Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaya mana ." ransa yayi mugun baci akan wanda yake ciki " me yasa ta fito cikin ruwa tana kiran sunanshi gashi ta jawo duk jikinta ya jike da ruwa har ya nuna sha shin jikinta ?a kallon da yake mata ta fahimci abinda yake nufi yana da tsanani tausayi da kulawa  ,tausayinsa  ya kamata shi din mutun ne me matukar tausayi ga mutane matsalarsa dai taurin kai idan ya tsaya akan abu babu wanda ya isa ya kawar dashi ko tsaida shi ,tarasa me zatayi domin ta canza shi ya dawo mutumin kirki a idanun duniya ."tsaki yaja  sannan ya riko tsintsiyar hannunta cikin nashi atare qirjinsu ya buga da matsanancin karfi ,ji yayi wani shock ya caki jikinsa da duk wasu jijiyo dake aiki ajikinsa,itama haka taji a sansar jikinta,”
maganad’insun son junansu ne ya shiga yawo a jijiyoyin jikinsu sai dai babu wanda yayi magana acikinsu har sanda  ya soma tafiya daita bai tsaya akoina ba sai ajikin motarsu ya bude murfin motar sai lokaci yaga ashe ba ita kadai bace aciki ita da ruky cousin dinta ne ,ta bude baki ta gaishesa amman yayi mata banza tamkar bai ganta ba da hannunsa ya nuna mata cikin motar sannan ya raba gefenta  ya cigaba da tafiya ya karasa inda motarsu take ya shiga yajata da mugun gudu yana jan tsaki ".


"Lafiya !?Anas ya tmbyesa "wacan motar dana taimakawa tsohon can ashe tanwer ce zaune a bayan motar tsabar rashin Imani da tausayi ta bar tsohon mutane ya fito cikin ruwa ita da cousing dinta  suna hakince abayan mota shiyasa naji motar tayi nauyi ya karasa maganar yana murza sterimg yana jan tsaki ."kai adnan tanwer din da consin dinta guda suke da zasuyi nauyi ?bai sake cewa komai ba dan haushi sannan bai  tsaya ba sai akofar gidan  anas .
“Sauka mana na qara gaba Ana's yace "ka shiga ka sauya wasu kaya mana ."ya girgiza masa kai ya kara  gaba da gudu  shi kuma anas ya shiga gidan  ya zauna a falo sharaf yana jiran princess dinsa ta fito tayi masa sannu da zuwa wacce  lokacin tana can tsaye gaban mirrow tana tsara masa kwaliya."
byn ta gama ta karasa  wordrobe dinta ta dauko daya daga cikin kayan da ammi ta dinka masu ita da shafiq ta saka ,ta  dauko dan karamin akwati dake dauke da sarkokinta  kowanne na cikin gidansa tare da dan kunnensu  ta dauki wanda take son sakawa ta fara saka dan kunne ta dauki sarka wuya zata saka kenan Ana's ya shigo dakin bakinsa dauke da sallama ."

A hankali ta motsa bakinta ta amsa masa tana sakar masa murmushi ya tsaya a bakin kofar dakin yana kare mata kallo tsab dan ba karamin kyau tayi masa ba ,naunayen ajiyar zuciya ya sauke sannan  ya tako zuwa inda take  tsaye ya tsaya ta bayanta tare da riko kugunta da hannunsa daya ,Kallo daya tayi masa ta cikin mirrow ta fahimci yana cikin damuwa  dan haka ta juyo gabadaya ta zuba masa ido tana sake karamtarshi ,meke damunka ka fita cikin damuwa ka dawo min da damuwa ? girgiza mata kanshi yayi alamun babu  ya kai lips dinsa ya tsotsa bakinta  kadan ya zare bakinsa  ."
Wani wahalallen numfashi ta sauke wani irin zazzafan soyayya take masa tana kallonsa ya karbi sakar dake rike a hannunta ya makala mata a wuya tare da shafa gefen wuyanta sannan ya zagaya da hannuwansa duka saman cikinta cikin kasalalliyar murya yake mata magana acikin kunnenta "my princess kina da kyau sosai a duk sanda na kalleki sai nayiwa allah godiya daya azurtani  da samun salihar mace  irin ki dan allah ki soni duk runtsi karki barni ".

Murmushi  tayi masa ta dago idanunta suka tsarke cikin nashi "nima ina alfahari da samunka matsayin miji  ,ya sake riketa gam yana lunshe idanunshi  yana busa mata numfashinsa ta hanyar shinshina wuyanta a karshe ya zira harshnesa cikin kunnenta gbdy ta wani rikice tsigar jikinta suka shiga mikewa ta soma kokarin zare jikinta shima a rikice ya  sake riko kugunta  sosai yasa dayan hannunsa ya hade fuskokinsu guri daya hade da daura lip's dinsa akan nata kasa jurewa tayi dan haka ta sakar masa jikinta ta soma maida masa da martani daga cikin salon data koya agurinsa sun dauki sama da minti shabiyar suna tsotsan bakin juna tunawa da amininsa yasa yayi saurin zare bakinsa cikin nata atare suka sauke numfashi ".Adnan ya tafi ya hadu da commissioner zai dawo ko bazai dawo bai sani ba tharoom dinta ya shiga ya dauro alwala ya fito ya dauki carbi ya zauna ya dan jingina da abun gado yana já ita kuma ta fita daga dakin.”

Bangaren   jaguwa kuwa  yayi tafiya me nisa daga gidan Ana's sannan ya samu guri yayi parking a daidai Devol hotel dake kan titi alabi ,yayi   baya da kujerar da yake zaune ya koma ya  kwanta ya runtse idanunshi  tanwer kawai yake gani cikin kwayar idanunshi shigar abaya da  tayi  yayi matukar masa kyau , kowani kaya ta saka sai ya zauna ajikinta  ,
bude idanunshi yayi  yana tunaninta yana duba lokaci har awa uku ta cika ya kira commissioner  Kira biyu ya dauka ya fada masa inda  zasu hadu , suna gama waya ya canza fuska ya shirya bindigarsa mai cin harsashi goma ya soke biyu ajikinsa  ya sake shirya biyu ya soke a kafafunsa yayi wa na karfasa shiri me kyau sannan ya dauki hanyar  water park  daman yana kusa da gurin tafiya kadan yayi ya karaso gurin yayi parking ta kofar baya ya fito ya shiga cikin inda mutane suke wasu da rigar wanka wasu kuma suna zaune akan kujeru na alfarma da kaya ajikinsu shima ya samu guri ya zauna ya kirasa  a waya "na karaso okay sir ".

Ko cikaken minti talatin  bai yi da kashe wayar ba ya soma jiyo qarar jiniya daman yayi tunanin bazai zo shi kadai ba dole sai da masu tsaronsa  nan take ya tashi ya boye har suka karaso ciki tare da masu tsaronsa yana maboyarsa yana kallonsa daga inda yake ya kirasa a waya yana kallo aka mika masa wayarsa "kana ina gani  nazo ?"Okay sir ina bayan ta gurin swiming  pool " kai kadai fa nace zazo ? "karka damu ni kadai ne .jaguwa yayi murmushin gefe baki  yana kallonsa yayiwa masu tsaronsa magana wasu suka biyosa ,wasu suka tsaya gbdy ya gama tsara yadda zai kawar dasu ya damki commissioner yana zaune commissioner ya karaso  daga nesa jaguwa ya daga masa hannu alamun shine commissioner bai karaso ba ya samu wani guri dabam ya zauna jaguwa ya karaso a natse cike da girmamawa kafin ya zauna
abinda yayi tunani shine ya faru masu tsaron commissioner mutun biyu da suka biyosa suka  fara kokarin duba jikinsa sai dai basu ga komai ba boyayyar ajiyar zuciya ya sauke sakamakon basu tabo bidigir dake boye a kafafunsa ba  ,commissioner ya nuna masa gurin zama yana cewa "ina bayyana mutuwar honorable Abdulaziz da inda gawarsa yake ?wondonsa yayi sama dashi kadan sai ga wani abu kamar roba shima yayi sama dashi sai ga  bindiga ta bayyana  muryarsa can kasa yace "ga bayyanan anan  " ya fada yana sauke wondonsa yana dubansa a tsanake ".

"Jaguwa !?
Commissioner ya furta ahankali ta yadda babu wanda zai ji dan tun ganin bindiga yanayinsa da komai nasa ya canza jaguwa ya lumshe masa idanunsa yana cewa " nasan ka girgiza da ganina ko ?amman karka girgiza ,nayi haka ne saboda banason na rasa wani na kusa dani ,ku kuma burinku na rasa kowa nawa ciki kuwa  har dani kaina, yanzu yanzu ka sallame masu tsaronka kafin muyi mutuwar kasko  dan ni da ka gani  mutuwa bata tsoratani da shirinta na fito ."
dago kai commissioner yayi yana basu umarni su matsa daga guri babu shiri suka yi nesa dashi jaguwa na ganin haka ya zaro bindiga ya soke ajikinsa yace "oya  tashi ko "! kamar wani karamin yaro commissioner ya mike tsaye suka jera ta baya yabi dashi  inda motarsa take "banason na taba lafiyar tsoho kamarka amman fa sai kayi abinda nake so zaka tsira da ranka da lafiyarka ."

Cikin mintunan da basu wuce uku ba jaguwa ya fice da commissioner suka nufa inda  motarsa  yake ya bashi umarnin ya zauna a  bangaren direba shi kuma ya shiga baya "ka  ja motar  muje suka bar area gurin gbdy shi kuma yana baya hakince ya saita kan commissioner da bindiga ,babu wanda yaga saita kan commissioner da jaguwa yayi kasancewar glass din motar baki ne "idan kayi aiki acikin second daya, kaima zan barka acikin second daya kayi tafiyarka ka cigaba da rayuwarka cikin koshin lafiya .”commissioner bai ce komai ba saboda matukar girgiza da yayi ,bama dansa ko wani nasa ba ,ko cikin yaran aikinsa zaa danawa tarko ba shi da kansa ?
"lallai wannan barawon ya wuce yadda suke tsammani"kasa a sako min yarona a yanzu nima na sakeka yanzu Idan wani abu ya samu yarona lallai kasawa ranka mutuwa, ban taba kashe kowa ba amman zan fara akanka muddin wani abu ya samesa ba ."

"Babu abinda zai samesa amman kai ka mika kanka  zuwa ga hukuma tunda daman an kamashi ne saboda ya bada bayanai  akanka ,idan ka mika kanka nayi maka alkawarin zansa a maka hukunci mai sauki ,  lokacin dana fara alqallarta kasani ko na nemi shawarka bare yanzu ka bani shawara na dauka"?ni nan da kake gani kamani zai yi matukar baku wuya  saboda nayi rayuwa acikinku nasan in and out dinku kai bakayi mamakin yadda na samu number office dinka ba "?"Ace  baka bani number ba zan samu kuma cikin sauki  kuma na tare da kai ne zasu bani dan haka babu ruwanka kayi abinda nake bukata kawai ka tsira da ranka ,babu waya a hannuna da me zan kira headquarters? sun yi tafiya me nisa sannan jaguwa ya tsaidashi alokacin duhun dare ya shigo dan bakwai da wasu mintuna sun wuce  .

Yayinda water park na can ya hargitse  adalilin neman commissioner da akayi aka rasa kafin kace me headquarters ya samu labari aiko nan ma ya hargitse ska soma Kokarin baza manya  ma'aikata titi titi lungu lungu domin bincike kowace mota jaguwa ya kira number Ana's kira daya ya dauka  yana tambayarsa halin da yake ciki "nayi nasarar kamashi abokina kasan na fada maka rikitaccen tsoho ne gashi ma na sashi yin abinda ya jima bai yi ba sai dai ayi masa ,tuki mana ai shi ya tukoni ,sai anjima daman na kiraka né kasan ina cikin koshin lfy dan nasan hankalika bazai kwanta ba yana gama wayar yace "wa zaka kira acikin wadan da suke karkashinka ?
"Mataimakina !"
Ya fada yana sauke numfashi "ina jinka karanto numbersa bai bata lokaci ba ya kirawo masa number sai da jaguwa ya boye number sannan ya kira tare da sata a hands free ,kira biyu cikin na uku A kwantagora ya dauka jaguwa ya manna masa wayar a kunnensa cikin harshen turanci yace "hello kwantagora ni ne  commissioner hope baka cikin mutane ?okay abinda nake son fada maka rayuwata tana cikin hatsari ,yanzu abinda nake da kai ka faki idanun kowa ka fito da yaron jaguwa da'aka kama  idan ba haka ba sai dai ku tsinci gawata  okay!!!
jaguwa ya katse wayar  ya gyara zama .

Bayan kamar minti talatin suka sake kira "sir gashi na fito dashi ina zan kai shi ?kaje under bridge din iyanapaja zan turo wanda zai daukesa yaji sautin wata muryar amadadin yaji ta commissioner bance karaka ka tafi da ma’aikatan sirri ba kaje dasu ni kuma nan zanji da commissioner. babu wanda zanje dashi dan allah karku taba lafiyrsa dan ….”
Jaguwa bai tsaya jin me zai ce ba ya katse kiran
Hankali a tashe kwantagora ya figi mota ya dauki hanyar iyana paja shi kuma jaguwa ya kira layin eku ya bashi umarni  zuwa iyana paja cikin mintuna talatin kwantogora ya isa sai dai dole yayi parking ya jira kira daga jaguwa ,alokacin shima eku ya karasa ya kira jaguwa ya sheida masa nan take ya kira number kwantagora yana dauka yace "kana daidai ina ?
"Ina daidai inda ake shiga motar ondo ,da uniform ne ajikinka ?eh !Ya   katse kiran ya kira eku sukayi mgn sannan ya sake  kira kwantagora yace ya bawa scorpion waya ya mika masa wayar sukayi mgn suna gama waya kawai yaga scorpion ya fito daga cikin mota  yana dingisa kafasarsa tun yana iya hangosa har ya daina akan titin mowe ibafo jaguwa ya ajiye commissioner ya kara gaba ."

A tare jaguwa da eku suka karaso gida gbdynsu babu wanda bai yi mamaki  ganin Scorpion dan basusa rai zai fito acikin kwana daya ba ,lokacin da jaguwa ya fad'a musu abinda yayi kafin scorpion ya dawo sunyi matukar jinjina masa,a daren ya  kira likitansa tazo tayi masa allura ta rubuta masa magani sannan eku ya taimaka masa ya shiga bayi yayi wanka dan jikinsa Kmr  gyenbo yake jinsa.
kwana daya kawai da yayi a hannun police yaji kamar kwanaki dubu yayi ya kalli jaguwa da idanunshi daya kunbura "police basu da Imani a gobe suke shirin min izaya ta karshe duk da bansan wacce irin izayya zasu min ba a fadar wani police naji tsoro ya kamani ."tausayinsa ya kama jaguwa  muddin ina raye bazaku tagayyara ba kwana sukayi suna hirar irin azabar da akayiwa scorpion.”

washegari Ana's yazo  shima yayi matukar murna da dawowar scorpion "su jaguwa na jin dadin su a gida yayinda headquarter ta hargitse da gulmace gulmace na neman scorpion da akayi aka rasa "akwai wani abu guda daya dana rigada na  yarda dashi yanzu
Commissioner  da mataimakinsa suna da  saka hannu acikin abinda ya  faru "me yasa ka fadi haka ? Inji asp isa .Dcp yace "yaron  dan fashin guda aka kama amman dan an raina mana hankali aka nemi commissioner aka rasa bayan awa shida aka nemi scorpion tare da mataimakin commissioner aka rasa  sannan bayan wasu awanni aka sako commissioner wannan kawai ya tabbatar min dole akwai hadin bakinsu ,kowa fa yanzu su  yake tunhuma ,mu kasa kunne muji ne ig zai ce amman lallai nasan sai an tuhumesu.”

******

Bayan sati daya

Jaguwa na zaune a dakinsa sanye da wondo baki da Riga baki mai hula yana duba wasu takardu masu matukar mahimanci kawai yaga an turo kofar dakinsa an shigo ya dago kanshi  a hankali  ya kalli   Kofar tanwer ya gani tsaye  yana ganin itace ya dauke kansa  ta karaso ta zauna gefensa ya mike zai wuce ta riko hannunsa da sauri "please adnan ka tsaya kaji me ya kawo ni, banza yayi mata ya fixge hannunsa ya cigaba da tafiya ta biyosa tana nasa mgn "wai me yasa kake min haka ne ?
"Bansani ba amman  banason na tsaya dake bare nayi magana dake ,saboda ka tsaneni ko?duk ma yadda kika dauka haka ne kar kuma ki manta nace karki sake zuwa inda nake me ya kawoki yanzu ?
"Na kasa samun kwanciyar hankali ,wallahi ina cikin  wani hali  akan fushin da kake yi dani ,Idan kina cikin wani hali ina ruwana  me zan miki karki sake fad'a min cewar kina cikin wani hali akaina wannnan sakaran zaki fadawa bani ba  .”

Zagayowa tayi ta kwanta a gadon abanyasa ta daura hannuwanta a daidai qirjinsa dake bugawa a tun shigowarta dakin  ,kayi hakuri adnan dina nasan ban kyauta maka ba  tana magana tana shafa qirjinsa ,"
amman kai ma kasan daga ni har kai muke da laifi , da tsayuwar da kayi kana fad'a min mgn a gaban dr da daukata kayi ka tafi dani ka yanke min duk hukunci daya dace bazan damu ba amman a gaban dr ko wasu bazan ji ..."
Riko hannunta yayi tare da fixgota ta dawo  gabansa suna fuskarta juna atare suka sauke numfashi  ta matso shi sosai ta zagaye wuyansa da hannunta daya yayinda dayan hannunta ke fama shafa fuskarsa zuwa faffadan qirjinsa tana kokarin kai bakinta kan nashi ya kawar da fuskarsa gefe ya rike hannuta dake qirjinsa da wanda ke wuyansa  ya soma tafiya daita har ya isa jikin bango ya mannata still kokarin matso shi take ta hade bakinsu domin tasan suna haduwa guri daya shikenan fushin da yake yi daita ya  kare amman yaki yarda .

"wannan bakin yafi karfinki yanzu sai dai wata .” yana gama fadar haka ya sakar mata hannu ya nufi kofar fita tabi bayansa da kallo qirjinta na dokawa da karfi har ya fice daga dakin idanunta na kallon kofa taji kamar tasa kuka ta runtse idanunta tana kokarin danne damuwarta amman sai da kwalla ta zubo mata, a qalla ta dauki sama da minti goma tsaye idanunta a runtse suna tsiyayar hawaye sannan ta budesu suka sauka akan gadonsa inda takardu da yake aiki akansu suke zube  ."
Jikinta a sanyaye ta karasa inda takardun suke zube ta soma dubawa a irin haka ta san alhji tahir ne ya aikosu  gidansu domin fashi wa mahaifinta dukkanin ayyukansa suna rubuce kuma tare da hotunan mutanen da yayi wa aiki a hankali ta soma dubawa cikin haka ya dawo dakin tana ganinsa tayi saurin ture takardun ta mike tsaye yaja tsaki sannan ya nuna mata kofa da babban yatsansa "out !."
Ta mike tsaye ta dauki jakarta ta rataya  tana jan tsaki  “aikin banza kawai dan kaga na damu da kai shine kake wulakantani daga yau bazan sake zuwa inda kake ba kaje ka auri duk wacce kake so bazan damu ba “daidai kenan na kuma ji dadi da kika yankewa kanki shawara me kyau nima kuma na huta da naci .”

“Allah ya saka min cutar da kayi min bazan taba yafe maka ba mayaudari kuma makaryaci kawai , me muguwar zuciya har ta juya tana kuka ya riko hannunta ya dawo daita jikinsa yana kallon fuskarta da hawayen dake tsiyaya a idanunta “ni ne mayaudari tanwe ? Me yasa kika kirani da wannan kalmar ?tayi masa banza tana kokarin zare jikinta ya rike kugunta sosai “me lie tanwer ?kiyi bude baki ki min magana dont think am play with you ,”Who is playing with you too? bai yi mamaki dan yasan zata iya fiyye da haka .”

“You also call me makaryaci karya me nayi miki ? “bansani ba ka sakeni na kama gabanaba ,sai ka qara gani na arayuwarka sannan zaka cigaba da wulakantani “All these you can’t happy if they call you that and you are calling me mayaudari makaryaci why ?dan ban amincewa soyayyarki ba shine na zama makaryaci mayaudari me muguwar zuciya “?tsaki taja ta fixge jikinta ta fita da sauri murmushin gefe baki yayi yana cewa “tanwer kenan bazaki gane ba allah ya tsareki ,kamar wasa gbdy cikin kwanacinki tanwer bata kira shi ba sai kuma yaji ya kasa samu natsuwa a qalla sai da yayi kwana goma bai ga kiranta ba ko kiransa akayi yana allah ya duba ya gani ko itace sai yaga ba ita bace ya shiga damuwa sosai sai dai ya danne ."

********
Sannu a hankali scorpion ya samu sauki ya dawo tamkar yadda yake babu inda baya zuwa Adaidai wannan lokacin suka  samu sakon gayyata daga nabel  saboda suyi aiki dashi  ,nabel jami'in tsaro ne da kasa take alfahari dashi  kuma rikakken dan ta'adan  ne da yan taada ke ji dashi ,shi kansa dila ne na safarar miyagun kwayoyi uniform dinsa ne kawai ke rufe da asirinsa , akarkashinsa akwai jami'an tsoron da suke attare dashi ciki har da shugaba efcc gashi mugu ne na karshe bashi da Imani abu kadan idan kayi masa zai aikaka lahira baya yafiya ."sai byn da jaguwa da Ana's suka zo suka fahimci bikin cikar shekararsa ake yi dan haka suka samu guri suka zauna suna kallon manya masu kudi na garin lagos ,da kusoshin gwanati dake shigowa  sai dai har lokacin nabel bai samu damar shigowa ba ."


tsaye nabel  yake cikin fararen suit yayinda gbdy yaransa ke tsaye cikin suit bakake , wani mutun tsaye a gefensa yana kuka yana bashi hakuri amman ko kallonsa bai yi ba ya kai Karan sigari bakinsa ya kunna ciki muryar kuka wannan mutumin yace "ranka ya dade dan allah ka taimakeni nasan nayi maka alkwarin bazan sake fita da sirrinka ba wannan ma Kuskuren né ka taimakeni ka gafarceni ya fada yana goge hawayensa "duk mutumin da bai yi Kuskuren ba bazai taba yin kuka ba ."
nan take mutumin ya fara dariya "ranka ya dade ai ba kuka nake yi ba  gashi ina dariya " duk mutumin da bai yi Kuskuren ba tô bazai tabayin dariya da wuri haka ba, yana gama fadar haka ya soma tafiya wasu daga cikin yaransa suka biyosa ciki har da mutumin dake kuka ,cikin sauri mutun daya acikinsu ya bude masa kofa mutumin ya biyosa yana kuka " ni yanzu ranka ya dade ka fada min me zan maka ka huce abinda nayi maka lokaci "ni a yanzu babu abinda zan ka iya min nima kuma babu abinda zan maka yayi mgnr yana turesa  da hannunsa "kar ka sake bina rayuwarka tazo karshe ya wucewarsa."

mutun biyu cikin yaran nabel suka rikesa ta karfin tsiya suka danne masa makoshi yana ihu ataimakesa amman ina cikin kankanin lokaci numfashinsa ya bar gangar jikinsa lokacin da nabel ya samu shigowa hadadden hall din dazaa gabatar da birthday dinsa dayawa mutane sun mike tsaye domin girmama da tayashi murna sai dai banda jaguwa anas yayi kokarin mikewa amman jaguwa ya dawo dashi a haka yazo ya wucesu yana dagawa mutane hannu wasu kuma yna mika musu hannu .”
ya zagayo ya sake dawowa inda jaguwa suke tare da babban yaronsa ya tsaya yana gabatar masa da jaguwa "boss wannan shine jaguwa ya mika masa hannu yana murmushi "jaguwa nice name "gaku yara daku wallahi amman kuna yin abubuwan da suka fi karfin shekarunku nabel ya matso da bakinsa daidai kunnen jaguwa "ka tsaya a iya matsayinka sannan ka nemi alhj tajudenni ka bashi hakurin wulakacin da kai da wannnan banzan abokin naka kukayi masa domin har idan kukayi Kuskuren kin bin umarnina ya dauke fauskarsa akan jaguwa zuwa ta Ana's "ina tabbatar maka zan harbeka zan fasa kwakwaluwarka ina fatan kun fahimceni ni ba kamar commissioner bane yana gama fadar haka ya wucesu ran jaguwa ya baci matuka a zahiri ake iya hango tashin hankalinsa tunda yake bai taba samun wanda yayi gaba da gaba haka ya fada masa magana ba sai yau hasalima shi mutane suna shakkar fada masa magana."

bai iya cigaba da zama agurin birthday din ba ya juya shima anas ya biyo bayansa suka shiga mota dukkanisnu agidan baya suka zauna eku ya tayar da mota sai dai babu wanda yayi magana acikinsu wanda hakan shi yafi daga hanakalin anas yaso yace wani abu akan nabel gdy yafishi shiga damuwa sai fesar da numfashi yake jikinsa na wani irin rawa "shiyasa nace bazan zo ba ka takuramin ga irinta nan "bashi da hanyar da zai iya ganawa damu bare ya samu damar fada mana mgn son ranshi sai ta wannan hanyar," kaga a haka ma munfi karfinsa domin kuwa yaji tsoron zuwa inda muke inji cewar jaguwa.

"har ya isa yayi mana kashedi  da barazana "wai me yasa kake yin haka né Ana's ?yanzu kan  d'an wannan abun zaka nemi ka daga hankalinka wallahi wannan karamin abu ne, ya fad'a adaidai  lokacin da suka karaso bakin get din gidan anas jaguwa ya bude kasancewar yana da remut din get din gidan a hannunsa suka shiga anas ya fito koina ajikinsa rawa yake jaguwa ya kamosa ya shigar dashi cikin babban falonsa "karka kuskura  ka sakawa zuciyarka tunani har matarka ta fahimci kana cikin damuwa "ko dai bakaji abinda ya fada mana  bane ?"

"naji  komai mana amman babu abinda zai iya "ina ban yarda ba wannan mutumin zai yi wani abu "byn shi sau daya kawai ya fada karka manta mutane nawa muka sha fadawa hakan kuma bamuyi komai akansu ba "mu muna da wankakkiyar zuciya né amman su

Please Login or Register in order to submit comment