Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a duk sanda suke tare.. ..

"Ni ka yiwa gargadi  sai gashi  kai ne ka aikata hakan, jin haka yasa Jaguwa   mikewa ya sauko  yana gyara zaman gajeren wandonsa  dinsa daya dan zamo  daga kugunsa ya nufi kofar fita "bai dace ba gaskiya ,abinda mukeyi ne fa  kana  mana faɗa   me yasa zaka yi  ...?saurin dakatar dashi yayi   "ni din ma ba da wata manufa na d'aukota ba ,na d'aukota ne da niyyar  azabtar daita, na gana mata  azaba na nuna mata kuskurenta akan  abinda ta min sai....
Yayi shiru ya kasa karasa maganar  "sai kuma ka bige da  .......

dakata dan Allah malam ni babu abinda nayi daita "to me amfanin rike musu yarinya da kayi  ?  "Ka ....
kit ya katse kiran yana dafe goshinsa tare da rike kugunsa da daya hannunsa  wani kiran ne ya shigo ya sake katsewa ya kashe wayar gaba-daya ya koma d'akin  yana Kallonta idanunta a lumshe alamun tana  jin bacci rabawa yayi jikinta ya kwanta  tare da  matseta   ganin haka yasanya shi gaggawar birkitota suka fuskanci juna  eye's dinsu suka haɗu zuciyarsu yayi mummunar bugawa a tare laulausan tafin  hannunsa  taji yana yawo ajikinta  tun tana jin abinda yake  har bacci yayi nasarar  d'aukarta amman stil tana jinsa  , gabad'aya ya gigice irin gigicewar da bai taba yi akan kowace mace  ba, duk tunaninsa ya kau burinsa kawai ya samu biyan bukata sai dai  bazai iya  aikata komai daita ba.......

sama da awa biyu ya ɗauka yana romacing din  jikinta daren da yake jin  kasancewarsa  na  musamman  gareshi dan kuwa ji yake tamkar yana tare da matarsa ce  ina ma  zai iya daya yaki zuciyarsa ya  aureta kamar yadda ta bukata dan  yasan zai samu dukkanin wani kulawa daga gareta ,zata shayar dashi soyayya  ,a hankali  har ya samu natsuwa ya kwantar daita a saman faffadan kirjinsa yana sauke numfashi   ...
hannunsa ya daura saman gashinta  yana shafawa  zuwa gadon bayanta haɗe da  kissing foring head d'inta  "acikin zuciyar tanweer kuwa addu'a take da Allah ya tsaida shi iya haka batare da ya kusanceta ba , Allah kasa wannan bawa naka ya aureni  dan zan sha  soyayya shi din na daban ne i love you adnan ta furta haka acikin ranta , rufe musu jiki yayi yana sake lumshe kyawawan idanunshi har bacci yayi nasarar daukarsa.....

*****
A hankali ya bude  kyawawan idanunshi ya  daura akan  ƙaramin agogon dake ajiye akan abun gado,  karfe  takwas ya gani har  ta wuce da wasu yan mintuna tsaki yaja saboda ya makara idan akwai abinda ya tsana bai wuce makara gurin sallah ba , ya  kwantar daita tare da lullu'beta da bargo ya mirgina ya sauko  ya janyo towel ya d'aura ajikinsa cike da natsuwa ya  shiga   bathorrom , bathtube ya shiga ya tsaya ya soma sakarwa jikinsa ruwa, wankar tsarki yayi tukuna  domin tsaftace jikinsa sannan yayi wanka soso da sabulu bai dade ba   ya fito yana goge jikinsa yana kallon fuskarta da gashin kanta mai tsantse da sheki komai nata mai kyau  ya furta hakan a kasan ranshi ..

Jallabiya ya ciro wani design din yasa ya  karasa kibabben gurin sallarsa ya soma gabatar da sallah gabansa na faduwa , yana matukar fargaba da tsoron mahalincisa a duk sanda zai yi sallah sai yaji gaba-daya komai ya kwance masa ,yasan abinda yake aikatawa bai da kyau har yana jin tamkar ibadar da yake ma ba'a amsa ,yayinda take zuciyarsa ta kawar masa da wasi wasin data shiga ya dinga yi mata naci da karfafa gwiwar da   ana amsa har ya idar zuciyarsa rawa take ya  mike ya dawo inda take kwance tana sauke numfashi hannuwansa duka ya kai jikinta ya d'agota ta zube jikinsa ta lafe tare da turo masa karamin bakinta gaba , bakinsa ya kai cikin kunneta "ki tashi kiyi sallah lokaci ya tafi  mika tayi ajikinsa wanda ya haddasa masa jin wani irin shock , "uhm zanyi  zuwa anjima bacci nake ji jikina duk ciwo yake min ,gefen kunneta ya  ciza da dan karfi ta saki qara tana sake  shigewa jikinsa "dole ki tashi kiyi sallah me kika yi da kika gaji  ya k'arasa maganar yana busa mata iskan bakinsa take tsigar jikinta suka mike sake turo masa  bakinta  tayi tana kokarin buɗe bakinta taji yayi sama daita ya shige bathorrom daita ya sakata  a bathtube "ba'a lattin sallah a gidana oya kiyi alwala ya juya ya koma d'aki bayan kamar minti uku ya dawo hannunsa rike da jallabiya ya ajiye mata ya sake fita ..

Jiki a mace ta fito tana kallon inda yake zaune rigingine da gado ta isa inda taga dadduma ta tada sallah bayan ta idar    ta koma dayan bangaren da yake ta zauna "good morning ?"morning ya faɗa atakaice batare daya kalleta ba "ya kamata na koma gida ina so..
"zaki tafi nan da wasu awani dan zamanki bashi da  wani amfani , ya fada yana mik'ewa akan  katifa    bata sake cewa komai ba  ta zame ta kwanta tana runtse idanunta "komai cikin gadara da isa da nuna rashin kulawa ta fadi haka a kasan ranta .......

ya mike ya fita daga dakin zuwa  wani dakin , yayi shirin fita operation dinsa tsaf ya shirya cikin bakaken kaya  riga da wonda na suit  ya ɗauki bindigarsa pistor guda  har guda biyu ya soke ajikinsa yabi jikinsa da turare mai sanyi  kamshi  sannan ya  fito zuwa babban  parlou'n gidan  yana d'aura agogo a tsintsiyar hannunsa turus yayi ganin jabir kamil jubi da Anas zaune suna   tautaunawa akansa  ganinsa yasa  suka mike  suna kallonsa , kallonsu shima  yayi daya bayan daya yana tabe baki  sannan yace "ku kuma fa ? "a tare  suka bude baki mun zo ne akan wannan fitartaka  bama son ka fita aikin nan dan Allah ka hakura  ,"me yasa bakwa gajiya da magana ɗaya nifa wannan ba sabon abu bane agurina,",Koda yaushe kana jayayya damu akan ra'ayinka  amman  akan  wannan   dole  mu fi karfin ka "karfin wa ? ya furta   yana musu wani irin  kallon kasan ido
"Duk ma abinda zakuce kuce but I must   face tanko gote zasu sake magana ya dakatarsu har zai  fita yaji jikinsa yayi masa  wani iri a hankali ya juya ya koma ciki ,kai tsaye d'akin  da tanweer take ya shiga ya hawo har saman  gado  ya shige jikinta yana kissing din bayan wuyanta jinta yake kamar matarsa ya zira harshensa cikin kunneta sannan ya kamo hannunta cikin  nashi "zani wani aiki mai mahimmanci da zarar na dawo zan kai ki gidanku  ajiyar zuciya ta sauke tana juyo ta zuba masa ido batare da tace komai ba shima bai sake furta komai ba wani iri suka ji ajikinsu a lokacin da kwayar idanunsu suka tsarke cikin juna ,bai sake cewa  komai ba ya fice tabi bayansa da kallo kamar ta hanashi fitar duk da batasan inda zashi ba , har lokacin su Anas   suna  tsaye ya nufi haraban gidan suka biyo bayansa   suna masa magana amman ko tari bai yi bare su saka rai zai amsa musu   , kai tsaye dakin ajiye makamansa ya nufa ya dibi harsashi da kudi masu yawa ya ɗauki keyn motarsa city ya  fito still suna biye dashi ya karasa inda aka tanada domin ajiye motocinsa  ya danna key din hannunsa ya bude  kofa mazaunin direba  ya shiga ya tayar mai gadi na ganin hancin motarsa ya bude masa, ya cilla motarsa waje  .

mutanen dake tsaye jiran fitowarsa suka mike tsaye ,kamar ba zai tsaya ba sai kuma ya tsaya   batare daya kashe motar ba ,yayi warning glass din motar ya  ciro bandir din kudi yan dubu day day ya soma  raba musu kamar yadda ya saba suka dinga  amsa suna zuba masa ruwan addu'a da samun nasara  yana kada kai ,sai  daya sallamesu sannan ya dauki hanyar zuwa donping estate   ..

     "Taurin kai taurin kai mutun kamar mutanen farko duk abinda kaji ance ka barshi barinsa shine alkhairi duk kuma abinda zaka samu a duniya zaka bar shi jubi ya faɗa cike da taikaici da bakinciki taurin kan Jaguwa "wayyohlly Allah wallahi har na fara tausayawa yan'uwansa da halin da zasu shiga idan wani abu ya faru dashi  kamil ya fada yana marairaice fuska , jabir yace " wallahi tunda ya soma shirin aikin nan naji ajikina babu nasara  "muyi masa addu'a kawai Allah ya dawo dashi lafiya domin shine karfin gwiwarmu bamu taba samun saɓanin ra'ayi ba sai a wannan lokacin inji cewar anas daya fi kowa shiga damuwa " ameen suka had'a baki gurin fadar haka..

A hankali yake murza stearing  yana tunanin yadda abubuwan zasu kasance gaba-daya ya gama tsara komai da yadda zai shiga ya fito har ya dauki  titin da zai kai shi  estate din  ya  karaso bakin get din estate din yayi parking ya ɗan dade sannan ya fito     daga cikin motarsa yana gyara zaman suit d'insa kai tsaye gurin securitys din bakin get ya nufa suka gaisa a mutunce bazakace masa dan fashi ba bayan sun gaisa yace "ina son ganin Alhaji tanko gote  ..
Daya daga cikin securitys ya leko daga cikin wani karamin daki yana dubansa ganinsa cikin shiga ta kamala ya koma ya zauna dayan yace "me ye sunanka na duba ko kana cikin list din masu son ganinsa ? Shiru yayi ya kasa magana yana ciza lip's d'insa na kasa security ya sake kallonsa yana  tambayarsa "uhm don't worry bari na kirasa "better dan ba'a bawa Kowa damar shiga sai da izininsa  wayarsa ya ciro kamar zai yi kira ya koma cikin motarsa ya zauna yana tunanin yadda zai shiga cikin sauki .

"  Anas........"
jabir  ya kira sunansa yana zama a gefensa "na'am jabir Anas ya amsa jiki a sanyaye"  everything will be fine naga duk ka damu tunda jaguwa ya bar gidan nan  "dole na damu jabir ina jinsa tamkar danuwana bana son wani abu ya sameshi bana son na rasashi yayi mgnr kamar zai zubar da kwalla "jaguwa ba kamar sauran mutane bane , gabad'aya alamuransa akwai lisssfi  ,yana da kaifin kwakwaluwa bazai bari mu rasa shi ba saboda yasan muna son shi "jabir nasan da haka nasan yana son mu duk duniya bashi da aminan da suka kai mu but bansan me yasa yayi irin wannan taurin kan ba ,nayi kokari fahimtar dashi nayi komai akan ya bar wannan aikin amman yaki ya kasa fahimtata jabir zuciyata na cike da tsoro yanzu idan wani abu ya sameshi  adalilin tango gote ya zanyi da rayuwata ? "Anas kana tsoro da tausayinsa with  reason nima zuciyata tana cikin damuwa amman abinda na lura dashi  yana sane so yake mu rasa shi inji cewar kamil wallahi idan wani abu ya sameshi bazan taba yafe masa ba yayi maganar yana goge hawaye "ba haka bane kamil  Anas ya fada shima hawaye ne cike da idanunshi "zai dawo   zai dawo anas ya dinga maimaitawa zai dawo da kafafunsa domin shi din ba mutun bane kamar sauran mutane mutun ne mai matukar amfani ga rayuwar mutane yayi handling din matsaloli a rayuwar data gabata ina da tabbacin zai dawo da kafafunsa suka rungume juna suna kuka ..

****
Alhaji tanko gote  zaune a cikin  tangamemen parlou'n sa daya ji kayan more rayuwar duniya tare da manya abokansa kowane hannunsa rike da glass cup  suna kurban ruwan  win yayinda gabansu table ne dake dauke da kayan itatuwa kala dabam dabam,tun daga kan ginin gidan da tsarin da'aka bi dashi za ka san mamalakin gidan attajirin ne,gidan  zagaye  yaje da flowers sannan  yafi Kowane gida dake cikin estate din kyau da tsaruwa  .

shewa ne ke tashi acikin parlou'n "mutunen  da zasu ce meye namu acikin lamuran   kasar nan ina tunanin mutanen sun tabbata    dakikai ne , domin daga kasar nan tamu har  zuwa kashen ketari sunanmu ya zagaya sannan a san da zamanmu,   maga Wanda ya isa yace meye namu acikin lamarin kasar nan bayan mune gwanati  "wannan haka ne inji cewar Alhaji amadu dan iya wanda ke fuskantar alhj tanko gote   "muna da tarin kudi muna da tarin mutane muna da hanyoyi daban daban akwai connection me muke so  acikin kasar nan da bamu samu ba  da har wasu zasu dinga cewa meye namu aciki ?  "babu ma wanda ya isa domin mune gwanati kuma ko ana so ko ba'a so dole a dama damu  kuma muyi abinda muke so  "wannan gaskiya  ne ...

"waɗan kananun maganganun yasa  nake gudun shiga siyasa Gara na tsaya iya haka tunda duk abinda nake nema ina samu sannan ina juya waɗan da nake so  na bada umarni kuma abi inji cewar Alh Tanko gote   suna cikin hirar wayar Alhaji tanko gote ya ɗauki kara ya mike sanye da bakin kaya wando da riga da hula ya ɗauki glass cup  ya dauki  wayarsa ya miko dogon coridor din gidansa  sannan  ya ɗauki wayar  ya soma magana kasa kasa   "ranka ya dade  aka fada  daga dayan bangaren na turo  da kudaden  yanzu haka yarona na bakin get din  estste " oooooo my  god me yasa baka da fahimta ni da nace a wuce akai kudi banki shine zaka turo min yaro madadin ma ka kirani na turo body guad "am sorry  sir gani nayi idan na turo kudin zaka fi maida hankali   "haka ne   kana da  fahimta dan   a daidai wannan lokacin ina tare da  shi wanda zai saka hannu   "to kagani sai ka  bashi ayi agama komai dan so nake ya fito zuwa jibi dan Allah kasa a kashe wani a madadin falsa .." shikenan  a gama karkaji komai  " zan bada umarnin a shigo da yaron  yanzu ya fada yana  canza magana "you have to understand that you should  know that what someone like us can do  in this land be left ,ya maida  wayar zuwa dayan kunnenshi  tare da shiga karamin parlou'nsa ya  bude window dining area  "nasani ranka ya dade  nasan zaka iya komai murmushi tanko gote yayi" ka kwantar da hankalinka komai zai tafi daidai cikin haka amaryarsa ta shigo  tana taku day day ta nufi inda yake tsaye ta rike hannun daya daga cikin kujerun dake zagaye da dining yana ganinta yayi saurin "cewa  I will call you later  uhm alright "my dear  ta matso jikinsa ya cire wayar a kunneshi yana rungumota jikinsa ya manna mata kiss tayi murmushi "darling  har na fara kewarka da tunanin tsawon lokacin da zaka ɗauka idan ka tafi hong Kong dan Allah kar ka dade  kamar sauran lokuta karka  ɗauki lokaci mai tsawo  bana son ka  dade ka dawo da wuri   duk yau sati ne fa da dawowarka  "uhmmm gaskiya ne amman this time a round just 1 month zanyi na dawo nayi wata uku ban fita kowace kasa ba   "really ?  ya gyada mata kai "idan zan dawo zan biya ta itly  "kai dan Allah tayi maganar a shagwa'be "dole na biya dan akwai abinda zai kai ni daga nan naga bilal  ta soma tafiya tana farinciki  yana biye daita  abaya suka zauna akan farar kujera mai zaman mutun biyu har zai ajiye wayarsa ya tuna bai kira securitys ba ya soma ƙoƙarin kiransu kira ɗaya suka ɗauka "hello sir daga ɓangaren Tanko gote yayi shiru yana tsotsa keya yana ciza baki saboda bai tambayi sunan yaron da aka aiko gurinss ba iska ya furzar yaceb"akwai wani yaro  yana ....
"Okay sir gashi nan ma "yauwa ku barshi ya shigo "okay sir ya katse kiran tare da janyo amaryarsa jikinsa ",zanyi missing din waɗan abubuwan ya kai hannu ya shafo qirjinta bata yi sanya a gwiwa ba ta kai hannunta ta soma wasa da sansar jikinsa kusan minti goma suna rungume da juna wayarsa ta sake ɗauka qara  ya zareta ajikinsa yana ƙoƙarin  d'aga wayar  gabansa yayi wani irin muguwar  faduwa  yayi shiru rike da wayar ya kasa ɗauka babu abinda yake ji sai faduwar gaba.

Saurin mik'ewa yayi yana kallon parlou'n kansa na juyawa a matukar zabure amaryarsa ta mike "what happened ?  "gabana ke fad'uwa da matsanancin karfi "gabanka ke faduwa ta maimaita tana kallonsa" ina jin kamar takun mutane "how is there tayi maganar tana kallon kofar parlou'n  tayi maganar a tsorace ganin haka yasa ya riko hannunta "colm down never mind  "what  do You mean never mind ?  tayi maganar a tsorace "don't leave the parlou "ban fahimceka ba  ? " Ina zuwa  yayi foring head d'inta kiss "i think  I will back don't leave the parlou   ya  juya ta riko hannunsa da sauri  "karki damu zan dawo yanzu ya sake rungumeta ya mannata mata kiss  ita dai a sanyaye ta bishi da kallo "meke faruwa ne haka daga gabansa na faduwa yace na tsaya anan na jirasa zai dawo  tafiya yake gabansa na faduwa ya biyo dogon coridor da zai kai  mutun wata kofa data fuskanci hagu ya fito a hankali yana dube dube har inda wata motar take parke yana dubawa gabansa na faduwa wanda duk sanda yaji haka  yasan akwai wani mummunar abu da zai samesa    cigaba da dube dube yayi  a hankali ya juyo yabi wani hanya stil bai ga kowa ba bai ga komai ba, ya tsaya yana waige waige hagu da  dama sannan ya sake juyawa ya nufi kofar daya biyo "Alhaji tanko gote.........."
yaji sauti daga bayansa cak ya tsaya tare da juyowa gabansa na wani irin dokawa a hankali Jaguwa yake daga kafafunsa "waye kai ? tambaya kake ko neman sani ? "duka ya fada cike da tsoro , jaguwa yayi murmushin  "colm don Tanko gote  zaka san komai cikin second daya yayi mgnr  haɗe da ciro bindigarsa daga maajinta  ya soma  gyarawa  yana kusanto inda tanko gote yake tsaye a matukar tsorace yake kallonsa  da bindigar hannunsa alama su shiga ciki yayi masa babu mutsu ya juya Jaguwa  na biye dashi har suka shiga parlou'nsa na uku ya tsaya " ba wani abu ne ya kawoka ba illa kudin da'aka ...
"Dakata kafin wannan kamar baka ganeni ba ?ya girgiza masa kai "Jaguwa yayi murmushin "daman mutane irinka basa iya gane mutane abinda yafi haka ma zaka iya saboda mutun azzalumi irinka ba lallai ne ya zamanto mara mantuwa ba well ba wannan ne abinda ya kawoni ba shiga ka fito dan zuwa yanzu ka fahimceni "sosai ai idan kudi ne zaka samu har sai kabari ni Dai ka barni da Raina da lafiyata "ban soma wannan aikin dan na dauki ran wani ba sai dai a rashin sani amman   kai wallahi  zan iya daukar naka  take jikin Tanko gote ya sake ɗaukar rawa ....

"   muje inda kudin suke jikinsa na rawa ya nufi wani daki suna shiga sanyi ac ya ratsasu buhu ne cike da kudade  daban daban na kasar  negeria  da kasashen ke tare ka ɗauki duk wanda yayi maka "Jaguwa yayi murmushin  yana shafa qirjinshi da hannu "ai gaba-daya zan wuce dasu dan haka   ka soma ɗauka  daya bayan daya "ka bari na bada umarni  a  kai maka  su cikin motarka  tana ina  "ance maka ni karamin kwaro ne karka bata min lokaci ka soma abinda ya kamata kafin na fasa maka kwakwaluwa .....

Darling's


💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

    WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

https://my.w.tt/lcJskJdtpbb

🅿️09

.....Mamakin jin furucin Jaguwa na karshe  ya cika zuciyar Alh tanko gote  mutumin daya shahara a cikin fadin duniya  da aikata masha'a bangaren neman mata  cin amana  ,makirci, son abun duniya  ba dan bashi dashi ba ,daurawa mara laifi laifi domin bawa mai laifi gsky saboda  abun duniya  ,idan  kana son ka  kasance dan ta'adda  mai lasisi da  neman gindin zama acikin kasar nan  nemi  tanko gote,idan aikinka garkuwa da mutane ne  fayde zama dilan kwaya  da sauransu nemi tanko gote  duk zai tsaya maka asirce kaci karen babu babbaka ko an kamaka zai sa a sakoka cikin kankanin lokaci .............

Duk  wannan mugun aikin daya ɗauki tsawon   shekaru yana aikatawa adalilin  connection din da yake da acikin yan siyasa   babu  wani mutun ko  ɗan fashin da makamin  daya taɓa kawowa  rayuwarsa farmaki  ,
hasalima yana jin  sign dinsu ajikinsa  kafin su karaso gareshi yake maganinsu , sai gashi  yau da ranar Allah dan fashi kwaya daya tal ya farmaki rayuwarsa har yana masa barazana da rayuwarsa ,  jiki a matukar sanyaye  ya soma jan buhun  kudi  jaguwa na gefensa  "idan kayi wata alama da wani zai gane halin da ake ciki  wallahi zan ɗauke numfashinka daga doron kasa sai dai nima a ɗauke nawa numfashin wanda daman ni da wannan shirin na fito mutuwa ko akasin haka ..... "

"Karka damu babu wanda zai fahimci komai ya fada hannusa na karkarwa, kai tsaye bayan but din motar Jaguwa suka nufa ya jefa buhun kudin  da kyar yana haki , haka suka dinga jerewa suna shiga  yana dauko  buhun kudi   har ya kwashe tasssss ya tsaya tare da nad'e  hannunwansa guri daya har lokacin zuciyarsa cike take da mamakin irin gogewa da kwarewar  jaguwa .

Jaguwa ya manna  gun a gefen brain  d'insa  "muje ka kaini gurin yar gaban goshinka  Alh tanko gote ya  kalleshi a  matukar frigice zuciyarsa na dokawa da karfi  "karka taɓa lafiyar iyalina idan wadan nan  kudin basu isheka ba zansa akawo ninkisu yanzu
" yayi kyau shugaban fataken dare sai dai  kar kwakwaluwarka tayi  maka  wanann banzan  tunani dan nasan  daraja da kimar  dan adam ba irinka ba wanɗa  yake  danne hakin dan Adam domin son  duniya , a  hankali ya dinga daga kafafunsa zufa na karyo masa a  gaba-daya sansar  jikinsa yana tunanin "waye shi  wannan  ? "da dukkanin alamun yasan shi farin sani    har suka shigo parlou'n  zuciyarsa na cikin frigici  , yayinda har zuwa  wannan lokacin amaryarsa na tsaye  hankalinta a matukar tashe  tana ganin bindiga a gefen brain din mijinta tayi saurin durkushewa bisa gwiwowinta tana furta "na shiga uku me zan gani haka ni salma ? Alama jaguwa  yayi mata da bindiga take tayi shiru jikinta ya kama  kyarma ..

"kin san me yasa na bukaci wannan azalumin mijin naki  ya kawoni gareki ban bukaci ya kai ni  gungu mattarar tsiya ba ? tayi saurin girgiza masa kanta jikinta na rawa  "saboda nasan kece tauraruwar gidansa da dokarki ake aiwatar da komai na gidan nan  , sai yadda kika so za'a yi dan  tanko gote  mijin tace ne agurinki  sai yadda kikayi dashi "ki faɗa masa kar ya kuskura ya kawo wa aikina hauka , bayan wannan  ya kamata ki san  ko waye wanda ke tsaye a gabanki  duk da idanunki a halin yanzu a makance suke  ,"sunana jaguwa  akaro na farko da wani  a duniya zai  san wani abu daya danganceni sannan ya san sunan dan fashin daya gagarin kasa da yan sanda "

" a wasu shekaru da suka gabata anyi  wani natsatsen yaro wanda ya taso cikin gata da kulawa, yana da mahaifi da mahaifiya da   kane gudu  hudu  namiji daya mata uku , wahalar duniya tayi musu yawa naci ma da kyar suke samu  sai da wannan azzalumin mijin naki yayi nasarar jefa rayuwarsa cikin gararin rayuwar da yasa ya dawo wannan mutumin dake tsaye agabanki , jaguwa ya sake tsuke muryarsa  ya cigaba da magana  "abinda yasa na dan  baki  labari ,mijinki ya cancaci na kashe shi bisa girman laifin da yayi min a shekarun da suka gabata  sai dai na barshi  da halinsa dan hukuncin Allah zai fi akan nawa hukunci ,sai abu na gaba " idan mijinki  yayi  kuskuren ko gigin sako jami'an tsaro ciki aikina  domin yunkurin tona min asiri ko bincike akaina zan.....
da sauri tace" he wont involved the police farinciki ya ziyarci zuciyar jaguwa saboda ya hango firgici da matsanancin tsoro attare daita, yana gama jin abinda tace yace    "shiga muje kou " Alh tanko gote yayi saurin waigowa gefensa inda  Jaguwa ke tsaye fuskarsa da alamun tambaya  "karka ɗauka bansan abinda nake ba ,nasan halin  mutane azzalumai irinku masu bin mutane da bita da kulli ka shiga muje kawai ban gama da kai ba idan kuma  mutsu zaka min   yanzu na harbeka  na harbe  kaina muyi  mutuwar kasko ,babu mutsu  ya shiga gaba jaguwa na biye dashi har cikin  mota ,Jaguwa ya zagaya ya shiga bangaren direba ya tayar ya nufi get ....

Suna karasowa bakin get securities suka tsaida shi  warning  glass din bangaren Alh tanko gote yayi suna ganinsa suka shiga rigerigen kawo gaisuwa cike da girmamawa, daya daga cikinsu ya  bude tafkeken get din estate din jaguwa  ya

Please Login or Register in order to submit comment