Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

san zaka shiga damuwa ba ,amman kuma tunda baka saba ba me zai sakaka ka shiga damuwa har kayi kewar rashina ya waigo cikin idanunshi ta hango bacin rai sosai da furucinta ya dan girgiza kai “yanzu abinda kika fada kin kyauta ? Tai shiru kawai bai kara cewa komai ba ta danyi tunani maganar data sanar masa“amman kuma tunda baka saba ba me zai sakaka ka shiga damuwa har kayi kewar rashina ta danyi murmushi ganin bata fadi abinda zai bata masa rai ba shiru ta cigaba da yi,ya tsura mata ido “kin kyauta abinda kika fada min hakan ya nuna baki yarda dani ba sannan baki damu dani ba bakya kwadayin kasancewa dani “?
Yanzu kam maganar tafi karfinta shiru tayi kunyarsa ta addabi zuciyarta sai ta dan bata rai alamun tashin hankali ta dan janye jikinta daga nashi ya dan yi murmushi yana kare mata kallo “kin canza fuska sbd baki qaunata ko ?ta danyi dim “me yasa zakace hk tay mgnr muryata na rawa ?”sbd kin gujeni a ranar dayafi dacewa ki kusanceni ta sauke idanunta kasa bata ce komai ba ya sake maimata abinda ya fada hakan yasa tace “nima fa idan ka lura bani da laifi banyi da wata manufa ba ya kai hannu ya shafa qirjinta abinda yasa ta zabura kenan da sauri murmushi yayi “lallai kina da aiki agabanki ya matso sosai allah ya taimaketa wayarsa ta soma ringing ya tashi tsaye cikin jan tsaki da damuwa ya nufi inda ya hango ta yana dubawa sunan jaguwa yagani yana yawo akan screen din wayar nan take ya saki fuska ya dauka “suka gaisa jaguwa na kokarin neman gurin zama a parlaur ,ka fito ina jiranka a parlour .
ya kalli hally dake binsa da kallo sannan yace okay ya fita zuwa falon yana zaune anas ya danyi murmushi yace “ya haka da sanyin Safiya karka manta kai fa sirikina ne ya kamata ka dinga neman izini tun daga waje kafin ka shigo gidan nan ?”
Ya dan yi murmushi yana sosa keya “haba anas Kmr a film?anas ya kallesa “Au haba ko ? Kai dan allah ka dame ni ina hallay ? murmushi anas yayi “na cinye ta,kai ka fara wannan danyen aiki ka dai ci ka rage ta shine zaman lafiyarka suka sa dry gbdy .
“wallahi jiya na kasa bacci sbd tausayinta ,au a she babu dadi kake cin tanwer kuma kaki aurenta ? yayi shiru yana kallon tsakiyar kafet din falon tausayin tanwer ya kamashi duk kwanakin nan tana ransa cike da matsanamciyar shaawarta dan duk sanda ya tuna da kayan marmarinta hankalinsa tashi yake jira yake ya gama da komai na bikin nan ya ganta
yasan itama tayi kewarsa ta dai kyalesa ne taga iya gudun ruwansa.
“ina hally anas na damu nasan halin da take ciki ?tana daki cikin koshin lafiya hankalinsa bai kwanta ba sai da anas ya tashi ya kirata ta fito ya ganta ras babu wata alamun damuwa ko ciwo sannan hankalinsa ya kwanta ta durkusa har kasa ta gaisa “ina kwanta yaya ? .
“Kin tashi lafiya auta ? lafiya yaya ta fada tana sunkuyar da kai yace “ga kular abinci can akan dining daga ammi anas yayi murmshi yace “allah sarki ammi allah saka miki da alkhairi hally takarasa kitchen ta dauko plet da spoon guda biyu ta dawo ta zuba musu abincin ta ajiye musu ta koma ta bude fridge babu abinda babu na drks ta dauko energy drkns guda biyu dan tasan yayanta na matukar son shi ta ajiye masu ta wuce da kular dakinta .”
“Adnan yasu kamil ? suna gida “Me yasa baku zo tare ba ? “Kai dai ka samu natsuwa tukun shi aure fa da kake ganinsa ba abun wasa bane karka manta alqallarmu yana da kyau gida ka da iyalinka su zamo asirance .

“sai abu na gaba bazan gaji da fada maka ba kayi hakuri da hally nasan zaka fuskanci abubuwa masu tattate da kuruciya atare daita sabanin matan da kayi muamula dasu “.Wallahi haka ne dan ta gwada min kuruciya kiri kiri yarinyar nan ta rufe min kofa jiya case din muke yi kiranka ya shigo ka duba min an daura min aure da matar da nake so nake muradi duk na danawa zuwanta sai kuma ranar tazo ta wargazamin shiri ka duba kagani kullum bani da mafarkin daya wuce aure dana hadu daita mafarkina itace tunanina son ganinta kadai ya kan sa na rasa sukuni ya runtse ido ya dan já jiki ya koma kan kujera kwanta ya kasa cigaba da cin abinci .
jaguwa yay murmushi ka gamawa mutane kurin gauraye kai ma gashi har yanzu a layinmu kake wallahi su jubi najin wannan sai sun tasaka gb da dariya sun jima suna hira ya tashi tsaye anas ya shiga ya kira hally sannan ya nufi hanyar waje jaguwa ya kalleta “hope babu wata matsala ?babu komai yaya .“Alhamdullahi ki sanyawa zuciyarki hakuri Kinsan gidan aure gidan zaman lafia ne da hakuri ,Jin dadi wani Abu ne da yake zuwa babu Kuma babu tabbas din zuwansa iyayen mu ba Wani dadi sukeji ba arayuwar aure su amma zaman lafia da hakuri yasa mutuwa ce ta rabasu kiyi duk abinda mijinki ya umarceki sabanin haka tsinuwar malaiku ne ,tunda ya fara magana kanta ke sunkuye akasa “ni zan wuce zan kawo miki shafiq wani sati inshaallahu to yaya na gode sosai allah qara girma allah kuma ya tsare mana kai ,”Ameen ya fada yana sa kai ya fice.
Aharaban gidan ya iske anas tsaye ,ya bude motarsa yana kokarin shiga “karka yarda naga kafafunka a waje ko kace zakazo gurin mu ka zauna kaci amarcinka har sai mun nemeka sai an jima ya fada yana shigewa ya tada mota ya wuce.
shi kuma anas ya koma cikin gida yana shiga falon yaji motsinta a kitchen dan haka ya karasa ya tsaya a bakin kofar kitchen din yana kallonta tana wanke plet din da sukai amfani dashi yana tsaye har ta gama ta goge hannunta sai dai ta kasa motsa jikinta da zumar barin kitchen din saboda yayi bake bake ya rungumee hannuwansa akirji yana kallonta a ranta tace “wannan kallon maitan da yake min yana matukar daga min hankali ta juya masa baya tana kallon wani bangare a natse ya sauke hannuwansa ya tako zuwa inda take sam bataji motsinsa ba sai saukar laulausan tafin hannunsa taji a kugunta a matukar tsorace ta zabura ta waigo aiko cikin sautsayi hannunta ya bugi glass cup yayi tsalle ya fadi akan tays ya fashe a daidai gefen kafarta cikin tsananin tashin hankali ya tsuke fuskarsa yana kallonta jikinta har wani rawa yake itama shi take kallo ido cikin ido suke kallon juna yadda ya kasa dauke idanunshi akanta cikin damuwa haka itama ta kasa dauke idanunta cikin tsoro .
ganin yaki dauke idanunshi, ta nemi gurin kallo tuni kanta yayi kasa tana kallon kasan kitchen “kayi hakuri ,da akayi me kenan ?”
Ya tambayeta yana kallonta tun daga kasanta har sama “uhmmm na …..”sai kuma tayi shiru ta kasa karasa mgnr domin rasa abinda zatace dan tasan bata kyauta ba “tsoro ma yasa kin kasa yin magana kawai saboda kin tsanane “.
Ta dago idanunta ta dube shi Kmr zatai kuka “ni na tsaneka ?allah ya tsareni tayi mgnr tana wasa da yatsun hannunta yayi dan gudun murmushi “idan ba haka ba mai zai sa ki dinga guduna daga jin na tabaki kinyi yunkurin gudu dan kawai ki jazamin yanzu da glass din akafarki ya sauka me kike expecting?
tayi shiru kawai domin ganin yafita gsky ya kai hannu ya riko ya zagayo daita ta gefen inda babu kwalbar ya mannata ajikinsa yana sauke numfashi “haba my princess me zai sa ki dinga guduna nifa mijinki né na sunnah idan baki tabani ba ni bai kamata ace in na kawo kaina ki dinga yunkurin guduwa ba komai zan miki ke din tawa ce bata kowa ba still bata ce komai ba ,ta dan tayi karfin halin mgn nifa ba gudunka nake yi ba kai kasan bazan gujeka ba abun nan ne dai kawai nake ….”
“Wani abu kenan ?
Tayi shiru wannan abu yafi karfin bakinta sarai ya fahimceta “ ki dan rage tsoron nan dan zai wahalar dani ya karasa mgnr yana tafiya daita zuwa falo ya zauna akan kujera mai zaman mutun uku ya kwanto daita jikinsa fuskarsu daf da juna yana shafa bayanta yana shakar numfashinta da kamshinta sosai tayi luf ajikinsa tai zurfi cikin tunani .

ta hanyar tsotsan bakinta ya dawo daita tunaninta “in har kina guduna hakan na nuna rashin damuwar rashina atare dake tô kuma zuciyata taza yarda babu soyayyata acikin ranki ta girgiza masa kai “haba ya anas allah ba haka bane ba kuma bana damuwa da kai bane , ka fahimceni ina jin tsoro ne allah ka tmbyi ammi ni daman can abu kankani ke firgitani da kaina ma tsorata kaina nake ya muskuta ya sake motsawa ya shige mata har tana jin harbawar jijiyarsa hakan yasa ta kawar da kanta gefe tana cewa kayi hakuri “daman kullum cikin hakuri nake my princess amman ina son ki fahimci ina cikin tsananin bukatarki ina son naga alamun kina bukatata wannan tsoron da nake gani a fuskarki yana maseefar daga min hankali cike da wayo da dabara irin na maza ya dinga romamcing dinta wannan abu da yake mata yasa ta sake lula
duniyar tunaninsa .”
Yau kwanan hally shabiyar agidan wadan kwanakin tayi su cikin zullumi da tsananin tsoron da ta kasa fiddashi bare ta bari wani abu ya shiga tsakninsu da Ana’s , shima bai sake nuna mata damuwarsa ba ya cigaba da tsabgoginsa dan har ya soma fita duk da bai samu sex ba ya samu kwanciyar hankali tunda yana tare da matarsa yana sonta kuma dukkanin alamu sun nuna tana son shi dan tana bashi kulawa gurin ci da tsaftace masa muhalinsa da jikinta domin kuwa tun data zo gidan bai taba jin wani abu byn kamshi ajikinta ba haka ma gidan matsalar dai rashin samun sex ne shima zai cigaba da lallabata yana ma sa rai nan kusa zai amshi abu mai mahimanci agurinta.”

******

Haddden gidan rawa né mai hade da gurin shakatawa acikin Ikoyi hotel ,duk da dare ne amman gurin tamkar safiya ne agurin sakamakon hasken fitilun da suka haskaka gurin , guri ne na sai wane da wane da manya kadangarun bariki wadan da suka amsa sunansu,matan bariki ne kala dabam dabam kowacce da shiga ta tsiraci yayinda wasu ke rawa a tskiyar maza wasu kuma suna zaune akan kujeru na alfarma ciki kuwa har da babban aminin tanko gote wanda ya kasance dillalin koken da abokan alqallarsa mutun uku suna zaune daga baya gurin shakawatar suna tautaunawa akan business dinsu .”gabansu makeken table ne wanda ke dauke da ruwa da manya drinks masu tsada .”
alhj tajjudeen ya kalli abokin alqallarsa dake sanye da complete din bakajen Kaya “Kilo arbain fa kace idan kana bukata zan maka rangi kilo goma daga ciki , ya numfasa sannan yace ina kayan suke?suna border idiroko ya bashi amsa yana daukar kwalbar wine mai dauke da tattaccen ruwan inibi ya bude ya tsiyaya a glass cup yana kokarin kaiwa bakinsa alhji tajjudini yace “cinikin zai yuwu sai dai mai dauko min kayan ne matsala saboda sai mun samu wanda muka yarda dashi” karka damu da wanda zai fito maka dashi inji cikon na hudu ya cigaba da mgn “akwai wanda zai yi alqallar cikin sauki .
“waye shi ? ya tambayesa yana tsaresa da jajayen idanunshi “Jaguwa!
“Jaguwa ?
ya furta sunan ahankali yana tunani inda yasan sunan, idan kuma bai san sunan ba to lallai ya taba jinsa kuma abakin takon gate. “jaguwa ya kasance babban dan fashi da makami ne a kasar nan sannnan yana da basera da zai iya shigo maka da wannnan kayan cikin sauki batare da wata matsalar ba .“Kana ganin zai iya “?
“shine kawai zai iya kawo maka akoda yaushe cikin aiki yake kuma sam bashi da tsoro ko tunanin abinda gwanaty zatayi “well done haka nake son mutun mara tsoro ,yanzu ya zaa yi na samu ganawa dashi “? “ ina da wani abokina yana da number na hannun damansa wanda ya kasance babban amininsa “ tô shikenan ka nemishi ka fada masa sannan kayi masa biya mai kyau, ka dai san hatsarin aikin namu akwai hatsari karka biyasa kudi kadan “
“Haka ne sai dai zan kara tabbatar maka ka sa aranka babu wani matsala zan hadu da abokina gobe zamuyi mgn kuma a goben zaa kirasa ya karasa maganar tare da mikewa yayi masa sallama yana tafiya alhj tajjudini ya mike tsaye shina jami’an tsaron dake tare dashi ya mike shima mutun dayan daya saura ya mike suka jera suna magana wacce zaka dauka ta arziki ce nan kuwa ta kwaya ce.”


Anas na zaune a babban falo jaguwa wanda shigowarsa kenan aka kira layinsa yana amsa waya jaguwa da jubi da kamil har ma da jabir suka shigo suka fara neman gurin zama “lallai muna yi amman bama yin wannna alqallar yana gama fadar haka ya katse kiran “meye shi bama yi ?
“Alqallar safarar miyagun kwayoyo bai yi magana ba ya daura kafarsa kan daya yana girgizawa jubi ya kallesa yace “wannnna ai ba komai bane me zai hana muyi ana samu kudi sosai ? sai lokacin jaguwa yayi magana rai a bace kai kake ganin ba komai bane amman mu agurina komai ne har gara fashi da wannan sanar “ka daina cewa haka muna aiki dan mu samu kudi kaga bamu da choice akan kowani irin aiki da zaa kawo inji cewar kamil “nima shine abinda nagani tunda mun sadaukar da rayukanmu me kuma yayi saura? jaguwa ya cire kafarsa akan dayar ya fuskancesu gbdy “a yanzu zaku iya fadar komai amman me yasa da police suka farmaki rayuwarmu a wancan ranar abuja kuka shiga damuwa da tashin hankali tunda kusan kun sadsukar da rayukanku“?
Shiru sukayi babu wanda ya sake cewa uffan “kuna son zama dani ya zama dole kubi abinda nake só ban yarda ba sannan ban amince ba duk kuma wanda yayi kokarin yin wannan aikin abayana zai sha mamaki.”har gama Babu wanda ya sake cewa komai anas ya lumshe idanunshi dan dadin abinda ya fada wannan shine karo na biyu daya burgesa a rayuwarsa “




Mmm sudais



💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️35

………Alhaji tajjudeeni ya dauki sama da awa daya zaune kwakwaluwarsa na mamakin maganar da yaronsa ajuwon ya kawo masa akan tautaunarwasu da jaguwa bayan sunyi waya dana hannun damarsa babu nasara suka tunkaresa kai tsaye shima dai maganar daya ce ta shiga tsakaninsu dashi basa yin wannan alqallar ,sai daya sake yiwa yaronsa duban tsanake sannan ya numfasa yace “ka sheida masa aikina zai yi da har ya tsaya maka taurin kai ?
“Tabbas ya sani domin kuwa nayi masa bayaninka dalla dalla da irin matsayi da karfin ikon fada aji da kake dashi a garin nan ,amman isa da izzarsa suka rufe masa idanu har yana cewa babu ruwansa da wani matsayi da karfin ikonka ,“wannan ikon da isan sai dai kayi wa karnunka yaranka da kake iko akansu amman shi babu wanda ya isa yayi masa dole akan aikinsa “.

nan take zuciyar alhj tajudeeni ta dagule ta soma masa ciwo yaji kamar ta kama da wuta tsabar bakinciki ,ya tattara kan takardun dake gabansa da sauran kayayyakin da yake aiki akansu ya ajiyesu amaajiyarsu sannan ya mike tsaye ya zagayo ya bar kan kujerarsa ya fara zariya acikin office dinsa goye da hannuwansa duka a bayansa yana sake jin mamakin jaguwa .”
cak yaja ya tsaya yana fuskarta ajuwon tamkar shine jaguwa sannan yaja wani wawan tsaki tare da kai hannu ya daki kan makeken table din dake office din “lallai ya kamata naga wannan tantirin yaron yana gama fadar haka ya dauki manya wayoyinsa guda biyu ya nufi hanyar fita ajuwon ya biyo shi da sauri yana masa magana cikin tsananin tashin hankali “shi fa wannan ba kamar sauran mutanen da muka saba mu’amula dasu bane ,shi mutun ne da yasan abinda yake , mutun ne da idanunsa suke a bude tunda ya nuna bazai yi aikin nan ba kawai aganina gara a hakura dan…”
“Baza’a hakura ba duk abinda ka lissafa kai ka san shi ,ni bansan haka ba baya ga karfin ikona da ikon fada aji da nake dashi sautin furucin alhji tajudeeni kenan wanda yasa ajuwon ya katse maganarsa da sauri ya cigaba da binsa yana cewa “sorry sir !.
kai tsaye haraban companie dinsa TGI GROUP ya fito yana kiran number direbansa wanda shi tuni tun fitowarsa ya zabura ya mike ya soma kokarin karasowa inda kafin ya karaso escourt dinsa sun zagayesa rike da bindigu ,daya daga cikinsu ya bude masa gidan baya ya shiga ya zauna yana jin tuttukin bakin ciki acikin zuciyarsa a fusace ya bawa escort dinsa umarnin karsu biyosa .”
ajuwon ya zagaya ya bude gaban mota ya shiga ya zauna a lokacin da direba ya shiga har ya tada mota yana cewa ranka shi dade ina muka nufa?
“Ka fada masa inda zamu alhj tajuddeeni ya fada a fusace yana kallon wani gefe ,allah allah yake kwayar idanunshi ta sauka akan jaguwa da dan iskan na hannun damarsa zai nuna musu karfin ikonsa ,zai nuna masu yadda ake saka mutu yayi abinda bai yi niyya ba sai dan karfin iko ,zan nuna masu isar da nake dashi da karfin iko da fada ajin da nake dashi a garin nan .”yayi maganar aransa yana jijiga kafarsa daya.

a hankali ajuwon yake direct din direba har suka karaso igando tun daga nesa ya nuna masa gidan suna gama isa bakin tangamemen get din gidan ya tsaya tare da yin hon ,mai gadi ya mike da sauri ya leka ta karamin hujin get ganin bai san motar ba ya rufe ya fito gbdy alokacin har ajuwon ya fito daga cikin mota ya mika masa hannu shima mai gadi ya mika masa hannu suka gaisa “dan allah ko jaguwa yana around“.?
“Eh yana nan sai dai bai sheida min cewar wani zai zo nemansa ba amman zaku iya kiransa idan yasan da zuwanku zai kirani,“no ka bari mu shiga da motar ciki sai kayi mana iso gurinsa “A’a bari dai na fara sheida masa idan ya amince babu matsala sai ku shigo din wa zance ?.
ajuwon da maganar mai gadi ta bata masa rai ya dai daure ya motsa bakinsa da kyar“kace masa ajuwon ne mu zo ne tare da alhji tajudeeni“to shikenan ka bani minti biyar zan dawo yanzu mai gadi ya juya da sauri ya koma ciki shi kuma ajuwon ya koma jikin mota ya tsaya rungume da hannunwansa alhji tajudeeni yayi wani glass din bangaren da yake zaune “tsayuwar me mukeyi anan ?.
“Wai sai ya nemi izininsa sannan zai bari mu shiga “ ya kalli get din gidan yanawa gidan wani irin kallon tsana sannan yace “wa dan fashin yake da wannan matsayin ?ai fa ya wuce duk wani tunanin mutane gagara badau ne dan dai bakasan shi bane shiyasa amman idan kana jin oba loud ,Ijile , jagu…..“.
tsakin da alhji tajudeeni yaja yasa yayi shiru yana kallon wani gefe yana dariyar mugunta a ransa yace “kadan ka gani yau dai matsayinku yazo inda bashi da amfani.”

mai gadi bai dauki lokaci ba ya dawo yana cewa “wai yace ku shigo amman banda motar ku “.
ajuwon ya sheidawa alhji tajudeeni abinda jaguwa ya fada nan ya sake shiga tashin hankali matuka har ya shigo cikin hadadden falon da’akayi musu masauki mamaki yake .parlour yayi shiru kamar yadda alhj tajudeeni da ajuwon sukayi sai dai idanunsu na aikin karewa falon kallo ne komai tsaf sannan kuma a tsaftacce a tsare ,ahankali suka fara jiyo kamshin dadaddan turare na kamfanin flower mai dadin kamshi a natse alhji tajudeeni ya waigo idanunshi zuwa dogon koridor dake gefensa da jaguwa idanunsa suka fara yin tozali cikin wando da rigar shan iska mai hannun singlet mai azabar kyau .”
anatse ya cigaba da taku cikin isar nan nashi yayinda abokansa ke biye dashi kowannensu cikin kanana kaya kallonsa yake har sanda ya karaso ya samu guri ya zauna ya daura kafarsa daya akan daya yana girgiza wa haka ma abokansa banda anas suka yiwa kansu gurin zama eku ya karaso gabansa cike da girmamawa ya ajiye wayoyinsa akan hannun kujerar da yake zaune sannna ya koma cikin yan’uwansa suka tsaya rungume da hannunwansu akirji .”
Shiru babu wanda yayi magana acikinsu hakan ya tabbatarwa alhji tajudeeni lallai yana da izar da aka fada masa yana daita ,kiran daya shigo wayoyinsa ne ya katse masa zance zucin da yake anas ne dan haka yayi hanzari ya daga dan tun safe bai ji sautin muryarsa ba kuma ya kirasa bai shiga ba “anas ina ka shiga ne nayita kiran wayarka bata shiga ?.”
“subhallah ya fada wanda hakan ya janyo hankular sauran abokansa gbd suka tattara hankalinsu da natsuwarsu garesa “okay allah ya baka lafiya hope kasha magani? Okay shikenan sai ka shigo yana gama wayar ya katse ya kai hannu ya zaro bindiga akarkashin kujerar da yake zaune ya rike yana kallonta yana shafawa still bai ce komai ba .”
da idanu yayiwa sky alamar ya kunna masa tv ya karasa da hanzari ya kunna ya dauko masa fear less mai sanyi ya ajiye akan karamin table ya janyo gabansa ya koma matsayarsa ya kame .
Jaguwa ya gyara zama ya fuskanci tv yayi kamar bai san da zaman wasu halittun mutane agurin ba har lokacin da anas ya karaso cikin shiga ta kamala ya mika musu hannu d’aya bayan d’aya sannan ya samu guri kusa da jaguwa ya zauna suka kalli juna ya kai hannu ya shafa wuyansa yaji zafi sosai alamun baya jin dadi “kaji abinda naji kuwa ajikinka anas ?jikinka kamar garwashin wuta sky kawo masa magani ya sha dan da alamun bai sha ba”.
Sky ya juya da sauri ya bar gurin “nan su jubi suka fahimci shine bashi da lafiya gbdynsu suka masa sannu ya amsa yana dafe kansa dake masa mugun sara sannan suka sake maida hankalinsu akan wayoyinsu yayinda alhji tajudeeni ya maida hankalinsa kacokan akansu duk ya qagu jaguwa bai masa mgn ba gbdy sai yaji ya munzanta agurin har yayi daya sanin zuwa ajuwon ya kai bakinsa daidai kunnensa yayi masa magana cikin rada “wannan daya shigo yanzu shine anas na hannun damarsa kai kawai ya gyada alamun ya fahimta .”sky ya dawo hannunsa rike da magani da ruwan roba ya mikawa anas cike da girmamawa anas ya mika hannunsa ya amsa yana masa godiya sannan ya sha, jaguwa ya sauke numfashi yana sake masa sannu idan bakaji sauki ba sai muje gurin sadiq ya duba min kai “inshaallahu ma zanji sauki daman rashin ban sha magani ba .”


Gyaran murya alhj tajudeeni yayi yace “jaguwa kake ko wa kana kallon mutane amman kayi kamar baka san da zama na ba sai faman uzurin gabanka kake ?jaguwa bai dago ya kallesa ba yace “kar nayi uzurin gabana acikin gidana abun ikona? “ ka kuwa san ko waye zaune a gabanka ? sai lokacin

Please Login or Register in order to submit comment