Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ajiye mata kudi bandir din yan dubu day day na 50k “ga wannan babu yawa ni zan wuce ,haba anas har da wata hidima?babu wani hidima ammi ki samin albarka shine abinda nafi bukata daga gareki ,allah yayiwa rayuwarku albarka gbdy ya daukakaku a idanun duniya ya rufa muku asiri duniya da lahira Ameen ammi na gode sai anjima ya sa kai zai fita hally ta biyo bayansa domin masa rakiya ,”

A haraban gidan haseera ta samesu kamar zasu shige jikin juna ganinta yasa suka dan bawa junansu tazara ta karaso tana cewa hally ki dan mana exuse bata damu ba sai ma shigewa ciki da tayi haseera ta gyara tsayuwa tana tsura masa ido “ada tunanina kana cikin wadan da suke zuga adnan akan kin aurena amman a yanzu na fahimci Kai mutumin kirki ne sannan nasan kasan matsayin da nake dashi azuciyar abokinka ko zan iya sani wani abu karka min karya ka fad’a min gsky sbd allah ?” yayi shiru yana kallonta d’an ta dauresa tunda ta kira allah ,
“Adnan yana da burin aurena ko kuwa wata can yake da burin aura?Kamar yace mata eh sai kuma yayi shiru” idan ma bashi da burin aurena gara ya fada nasan matsayina ba nayita jiran gawon shanu ba “kibi komai a hankali haseera Kinsan shi alamarin na aure nufi ne na allah da zarar lokaci yayi kuma kece matarsa zaa yi idan bake bace haka zaki hakura“.

“Bama zai zamo bani bace matarsa dan da yaje ya kwaso wata gara ace nice zan shiga gidansa kai ni aurensa ko ba alkhairi bane ina rikon allah ya mallaka min shi yayi shiru yana kallonta yana hadiye wani dunkukallen abu daya tsaaya masa a makoshi
“jikina yana bani zuciyarsa naga wata amman nasan kowacece bazata fini da komai ba sannan bazata zamo min natsala ba ,ga sako ka fada masa idan ma zai dawo da hankalinsa gareni yayi idan bazai dawo ba sai dai ya mutu bai yi aure ba amman ko zanyi yawo tsirara sai na zama mata agidansa domin shi din nawa ni kadai , idan baka sani ba na fada maka wani abu mahaifina ne ya taimaka masa har ya kawo matsayin da yake a yanzu amman dake shi dan adam masu manta alkhairi , yanzu kai a ganinka ya dace sakayyar taimako da mahaifina yayi masa ya fada akan wata bani ba …?

Sai allah ya kaimu byn sallah ayi sallah lafiya karku manta da naman sallahna lol love you guy’s



Mmn sudais



💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️39



......Tunda ta  fara magana yake kallon bakinta yana jin wani irin zallar'bacin rai mai tsanani  ,dan idan akwai abinda ya tsana  a rayuwarsa bai wuce yaga ana shiga rayuwar jaguwa ba ko ai bantashi , bai sake ce mata komai  ba har  sanda ta  gama  magnrta , sai dai kallo daya zaka masa ka fahimci fuskarsa ta canza daga farinciki da yake ciki zuwa bakinciki ,tayi shiru ta zuba masa idanunta tana kallon fuskarsa da sam babu annuri kwance akai
a hankali ya dauke kansa daga kallonta .”
cigaba da kallonsa tayi tana jiran taji mai zai ce mata ,ganin yayi shiru yaki cewa komai yasa
ta gyara tsayuwarta tace "da fatan zaka fada masa sakona?."bai kalleta ba ya furta "a'a bazan fada masa wannan sakon ba amman idan ke kinji zaki iya to Ki samesa da kanki ki fad'a masa watakilla ma zai fi fahimtarki akaina ". yana gama fadar haka bai tsaya jiran me zata sake cewa ba ya juya a natse  ya nufi get din  gidan, bayansa tabi da kallo  yana taku a hankali shima kamar adnan din yake ta  fada a kasan ranta ,komai nashi mai kyau da tsari to ya ma za’ayi abokansa ba zasu kasance kamarsa ba ?."Jiki a sanyaye ta juya ta nufi cikin gidan tana nazarin yanayin daya shiga a lokacin da take masa magana akan adnan "kamar bai ji dadin maganarta ba ?tayiwa kanta tambayar  ,tabe labbabta tayi  tana cewa "kar allah yasa kaji babu dadi  aranka tunda zaginsa nayi da zaka wani ‘bata rai taja tsaki tare da shigewa ciki ."

Ahankali anas ya bud'e motarsa ya shiga ya zauna da kamar ya kira hally ta fito suyi sallama  sai ya fasa ya kira layin ta yana kokarin yiwa motar key  har ya bar unguwar suna waya tana zuba masa shagwaba lokaci daya yaji ta yaye masa dukkanin damuwarsa ,bai tsaya akoina ba sai a kofar gidan jaguwa yayi hon mai gadi ya taso ya bude karamin hujin get, ganin shine ya soma kokarin bude masa babban get ya sanyo hancin motarsa cikin haraban gidan mai gadi na daga masa hannu ,ya karasa inda yake parking din motarsa yayi parking ya kashe motar ya fito yana gyara zaman rigarsa adaidai lokacin da mai gadi ya gama rufe get ya karaso gurinsa cike da girmamawa har zai rusuna masa Ana's yayi saurin dakatar dashi yana cewa "haba baba sau nawa zance maka ka daina duka min ? ai ko baka haifeni ba kayi kani kusan na biyar dani please ka daina bana so ,ya fda yana mika masa hannusa ,gaishesa mai gadi yayi yana murmushin jin dadi dan ba yau bane karo na farko da anas din ke hanashi rusuna masa sabanin sauran ya amsa masa gaisuwar a mutunce kamar koda yaushe sannan ya nufi ciki gida yana shafa sumar kanshi ,binsa mai gadi yayi da kallo gabadaya rayuwarsa ta sake sauyawa ,kamala da natsuwa sun samu kyakkyawan zama ajikinsa har wata yar kiba yayi ta kwanciyar hankali ."


Zaune ya iske jaguwa zaune akan kujera a parlour ya daura kafafunsa saman table jikinsa sanye da jajayen kaya wando da riga yana operating laptop , cup din coffee na daga gefen laptop dinsa ,yayinda jabir ,
kamil da jubi suke zaune suna kallon wani film din  soyayya mai suna kuchi kuchi hotahe, sai faman murmushi suke ,sallamrsa ce ta dawo da hankalinsu bakin kofar shigowa   har shi jaguwa sai daya dago kanshi a natse daga kallon laptop da yake ya maida idanunshi kan anas dake tsaye yana dubansu alokacin murmushin farinciki bayyane akan fuskarsa  yace "da dai kunje kunyi aure da wannan kallon da kukeyi ,a aure ne kawai zakuji gardin soyayyar gaskiya  ba irin wannan na film ba  wanda nishadi kawai zai dinga saka ku .” ya karasa maganarsa yana mikawa jubi dake kusa dashi hannu domin su gaisa  still fuskarsa dauke da murmushin tsokana ."


     jubi ya hade hannuwansu guri daya  ya tsarke sosai yana cewa "kai ma ba wayonka ne ya baka auren  ba ,  taimaka maka akayi aka baka ko kuma nace shishigi da nemana gindi zama da kutse acikin arayuwar wasu yasa akabaka aure if not da haka zaka mutu babu aure dan babu wacce zata aureka da irin rayuwar da kake ,ko ka manta kai din dan giya ne ? sannan kuma mane min mata ?."
"Idan ka manta na tuna maka wane ne kai ,mu ka barmu a yadda muke din nan yafiye mana  dadi da wata rayuwar aure can wanda babu komai acikinsa sai takura ,wani dadi kake ji a aure da mu bama ji ?." ya tambayesa yana kafesa da jajayen idanunshi
“kwana kake da mace muma idan muna bukatar kwana da mace zamuyi ko ba haka ?”saurin maida idanu jaguwa yayi akan jubi wanda ke maganarsa hankali kwance yana duban sauran abokansu babu wata shakka ko fargaba daya nuna a fuskarsa .”
jubi ya cigaba da magana a zafafe "shasha yana da kyau ka dinga iya bakinka akan komai dan zakewarka tana dada yawa idan ba haka ba zaka tsinci kanka cikin nadama .”ya saki hannunsa ya fusace ya maida idanunshi kan kallon da yake wanda hakan yasa sauran basu samu damar furta abinda ke cikin  ransu ba dan duk abinda suke son fad'a jubi ya rigada ya fad'a masa hakan kuma ya wanke zuciyarsu."
  
  hakan nan maganar jubi ta caki zuciyar jaguwa sosai  har ya kasa dauke idanusnhi akansa bare ya cigaba da aikin da yake sai daya maimata maganar jubi kusan so uku acikin ransa kafin ya dauke idanusnhi ya kalli anas da yake tsaye kikam yana kallonsu jiki a sanyaye ,a kallon da yake masa ya fahimci jikinsa da kafafunsa rawa suke ,shi kansa cikin tsananin kaduwa da bugawar zuciya yake cigaba da kallonsa yayi sam bai ji dadin kalaman jubi garesa ba haka zalika yasan anas din ma bai ji dadi ba dan gabadaya yanayinsa ya sauya amman yasan babu matakin da zai dauka ,nemo jarumta Ana's yayi ya sanyawa jikinsa.”

"Friend !".

Ana's ya  kira jaguwa a natse yana sakar masa murmushin dole dan da zaa bude zuciyarsa bakinkirin zaa gani tsabar bacin rai ,jaguwa bai
amsa ba illa kallonsa da ya cigaba da yi ,shi kuma ya samu guri ya zauna a kusa dashi  yana basarwa tamkar maganar jubi bata ta’bashi ba a kallon da yakewa jaguwa ya Karanci damuwarsa ,hargaginsa yake gani tamkar daminsa daya ga abinsa kuma yake shirin rasashi domin nuna masa bai ji haushi ya ba ya maida hankalinsa gasu jubi yace "kuyi hakuri frindes ban san maganata zata bata maku rai ba da banyi ba amman ni da wasa nake muku tunda nasan komai yana da lokaci shi aure kamar mutuwa ne idan .." dan allah malam ka rufe mana baki kasani mana “. Kamil ya katseshi yana  zaro masa ido kamar zai cinyesa tare da jan tsaki ,anas ya dan kallesu a firgice zuciyarsa na buguwa da karfi ".
“Tunda kayi aure ka karo sabon wulakanci akan wanda kake yi ,sai  wasu abubuwa kake yi kamr akanka aka fara aure ko zinariya ka aura iyakcin abinda zakayi kenan bare ba zinariya bace mutun ce dai kamar kowa da zaka wani damu mutane ."

tsam jaguwa ya tashi daga shi har laptop da coffee dinsa ya soma tafiya tun kafin zuciyarsa ta tarwatse  dan bazai dauki wannan rashin mutuncin akan jininsa ba ,idan kuma yace zai cigaba da zama to lallai zasaka bakinsa kuma hakan zai sa su yi korafi akan yayi side din anas ,shima Ana's ya tashi tsam ya biyosa zuciyarsa ta tafarfasa sai dai yana ta kokarin tausarta.”
kusa atare suka shiga dakin jaguwa ya samu guri ya zauna a kujerar falonsa qirjinsa na zafi da ciwo shima Ana's ya zauna a gefensa ,jaguwa  bai kalli inda yake ba haka zalika bai ce masa komai ba dan bakaramin haushi ya bashi shi kansa anas ya fahimci haka dan haka ya motsa bakinsa "kayi hakuri ya fad'a yana kallonsa cikin tsananin damuwa ."
Jaguwa ya dan ciza lip's dinsa na kasa da karfi  "me yasa Ana's ?"
"Me yasa kake yin abinda banaso ?"Am so sorry adnan bazan sake ba kuskure ne ya fad'a jiki a sanyaye yana gyara zamansa yana qawalo murmushin dole "tunda sun nuna basa son kana shige musu me yasa bazaka hakura ba ? .”
“Ko dole sai ka tsokanesu? shiru anas yayi yana dubansa “.ya kamata zuwa yanzu ka san yadda zaka dinga yin muamula dasu tunda sun nuna basa son kana masu irin wadan nan zantuttuka na tsokana please ka daina ." murmushi stil anas ya sake yi yana cewa "shikenan an daina inshaallahu "kai fa baka daukar tsanar da suke  maka a kwanakin da mahimanci ,ni kuma na dauke shi da mahimancin daya zarta tunanin jama'a ,a nawa tunanin ma gani nake sun tsaneka ne tsana mai muni amman dai nasan yadda zanyi da...... ".

"Kai haba dai kai kuwa karka yi wani tunanin dabam akansu nifa bana ganin laifinsu ko kadan sai namu,duk kai ne ka jawo komai daga lokacin da'aka boye musu maganr aurena na fahimci basu ji dadi hakan ba shima dalilin sauyawarsu gbdy ,kuma ko ni ne haka zanji  babu dadi araina."
"  duk da haka bai kamata idan ma haka ne ai bai kamata su rike abun  acikin zuciyarsu har haka ba ."lumshe ido anas yayi "babu komai zan sake basu hakuri kai ma ka basu hakuri mu cigaba da rayuwarmu kamar yadda muka saba babu jin haushin juna babu kyashi ko hassada a junanmu sannan ya dauko wayar jaguwa dake ringing ya mika masa sunan da ya gani ne yasa ya ajiye wayar ya dauki cup din coffee ya kai bakinsa yana kurba a hankali.”
kallon mamaki  Ana's ya zuba masa sannan ya dauki wayar yana duba screen din wayar  nan yaga sunan tanwer yana yawo ya waiga ya kalli jaguwa  "ban fahimci kin daukar wayarta da kayi ba?  batare daya kallesa ba yace "bashi da amfani ne shiyasa  naki dauka "ya kamata kayi hakuri adnan haka ,komai na rayuwa fa mai wucewa ne wallahi this duniya is noting adnan yau idan mune gobe bamu bane yarinyar nan tayi nadama dan allah ka yafe mata tana sonka dayawa bazata iya rabuwa da kai ba yana da kyau kasan darajan soyayya me ye laifin wanda ke sonka ?.

"Babu !.
Ya bashi amsa atakaice "to why adnan kaima fa baka kyauta mata ba ,dan bai dace abinda kayi mata a gaban mutane ba ,kamata rashin mutunci a gaban saurayin da bata so sannan ka hadata da kalmar useless ai kowa ma kayi haka zai iya haukace maka .”jaguwa ya saki wani murmushi da ajiyar zuciya atare yana shafa gefen fuskarsa ko yanzu fuskarta ke masa yawo acikin kwakwa luwarsa ,ita kadai ce ta samu wannan matsayin acikin arayuwarsa, dan bai iya mantata duk abinda yake tana nan makale a ransa tana yawo a jinin jikinsa  tun yana mamakin matsayin da take dashi a zuciyarsa har ya zo ya daina."
Sai daya numfasa kana ya motsa lip's dinsa "kenan ta kiraka ta fada maka na kirata da useless?".sosai kuwa dan abun ya dame ta matuka tana min bayani tana kuka "idan har ta fada maka daidai a maganata babu inda nace mata useless ,i said that who is doing that they will be thinking that is useless that's ol ,duk da haka dai bai dace ka fadi haka ba ,a natse Ana's ya dinga rarrashinsa yana bashi hakuri ya yafewa tanwer sannan ya amince da soyayyarta shi kuwa sai murmushi yake yake wa anas yana jijiga kafarsa daya ."

Ana's ya sauke ajiyar zuciya yana dubansa "ka hakura ta kiranka komai ya wuce ?"Kira kuma na  sau nawa ai tun jiya take kirana ban dauka ba dan banga amfanin kiran ba bare na dauka ,dazu da safe ma naga shigowar sakonta ya karbi wayarsa yana nuna masa sakonta ,"Assalamu alaikum ,Good morning how are you doing my love"how was your night ? hope you had a great night?let us thank allah for the gift of another day and please forgive me and forget what I did to you  " girgiza kai kawai anas yayi yana cewa "kai  dai anyi mugu mai taurin zuciya ,
yanzu kai bakajin tausayin yarinyar nan ?ya girgiza kai batare daya kallesa ba .
“Kaga kuwa ni ina jin tausayinta wallahi har hawaye nake zubar mata dan tana mutuwar sonka ,kaso mai sonka adnan ka tausaya mai sonka ko da yake ai kana sonta soyayyarta ma ta musamman ce a zuciyarka ya fada ta tsigar tsoka , jaguwa ya waigo ya kallesa a natse sai dai bai ce masa komai ba hakan kuma ya nuna bazai ce din ba “allah dai ya shiryeka sarkin zuciya da taurin kai jaguwa yayi murmushi yana shafa sumar kansa ,bari  naje na sake bawa friend's hakuri magana ta wuce banason ina tare da mutane naga na bata musu rai “jaguwa yace “sauka lafiya aminin kirki .”anas ya mike ya fita daga dakin shi kuma ya cigaba da aikinsa yana murmushi yana tuna tanwer ".


Suna zaune har lokacin a falon ya samu guri ya zauna yana fuskantarsu sunga shigowarsa da zamansa amman sukai masa banza tamkar basu san da zaman mutun agurin ba ya gyara zamansa ya kirasu "friends!" amman babu wanda ya juyo daga cikinsu ya kallesa bare yasa rai zasu amsa masa "please kuyi hakuri idan akwai wani laifi da nayi muku yasa kuka tsaneni yanzu ,ni dan adam ne ta yiwu nayi muku Kuskuren bisa rashin sani amman ni atunanina idan nayiwa daya daga cikinku laifi kamata yayi ku kirani ya fad'a min domin in gyara kuskurena ,dan idan ni ne bazan rikeku araina ba zan fada muku komai ya wuce mu cigaba da rayuwarmu cikin soyayya da walwala ,dan allah kuyi hakuri ku yafe min ."

shiru falon yayi babu wanda yace masa uffan ya mike daga inda yake zaune ya karaso ya zauna akan table din dake tsakiyar dakin ya riko hannun jubi domin a komai shi ke fara daukar zafi "kayi hakuri abokina duk da wallahi ban san nayi muku laifi  ba  amman ita rayuwa haka take wani abu Kalilan zai iya kawo fitinar da zai shiga tsakaninka da kowa ya fad'a yana kallonsu daya bayan daya a tare suka sakar masa murmushi wanda da gani na yake ne "karka damu komai ya wuce inji cewar jubi "na gode Kwarai da gaske amman dan allah me nayi maku ?ina son sanin abinda nayi muku saboda na kiyaye dan gaba "me ye amfanin aita tada magana anas bashi da wani amfani allah dai ya yafemu gbdy jubi na rufe baki anas ya mike ya juya yana masu godiya sai ganin jaguwa yayi tsaye ya rungume duk hannunwansa a qirjinsa fuskarsa da alamun annurin farinciki dan yaji dadi kwarai da suka fahimcesa ."
"Ya ka tsaya ka karaso ka zauna ka karasa bayyana murmushin farinciki dake ranka?inji cewar kamil .
jubi yace "ai dole kaga farinciki a fuskarsa tunda anas ne bakaga dazu fushi yayi ya tashi ya bar gurin saboda an taba zuciyarsa ba ," ya karasa maganar yana fakar idanun jaguwa ya zabgawa anas harara dan shi hakurin dole yayi da yafiyar dole saboda ganin tsayuwar jaguwa daya gani ,kuma idan suna son cima burinsu akan anas lallai sai sunbi komai a hankali."

"ai dole na tashi na bar maku guri tunda naga abun naku har da wulakanci so kuke ku tarwatsa min zuciya, ga ciwa aminina mutunci ga tabo jinina ai abun yayi min yawa suka sa dariya gbdynsu  a hankali ya cigaba da mgn yana takowa ya tsaya a tsakiyar falon "rayuwarmu a tun farko a tsare take babu wanda ke jin haushin wani hakan kuma yana min dadi ,wannan yace ayi kaza wannan yace ayi wannnan kuma duk muna bin tsarin juna babu mutsu ko jayya a yanzu ma yana da kyau mu cigaba a yadda muka dauko dan babu cin amana a tsakaninmu .”
“ban hana kowa aure acikinku ba ,wallahi duk wanda yake bukatar aure acikinku ya nemo mata zan tsaya masa da iyakacin karfina na taimakeku
sai dai idan abun ya gagareni idan kuma hakan ta kasance zan shigo da wasu ciki ayi komai cikin sauki da nasara .”

Yayi shiru yana kallonsu daya bayan daya yana nazarinsu alhamdulillah ya fahimci duk sun sauko daga mummunar fushin da suka jubi ya kallesa yana murmushi wanda bai kai har cikin zuciyarsa ba sannan bai jin zai canza daga idar da nufin sa,wani irin zafi yake ji acikin zuciyarsa "tunda ya basu damar aure yace mahaifiyarsa ta haifo masu mata kamar yadda ta haifawa Ana's wannan shine maganar dake kwance akan harshensa sai dai yasan matsawar yayi ganganci ta fito daga bakinsa allah ne kadai yasan maseefun dazasu faru ."
A natse jaguwa ya dinga jansu da hira yana bawa kansu shawarar har suka shigo da wata hirar cikin nishadi kowannensu na tofa albarkacin bakinsa shi dai anas yanata taka tsantsan da abinda zai fada dan hararar da suke fakar idanun jaguwa suna masa ya tsaya masa arai sallah ne kawai ke ta dasu har biyar tayi anas ya mike alamun zai wuce jaguwa ya kallesa “har zaka wuce ?ya gyada masa kai zanje na dauko hallay a gidan ammi mu wuce gida ,okay gobe ka shigo da wuri saboda fitar sconpio ya gyada kai sannan yayi musu sallama ."

*****

Karfe shida daidai a kofar gidan ammi tayi ma anas ya shigo a natse ya gaishe da ammi ,hally tana ganinsa ta mike tsam  ta soma shirin tafiya ta dauki bakar ledar da ammi ta bata wanda yake cike da kayan  sawa wanda ta dinka masu ita da shafiq sai wata leda dake dauke da magungun Kara ni!ima sukayi mata sallama hasera har bakin mota ta
rakasu suka shiga mota suka kama hanyar zuwa gida da zarar yaga tayi shiru zai tsokanota ita kuwa kewar amminta take dan ji tayi kamar karta koma gidanta ta cigaba da zama tare da amminta.
Ana's yayita kokarin kawar mata da tunaninta da hirar soyayyarsa mai cike da zolayar da ban dariya wanda yayi nasarar share dukkanin wata damuwar anas .
Suna shiga gida ta shiga gida dakinta ta ajiye kayan data zo dasu sannan ta cire mayafinta ta fito ta shiga kitchen ya biyo bayanta ya rike kugunta yana cewa "kada ki daura komai ki hutawarki zanyi mana order abinci hakan daya fad'a yasa ta ajiye abun kunna gas ta biyosa suka fito daga kitchen yana manne daita "sannu duk kin gaji ko?".
"Babu wani gajiya ina dai son hutawa ne ."yayi murmushi "ai gani indai hutawa kike son yi sai muyi tare ai zaki fi jin dadi yayi mgnr tana daura gabarsa a wuyanta ta hararesa tana cewa "kai ko".
"Ni ko me ? kodan na fiyye sonki dayawa haka allah yayi ni ni mai son hally ne kuma hakan abun alfahari ne agurina ta dan yi murmushi ya zareta ajikinsa ya fita bai shigo ba sai byn sallahr ishai wannan shine kaidarsa tunda ta tare a gidan baya  shigowa sai yayi ishai ,a fadarsa tace mata ana karatu a masalacin dan haka yake zama har a idar da ishai sannan ya shigo, sai byn takwas da rabi  ya shigo masu da lafiyayyen abinci byn sun ci suka makale juna suna kallo wannan daren ma sun more junansu cikin tsabanin so da kulawa ."

washegari bai tashi da wuri ba saboda gajiyar sex sai gurin karfe goma ya tashi da wani matsanancin ciwo kai ya dafe goshinsa da hannunsa daya bai tasheta ba ya shiga bayi ya fara sakarwa kanshi ruwa kafin yayi wanka a daddafe ya fito ruwa na kwance a sansar jikinsa still tana kwance  cikin bargo tana baccinta hankali kwance ,ya goge jikinsa yana ciza lips dinsa ya shafa lotion ajikinsa yana sake jin yadda kansa ke mugun sara masa wardrobe dinsa ya nufa  idanushi na kanta yana kallonta ya shirya cikin kananan kaya ya  karaso ya zauna a bakin gadon yana kallonta tana sauke numfashi a hankali ya kai  hannunsa yana shafa fuskarta yana jin kamar ya cigaba da mata numfashi ta huta .”
bakinsa ya kai daidai idanunta  yayi kiss  a hankali ta bude idanunta dake cike da bacci dishi dishi take kallonsa wani murmushi ya sakar mata yana dage mata gira "zan fita my princess sai dai wata killa zan dade yau ban dawo gida ba ki kular min da kanki .
Ahankali ta motsa lip's dinta "a dawo lafiya allah ya tsare min kai ,kai ma ka kular min da kanka please matsota yayi sosai Kmr zai shige jikinta dan baya gajiya daita ,suka dan zubawa juna ido ko kyaftawa basayi   ahankali ta maida idanunta ta rufe saboda baccin dake cikinsu shima naunayen ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mike yana duba time  agogon dake daure a

Please Login or Register in order to submit comment