Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yarinya ce sai ka kara hakuri daita sannan kayi kokari ka fada mata cewar kana sonta zaka ga sauyi na ban mamaki "sai na furta ina sonta zata daina kula maza ?yayi masa tambayar a fusace yana fesar da hayaki idanun shi sunyi jawur sun canza kala tsabar tashin hankali da shan sigari dan ya kusan tashi da kwali daya ,"no adnan ba haka nufi ba zata dai ...."kaga ya isa ya isa !! kama hanya ka wuce gida kawai muradin ranka na can tana jiranka ," Ana's bai san sanda dariya ta subuce masa ba ai kuwa ya shiga yi yana kallon jaguwa ,shi kuwa tsaki ya ja ya soma zariya a dakin still yana  bankawa cikinsa hayaki sai da anas yayi dariya mai isarsa sannan ya matso kusa dashi ya amshi sauran sigarin hannunsa ya dauki kwali ya bude ya duba sauran kara daya aciki "me ye haka adnan ?jaguwa ya tsaya tare da juya masa baya "karka sake shan sigari wanda ka sha yanzu ya isa haka, haba zaka kashe kanka ne akan mace just common mace fa ? yarinyar ma dakace baka sonta me yasa zaka damu kanka dan kaganta da wani "?.

Ya juyo a hankalin ya fuskancesa sosai zuciyarsa na karkarwa da zafi kamar ana diga masa wutan dalma, kamar yayi kuka yaji saboda maganarsa sai dai shima yasan haka ba me yuwa bane agurinsa ya bari anas yaga rauninsa akan tanwer ,a hankali ya motsa lip's dinsa ya soma magana cikin sanyi murya "gsky bai kamata na damu ba well daman bawai kishi bane kawai dai naji babu dadi ne ,ganin yadda wancan mutumin yayi kusa kusa daita kamar zai cinyeta amman daga yau inshaallahu bazan sake damuwa ba ko naganta dani .
"very gud abinda ya kamata kayi kenan tunda baka sonta bazaka aureta ka barta ta cigaba da rayuwarta cikin salama da kwanciyar hankali,ka barta ta kula duk wanda take so kuma a sanda taso ,ko cinyeta zasu su cinyeta ina ruwanka tunda kai bata da amfani agurinta?  "ya karasa maganar yana danne dariyarsa jaguwa yayi masa  wani rikitaccen kallo yana maimaita abinda ya fada a kasan ransa babu kalmar data nemi zautar dashi kamar "ko  cinyeta zasu su cinyeta ina ruwanka . ya lunshe rikitattun idanunshi yana jin zafi da ciwon maganar "Ana's me yasa zaka fada min irin wannan maganar "?Wacce magana  na fada maka ?saurin bude idanunshi yayi yana dubansa sakamakon jin abinda ya fada a she a fili yayi manager bai sani ba ,murmushi ne sosai akan fuskar anas dan shi abun nasa dariya yake bashi amman kuma babu halin yinta ."

jaguwa ya tsura masa ido kawai yana kallonsa tare da nazarinsa a hankali ya kai hannu yana shafa fuskar anas yana cigaba da kallon fuskarsa da yake kallon alamun dariya a tattare daita muryarsa a kasalance yace "Ana's dariya ko ? yay saurin girgiza masa kai alamun a'a "no karka ce min haka mana dariyar ne a fuskarka "dole yasa dariya ta bayyana a fuskar anas,jaguwa ya juya zai bar gurin yayi saurin riko hannunsa ya fixge hannunsa a fusace yana cewa "dole kayi min dariya tunda ga mahaukaci a gabanka ka samu ,please ka saurareni ba dariya bane ,bazan iya sauraron ka ba, zo dai ka wuce gida na sallameka wata dariya ta subucewa Ana's yana cewa "maganar tsara aiki fa ?an yafe maka kuma an sallameka bye ya fada yana zubewa akan gado ya kwanta flat yana fitar da numfashi sama sama ya runtse idanunshi sosai yana ciwo mai tsanani aransa anas bai yi magana dan yasan taurin kansa ba saurararsa zai yi ba dan haka ya dauki faranti zuba tukar sigari da kwalin ya fita zuwa falonsa ya ajiye karamin faranti ya fice da kwalin sai dai bai bar gidan gbdy ba ya samu guri ya zauna a falo cikinsu anas basu nuna masa komai ba aka cigaba da hira dashi ."


Bangaren tanwer kuwa da Kuka ta karaso gida ta bude murfin ta fito daga cikin mota bata tsaya rufewa ba ta shigo babban falon gidansu ta zauna a hannun kujera tana kuka kamar wata karamar yarinya kuka take sosai har mumy da masu aiki suka fito lokacin ita ruky tana daki tana sallah ganinta yasa masu aiki suka juya suka koma kitchen mum ta isa inda take tare da dafa kanta "me ya faru tanwer ? kuka ta cigaba batare data bata amsa ba "tanwer taso mu shiga ciki ki fada min me ya faru dake kike kuka haka ? hannunta mumy ta riko suka shiga dakinta ta zaunar daita a bakin gadonta a lokacin kukan nata ya fara tsayawa "me ya sameki haka kike wannan uban kuka ? duk yadda mumy tayi daita ta fada mata dalilin kukan taki ta fada mata duk da mumy ta fara zargin ita da adnan ne domin idan bashi bane babu abinda zai sa diyarta kuka irin haka "adnan ne ko !?.

Tayi shiru har sai da mumy ta sake maimata tambayarta sannan ta gyada mata kai tayi shiru tana nazarinta sannan ta numfasa ta soma rarrashinta tare da mata nasiha akan rayuwar duniya"kiyi hakuri tanwer rayuwar nan sai mutun ya jajirce mata ya koyi hakuri da juriya hade da dakiya akan duk wani abinda zai samesa karki manta komai qaddara ne rabonka bazai taba wuceka ba ,wallahi duk abinda kika ga bai zo hannunki ba to barabonki bane amman muddin rabonki ne kina zaune zai zo ya sameki , sai abu na gaba banason nasan abinda ya hadaku amman idan kin san kece mai laifi kiyi kokari kikirasa ki bashi hakuri amman idan kin san shine mai laifi ki rabu dashi idan ya huce zai nemiki idan yana sonki "tabbas nasihar mumynta ya shigeta sosai nan take ta yankewa zuciyarta zata jajurcewa rayuwa zata koyi hakuri zata koyi yadda zata danne damuwarta akan adnan sannan bazata sake furta masa tana son shi gara ta fadawa wani akansa
Tayi shiru tana tunanin abinda ya faru yau laifin waye acikin ita dashi .."?tayiwa kanta tmbyr tana kallon mumy dake zaune a gabanta kamar zata mata numfashi ."

"Ki kwanta ki dan huta ko zaki ci abinci ne akawo miki ?bana jin yunwa mumy ta fada a shagwabe,ban yarda ba dan nasan tun breakfast ne acikinki baki  ci komai ba ko ba haka?haka ne mumy amman a koshe nake ,saboda kun samu matsala da adnan ba ?mumy tayi maganr tana shafa fuskarta "no mumy ba haka bane kawai cikina ne a cushe ,yana daga cikin dabiyarki yanzu idan kin samu problem da adnan sai kiki cin abinci kefa likita ce kinfini sanin illarsa ,bari naje na kawo miki ko kadan ne kici kinji mamana ta gyada mata mai kawai ba dan tana jin yunwa ba sai dan kawai ta kwantar mata da hankali.
mumy ta mike tsaye tana sakar mata murmushi ta fice daga dakin bata jima da fita ba ta dawo hannunta rike da tire tanwe ta mike da sauri ta amsa tiren a hannunta "sannu mumy that's why I love more than anything ina sonki mamana ta fad'a tana ajiye tire "nima ina sonki kici abinci ina zuwa ta sake juyawa ta fita tanwer tayi shiru ta kasa bude abincin bare tayi tunanin ci gbdy  abinda ya faru tsakaninta da adnan    ya tsaya mata arai ta rasa waye mai laifi acikinsu dole ba dan tana so ba tabawa kanta laifi ,nice mai laifi tunda na kirasa sister dinsa da Aunty’s dinsa da useless alhalin shi misali ya bani
ta fada hawaye na zubo mata akan kuncinta ,kenan nice ya kamata na kira na bashi hakuri ?ta aikawa wankakkiyar kwakwaluwarta tambayar .”

Jiki a sanyaye ta yunkura ta mike ta tashi tsaye tana goge hawayen dake tsiyaya daga cikin kwarnin idanunta ,ta dauki tiren abincin da mumy ta kawo mata ta fito zuwa parlour inda ta iske ruky zaune tana buga game a wayarta tana ganinta ta bar abinda take ta fuskanceta tana cewa “amaryar a gidan adnan yaushe kika dawo ?tanwer ta sakar mata murmushin yake tana boye damuwarta sannan tace “ban wani jima da dawowa ba akwai labari ne ?
“Sosai kuwa idan kin huta kizo kiji , amman dai yau kin dawo da wuri ,eh babu wani aiki dayawa ne ta bata amsa tana shigewa kitchen ,ruky tabi bayanta da kallo aranta tace “ko me ya sameta duk tayi wani iri da alamun ma kamar kuka tayi ?allah dai ka iya mana abinda bazamu iya ba, allah karka barmu da zabinmu ka zabamana abinda yafi alkhairi a rayuwarmu, tanwer ta ajiye tiren ta fito ta dauki handbag dinta ta koma dakinta .”


ta zauna a tsakiyar gadonta ta fito da wayarta tana kallo tana jin mummunar faduwar gaba dake tattare da tsinkewar zuciya mai tsanani wankakkiyar zuciyarta ce ke bata shawarar ta kirasa ta bashi hakuri yayinda wata zuciyar ke kwabarta tana tuna mata gargadinsa gareta “my advice to you stop call me or chart me again ,and I don't won't to see your face again in my life ,stay a way from me tanwer idan kuma kikayi taurin kai da gangancin zuwa inda nake ko kiran layina wallahi sai nayi kwallo dake na fasa kanki da harsashi nan take idanunta suka ciko da ruwan hawaye jikinta ya dauki zafi ta koma ta jingina bayanta da abun gado hawaye na bin gefen idanunta “me zanyi yanzu ? tayiwa kanta tmby zuciyarta na rawa sosai ta shiga tunanin yadda zata yi “me zai hana ki kira anas tunda kina da numbersa gyara zamanta tayi sosai ta soma neman layinsa kira daya ya dauka yana kiran sunanta .”

“Tanwer !
“Na’am anas ina yini ?
“Lafiya tanwer ya aiki da fama da jama’a ?alhamdulillah ta bashi amsa muryata a sanyaye ,
shiru ne ya biyo baya na kusan second biyar tana son tmbyrsa jaguwa tana jin tsoron ko yana kusa dashi tajawa kanta bala’i dashi karon kanshi jin tayi shiru yace “yaakayi tanwer ?,adnan fa ? tayi mgnr muryarta na rawa “yana dakinsa jin haka yasa ta sauke wani wahalallen numfashi da ajiyar zuciya atare ,me yake yi anas ?gskya ban sani ba ya dai kwanata yanzu ma nake son na koma dakin na tashesa dan bai yi sallah ba .”
“Okay daman na kira ne dan allah ka bashi hakuri akan abinda nayi masa nasan ya fad’a maka komai daya faru ,yayi hakuri kuskure ne bazan sake ba amman shima ka fad’a masa komai zai min bana son yayi min a gaban kowa gara yayi min daga ni sai shi ko kasheni zai yi yayi na yarda bazai dameni ba amman a bayyana nasi banaso Ana’s ta karasa maganar tana fashe masa da kuka .”

Naunayen ajiyar zuciya ya sauke “karki damu tanwer inshaallahu zan fada masa sakonki , kema ki cigaba da hakuri da wannan rigimammen abokin nawa abinda kuma yayi kishi ne ba komai ba “wallahi zan iya rike alqurani nayi rantsuwa dashi babu komai acikin raina akan dr muyis ,ba tun yau ba munyi maganar dashi dr muyis a abokin aikina na daukesa shi dai yana sona amman ni sam sam babu soyayyarsa acikin zuciyata adnan kawai zuciyata ke só amman yadda yazo yayi min agaban dr muyis ya bani haushi shiyasa nayi masa abinda nayi amman dan allah ka bashi hakuri bana son nayi abinda zan bata masa rai ,adnan yasan yadda nake sonshi wallahi da wani abu ma idan ance yayi min bazai ba i love him so much please let him try to understand naso nazo a yanzu amman yayi min gargadi kuma na tsorata da gargadinsa ta karasa maganar tana sheshekan kuka tanwer don’t cry please and kiyi zamanki zan fada masa sakonki idan ya huce zan kiraki a waya na fada miki yadda mukayi dashi sai ki kirasa kuyi magana “.

tayi shiru tana tsaida kukanta can tace “Ana’s kana ganin kuwa adnan nasona kuma zai aureni?gsky ni dai a tawa fahimtar yana sonki kuma yana da muradin aurenki amman dole sai kinyi hakuri da adnan tanwer amman dan so adnan na sonki zuciyarsa ce ke yaudararsa amman jikina yana bani lokacin yayi da zaki mallaki zuciyarsa gbdy abinda yayi ma dazu cikin so ne tanwer idan bai sonki bazai yi kishinki ba ke dai ki kara hakuri ki kuma yi addua abinda yafi zama alkhairi a tsakaninki dashi allah ya tabbatar mana sannan ki daina kula wannan dr din
Sun dan jima suna waya yana fada mata adnan na sonta murmushi jin dadi ne ya bayyana akan fuskarta take taji kashi saba’in acikin damuwarta ta kau a karshe sukayi sallama ,”


*******


A hankali bacci ya dauke jaguwa daga kwanciyar da yayi duk da bacci yake amman hakan bai hana zuciyarsa suya ba har kusan karfe uku bai fito ba anas ya mike ya koma dakin ya dubosa stil bacci yake ya karasa inda akwatin kudi yake ya bude ya dauki daidai wanda zai bukata ya fita ya aiki sky yayi musu order abinci ya sake komawa dakin ya zauna ya kira layin hally kira biyu yayi mata sannan ta dauka muryata cike da mayen bacci ta gaishesa ya amsa yana cewa “my princess me kike ne ?tayi narai narai da idanunta tana sauke masa numfashinta akunnensa ya sauke numfashi “bacci kikeyi ne ?
Tace “eh! Okay tashi kije kiyi wanka kici abinci idan kin gama ki min flash ya katse kiran a lokacin da itama ta mike ta shiga bathroom.”


Karfe biyar daidai jaguwa ya farka daga baccinsa ya sauko daga kan gado yana mika sannan ya janyo towel ya shiga bayi wanka yayi hade da dauro alwala ya fito yana goge jikinsa da karamin towel yana tsaye ana’s ya shigo fushi ne sosai cike da zuciyarsa da fuskarshi ganin zai saka kaya yasa ya fice ya bashi guri ya koma parlors bai jima da zama ba sky ya dawo yayi knowking ya bashi umarnin shigowa izinin shigowa anas ya bashi , sky ya shigo cikin parlour hannunsa rike da ledodi cike da girmamawa ya rusuna yana kokarin ajiye ledodi .
Anas ya yunkura anas yayi yana duba ledodin “ya baka ajiyewa su kamil nasu ba ko sun fita ne ?no suna anan falo ,okay ka dauki nasu ka wuce dashi sky cike da girmamawa ya dauki leda uku ya fita shi kuma ya dauki nasu ledodi Ya nufi bedroom din jaguwa kallo daya yayi masa ya dauke kansa yana taje sumar kanshi da cum a zuciyarsa yana mai jin haushi tanwer yana gamawa ya nufi hanyar fita anas ya biyosa yana kiran sunansa “adnan ga abinci fa ,bana ci ya fada a takaice yana cigaba da tafiya
bai tsaya akoina ba sai falonsa “haba muradin tanwer karmuyi haka da kai please jaguwa ya zauna akan kujera ya a wurga masa harara “allah ya tsareni da wannan useless girl din “uhmmm banaso karka sake kiranta da useless dan baita bace idan ita useless ce kai fa me zaa kiraka dashi ?tsayawa yayi yana kallonsa a hankali ya sauke numfashi anas
ya bude ledar abinci ya fito da takeaway ya tura masa abinci gabansa “kaci abinci !”.

ya lumshe rikitattun idanuntmsa saboda yunwa da fushi,amman bai tunanin bacin ran da yake ciki zai barshi yaci wani abinci “dan girman anas ka dauke abincin nan a gabana abinda nafi bukata daga gareta yanzu shine dariya shi kawai nake son gani a kwance a fuskarka domin na tabbatar da na haukace gbdy “Kayi hakuri dan girman allah da darajan iyayenka ka sanyawa zuciyarka natsuwa kaci wani abu yayi maganr in a serious way “idan baka ci abincin nan ba wallahi yau babu inda zani anan zan kwana na bar hally ita kadai ya karasa maganar Kmr zaiyi kuka .”
Jin abinda yace kuma yasan zai aikata akansa dan haka ahankali ya soma dibar abincin yana kaiwa bakinsa,sai idan duk lomar da zai yi sai tanwer ta fado masa a rai hade da bugun zuciya sai kuma ya dade bai sake kai abinci bakinsa ba daman kuma haka yanayin cin abinsa yake baya sauri “.
shiru anas yayi yana kallonsa har sanda ya ajiye spoon ya mika masa ruwa ya kallesa “amman kai bakaci abincin ba mo me yasa?zanci nafi son naga kasamu natsuwa “yadda anas ya takuresa yaci haka shima yasashi yaci anas yaso yayi masa maganar tanwer amman dai yayi tunanin ya bari zuwa gobe ko anjima anas na gamawa suka mike atare jaguwa ya karasa ya kwashi wayoyinsa suka fito ya na gaba anas biye dashi har zuwa falo inda su jubi suke .”

Ya tsaya ya jingina jikinsa da bangon falon yanayin tsayuwarsa ya fahimtar dasu jubi magana zai yi mai mahimanci dan hk suka tsura masa idanunsu tattare da hankalinsu suna jira daga garesa wanda adaidai wannan lokacin tuni anas ya fita kiran sauran yaran kusan atare suka shigo falon jaguwa ya kallesu daya byn daya sannan ya fara magana a tsanake “aiki né kamar koda yaushe ga sambo sama’ila ,sai dai bazamu samu damar zuwa ba zan tura ka scorpion jibi yayi mgnr yana dubansa sannan yayi taku uku ya karasa inda system dinsa yake ya zauna tare da kunnawa “zan tura maka address din inda zaka samesa acikin apapa oil and gas alhj madu gwani
shi kadai ne acikin apapa bashi da na biyunsa mutumin maiduguri ne baki ne dogo mai jiki zan tura maka hotonsa da komai nashi tru what’s app dinka kayi aiki da baseera ,akwai hanyoyi masu sauki da zaka fita koda wata matsala zata faru bama fata yana masa bayani yana kallon system dinsa yana operating tunanin tanwer na zuwan masa.”

shiru yayi yana kokari ture tunaninta daga zuciyarsa amman ya kasa daga karshe dai ya tabbatarwa da kansa bazai iya raba zuciyarsa da tunaninta ba ya janyo system a gabansa ya cigaba da aikin tunaninta hakan ya fahimtar dasu ya gama bayaninsa daya byn daya suka kama gabansu ,”anas ya matso kusa dashi yana mika masa hannu “zan wuce gida dan allah ka kara hakuri adnan rayuwar nan ma guda nawa take ?ina son zuciyarka ta koyi yadda ake yafiya da sauri .
ko gezau bai yi ba bare ya dago ya kallesa ko ya mika masa hannu Kmr yadda ya mika masa “ka yafe min idan na bata maka rai banason kana fushi dani dan sai naji duniyar duk ta Isheni wannan maganar tasa yasa jaguwa ya dan sauko da idanunshi ya dubesa yana dan sakar masa fuska ,dan allah ka saki fuskar nan taka “shikenan nayi “yayi mgn yana murmushin gefen baki “to ko kai fa wallahi har raina yayi sanyi gobe zan kai hally gurin ammi wata killa bazan samu shigowa da wuri ba ya gyada masa kai kawai alamun yaji suka yi sallama ya kama hanyar zuwa gida .”

Yau ma kamar jiya a bakin kofar shigowa falon ya tsaya yana sallama ta leko daga kitchen tana yi masa sannu da zuwa ,ya amsa yana cigaba da tsayuwa agurin yana kallonta cikin doguwar riga ya kashe masa idonsa daya “me kike jira da bazaki karaso ki tarbi mijinki ba tunda Kinsan abinda tsayuwatsa take nufi ?”kai ya anas!
“Kai ya Ana’s ko gskiya ina jira ta koma cikin kitchen din ta wanke hannunta ta fito ta tsaya a gabansa cike da shagwaba ya dage mata girarsa daya ya janyota kusa dashi sosai ta fada jikinsa ya rungumeta tsam ajikinsa yana sakin numfashi sai daya gama jin dumin jikinta sannan ya sausauta rikon da yayi mata ya hade bakinsu guri daya ya shiga tsotsa “bayan runguma har da wannan nake bukata okay.

Ta zare jikinta taja shi zuwa ciki sosai ta zaunar dashi akan kujera tana shafa fuskarsa “ina ka tsaya yau ka dade ,ina tare da adnan tun fita ta bari na kawo maka ruwa ka sha da alamun akwai gajiya atare da kai ta mike ta shiga kitchen ta dauko ruwan gora mai sanyi da cup ta fito ta tsiyaya ta mika masa ya amsa hade da hannunta yana dubanta itama shi take kallo ya zaunar daita a cinyarsa ya kai cup bakinsa ya sha kadan ya mika mata ta ajiye cup din akan table “ki shirya gobe zan kaiki kiga ammi ,da gaske ta fada tana zubewa jikknsa gskiya naji dadi sosai amman kwana zanyi ko ?ya riko hannunta cikin nasa yana kallonta “kwana my princess?ta gyda masa kai “idan kika kwana ni kuma na kwana dawa?ta marairaice masa fuska ,kiyi hakuri kije kiyi ma ammi yini na rigada na saba kwana ajikinki amman idan ki yarda kawai sai mu kwana tare tayi saurin zaro ido waje ,yes dan gsky bazan iya kwana ni kadai yanzu ba “.

“Shikenan naji amman sai dare zakazo ka daukeni ?ya dage mata gira ,muje kayi wanka kaci abinci ,
Wanka dai amman abincin nan no space kamar jiya suna tsaka da hirar soyayyarsu aka kira sallah ya fita zuwa masallaci a daren ma kwanan farinciki sukayi rungume da juna sabanin tanwer da adnan .
washegari da safe ta tashi ta hada musu break suka ci suka fice ya bude mata gaban mota ta shiga ta zauna ta rufe ya zagaya ya shiga ya kunna motar suka bar gida bini bini zai jiyo ya kalleta sai murna take zata gida ,ya lalubo tafin hannunta cikin nashi yana murzawa yana janta da hira da tsokana har suka karaso unguwarsu yayi parking adaidai kofar get din gidansu zata bude bangarenta yayi saurin cewa “no my princess bari karki wahalar da kanki ya fita da sauri ya bude mata a hankali ta fito ya kulle motar suka jera suka shiga gidan ,”

A haraban gidan anas yaja ya tsaya ta shiga falon bakinta dauke da sallama ammi na zaune bisa kafet ita da haseera suna breakfast ammi ta dago ta kalleta ta kuma kalli bayanta “ina bin malik din yake ?ta karaso ta tsugunna a gabanta tana gaisheta ammi bata damu da ansa gaisuwar ba ta sake tmbyr anas “yana waje ammi ta bata rai “dan sakarci irin naki me yasa zaki bar min yaro a waje maza ki tashi kice ya shigo cike da mamakin irin wannan qaunar da ammi take masa ta mike tana riko hannun haseera “aunty hasera ya kwana biyu ?Lafiya lau auta duk kin wani canza kinyi kyau Kmr wata india tayi murmushi ta nufi kofar fita ta tsaya a gabansa “muje ko dan kasa mamanka tana min fada tai mgn tana zumboro masa baki yayi murmushi ta juya yana biye daita .”

Cike da ladabi da biyaya ya shigo bakinsa dauke da sallama ammi ta amsa tana fadada fuskarta da murmushi dan shima yayi kyau kamar yadda diyarta tayi hally ta dauko dadduma ta shimfida masa ya zauna kusa da ammi “anas ya aiki da hakuri da auta ? Alhamdullahi ammi babu abinda zance sai Godiya hasera na kallonsa amman bata ce masa uffan ba abun ya dan tsotsa ran hally shi dake mai saukin kai ne yace “hasera ina yini fuska a hade ta amsa da “Lfy! atakaice dan gani take har dashi acikin masu zuga adnan kar ya aureta hasera ta maida hankalinta gurin hally “hally uwar kyau wannan ai kinfi karfin akiraki mai kyau sai dai uwar kyau hally tayi mata banza “kinga kuwa yadda kika kara kyau kika murje?da kyar tace “na gode mumy kuwa abincin gabanta ta turawa Ana’s tana bashi umarnin yaci babu mutsu ya fara ci hally tasan ya koshi amman bazai iya mutsu daita ba ta tsura musu ido kawai tana jin dadin yadda ammi take qaunarsa byn ya danci kadan suka koma kan kujera suna hira ita ammi da anas da ita kanta hasera sunyi hira sosai cikin haka anas yayi wa ammi sallama ya

Please Login or Register in order to submit comment