar  maidake gidanku   sannan kiyi k'okari ki rage wannan  soyayyar da kike  masa  idan ma da hali ki cireta  gbdy  ya saketa ya koma jikin window  ya tsaya yana kallon farfajiyar  gidan  kusan minti biyar yana tsaye sannan ya juyo "me zaki  ce akawo miki  kici  ki sha magani ? babu abinda zanci ta fad'a a fusace  tana dubansa hawaye na tsiyayowa akan quncinta  "daman Kin saba  kwana da yunwa  idan shi kike ra'ayi  fine  ,I don't care ya nufi  kofar fita daga d'akin ya barta cikin tsananin damuwa da sake  shiga tashin hankali ."

Yana fita number minister ya fara nema kira uku yayi kafin a d'auka ,hajiya zainab ce ta dauka cikin   sanyayyiyar   murya  tace" hello yana jin sautin muryar ya fahimci mahaifiyar tanweer ce dan bazai manta da muryar ba da irin kuka da kururuwan da tayi a daren  da zai taho da tanweer muryarsa a dikile ya soma magana cikin Isa " Ina minister ?ta waiga a sukune ta Kalli Inda minister yake zaune aqasan tayis yayi tagumi da hannunsa d'aya cikin tsananin tashin hankali "wake magana ?ta tmby cike da faduwar gaba "babu buqatar sanin haka sai dai dalilin Kiran shine ki fad'awa mijinki idan yana kusa " cewar ya dakatar da kawalayen daya tura haushi  gari dan nemammamu  wato jami'an tsaro  idan ba haka ba zai zama  sanadin rasa rayuwar diyarsa tanweer   ".
nan take jikin hjy zainab ya kama rawa hawayen dake makale a kwarnin idanunta suka sauka akan quncinta , a hankali ta soma karanta hasbinallahu wa ni'imal wakil  tana  cigaba da  sauraransa "ki fad'a masa ya janye if not you'll lose your daughter  ko Kuma musa ayi reping dinta mu yada a social media  yana gama fad'ar haka yayi disconnecting din kira yana fesar da iska.
wani kuka hjy zainab ta fashe dashi ta zube kasa tana  furta kalmar  " inna lillahi wa inna ilaihi rajiun da sauri minister ya matso kusa daita dan tunda ta d'auki wayar tana kallonsa shima ya tattara hankalinsa da natsuwarsa gurinta a rud'e yake tambayarta "menene zainab me akace miki   a  wayar  da'aka  kira ?" dan girman  Allah ka kira   office  din commissioner yanzu yanzu ka  sheida masa a tsaida jami'an tsaron nan bana son na rasa tanweer ,bana son wani mummunar abu ya faru daita  iya abinda ta fad'a kenan ta zube jikinsa tana sake fashewa da wani sabon kuka  numfashinta na sama

Please Login or Register in order to submit comment