Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganki ke  kadai shiru  ina ita wannan yarinyar ?" ya tambayeta gabansa na faduwa kar ace bata nan .
"Tana d'aki yanzu ta shiga "
naunayen ajiyar zuciya ya sauke yana samun natsuwar zuciya "hankalina na kanku saboda nasan na barki cikin wani hali "ai inshallahu komai yazo karshe ta fad'a tana fad'a masa yadda sukayi daita da safe byn fitarsa  "Allah yasa Iya wahalarmu kenan  tace Ameen "ai muddin ta saba alkwarin taki natsuwa acikin gidan nan zan bata mamaki domin dole ta zaba komu ko shi wancan dan iskan barawon banza inji cewar dady.
ita kuwa uwar gayya tunaninta ba'a kansu yake ba dan tana shiga daki ta d'auki wayarta abun mamaki missed calls din jaguwa ta gani guda uku ajere murmushin jin dadi tayi ta soma neman layinsa kira d'aya ya dauka alokacin yana zaune akan kujera a falonsa system ne a gabansa ya dauka ya manna a kunne idanunsa na kan screen din wayar "hello tanweer ?"
Shiru tayi tana sauke naunayen ajiyar zuciya tare da Jin dadin zazzakar muryarsa "ina yini ?"
"Lafiya ya Kike fatan komai lfy ko dan jiya da tunanin abinda zai faru a gidanku na kwanta hope babu abinda aka miki?"
Babu komai fad'a ne kawai Kuma kamar yadda kace hakuri nayita basu "that's good haka ake so ".
yayi shiru itama tayi har sai data d'auka ko ya kashene ta cire wayar a kunnenta ta duba taga har lokacin yana kan layi ta maida tana sauke masa numfashi tana cewa "hello !
"Ina jinki tanweer yaakayi ?"
"last Kafin zuwana jiya gurinka kace min zaka zo gidanmu ?"
Shiru yayi yana sauraronta batare daya ce komai ba illa mikewa da yayi tare da gyara rigarsa sannan ya nufi d'akinsa ya d'auki wasu abubuwan amfaninsa ya karaso Inda akwatinsa  red and black yake ya bud'e sama ya zubasu sai lokacin yace "ina sauraronki sauri nake domin akan hanya nake tafiya zanyi zuwa Abuja jirgina karfe shida daidai zai tashi ".
me zakaje yi abuja ?" Tayi mgnr kmr zatai kuka dan tuni idanunta sun cicciko.
"alqalla !" Yana daure fuska dan karta kawo masa wasa a aikinsa.
shiru tayi kamar ta karasa fashewa  da kuka "banason aikin nan  adnan ......"
"kullum maganarki kenan " ya katseta ta hanyar fadar haka cikin zafin rai "shine damuwata nafi son ka zauna empty baka aikin komai akan wannan sana'ar, ka tausaya min mana  "naji !" Kukan da take dannewa ne yayi nasarar kufce mata ta soma rera masa kuka har da shesheka "meye hk Kuma ?"ke me yasa kuka baya miki wahala né ?"
"idan wani abu ya sameka ya kake son nayi ?
Sosai tausayinta ya kamashi dan hk ya kwantar da muryarsa kmr tana gabansa "ki kwantar da hankalinki babu abinda zai sameni zama yayi domin rarrashinta wanda bai san yanayin hakan ba ,
" kwana nawa zakayi ?" zanyi kamar sati daya zuwa kwana goma "haba Adnan me yasa baka tausayina ne kwanakin nan sunyi yawa ".
Ya sake yin kasa da murya abinda zai kaimu  din ne dole sai munyi  taking time   "shikenan Allah ya tsare min Kai  "ameen ya furta a can kasan makoshi  yana lumshe idanunshi "yanzu sauran awa daya da wani abu kenan ku bar gida yace  "um ! "zanzo na ganka kafin ku fito zuwa airport Kona zo airport din direct "?
"No karki zo "
ya fad'a atakaice tare da katse Kiran dan bai  son tazo sannan bai son mgn dayawa  dan ma itace shiru tayi rike da wayar taso taje ta ganshi kafin ya wuce har ta fito mumy ta kasa ta tsare kamar tayi kuka ganin take iyayenta basa mata adalci a hukuncin da suka yanke mata a zatonsu zata iya zama na tsawon lokaci batare data d'aura idanunta akanshi ba ?".
ta lumshe idanunta daga tsayen da take "bazan iya ba gsky sai daí kuyi hakuri wallahi ta cigaba da sakar zuci .

Dady zaune a d'akinsa byn yayi wanka ya sauya kaya zuwa jallabiya ya jima zaune yana tunanin rayuwa kawai yana Jin ciwon abinda tanweer take aganinsa hakuri ya dace tayi .
ya mike da kyar ya goya hannuwansa duka abaya yasan babu tantana wannan yaron da take zuwa gurinsa yana ta'bata .
mace akan jijiya babu abinda bazata iya yi ba tunda taji dadinsa da matukar wahala ta iya rabuwa dashi sai ya tashi tsaye yayi amfani da karfnsa da kudinsa da matsayin kujerar mulkinsa .
ya runtse idanunshi "duk fa zunubinsa ne ya kare akan tilon yarsa haka rayuwa take shine wanda yake cin mata a office ,Shine yaci a hotel hotel ,shine yaci a mota Kuma duk yara kanana brain dinsa ta hasko masa fuskar Hibbat yarinyar yar kimani shekara sha takwas a duniya a mota  yayi yayin cinta a car park yawon zuwan da yake gurinta Kuma duk sanda yaje sai ya ci yake komawa gida mutane dake gurin suka fahimci haka wata rana Yana tsaka da yi suka zo suka tsaya ajikin motarsa suna buga kofa.
yayi saurin tashi akan hibbat Yana Maida wondonsa ai kuwa suka taru ajikin motarsa har   sai daya fito  gashi babban mutun ga hibbat yarinya karama siririya  doguwa  kyakkyawa jinin saurata  .
nan fa suka haushi da fad'a taya kamarsa zai dinga irin wannan rayuwar da yar cikinsa  case  har gurin sarkin agege , ganin  shi din babban   mutun  ne  ga Kuma yarinyar diyarsu ce  idan ma suka ce zasu daga maganr cikinsu  zatayo  kamar sun tonawa kansu da sarautarsu  asiri ne yasa aka bar maganar Amman fa duk da  hakan bai sa ya rabu daita ba suna haduwa daita  akan titi depomu  express ya d'auketa suje hotel yayi yadda yake so daita idan kuwa yayi tafiya zuwa Abuja ko Kaduna shikenan kofar sikanci ya bud'e sai a hada masa yammata uku alokaci daya   yaci wannan ya gama yaci wannan haka yayi ta rayuwarsa sai  gashi sanadiyyar iskancinsa ya janyowa    yarsa  " .
"me yasa nayita zina da ya'yan  mutane gashin abun ya dawo kaina ..?"
Yana cikin zagaye d'akin wayarsa ta soma ringing naunayen ajiyar zuciya ya sauke yaje ya d'auka yana dubawa ,number ne kawai babu suna har zai ajiye wayar  sbd bai daukar number da babu suna sai kuma ya fasa ya dauka tare da yin  shiru  "hello aka fada daga daukar wayarsa shima hello yace "alhaji ili ne.
"okay ili ya kake ?"Lafiya alhj  kwana biyu banga kiranka ba shine nace na kiraka muyi bakin mata daga kano gasky akwai daya dana tana da maka zaka ji dadinta "ili ai tunda kaga bana kiranka ai kasan akwai damuwa yanzu dai  magana ta kare dan a yanzu bana cikin kwanciyar hankali sakamakon abinda na dade Ina yi a boye ya shafi dilon diyata dan haka zina ta fita araina daga yau karka Kara kirana akan mata  yana gama fad'ar haka ya katse Kiran tare da juyowa bayansa Ido hud'u sukayi da mumy .."
Kallon mamaki ta dinga binsa dashi tamkar bata san shi ba bancin da kunuwanta taji yana maganar da tace karya ne idan wani ne ya fad'a mata .
Hawaye suka shiga zubo mata shi Kuwa gabansa ne ya dinga faduwa ,ya dinga Karanto Kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun wani irin zufa ke tsatsafo masa bisa goshinsa kamar an watsa masa ruwa .
gbdy sukayi sit na tsawon mintoci daga shi har ita shi tashin hankali ya hanashi magana ita Kuma mamaki ne ,mumy dake zubar da hawaye bai yi auni ba yaga ta zube kasa ta zauna  dabas tana cigaba da kallonsa yayi saurin yayo kanta zai ta'ba tayi saurin dakatar dashi da hannunta "karka tabani Allah sarki tanweer ashe ubanki ne yayi silar jefa rayuwarki cikin kunci hakika ka cutar da tilon diyarka, ni Kuma ka yaudareni ta fad'a  tana  goge hawayenta kana ta numfasa ta cigaba da mgn " na kan zauna ina tunani me yasa abubuwa suke faruwa damu haka ashe da walakin kuskurenka ne ya shafita bata ji bata gani ba kaga rayuwa ko ?"Kai din ba barowa ba ,ba mahainci ba duk wanda yaganka yaga responsible man amman Kalli ta inda Allah yayiwa ya'yan mutane sakayya dan fashi yazo har gidanka ya saci kudinka sannan ya  tafi da diyarka ya kwana daita ta kamu da mutuwar sonshi saboda ba'a cin bashin Allah akwana Lafiya  ,wallahi da wani ya  fad'a min cewar kana neman mata bazan yarda ba sai gashi da bakinka wallahi abban tanweer kabani mamaki kullum yabonka nake ashe kai din ba kowa bane sai fasa gurbi acikin mutane nayi danasanin aurenka.
" ka taba fad'a min zaka kara aure na hanaka bare kace shine hujjar bata ya'yan mutane?"
"wallahi a yanzu na daina ganin laifin tanweer dan haka ni zan goyawa tanweer baya ta auri wanda take so ,ta fad'a yaron  ya fito suyi  aure  a wuce gurin kowa ya huta,  haka  Allah ya so da rayuwarta nata qaddarar kenan.
dady ya sauke numfashi sukayi zugun  kafin a hankali yace "bazan yarda ba, bazan bawa dan fashin da kasa ke nemansa   Ido rufe diyata  ba , bazan iya wnnan kwamacalar ba ."
ta mike tsaye da kyar ta karaso gabansa ta buga table dake d'akin wanda takardunsa da system dinsa ne Akai tace "haka nan zaka hakura da abinda take  so , zan fada mata da  kaina cewar kace ya turo iyayensa idan Kuma kaki bakaki gani ba domin masu irin halinka suna nan cike a agarin nan."
zuwa yanzu gbdy jikin dady tsuma yake kanshi yaji yana jujjuyawa dashi saboda tashin hankali "wallahi ka cuceni ban taba hanaka aure ba amman kake neman mata tana gama fadar haka ta fice daga d'akin ya biyota da sauri yana kiran sunanta "zainab karki soma wannan dayen aiki "zan yi domin wannan shine hukuncin dayafi dace wa da kai ,data dinga binsa yaje ya sake yi mata  wani cikin gara ta auresa tunda taji ta gani tana sonshi  "karki min haka zainab arayuwa kinsan Ina matukar sonki fiyye da kowa da komai a duniya ban taba tunanin idan kinji abinda na  aikata zaki yanke wannan hukuncin akaina ba.
na duara burin duniya akan diyta zata auri mijin da zatai alfahari koda bata auri Ibrahim ba  dan haka kar muyi haka dake...."
" zamuyi koma nace muyi data zubar mana da mutunci kmr yadda kake yi a waje Allah gara ta aureshi ai shiriya ta Allah ce sai kaga ya shiryu  a sanadiyyarta  "bafa zan yarda ba, tanweer diyata ce "please ka fitar min a daki kana damuna da surutun banza,kai bana ma son ganinka  kuma kasan allah babu wanda ya isa ya hana aure nan ".

da misalin karfe shida na yammacin rana
Suka fito cikin shiga iri daya sai dai kalar kowannensu dabam sannan kowannensu goye da school bag kawai jaguwa ne kawai mai akwati wanda yake dauke da kayan aiki da school bag idan ka gansu zaka dauka yan wasan kwalo ne saboda irin shigarsu sukayi suka shiga mota daya scopio yajasu suka bar gidan .
kai tsaye airport suka nufa koda suka isa jirgi ya kusan tasshi daman kuma suna sane suka fito late dan su samu damar wucewa da makamansu
da dan sauri suka isa reciption suka Mika body fast dinsu nan maiakatan wajen sukace sunyi lattin jirgi ya kusan tashi .
daya daga cikin maakatan gurin ya tashi kasancewar yasan jaguwa adalilin tafiye tafiyen da yake ,ya karbi akwatin jaguwa suka nufin filin jirgi cikin sauri ya karbi lebet a hannu wani ya manna a akwatin aka sakashi acikin kagon jirgi sannan suka shiga kowannensu ya nemi set dinsa .

Yayinda eku daya rigasu isa abuja tun safe
ya kama musu daki a humble star hotel a second floor ,yayi musu shopping kayan bukatarsu sannan ya zauna zaman jiran karasowarsu karfe bakwai daidai ya nufi airport ya jima kadan kafin ya karasa saboda nisan dake tsaknin inda yayi musu louge yana gama karasowa ya tsaya ariver domin jiran karasowarsu .
Karfe takwas daidai suka sauka,suna sauka eku ya dukesu kai tsaye unguwar Funsho Williams avenue suka nufa bai tsaya akoina ba sai abaki tafkeken get din humble star hotel ,get din abude yake kmar koda yaushe ya sanya hancin motar cikin haraban hotel din maakata hotel din suka taso suna nuna masa inda zai yi parking yana gama parking suka fito daya bayan daya cike da jin kai suke taku har suka karaso cikin reciption "gsky eku ka kama guri mai kyau da sirri allah yasa yadda wajen hotel yayi kyau cikinsa ma haka yake?"inji cewar kamil "ai kana gani ba magana jabir ya fada yana sosa keya suna gama karasowa second floor ya mikewa kowanensu key'n dakinsa sannan ya karasa da sauri bakin kofar dakin jaguwa room 120 ya bude ya tsaya har sai da jaguwa ya shiga sannan ya biyo bayansa babban daki ne dayaji komai da kayan more rayuwa zama yayi akan kujerar kwaya daya dake ajiye adakin eku ya dauki remut ya qara masa karfin ac dake aiki a dakin yayida jaguwa yayi shiru yana kallon tsarin dakin murya cike da ladabi eku yace "boss me zaa kawo maka?shiru kamar bazai yi magana ba sai kuma ya motsa lips dinsa "wani abu mara nauyi "okay sir ya juya ya fita jaguwa ya zuge zip din yar saman rigarsa ya ajiye akan gado ya kwanta flat yayi pillow da hannuwansa duka sannan ya runtse idanunshi babu wacce yake gani acikin kwayar idanunshi sai tanwer dinsa laulausar gashinta,surar jikinta uwa uba dukiyar fulaninta a yanzu ko baa fada masa ba yasan yana quanrta kamar shine ya haifeta musaman a irin qaunar da take masa mai tsanani sai dai duk wannan qaunar da yake mata zai rusheta ya zamanto kamar baa yi ba , zai bar wannan sirri acikin zuciyarsa bama zai bari wani mahaluki ya fahimci halin da yake ciki ba .
a hankali ya fara jin ana knocking a kofar dakin da kyar ya bude bakinsa ya bada Umarnin shigowa kuma har lokacin bai bude idanunshi ba maaikaciyar hotel din ce sanye cikin riga da siket iya gwiwarta ta gaishesa bai amsa ba ta ajiye faranti silver ta juya ta fita ta rufo masa kofa .
Byn fitarta da kamar minti gomasha biyar ya mike zaune yana jin sauyin yanayi ajikinsa ,iska ya furzar mai zafi sannan ya kira number anas da sauran abokansa kana ya janyo akwatinsa ya bude bindiga pistol ya soma fitowa dasu daya byn daya yana kallo kusan guda shida yana kokarin fito da cikon ta bakwai suka fara shigowa one by one anas ne ya shigo akarshe yayi wa kofar key.
Zama sukayi gbdy a gbansa suna kallonsa ya dago ya kallesu "bana bukatar kowanne aciinku ya kwana da kowace mace daga yanzu har zuwa sanda zamu Kammla abinda ya kawomu,bamu samu isashen lokacin tautaunawa ba kafin mu taho amman nasan kowa yasan abinda ya fito damu abu ne mai mahimanci.
Gyada masa kai sukayi "yanzu dame zamu fara?"jabir ya tambaya ya mike tsaye ya jingina da bangon dakin tare rugunme hannuwansa"zamu jira sky muji bayyanan daya samo mana akansu tukun idan ta kama ma a daren nan ma zamu iya fita .
zamuyi wannan aikin bisa kasada da rayuwarmu idan mun fadi ku yafemin idan kuma munyi nasara muyi farinciki tare.
" inshaallahu zamuyi nasara inji cewar Ana's "idan kaji ajiknka zamu fadi mu hakura mana?jubi ya fada yana dubansa "sam banji ajikina cewar zamu fadi ba amman wannan rayuwar tattare take da abubuwa ya fada yana lumshe ido sun jima suna tautaunawa har karfe dayan dare basu samu wani bayani daga sky ba dan haka ya sallamesu byn ya mikawa kowannensu bindiga sannan ya shiga yayi wanka ya fito ya kwanta ruf da ciki gbdynsu sun yi bacci amman Banda jaguwa bini bini zai dauki wayarsa ya duba ko zai ga wani bayani daga sky à hankali Sakonni sky ke Shigowa wayarsa ya zabura ya mike daga kwance da yake ,kwana yayi yana tsara yadda fitarsu zata kasance yayinda minister suka kwana suna tashin hankali da hjy zainab .
Washegari yana tashi ya bude school bag ya dauki brush da toothpaste ya shiga bayi bai jima ba ya fito yana kallon murdadden jikinsa zuwa kan nipple dinsa abinda yafi daukar hankali mata kenan akanshi inda zai sakewa mata da ya ci mata bilaadadin ya goge jikinsa ya fito da turare mai dadin kamshi ya feshe ilahirin jiinsa ya dauki riga da wondo bakake ya saka ya janyo wayarsa nan ya sake cin karo da sakon sky cikin sauri ya shiga neman layukan abokansa ,a haraban hotel din suka hadu suka shiga mota suka fita ."

tun da sanyi safiya shima dady ya shigo d'akin mumy ya isketa zaune ya tsaya a gabanta yana dubanta idanunta duk sun kubura saboda kuka "ni zanyi tafiya zuwa kaduna  wata killa na dawo yau ko gobe "bata kallesa ba ta cigaba da jan casbaha ",kiyi hakuri zainab a halin yanzu zuciyata cike take da gariri da tashin hankali bama haka ba har cikin zuciyata nake Jin nadamar abinda nayi .
Wallahi Zainab nayi nadama tun kafin kisan komai na dade wani abu bai sake shiga tsakanina da diyar kowa ba adduata Allah ya yafe min ya Kuma min sausauci bata ce masa um ba bare um'um har ya Karaci maganarsa ya juya ya
tsallake ya bar  garin zuwa kaduna yana fita
mumy ta tashi ta shiga d'akin tanweer ta sameta kwnace lamo  tana tunani jaguwa yayinda hannunta ke rike da casbaha  tana ja tana masa adduar
Allah ya karesa  mumy ta samu guri ta zauna kusa daita  tana shafa kanta  hawaye suka  shiga gangaro mata tanweer ta yunkura ta mike zaune  taga mumy na Kuka cikin muryar kuka tace "kiyi hakuri mumy nasan saboda ni kike kuka ko ?" inshallahu zan canza, ta girgiza mata Kai tare da riko tafin hannunta cikin nata cike da tausaya mata
Sun dade a haka Mumy na shafa kanta so take ta furta mata abinda ke ranta amman ta rasa dalilin dayasa ta kasa .
cike da jajircewa irin ta sky jaguwa da abokansa sukayi nasara domin kuwa sun amshi makudan kadade kimanin million hamshin a hannun alhj usman koko betse farmer farm sectry , mutun biyu suka rage dan hk suka dawo masaukinsu cike da farincki sun so suyi ashararanci jaguwa ya hanna dan baya wasa da aikinsa sannan kuma baya son aka masa wasa".
Washgari suka fita neman Alhaji sani fefa shima cikin saa suka shiga gidansa suka amshi kudi mai yawa a hannunsa mutun daya yayi saura wato ajirebi .”

Su jaguwa na fita daga gidan alhj sani fefa suka kama gabansu ,shi kuwa zama yayi jagwab akan kujera mai zaman mutun daya zuciyarsa cike da matsanancin mamaki “shi da yake wa mutane fashi shine yau aka wayi gari har gidansa aka biyosa? dadinsa ma basu taba masa lafiyar iyali ba koda yake sun fada masa abinda ya kawo su “kudin da yayi ruwa yayi tsaki aka dannewa marayuwa suka zo amsa “.
Cike da rawar jiki da tashin hankali ya kira number alhj usman farmer farm sectry yana dauka ya fara cewa”anyaka tata shi fa domin kuwa anbiyo kudin da mukaci satin daya gabata “.
Naunayen ajiyar zuciya alhji Usman ya sauke yana mikewa tsaye daga zaunen da yake “sosai kuwa nima cikin tashin hankali nike domin kuwa jiya iwar haka ina cikin tashin hankali har gida barayi suka zo suka yasheni tasss “ kace kai ma anzo maka kenan nan?
“Kwarai kuwa?
“amman me yasa baka kira ka sanar dani ba har kabari suka riskeni har da takamar kudin marayu suka zo amsa ? kasa kunne nayi naga ta inda zanji wanda zaa wa acikin mu tunda yanzu anzo har gida anyasheka nasan ba daga gurinka bane nafi tunani daga sama ne tunda nima sun fada min wannan kalmar kudin marayu suka zo amsa “ ya karasa maganar yana cewa bari na hadamu conference cikin minti biyu kacal muryar ajirebi data galadima da garunmallam ta bayyana a bayanin da Alhaji sani fefa ya cigaba da yi yasa suka fahimci komai “ to wa yasan da wannan maganar “.?
“Byn mu biyar din nan babu wanda yasani “lallai akwai wanda yasani munyi shuka ne a idon wasu , lallai ya kamata mu san ko su waye suka fara bibiyarmu domin bana tunanin wanda zai iya karawa damu bare har ya bibiyemu, “ wannan gsky ne“.
“Gani nan zuwa kafin nazo ka kira jami’an tsoro lallai dole akama wadan nan yan fashi tun kafin su riski sauran dan haka lallai su maida hankali a kamo wadan nan barayin farmer farm sectry na gama fadar haka yayi disconnecting din kira yadda yayi haka sauran sukayi cikin tsananin tashin hankali ajirebi ya hada kudaden daaka raba aka bashi ya zuba cikin akwati ya bar gidansa dan daman cash suka amsa domin gudun idan asiri ya tono ko anbi diddigi bazaa gano daga inda kudn suka shigo ba.”

Shi kuwa Alhaji sani fefa ya soma neman layin jami’an yansanda ya zayyane musu duk abinda ake ciki,cikin kankanin lokaci suka karaso har zuwa babban falonsa ya mike yana sake musu bayani suna dube dube tare da tambayarsa ko akwai wata sheida da zaa iya kama yan fashin “shiru yayi yana tunani mai zufi,“ina iyalin naka suke “?
“Suna wancan dakin ya basu amsa yana sake zurfafa tunaninsa “fatan dai basu taba lafiyarsu ba “?babu wanda suka taba dan lokacin da suka bude kofar suka shigo basa wannan falon suna wancan bangaren ya karasa maganar yana sauke numfashi yana mamakin taaddacin yan fashi “abinda zai baku mamaki kamar walkiya nagansu agabana ni har yanzu mamakin nake yayi shiru goye da hannunwansa duka abayansa can yace “yauwa akwai ajiyar kamarar camerar dana yi a falon ya karasa da sauri inda karamar camerar daya makala a bangon falonsa take mai kallon duk wanda zai shigo.
ya ciro memory “sun yi son ransu amman da wannan bazasu tsira ba domin duk fuskokinsu a bude yake yana magana yana kokarin jona momery din acikin flash sannan ya jona da tv bangon dake manne a falon ana gama hada komai sai ga fuskokin su jaguwa daya byn daya ta bayyana kowannensu rike da bindiga .
daya daga cikin jami’in tsoro yace “gsky kayi dabarar saka wannan karamar camera dan sam babu wanda zai fahimci akwaita dan haka gbdynsu bazasu tsira ba duk inda suka shiga acikin garin nan sai an fito dasu .
“gsky a fito dasu shine kawai kwanciyar hankalina “an gama ranka shi dade “.
Sosai suka maida hankali ga tv duk inda aka hasko fuskar jaguwa da abokansa sai yansada sun dauki hoto , fuskokinsu tas ta fito bazaayi wahalar kamosu ba, cikin kankanin lokaci suka tura hotunansu zuwa headquarters sannan aka tuwa kowaneni maaikaci dake aiki cikin garin sannan suka masa sallama suka wuce …..”
Jaguwa na zaune a mota sakon sky ya shigo “boss byn fitarku a gidan jami’an tsaro sun zo gidan alh sani ku hanzarta komawa masaukinku “.uhm “!
Kawai ya furta a hankali sannan ya katse kiran.
a rana ta uku basu samu bayanin komai ba akan mutun na uku da suke hari daga bakin sky haka ma rana ta hudu wasa wasa suka share kwanaki suna nemansa batare da sun gano inda yake ba dan haka gbdy suka raba kansu suka bazama nemansa yayinda hotunnsu ya baza acikin garin abuja tare da baza jami’ai a kowani titi.
******

Cikin wata shiga ta kamala wacce idan ka kallesu bazaka taba cewa su din masu sata da azalumai da gwanati bane suka shigo cikin club kowannensu ya samu guri dabam ya zauna yana kare wa yanayi gurin kallo har sanda babban yaron ajirebi ya shigo ya isa inda aka ajiye empty chairs ya zauna tare da ciro wayarsa yana daddanawa atare suka kalli juna sannan sukayiwa junansu sigina da ido.
Zaman sa bai fi da minti biyar ba maikatan club din suka karaso inda yake yana tambayarsa abinda yake da bukata , "yallabai me zaa kawo maka ?" ya dago a hankali ya kalli matashin maaikacin dake

Please Login or Register in order to submit comment