Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

riga orgen da bakin wondo ya matso kusa dashi “dan soyayya ya furta cikin zolaya .
jaguwa yayi saurin dawowa haiyacinsa yana cewa "me ka ga nayi ?"Ka tafi duniyar tunaninta mana ".
Meye haka kuma kamil?"shikenan bani da wani abun tunani sai nata ? Yes kullum kana zuwa hospital gurinta gbdy ka ajiye ayyukanmu baka da lokacin komai sai nata ya dai kamata ka dawo normal muyi abinda ke gabanmu".
Sai daya furzar da iska iska me zafi yace “nifa ina zuwa hospital ne saboda .."sai kuma yayi shiru ya kasa karasa mgnrsa "saboda ka fada soyayya ba ?
“mu dai bamu hanaka yin soyayyarka ba amman ka maida hankali kan aikinmu ko ba haka ba friends ?"yayi mgnr yana dubansu duk suka gyada masa kai alamun "eh! Banda anas.
"Haba kamil kai ma zaka bi layin anas ko?"
Gbdynaku kusani saboda ina tausaya mata ne nake mata komai ba wai dan wannan abun ba "tunda anas yake mgn akanta jinsa kawai nake .”
Kamil yace “amman alokaci da zaa kai yarinyar nan hospital naga wani abu acikin kwayar idanunka ".
"Meye shi ?"Jaguwa ya tamvayesa zuciyarsa na rawa Kar dai sunga hawayensa ?"
"Koma dai menene naga kamar hawaye .
"Bazan iya tuna wannan ba inji cewar jaguwa ya fada yana tamke fuska dan ma kar su sake gigin kawo masa raini duk sukayi tagumi suna dubansa shima din su yake kallo daya byn daya sannan a karshe ya saida idanunshi akan anas yana cewa "kaima kasan na damu ne saboda"..
"No jaguwa kafa kamu da soyayyarta dan ka rasa dukkanin natsuwarka akanta nidai babu ruwana bama zan sake yin maka magna akanta ba ni dai yaushe zaka samu lokaci muje gurin Ammin ?
“Bansani ba ai kasan hanyar zuwa dole sai dani?
“Shikenan zanje da kaina yana fadar hk yaja bakinsa yayi shiru gbdy jaguwa ya kasa samun sukuni “a inda zaka samu taka matsalar kenan menene ma yasa ka fada soyayya?" jubi ya tamvayesa idanunshi na kanshi ."Soyayya kuma jubi ?"yayi masa tmbyr yana murmushi dan allah mu ajiye wannan maganar muyi na aikinmu komai zai zama normal nan suka cigaba da tautanawa akan alqallarsu ta gaba wayarsa ce ta soma ringing a natse ya kai hannunsa kan center table ya d’auka tare da kunna koren maddani shiru yayi yana sauroron mai masa mgn “okay babu damuwa asibitinku kenan ? Idan na samu time zan zo “ ya katse kiran yana dubansu .
“me kuma ya faru? anas ya tmbyesa “tanwer ce wai dad dinta ya maidaita hospital dinsa “ai shikenan zariya ya kare inji cewar jubi gbdy suka kwashe da dariya “inji wa ? ai har hospital din zani sai dai idan banga dama zuwa ba ai tunda diyarsa ta kamu da sona sai dai yayi hakuri yana karasa fadar hk ya bar musu falon yana murmushi “.


Yau kimanin sati daya kenan jaguwa bai samu damar zuwa gurin tanwer ba haka zalika bai kirata ba sakamakin bincike da yake akan masu safarar miyagu kwayoyi,a hankali ya sanyo hancin motarsa cikin haraban hospital din yayi parking tare da kashe mota ya fito cikin riga baki mai gajeren hannun har ana iya hango saukowar zanen hannunsa da wando army green tsinsiyar hannunsa daure da agogon fata baki haka ma kafafunsa rufe suke cikin takalmi baki kansa sanye da facing cap baki sai kamshin turare dio ke tashi a gbdy ilahirin ajikinsa .
ya jingina jikinsa ajikin mota yana kokarin kiranta,
byn ta dauka tace ya tsaya daidai bakin kofar shigowa reciption zata turo masa wanda zai shigo dashi dan bazaa bari ya shigo inda take ba sai da izininta .
Tana zaune akan Katifa yayinda kafarta daya dake nade da bandej tana saman pillow jikinta sanye da farar doguwar riga ta rufe kanta da hula baki ya shigo dakin a natse bakinsa dauke da sallama , ta amsa aciki tana nuna masa gurin zama .”
Ya tsaya yana kare mata kallo tsab ,shigowarsa ya canza cent din dakin zuwa ta kamshin turarensa mai bugar da zuciya Ahankali Ya zauna akan kujerar dake fuskantarta yana sake kallon Fuskarta
gbdy yau fuskarta babu annuri dan ko gaishesa bata yi ba .a duk sanda zata gansa sai ta rasa sukuni amman yau ta kudiri aniyyar zata canza masa dan me zai zo mata da shigar da zata nuna zanen hannunsa? kallonta ya cigaba dayi kamar ranar ya fara ganinta tayi matukar masa kyau sosai Kmr ya sureta ya gudu sai dai ganin yadda ta hade rai kamar taga mutuwar ta ya dauke idanunshi akanta yana kallon dakin da take ciki kamar baa hospital ba yadda bata masa magana ba haka shima bai mata magana ba ya cigaba da zama yana cizan lips dinsa na kasa,shi dayasan wannan iskancin zatayi bama zai fara tunkaro inda take ba .
Ganin muddin ba ita bace tayi mgn bazai yi ba ko zasu kwana yasa muryarta a raunane ta kira sunansa"adnan ...!"
Ya tsura mata ido kawai yana kallonta qirjinsa na bugawa da matsanancin karfi “adnan kawai babu adnan dina data saba fada “lallai yau akwai matsala,
bata jira amsawatsa ba ta fara mgn "lokacin da nake karatu a london wata kawata tayi zanen a hannunta na hagu saboda gbdy duk cikin yaran kasata ta nigeria itace ke cinye hankalin gayun makarantarmu agurin iskanci , ni kuma saboda tsanar danayiwa zanen nã rabu daita rabuwa ta har abada ,amman sai gashi kai kana dashi hagu da dama amma bai taba damuna ba sai yau ?
Shiru yayi batare dayace uffan ba illa kwayar idanunshi daya zuba mata yana kallon karamin bakinta da take magana dashi kafin a hankali ya motsa bakinsa “karki sake min tambayar da kikasan amsarta sannan wannan fuskar acanzata ta koma yadda take bana son ganinta haka yayi mgnr a fusace yana tsareta da rikitattun idanunshi yadda taga yana kallonta yasa taji wani irin mummunar faduwar gaba “.

Mmn sudais



💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️33



…….Gabadaya ta nemi natauwarta ta rasa ji take kamar zuciyarta zata buga sakamakon faduwar gaban data risketa ,haka né ma yasa jikinta ya kama rawa gashi yaki dauke rikitattun idanunshi akanta masu cike da miskilanci ,kai adnan ba dai miskilanci da jin kai ba ,a kallon da take masa ta fahimci ransa ya gama baci da tambayar da tai masa shiyasa ma yake hukuntata da idanunshi “ya rabbi me yasa nayi masa tambayar?” tayiwa kanta tambayar tana sake jin faduwar gaba mara iyaka.
a hankali ta sunkuyar da kanta kasa ta hade hannuwanta guri daya tana wasa da yatsun hannunta ko zata samu sausauci yayinda idanunta suka ciko da ruwan hawaye .”
Ya numfasa sannan ya mike tsam daga kan kujerar da yake zaune ya soma takowa a natse har ya karaso gabanta ya d’an rusuna ya kai hannunsa ya d’ago habarta ya sanya kwayar idanunshi cikin nata atare zuciyarsu ta sake bugawa da karfi sakamakon idanunsu daya tsarike cikin juna ,wasu abubuwa ta dinga gani suna fita daga cikin idanunshi suna shiga nata idanun da sukayi rauni ,ta kasa rike hawayen dake cikinsu dan haka ta barsu suka shiga gangarowa kan Kuncinta .
A natse yabi hawayen dake tsiyaya acikin tafin hannunsa suna saukar masa da kasala bai yi magana ba sannan bai ce ta daina zubar da hawayen ba illa cire hannunsa da yayi ya dangwali hawayen yana kallo kamar bai san menene ba.”
ta runtse idanunta gam tana sake jin faduwar gaba mara misaltuwa bata ankara ba taji saukar lip’s dinsa akan nata tayi saurin bude idanunta hade da zaro ido waje wanda hakan ya sake bawa hawayen idanunta damar zubowa sosai ,kokarin kamo lip’s dinta na kasa yake yaji sautin muryarta cikin karfin hali “please adnan dan allah ka daina bana ….”
Bai bari ta karasa maganarta ba ya hade bakinsu guri daya atare suka sauke naunayen ajiyar zuciya still kwayar idanunsu na cikin na juna,tsotsan bakinta yake cikin wani irin salo da shauki har wani duhu duhu yake gani a idanunsa.”

sakwanni nata wucewa har aka fara shiga mintuna amman jaguwa yaki sakar mata baki yana fama sarrafa harshenta da hokoranta da lip’s dinta ganin idan batayi da gaske ba mutanen gidansu da masu zuwa dubiya zasu iya riskarsu a wannan yanayin uwa uba ma bazata iya jurar sakonnin da yake mata ba ,
a yanzu idan ta biye masa komai zai iya faruwa atsakaninsu dan ita kanta tana matukar bukatar kasancewa dashi tayi kewar abubuwan da yake mata matuka,sakonninsa masu wuyar mantawa né ,sannan masu zama né acikin kwakwaluwa da zuciya né ,sai dai duk da haka bazata yarda wani abu ya sake shiga tsakaninsu ba zata jure abinda take ji akansa .”
A hankali ta kai tafi hannunta zuwa qirjinsa tana kokarin turesa amman ina kamar dutse ta taba dan ko girgiza bai yi ba bagarensa kuwa ji yayi kmr ma kara tunzirasa tayi da sake kuno masa wutar shaawarta ya kasa sakar mata baki dan abinda yafi qauna kenan .hannunsa ya kai bayan keyarta ya tallabo kanta har hullar kanta ya zame kallonshi tayi gbdy baya cikin haiyacinsa dan bai ma san tana turesa ba shima kallon cikin kwayar idanunta yake yana sake jin wata zazzafar shaawarta mai karfi ya lumshe rikitattun idanunshi yana sauke numfashi .

rasa yadda zatayi dashi yasa cike da shagwaba ta cigaba da zubar da hawaye ,duminsu yaji a fuskarsa ahankali ya bude Idanunshi da suka canza kala ganin har lokacin tana hawaye har da shesheka ya fara controlling kanshi ya sakar mata baki ya zauna kusa daita yana matsota tare da sauke numfashi.”ta dan matsa kadan daga jikinsa dake gugan nata dan gbdy yanayinsa ya canza har hakan ya nuna acikin kwayar idanunshi ya sake matsota ya janyota jikinsa qara ta saki mara sauti “ouch!
Jikinsa a mace ya fuskanceta yana tambayarta “Lafiya?! Taí masa banza tamkar ba daita yake ba ta cigaba da rera masa kuka, matsota ya sake yi muryarsa can kasan makoshi saboda halin da yake ciki “tanwer menene yasa kike kuka haka alhalin kinsan bana son ganin hawayenki ? ko dan na d’an tsotsi bakinki ne ?ta dan saci kallonsa ta kasan idanunta acikin zuciyarta tace “d’an tsotsa ma kayi kenan ? da zan barka Kennan sai kayi fiyye da haka kenan ? “Eh ! Ya bata amsa a she a fili tayi maganar
ya cigaba da magana muryarsa a kasalance “ok am really sorry nayi kokarin kar nayi hakan ban san abinda yasa ba amman dai nafi ganin laifin wannan fuskartaki ce ta janyo haka me yasa kika canzata?yayi maganar yana shafa gefen fuskarsa ta buge masa hannu tana cewa”stop !”
“Stop what? ya tambayeta a dan rikice “abinda kake yi né banaso bai sanda ya kai bakinsa daidai wuyanta ba ya fara lasar skin dinta wani sabon bakon alamari taji yana bin sansar jikinta mai tattare da shauki ya zarce har cikin kunnenta yana hura mata iskar bakinsa wani irin zillo tayi jin wani sabon dadi daya ziyarceta murmushi yayi ganin yadda ta natsu tana amsar sakonsa jikinta na rawa , juyowa tayi ta kallesa da idanunta wanda suka sauya kala shi kuwa babu abinda yake aika mata dashi sai murmushinsa mai matukar burgeta da birketa mata lisafi “na cigaba ne? Ya fada yana gyara mata sumar kanta hade da kissing din wuyanta nan take tsigar jikinta suka mike yabi hannunta da ido yana kallon yadda tsigar jikinta suke mikewa , ya kai hannu yana shafawa a hankali yana sake kashe mata sansar jiki .
“me yasa tsigar jikinki ya tashi ?Tai shiru ta kasa bashi amsa tambayar da yayi mata,kallonsa da wasaninsa na matukar birkita mata lissafi har ma ta manta da kanta kuma ta lura ya fahimci haka shiyasa yake mata wasu abubuwa da zasu sake dilmiyar daita soyayyarsa .
”tanwer!
Ya kira sunanta da wata rikitacciyar murya da duk sanda yayita yana cikin kololuwar bukatuwa “ki barni nayi romance dinki please “sannu mijina idan kasan kana bukatar romancing da abinda yafishi sai ka hanzarta barin sana’arka ka kuma kawo sadaki amman for now na daina barin kayi yadda kaga dama da jikina.”ya fadada murmushinsa har fararen jerarrun hakoransa suka bayyana yana sake yamutsa tafin hannunta cikin wani irin salo saboda hannunta dake kife cikin nashi hannu “Wato ga shasha ka samu ina magana kana min murmushi dan….”
Saurin hade bakinsu yayi tare da matsota sosai yana kokarin zuge zip din gaban rigarta ta rike masa hannu gam amman yaki sakar mata baki sannan yaki cire hannunsa itama ta kasa dauke hannunta a saman nashi wani irin kissing yake mata mai fitar da mutun daga haiyacinsa duk da tana jin sakonnin da yake mata amman zuciyarta gbdy ta cika da tsoro kar a shigo a sanesu haka zuciyarta wani irin bugawa yake da karfi shi kuwa sai faman tsotsar bakinta yake yana lumshe rikitattun idanunsa sonta da son kasancewa tare daita yayiwa rayuwarsa illa.”

ya dauki lokaci yana sarrafa bakinta ganin yadda take girgiza masa kai tana nuna masa kofar shigowa da hannunta ya zare bakinsa a natse zuciyarsa na cike da tsoro da fargaba sai dai bazaka gane hakan a zahiri ba saboda baiwar dakiyar da allah yayi masa zuciyarsa na dukan tara tara ya juya bayansa wayam yagani babu kowa ,sauke numfashi yayi da karfi yana watsa mata harara.”

ta janye jikinta byn ta dauke kwallar idanunta “da alamun baki son na barki lafiya yau bakisan wannan hawayen da wannan bata ran da kike yi dauka zanyi kina bukatata ne ?to ni me nayi kuma?
“Bakiyi komai ba amman dan allah karki saki fuskarki ,wallahi zan baki mamaki kafin na bar nan ya karasa maganar yana sakar mata murmushin mugun ta kallon kyakkyawan fuskarsa tayi tasan zai iya aikata fiyye da abubuwan da yayi mata a yanzu ta cigaba da kallonsa har ya tashi ya koma mazauninsa yana kallonta itama kallonsa take ya kashe mata idonsa daya yana sakar mata murmushi “komai yayi kyau yake masa haka kawai taji damuwarta ta kau “wayyo ni allah son bawan nan naka yayi illa bazan iya fushi dashi ba ,allah kai jarabeni da son shi allah idan ba alkhairi bane ka yaye min na huta.

“Tanwer! ya kirata cikin wata kasalillyar muryasa dake tattare da tsananin shaawa ,ta tsura masa ido kawai tana kallonsa gabanta na dokawa batare data amsa ba “I dont wont to see your tears ya fada yana kashe mata idonsa daya “ nan take ta goge hawayenta tana kallonsa “ki saki fuskarki sannan ki bani labari wanda zai kwantar min da hankali if not zanyi miki abinda yafi na farko kuma anan dan haka ki bari mu rabu lafiya kafin nayi miki karfa karfa na gwada miki kunjina ya zarta duk yadda kikayi tsammani .
jarumta ta sanyawa jikinta sannan ta saki fuskarta ta fara magana a hankali "inda banyi tsammani ba anan na fadi sai dai banji zafi ba tunda adalilin kallonka ne, shiru yayi yaki cewa komai ya cigaba da kallonta yana murmushi daga ciki domin dai yasan ta rasa abinda zata fada ne "adnan ..!"
Ta kiran sunasa a shagwabe ya jita sarai amman yaki ansawa ya cigaba da kallonta murya a shagwabe tace “kace na saki fuskata nayi ,kace na baka labari gashi nayi amman kayi shiru kana kallona inata magana kaki kace komai “
“Baki fada abinda ya kamanta nayi magana bane ki cigaba ina jinki idan akwai abinda zance zanyi .
“Kana jina?ya gyada mata kai alamun "eh!tare da fito da bindigar pistol ya ajiye a saman table din gefensa dan ya sake tsoratata Da sauri ta zaro idanuwanta waje cikin tsananin tashin hankali tana dafe qirjinta da duka hannuwanta muryarta a sanyaye tace “dan girman allah ka maidaita mutane na kawo min kayan marmari a matsayin kayan dubiya amman kai ko sau daya baka kawo min komai ba sai bindiga zaka fito min daahi ?".
Ta karasa mgnr tana sake canza fuska tamkar an aiko mata da sakon mutuwa "gasky ban gode da zuwanka nan yau ba.."
Ganin yadda ta fassara abun yace "Ammmm….. "
tayi saurin katsesa ta hanyar cewa “No karka ce min komai ka dauka kawai ka maidaita inda ka fito daita tun kafin mumy da mutane suzo su gani na shiga uku .
naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfi sannan ya dauka ya soke bindigar ajikinsa shiru ne ya ratsa dakin na tsawon minti shabiyar banda saukar numfashi su baka jin komai a dakin kowannensu da abinda zuciyarsa ke tsakawa akan danuwansa ganin yadda ta hade rai tana hura hanci ya furzar da iska mai zafi sannan ya bude bakinsa da kyar "karki dauka wani abu ,nayi haka ne dan na takureki amman ban san hakan zai bata miki rai ba yana rufe baki mumy na turo kofar dakin bakinta dauke da sallama a hankali ya dago ya dubeta yana amsa sallamarta ta tsaya abakin kofar dakin tana kare masa kallo sama da kasa da sauri ya dan rusuna ya gaisheta tare da sunkuyar da kanshi kasa yana mai jin tsananin faduwar gaba da kunya.
"wannan shine adnan ?" ta fada tana kallon tanwer ta gyada mata kai tana wasa da yatsun hannunta,
gaban mumy ya shiga faduwa "wannan fuskar kamar ta taba ganinta amman wallahi ko zaa daura mata bindiga a yanzu ta manta inda tasanta amman tabbas ta san wannan fuskar bata sake cewa komai ba ta karasa inda table din da ake ajiye abincin mara lafiya ta ajiye basket din hannunta ta juya ta shiga wani karamin daki a lokacin ya dago kanshi ya bi bayanta da kallo yayinda tanwer ta rike habarta tana kallonsa shi kuwa tunanin yanayi da mumy ta shiga data ganshi yake so yake ya gano abinda ke tattare daita ya soma kokarin mikewa ta yatsina fuska alamun bata son ya tafi "mutane suna mana kallo wani irin wanda shi kanshi aikin fashi da muke muna yi né domin raya wasu da kwatowa wadan da aka zalinta hakinsu "nasani amman su mutane wani irin kallo suke muku.
"ku barsu a haka amman babu wani bambamci mu din kamrku muke idan ma akwai bambamci kadan ne "haka ne allah ya muna min ranar da zaka ajiye wannan aiki ,wallahi da har aikin haji zan koma domin muna farincikina da godiya ga allah ".ta karasa fadar haka tana sakar sakar masa murmushi , yay mugun tsareta da rikitattun idanunshi yana kallonta kafin daga bisani ya sakar murmushi sannan yay mata sallama "zan wuce zan kiraki da daddare naji lafiyarki ya soma taku a hankali tabi bayansa da kallo tafiyarsa kamar ta maaikaci kaki sam bayi kama da dan fashi ba uniform yafi dacewa dashi .
Ahankali ta lumshe idanunta tana jin wani iri yanayi ajikinta bata jin zata iya hakura dashi ko tayi fushi dashi na wani lokaci né zata huce komawa tayi ta kwanta tana tuna moment din da suka kasance tare mumy kuwa bayan shigarta daki soja kaninta ta kira a waya byn ya dauka suka gaisa tace “acikin abokanka da kukayi karatu a NDA waye adnan ?a zaune yake amman sai daya zauna saboda tmbyr datai masa ta kusan mintuna shabiyar tana sauraronsa akarshe sukayi sallama ta katse kiran ta koma inda tanwer ke kwance ta kira sunanta.
Ta bude idanunta da kyar sannan ta yunkura ta mike ta zauna tana cewa “mumy ya kika ga adnan dina?mumy tayi murmushi “tanwer kenan gbdy soyayya ta caczaki idan aka ce min zakiyi kaca kaca a soyayya zan karya sai gashi ina gani da idanunta allah yasa kar soyayyar wannan mutumin ya zautar dake.
Allah ma bazai sa ba mumy ai ya cancaci aso ne har ma fiyye da haka mumy ta dauki pillow kujerar da take zaune akai ta wurga mata “lallai tanwer allah ya shirye ki ya kuma tsare min ke daga sharrinsa “Ameen mumy amman ya kika gansa yayi ko bai yi ba ?.
“Perfect! mumy ta fada tana mikewa tsaye bari na zuba miki abinci dan soyayya ta mantar dake yunwar da kika kira kina ji ta karasa ta bude kular abincin data kawo tanwe ta mike ta soma tafiya tana dingisa kafarta daya ta karaso inda mumy take tsaye tana zuba mata abinci a plet “mumy dan allah kiyiwa dady mgn kema ki yarda da aurena dashi ni kuma zanyi kokarin naga ya canza .
“abinda nake ta kokari fahimtar da dad dinki kenan yaki ya kafe akan lallai bazai yarda ba intakaice miki yace ko mutuwa zakiyi abarki kiyi amman bazai yarda da wannan auren ba “haba mumy kiyi duk yadda zakiyi dady fa naji dake yana kuma jin maganar ki ,wannan karon yaki ya lashi takobin yaki matsalar dai aikinsa ta juya ta ajiye plet din abincin akan karamin table ,zoki zauna kici kasa bin umarnin mahaifiyarta tayi ta tsaya tana kallonta ranta duk a dagule,mumy ki tsaya min dan allah ni kuma nayi miki alkwarin bazan auri adnan da wannan saba’ar ba wallahi dana auresa a matsayin dan fashi gara na mutu …”
Shiru mumy tayi tana dubanta tare da nazarinta tabbas maganarta da yanayinta ta nuna har cikin zuciyarta haka take nufi ,”zanyi kokari tanwer nima yaron ya kwanta min arai.

Kai tsaye jaguwa gidansa ya wuce zuciyarsa cike da tunanin tanwer yayi hon mai gadinsa ya bude masa tafkeken get ya shigo tun bai karasa parking din motarsa ba ya hagi mutun uku zaune jabir kamil,da jubi suna sha tabar wiwi yayinda kwalabar explorar ke ajiye agaban kowa ya karasa yayi parking din motarsa ya fito yayi mata key ya soma tafiya har ya karaso inda suke zaune idanunsu tamkar garwashin wuta, jaguwa ya dan tsaya nesa kadan dasu yana tambayarsu “anas fa?da hannu suka nuna masa inda yake ya juya yasa kai ya nufi hanyar part dinsa na baya anan ya tarar da anas zaune yayi shiru tare da zabga tagumi yana tunani iri iri acikin zuciyarsa har ga allah baya marmarin su cigaba da wannan aikin sai dai uban gayyan yaki bashi hadin kai dan koda yace masa a abuja idan sun dawo gida zasu yi mgn bai bashi lokacinsa ba lamuran gabansa ya cigaba duk da yasan ba wai ya manta bane lokacin maganar ne bashi dashi .”
daga wannan tunani ya ajiye ya shiga ta aure “yanzu wace yarinyar zai samu ya aura da wannan rayuwar da suke yana jin tsoron faruwar wani abu akansu batare da suna da yayan da zasu nema masu sausauci agurin allah ba “? dama yana da uwa ko uba ne ko dangi da zasu dinga binsa da addua byn baya raye bashi da kowa “waye zai tallafa masa idan sun shiga hannu tunda yasan lallai idan har basu tuba sun daina ba wata rana zasu kamu tunda kwana dubu na barawo ne rana daya na mai shi ?”.
jaguwa ya dade tsaye akanshi anas bai sani ba har sai daya dafa kafadansa batare daya kira sunansa ba ya waigo a dan firgice ganin jaguwa ne ya sauke naunayen ajiyar zuciya yana riko yatsun hannunsa ya zagayo dashi gabansa ya zaunar dashi akan kujera “bazaka rabu da tunanin aure ba ko? ai shine mafuta akarshenmu”
“bashine ba mafuta ba kanason mu tafi

Please Login or Register in order to submit comment