Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

tsaya ba ya  nufi d'akinta  ya  shimfideta  akan   gado   idanunshi 
na  kanta  yana tsaye yana kallonta sai ga anas ya shigo d'akin cike da tashin hankali yana ganinsa ya janyo blanket ya lullu'beta yaja ya tsaya tare da rungume hannunwansa duka a qirjinsa cikin tsananin damuwa
anas    ya  zubawa tan Ido yana kallonta Ko cikakken minti biyar bai  yi ba sai ga jabir, jubi ,kamil sun shigo  .

duk  suka  zuba  mata  idanunsu suna kallonta  kowa da abinda yake sakawa a cikin  ransa a hankali  jaguwa ya runtse  idanunshi tare da Kai hannunsa daidai saitin zuciyarsa dake bugawa da sauri sauri ,anas ne yayi karfin halin tambayarsa abinda ke faruwa daita "daman itace babu Lafiya me ya sameta ?"aikin wancan tsinanniyar yarinya ce ya fad'a a tsawace "wacce yarinya kenan ?anas ya tambayesa a rud'e "wace ce banda waccen yar iskan zahra din asiri tayiwa yarinyar mutane amman na rantse da Allah sai naci ubanta inga uban daya tsaya mata acikin garin nan"take it easy jaguwa Kai ya akayi kasan tayi mata asiri ? tsaki jaguwa yaja da karfi idanunshi na kan tanweer dan yasan daman haka zai ce tunda baya ganin laifinta  .
a tsanake jabir yace "Allah ya kyauta yanzu dai me ye solution dan  naga kmr yarinyar bata numfashi ?ga tan nan dai tana numfashin sai dai ba sosai ba da kyar na samu numfashinta ya dan dawo wallahi muddin wani abu ya ta'ba lafiyarta zan shayar da Zahra mamaki inji cewar jaguwa ,gyada kai suka yi  gbdy sannan jubi , jabir ,kamil suka juya suka fita daga d'akin dan babu me iyawa dashi idan yana cikin fushi sai anas ."

"kayi hakuri jaguwa ba lallai abinda kake zargi akan zahra  ta aikata ba anas yayi mgnr yana dafashi a fusace ya buge masa hanun yana cewa "Daman nasan haka zakace  tunda kafi qaunar dani "no !no !! jaguwa saboda qaunar da zahra take maka yasa nake kulata taya ma zaka had'a matsayinka daita gsky karka sake min hk banaso Kai fa jinin jikina ne  ita Kuwa fa ?  jaguwa yayi shiru tare da  tsurawa tanweer Idanunshi wasu kwalla masu zafi suka zubo akan kuncinsa cike  da  takaici da nadamar abinda ya aikata mata, nadama irin wacce bata da amfani .
anas yayi matukar mamaki ganin jaguwa ya tasa tanweer gaba yana kwalla "lallai haka rayuwa take tana cike da abun mamaki "jaguwa ne yau yake kuka akan mace ? "Jaguwa !
Anas ya kira sunansa "yana jinsa yayi masa banza tamkar ba dashi yake mgn ba " kana mutuwar son yarinyar nan amman Kaki yarda da kana sonta , Kalli yadda kake zubar da hawaye akanta ,Kalli yadda tausayi mai hade da soyayya suke dawainiya da Kai ,ka yarda jaguwa kana sonta ka daina karyata zuciyarka , ka daina hasashen bazaka iya sonta ba, ita fa rayuwa kafi ni sanin rubutaccen alamari ne daga rabbi, hatta wannan Sana'ar tamu qaddara ce Killa da iyayenmu sun san zamu zo duniya mu kasance yan fashi wallahi da tuni sun kashemu da hannunsu ".yayi shiru yana dubansa "ka yarda Kuma ka amince kana sonta sai mu taru mu bar wannan rayuwar ,zamu tayaka inganta rayuwarka jaguwa domin sama maka farinciki .........."
"ka daina fad'a min haka anas banaso ji wannan kalmar  daga bakinka sau nawa zan fada maka tausayi ne ba so ba ?"yayi saurin karyata amininsa taya ma zai sota byn tanweer tafi karfinsa a aure, waye shi ,? waye yan'uwansa a fad'in kasar nan ?
duk da a yanzu ya taka matsayin da kudi ba matsalarsa bane amman yasan aurenta zai masa wahala, ya sake fuskantarta sosai yana Jin kamar yayi mata numfashi ,sosai  ya  fad'a kogin tunani hankalinsa ya bar duniyar da yake ciki ya Lula wata duniyar dabam ."

"Bamu saba boyewa kanmu komai Daya shafi rayuwarmu ba ,jabir, jubi kamil ,duk tare suka ganmu kana fada min  gaskiyar dake cikin zuciyarka akan komai amman akan wannan yarinyar ne kawai ka kasa fad'a min matsayinta a zuciyarka ,kana tunanin zan hanaka soyayya ne da ita ko me?wallahi kamar yadda kaji na fada maka ni me rungumar komai ne akanka Koda kuwa mutuwa ce, Ina maka soyayyar da zan iya sadaukar da rayuwata akanka, karka manta mu din masoyan juna ne da muka yarda da juna Kuma muke son juna saboda Allah, zuciyata ta yarda ta amince kana son yarinyar nan so me tsanani ko dan tana diyar minister yasa kake gudun fallasa sirrin soyayyarka ?
"ko d'aya  bana  dai sonta ne " kama saukakawa kanka nan kusa ma ammi zata min mata ka san kuwa zuciyata bata da wani zabi daya wuce nata dan haka ka cire wannan tunanin a ranka ya k'arasa maganar still idanunshi na kanta " yana dasa Aya anas ya juya a hankali ransa a matukar bace.

"ta yaya gashi yana kallon tsagwaron qaunar yarinyar a idanunshi amman yake ja inja dashi ? ranar ce rana ta farko da jaguwa yayi masa abinda   har yaji ya tsaya masa arai , Jin motsin Bude  kofar d'akin ya sa jaguwa ya waigo da Kansa anas ya gani zai fita daga d'akin shima kmr ya bar d'akin sai ya tsinci Kansa da kasa aiwatar da hakan yaji bazai iya barinta ita kad'ai ba dan haka ya hau gadon ya janyota ya d'aurata a saman  faffadan qirjinsa, a hankali  yana shafa bayanta, ajiyar zuciya ta fara jerawa tamkar wacce ta sha gudu tsira  ,qara   makaleta jaguwa  yayi   tamkar  wani zai kwaceta a hannunsa "Anya   kuwa adnan  baka  fara  son yarinyar nan ba ?" ya  tambayi kanshi yana shinshina wuyanta" ka fara sonta mana tunda kana tsananin qaunar kasancewa daita zuciyarsa ta bashi amsa da hakan  "Ina  ba  haka bane tausayi ne kawai babu wannan a tsakanina daita ,gyara mata kwanciya yayi sosai ta yadda bazata takura ba ya sauko daga kan gadon zai fita yaji ta riko hannunsa waiwayota yayi zuciyarsa na dokawa da matsanacin karfi ya kalleta sosai bacci take da alamun ma bata san ta aikata hakan ba , ya fito daga d'akin zuwa bedroom dinsa kana ganinsa kasan baya cikin haiyacinsa zama yayi yana neman layin sadiq ya kira sakamakon ganin missed calls  dinsa ya d'auka yana d'auka yace "father komai normal dai ko ka Isa gida lfy ? "Normal sadiq komai  daidai na gode da kulawarka dan uwana , sukai sallama kmr ya nemi layin zahra dan yasan adaidai wannan lokacin idanunta biyu Killa ma tana can yawon ta zubar amman ya share yana zaune  zata zo ta samesa .."

Can  bangaren  IPO  kuwa  yana ganin dawowar jaguwa yasan sun yi missing dinsa wayarsa ya ciro ya shiga neman number dcp baba abare  yana d'auka yace "sir Kuna Ina ne  ? daga can bangaren dcp yace muna kan titi har yanzu bamu ga dawowarsa  ba "gsky kunyi missing dinsa dan ya dawo gida "shit ...." dcp ya furta a fusace sannan ya cigaba da magana "amman a juri zuwa rafi wata rana tulun zai fashe "wannan haka ne sir idan kere na yawo zabo na yawo  wata rana zasu  had'u ne ",ai kuwa haduwarmu bazata yi kyau ba dan bazan Kai shi ga office din  hukuma ba bare a samu damar bada belinsa tarwatsa masa Kai zanyi kowa ya huta yana gama fad'ar haka ya katse Kiran a fusace  yana bawa yaransa umarni ."

*****

Washegari da misalin karfe takwas ya fito zuwa falonsa sanye cikin gajeren trouser  baki da riga fara mai hula da ratsin baki ,sanye da takalmi fari mai azaban kyau yayi kyau sosai sai dai fuskar nan tashi a murtuke tamkar jinin sarauta sannan kallo d'aya zaka masa kasan zuciyarsa a dagule take jira kawai yake a tabashi ya hau mutun , ya d'auki remut ya kunna tv ya Kai  chennel  zuwa na labarai  yana ƙoƙarin  zama friends dinsa suka shigo suka zagayesa har kamil Suma cikin shiga ta alfarma atare suka had'a baki gurin cewa"ya lafiyar yarinyar nan ?Kamar bazai ce Komai ba har sun fidda rai da zai Yi mgn suka ji yace "alhamdulillah har yanzu dai tana bacci  ".Shiru sukayi dukkaninsu babu wanda ya sake yin magana sai numfashi da suke fitarwa idanunsu na kan tv yayinda  anas ke son yi magana akan zahra zata zo dan tun safe ya kirata ya sheida mata abinda ke faruwa  sosai ta daga hankalinta  ,amman yadda yaga jaguwa ya had'e rai yasa ya kama Kansa ya ciro kwandala  a cikin aljihunsa ya murza akan center table din dake gabansa  take ta fara juyi a karshe ta kife ya tsurawa kwadalar Ido kawai yana kallonta  ."

Suna zaune sai ga zahra ta shigo cikin doguwar riga marun colour tana karairaya tana gama tsayuwa a tsakiyar falon onexpecting taji jaguwa ya mike  ya ɗauketa da wani gigitacen mari da sauri ta dafe daidai Inda ya mareta tana dubansa "ki fita rayuwata  Zahra , ki tsaya matsayinki"  zahra  tace "me yayi zafi haka Adnan ? "dazu anas ya kirani yake fad'a min abinda kake zargina akai amman ka sani ......
"wani marin ya K'ara kifa mata sai data ga taurari masu duhu "amman kasan me din ubanki ?"me zaki fad'a min na yarda dake maci Amana kawai,  daga karunwaci kin koma bin bokaye saboda ke katuwar jahila ce wannan ya zamo Karonki na farko ya Kuma zamo na karshe babu ruwanki da yarinyar nan wallahi muddin wani abu ya sameta sai na kasheki da hannuna , wai ma meye hadinki daita? ni kike wa kwakwa ni Kuma nace banayi ko dole ne  sai na aureki ?ya tambayeta yana sake tsare girar kasa da sama. "duk ta rud'e sai wani gumi take fitarwa cike da matsanacin firgici tace "ka yarda wallahi babu hannuna ci...ciki " ta k'arasa maganar tana in Ina gani yadda yake mata mugun kallo yasa ta soma neman hanyar guduwa dan kallon  fuskarsa kad'ai ya Isa ya tsorota mutu da sa mutun ya shiga hankalinsa sam sam babu alamun wasa atare dashi kafa yasa mata sai gata ta zube kasa bisa gwiwowinta tana kallonsa cikin muryar kuka tace "ni kad'ai kake bi bare kayi tunanin nice na aikata abinda kake zargina? Ina Jin tsoron Allah Adnan bazan iya ......"shiiiiiiiii ! banason Jin komai d'aga bakin makira irinki ."
"Zahra!
ya kira sunanta muryarsa a tsarke ta zuba masa Ido tana amsawa da" Na'am "babu tsoron Allah"n daya halicceki acikin zuciyarki dan hk nasan zaki iya aikata komai akan cikar burinki ,masu kyakkyawan zuciya da tsoron Allah su suke tsoron aikata mugunta ke Kuma baki da ko daya aciki "yayi shiru yana numfasawa sannan ya cigaba da mgn "daga yau idan kika sake shiga harkata zan mugun baki mamaki kuma dan Allah karki cire hannunki akaina da duk wacce zaki ganni idan Kuma kinki yiwa kanki kiyamul lail zaki hadu da cuuttuka ,sannan zan ganar dake da yaren da zaki gane yana kaiwa nan yace " ki tashi ki bani guri bana son ganin wannnan fuskar taki ".

"naji zan tafi amman kayi hakuri kayi bincike sosai akai muddin aka tabbatar maka  Ina d'aya daga cikin wad'an da suka aikata wannan laifin ka min hukuncin da yafi wannan "wani bincike zanyi bayan nasan babu me shegen naci a rayuwata kamarki ?ya matsota sosai ya cafki makoshinta idanunta suka yo waje "ki fad'a min gsky kece kikayi mata asiri ?ta shiga girgiza Kai alamun a'a "bazaki fad'a gsky ba ? girgiza masa Kai ta sake yi  anas ya taso ya rikesa karka yi kisan Kai Adnan "ka rabu daita  karka kashe yar mutane "kace mata ta fad'a min gsky da bakinta
"me yasa  tayi wa yarinyar mutane  asirin data kawo min kanta gareni na aikata abinda ban yi ra'ayi ba? ya fad'a yana filinging daita sauran kad'an kanta ya bugi bango anas yayi saurin riketa  yana bawa jaguwa hakuri .wani sanyayyayen numfashi Zahra  ta sauke da kyar tana jin dadi aranta burinta ya  cika tunda ya kusanceta rabuwarsu tazo duk nacinsa dole su rabu  ,abokansa kuwa da Ido suka bisa suna mamakin jin furuncinsa ,me yasa kika yiwa yarinyar mutane  asirin da ta kawo min kanta gareni na aikata abinda ban yi ra'ayi ba?  suka tambayi zukansu suna dubansa  fuskokinsu d'auke da qarin bayani .

"Anas kaji abinda yake fad'a , dan jarabansa ya ciyosa ya kwana  da  yarinyar mutane shine zai d'aura laifina akaina , kasani babu  hannuna  acikin wannan aika aikan  " ,jaguwa  juya mata baya  ya tsuke fuska alamun bai son jin komai daga bakinta muryarsa a tsawace yace "anas ka sallameta daman  Kaine kake gayyatota  zuwa gidan nan " da sauri anas  ya riko hannunta ya nufi kofar fita daita "anas ka sakeni na fahimtar dashi gaskiya "bazai ta'ba fahimtarki ba kije kawai dan Allah nima daga yau karki sake kirana na yanke muamula dake bazan Kara kiranki ba banason na samu matsala da abokina, aminina ,farincikin rayuwata .
fixge hannunta tayi daga cikin nashi adaidai lokacin da suka fito zuwa haraban gidan ta tsaya a hassale tana  dubansa "ka dade baka daina kirana ba ,bazan  kiraka ba shima bazan kirasa ba Amman na rantse sai Adnan ya dawo ya nemeni da kansa ka rubuta ka ajiye a Inda bazai goge ba ..."

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK
FREE PAGE
 WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686
alert  domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu  a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️16

"Kenan   da   gaske  kin aikata  abinda   yake   zarginki   akan shi  ?" idanunta  da suka  rikid'e sukayi  jazur  ta cigaba da  kallon   anas  wanda yake  tsaye  a  gabanta yana  huci kamar zaki  dasu "eh  na  aikata  Kuma   bazan  tsaya  iya  nan ba  ta  fad'a a matukar fusace  "  zan   d'aura  daga   Inda  na fara , zan tabbatar  da na  azabtar da   yarinyar  nan   da azaba  mafi   muni   , ba  dai  duk akanta   ya mareni  ba?"  ya mareni  akanta anas , ya ci  mutuncina   akanta  ya wulakantani a rita lori akanta ,wallahi   ya   kwana da sanin   zan fanshe  duk abinda yayi min  akanta   'zan  mata  azaban   da  rad'ad'insa  yafi  zafin  dalma ,  zan   rikirkita  mata  rayuwa  zan....."saurin   dakatar  da  ita  yayi ta  hanyar  buga  mata wata razananniyar  tsawa  yana cewa  "enough !
"karki  fara  zahra  dan bazaki   ci  riba  ba , wad'an  da  ma  suka fiki  sunyi  sun   hakura  sun barshi  dan ba zasu iya ja dashi  ba   domin shi din  dokin  tsere ne  bazaki iya  karawa  dashi ba ,shi  guguwa  ne idan ya  tashi  zai  tashi da rayuwarki  , zai  juya  rayuwarki  daga sama  zuwa  kasa ki rasa gane  kanki ......"ya k'arasa maganar  yana nuna da yatsansa .

"Zahra !

Ya  kira sunanta cikin tsananin  'bacin rai " ki tsaya   daga  Inda kike idan   ba  haka ba  ki shiryawa   gudun  tsere da  mutuwarki  , dan akan  ki ta'ba wannan  yarinyar  gara kin  rungumi mutuwa  da hannuwanki." Adnan  yace   bai sonki ya nuna  azahirin   bai sonki, tunda  ba  tare aka halliceki   da   soyayyarsa ba  ya kamata    ki  hakura ki rabu dashi ki  tsira da rayuwarki  dan  akan  yarinyar nan  ba zai raga  miki  ba  zai iya  destroyed  din rayuwarki,  ki  manta da kin ta'ba muamula da Adnan a rayuwarki  ". wannan  shine  abinda  zan  fad'a  miki   idan  Kinga dama ki d'auka ki  cire hannunki  akan  mugun nufinki  ki zauna  lafiya idan kinga dama ki cigaba kece zaki kare rayuwarki a  nadama  ".

Tunda  ya soma magana zuciyarta  ke bugu  very  fast ta kafe shi da   idanunta   ta cigaba da kallonsa  ,a yau gbdy babu  sauran  burbushin tausayin  data  saba hangowa  acikin kwayar idanunshi  a duk lokacin da hargitse ya shiga tsakaninta  da adnan , yau  ce  rana ta farko da anas yayi  hannun riga daita . ka'fafunta ne suka  kasa d'aukarta ta durkushe kasa  bisa gwiwowinta tana  wani irin kuka tana cewa "kasan  kuwa  yadda nake ji a zuciyata ? "maganganunka suna huda min    zuciya, me yasa  zaka    nisantani  da  Adnan  ? ya kalleta cike  da  matsanacin  bakinciki  dan gbdy ya  fuskanci  bata  da niyyar saduda  shi kuma  a yau gbdy  babu  wannan tausayin da yake ji nata,  da tayi  silar rabashi da masoyinsa  da yafi qauna akan  komai a rayuwarsa gara ya  yakiceta  ta  karfin tsiya  sunyi  hannun riga  daita "amman kai kana ganin zan iya rabuwa da Adnan dan yace bai sona  ?ko kana tunanin zan iya daina sonshi  ne ? Me yasa zaka ce na manta da soyayyata ?  "haba anas  idan kayi min haka baka kyauta min ba ,yanzu adalci ne  daka nuna  kafi   bukatar  rabuwarmu dashi   ?
ya gyada mata Kai alamar"eh! " cikin firgici da tashin hankali ta shiga girgiza masa kanta  sannan ta cigaba da magana "ada tunanina kana sona da Adnan ne  a she duk ba haka bane karya ne baka qaunata dashi  ? to bari kaji  in fad'a maka maganganunka  ba zai sa  na  fasa duk abinda nayi niyyar aiwatarwa  ba  ko da kuwa zan mutu  ." ta  k'arasa  maganar tana sheshekar  kuka  "karki fasa  zahra bazan baki  hakuri  ba  kije kiyi  duk  abinda zakiyi amman Ina tabbatar miki wahalar banza   zakiyi dan ba zaki yi nasara ba hasarar  kudinki  da lokacinki  kawai zakiyi yana gama fad'ar haka yace ki  tashi ki  'bace min da gani yadda Adnan baya son ganinki  nima hakan take gareni  ".

Batace  masa   komai ba ta  mike da  kyar ka'fafunta na rawa  ta juya  ta soma tafiya  hawaye masu zafi  da ciwo   na sake   zubo mata akan  quncinta , zuciyarta bata ta'ba karaya ba atun sanda  jaguwa yake  furta mata kalma bai sonta sai a yau da anas ya sake maimaita mata  , duk da ba yau ta saba jin kalmar baya  sonta daga bakinsa  ba amman ciwon na yau daban ne a cikin zuciyarta sannan  ya mugu  mugun  tsaya mata  arai   ya d'aga mata hankali ya dagula mata lissafin tsarin rayuwarta   data shirya  dashi , Kuma duk runtsi  duk wuya sai tayi abinda zai furta mata  Kalmar so  da bakinsa , sai ya dawo  yayi  kuka da idanunshi yana rokon ta amshi  soyayyarsa,  ko zatayi yawo tsirara sai ta aureshi idan Kuma   hakan bai samu  ba   zata  saka rayuwarsa  ta quntata  . "

anas  ya  yabi bayanta da kallon bakinciki  ,ya rasa wani irin  naci ne  irin nata , mutun ya nuna miki  da Ido  ya nuna miki  da jikinsa  har ya fito ya furta miki amman ki tsaya kina hauka akanshi,  tsaki yaja ya juya ya  shiga ciki falon zuciyarsa cike da takaicin abinda zahra tayi  . Inda ya bar jaguwa anan ya  iskeshi   tsaye   a tsakiyar  falon   rungume  da duka hannuwansa a qirji  sai  faman cika yake  yana   batsewa .
jikin  anas a sanyaye  ya   samu guri   ya tsaya kusa dashi   ya  dafa  kafad'arsa,  jaguwa  ya  juyo  ya   kalleshi  yana cije lip's dinsa  na  kasa a hankali ya sake juya masa  baya    yana  furzar  numfashi   kana yace  "ka   gama  munafurcin ?wani irin bugu qirjin anas yayi da karfi  " a hankali  sautin  muryarsa  ya fito yana cewa"idan  zanyi  munafurcin  kowa  bazanyi  naka ba,  idan zan cuci kowa bazan  cuceka ba, kama  daina  min irin wad'an nan  abubuwan dan wallahi  suna  Kona min rai da  mugun   tayar  min da hankali ".
Jaguwa ya waigo  ya fuskanci anas sosai  yana  sake furzar da iska  mai zafi  daga bakinsa "muddin  kana son zuciyata  ta cigaba da amincewa da Kai    sannan  na daina fad'ar  haka akanka  anas  ya zama dole sai kayi hannun riga da zahra bana qaunarta bana qaunar ganinku tare muddin zaka kasance dani sai dai ka za'ba ko ni  ko ita ?  taku daya biyu yayi ya matsa daga  kusa da anas  yana tafiya a hankali  still yana rungume da hannunwansa.

"jaguwa !

anas ya kira sunanshi cikin yanayi na firgici  da tashin hankali , idanu kawai jaguwa  ya tsura masa  batare daya amsa masa  ba"  shakka babu duk duniya nafi sonka akan kowa, Ina qaunarka fiyye da ni  kaina  maganar zabi  ma  bata  taso  ba dan kasan waye  zabina"  yayi mgnr hawaye na ciccikowa a idanunshi  "Kai ne zabina Adnan  Ina  sonka fiyye da kowa da komai  nawa "  tautausan murmushi  jaguwa ya  sakar  masa yana mai Jin sanyi  acikin  zuciyarsa , cike da  farinciki  ya mika masa hannunsa
da sauri anas ya mika masa nasa  hannun suka  rungume juna suna sakin numfashi   atare ,  jabir , jubi  ,kamil  da suke  zaune  duk sukayi  shiru suna dubansu  dan  ba wannan   bane karon    na   farko  da suke samun matsala  a tsakaninsu  kuma  cikin kankanin lokaci suke  daidaita kansu. 
kuka sosai anas yake  jaguwa na shafa bayansa kamar wani karamin yaro  "is okay  anas  na sani , nasan kana  qaunata  da gsky kmr yadda nake qaunarka   am really sorry for  my active  har  cikin  zuciyata nake jin  qaunarka , Kai  zinari ne acikin zuciyata  Ina sonka anas  "Nima Ina sonka  kyakkyawan abokina had'e da qauna  mai  karfi , cikin  kankanin  lokaci   komai  ya daidaita  a tsakaninsu  suka  samu guri suka zauna cikin sauran abokansa  nan hira  ta barke a tsakaninsu .
su jubi sun so kwarai su sake samun qarin haske akan maganar  jaguwa ta d'azu  akan yarinyar  amman    yaki bada dama   amman duk da haka sai da kamil yayi magana Cike da kulawa kamil yace "anyi maka tambaya  akan yarinyar nan  ka wani  share  mutane " to  me  yasa meka a goshi  Kuma ?  ko baku  lura da goshinsa  ba  ?ya fad'a yana kallonsu  d'aya byn daya  ,kun san halin miskilancinsa  ai  ba lallai ya fad'a ba ni tun jiya  na gani sanin halinsa yasa na share  inji cewar jubi .
"ku manta da wannan maganar idan akwai wacce ta fita  mahimmam ku kawo  muyi  kawai  " anas ya  fad'a  dan  jaguwa wayarsa ya d'auka yana duba sakonin mutane , basu  tashi a falon  ba sai da suka tsara yadda  tafiyarsu  Ogun state zata  kasance a gobe  .
" Yadda  suke  tsara  komai akan aikinsu   haka  Suma  jami'an tsaro dana  sirri  suke shirya yadda zasu  kamasu  a yanzu ma  Asst  Commissioner   of  police ne ya kira layin  d .c .p   baba abare  wato  lawan  numan   byn  ya  d'auka suka gaisa   ya fara magana  cikin   zafin rai " wannan mutumin  bai  kamata a  barshi har zuwa  wannan  lokacin  batare da anka  mashi  ba , yayi mgn tare da yin shiru  "eh  to haka ne  amman  abinda nafi  bukata a Kara saka Ido sosai  akan  duk  wani  motsinsa  da shiga da fitarsa  bama  iya rayuwarsa ta fashi ba  hatta rayuwarsa ta duniya ma sai na tabbatar  da ta ru'bance idan yazo hannu , sun  dauki  lokaci  mai tsawo  suna tautaunawa akan jaguwa da  yaransa  kafin daga bisani suka yi sallama.  "

*****
"Nazifi   haka   mukayi  da  Kai ?a she baka  da amana ban sani ba  ? ya rufe shi da fad'a ta Inda yake shiga ba ta nan yake fita ba  cike da matsanacin firgici nazifi yace "dady me nayi  Maka  ?  bangane me kayi  min ba ? ya tambayesa yana maxurai ",ni zakawa  tambayar  rainin hakali ?  to  yau  duk  a zaune naga Ibrahim  alhalin na fad'a maka bana son ganinsa a zaune sai akwance  dan  lokacin tashinsa bai yi ba tukun  "sai lokacin nazifi  ya fahimci   rashin  amanar da  yayi  masa .   ya  shafa sumar Kansa  yana cewa  "Allah  dady  Ina  iyakacin k'okarina  Ina yin  komai yadda ya kamata  alluran  da na saba yi masa shi nake masa haka zalika maganin da  yake   sha  shi    nake kawo wa  ban canza ba  ".
"wannan karya ne nazifi  "da gaske dady baza yi maka haka ba ,ai duk abinda kace shi zanyi tunda ka zabi abarshi cikin wannan yanayin ni me zaisa naki?" ai ya  zama  dole nabi
duk wani  umarninka  bayan haka ma  duk  sati  sakokan  na shigowa account dina ,nafi tunanin yawon  magani da allurar  da ake masa  ne yasa suka daina aiki   ajikinsa Ina ganin me zai hana a canza  masa ? ". ya fad'a yana tsine masa  acikin zuciyarsa domin kuwa  mutane  masu hali  irin na alhj Tahir sam basu ya  kamata su haifi  d'a irin Ibrahim  ba. "to shikenan na d'auka kana cin amanata ne ?Ina ai bazan ta'ba cin amanarka ba  wannan ai sirri ne a tsakaninmu " alhj Tahir yayi murmushin jin dadi  yana cewa
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment