Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannunsa ya karasa inda ya ajiye wayarsa ya dauka yana kokarin sakata aljihunsa kira ya shigo ya daga "me kake yi ne har yanzu ?".
Da kyar ya bude baki yace gani nan fitowa yanzu "me ya faru naji muryarka haka jin muryarka ya daga min hankali?".

Ya nufi kofar fita yana cewa "wallahi da ciwon kai na tashi mai tsanani ban kwanta dashi ba amman na tashi dashi "oh sorry my dear ina hally take ?tana bacci ya fada yana shiga dakinsa ya zuge mirrow dinsa wata karamar kofa ta bayyana ya shiga ya dauki bindiga pestol ya soke ajikinsa "kana jina?
"Eh ina jinka ya bashi amsa yana runtse idanunshi "karka fito kayi zamanka a gida ka huta tunda baka da Lfy idan scopion ya dawo daga aiki zan zo da kaina muje hospital a duba min kai wannan ciwon kan yayi yawa "okay !"
“Ni kaina na fara tunanin ganin likita,okay shikenan
Amman ka bar wayarka a kunne bana son na kira naji akashe anas yace "to! ajiye bindigar yayi ya fito ya maida kofar ya rufe ya dawo falo ya kwanta dafe da goshinsa gurin karfe shabiyu saura hally ta tashi ta fara gyara dakinta sannan ta fito zuwa falo domin ta gyara turus tayi sakamakon ganinsa kwance dafe da goshinsa ,da sauri ta karaso gurinsa ta durkusa agabansa ta riko dayan hannunsa cikin nata tana murzawa wani zafi taji ya ratsata ."
Bude idanunshi yayi da kyar yana kallonta “kace zaka fita kuma zaka jima baka dawo ba ?ya lunshe mata ido “kaina ke ciwo bazan iya fita ba “sannu !.”
Ta fada tana dafe masa goshi “ka sha magani ma kuwa ?ya girgiza mata kai alamun a’a ta mike da sauri ta nufi dakinta tana cewa “me yasa zaka zauna baka sha magani ?.”
Yana kwance ta dawo hannunta rike da magani ta shiga kitchen ta dauko ruwan mara sanyi ta fito ta mika masa magani tana rike da goran ruwan ya amsa ya kai bakinsa ta mika masa ruwa tana masa sannu da kyar ya sha magani dan bai son shan magani sannu tayita jera masa tana jin kamar ta maida ciwon kanta ya tashi ya tafi inda zashi ya koma ya kwanta ita kuma ta cigaba da aikinta .”

Da misalin karfe daya daidai na rana sconpio suka fito tare da jaguwa zuwa haraban gidan suna magana kasa kasa wanda duk nacinka baka isa kajiyo me suke cewa ba ,jaguwa ya dafa kafadansa yana kallon shigar jikinsa , manya kaya ne sanye ajikinsa su bama su haske can ba haka zalika ba masu dotti ba , kansa har da rawani wuyansa zagaye da manyan carbi tamkar dai irin shirin da malaman darika suke kafafunsa rufe cikin black shoe’s ,
yadda kafafunsa suke rufe da bakaken takalmin haka jikinsa suke sanye da bakaken kaya rigarsa ce kawai multcolour amman hatta jeans din jikinsa baki ne gefe da gefen west dinsa na makale da bindigar pestol kai tsaye inda machinan aikinsu suke jere jaguwa ya nufa dashi ya damka masa key yana cewa “ka hau wannan .” ya hau wanda jaguwa ya nuna masa yana kokarin ta dashi yaji ya cigaba da magana “ka kula sosai scorpion banason kuskure a aiki sannan ka kula da abun kunnenka daga yadda yake din nan zan dinga jin komai dake tafiya haka zalika zan dinga ganinka ina maka fatan nasara yana rufe bakinsa scorpion ya nufi get yana tsaye agurin mai gadi ya bude masa karamin get ya fita sannan ya juya ya koma ciki hannuwansa duka goye a bayansa.”

Scorpion na fita cid ya kira headquarters na polisawa kai tsaye aka dauka da “hello ! “kana ina dcp ? Okay to kayi hanzari ku isa address din dana tura maka , yanzu haka yaronsa ya fita kuma shi kadansa kamar yadda na sheida maka naji suna tautaunawa, yana sanye cikin fararen kaya shirin malunta “dan allah karka bari mu rasa wannnan damar at least ko mutun daya muyi nasarar kama wa acikinsu .”
“karka damu zamuyi iyakar kokarin mu sannan ka tabbatar duk abinda ka gani ka daukar mana komai da komai akansa da yaransa a wayarka domin itace hujarmu ,da zarar ya shigo hannu sai mun tona masa asiri a idanun duniya ,shi kuma yaronsa idan ya shigo hannumu yaki bamu damar muyi binkice akan mai gidansa harbesa kawai zanyi mu huta.”
cid na katse kiran dcp ya shiga kiran yaransa daya bayan daya kafin kace me sun hadu a wani daki na musamman nan ya shiga basu umarni daman kuma a shiryensu suke kusan atare suka fito suka shiga motocinsu suka fita yayinda scorpion ya isa inda me gidansa ya aikesa cikin nasara ya samu guri nesa kadan da inda aka aikesa yayi parking bisa umarnin ogansa ya sauka akan mashin din ya soma tafiya a natse tamkar mutumin kirki yana jin jaguwa nace masa “karka kuskura ka waiga bayanka cigaba da tafiya kawai domin waigawarka zai sa polisawa dake aiki agurin suyi suspecting dinka sannnan ka fara neman taimako gurin mutanen dake kai kawo agurin .”

Bai yi magana ba ya kebe kansa gefe guda ya zaro daya daga cikin carbuna wuyansa ya soma ja yana motsa bakinsa a hankali yana mikawa mutanen dake kai kawo agurin hannunsa ,nan take mutane suka shiga mamaki ganinsa domin dai baa bara a kofar get din maaikatar hasalima korar masu bara ake agurin amman cikin ikon allah sai gashi shi ko kallonsa da tsigar kora babu wanda yayi ,wasu daga cikin mutane suka fara bashi sadaka yayinda wasu ke wucesa suna ganin wani sadaka zasu bashi bayan shi din ba nakkasashe bane kawai malunta ce tayi masa yawa ,wasu ma ko kallosa basayi ba .
wata mata ya hango sanye cikin doguwar rigar after dress yanayinta tsam bahausheciya tana daf da wucesa ya biyota da sauri yana rokonta “dan allah ki taimaka min da abinda zan ci saboda allah rabona da abinci tun jiya “ta tsaya tana kare masa kallo sannan ta dauke kanta tana duba Jakarta dagowa tayi tana yatsina fuska “nayi niyyar baka amman gsky bani da canji dubu daya ne “ta fada tana kokarin wucesa ya biyo da sauri yana cewa “ina da canji ,ban gane kana da canji ba sai kace dole sai na baka sadaka?” dan allah matsa ka bani guri , ku zauna kuna bara duk zuciyarka ta muta , kalleka fa da kafafunka da komai amman ka zauna kana bara ta wucesa shi daman so yake ya samu yayi kusa da office din zai shiga kuma yayi saa ,a qalla ya kusan mintuna talatin tsaye a kusa da office din alhj madu sannan yajiyo sautin muryar jaguwa ta cikin abun kunnesa “ lokaci yayi da zaka shiga.”

tsam scorpion ya soma tafiya ya nufi kofar office din alhj madu ,cikin saa yayi attacking din PA dinsa shi kadai zaune ta hanyar daura masa bakin bindiga yana cire rawanin kamshi yayi cilli dashi yana tmbyrsa alhj madu ,kai tsaye ya nufi office din alhji madu dashi , a daidai wannan lokacin polisawa suka karaso suka raba kansu kashi kashi kamar yadda mai gidansu ya tsara masu.”
Suna shiga office din alhj madu ya dago a matukar firgice yana kallon kofar shigowa dan haka nan yaji faduwar gaba da ana murda handle din kofar ,
gabansa ya cigaba da faduwa tare yin mutuwar zaune akan kujera scorpion ya tura PA cikin bayi ya kulle sannan yayi facing dinsa yana saita kansa da bindiga jikinsa na rawa yace “karka kasheni ka fada min abinda kake bukata zan baka ? “kai ma ai ka rigada kasan abinda ya kawoni ?
“Ba….babu kudi a…..”
“Gasu can ya nuna masa katuwar jakar ghana most go dake ajiye a kasa sakamakon ganin scorpion a gabansa yana gyara bindiga yana mazurai fuskarsa babu alamun wasa ,jikin alhj madu ban da karkarwa babu abinda yake domin baa taba kawo masa hari ba sai yau ,scorpion ya isa ya bude jakar daloli kudi ya gani makil aciki suna kyali,ya maida zip din jakar ya rufe ya cire manya kayan jikinsa da carbuna wuyansa ya watsar ,ainihin kayansa suka bayyana ya fito da bakar hula aljihun wondonsa ya saka, ya dan durkusa ya ciro safar hannu a gefe da gefe safar kafafunsa ya zira a hannuwansa sannan ya dauki jakar kudin ya janyo kofar ya kulle shima acikin office dinsa sannan ya fito ya soma tafiya a natse .”

polisawan da suke zagaye da gurin gbdy a hankalce suke sai dai sam basu ga wani mai irin shigar da cid ya fada musu ba dan haka dcp yayi kokarin afkawa cikin office din alhj madu da sauri à daidai lokacin da scorpion ke kokarin fitowa sukayi karo da juna har abun kunne scorpion ya cire ya fadi kasa kamar gillamar walkiya jaguwa yaga wulgawar wani da bai san ko waye ba sannan ya daina ganin komai dake faruwa ai kuwa hankalinsa yayi matukar tashi ya zabura ya mike tsaye daga zaune da yake a gaban system qirjinsa na bugawa ya rike kugunsa da hannu daya stil idanushi na kallon computer.”
dcp bai tsaya yabi ta kansa ba ya wucesa da sauri yana cewa “so …sorry.” scorpion yayi saurin yin kasa ya dauki abun kunnensa amman kuma bai yi azancin maida shi kunnesa ba ya cigaba da tafiya cikin sauri rike dashi yana tunanin inda ya yasan wannan fuskar da sukayi karo yanzu ,da wannan tunanin ya karasa ficewa ,dcp na gama shiga office din ya soma jiyo sautin muryar alhj madu yana ihun barawo!!!.
Da sauri dcp yace “yana ina sawunsa muka biyo ?”yanzu yanzu ya fita sanye da bakaken kaya hannunsa rike da ghana ..” ai bai tsaya ya gama jin abinda zai fada ba ya juya da sauri dan tuni kwakwaluwarsa ta hasko masa fuskar mutumin da sukayi karo dashi da zai shigo da wani saurin yake tafiya yana kiran layukan yaransa dake da connecting da wayarsa yana kwatanta masu kamanin scorpion da shigar jikinsa .”


Tun daga nesa suka hango tahowarsa “gashi nan babu tantama shine wannan barawon “daya daga cikin polisawa ya fad’a ahankali ,dan haka suka sake shiri domin farmakansa har ya karasa inda ya ajiye mashin dinsa idanunsu na tsaye kyam akansa yayinda dcp ke tahowa ta baya cikin hanzari ,
scorpion ya hau mashin dinsa tare da ajiye ghana most go a gaban mashin dinsa ya manna abun kunnensa ,nan take jaguwa ya sauke naunayen ajiyar zuciya amman kuma sai yaji wani mummunar faduwar gaba sakamakon mutumin daya hango ta bayansa yana kokarin isa inda yake , har scorpion ya kunna mashin dinsa yaga mutumin da sukayi karo dashi ya bayyana a gabansa bai tsaya wata wata ba ya saita kansa da bindiga sannan ya kai dayan hannunsa ya kashe mashin din ya zare key yana dubansa akaskance .”
shima scorpion kallonsa yake a matukar firgice gabansa na faduwa yayinda polisawa suka fara fitowa daya bayan daya daga maboyarsu suka zagayesa take jikinsa ya kama rawa sai lokaci ya gane waye a gabansa dcp ne agabansa ya kalli gabas da yamma sune ta koina babu inda zai gudu dan haka yayi sounder ya sauko daga kan mashin din tun kafin abashi umarni ya daga hannuwansa duka sama wani wawan tsaki jaguwa yaja yana furta “oh scorpion …….”
Wanda hakan ya janyo hankalinsu jabir zuwa garesa da sauri suka mike suka nufi karamin falon da yake suna kiran sunansa ,shima kokarin fitowa yake hannunsa dauke da computer ya fito a bakin kofa sukaci karo “an kama scorpion “what?”
Suka hada baki gurin fadar haka hankalinsu a matukar tashe ,babban falo suka dawo jaguwa ya ajiye computer suna kallon abinda ke faruwa ,
damke hannunwansa cikin juna jaguwa yayi jikinsa na daukar zafi ,yana kallon polisawa suka tasa keyar scorpion zuwa cikin motarsu byn sun saka masa handcuff ,mutun biyu suka sakashi a tsakiyarsu sauran suka zauna a baya tare da jakar kudi .”

Kai kawo jaguwa ya fara acikin falon dafe da goshinsa yana tunanin mafuta kwakwaluwarsa tashiga tunanin mai zurfi “ya ma akayi suka san da fitar scorpion?yayi wa kansa tmby “Kenan har yanzu suna bibiyarsa?a hankali ya juyo jikinsa na zafi ya tsurawa computer idanunshi , hankalinsa a matukar tashe yake kallon bakin scorpion dake motsi a hankali , sosai ya matso yana son ya fahimci abinda yake fad’a ai kuwa take ya fahimta “boss karka barni haka shine kawai abinda yake fad’a yana sake maimaitawa kana kallonsa kasan yana cikin firgici mai tattare da tashin hankali,”
“Bazan barka ba scorpion duk yadda zan fitar da kai zanyi koda kuwa zan rasa komai nawa da rayuwata né amman zan fito da kai ,yana kallonsa ya lumshe idanunshi alamun ya gamsu da maganarsa,cikin kankanin lokaci suka isa headquarters dashi scorpion ya fito daga cikin mota zuciyarsa cike da kwarin gwiwa,haka suma polisawa suka firfito fuskokinsu kwance da nasara kamo daya daga cikin yaran jaguwa aka nufi wani bangare da scorpion aka ajiyesa wasu polisawa guda biyu suka fara seaching dinsa suka rabashi da wayarsa da bindigarsa da abun kunne wanda hakan ne yasa jaguwa ya daina ganin halin da yake ciki ,yaja tsaki yana kiran aikin banza kawai “.

Ranar karasa yini sukayi cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa kowa ka kalli fuskarsa babu annuri ,kuma shiru har karfe biyar anas bai kira ba shima kuna bai kirasa ba kamar yadda yace ya bar wayarsa a kunne zai kira ,dan haka ya kira layinsa kira daya hally ta dauka tana gaishesa cike da girmamawa,bai amsa ba yace “ina Ana’s?”
“Yana bacci yaya bashi da lfy ko na tashesa ne ?”.
“No karki tashesa but idan shida tayi bai tashi ba ki tashesa kice ya kirani kinji “to !ta fada ya katse kiran yana runtse idanunshi ,kwakwaluwarsa tunani hanyar da zai fito da scorpion take ba tare daya dauki lokaci a hannun polisawa ba.”
daren yayi babu wanda ya runtsa acikinsu har anas dan sunyi waya daga baya kuma ya fada masa komai alokacin yaso zuwa shine ya hanashi hatta hally ta fahimci akwai damuwa sai dai tayi masa tambayar duniya yace babu komai allah allah ya dinga yi gari ya waye ya isa gidan su san yadda zaayi.”

Washegari

A hadadden falon jaguwa zaune wasu mutane suke akan kujera suna fuskantar juna daya sanye da bakaken kaya yayinda dayan ke sanye da fararen kaya  jaguwa na  zaune akan wata karamar kujera ya juya masu baya jikinsa sanye ciki blue black din riga da Wando gbdy yaransa suna tsaye ban da anas bai samu damar karasowa ba ,a hankali daya daga cikin bakin mutane da suke zaune ya fara magana cikin zafin rai "kasan irin hasarar da nayi dalilinka kuwa ?  kasan irin abinda na rasa dalilinka sakarcinka?” ko bakaji ina maka magana ne kayi banza da kanka wai kayi dani ? Jaguwa sam bai juyo ba sai danne danne yake acikin wayarsa zuciya tazo masa wuya damuwa kashi da kashi sun sanyoshi gaba .”
“ban da sakacin banza da rainin hankali irin na......."Ana's wanda ya karaso yanzu sanye da blue jeans da riga ash colour yayi taku daya biyu yana cewa " kai kai kai  !!! Ya fuskanci wanda ke gabansa "da kai nake yin maganata wai meke faruwa ahankali ya juya ya kalli na bayansa ina tambayar wai meke faruwa abani amsa mana.” wai yanzu har kuna da zuciyar da zakuyi mana maganr akan wani abu naku bayan mun sha biya muku buririnkanku lokaci dayawa mun sadaukar da rayukanmu.”

ya juyo ya kalli mai farin kaya "bakasan iyakacin sau nawa bane muke shiga hatsari duk adalilinku ya karasa maganar yana nuna masa kofar fita da d'an yatsansa babu mutsu ya mike tsaye jiki a sanyaye "kunyi kuskure domin lokaci ya rigada ya canza ya kai hannu ya dafa kafafan jaguwa "wai me yake faruwa né ? "Kai kabasu dama su dinga mana magana irin haka inji cewar kamil ya fada yna fuskatar jaguwa ?.
Jubi yace "wadan nan fa costom department ne Kullum kawai matsalar jami'an tsoro costom gashi mu bamu da kowa acikin jami'an tsaro ,acikinmu babu wanda yake da halaka da polisawa sai dai da yarinyar minister  kawai ,shin yana haduwa da minister ne ko kuma da yarinyar minister  kawai , koma dai menene ita kan bata da wani amfani agurinmu ,gashi scorpion ya shiga hannu bamu san a wani hali yaje ciki ba ga wadan nan mayun kudin sunzo karbar kasonsu ,yanzu da me zamuyi amfani mu fito da scorpion “?


“Jaguwa shi ya saba sace yammata ya nuna kwarewa rasa ya sato mana karamar kanwar dcp bincike mu ya nuna wani sati zaa fara bikknta ya karasa maganar yana dariya ,gbdy suka sa dariya banda anas da jaguwa dan ransa a bace yake gbdy suka fita , falon ya saura daga shi sai ana babu wanda yayi mgn acikinsu wayar jaguwa ta soma ringin ya duba tanwer ce yaki dauka ta sake kira yaki dauka cikin haka wayar anas ta fara ringin ya ciro ya duba "tanwer ce ..” ya fada jikinsa a sanyaye “ka rabu da wannan yarinyar abinda nake gudar mata kenan ta kasa fahimta , irin wannan matsalar anas, nifa nasan da rayuwata da nata da kai da hally duk suna cikin hatsari yanzu kuma kaji abinda jubi ya fada ni ne na saba satan yammata " yayi maganar tamkar zai zubar da hawaye “ka manta da maganr jubi ni ban damu da abinda yace ba .
Ya mike daga zaunen da yake ya goya hannunwansa duka a bayansa ya soma zariya acikin falon gumi na karya masa,hankali ya kamo lip’s dinsa na kasa ya ciza da karfi Ana’s ya karaso ya dafashi “dan allah karkasa damuwa aranka hanyar fito da scorpion ya kamata mu fara nema ,”yanzu ba wannan bane a gabana domin kuwa gabadaya nagama tsara komai na fitowars scorpion matsalar dai yarinyar nan tanwer halin zata shiga kawai nake tunani ranar dana shiga hannu .”…


Fatan munyi sallah lafiya allah maimata mana ,allah ya biya mana bukatunmu na alkhairi,allah kuma ya jikan iyayenmu,mu kuma allah ya gafarta mana .”

Mmn sudais



💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert  domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️40

"Ana's yayi shiru yana kallonsa yana nazarin maganarsa "yanzu ba wannan bane a gabana
domin kuwa gabadaya na gama tsara komai na fitowar scorpion matsalar dai yarinyar nan tanwer halin da zata shiga kawai nake tunani ranar dana shiga hannu ."Ya maimaita maganar yafi sau uku acikin ransa yana dubansa tamkar ranar ya fara ganinsa,bama halin da mahaifiyarsa da kannensa zasu shiga ne damuwarsa ba halin da tanwer zata shiga ne yafi d'aga masa hankali ".?"lallai abinda yake gudar masa ne yake shirin faruwa dashi fad'awa cikin makauniyar soyayya ."

nan take shima zuciyarsa ta hasko masa matarsa hally baiwar allah "tabbas shima ita yafi ji da tausayawa ,gara ma tanwer tasan waye jaguwa da alqallarsa  shifa ?".halima bata san komai akansa ba  ko ya zataji idan tasan alqallar mijinta da yayanta "?
"Subhallah ya furta a fili kana ya numfasa yana jin wani tashin hankali na sake mamayesa , jiki a Sanyaye ya soma magana  qirjinsa na dokawa "shiyasa nake gaya maka mu bar sana'ar nan idan ta kama ma sai mu canza gari mu cigaba da rayuwarmu da iyalinmu tunda babu wanda yasan ainihin fuskokinmu "ana wata magana anas kana wata “ yayi mgnr a fusace  wanda a zahiri ake iya gani jijiyon kansa da suka tashi sukayi rudu rudu "kana ganin barin wannan sana'ar kai tsaye ko canza gari abu ne mai sauki .?"bafa abu ne mai sauki ba  kamar yadda hasashenka yake hango maka   ."



Dukkaninsu shiru sukayi suna duban juna suna tunani me zurfi kafin daga baya anas yaja numfashi da karfi ya sauke "to yanzu taya ka tsara fito da scorpion ? hanya daya ce na tsara ,rike wuyan dcp ,"taya zaka samu damar isa inda yake bare ka rike masa wuya ?"Ka kwantar da hankalinka kana nan   zan fara aiwatar da komai amman ni kadai zanje gurinsa ,"bazan iya barinka kaje kai kadai ba saboda ina matukar bukatarka araye banason kayi kasadar daka saba akanmu,idan kuma lallai sai kayi kasadar sai dai muje tare amman bazan iya barinka kaje kai daya ba ." ya karashe maganar cike da rauni ."na sani ana's kana gudun wani abu ya sameni kamar  yadda nima  ina jin tsoron abinda zai sameka,abinda zai sameka idan ina da dama kafin  ya sameka  ya fara samuna  bare  kuma babu abinda zai samemu daga ni har kai saboda bamu  rayu dan mu  matu a hannun makiyanmu  ba ,dan haka ka kwantar da hankalinka anas babu abinda zai faru dani  zan tafi kuma ni kadai , Kai dai kayi min addua kawai  shine abinda nafi bukata daga gareka ."

"Yaushe zaka tafi "?.

"May be yau ko gobe at anytime dai zan iya isa garesa idan shirina ya kammala ".

anas ya sake yin shiru tare da zuba masa rinannun idanunshi  ,can yace "nifa  ina tunanin kamar akwai masu bibiyarmu dan nayi mamakin yadda akayi dcp yasan da fitar scorpion"?"Eh nima nayi tunanin haka sai dai na kasa tsaida zuciyata akan kowa acikinmu kar nayi kuskuren da nayi a watannin baya wanda hakan yana cikin dalilin da yasa su jubi suke mana wani duba ."Haka ne kuma gara ma da baka ce musu komai ba amman ni kuma a tunanina sai ina ganin kamar aliyu ne ."shiru jaguwa yayi yana tauna lips dinsa da karfi yana nazarin maganar anas "zuciyata ta rigada ya yarda dashi anas bana tunanin aliyu nada saka hannu acikin abinda ya faru ".
"me yasa ma zakayi tunanin haka akansa ? sam sam bama zai ta'ba yi min haka ba ,yaron dana daukesa tamkar jinina na 'yanta shi daga wahala zuwa dadi ,kai kasan irin abinda nayi facing kafin na samarwa aliyu aiki a ma'aikatar kudi ,to me yasa zakayi tunanin zai min haka ?."

Anas yayi shiru yana cigaba da dubansa batare daya ce komai ba "Karka manta aliyu baya tare damu na tsawon lokaci sannan har ya bar gidan nan bai san sana'ar mu ba ,bugu da qari bashi da app dinmu da muke ganin komai da sautin muryar  juna a duk inda muke yayi maganar yana zagaye anas ".
"shi kansa anas tunani me zurfi yake sosai yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa kanshi ne ya kulle  har  yayi wannan tunani domin ya rasa wa zai zarga da munafuntarsu ,a hankali jaguwa ya kai hannunsa ya dafa kafadan anas tare da tsayawa cak yana dan jin tsoron faruwar abinda Ana's din yayi tunani akai ,hakan fa zai iya faruwa ko  anas ? Yayiwa anas da kwakwaluwarsa tambaya".

"A wannan zamanin mutane sun zama abun tsoro cin amana ne qarara ke zagayedamu bamu sani ba , babu abinda mutane bazasu iya zama ba ,ko su canza akowani lokaci , wadan da muka taimakawa a karshe  zasu iya zama silar fadawarmu halaka ,kai kasan wannan aikin da muke yi baya bukatar yarda da mutane ,lallai a nemoshi a tunhumesa yanayinsa

Please Login or Register in order to submit comment